Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta samu amsa a yanzu ba.


A gajiye ta shige toilet dan watsa ruwa ga ciyon kai da ke damunta, nan kuma ta ji tunanin Prince ya faɗo mata a rai lokaci ɗaya ta saki murmushi tana mai lumshe ido, a hankali ta furta "Miyar yauƙi....." Yanda ta ja sunan ne ya bata dariya ai kuwa ta shiga dariya ita ɗaya a bayi, ta ɗauki mintuna goma kafin ta fito tana mai tsane gashin kanta.


Kan kujerar da ke gaban mirrow ta zauna sannan ta fara shafa mai, a hankali Meera ta ɗago tana faɗin "A gaskiya lamarinki na rikitani Najmeer"


"Meyesa ki ka ce hakan?"

"Kin san abin da nake nufi ai, shi kuma Dad ɗinsu Sultan a ina ki ka san shi? ko yana cikin Alhazawanki ne"


Bushewa da dariya Najmeer ta yi "Wai dama duk wannan ya sa ki ke faɗin haka? mtsss ni fa ko saninsa ban yi ba kawai taimaka mana zai yi"


Duk abin da ya faru Najmeer ta kawashe ta sanarwa Meera, cikin kiɗima Meera ta ce "Mun shiga uku kina nufin gidansu Sultan zamu koma da zama? ai kuwa akwai babban tashin hankali marar ƙarshe"


"Ke dallah Malama babu wani tashin hankali sai dai ayi ta gwarama duk rana ta Allah, dan ba zan raga musu ba har uwarsu me ɗaure musu suna yanda suke so, ke har Junaid sai na koya masa hankali a gidannan dan bawa zan maida shi"

Dariya Meera ta fara har da riƙe ciki "Junaid ɗin ne za ki mayar bawa? lallai akwai yaƙi a gabanki"



"Au kina ɗauka ba zan iya ba kenan? ai zamu gani sai ki zuba ido tun da tare da ke zamu zauna a gidan sai kin ce na faɗa miki"


Jinjina kai Meera ta yi "Hmmm nikam zan ga chakwakiya Sultan Junaid Meera a gida ɗaya ai kuwa sai gidannan ya kama da wuta"


"Hhhhhhh kin ga Meera barni haka dan Allah bacci nake ji gobe zamu ƙarasa wannan zancen" Najmeer ta faɗa tana mai hayewa kan bed.



..........................

A gefen su Sultan kuwa yau tun da garin Allah ya waye Mom ta hana masu aiki girka komi a gidan, Sultan da Junaid ma a office suka karya, Dad kam be ƙara bi ta kanta ba dan ya san duk wannan abin da take saboda su Najmeer da zai kawo gidan ne.

Har yamma ta yi Mom ta kasa samun natsuwa, wayarta ta ɗauka tare da latsa numbern ƙawarta Hajiya Halima bugu ɗaya ta ɗaga tana mai faɗin "Da girman kujerarki manya-manya maganin ƙanana"

Cikin damuwa Mom ta ce "Hajiya Halima ina da damuwa wallahi na rasa yanda zan ɓullowa wannan lamarin?"


"Subhanallahi me yake faruwa ne? fatar dai ba aure Alhaji zai ƙara ba?"


Mom ne ta ce "A a ko ɗaya amma kamar auren ne, dan duk wanda zai kwaso maka talakawa ƴan fashi da makami ya kawo cikin gida ai kamar kishiya ce ya ƙaro maka"


"Banganeba Hajiya Salma ki yi min yanda zan fahimta" Sai da Mom ta sauke ajiyar zuciya kafin ta kwashe duk abin da ya faru ta zayyanawa Hajiya Halima.



"Kutumar ubancan, yanzu Alhajin ya rasa waɗan da zai kawo gidansa sai yarinyar da ta tashi kasheki da ƴaƴanki? wai tsaya ki ka ce ya maidata ƴarsa, bakya tsoron ya tattara dukiyarsa ya mallaka mata"

A rikice Mom ta ce "Ƙarya ne wallahi ai baza ta saɓu ba, idan har suka shigo gidannan da ƙafarsu za su koma dan sai na hana su zaman lafiya"


"Yawwa ƙawata ki hana su shan iska dan lamarinnan ya fi a zuba ido dole ki tashi tsaye tun kafin a rabaki da kowa naki"

Cewar Hajiya Halima tana mai ɗaga murya, sosai maganganunta suka shigi Mom har ta ƙara jin ƙarfin gwuiwa.

