Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka suka yi Oder Julof na indomie wadda ta sha ƙwai, sai naman kaza da kuma drinks, rabon da Meera ta ci naman Kaza har ta mance, ai kuwa ta zage damtse ta ci har ta ture, Najmeer dai sai kallonta take tana murmushi.


Ƙarfe sha ɗaya ta yi musu ne a bakin Clup ɗin, tun daga waje ka ke jin ƙarar sauti na tashi, tabbas gurin ya tsaru wanda ƙarya ne kaga ɗiyan talakawa a nan, ido Meera ta waro da mugun firgici bakinta na rawa take nuna sunan Clup ɗin "Soultan Clup......."


"Yes Soultan Clup, wani abun ne ya faru?".

Najmeer ta tambaya.

Meera da duka ta daburce ta ce "Kin san waye Sultan kuwa, kin san waye Ubansa, kin san waye shi kuwa?"

Meera ta jero mata duk wannan tambayoyin a lokaci ɗaya tana ƙoƙarin komawa da baya, a fusace Najmeer ta damƙo hannunta a lokacin idanunta sun koma dark blue, gaba ɗaya farin idonta ya ɓace, cikin yarda da kai ce "Meera wannan ba shine lokaci na farko da na taɓa zuwa ba, asalima abokin me Clup ɗin muna shiri da shi sosai, me Clup ɗin ne kawai ban taɓa gani ba kuma ban san shi ba"

Ajiyar zuciya Meera ta sauke tana mai kawai da kai gefe ganin yanda idon Najmeer ya canja, ba tare da fargabar komi ba suka shige, cike da ƙasaita Najmeer ke taka steps kamar yanda ta saba.


Ba ƙaramin tsaruwa Clup ɗin ya yi ba, daga ƙofar shiga wasu manya manyan majiya ƙarfi ne suka nufo su, amma suna ganin Najmeer suka basu hanya cikin girmamawa har ma ɗayan na faɗin "Allah ya ja da ran Shalelen Alhazawa, ke ba sa'arsu ba ce ta manya ce, ke ɗin tauraruwa ce me haskaka duk wanda ya yi arba da ke"

Jin yanda ake zuba mata kirari ne ya ƙara ba Meera mamaki, Najmeer kuwa ta ciro kuɗaɗe ƴan dubu-dubu ta fara zuba musu, nan fa kirari ya ƙara yawa har mutanen da ke ciki suna jin yanda ake koɗata, hakan ya ƙara tabbatar musu cewa Shalele ta shigo, cikin sauri Majeed ya fito wanjen dan ganema idanunsa, ai kuwa ya yi arba da ita, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ƙaraso suka rungume juna tare da kashe hannu, "Hi Shalele, gaskiya mun yi kewa sosai, ni na tabbata za ki shigo yau shiyasa ma na yiwa Oga na arbishir da samunki" Wani irin fari da ido ta yi tana mai faɗin "Waye kuma wannan da ba zai iya zuwa da kansa ba har sai ya turo ka?"

"Friend ɗina ne kuma shine me wannan Clup ɗin".

"Friend ɗinka fa ka ce? kaga na yi kama da wadda zata yi harka da low class masu irin shekarunka......"

Saurin rufe mata baki Majeed ya yi "Hold on Shalele dan Allah kar ki jaza mana, kin san waye Sultan kuwa? wallahi ko ba ki amince da shi ba zai iya sa ki dole kuma babu abin da za'a iya a garinnan" Ran Najmeer ne ya mugun ɓaci jin abin da Majeed ke faɗa "Toh wallahi banga wanda ya isa ya sa na tarbi abokin naka ba, idan kuwa akwai shi sai ka kawo na gani" Ta ƙarasa maganar tana shigewa daga ciki.


Jikin Meera na rawa ta kalli Majeed "Dan Allah ina Sultan ɗin ne? nikam zan koma gida dan baza ta jaza mun ba"

Ƴar dariya Majeed ya yi ganin tsananin tsoron Sultan kan fuskar Meera.

"Ai be ƙaraso ba, a tare muka fito amma ya tsaya wani gurin, na tabbata duk inda yake yana kan hanya a yanzu......" Majeed be gama rufe baki ba gate Man ya wangame gate.


