Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita, amma hakan be sa ya kawo wani abun a ransa ba, wayarsa ce ta yi ƙara a ladabce ya nemi izinin fita sannn ya fice tare da ɗaga wayar.


Daga can ɓangaren ba ka jin abin da ake faɗa amma Alhajin ya yi shuru da alama ana magana ne, kusan mintuna uku yana saurara kafin ya ce "Idan muka nemi ɗaura auren a yau akwai matsala dan za su iya zargin wani abun, amma a saka ranar auren hakan zai fi"

Ƙara dakatawa ya yi alamun ana masa magana, sai can ya amsa da "Kar ka samu damuwa Najmeer ta zama mallakinka da yardar Allah ta shigo hannu" Sallama ya yi tare da kashe wayar, yana juyowa suka yi ido huɗu da Meera da ke tsaye tana mai sauraronsa, bakinta na rawa ta ce "Dama ba kai za ka auri Najmeer ba wani ka ke nemawa aurenta?"

Da sauri ta juya zata koma ya yi hanzarin kama hannunta "No Meera please ki tsaya ki fahimceni zan faɗa miki koma menene amma sai idan baza ki hana aurennan ba"


Mugun kallo Meera ta watsa masa tana mai ƙwace hannunta "Kana tsammanin za'a haɗa kai da ni a yaudari babbar aminiyata"


"Ba haka nake nufi ba ki fahimceni Meera Oga na ne ke son ƙawarki, kuma baya ƙasar nan kawai ina masa aiki ne har zuwa lokacin da zai bayyana kansa"


"Waye Ogan naka?"

Cewar Meera a fusace.

Sai da Alhajin ya duba gabas da yamma kudu da arewa kafin ya matsa kusa da Meera yana mai rage murya "Zan faɗa miki wannan alƙwari ne amma please kar ki sanar da Najmeer, ga number na sai ki kirani zuwa ajima bayan mun koma duk abin da ke faruwa zan sanar miki"

Ba dan Meera ta so ba ta karɓi numbersa tana mai barin gurin cike da fargaban abin da zai je ya dawo.


Komawa ciki Alhajin ya yi inda ya samu an tsayar da rana sati ɗaya Friday me zuwa za'a ɗaura aure, sosai ya ji daɗin lamarinnan ganin iyayen basu kawo matsala ba, kayan abinci da na sha kuwa sai da suka ture dan ba wani ci suka yi ba, duk abin da suke buƙata akwai shi a gurin, nama ko kala-kala ne kama daga naman shanu naman rago da sauransu.

Million ɗaya suka aje tare da ficewa, sai da suka fito kafin aka kira Najmeer da Meera dan su gaishe da mutane, Najmeer na sanye cikin mayafinta me girma kamar gaske sai sunne kai take, sosai mutanen suka yaba kyawunta da kuma natsuwarta.


Ba wata magana suka yi da Alhajin ba ta koma ciki, sosai ta ji daɗin yanda komi ya tafi yanda ta tsara, a parlour ta sami Mamu zaune ta haɗe ƙafa, ba tare da Najmeer ta kalleta ba ta maida dubanta kan Dattijan da ta hayo ta ce "Yawwa aikin yau ya kammala za ku iya tafiya har sai ranar ɗaurin aure nake buƙatar ganinku, na aje muku abubuwan buƙata da kuɗi a ɗakinku bana da wata alaƙa da ku sai wani satin a ranar da za'a ɗaura aurena" Godiya sosai suka yi mata tare da barin gurin.


Mamu ce ta ce "Au dama ba gidansu ba ne? ikon rabbissamawati, Najmeer hayar iyaye ki ka yi? innalillahi wa inna ilaihir raji'un ni Mamu tsohuwa ga Najmeer"

"Haba Mamu dan Allah ki shafa min lafiya, kema ai farincikin ki ne na yi aurennan ko za ki huta"

"Amma ba irin wannan auren ba ja'irar yarinya me nema mana abin kunya, hauka ake da za'a ɗaura miki aure da gandamemen ƙato kamar wannan"


Cikin fushi Najmeer ta ce "Ai ba a kanki zai zauna ba"

"Ko ba'a kaina zai zauna ba ina ke ina wannan garjejen? ko Ubanki ba zai girmesa ba marar kunya kai"


"Yanzu dai aikin gama ya ri ga ya gama aurena wani sati idan kin isa ki hana" Najmeer ta faɗa tana haurawa sama.

