Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da take, "Ranki ya daɗe na haɗa miki idan kin gama sai ki shiga daga ciki" Najmeer ta kai kusan mintuna uku kafin ta ce "Okay" Tana mai miƙewa dan rage kayan jikinta, kasa haƙuri Alhajin ya yi domin ta gama firgita shi, a ruɗe ya rungumota yana mai kissing ɗin gefen wuyanta jin wani ƙamshin da ke tashi a jikinta, Najmeer kuwa bata hana shi ba sai ma murmushin muguntar da take a zuciya har suka zube ƙasa, a wannan lokacin ne ta samu damar ɗaukar hankacif ɗin da ke aljihun wandonta ta shaƙa masa a hanci, lokaci ɗaya ya ja numfashi tare da zubewa a sume.

Wata irin dariyar mugunta Najmeer ta saki tana faɗin "Yanzu aka fara Alhaji" Wanka ta shige abinta, ta jima a ciki kafin ta fito ɗaure da tawul, kamar yanda ta barshi hakan ta same shi, sai da ta gama duk shirin baccinta hankali kwance, ɗakin ta fara bincikawa cikin ƙwarewa da iya sata, duk wasu Gold da kuɗaɗensa sai da ta kwashe, sannan ta yiwa kanta tranfer na kuɗaɗe tana mai cigaba da dariya.

A hankali ta nufi ƙofar fita ta danna mata key, dan ta san idan ta ce zata bar gidan a yanzu asirinta zai iya tonuwa, dan haka ta koma ken bed ta yi kwanciyarta tare da addu'ar bacci, cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya yi awon gaba da ita.

Asubar fari ta farka har tana zamewa, a gaggauce ta shiga bayi, har ila yanzu Alhaji na kwance yanda ta barshi, bayan ta fito ne ta duba hijab a wadrop da mamaki ta samu sabon hijab har ƙasa, sai da ta gama sallah kafin ta kama hannayensa ta ja shi zuwa ƙarƙashin bed sannan ta rufe shi da zanin gado, toilet ta koma tana mai kunna shawa sannan ta fito.

A daidai lokacin da aka fara buga ƙofar room ɗin, sai da Najmeer ta daidaita natsuwarta sannan ta ɗauki jakkar da ta zuba kayan da ta sata tana faɗin "Am coming" Ƙofar ta buɗe da mamaki take kallonsa "Waye kai?" Cewar Najmeer a taƙaice "Ni ne me kula da Sir a kullum safiyar Allah"

"Okay ya shiga wanka already mun yi sallama da shi ni zan tafi" Kamar matashin be yarda ba sai kuma ya gyaɗa kai saboda jin ƙarar ruwa daga toilet ɗin.

"Okay Shalele za ki iya tafiya, idan ba damuwa mu tafi na kaiki gida" A tsorace Najmeer ta ce "Ya aka yi ka san sunan da ake kirana"

Murmushi Matashin ya yi "Ai yanda naga Sir ya laƙe miki daga jiya zuwa yau ne ya sa na ba ki wannan sunan" Cikin samun natsuwa Najmeer ta ce "Bana buƙatar rakiyarka" Ba tare da jiran abin da zai ce ba ta bar gurin.


Tun da ta yi nisa da gidan hankalinta ya fara kwanciya a lokacin haske ya fara, adaidaita ta samu tare da yi masa kwantancen inda zai sauke ta, a can bayan layinsu ya aje ta.

Allah ya sa Mamu tana ɗaki cikin sanɗa ta shige nata ɗakin tana rufo ƙofa, kamar daga sama ta tsinkayo muryar Mamu na faɗin "Idan kin gama laɓe-laɓen sai ki fito ki faɗa mun gidan Uban da ki ka kwana"

"Dan Allah Mamu ki shafa mun lafiya, gidan Ubana na kwana mana, shikenan ba zan leƙa waje ba sai ki rinƙa zargin ina kwana a waje, to baza a fito ba idan kuma akwai wanda ya isa ya fito da ni"

"La'ilaha illallahu mahammadan rasulillah, Najmeer ni ki ke faɗawa magana haka? laaaaa biri ya yi kama da mutum, ashe bancin Karuwanci har shaye-shaye ki ka fara"

Banza Najmeer ta yi tana mai kwanciya domin bacci take ji.