Wata farar Mota ce a gaba bugagga wadda sai ƴaƴan manya za su iya shigarta, a bayanta motoci tara ne masu jahilin kyau, jiniya kawai ke tashi har suka gama shigowa daga ciki, duk mutanen da ke cikin Clup ɗin fitowa suka yi dan sun san cewa tabbas Sultan ne, kuma idan har ya zo gurin kowa fita yake sai ya fara shiga kafin mutane su shigo daga baya.


Sai da aka gama fitowa amma banda Najmeer wadda ke zaune kan wata arniyar kujera me kafurin kyau da tsada wadda aka aje domin zuwan Sultan.


A hankali Meera ta taɓa Majeed tana faɗin "Wai ina Najmeer ɗin ne? nifa banga fitowarta ba" Zaro ido Majeed ya yi ganin da gaske Najmeer bata fito ba, daidai lokacin da Driver ya buɗewa Sultan ƙofar mota, daga nesa kana hangen walƙiyar da sarƙar Gold da ke wuyansa ke yi, kunnensa kuwa ƴan kunne ne da ake mannawa shima na Gold, gashin kansa a gyare tamkar baza a mutu ba, wasu rikitattun kaya ne jikinsa masu kafurin kyau, wando ne da kaɗan ya wuce gwuiwarsa ya zazzalo da wandon ta ƙasan mazaunansa, daga ciki kuwa guntun wando ne me kyau da tsada, rigarsa maroon ce me ɗauke da zanen fuskarsa, a gaban rigar an rubura Soultan Chif, lokaci ɗaya turarukkan jikinsa ya fara baje harabar Clup ɗin.

Takalman ƙafarsa kuwa sawu ciki Black na gaban kwatance, sai da ya ɗauki mintuna uku yana ƙarewa mutanen da ke gurin kallo kafin ya fara tafiya, ai kuwa kowa ya ɗauki sowa da tafi ana masa kirari, ɗaga musu hannu ya yi alamun ya isa, nan take kowa ya yi tsitttt, daga ɗan nesa ya hangi Majeed da Meera sai da ya ƙarewa Meera kallo kafin ya ja dogon tsaki a ransa yake faɗin, ashe wannan jahilar zai kawo mun na zata wata zazzafa ce, kai tsaye ya nufi gurin da suke tsaye shima Majeed ya nufo sa yana miƙa masa hannu suka tafa, kallon wulaƙanci ya yiwa Meera wanda hakan ya sa ta ji fistari na neman suɓuce mata, tun da take bata taɓa ganinsa ido da ita ba sai yau, gaba ɗaya kyawunsa da kwarjinsa sun gigitata, cikin ƙasaita kamar me ciyon magana ya ce "Wannan ce Karuwar.......?"


Muryar Majeed cike da rashin gaskiya ya ce "No...no....no...haba ba ita ba ce"


"To ina wadda ka ce mun?" Sultan ya faɗa yana ɓata fuska gami da shan ƙamshi.


"Ai tana daga ciki" Cewar Majeed a kiɗime.


Wata irin tsawa Sultan ya daka wadda ta sa kowa tsorata a gurin, idanunsa sun gama rinewa jijiyon kansa kuwa sun yi ruɗu-ruɗu, bakinsa na rawa ya ce "Uban waye ya ce mata ana shiga daga ciki ba tare da na fara shiga ba?"

Haƙuri Majeed ya fara bashi wanda hakan ya sa Meera cewa "Dan Allah ka yi haƙuri ka yafe mata......."

Ido Sultan ya waro jin yana magana Meera ta saka masa baki, ai kuwa ya ɗaga hannu da niyar sharara mata mari, kamar daga sama ya ji an damƙe hannun daga bayansa, wanda hakan ne ya hana shi samun damar marin Meera, kamar wani me ciyon jiki haka ya fara juyawa dan ganin wani me tsautsayin ne ya dakatar da shi daga abin da yake son aikata.










*SHALELEN ALHAZAWA*

*Writing and story*

*By*

*Asmeetar Hydar*


(Asma'u Ayuba)

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATON*





P. 3



A tsaye take cikin gadara da nuna isa.

