Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba magana nake son mu yi da ita"


"Wallahi ƙarya yake azzalumi jiya har fyaɗe ya tashi min a cikin bainar jama'a, hmmm ai Mamu idan na nuna miki yanda ya mayar da jikina sai kin sha mamaki, shine fa ya biyo ni har gida"


"Keeee waye ya tashi yi miki fyaɗen?"

Prince ya faɗa cikin mugun mamaki.


Ɗago kai Najmeer ta yi tana mai yi masa gwalo sai kuma ta fashe da kuka har da birgima a ƙasa tamkar ƙaramar yarinya, hawaye kuwa daki-daki a idanuwanta, rarrashinta Mamu ta shiga yi tana faɗin "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un yanzu bawan Allah jikanyar tawa ka tashi lalatawa? yarinya kamila me tsoron Allah shine za ka yi mata fyaɗe, Allah ya fika da izininsa"

Cewar Mamu itama tana fashewa da kukan, majina Najmeer ta sharce kafin ta ce "Ina faɗa miki Mamu sai riƙe sa ake mutane na bashi haƙuri amma haka ya rinƙa ture kowa da ke gabansa cikin tasha ya nufo kaina da niyar ɓata min rayuwa"

Wannan karon kasa haƙuri Meera ta yi ta bushe da dariya har da riƙe ciki, Prince kam kasa magana ya yi idanuwansa sun rine jajir ransa ya mugun ɓaci jin sharrin da Najmeer ta laƙa masa, kuma daga zaran ya ɗago ido sai ta kawar da kai dan babu abin da take tsoro sama da kallon idanuwansa.


"Kin gani ko Mamu wai na zo"

Najmeer ta faɗa tana lailaya ido.

Tsammm Prince ya miƙe yana mai ficewa waje ransa a mugun ɓace.


Najmeer na ganin haka ta bi bayansa da gudu a lokacin har ya kusa gate, "Hi Mr Prince Miyar yauƙi"

Ta faɗa tana kama ƙugu.

Ran Prince a matuƙar ɓace ya juyo "Waye Miyar yauƙin?" Ya faɗa yana mai tsalle ɗaya ya damƙo gashin kanta, ihu Najmeer ta kurma kamar wadda ake cirewa rai "Sunan da ki ka samun kenan? ai kuwa zan koya miki hankali" Ya faɗa yana mai ƙara matse gashin kanta, sosai zafin ke shiga har tsakiyar ƙwaƙwalwarta, "Washhhh Allah please ka sake min gashina"


Ba tare da ya saurareta ba ya cigaba da jijjiga kanta tsabagen mugunta, ai kuwa Najmeer ta rinƙa rafka ihu har su Mamu suka fito, Mamu ce a gaban Meera har tana ƙoƙarin zamewa ita ala dole an taɓa mata kamilar jikanya, Prince na ganin Hajiya Mamu na yanka gudu ta nufo inda suke ne ya sa ya sake Najmeer tare da ficewa da sauri.


Sosai kan Najmeer ke sarawa tana ganin Mamu ta ƙaraso ai kuwa ta zube ƙasa tare da runtuma ihu "Wayyooo Allah kaina, wayyo Allah jama'a ya kasheni ku duba min ƙwaƙwalwar kaina ina ganin ya tafi da shi"

Kamata Mamu ta yi tana duba gashin kan nata, "Mtssss ke rabani da shirmen banza ba abin da ya samu kan naki"


"Dama Mamu na san kin daina ƙaunata imba haka ba ga kwanya na zuba ƙasa amma za ki ce ba abin da ya sameni"


Najmeer ta faɗa tana dalalo yawu wai shine kwanya, Meera ce ta ce "Kai Najmeer ai wannan yawu ne ba kwanya ba, kuma dama idan an kama gashin kan mutum da ƙarfi sosai har zubar yawu zai rinƙa yi tsawon sati ɗaya"


Najmeer na jin haka ta ƙara tattaro yawu ta cigaba da dalalowa tana ɗaga kai sama "Kin ji ko Mamu, shikenan Miyar yauƙi ya gama da ni haka kawai ya tasa ni gaba"


Ɗagata Mamu ta yi tana zuba masifa ta inda take shiga ba tanan take fita ba, zagi kuwa babu wanda Prince be sha ba gurin Mamu har suka koma daga ciki.