Mamu ta jima tana zuba masifa amma ko uffan Najmeer bata kuma cewa ba har ta gaji ta koma nata ɗakin.


Yau kwana biyu kenan Najmeer bata fita koda nan da waje ba, ba ƙaramin daɗi Mamu ta ji ba hakan ya ƙara mata natsuwa duk a tunaninta Najmeer ta shiryu, sallamar da yaro ya yi ne yasa Mamu amsawa tana faɗin "Wa ka ke nema?"

"Wai Jabir yana sallama da Najmeer" Najmeer da fitowarta daga bayi kenan cikin shigar doguwar riga irin ta larabawa me adon duwatsu rigar ta masifar yi mata kyau, pink colour wadda zata kai kimanin dubu ɗari, gashin kanta ta laulaya shi sannan da ɗora mayafi ƙarami a kai, ƙafarta sanye cikin silifas me taushi "Tafi ka ce masa ko Ubansa Bukar be isa ya kira ni na tafi ba balle shi ɗan Akuya" Cewar Najmeer tana jifar Yaron da aka aiko da butar da ke hannunta, da gudu yaron ya fita yana ihu, salati Mamu ta rafka "Yoooo ni Mamu naga ta kaina, ke Najmeer surukin naki ki ka ambata haka?"

Tun kafin Najmeer ta amsa wani yaron ya sake shigowa "Wai dan Allah ta yi haƙuri ta fito" Da mugun gudu Najmeer ta nufi randar ruwan da ke tsakar gidan har takalmanta na cirewa, sai da ta cika wata roba da ruwa ta nufi hanyar waje, Mamu na ganin haka ta miƙe tana kiran sunanta amma ina har Najmeer ta fice, wani matashi ne da zai kai kimanin shekaru ashirin da bakwai sanye cikin fararen kayansa, ɗan mashin ɗinsa na gefe ya sha wanki, fuskarsa ɗauke da murmushi, ba zato ba tsammani ya ji an kwara masa ruwa, ai be ankara ba ya ji an zuba masa ƙasa a jikinsa, sai da Najmeer ta shafe mashin ɗinsa da duk jikinsa da ƙasa tana mai banka masa harara, Mamu da ƙarasowarta kenan ta damƙo hannun Najmeer tare da sharara mata mari, ai tun kafin Mamu ta sauke hannu Najmeer ta watsawa Jabir mari cikin mugun rashin kunya ta ce "Ƙarya ne wallahi, baza a mareni saboda kai ba, munafukin banza yau sai na illataka jira ni kaga" A fusace ta shiga gida tana surutai kamar zararra, gaba ɗaya mutane sun taru a ƙofar gidan, Jabir kam kasa magana ya yi Mamu sai haƙuri take bashi, duk mutanen da ke wajen suna yi ta cewa ya gudu tun kafin ta fito, ihun Najmeer suka jiyo daga bayansu ta nufo shi da Wuƙa a hannu fuskarta banu alamun wasa, ai kuwa ƙafa me naci ban baki ba, Jabir ya runtuma da gudu ko ta kan Mashin ɗinsa be bi ba, mutanen da ke gurin suma duk sun watse dan sun san cewa ba shakka Najmeer na iya dawowa kansu.

Mamu kam zaman dirshan ta yi tare da dafe kanta tana mai karanta duk addu'ar da ta zo bakinta.