Surutu Mamu ta shiga yi inda take shiga ba tanan take fita ba har Najmeer ta ɓullewa ganinta.


A room ta sami Meera ta yi tagumi jikinta a sanyaye, dafa kafaɗarta Najmeer ta yi hakan ya sa Meera tsorata tana mai dafe ƙirji "Washhhh har kin tsoratani fa"

"Tunanin me ki ke haka? ko Malik ki ke son gani"

Dogon tsaki Meera ta ja tana mai taɓe baki "Kawai na rasa abin da ke min daɗi ne amma ba wani abun ba ne"


Zama Najmeer ta yi tare da fuskantar Meera sosai "Kema kina tsoron kar na auri Dattijo kamar Alhaji ne?"

"Ina tsoron kar ki auri wanda ba ki saniba dai" Meera ta faɗa bata san lokaci ba.

Da mamaki Najmeer ta ce "Me ki ke nufi da hakan, Alhajin ne bansaniba ko me"

Kame-kame Meera ta fara alamun rashin gaskiya "No ina nufin ba ki san halinsa ba"

"Halinsa be shafeni ba idan har yana da kuɗi, ke nifa bana tsoronsa ko shan jini yake sai na aure shi na kwashe masa dukiya dan ubansa"

"Allah ya ba ki sa'a amma fasa wannan auren zai fiye miki wallahi"


"Meera wai meye matsalarki ne? ki barni duniya ta faɗa min amma ba ke ba"

Najmeer ta faɗa tana miƙewa tsaye, sai da ta isa bakin ƙofa kafin ta juyo "Ki shirya zamu tafi wani gida anjima da dare, ina tsammanin kuɗin da ke account ɗina baza su isheni sayen kayan ɗakin da nake ra'ayi ba, shine na yanke hukuncin mu haura ginar wasu"

Najmeer ta ƙarasa maganar tana ficewa daga ɗakin, mamaki ne ya cika Meera har ta kasa koda motsin kirki, a ranta ta ce sata Najmeer ke son mu tafi ko me, gaba ɗaya tunani ya cika mata kai hakan ya sa ta miƙe tare da shigewa toilet.



Misalin ƙarfe ɗayan dare ne Najmeer da Meera suka fito cikin shigar baƙaƙen kaya kana ganinsu ka ga ɓarayin dare, fuskarsu a rufe har suka fito harabar gidan, Najmeer ce mazaunin dirver Meera na gefe cike da fargaba, duk wannan abin da ake Mamu na ciki tana bacci bata san wainar da ake toyawa ba, cikin sauri Najmeer ta yi horn gate man ya wangeme ƙofa.


Tun da suka fara tafiya Meera ta kasa samun natsuwa, dole ya sa ta tambayi Najmeer inda za su tafi, murmushi Najmeer ta saki wanda ya bayyana kyawunta "Gurin Malik za mu tafi"

Zaro ido Meera ta yi a tsorace "Malik kuma, me zamu yi a gurinsa?"

"Fashi zamu je a gidansu Sultal"

"Innalillahi ki rasa inda zamu tafi fashi sai gidansu Sultan, dan Allah ki rufa mana asiri dan wallahi wannan karon haɗuwarku baza ta yi daɗi ba"


"Kin ga Meera idan baza ki iya ba tun yanzu ki sanar da ni na aje ji kan hanya, abin da ya sa nake son mu tafi da Malik na tabbata ba zai rasa bindiga a gurinsa ba"


"Hmmm na shiga uku ni Meera yanzu kina nufin Sultan ba zai ganemu ba"


Dariya me sauti Najmeer ta yi a karo na farko "Kalli yanda muka yi shigar jikinmu na tabbata ko Malik ba zai gane mu ba balle wani banza Sultan"