Suna shiga Najmeer ta yi baje-baje kan kujera tana ɗaga harshe sama, Mamu kuwa sai sannu take yi mata har da ɗauko tsumma ana goge yawun da ke zuba, sarai Meera ta san Najmeer ƙarya take ita da kanta take zubar da yawun, kamar me ciyon farfaɗiya Najmeer ta ce "Mamu na san cewa mutuwa zan yi tun da har ki ka ga ban daina zubda yawu ba, yanzu haka idona sun fara rufewa da buɗewa ina ganinki ne uku-uku dan Allah ki yafe min duk abin da na yi miki"

Mamu na jin haka ta matso ƙwalla gami da sarce majina "Baza ki mutu ba Najmeer sai na ga ƴaƴanki da yardar Allah, ai shi ciyo ba mutuwa ba ne"

"A a mutuwa zan yi Mamu, ina ji a jikina dan har wani sanyi-sanyi ke tashi daga tsakiyar kaina da alama mu ne gaba a gidan Aljannah"

Najmeer ta faɗa tana wuwwula ido.

"Ƙwarai kuwa ku ne a gaba ƴarnan, ai ina ji a jikina, amma dan Allah kar ki mutu har sai kin kaini umrar da ki ka ce"


Daga Najmeer har Meera bushewa da dariya suka yi, cikin dariya Najmeer ta ce "Wai dama duk wannan tarairayar da ki ke min dan kawai zuwa umra ne? na zata duk cikin soyayya ce"


"Mtsssss rabani dan Allah da shirmen banza da wofi, yooooo ni meye abin tarairaya gurinki idan ba wani abin nake so ba"


"Ƙara narke fuska Najmeer ta yi tana mai karkace baki ta cigaba da magana kamar ɗazu "Wayyyooo Allah kwanyar kaina na zuba Mamu ki taimaka min ya raunatani"


Ko kallonta Mamu bata yi ba ta haura sama.


Wayar Najmeer da ke gefe ne ta ɗauki ƙara cikin hanzari ta duba tana mai jan dogon tsaki, sai da ta kusa yankewa kafin ta ɗaga.

Daga can ɓangaren Alhaji ya ce "Shalelena sai kira nake ba'a ɗagawa"


Ɗan taɓe baki Najmeer ta yi cike da salo ta ce "Yes mun tafi Abuja ne da Mom ɗina amma anjima zamu dawo"

"Okay dama zamu zo da iyayena gobe da safe neman aurenki kamar yanda mu ka yi magana a baya, kasancewar wasu abubuwan ne suka tsayar da ni"


Wani irin juyawa cikin Najmeer ya yi amma sai ta dake "Okay ƙarfe nawa za ku shigo goben?"


"Misalin sha ɗaya na safe"


"Allah ya kaimu" Najmeer ta faɗa tana kashe waya.

Duk gumi ya wanke mata jiki, "Lafiya dai Najmeer?"

Cewar Meera.


Sai da Najmeer ta ƙara sharce gumi kafin ta ce "Wai Alhaji ne zai shigo neman aurena gobe"

"Mun shiga uku, kina nufin zai gane ƙarya ki ke masa duk tsawon wannan lokacin"


"Ba ma hakan ba Meera ina da auren Jabir a kaina fa"


"What.........?"


Meera ta faɗa da ƙarfi.


"Yes Meera ranar da na koma gidan da ku ke zama a ranar aka ɗaura aurena da Jabir, shine dalilin da ya sa na bar gidanmu"


"Amma Mamu ta ce min ba'a ri ga da an ɗaura auren ba"

Ɗago kai Najmeer ta yi tana mai kallon Meera "Kin tabbata hakan ta ce miki"

"Sosai kuwa na tabbata dan mun yi firar sosai, ta sanar da ni cewar an fasa ɗaurin auren saboda kin bar gida"

Hamdala Najmeer ta yi tare da godewa Allah, dama wannan dalilin ne ya sa a kullum take jin ɓacin rai, gyara zama ta yi kafin ta kuma cewa "Ya ki ke ganin za'a yi, ni da iyayena sun rasu duk ƙarya ce nake shirya masa yanzu idan ya zo ya samu ba hakan ba ne fa"


"Wai kina nufin aurensa za ki yi?" Meera ta tambaya.