Labari ko har ya kai kunnen Kawun Najmeer, a fusace ya nufi gidansu Jabir, tun daga bakin ƙofa ya fara jiyo Mahaifin Jabir na zuba ashar, da sallama Kawu Jamilu ya shiga gidan "Kar ka tako ƙafarka cikin gidana idan ba haka ba wallahi sai ran kowa ya ɓace, har ni wata Karuwa za ta wulaƙantawa yaro? yoooooo me ake da wata ƴar tasha wadda bata gaji mutunci ba, daga yau na saka wuƙa na datse alaƙar Jabir da shashashar yarinyarku" Haƙuri Kawu Jamilu ya shiga bashi yana mai neman afwa, "Haba Bukar me ya yi zafi haka? wallahi idan a yau ku ke son aurennan za'a iya ɗaurawa" Zumbur Jabir ya ce "Eh a ɗaura a yau kowa ya huta, Baba dan Allah ka yarda na aureta ina msifar son Najmeer" Ba ƙaramin so Bukar ke yiwa Yaron nasa ba kasancewar shi ɗaya Allah ya mallaka masa, ba wata dukiya ce da su ba amma duk Unguwar sun fi kowa rufin asiri shiyasa ma Kawu Jamilu ya liƙe musu domin ya lashi arziƙi.

"Shikenan a ɗaura a yau ɗin, amma idan har ta ƙara wulaƙanta min Yaro babu wanda ya isa ya haɗa aurennan" Godiya Jabir da Kawu Jamilu suka shiga yi, miƙewa Jabir ya yi yana mai faɗin "Bari na shiga na shirya, Baba a samu a ba Kawu kuɗin sayen goron ɗaurin aure" Jikin Kawu na rawa ya ce "Yawwa yaron kirki ashe ka gane" Dubu goma aka miƙa masa, carafffff ya karɓe yana washe baki.



Ƙarfe huɗu suka isa gidansu Najmeer, wannan karon har da limamin Unguwar da wasu dattijai uku ƴan uwan Mahaifin Jabir.


A lokacin Najmeer na zaune tsakar gida tana cin shinkafa da miya sai naman kajin da ke saman abincin, gefe ɗaya kuwa drinks ne masu sanyi, sai sautin waƙar M-Sharif ke tashi wadda ta kunna a wayarta, Mamu na zaune tana linke kayanta wanda ta karɓo daga gun wanki.

Sallamar su Kawu ne ya sa Mamu ɗagowa tana amsawa fuskarta ɗauke da murmushi, amma tana ganin su Bukar da Yaronsa har ma da Liman ta ji gabanta ya faɗi, maraba ta yi musu tare da nuna musu shimfiɗa, duk bidirin da ake Najmeer bata saniba saboda ƙarar waƙar da ke tashi, bayan sun gaisa ne Kawu ya kalli gefen da Najmeer ke zaune tare da daka mata tsawa ganin abin nata yana son wuce gona da iri "Ke dan Ubanki ba kiga mutane ba ne? ki ke wannan haukar" A tsorace Najmeer ta miƙe jikinta na ɓari, sanye take cikin wando da kaɗan ya wuce mazaunanta sai ƴar rigarta marar hannu wadda ko cibiyarta bata rufe ba, gashin ganta ya sauko yana rito fuskarta ɗauke da simple makeup, ba Jabir ba har Liman da sauran mutanen sai da suka gigice, ji ka ke kawai Liman da Mahaifin Jabir sun buga salati, Liman ya ce "Subhanallahi, Allah ya shirya"

Sai a lokacin Najmeer ta tuna da kayan da ke jikinta, da sauri ta nufi ɗaki ƙirjinta na dukan uku-uku kar dai a ce ƙararta Jabir ya kai gurin Kawunta, to idan ƙarar ta ya kai meyesa Liman ya zo gidansu abin da bata taɓa ganiba.


Gaba ɗaya ta kasa ba kanta amsar waɗannan tambayoyin, Mamu ce ta ce "Sannunku da zuwa, Allah dai ya sa lafiya naga har da su Liman" Murmushi Liman ya yi "Lafiya ƙalau alkhairi ne ke tafe da mu, da farko dai ga goron ɗaurin aure, yanzu haka na saka a tara jama'a a ƙofar gida domin su shaida auren Jikanyarki Najmeer da ɗan wajen Malan Bukar Jabiru" Wata irin muguwar ashar Najmeer da ke laɓe bakin ƙofa ta ja, "Allah ya tsinewa mutanen da ka tara a ƙofar gidanmu daidai gwargwado, kai Liman har ka isa ka ɗaura mun aure, wallahi duk sai na shuka muku rashin mutunci" Jikin Jibir ne ya fara rawa dan yanzu kam tsoronta yake, Kawu Jamilu ne ya miƙe rai ɓace ya nufi ɗakin, Najmeer na ganin haka ta kwasa da gudu, ai kuwa ya rufa mata baya, daga waje kana jiyo ihunta taja faɗin wallahi ta yarda da auren, kuka take kamar ranta zai fita, ita kanta Mamu bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, ba ƙaramin tausayin Najmeer take ba, ta san cewa dukanta Kawu Jamilu ya yi, a duniya ba abin da take son gani fiye da farincikin Jikanyar tata.