A haka suka cigaba da surutun har unguwarsu Malik, a bakin gate Najmeer ta tsaya tana mai faɗin "Ki shiga ki duba idan yana ciki lokaci na tafiya yanzu ƙarfe ɗaya da rabi ta kusa bugawa"

A ɗan tsorace Meera ta ce "Sai dai ke ki shiga ko mu shiga a tare"

Ba yanda Najmeer ta iya dole suka nufi cikin gidan, daga harabar kana jiyo sautin waƙa na tashi da kuma hayaniyar mutane, hakan ya sa Najmeer ɗaga ma Meera hannu alamar ta tsaya, a hankali Najmeer ta kunna kai cikin ɗakin tana mai yaye labulen, maza da mata ne cike ana shaye-shaye wasu na gefe sai zuba iskanci ake, daga gefe kuwa Malik ne zaune yana zuƙar shisha, ɗago kai da zai yi suka yi ido huɗu da Najmeer, cikin layi ya miƙe tare da ɗaga hannu alamar kowa ya dakata, nan fa gurin ya ɗauki shuru.

Malik ne ya ce "Ke kuma wacece haka kamar ƴar daba?"

Meera da ke bayanta ne ta ce "Malik Meera ce"

Jin abin da aka ce ne ya sa duk mutanen ɗakin sakin shewa da ihu, Najmeer ce ta ce "Ya isa haka please, Malik muna son ganinka akwai wani babban aiki da za ka yi mana zan biyaka Dubu ɗari biyar"

Cikin sauri Malik ya ƙaraso gurin Najmeer har jikinsa na rawa "Dubu ɗari biyar? mu tafi yanzunnan zan aikata duk abin da ki ka yi umarni"

"Good hakan nake son ji, amma ina buƙatar maza biyar daga cikinku waɗan da ke da makami a hannunsu"

Kafin ta rufe baki wasu manyan ƴan iska suka fito bakinsu ɗauke da sigari, kana ganinsu ka ga Tantiran gari, ɗaya daga cikinsu ne ya ce "Shugabata ni a ganina me zai hana mu bari zuwa gobe saboda mu yi shirin da babu wanda zai gane mu, na tabbata babban aiki ne tun da har ki ka ambaci makamai"

Najmeer ce ta ce "Ƙwarai kuwa babban aiki ne ina buƙar bindigogi masu rai da lafiya"


"Gaskiya ƙwara ɗaya muke da a gurinmu shima dan kare lafiyarmu ne idan wasu kafuran sun durfafo mu, sai dai waɗan da babu bulet a ciki"

Malik ya faɗa yana huhhura hanci.

Meera ce ta ce "Muna buƙata a hakan tun da ba kisan kai zamu yi ba, yanzu wanne lokaci zamu fito goben?"



"Daidai wannan lokacin" Malik ya bata amsa.



Godiya Najmeer ta yi musu kafin suka fice daga gidan.



Washe garin ranar tun da safe Mamu ke zuba masifa wanda ya hana kowa bacci, dole ta sa Najmeer fitowa room ɗinta sanye cikin kayan bacci da alama surutun Mamu ne ya tashe ta, a ƙufule Najmeer ta ce "Wai Mamu lafiya ki ka tasa mu gaba kamar waɗan da suka kashe miki wani naki"


Mamu da ke zaune kamar an dasa ta ne ta ɗago sai kuma ta ja dogon tsaki har tana rusunawa kamar me roƙon gafara "Ina fa lafiya yanzu nake jin labari a redio wai yaron hamshaƙin me kuɗinnan Chief da ke G R A ya tafi neman aure a ƙasar London amma matar ta ce yayansa take so ba shi ba, gaskiya lamarin akwai ban tausayi" Mamu ta ƙarasa maganar tana share hawaye kamar wadda ɗan uwanta ya mutu.