Lokacin da ya sauke rikitattun idanuwansa kan kyakykyawar fuskarta ne ya tsaya chakkkkk na tsawon mintuna uku, wanda hakan ya bawa gurin damar yin tsittttt kamar an ɗauke ruwan sama, wani mugun kallo Najmeer ta watsa masa tana mai jefar da hannunsa gefe, cikin muryarta me daɗin sauraro ta maida kallonta kan Meera tana faɗin "Me ki ka yiwa wannan yaron yake son ya ɗaga ƙazamin hannunsa kan fuskarki..."

Wani irin gummmm.....kunnuwan Sultan suka yi dan ji yake kamar a mafarki ake yarfa masa kalamannan.

Ba Meera ba hatta mutanen da ke gurin jikinsu rawa yake dan babu wanda ya san abin da zai biyo baya, idanunsa ne suka rine jajir gashin jikinsa sun mimmiƙe, hatta ƙafarsa rawa take, ƙirjinsa kuwa ya ƙara tashi wanda har kana hangowa daga wajen rigarsa.

A tsawace Najmeer ta kuma cewa "Magana nake miki, wanne laifin ki ka masa?" Bakin Meera na rawa ta ce "Dama.....dama....dama..haƙuri na basa saboda kin masa laifi"

"Wacece ta masa laifin"? Najmeer ta kuma tambaya.


Majeed ne ya yi saurin katse zancen da faɗin "Shalele please ki ba Sultan haƙuri wallahi akwai matsala..."


Ɗaga masa hannu Sultan ya yi kafin ya ɗago idanuwansa da ko garwashin wuta ba zai nuna masa ja ba, "Wacece wannan.....?" Ya faɗa yana jan mugun numfashi, Majeed ne ya kuma cewa "Ita ce wadda na faɗa maka" Tun kafin Majeed ya gama rufe baki Sultan ya damƙo gashin kanta da tsananin ƙarfi, tun da Najmeer take babu wani mahaluƙin namijin da ya taɓa damƙe gashin kanta da niyar muzgunawa, daidai saitin fusarsa ya ɗago tata fuskar har suna jin saukar numfashin juna, duk da cewar raɗaɗi da azaba na shigar Najmeer amma hakan be sa ta nuna alamun tsorata ba, a hankali Sultal ke kallon kwayar idanunta ganin gaba ɗaya blue ne babu ɗigon fari ko kaɗan, ya tsorata matuƙa amma hakan be hana shi faɗin "Ke ƴar gidan Uban waye? da har za ki dakatar da ni daga yanke hukunci"

Shuru Najmeer ta masa dan ganin take ya yi yaro sosai ta tsaya magana me tsayi da shi kamar haka.

A fusace ya kuma cewa "Na ce ke ƴar gidan Uban waye" Kamar wadda aka cilla haka Najmeer ta mugun daka tsalle sama tana mai ture shi daga jikinta, lokacin har mutane sun fara guduwa saboda abin ya fi ƙarfin ganinsu, cikin mugun zuciya ta ɗauki wata kwalbar giya da aka aje gurin ta damɓara masa a kai, ji ka ke tassss, ai kuwa tuni mutane sun watse da gudu ganin an bugawa Sultan kwalba.

Jiri na ɗibarsa jini na zuba ya dafe kansa, masu tsaronsa ne suka rugo da gudu sai Majeed da ya kama shi ta baya dan kar ya faɗi, Najmeer na ganin haka ta kama hannun Meera suka fice daga gurin da matsanancin gudu.


Dirrect hospital aka nufa da shi, da farko likitocin basu so karɓarsa ba, dan sun ce sai an kira police, sai da Majeed ya faɗa musu ko waye Mahaifin Sultan kafin aka shiga da shi cikin gaggawa.


Ba wani ɓata lokaci aka tsayar da jinin tare da saka masa bandeji da kuma allura.