Fuska a murtuƙe Kawu ya dawo tare da zama kusa da Jabir "Kwantar da hankalinka Najmeer ta zama matarka, ke kuma Mamu ga naki goron ki rabawa mutanenki, mu zamu tafi daga waje mutane na jira" Ya ƙarasa maganar yana miƙewa tsaye, Malan Bukar da su Liman ma suka rufa masa baya, suna fita Mamu ta nufi ɗakin Najmeer dan har yanzu tana jin sautin kukanta.




LONDON
.................

Wani irin numfashi ya sauke wanda ya sa matashiyar da ke kwance sauke ajiyar zuciya, sun jima a haka kafin ya ƙara ƙanƙameta a jikinsa na tsawon mintuna biyar, a hankali ya koma gefe yana sauke numfashi.


Cikin salo da iyayi matashiyar ta ƙara haurawa saman jikinsa ta shafo haɗaɗɗen sajensa, "Love you are so sweet, but why do u want to go back to Nigeria?" Ta tambayesa tana shafa ƙasan mararsa, kyakykyawan matashin da zai kai kimanin shekaru ashirin da takwas ne ya ce "Colm down Babe you know my Dad said i should go back, and yau satina ɗaya da ƙare School amma kin hana mun komawa"

"Amma Love........"

"Shhhhhhhhhh......." Ya ɗora yatsarsa a lips ɗinta "Not another word Babe, anjima jirginmu zai ɗaga zan shiga wanka" Ya faɗa yana miƙewa daga kan bed ɗin, sanin halinsa ne ya sa ta kasa magana, zubawa halittarsa ido ta yi tamkar yau ta fara ganinsa, dogo ne daidai gwargwado me faffaɗan ƙirji, gashin kansa kamar na larabawa, shi ya ƙara bawa fatar jikinsa da ke fari tassss damar fito da kyawunta, yana da manyan idanu farare masu jan hankali ɗauke da gashi zara-zara, idan ya motsa bakinsa kuwa zaka iya ɗauke muntuna biyar ba ka daina kallon bakin nasa ba, ɗauke yake da red lips me laushi tare da fararen haƙora masu jan hankalin me kallonsa, dogon hancinsa kuwa har ya ɗan kwanta a sama kuwa ya yi tsayi gwanin sha'awa, gashin girarsa baƙi ne wulikk ga cika ga kyau, yatsun ƙafarsa zara-zara ne masu ɗaukar hankali, kamar yanda gashin ƙirjinsa ya kwanta luff-lufff kana gani ka san cikakken namiji ne me tsafta da kwarjini, cigaba da ƙura masa ido matashiyar ta yi har ya shige ƙayataccen toilet ɗin da ke ɗakin, duk da cewar itama ba ƙaramin kyau ne da ita ba, haskenta ma har ya haɗa da sirkin ja, saboda gashin kanta ba wani baƙi ba ne, kana ganinta ka san Baturiya ce cikakkiya, kamar wadda aka tsikara ta miƙe tare da shigewa toilet ɗin, sun ɗauki kusan mintuna talatin a ciki, sannan suka fito a tare daidai lokacin da wayarsa ta fara ƙara, cikin taƙama ya ƙarasa yana mai kallon screen ɗin, ganin sunan Dad ne ya sa shi saurin ɗagawa amma be ce komi ba.