Sallama suka yi a kan cewa za su yi waya anjima.


Junaid ne ya shigo Sultan na rufa masa baya da alama daga aiki suka fito bakinsu ɗauke da sallama, yau an yi sa'a Sultan har da gaisuwa.


A gajiye Junaid ya ce "Mom ina wuni?"

"Lafiya ina Dad ɗin naku? ko da yake Sultan kai zan tambaya tun da a guri ɗaya ku ke"


Kallon Junaid Sultan ya yi alamun ya faɗa ko ya yi shuru, Mom ce ta kuma cewa "Sultan magana nake ina Dad ɗinku?"


"Ya tafi ɗauko ƴar fashi da ahalinta"


Sultan ya faɗa yana mai barin gurin, salati Mom ta rafka har da tafa hannu "Shikenan za su raba ni da mijina, saura kuma ƴaƴana da alama wannan shegiyar yarinyar masifa ce a rayuwarmu tun da har an fara ta kan uban ƴaƴana"

Junaid ne ya ce "Mom please ki kwantar da hankalinki Dad ya ce yarinyar nan ba halinta ba ne kuma ya ce aure ma zata yi"

"Kai amma shashasha ne marar tunani, kana ganin za'a raba ku da dukiyar mahaifinku amma ko a jikinka"


"Ki gafarceni Mom amma a ganina kamar taimako ne wannan"

"Taimakon ubanka na ce taimakon ubanka zai yi? ba dan Allah ya sa ina da rabon shan ruwa ba da yanzu na daɗe da mutuwa, a gaban idonka shegiyar yarinyar ta ɗoran bindiga a kai amma ka ke faɗin taimako tashi ka bani guri tun kafin ranka ya ɓaci, na lura kaine ka biyo halin uban naka gurin taimakonku wata rana sai kun haɗu da Aljana"

Mom ta ƙarasa maganar rai ɓace, haƙuri Junaid ya bata kafin ya nufi room ɗinsa, sanin cewa duk abin da zai faɗawa Mom a yanzu baza ta saurare shi ba balle ta yarda.



Dad kuwa har bakin gate ɗin suka isa tare da horn gate Man ya buɗe musu dan Najmeer ta faɗa masa cewar tana da baƙo, motoci hamsin ne masu uban kyau da ɗaukar ido, har pearking space suka isa sosai mamaki ya kama Dad ganin gidan da su Najmeer ke ciki.




A parlour Maryam ta masa rakiya tare da zube masa kayan abinci kala-kala, dan Najmeer ta dawo da Maryam nan gidan kafin su koma nasu gidan.


Ruwa kawai Dad ya sha dan baya jin yunwa, ba jimawa Meera da Najmeer suka shigo sai Mamu da ke bayansu, Najmeer ce kawai ta yi shigar banza dan wando ne daidai santala santalan cinyoyinta da ƴar ƙaramar riga me gajeren hannu, ba ƙaramin kyau shigar jikinta ta yi mata ba, kallo ɗaya Dad ya yi mata ya sauke kai ƙasa, Mamu kuwa har ƙasa ta tsuguna tana gaishe shi da sauri Dad ya miƙe yana mai faɗin "Haba Hajiya dan Allah ki miƙe ai ni ne ya dace na gaisheki, fatar mun sameku lafiya?"