Najmeer ce ta ɗan taɓe baki tana faɗin "Meye sunan yaron da aka ce? na san baza su rasa faɗin sunansa ba"

Ɗan shuru Mamu ta yi alamun tana tunanowa, Meera da ke saurarensu tun lokacin da suka fara ne ta ce "Sultan Chief ko Mamu"

Carafffff Mamu ta karɓe zancen "Ƙwarai kuwa Sultan Chief yaron kirki me addini da sanin ya kamata ga ibadah, gaskiya shegiyar baturiyarnann ta yi asara"

"Wai ke Mamu kin san shi ne da ki ke yabonsa haka? har da wani faɗin me addini imma shine limamin unguwarsu wannan matsalarsu ce ni be shafeni ba"

"Dama ai ban ce taki matsalar ba ce shashashar banza, abun baƙin ciki ya sami ɗan Lajeriya ai dole na yi kuka"


Bushewa da dariya Meera ta yi kafin ta ce "Nigeria ake cewa ba Lajeriya ba"


"Sannu iyawa matar iyayi ina ruwanki da yanda na faɗi sunan ƙasata? na fahimci baƙin ciki ku ke yi dan be auri ƴar ƙasarku ba ya tafi neman aure wata ƙasar"


Haushin maganarta ne ya sa Najmeer barin gurin cike da tsanar Sultan ɗin a ranta, a duk lokacin da ta tuna shi ko ta ji an kira sunansa wani mugun haushinsa ke taso mata musamman yayansa Junaid.




Kamar yanda suka tsara a jiya haka kuwa aka yi ƙarfe ɗaya da rabi ta yi musu ne a bakin gate ɗin su Malik, duk wanda ya ga shigar da ke jikinsu ya san ba alkhairi za su shuka ba, musamman Najmeer da ko yaya ka san fuskarta ko kuma yanayinta baza ka taɓa ganeta ba, Malik ma sun rurrufe fuskarsu kamar yanda su Najmeer ɗin suka yi, mota ɗaya ce ta kwashe su zuwa gidansu Sultan Najmeer ce me driving cike da gadara har suka iso babban gate ɗin gidan, nan fa kowa ya fara shiri Meera da Najmeer na riƙe da bindigogi, bindigar da ke hannun Najmeer ce kawai me bulet amma sauran fanko ne.



Cikin biyayya Malik ya ce "Shugaba kina nufin gidansu Sultan Chief zamu yi fashi?"

Sai da Najmeer ta yi dariya irinta riƙaƙƙun ƴar tasha kafin ta ce "Sosai ma kuwa duk yawan masu tsaron gidannan ba zai hana mu shiga ba, ku dai kawai ku jira ni a mota kar wanda ya yi motsi har sai na ce ku shigo"

Ba tare da tsoron komi ba Najmeer ta fito motar, gaba ɗaya ƙofar gidan akwai haske kamar ba dare ba, duk fitilun gidan sun haske ko'ina, ta bayan gida Najmeer ta koma yanda su Meera baza su ganta ba, cikin secons uku ta rikiɗe zuwa Mage tare da haurawa kan ginar gidan ta faɗa ciki, a hankali take tafiya har ta kawo bakin gate ɗin, sai da ta tabbata masu tsoron gidan sun jima da bacci kafin ta danna wani madanni da ke bada haske, gaba ɗaya wajen gidan da harabar gidan ya yi duhu fitulun suka ɗauke.

Lokaci ɗaya ta rikiɗe zuwa mutum, me gadin ne ya fito ganin haske ya ɗauke, a tsaye ya ga mutum na ƙoƙarin buɗe gate, har ya buɗe baki da niyar magana Najmeer ta nuna shi da yatsa ai kuwa bakinsa ya kasa motsi kamar an manne shi, kuma ya kasa matsawa daga inda yake tsaye.


Ganin haka ya sa Najmeer buɗe gate tare da ba su Malik umarnin shigowa daga ciki, ba ɓata lokaci suka kunno kai cikin gidan kowannensu riƙe da mugun makami, dirrect parourn gidan suka nufa wanda Najmeer ke da tabbacin daga nan za su fara.