Daga can ɓangaren Dattijon ya ce "Sultan baza ka yi magana ba ne? har yanzu kana London kamar wanda aka jona jininsa a ƙasar, to na ba ka nan da anjima ka shigo Nigeria if not sai na ɓata maka rai" Ba tare da jiran abin da Sultan ɗin zai ce ba ya Dad kashe waya, da ƙarfin tsiya Sultan ya buga wayar tasa a ƙasa ƙirar iphone 15promax nan take ta yi kaca-kaca, wani irin mugun huci ya furzar yana dafe saitin zuciyarsa, a kiɗime Matashiyar ta ja baya ganin halin da ya shiga, ba tare da ya kalleta ba ya fara shiryawa cikin wasu tsadaddun ƙananan kaya masu masifar kyau da ɗaukar ido, wani ƙayataccen agogo ya saka na Gold yana mai fesa turarukka masu daɗin ƙamshin, a lokacin zuciyarsa ta fara sanyi amma idanuwansa sun rine sun yi jajir, "Malika what are you waiting for?" Ya faɗa a tsawace.

Jikin wadda aka kira da Malika na rawa ta ce "Am......am......am waiting for you".

"What.......? idan na buɗe idona na ganki a nan sai na kakkarya ƙasussan jikinki" Tun kafin ya gama rufe baki ta kwashi kayanta a hannu tare da barin ɗakin cikin mugun gudu, dan ta san cewa yau ransa ya ɓace.



Cikin ƙanƙanin lokaci ya nufi airport, ba ɓata lokaci jirginsu ya tashi, gaba ɗaya mutanen da ke cikin jirgin kallonsa suke musamman mata, ganin tsananin kyawun halittarsa me matuƙar jan hankali.


Cikin ƙanƙanin lokaci jirginsu ya sauka a babban airpor na garin Jos, wata Matashiya da ke bayansa ne ta ƙura masa ido har suka sauko daga kan matattakalar, daga nesa Drivernsa me suna Umar ya hangesa cikin hanzari ya ƙaraso yana mai karɓar Trolyn da ke hannunsa, "Ƙaramin Alhaji barka da zuwa?" Drivern ya faɗa yana murmushi ko kallonsa Sultan be yi ba ya bar gurin, bayansa Umar ya bi cikin rashin damuwa dan sun saba da halinsa a gidan, balle yanzu da ya tafi ƙasar turai ai dole zai ƙara hartsinewa.

Motoci uku ne masu masifar tsada suka zo tarbarsa, daga cikin motocin akwai ƙirar Loxes me jan hankali, glass ɗinta black ne ba ka ganin wanda ke ciki, amma da alama akwai mutun a cikinsa, cike da miskilanci Sultan ya kalli Drivern da ya saka troly a boot "Waye a cikin motar nan?"

"Ƙaramin Alhaji ai Oga Junaid ne tare da shi muka zo" Da sauri Sultan ya nufi motar cikin mamaki dan be yi tsammanin Brother ɗin nasa zai zo tarbarsa ba, Drivern da ke jan motar Junaid ne ya yi saurin buɗewa Sultan ƙofar motar, ai kuwa ya shige cike da ƙasaita.

A zaune ya same shi waya kare a kunnensa, ƙamshin turarensa ya gama hautsine gaba ɗaya motar, a cinyarsa kuwa Laptop ne da alama aiki yake yi, Matashi ne fari sol me matuƙar kyau wanda kana ganinsa ka san hutu da kuɗi sun gama baje hajarsu a jikinsa saurayi me taƙama da aji ɗan shekaru talatin daidai a duniya, kamanninsu ɗaya da Sultan har ma zaka kasa gane wanda ya fi wani kyau a cikinsu, sai dai shi Junaid lips ɗinsa pink ne saɓanin Sultan da nasa red ne, sanye yake cikin manyan kaya yadi me masifar tsada da ɗaukar ido wanda kana gani ka san kuɗi sun yi kuka, wayarsa ƙirar 15promax ce ya sauke a hankali yana mai kallon ɗan uwan nasa, cikin muryarsa me ɗan karen daɗi ya ce "Ba ka iya gaisuwa ba ne Sultan" Ɗan cije lips Sultan ya yi dan baya son abin da Brother ɗin nasa yake masa, amma babu yanda ya iya dole ya sosa gashin kansa fuska a haɗe ya ce "Barka da war haka"

Sai da Junaid ya ɗauki mintuna uku yana latsa Laptop ɗinsa wanda har jikin Sultan ya fara rawa tsabagen takaici babu abin da ya tsana irin wulaƙanci, kamar daga sama ya ji ya ce "Lafiya ya hanya"

"Hanya Alhamdulillah" Sultan ya amsa a taƙaice.