Bakin Mamu na rawa ta amsa da "Lafiya ƙalau Cheif ya jama'a da hidima" Sai da Dad ya yi murmushi kafin ya ce "Alhamdulillah, amma Hajiya ya aka yi ki ka sanni har haka" Caraffff Mamu ta karɓe da cewa "Ai Najmeer ce ta ce za ka zo gidanmu a yau, na zata ƙaryar da ta saba ce ta sharara min ashe lamarin azimun ne, Allah ya yi da rabon zamu gana"


"Masha Allah abin da jikanyarki ta faɗa miki gaskiya ne tashi ki zauna kan Kujera" Dad ya faɗa yana nuna mata guri, Najmeer da Meera ko suka gaishe shi cikin girmamawa, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Najmeer je ki saka hijab ki dawo" Har zata yarfa masa magana sai kuma ta kasa saboda gwarjinin da ya yi mata, dole ta sa ta nufi room dan ɗauko hijab ba dan tana so ba.

Sanye cikin ƙaton hijab ɗinta ta fito tana tura baki, anan ta samu Mamu sai zuba zance take babu abin da bata sanarwa Dad ba har da auren da Najmeer zata yi da kuma iyayen ƙarya da ta hayo, sosai Dad ya girgiza jin cewar Najmeer ƴar bariki ce, a ransa ya ce shiyasa bata kunyar irin wannan shigar, kusa da Meera ta zauna tana mai haɗe fuska.


Sai da Dad ya ƙare mata kallo kafin ya ce "Najmeer gaskiya kin aikata babban kuskure, kuma kina cikin aikatawa, ina ki ka taɓa ganin mace ta sakawa kanta rayuwar ƙarya irin haka? bakya tsoron mijin da za ki aura ya gane ke wacece?"


Sunkuyar da kai Najmeer ta yi alamun kunya, sai kuma ta ɗago tana mai kallon Dad idanunta sun ciko da ƙwalla "Wallahi ban taɓa aikata zina ba, kuma bansan daɗin zina a rayuwata ba, ko wannan abin da nake ba yin kaina ba ne, addu'ar ku kawai nake nema amma ba zan iya daina yawo da rayuwar ƙarya ba ko da kuwa aure na yi"


"Hehehe haukar banza waye ki ke cewa ba ki taɓa aikata zinar ba? je ki faɗawa shashashu amma ba mu ba, wasu lokutan ko gida bakya kwana kina can gurin yawonki na banza da wofi shine za ki ce ba ki taɓa kwana da namiji ba, ashe haihuwar jiya-jiya ce mu da ki ke faɗa mana shirme"

Mamu ta faɗa tana mai jan dogon tsaki, Meera ce ta ce "Ni shaidata ce Najmeer bata taɓa aikata zina ba, saboda yanda take riƙo da addini ba zai barta ta aikata wannan babban laifin ba saboda ita sallah ma tana ƙarawa bawa imani a ransa musamman idan yana yinta cikin lokaci"


Harara Mamu ta gallawa Meera "Yooo ai duk halinku ɗaya kawai ƙarya ce Najmeer ta fiki iyawa da kuma wayewa, amma yanzu zata iya buga waya ta ce gasu nan hanyar zuwa wata ƙasar ita da ƴan gidansu alhalin ko hanyar da jirgi ke bi bata saniba" Dariya su Dad suka kwashe da shi har da Najmeer jin abin da Mamu ke faɗa, kuma sai ta haɗe fuska sosai tana ɓaro zance.


Dad ne ya ce "Okay yanzu dai shikenan, ni kaina duk da cewar daga jiya zuwa yau na san wannan jikanyar taki amma zan iya yarda da abin da ta faɗa, kuma na yanke shawarar za ku koma gidana da zama amma da sharaɗi"


"Faɗi sharaɗinka Alhaji da yardar Allah zamu kiyaye"


Cewar Mamu cikin zumuɗi.

Gyara zama Dad ya yi kafin ya maida kallonsa kan Najmeer ya fara da faɗin "Da farko za'a tsayar da maganar aurenki har lokacin da ki ka fara makaranta ina son ku shiga School ke da wannan ƙawar taki na ji kakarki ta ce sunanta Meera, sharaɗi na biyu za ki daina kwana waje har abada, sharaɗi na uku za ki daina ƙarya"



Waro ido Najmeer ta yi sai kuma ta girgiza kai alamun baza ta iya ba, "Nikam ba zan daina kwana waje ba, kuma bana son makarantar da za ka saka ni zancen ƙarya kuma sai dai idan ba'a kirani ba"

Meera da ke gefe ne ta danne dariyarta ganin Najmeer ta dage baza ta daina halayyarta ba, ajiyar zuciya Dad ya sauke kafin ya kuma cewa "Dan Allah ki min wannan alfarmar ko dan matsayin ƴata da na ɗaukeki" Kallonsa Najmeer ta yi sai kuma ya bata tausayi, cikin shagwaɓa ta ce "Zan daina insha Allah amma sai kun bini a hankali saboda shi me hali a sannu yake dainawa"

"Shikenan na gode, zancen auren fa?"