Murmushi Najmeer ta saki me ƙarawa fuskarta kyau "Sosai ma kuwa aurensa zan yi, meye a ciki? daga zaran na yi sati ɗaya zan kwashe duk wata dukiyarsa sannan ya sakeni"

Bushewa da dariya Meera ta yi "Kina nufin be da hankali ne zai sakeki"


"Kin ga Meera duk wannan zancen mu aje shi a gefe, hankalina a tashe yake kar fa asiri ya tonu"


"Zamu yi tunani zuwa anjima yunwa nake ji yanzu, bari na kira Maryam ta ɗora mana girki"


Meera ta faɗa tana miƙewa.



..................
Yau ta kama Monday kuma a yau su Dad suka shirya zuwa London neman auren ɗansu Sultan, daga Junaid har Mom tare za'a tafi da su.


Dukkaninsu sun haɗe cikin kayan alfarma kana ganinsu ka san cewa ba ƙaramar dukiya ce tare da su ba, yau Junaid wankan ƙananan kaya ya yi wanda hakan ya masifar karɓar jikinsa, Sultan kuwa an sha manyan kaya sai washe baki ake.


Motoci hamsin ne suka nufi airport cikin tafiyar ɗaukar hankalin me kallonsu, jirgi ɗaya aka kama wanda zai ɗauke su, a can suka sami Surayya da Imran sai Alhaji Hafiz ƙanin Dad kasancewar da su za'a yi tafiyar.

Kana ganin Surayya zaka san hankalinta baya kanta, duk ta rame ta tsigale sai kallon Sultan take har lokacin tafiyarsu ya yi, wanda Sultan ɗin be sakar mata fiska ba, Imran da Junaid kuwa suna tare da juna sai magana suke ƙasa-ƙasa da alama akwai abin da suke tattaunawa.

Ba ɓata lokaci jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasar London.


Basu jima suna tafiya ba Sultan ya miƙe dan shiga toilet, hakan ya sa Surayya ta faki idanu ta bi bayansa jiki na rawa, kamar an ce ya juya kawai ya ga mutun tsaye a gabansa.

"Surayya lafiya?"

Ya faɗa yana haɗe fuska.


"Ba lafiya ba Sultan, tabbas ka san matsalata kuma kaine maganinsa"


"Kin ga kar ki soma please, yanzu fa ni mijin wata ne, ki yi haƙuri da ni ko kuma ki koma gun Junaid tun da shi baya da wadda zai aura"

Waro ido Surayya ta yi a tsorace "Rufa min asiri, ai Juanid ɗin na fara so kafin kai amma sanin halinsa ne ya sa ban yarda ya san ina son sa ba, amma kai na bayyana maka soyayyata ka kasa amincewa, dan Allah Sultan ka aureni ko zuciyata zata samu sauƙi"

"Ke wai ya zan auri ballagaza kamar ki, kalleki dan Allah duk wani abin da nake buƙata a gurin mace bakya da shi, a hakan zan aureki"


Fashewa da kuka Surayya ta yi tana mai roƙon Sultan amma be saurareta ba ya shige bayi abinsa, jiki a mace ta koma tare da zama inda ta tashi, duk yanayinta ya canja Imran yayanta ne kawai ya san halin da take ciki dan bata ɓoye masa komi, sosai tausayin ƙanwar tasa ya kama shi ganin yanda lokacin ɗaya ta canja.



Misalin ƙarfe sha biyu suka isa ƙasar, inda suka tarar da hamshaƙan masu kuɗi an zo tarbarsu, motoci fiye da ɗari ne ke gurin masu masifar kyau da tsada, da farko iyayen Malika sun haɗe fuska suna jiran ganin waɗan da suka zo neman auren ƴarsu, amma suna ganin kayan jikinsu Dad sai kowannensu ya fara washe baki, dan gaba ɗaya taronsu babu wanda ya saka kaya me tsada da ɗaukar ido kamar su Dad, Malika da ke can gefe ne cikin shigar ƙananan kaya waɗan da suka ɗame mata jiki duk wata halittar jikinta ta bayyana, da gudu ta ƙaraso tare da hugging ɗin Sultan, kiss ta sakar masa a goshi "I love you Babe"


Daga Dad har su Junaid kasa magana suka yi, ganin rashin kunya a fili.