Ba tare da Junaid ya kuma cewa komi ba ya ce "Driver we can go because i have alot to do"

Cikin girmamawa Driver ya ja motar, nan take sauran motocin suka mara musu baya, tun da suka fara tafiya babu wanda ya sake magana daga Junaid har Sultan kowa na ji da kansa.


Wata arniyar Unguwa suka nufa wadda suke kira da G R A, babbar area ce a cikin garin Jos wanda duk wani me kuɗi da ke ji da kansa zaka same shi a unguwar, a bakin wani tangamemen gate motocin suka tsaya nan take gate ɗin gudu uku suka ɗage sama, gida ne wanda tun daga wajensa zaka tabbatar da cewa ba ƙaramin hamshin me kuɗi ne ya gina shi ba, gaba ɗaya ginar gidan Golding Colour ne, gate ɗin kuwa na Gold ne wanda kafin ya ɗage sama sai ya yi searching idan har ba ka ɗauke da wani mugun abu, a pearking place suka tsaya wanda duk iya gulmarka baza ka ga ƙarshen motocin da ke baje a gurin ba, and you can't even count it.


Every where security's ne kowannensu riƙe da bindiga suna tsaron lungu da saƙo na gidan.


Gida ne me hawa-hawa har huɗu lafiyayyu na faɗa a ji, kowanne hawa da kalar pentinsa kuma kowanne hawa da kalar tsarinsa, a iya binciken da aka yi gaba ɗaya garin Jos babu gidan da ya kai gidan Chif Muhammad kyau, gaba ɗaya gidan Flowers ne masu ɗaukar hankali Golding colour waɗan da idanu basu taɓa gani ba, grass carpet ne a baje me matuƙar ɗaukar hankali, guraren shaƙatawa kuwa ya fi biyar a gidan, kama daga swimming pool har gadin.

Da sauri wani matashi ya ƙaraso tare da buɗe musu motar.

Cikin gadara Sultan ya sauko da ɗayar ƙafarsa yana ƙarewa gidan kallo zuciyarsa na kaɗawa, sai da ya ɗauki tsawon mintuna uku a haka kafin ya fito a lokacin Junaid ya jima da isa haɗaɗɗen parlourn gidan wanda ko gidan shugaban ƙasa be kai shi haɗuwa ba, ta ko'ina kayan more rayuwa ne kamar basu san zafin dukiya ba, manya-manyan TV ne guda uku masu rai da lafiya manne a bangon parlourn, ɗaya daga cikin haɗaɗun royal ɗin da ke gurin Junaid ya zauna bakinsa ɗauke da bisimillah.

Daga sama ya ji ana faɗin "Where's he?"

A hankali Junaid ya sauke rikitattun idanunsa kan Dad ɗin nasu "He's coming Dad just wait a minute" Daga haka Junaid be sake cewa komi ba.

Dattijon mutumin kuwa da ke cikin kayan alfarma ne ya fara saukowa daga matattakalar fuskarsa a haɗe, kana ganinsa ka san shine Mahaifinsu dan kamanninsu ya nuna hakan, sai dai shi ya fi su tsufa ne kawai.


Kayan jikinsa sun isa tabbatar maka cewar babu wani abun da suke nema a duniya face gamawa da ita lafiya.

Saman kujera me zaman mutum ɗaya ya zauna yana mai duba agogon gold ɗin da ke hannunsa daidai lokacin da Sultan ya yi sallama cike da taƙama, dirrect gurin Dad ɗin nasa ya nufa yana mai ware hannayensa "Hi Dad am back......"


"You are very stupid Sultan, is that how za ka gaida mahaifinka? ashe ka watsar da tarbiyyar da na yi shekara da shekaru ina ba ku".