Duk abin da ake Sultan na kallo amma bakinsa ya kasa furta kalma ɗaya, tun da Allah ya haliccesa be taɓa jin tsanar wani mahaluƙi kamar yanda yake jin tsanar Najmeer ba, daga zaran ya tuno da tozarcin da ta masa gaban mutane sai ya ji duk kunya ta kama shi, wai mace ce ta yi masa wannan haukar macen ma ƙaramar yarinya wadda ko kama ƙafar shekarunsa bata yi ba.

Wani irin mugun naushi ya kai wa glass Cup ɗin da ke saman ɗan ƙaramin table nan take ya tarwatse hannunsa ya fara fitar da jini, Majeed da shigowarsa kenan ya yi aurin ƙarasawa yana kama hannunsa "Sultan meye haka? jini ne ke zuba fa"


A mugun tsawace Sultan ya dakawa Majeed tsawa "An so what? don't try to calm me down idan har ina cikin fushi"

Ya faɗa yana ficewa daga room ɗin.

A harabar hospital ya samu motocinsa cikin ɓacin rai ya shige yana mai bada umarnin su koma gida, ba ɓata lokaci motocin suka nufi hanyar G R A cikin matsanancin gudu.


Kasancewar gate uku ne ya sa suka shige gate ɗin bayan gidan wanda zaka iya shiga ba tare da kowa ya sani ba, a lokacin sha biyun dare har ta wuce ana neman ƙarfe ɗaya,


A miskilance ya shigo parlourn ya mance cewar babu wanda ya san da fitar sa, steps ɗin ya fara takawa cikin iya tafiya me ɗaukar hankali "Sultan where are you coming from?"

Ya tsinkayo muryar Dad, ba tare da Sultan ya ce uffan ba ya juyo yana kallon Dad ɗin nasa da ke zaune kan ɗaya daga cikin kujerun da ke parlourn da alama yaron nasa yake jira.

"Don't let me repeat myself, and me ya sameka har aka saka maka wannan bandejin?" Dad ya kuma magana yana miƙewa tsaye, Junaid da ke saukowa daga steps ne ya ce "Dad a tare muke na riga shi dawowa ne kawai"

Murmushi Dad ya yi kafin ya ce "Ina ku ka tafi cikin wannan daren?"

Shi dai Sultan ɗan kallo ya zama jin yayan nasa na ƙoƙarin kare shi, har da yiwa Dad ƙarya abin da be saba yi ba.

"Ohh dama Sultan ne ya faɗi a steps shine muka tafi Hospital"

Junaid ya faɗa yana watsawa Sultan mugun kallo.

"Alright Allah ya ƙara tsare gaba, ai shi wanda nake tambaya ma ya mayar da ni banza kamar ba da shi nake ba, na rasa sanin yaushe Sultan zai daina wannan shegen miskilancin nasa, wani lokacin kamar ya fika wani lokacin kamar ka fi shi, Allah dai ya shirya mun ku gaba ɗaya" Junaid ne ya amsa da ameen, Dad kuwa ya nufi room ɗinsa.

Ba tare da Sultan ya kuma kallon inda Junaid ke tsaye ba ya nufi nasa ɗakin yana mai buga ƙofar da ƙarfin tsiya.

Toilet ya nufa tare da sakarwa jikinsa ruwa, bandejin da ke kansa kuwa ya fizge shi da ƙarfi ya cilla shi gefe, ya jima a hakan kafin ya fito jiki a sanyaye, jin wayarsa ta ɗauki ƙara ne ya sa shi matsawa yana duba me kiran nasa.


Majeed ya gani a rubuce kamar ba zai ɗaga ba sai kuma ya yi pearking a kasalance ya ce "Yes Majeed what do you want?"

"Nothing Guy ya jikin naka?"

"Mtsss is that why you call me?" Sultan ya faɗa cikin ɗaga murya.

"No calm down Guy Allah ya ba ka haƙuri good night"

"Hold on Majeed i want to ask you something"

"Ina jinka" Cewar Majeed zuciyarsa na bugawa dan ya san maganar me zai masa.