*Na gama typing tun ƙarfe biyar na yamma wuta ne ya hanani post, Mu je zuwa yanzu aka fara*






*SHALELEN ALHAZAWA*

*Writing and story*


*By*

*Asmeetar Hydar*


(Asma'u Ayuba)


*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*


P. 10

Littafi ya ɗauki zafi ya fara gangara wannan dalilin ne ya sa na ga ya dace na tsayar da free pages haka, kar ku bari wannan labarin ya wuce ku domin za ku nishaɗantu da ilmantuwa tattare da shi, akwai suger sosai tare da wannan book sai kun karanta za ku tabbatar da hakan, ga masu buƙatar cigaba da karanta book ɗin Shalelen Alhazawa sai su biya 500 ta wannan Account 3137937874 tani Bako first bank domin tabbatar da shaidar biyan kuɗi sai ku tuntuɓi wannan number ta WhatssAp 08082589590 ko kuma ku kira wannan number 08164403726 idan har ba waɗannan numbers ku ka tuntuɓa ba a gaskiya ba ni ba ce dan kar a yaudareku da sunan za'a ba ku book ɗina












Najmeer ce a gaba sai wani huhhura hanci take ita ala dole ƴar fashi har abin ma ya so ya ba Meera dariya amma sai ta matse tare da rufa mata baya, suna shiga parlourn Sultan suka tarar zaune ya haɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yana mai zuba musu ido.


A tsorace su ka ja baya gami da rirriƙe juna, lokaci ɗaya Meera ta saki fitsari ita da Malik wanda duk ya daburce saboda tsoro.


Jin saukar ruwa ne ya sa Sultal miƙewa tsaye.

"What ƙarar me nake ji haka?"


Meera ce ta yi saurin cewa "Malik ne ya saki fitsari wallahi"


"Ƙarya take ita ce ta yi fitsari idan ba ka yarda ba a duba jikinta, har za ki wani laƙa min tun da kin raina ni"


Sauran samarin ne suka juya da niyar tserawa Sultan ya daka musu tsawa "Gidan uban wa za ku tafi? ai sai kun aikata abin da ku ka zo aikatawa ko kuma duk na ɗaureku"


Samarin na jin haka suka fashe da kuka kamar ba gardawa ba har da majina.



Najmeer ce ta ce "Mtssss wai lafiya ku ke kuka kamar waɗan da aka yiwa mutuwa?" Kallonta ta mayar kan Sultan tana mai haɗe fuska "Kai ina iyayenka da mutanen gida?"


Shuru Sultan ya yi yana tunano inda ya san wannan muryar amma ya kasa tunawa, be gama nazarin ba suka fara jin saukowar mutum daga sama.


Mom da surutu ya tashe ta daga bacci ne ta ƙarasa saukowa, ai tana ganin ƴan fashi ga bindigogi a hannu ta ja baya a tsorace "Ƙalu innalillahi wa inna ilaihir raji'un, me zan gani haka"

Har ta juya da niyar komawa Najmeer ta daka tsalle ɗaya tare da dira a gabanta, bindiga ta auna saitin kanta "Idan ki ka yi motsi sai na fasa miki kai"


Sosai Mom ta tsorata dan shi kansa Sultan ya ɗan razana ganin an ɗora bindiga a kan Mahaifiyarsa "Kin ga ki sauke wannan bindigar duk abin da ki ke so zamu ba ki amma kar ki taɓa lafiyarta" Sultan ya faɗa cikin sanyin murya.

Dariya Najmeer ta bushe da shi sannan ta ƙara haɗe fuska "Na zata ba ka iya magana me daɗi ba, je ka kira min mutanen gidannan kafin na fasa kan wannan matar"

Cije lips Sultan ya yi ransa na zafi ya nufi sama, dakatar da shi Najmeer ta yi kafin ta ce "Ɗaya daga cikinku ya bi bayansa dan kar ya yi izgilancin kiran jami'an tsaro"


Duk da cewar Malik na tsoro haka ya rufa masa baya suka nufi sama, ba jimawa suka sauko tare da su Dad har da Junaid da ke tambayar dalilin da ya sa Sultan tashinsu cikin wannan daren.



Tsayawa suka yi ganin abin da ke faruwa, ga Mom hannun Najmeer an ɗora mata bindiga, cikin zafin nama Junaid ya nufeta da niyar karɓe bindigar, Najmeer kuwa ta ƙara saita Mom tana faɗin "Kana ƙara taku ɗaya zan ɗauke ƙwaƙwalwarta" Dole ta sa Junaid ja baya yana mai naushin iska.