Idanun Sultan ne suka ƙanƙance tsabagen fusata har jikinsa ya fara rawa jijiyoyin kansa sun tashi ruɗu-ruɗu, a fusace ya nufi matattakalar ba tare da ya ƙara magana ba, cikin tsawa Dad ya ce "Sultan don't add another step if not wallahi sai dai ka canja wani Uban amma ba ni ba......" Cakkkk ya tsaya yana mai damƙe hannunsa da ƙarfin tsiya, Junaid da ke jin duk abin da ke faruwa ne ya ɗago kyawawan idanunsa yana mai saukewa kan Sultan, lokaci ɗaya kuma ya miƙe tare da nufar Frigde ɗin da ke parlourn, robar ruwa ya ɓalle sannan ya zuba a Cup.

Cike da takunsa me jan hankali ya ƙaraso gaban Sultan da har yanzu tsaye yake kamar wanda aka dasa, "Take this ka sha ko zuciyarka zata yi sanyi, but remember one thing please he's our Dad not our mate". Hannunsa ya kama ya ɗora masa Cup ɗin sannan ya haura sama yana mai sakin murmushi.


A fusace Sultan ya ɗaga Cup ɗin ya kai bakinsa, kurɓa uku kawai ya shanye ruwan yana mai jingina bayansa kan ƙarfen da ke steps ɗin, duk abin da yake Dad na kallonsa yana mamakin zuciya irin ta ɗan nasa, sai da ya ƙara mintuna uku ahakan kafin ya fara saukowa kan steps ɗin a hankali, kujerar da ke fuskantar Mahaifin nasa ya zauna cikin sanyin murya kamar wanda ke ciyon magana ya ce "Ina wuni Dad ya gida" Sai da Dad ya ƙare masa kallo kafin ya ce "Lafiya lau ya karatun? ina fatar ka gama tattaro komi naka da yake can, saboda kai da ƙasar London har ƙarshen rayuwarka, waɗannan shekarun da ka yi ka gama sauya rayuwarka gaba ɗaya dama ko a can baya sai a hankali".

"Yes Dad amma na bar abu me muhimmanci da gaba ɗaya Family sai sun koma saboda shi"

"What are you saying Sultan, wanne abu ne haka da har zai sa Family su tafi wata ƙasar?"

"Dad wadda zan aura" Sultan ya faɗa cike da gajiya da magana dan ba ƙaramin wahala magana take yi masa ba.

Rai ɓace Dad ya ce "Ashe ka isa da kanka tun da har zaka tafi wata ƙasar ka kwaso mana wata macen acan, to bari ka ji na faɗa maka idan har na isa da kai kuma ni ne Ubanka babu kai babu wannam yarinyar" Ba tare da Dad ya jira abin da Sultan zai ce ba ya miƙe yana mai barin parlourn a lokacin da wata Dattijuwa ke saukowa daga saman bene fuskarta ɗauke da murmushi tana kallon Sultan, haɗaɗɗiyar atamfa ne jikinta me tsadar gaske duk jikin nata Gold ne, ba ƙaramin kyau ta yi ba, domin har hutu da jin daɗi na ƙoƙarin ɓoye tsufanta, Sultan na ganinta ya miƙe da sauri ya nufeta tare da hugging ɗinta kamar ƙaramin yaro ya ce "Hi Mom am back"

Ƙara faɗaɗa murmushinta ta yi "Hi Son welcome ya London ɗin?" Ta faɗa tana mai kama hannunsa suka koma kan kujera me zaman mutum uku.

Sultan na yamutsa fuska ya ce "So amazing but Mom kina jin Dad wai ba zai barni na yi aure a ƙasar waje ba"

Gefen fuskarsa ta shafa cikin so da ƙauna ta ce "Don't mind him babu wanda ya isa ya hana ka auren wadda ka ke so.

"Thank you so much Mom that's why i love you"

"Love you too Sweetheart ka je ka watsa ruwa kafin ka gama zan sa a haɗa mana abinci yau a babban parlour za'a ci abinci tun da ka dawo"

Fuskarsa ɗauke da murmushi ya miƙe yana faɗin "Okay Mom"

Cikin so da ƙaunar ɗan nata take kallonsa har ya haura sama cike da gadara.



A hawa na biyu

Please Login or Register in order to submit comment