Dad ya faɗa yana murmushi.


"Shima na fasa har sai na fara school, amma ni zan zaɓawa kaina makarantar da nake so"

"Okay fine duk makarantar da ki ke so zan saka ki da yardar Allah, ku shiya komi naku zuwa gobe zan turo a je da ku gida"



Cikin farinciki Najmeer ta rinƙa masa godiya, barin Mamu wadda har da kukanta, itama Meera ta masa godiya sosai da kuma addu'a.


Har gurin motocinsa suka yi masa rakiya kafin suka dawo ciki.


Tun a parloun Mamu ke sakawa Najmeer albaka, "Ƴar nan kin gama biya min Allah ya jiƙan magaba, wai yau ni ce zan shiga gidan Chief shugaban masu kuɗin garin Jos" Sai kuma ta ƙara fashewa da kuka har da kwanciya a ƙasa, taɓe baki Najmeer ta yi "Wai ke Mamu meye haka ne? idan na ga dama sai na ce ba inda zamu tafi"

Zumbur Mamu ta miƙe kamar zararra "Amma kin cika ƴar baƙin ciki me mugun hali, da farko kin cewa Cheif baza ki daina halayyarki ba yanzu kina faɗin za ki fasa zuwa gidan, idan kin fasa bakya wa Allah"

"Haka ki ka ce ko? shikenan na fasa zuwa"


"Au da gaske ki ke kenan? har da ƙara maimaitawa"

"Dama a zatonki ƙarya ne, yanzu ma zan bar gidannan sai na yi kwana uku kafin na dawo akwai wani suger Daddy wanda nake son mu shaƙata da shi"

"Waye kuma Sugari Daddyn?"

"Suger Daddy aka ce ba Sugari Daddy ba, saurayina kenan amma kuma ya haifeni a shekaru"

Najmeer ta faɗa tana mai jifa da hijab ɗin jikinta dama ya dameta sosai.

Bata jira abin da Mamu zata ce ba ta nufi room ɗinta tare da juya hips kamar wadda ke yin hakan da saninta.




...........
Tun a harabar gida Dad ya hangi Mom riƙe da ƙugu sai huci take har motocinsa suka tsaya, ba tare da ya ce uffan ba ya nufi hanyar parlour fuskarsa a ɗaure, ganin ba wanda ke biye da shi ne ya sa ta sauke ajiyar zuciya tana mai bin bayansa, "Sannu da zuwa Alhaji an dawo lafiya"


"Da ban dawo lafiya ba za ki ganni?"

Dad ya faɗa a taƙaice.


"Laifin me na yi haka? da ake ƙoƙarin sauke haushi kaina"

A fusace Dad ya juyo fuskarsa babu alamar wasa ya nunata da yatsa "Ki maida hankali ki saurareni da kyau Salma, na lura daga jiya zuwa yau akwai abin da ke damunki wallahi ki shiga hankainki bana cikin irin mazan da matansu ke juya su, idan har kina son zaman lafiya dole za ki girmama duk wanda na kawo gidannan a matsayin nawa"


"Amma Alhaji......." Saurin ɗaga mata hannu ya yi "Ban son jin komi daga gareki, in kina son zaman lafiya ki tabbata cewa gobe idan baƙina suka zo ki kama girmanki a matsayinki na uwa" Barin gurin ya yi cike da takaicin hali irin na matarsa, a rauwarta bata ƙaunar talaka balle wani ya zo gidanta.


Saukowar Sultan ne ya sa ta maida kallonta gurinsa, sanye yake cikin jallabiya fara me kyau gashin kansa ya sha gyara tamkar ba shi ba, ƙamshin turarensa ne ya baje gaba ɗaya parlourn har ya ƙaraso inda Mom ke tsaye kamar an dasa ta.