Surayya kuwa hawaye ta share a gefe tana mai jin mugun tsanar Malika a ranta musamman da ta ga kyawun da Allah ya yi mata, ɗan janyeta a jikinsa Sultan ya yi "Love you too Baby, ki gaida su Dad mana"

Sai da ta ɗan taɓe baki kafin ta ɗaga musu hannu tana faɗin "Hi guys welcome to London" Idanunta ne ya tsaya kan Juanid, ai kuwa ta nufesa da sauri har tana haɗawa da gudu-gudu, hannu ta ware da niyar rungumesa ya ɗaga mata yatsa tare da girgiza kai "Hi Malika ya ki ke?" Ya faɗa yana sakin murmushin yaƙe.

Hakan ya sa ta sha jinin jikinta, nan fa aka fara gaisuwa da yi musu barka da zuwa, duk da cewar Dad ya ga rashin tarbiyya a tattare da Family ɗin amma hakan be sa ya nuna ko a fuska ba, Surayya na gefen Mom a tare suka shiga mota, ba ɓata lokaci motocin suka bar gurin.

Kai daga ganin gidansu Malika ka san cewa ba ƙananan masu kuɗi ba ne, gida ne wanda ya amsa sunansa gida duk inda ka duba zubin dukiya ne tari-tari.

Wani ƙayataccen parlour aka sauke su tare da zube musu kayan more rayuwa, Malika idanuwanta na kan Junaid ko ƙyaftawa bata son yi har Junaid da Imra suka lura da hakan, Imran ne ya ɗan mitsini Junaid a hankali ya ce "Wai kana lura da wannan yarinyar kuwa? sai kallonka take nifa lamarinta ya fara bani mamaki"

Cikin cool voice Junaid ya ce "Ni kaina kallon ya isheni ka san bana son yawan kallo ai"

Daga haka suka bar zancen ganin mutane sun fara taruwa ana ƙara yi musu sannu da zuwa, baƙin ciki ne ya hana Surayya ɗaga ko cokali balle ta ci wani abun, ba laifi sun ci abinci amma ba sosai ba, nan aka kai kowannensu nasa ɗakin, sai dai Mom da Surayya ɗaki ɗaya suke Dad kuwa da ƙaninsa Junaid yana ɗaki ɗaya da Imran, gogan ne Sultan aka warewa ɗakinsa daban wanda ya mugun haɗuwa.


Ƙarfe huɗu za'ayi taro a harabar gida, wanda hakan al'adarsu ce idan har za'a zo neman aure sai an yi shagali tare da nunawa jama'a mijin da ya zo neman ƴarsu.


Kasancewar a gajiya Sultan yake ne ya sa yana shiga ya kwanta dan baccin da ke idonsa.


Dad kuwa tun da ya shiga ya kasa zaune ya kasa tsaye, tunaninsa ɗaya wannan wanne irin Family ne Sultan zai haɗa zuri'a da su.


Kamar yanda Dad ke cikin wannan tunanin haka ma Junaid da Imran waɗan da ke mamakin rashin kamun kai irin na Malika.


Ƙarfe huɗu da rabi na yamma an gama shirya gurin taron tamkar baza'a mutu ba, komi na gurin white and pink ne, haka ma kowa ya saka kaya white and pink hatta su Mom, wanda anko ne da aka kawo musu na taron.

Malika ta yi shiga cikin doguwar riga har tana jan ƙasa, a kanta babu ɗan ƙwali balle mayafi duk rabin dukiyar fulaninta a waje, wannan shigar ba ƙaramin ɓatawa su Dad rai ya yi ba, cikin fushi ya ja hannun Sultan gefe ransa a mugun ɓace ya ce "Sultan wannan wanne irin hauka ne haka? ka rasa wadda zaka kawo a matsayin matar aure sai wadda bata san darajar kanta ba"

"Dad please wallahi ina sonta sosai and zan mayar da ita yanda ka ke so bayan aurenmu"

"Haukar banza kenan, bayan sunana da zaka ɓata a gari har sunan ƴaƴan da zaka haifa ma dan babu wanda zai so haɗa alaƙa da irin wannan gidan, dukiyarsu ta banza ce tun da babu tsoron Allah a ciki" Dad ya ƙarasa maganar yana barin gurin, daidai lokacin da aka ce ana buƙatar Malika ta kama hannun mijinta ta kawo shi gaban taro.