"Kai marar kunya ko? sarkin zuciya"


Jin abin da ta kuma cewa ne ya ƙara fusata Junaid da Sultan, Dad ne ya ce "Ƴarnan me ku ke buƙata da mu?"


"Kuɗi mike so da gwalagwalai"

Najmeer ta amsa masa.


Malik ne ya ce "Gaba ɗayanku ku rage tsayinku tun kafin na fasa kanku"


Be gama rufe baki ba Mom da Dad suka rusuna ƙasa gami da ɗaga hannu, Junaid da Sultan kuwa sai da suka ja lokaci kafin Sultan ya fara rage tsayinsa sai kuma Junaid, dogon tsaki Najmeer ta ja rai ɓace "Na ga alamar da sauran raini a idanunku zan koya muku yanda ake ladabi"


Ɗaga ma Meera hannu ta yi alamun ta zo, cike da ɗari Meera ta iso Najmeer ta ce "Ki saita kan wannan matar daga zaran ɗaya daga cikinsu ya yi wani yunƙuri ki ɗauke kanta da bindiga"


"An gama Shugaba" Meera ta amsa.

Najmeer da Dad ne suka nufi ɗakinsa tana bayansa sai waige-waige take.


Har room ɗinsa suka shiga ya tattaro kuɗaɗe masu yawa tare da zubewa kan bed jikinsa na rawa, "Nawa ne wannan?" Cewar Najmeer tana ƙara auna masa bindiga.


Dad ya ce "Million goma ne"


"Baza su isheni hidimar bikina ba ka tura min ta account"


"Bikinki baiwar Allah?"

"Yes bikina aure zan yi kuma kuɗin da nake da baza su isheni haɗa kayan ɗaki ba shiyasa na yanke hukuncin na nemi kuɗi da ƙarfin iko na" Najmeer ta faɗa tana yarfa ido kamar ƴar daba.


Jikin Dad a sanyaye ya ce "Amma idan baza ki damu ba akwai wasu tambayoyi da zan yi miki"


"Faɗi yambayarka da sauri dan banada lokaci"


"Tambayar shine dama ke ƴar fashi ce ko kuma wannan dalilin ne ya sa ki ka fara zuwa fashi?"


Ɗan tsayawa Najmeer ta yi tana mai gyaɗa kai sai kuma hawaye ya zubo mata da sauri ta share dan kar Dad ya gani amma abin da bata saniba shine Dad ya ga lokacin da take share hawayen, kan bed ya zauna a hankali ya ce "Ina iyayenki suke?"


Wannan tambayar ce ta girgiza Najmeer hakan ya sa ta fashe da kuka gami da sakin bindigar da ke hannunta, sosai tausayinta ya kama Dad tare da jin wani abin a ransa game da yarinyar amma ya kasa gane menene wannan, sai da Najmeer ta ci kukanta Dad kuwa be hanata ba dan ya san akwai abin da ke damunta a zuciya, ƙyallen da ke fuskarta ta cire nan take kyakykyawar fuskarta ta bayyana lokaci ɗaya gaban Dad ya faɗi har ya miƙe tsaye be san lokaci ba, jikinsa na rawa ya ce "Yarinya wacece ke?"


Jin tambayar da ya sake yi mata ne ya sa Najmeer faɗin "Ba kowa ba ce ni face marainiya wadda ta rasa uwa da uba tun bata san komi ba, na kasance talaka me ƙaramin ƙarfi wadda ta ɗauki rayuwa irinta manyan yara, a halin yanzu na saba da daula ba zan iya rayuwa cikin talauci ba"


"Amma meyesa ki ka zaɓawa kanki mummunar rayuwa irin wannan?"


"Saboda haka suke son ganina cikin rayuwar shiyasa na nuna musu cewar zan aikata fiye da yanda suke so?"

Mamaki ne ya kama Dad dan be san su waye take magana ba, kawar da zancen ya yi da faɗin "Akwai inda ki ke zama ne? ina nufin tare da wa ki ke zaune a yanzu?"