Ƙarar bell ɗin ƙofar ne ya sa Sultan faɗin "Majeed come in"


Shigowa Majeed ya yi bakinsa ɗauke da sallama, gaida Mom ya yi ta amsa sama-sama tana mai barin gurin jiki na rawa, dan har yanzu ba wani sakewa da Sultal ɗin ta yi ba.


Hannu Majeed ya miƙa ma Sultan suka tafa, "Guy wallahi yunwa nake ji please a kawo min wani abun kafin a kira sallar magrib"

Sai da Sultan ya hararesa kafin ya ce "Zan yi maka dan Allah ba dan ka isa ba"

Kichen ya nufa Majeed kuwa ya haura ɗakinsa yana dariya.


A hankali ya tura ƙofar bakinsa ɗauke da sallama jikinsa ne ya hau rawa bakinsa kuwa ya shiga ɓari kamar wanda aka kunnawa lantarki ganin Zakanya zaune tsakiyar ɗaki tana mai kallon ƙofar, suna haɗa ido da Majeed ta yi saurin ɓacewa daidai lokacin da Sultan ya ƙaraso gurin da gudu hannunsa ɗauke da basket, da ƙarfi ya janyo Majeed ta baya, a mugun tsorace Majeed ya ja dogon numfashi gami da sumewa jikin Sultan.


A kiɗime Sultan ya shige da shi ɗakin yana mai faɗin "Sai da na ce kar ki zo amma kin kasa saurara yanzu kalli abin da ki ka janyo kuma kin tafi kin barni da aiki"


Dariya Sultan ya rinƙa ji amma baya ganinta abin da ya ƙara ɓata masa rai kenan ya nufi frigde a fusace, ruwan roba ya ɗauko me sanyi, ɓalle ruwan ya yi tare da kwara ma Majeed a jiki, sai da ya kwara masa ruwan so uku amma be farka ma, hankalinsa ne ya mugun tashi kar dai Majeed ya mutu, Sultan ya faɗa a ransa yana mai zama gefen bed, "Ba mutuwa ya yi ba yanzunnan zai farka kawai ka sake zuba masa ruwan da ke hannunka"


Zakanyar ta faɗa cikin muryata me rikitarwa ba tare da Sultan ya ganta ba, a hanzarce ya ƙara watsawa Majeed ruwan sai kuwa ya ja numfashi da ƙarfi, ɗagowa ya yi yana mai faɗin "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un wallahi Zaki a ɗakinnan" Yunƙurawa ya yi da niyar gudu Sultan ya damƙo shi "Kai amma marar hankali ne, mafarki ne fa ka ke yi tun ɗazu nake zuba maka ruwa amma sai ihu ka ke cikin bacci wai Zaki ya biyo ka" A mamakince Majeed ya zauna tare da dafe kansa "Mafarki kuma? na zata gaskiya ne amma ai bansan lokacin da na yi baccin ba"


"Ka aje duk tambayoyinka ni banada lokacin amsawa, ya za'a yi ka ga Zaki a ɗakina kamar dai a Jeji, malam ga abincinka can sai ka ci dan an kusa kiran sallah" Sultan ya faɗa yana mai barin gurin.


Abincin Majeed ya fara buɗewa yana mai gazgata abin da ya gani, dan shi kam ya san ba mafarki yake ba gaba ɗaya ya kasa yarda da idanuwansa.





.......................
Misalin tara na dare ne Najmeer da Meera suka fito cikin shigar ƙananan kaya kamar yanda suka saba, yau Najmeer ta ce za su tafi Clup na ƙarshe tun da gobe za su koma gidansu Junaid, ba ƙaramin kyau kayan jikinta suka yi ba doguwar riga ce red me adon duwatsuna daidai cinyarsa, daga saman na shanunta rigar ta kama sai ƙasan gurin manyan hips ɗinta da ke ƙarawa jikinta kyau, duk taku ɗaya sai mazaunanta sun juya hakan ya ƙara fitar da tafiyarta.