Cikin karairaya Malika ta miƙe tana mai tafiya a gadarance, kowa ya zuba mata ido sautin waƙa na tashi a hankali me daɗin dauraro, Sultan kuwa har da gyara tsayuwa yana mai sakin killer smile, da mamaki aka ga ta nufi Junaid fuskarta ɗauke da murmushi, nan fa kallo ya ƙara yawa dan mutane da dama sun san cewa ba Junaid ne angon ba.


Malika na isa ta kama hannunsa tare da jansa zuwa gaban taron, kamar wani wawa haka Junaid ke bin bayanta cike da mamaki kamar a mafarki, sai da suka isa kafin Malika ta ɗauki speaker tana mai ƙara gaida mutanen da ke gurin cikin harshen turanci, sannan ta cigaba da faɗin "Kamar yanda kowa ya sani a yau ne aka zo neman aurena daga Nigeria, kuma kowa ya buƙaci ganin wanda zan aura hakan ya sa na yanke hukuncin nuna muku wanda zuciyata ke ƙauna sannan nake fatar na aura"

Sai da ta kalli Sultan da duk idanunsa sun canja kala kafin ta cigaba da faɗin "Junaid nake so kuma nake burin na aura, dan haka a ɗaura min aure da shi ko na kashe kaina"


Tsittttttttt kiɗa ya tsaya mutanen da ke gurin duk suka ƙara yin shuru ana sauraren abin da Malika ke faɗi tamkar a mafarki.












*Jiya na ce zan yi posting bansamu na yi ba saboda matsalar rashin wuta da mike fama da shi a yanzu, wutar mu ta samu matsala bama samu kamar kowanne lokaci, dan haka a ƙara haƙuri ba kullum mike samun wuta ba*



*SHALELEN ALHAZAWA*

*Writing and story*

*By*

*Asmeetar Hydar*

(Asma'u Ayuba)


*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*


P. 9





A fusace Sultan ya ƙarasa gurin yana mai ɗauketa da wani rikitaccen marin da yasa kowa miƙewa tsaye, idanuwansa sun yi jajir kamar wuta jikinsa sai rawa yake tsabagen ɓacin rai, da yatsa ya nunata bakinsa na karkarwa ya ce "My Brother........, shine wanda za ki aura? wow Malika wow, ai bansan cewa ke ɗin marar tunani ba ce sai yau, and babban kuskurena shine yarda da ke da na yi, wallahi na yi nadamar saninki a rayuwata".

Sultan ya ƙarasa maganar yana mai barin gurin.


Dad da su Junaid suka rufa masa baya, aka bar Malika na rusa ihu kamar mahaukaciya, iyayenta kuwa sai zagin Sultan da Family ɗinsa suke, ko minti biyu masu kyau basu ƙara a gidan ba suka fito cikin shirin tafiya Nigeria, gaba ɗaya gidan ya ɗauka da surutun mutane sai kukan Malika da ya ƙara cika gidan ita ala dole Junaid take so idan ba haka ba zata rasa rayuwarta.


Jikin Junaid ya yi sanyi sosai ganin son da Sultan ke yiwa Malika, Surayya sai murna take a zuciya tare da zubawa Malika albarka dan ta gama biya mata komi.


Airport suka nufa ran kowa a ɓace musamman Dad da har suka isa Nigeria be ce ƙala ba, ransa ya masifar ɓaci dan ko Sultan ba zai nuna masa ɓacin rai a yau ba.


Tun a airport ɗin kowa ya kama gabansa, su Imran da sister ɗinsa suka nufi gida sai ƙanin Dad wanda shima be ji daɗin abin da ya faru ba, Mom kam sai rarrashin Dad take ganin yanda ransa ya ɓaci, a babban parlour suka sauka kowannensu da abin da yake tunani musamman Sultan, minti ɗaya be ƙara a zaune ba ya miƙe tare da nufar ɗakinsa.