Sai da Sultan ya ɗauki mintuna biyu yana nazari kafin ya ce "Ina buƙatar sanin ko wacece ita, kuma waye ubanta a garinnan, a bincika min sana'ar da uban nata yake yi nan da zuwa gobe"



Majeed ne ya ce "Wallahi yana da wahala a san gidansu, ni kaina ban taɓa jin wanda ya ce mun ya san hanyar gidansu ba ma balle gidan nasu, but i'll try my best"

"Good....." Sultan ya faɗa yana kashe wayar.


Sallamar Junaid ne ya sa shi maida kallonsa kan ƙofar, da alama ya ji wayar da ƙanin nasa ke yi.

Sanye yake cikin haɗaɗɗun kayan bacci milk masu shegen kyau, ƙamshin turarensa ne ya mamaye ɗakin har ya zauna gefen bed ɗin yana mai ƙurawa ƙanin nasa ido, kamar yanda Junaid ɗin be ce uffan ba haka Sultan ɗin kallo ɗaya ya masa ya ɗauke kai.

Gyaran murya Junaid ya yi kafin ya dafa kafaɗar Sultan cikin kulawa ya ce "Wacece ita Sultan?"

A ɗan tsorace Sultan ya kalli yayan nasa, sai kuma ya basar "Wa ka ke nufi Bro"

"Wadda ta fasa maka kai nake nufi" Junaid ya kuma faɗa yana haɗe fuska alamun babu wasa tattare da shi.

Shima Sultan ɗin haɗe fuskar ya yi dan yanzu ne ma yake jin mugun baƙin cikin abin da Najmeer ta masa, da ƙarfin tsiya ya miƙe ya fara dukan ginar ɗakin da hannayensa yana faɗin "She have to die, wallahi sai na kashe ta kuma babu abin da zai faru a garinnan"

Cikin sauri Junaid ya riƙe shi tare da rungume sa a jikinsa yana bubbuga bayansa a hankali, hannun shi ya kama suka isa gun Frigde ɗin da ke ɗakin, fuskar Junaid ɗauke da murmushinsa me matuƙar ƙara masa kyau ya zubawa Sultan ruwa me sanyi tare da miƙa masa, cikin hanzari ya karɓa ya kafa a baki, sai da ya shanye tasss sannan ya jefar da glass Cup ɗin nan take ya tarwatse.

Hannunsa Junaid ya kuma kamawa ya zaunar da shi kan bed, ɗan ƙaramin Box ɗin da ke kan table ya ɗauko ya fara gyara masa inda jini ke zuba a hannunsa da kuma gefen goshinsa, bandeji ya ɗaura masa yana shafa gashin kansa cikin so da ƙauna ya ce "Relax Sultan ka samu ka kwanta ko jikin naka zai yi sauƙi" Ba musu Sultan ya kwanta yana rufa blanket a jikinsa, ƙara gyara masa blanket ɗin Junaid ya yi kafin ya ce "Kar ka mance da addu'a, sannan ka cire zancen kisan kan da ka yi magana dan idan har ka kashe rai babu wanda zai barka, dan ko Dad zai yi duk yanda zai yi domin a ƙwatar mata haƙƙinta" Junaid ya ƙarasa maganar yana mai ficewa daga ɗakin.


Gaba ɗaya bacci ya ƙauracewa idanun Sultan, daga zaran ya buɗe ido sai ya rinƙa ganin fuskar Najmeer, abin da ya ƙara harzuƙa shi kenan.


Kamar yanda ya ga rana haka yaga dare, sai tara na safiya ya tashi bacci duk jikinsa na zafi kansa kuwa kamar zai rabe gida biyu, a haka ya faɗa toilet ya watso ruwa gamida da alwala ya fito, sallar ma a zaune ya yi a cewarsa ba zai iya duƙawa da miƙewa ba.


Yana gamawa ya haɗa ruwan tea ya sha sannan ya sha maganin ciyon kai.

Da sallama Mom ta shigo sanye cikin less me tsadar gaske fuskarta ɗauke da damuwa ta ƙaraso daga ciki, Sultan na ganinta ya miƙe daga kan sofa tare da hugging nata "Hi Mom how far"

"Not fine Love ɗazu Dad ɗinka ke faɗa min abin da ya faru, ya jikin naka"

"Da sauƙi Mom ba wani ciyon ba ne"

"Alright ka same mu a dianing kai mike jira"

Komawa ya yi ya zauna yana faɗin "No need yanzu na gama shan tea hakan ma is okay"

Murmushi Mom ta yi "Okay ka samu Dad ɗinka akwai maganar da yake son ya yi muku"


"Okay" Sultan ya faɗa yana mai latsa wayarsa.