Ko da suka fito ba kowa a parlourn hakan ya sa su ficewa cikin sanɗa tun kafin Mamu ta ankare.


Najmeer ce me driving Meera na waya da Saurayinta a gefe har suka iso Clup, a ɗan tsorace Meera ta ce "Wai anan zamu zo? ko kin mance abin da ya faru wancan lokacin"

"Dan wani abu ya faru sai a hana min zuwa Clup, ko wannan lokacin idan ya shigo sai na......" Tun kafin ta rufe baki ta ji kamassssss an daki motar da suke ciki, da sauri Najmeer da Meera suka fito dan ganin waye.


Motocin Sultan ne guda goma jere da juna masu tsadar gaske, gurin da aka daka Najmeer ta duba sai ga glup ɗin bayan motar ya fashe, "Kambala'i.........., wallahi ba ka isaba sai ka gyara min motana"

Inda Sultan ɗin ke tsaye ta nufa tana mai zuba masifa, tana isa bata yi wata-wata ba ta wanke shi da mahaukacin mari "Allah ya tsinewa gadara da nuna isa, na ci uwarka a iskanci" Ta faɗa tana mai kama kwalar rigarsa, a mugun fusace Sultan ya damƙo gashin kanta tare da jinginata bayan motarsa da ƙarfi cikin tsantsar mugunta, jikinsa ne ya hau rawa bakinsa ya shiga neman kalmar da zai fara magana kusan mintuna biyu a lokacin riƙon da ya yiwa Najmeer ya fara yi mata zafi dan har gurin ya soma yin ja, "Ki ka mareni....?"

Sultan ya faɗa muryarsa na sarƙewa.


Itama Najmeer cikin ƙarfin hali ta ce "Yes ammareka kai waye? kuma sai ka gyara min motana"


Meera da ke gefe ne ta shige motar da mahaukacin gudu ta bar Clup ɗin tare da nufar gida, dan ta san yau kam akwai bala'i.

"Na lura tun ranar da na fara haɗuwa da ke ki ke raina min hankali yau zan koya miki ladabi" Cewar Sultan yana rufe mata ido, umarni ya ba Drivern sa da ya ciro masa wani ƙyalle a mota, nan kuwa Driver ya kawo masa, da sauri Sultan ya rufewa Najmeer ƙwayar idonta saboda da shi take samun damar canja halitta, idan har idonta na rufe bata iya komawa Mage.


Buge-buge ta fara tana ƙoƙarin janye ƙyallen amma Sultan be bata damar hakan ba, dan ƙarfinsu ba ɗaya ba.


Cikin Clup ɗin ya nufa da ida wanda kowa ya fito waje sai shi ɗaya, sai da ya shige kafin mutane suka rufa masa baya ana koɗa shi da yi masa kirari.

A wani haɗaɗɗen ɗakin ya nufa da ita a lokacin Najmeer ta fara ganin jiri saboda bata jure rufe mata ido da wani abun, ɗaki ne me masifar kyau da ɗaukar ido wanda Sultan ke sheƙe ayarsa a ciki idan ya zo Clup.


Duk iya ƙoƙarin Najmeer na ganin ta janye wannan ƙyallen ta kasa saboda ya riƙe mata hannu, cikin salon mugunta ya ce "Yau zan kawo ƙarshen rashin kunyar da ki ke min tun da na lura cewar ke marar kunya ce" Ya faɗa yana haɗa kanta da ƙofar ɗakin, wata irin razananniyar ƙara Najmeer ta saki wadda ta sa ɗakin amsawa tana mai zubewa ƙasa a sume.


Ba tare da jin tausayi ba Sultan ya saki dariyar mugunta yana mai fara rage kayan jikinsa, ƙofar room ɗin ya saka ma key sannan ya dawo inda take kwance ya tallafota zuwa kan bed, a hankali ya ƙura mata ido yana mai kallon kyakykyawar fuskarta me ɗauke da ɗan ƙaramin bakinta be san lokacin da ya haɗe bakinsu guri ɗaya ba yana mai sakar mata hort kiss me rikita tunani.