"Gurin Mahaifiyar Mamana ita ce me kula da ni"



Jinjina kai Dad ya yi kafin ya ce "Na ɗauki nauyin komi na bikinki har da gidan da za ku zauna ke da mijinki, kuma na ɗauki nauyin komi naki ke da Kakarki za ku dawo gidana da zama duk abin da ku ke buƙata ki min magana, na lura sosai akwai babban al'amari tattare da ke"

Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce "Kina makaranta ne?"


"Primary kawai na yi daga nan ban ƙarasa ba, a gefen islamiyya na yi haddar alqur'an da sauran littafai" Ba ƙaramin burge Dad ta yi ba jin ta yi karatun islamiyya sosai.



"Ya sunanki?"


Ya sake tambayarta.


"Sunana Najmeer"


"Masha Allah Najmeer daga yau kin zamo ƴata kuma na yi alƙwarin riƙe ki hannu bibbiyu, yanzu ku koma gida amma kafinnan ki bani address ɗin gidanku zamu shigo zuwa gobe"


Godiya sosai Najmeer ta yi masa tare da bashi address ɗinsu, haka kawai take jin Dattijon har cikin ranta, a zuciya take faɗin amma Sultan ya yi sa'ar Mahaifi ba kamar shi me mugun hali ba.


Sai da ta rufe fuska kafin suka fito daga ɗakin.



Ba su Meera ba hatta su Junaid sun sha mamakin ganin Dad da Najmeer na saukowa cikin fara'a da annashuwa kuma ba komi a hannunta alamun bata karɓi kuɗin da ta ce ba.


Ai basu ƙara tsinkewa ba sai da suka ga Dad ya ce "To sai da safe a gaida mutan gida"


Najmeer na murmushi ta ce "Mutan gida za su ji Alhaji"

Ɗan ɓata fuska Dad ya yi alamun ya yi fushi "Kar ki sake kirana Alhaji ki kirani da Dad kamar yanda sauran Ƴan uwanki ke kira na"

"Afwan Dad ba zan ƙara ba"


"Yaww Allah ya yi miki albaka"


"Ameen Dad" Najmeer ta amsa tana mai kallon su Meera ta ce "Mu tafi ko" Ficewa daga gidan ta yi su Malik na bayanta kamar raƙumi da akala cike da al'ajabi.



Sultan ne ya ce "Dad me nake shirin gani, kana nufin wannan ƴar fashi ka ke kira da ƴarka?"

Kusa da Mom Dad ya zauna yana faɗin "Ƙwarai kuwa labarinta abin tausayi ne, shiyasa na yanke hukuncin dawo da su gidana tare da ɗaukar nauyin aurenta saboda shine dalilin da ya sa ta shiga wannan halin"


"Wallahi ba zai taɓa yuwa ba, babu wanda zai kawo mana ƴar fashi cikin gida" Mom ta faɗa a zafafe.

Junaid de ya kasa furta komi sai kallonsu da yake, tashi Dad ya yi yana mai gyara zaman rigarsa "Magana ta rage gareku hukunci na yanke ba wanda ya isa ya karya dokar da na shimfiɗa, dole su dawo gidana da zama"


Ba tare da ya kuma cewa komi ba ya nufi room ɗinsa.


Mom na masa magana amma ko gefen da take be kalla ba, bayansa ta bi tana kiransa tare da faɗin ba wanda zai kawo musu ƴar fashi cikin gida amma Dad ko a jikinsa sai ma shigewa ɗakinsa da ya yi.

Tsananin takaici ne ya hana Junaid ɗagawa daga inda yake Sultan ko sai huci yake kamar kumurcin maciji.



Su Najmeer kuwa tun da suka fara tafiya ba wanda ya ce ƙala har suka iso ƙofar gidansu Malik, anan Najmeer ta tura masa kuɗin da ta yi masa alƙwari har ma da ƙari, sosai ya rinƙa yi mata godiya tare da sauran samarin.


Barin gurin suka yi ganin ukun dare ya yi, gudu Najmeer ke yi kan titi har suka iso gida, Meera dai ta aje tambayoyinta dan ta san baza

Please Login or Register in order to submit comment