Kamar yanda ya saba haka ya sameta a zaune tana mai kaɗa jelarta sautin dariya na tashi daga bakinta wanda ke ɗauke da mugayen haƙora masu kaifin gaske, cikin fushi Sultan ya damƙo wuyan Zakanyar da hannu ɗaya ya shaƙe har sai da ta fara zare ido "Bari na fara kashe ki kafin burin rayuwata ya gama rugujewa tun da ke ce silar duk halin da nake shiga, na tabbata cewa ke ki ka hana wannan auren ba kowa ba"

Sultan ya faɗa yana mai jifa da ita gefe.


Ɗagowa Zakanyar ta yi a hasale ta doki cikinsa da ƙafa, ai kuwa Sultan ya yi tsalle sama tare da faɗawa kan bed, itama Zakanyar tsallen ta yi tana mai dira kan bed ɗin ta kai masa cizo daidai wuyansa amma sai ta tsaya cakkkk ba tare da ta cije shi ba, a hankali kuma idanuwanta suka fara fitar da ƙwalla wanda hakan ya sa Sultan hugging ɗinta gami da fashewa da kuka shima, sosai suke kukan a tare wanda duk yanda ka kai ga rashin imani idan ka gansu sai ka tausaya musu, tabbas ba ƙaramin abu ke tsakaninsu ba musamman yanda fuskar Zakanyar ta sauya lokaci ɗaya.

Cikin sanyin jiki Sultan ya janyeta yana mai shafa gefen fuskarta "I'm sorry Habibaty na kasa daurewa ne"

Ɗaga kai Zakanyar ta yi tana mai juya fuska "Na sani Sahibina ina son ka ƙara haƙuri har lokacin da burinka da nawa zai cika".

Ta ƙarasa maganar tana mai ɓacewa.

Naushi Sultan ya kaiwa bed ɗinsa a lokacin Junaid ya yi sallama tare da zama fuskarsa a haɗe, ko kallon inda yake Sultan be yi ba ya juya masa baya, Junaid ne ya ce "Me hakan ke nufi? ko kana tsammanin ni na hana Malika aurenka?"


Ɗan sosa kai Sultan ya yi yana mai janyo blanket ya fara rufe jikinsa ganin ya fara sauya halitta zuwa Kada, kasacewar Junaid be lura da hakan ba ne ya sa ya cigaba da faɗin "Ya kamata ka yi magana da ita a yau domin tabbatar da abin da ke faruwa, but please kar ka ɗauki wannan a matsayin laifi"

Miƙewa tsaye ya yi gami da taku ɗaya inda Sultan ke kwance "Amma kamar abin farinciki ne ka rabu da ƴar marassa tabiyya"

Kafin ya ƙarasa maganar Sultan ya ɗaga jelarsa tare da kai masa duka a baya ji ka ke timmmmmm, "Ya subhanallah" Junaid ya faɗa yana mai dafe gurin da Kadan ya dakesa, da sauri kuma ya maida kallonsa kan Sultan da ya rikiɗe zuwa mummunar Kada me ban tsoro, yau lamarin ya fi muni dan har wani baƙin hayaƙi ke fita daga bakinsa, ganin hakan ya sa Junaid ficewa daga ɗakin da yana mai dafe bayansa da ke mugun zafi.


..................
A ɓangaren su Najmeer kuwa sun gama tsara komi har da iyayen ƙarya waɗan da ta saya musu kayan da za su saka masu mafisar tsada, unguwar Rimi suka samu hayar wani haɗaɗɗen gida me hawa uku, sosai gidan ya tsaru tamkar baza a mutu ba, misalin sha ɗaya su Najmeer suka shirya cikin wasu masifaffun kaya masu shegen kyau less ne me tsada milk, anko su ka yi da Meera sai dai kayan sun fi zama daram daƙam a jikin Nameer, mayafinsu black ne kalar handbag da takalmar ƙafarsu wanda ya gaji da haɗuwa.