Sai da ya gama shan ƙamshinsa kafin ya nufi part ɗin Dad dan ya san a can suke karin kumallo, sosai part ɗin ya masifar haɗuwa dan shine ɓangaren da ya fi kowanne ɓangare kyau a faɗin gidan, hatta ƙofar shiga da Gold aka yi shi, kuɗin kujerun da ke part ɗin ya isheka gina ƙaton gida me rai da lafiya, a dianing ya same su har Junaid ɗin, yana sanye cikin ƙananan kaya wando black sai rigar white me taushi, fuskarsa ta ƙara kyau da kwarjini gashin kansa kuwa ya haɗe sosai, da sallama Sultan ya ƙaraso tare da zama yana gaishe da Dad, "Lafiya ƙalau Sultan ya ƙarfin jikin?"


"Alhamdulillah na ji dama"



Masha Allah suka amsa gaba ɗaya kafin kowanne ya fuskanci abincin da ke gabansa banda Sultan da ya nuna baya ra'ayi, Junaid kuwa mamakin rashin gaisuwar da Sultan be masa ba yake, amma sai ya share.

Bayan sun gama ne suka ɗan taɓa fira irinta Family kafin Dad ya ce "Ina son ku bani hankalinku sosai a nan"


Kallonsa suka yi tare da mayar da duk wata natsuwarsu dan jin abin da zai ce, gyaran murya Dad ya yi yana faɗin "Junaid kasancewar ku biyu Allah ya mallaka mun kuma kai ne babban ɗana wanda nake tsammanin kafi Sultan sanin ya kamata da kuma shekaru, hakan ya sa na zuba maka ido dan jiran matar da zaka kawo a matsayin wadda zaka aura amma har yanzu babu labari, ka duba yanzu duk wani abun da ka ke buƙata a rayuwa ka samu bayan haka kana aikin ka, ya kamata ka fito da wacce zaka aura tun kafin ni na zaɓa maka"

Numfashi Dad ya sauke kafin ya maida kallonsa kan Sultan "Kai kuma a ranar da ka dawo ka ke faɗa mun zancen ka samu matar aure a London, wanda na nuna maka ban amince ba, to na zauna na yi nazari sosai idan har ka yarda da tarbiyyarta sai ka fito da ita a ɗaura muku aure, amma fa duk abin da ya biyo baya ka kuka da kanka"


Dad ya ƙarasa maganar yana mai kallon Mom da itama shi ɗin take kallo, sunkuyar da kai Junaid ya yi kafin ya ce "Dad ayi mun afwa dan wallahi bana da kowa a halin yanzu a ɗan bani lokaci"

"Lokaci kamar ya? zaka ce mun duk matan da ke sonka babu wacce ka ke ra'ayi, shekaran jiya fa har gida wata ta biyo ka amma ka ke faɗa mun zancen ba ka da zaɓi"


"Am sorry Dad tarbiyyarsu ce bata mun ba, ina son na kawo macen da ta san darajar kanta, wallahi Dad dukkaninsu basa da kunya kuma babu me saka hijab wani lokacin ma a haka suke fita ba mayafi, kowanne namiji na son ya auri macen da ke suturta jikinta, duk wannan nuna tsiraicin da suke baya burgeni asalima ɗaukar mahaukata nake yi musu" Junaid ya ƙarasa maganar cikin gajiya da dogon bayanin da ya yi, daga Dad sai Mom ne kawai ke samun damar yin doguwar magana da Junaid amma ko a Hospital baya tsayawa bayani sai dai ya saka ayi.

Sultan da ke sauraronsu ne ya ce "Thank you so much Dad, insha Allah zan kira Maleeka anjima na sanar mata wannan babban albishir"

Ɗan taɓe baki Dad ya yi "Bayan haka zaka fara aiki ranar Monday a kanfanina, dama karatu ne kuma ka kammala".