Sosai Sultan ke sarrafa bakinsa cikin nata har ya fara ficewa a hayyacinsa, tun da Allah ya halicce shi be taɓa jin daɗin kiss ba sai wannan karon har ya mance wadda yake tare da ita, a haukace ya shiga sarrafata yana mai yamutsata har ya cire ƴar ficikar rigar da ke jikinta, wani mugun numfashi ya ja ganin halittar jikinta tamkar ita ta yi kanta, sannu a hankali ya fara shinshina wuyanta da ke fitar da ƙamshin turare.


Gaba ɗaya Sultan ya ruɗe ya fice a hankalinsa har ya fara ƙoƙarin shiga hanyarsa amma abun ya gagara, duk iya yinsa na ganin ya shige amma ya kasa, yanda ya rinƙa yi ne ya sa Najmeer jan numfashi saboda jin kafurin zafi na shiga ta ƙasanta, ba ƙaramin razana ya yi ba ganin ya kasa tafiya, mamakin duniya kuwa ya ishe shi, duk da cewar baya hayyacinsa amma sai da ya gane cewar Najmeer bata taɓa kwana da wani namijin ba, cikin sanyin jiki ya koma gefe yana mai dafe mararsa da ƙarfi, "Ya Allah......" Ya faɗa cikin sanyin murya, lokaci ɗaya ya miƙe a galabaice ya maida kayansa tare da ficewa ɗakin.


Sai da Najmeer ta kai mintuna goma a haka kafin ta fara motsi gami da dafe kanta, a rikice ta kurma ihu tana mai kiran sunan Mamu jin zafin da ke bi ta ƙasanta, ƙyallen da ke fuskarta ta cire sai yanzu take tunano abin da ya faru a tare kuma ta saki wani irin kuka me ban tausayi duk a tunaninta Sultan ya keta mata haddi, kuka take sosai wanda duk yanda ka kai ga rashin imani sai ka tausaya mata, ta jima tana kukan gami da zaginsa da saka masa Allah ya isa buhu-buhu, wata tsanarsa ce ke ƙara dira a ranta lokaci ɗaya ta saki ihun da ya sa gaba ɗaya Clup ɗin girgiza, nan take ta zama wata jibgegiyar Mage wadda ta lunka girman yanda take zama so goma, mutanen da ke Clup ɗin ko sun tarwatse jin yanda ƙasa ke girgiza kamar zata rufe da su.


A hankali ta dawo halittar mutum sanye cikin kayanta, takalmanta da ke gefe ta saka tare da ficewa daga room ɗin ta nufi titi kamar wadda ke ciyon jiki, tafiya take amma hankalinta baya jikinta hawaye na sauka tsiri-tsiri kan haɗaɗɗiyar fuskarta, a ranta take faɗin shikenan Sultan ya gama da rayuwata ba bu wani abin da ya dace face na kashe kaina a yanzu.


Jin ƙarar mota ne ya sa ta saya ba tare da ta juyo ba, motar na tsawa Nameer ta cigaba da tafiya sai kuma ta ji an ƙara yin horn a bayanta, a hasale ta juyo dan ganin waye amma hasken motar ya hanata gane wanda ke ciki.

Ta kai mintuna biyu a haka me motar be tafi ba ita kuma bata matsa ba, Allah ya sa titin ba kowa dan sai can ba'a rasa ba motoci ko mashin ke giftawa, ba zato ba tsammani taji an ja hannunta tare da matsar da ita gefe, ɗago kan da zata yi suka yi ido huɗu da shi, bakinta na rawa idonuwanta kuwa hawaye ne cike take furta "Prince...."


Sai kuma ta rungumeshi tare da fashewa da kukan da ke tsaye a ranta, sosai take kukan gami da ƙara matse shi a jikinta ko zata samu sassaucin zafin da zuciyarta ke yi, ganin yanda take kukan ne ya sa Prince kasa cire ta a jikinsa amma hannayensa a ƙasa ba tare da ya taɓa ta ba, rawanin da ke fuskarsa ya gyara kamar kullum ƙwayar idonsa kawai ake gani, cikin sanyin jiki ya janyeta

Please Login or Register in order to submit comment