Meera ce me driving Najmeer ne gefe Mamu kuwa tana bayan mota sai surutu take zubawa ba tare da sanin inda aka nufa da ita ba, suna isa ta yi horn Gate Man ya danna remote nan take ya ɗage masa Meera ta kunna kai ciki, bakin Mamu har yana dalalo yawu tsabagen kallo, kai daga gate ɗin zuwa harabar gidan ya isa tabbatar maka cewar an kashe dukiya me yawa.

"Aljannar duniya" Cewar Mamu tana fitowa.


Meera ta ce "Ai sai mun shiga daga ciki za ki tabbatar da gidan ƙarshe ne"


"Kina nufin wannan duk wasan yara ne? kin ga motoci kamar a gurin saidawa"


"Sosai kuwa Mamu ke dai mu ƙarasa daga ciki"


Meera ta faɗa tare da jan hannunta.


Najmeer na bayansu tana waya da Alhajinta har suka shigo ƙayataccen parlourn me ɗauke da duk wani abun da ake buƙata.

"Wai wai rangammm" Mamu ta kuma faɗa tana mai kama baki, parlour ne me ɗan karen kyau yana ɗauke da kujeru kala uku masu tsadaddun kyau.


Frigde kuwa uku ne ta kowanne ɓangere, sai Tv manya-manya guda biyu.


Bakin Najmeer ɗauke da sallama ta shigo tana mai katse wayar, "Yawwa Mamu kin ga wannan gidan zamu zauna na tsawon sati ɗaya saboda hidimar bikina, ina son ki kasance makauniya kuma kurma, ina nufin duk abin da ki ga gani ki kawar da kai kuma duk abin da ki ka ji ki yi kamar ba ki ji ba"


Mamu ce ta katseta da faɗin "Na boni na lalace ni Mamu tsohuwa ga Najmeer, ke dan ubanki auren ke za ki yiwa kanki da har za ki mayar da ni makauniya da kurma? yoooo ina uwayen da za su ɗaura miki auren bayan Kawunki Jamilu?"


"Mu ne uwayenta kuma jigo a gareta"


Cewar wasu Dattijai da ke saukowa daga upstairs cikin shigar alfarma, Namijin zai kai shekaru hamsin da ƴan kai, sai macen zata kai shekaru arba'in, fuskarsu ɗauke da murmushi.

Cike da tafiyar ƙasaita suka iso tare da zama kan kujera me zaman mutum uku, Mamu na ganin haka ta sauko har ƙasa ta rusuna sai da ta dunƙule hannu kamar me gaida Sarki ta ce "Barka da zuwa ranku ya daɗe, shugaba me daraja sannunku da saukowa"

Dariya ce ta kusa ƙwacewa Dattijan ganin yanda Mamu ke zuba gaisuwa amma sai suka ƙara haɗe fuska kamar yanda Najmeer ta tsara musu, Dattijon ne ya ce "Yawwa Hajiya ya hanya da mutanen gida?"


"Alhamdulillah ai mutane kune mutane ga kuɗi ga mulki, ku kam Allah ya sallemeku"

Mamu ta faɗa tana washe baki.


"To muna godiya tashi ki zauna a sama"

Dattijuwar ta faɗa tana mai murmushi, girgiza kai Mamu ta yi alamun aa, sai da aka yi da gaske kafin ta koma saman kujera, jin ƙarar motoci ne ya sa Meera kama hannun Mamu aka haura da ita sama, Najmeer kuwa ta ƙara tsara musu yanda za su yi sannan ta bi bayan su Meera.


Motoci hamsin ne aka shigo da su gidan wanda daga gani ka san ba ƙananan mutane ba ne, duk inda ka duba manyan Alhazawa ne ke fitowa cikin shigar kamala.


Daga gefe ɗaya Alhajin Najmeer ne sanye da farar shadda ya sha kyau sai murmushi yake, har babban parlour aka yi musu jagora inda suka tarar da Mahaifin Najmeer da Mahaifitarta na ƙarya da ta samo zaune suna mai yi musu maraba, cike da girmamawa aka gaisa kamar dama can iyayen gaskiya ne, ba ƙaramin mamaki Alhajin ya yi ba ganin iyayen Najmeer ko kaɗan basa kama da

Please Login or Register in order to submit comment