"Yes Dad nima na yi tunanin hakan"

Sultan ya faɗa cike da farinciki, dan shi zancen aurensa da Maleeka ne ya saka shi murna, tun da yake be taɓa haɗuwa da macen da yake jin daɗin harka da ita ba kamar Maleeka, kuma shine namiji na farko da ya fara kwanciya da ita shiyasa yake ƙara daraja ta.


Mom da ke murmushi ne ta ce "Yawwa ai yanzu sai kowa ya fito da matar da yake son aura, kai Junaid ka tabbata ka nemo mata nan da wata ɗaya idan ba haka ba zan haɗaka da Humaira ƴar gidan ƙawata dan naga alamun tana masifar sonka kuma ita ba kalar matan banza ba ce"

Ɗan sosa kai Nunaid ya yi "A dai ƙara haƙuri Mom zan nemo da yardar Allah amma wata ɗaya kamar ya yi sauri"

Dad ne ya ce "Ai sati ɗaya ma nake so ka nemo mata"

Dariya suka yi gaba ɗayansu jin yanda Dad ya yi maganar.




.............................
Najmeer kuwa tun da suka shiga gida ba wanda ya leƙo waje har garin Allah ya waye, bayan sun gama karyawa ne suka baje a tsakiyar parlour suna firar abin da ya faru daren jiya, Meera ta kalli Najmeer da ke game a wayarta ta ce "Kai amma ke hatsabibiya ce, yanzu Sultan ki ka wulaƙanta haka? ai ni jiya na rasa bakin magana shiyasa ki ka ga muna dawowa na kwanta dan a tsorace nake"

Murmushi Najmeer ta saki wanda ya ƙarawa fuskarta kyau "Ke Meera im banda abinki waye zai taɓa mun ke ya zauna lafiya, daga jiya zuwa yau na yi saba da ke sosai, ina jinki kamar ƴar uwata ta jini"

"Hmmm nima haka na ɗaukeki, Allah ya bamu ikon riƙewa juna amana"

"Ameen ya Allah wai ina Maleek ne? rabon da na saka shi a ido tun jiya"

Cewar Najmeer tana ƙunshe dariyarta.

Dogon tsaki Meera ta ja har tana rufe ido "Allah ya tsare ai ni yanzu ganin kaina nake babbar celebrity na wuce sanin Maleek, anjima zan kwaso kayana dan ba zan iya kwanciya a part ɗinsa ba"

Dariyar da Najmeer ke riƙewa ce ta ƙwace mata "Wai da gaske ki ke? Maleek ɗin naki"

"Mtsss zan zageki fa Najmeer wallahi ki fita idona, salon na koma ya cigaba da dukana"

Cike da jin haushi Najmeer ta miƙe zaune tana dafa kafaɗar Meera ta jijjigata da ƙarfin tsiya "Ashe ba ki san abin da ki ke ba, kar ki mance ke macece wadda zata iya shiga ko'ina, kar ki taɓa barin wani kafurin namiji ya rinƙa dukanki a banza a wofi, ke ɗin macece wadda take da ikon kanta, idan har kina son zama da ni sai kin koyi yanda ake dakawa maza gumba a hannu, sai kin zama jajirtacciya marar tsoro, ni da ki ke gani nan......."

Numfashi Najmeer ta ja kafin ta cigaba da faɗin "Bana shakkun kowanne ɗan iskan, ni kaina tsoron kaina nake, shiyasa na nunawa wancan yaron cewar iskanci ma guri ya samu" Ta ƙarasa maganar tana mai komawa ta kwanta.

Sosai maganganunta suka shigi Meera, ai kuwa ta miƙe zumburrrrrr ta fice waje, a harabar gida suka ci karo da Maleek wannan karon be sha komi ba, kallonta ya yi sama da ƙasa kafin ya ce "Ke gidan Uwar wa ki ka kwana? a jiya ma na yi mafarkin kin samu wata ƴar tujara wadda ta zabgan mari, sai da na farka nake ganin ashe ba gaskiya ba ne dan na san babu wata ƴar

Please Login or Register in order to submit comment