Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tattausan lafazin ki nake saurare yake abin kyaunata, komai naki daban dana sauran 'yan mata, da zan kwana ina misalta kyawun halittar ki, ba zan iya kaiwa karshe ba, koda kuwa zan wanzu ina yi har karshen rayuwata"

Kasa danne kukanta tayi, cikin kukan ta bude bakinta, domin ta faranta mishi rai, tana sheshshekan kuka take cewa.....
Akwai matsala deeni"

Wani irin nufashi yake fitarwa, kasa yayi da murya sannan yace..... wacce irin matsala kuma asma'u ? bakya so nane?

Hannu tasa ta share hawaye da majinan dasuka dame afuskanta, sannan tace......
Ina sonka tamkar yadda ba zan iya bayyana maka ba, ina sonka tamkar yadda baza ka iya kirga adadin ruwan sama ba, kada ka zubar da hawayenka, yayin da wani ya bata maka rai, tuna da wacce kake so, ka ke kauna, sai zuciyarka tayi fari, ina sonka abin kaunata, na kasance a cikin matsin kasa bacci yayin da dare ya tsala, bani da komai sai tunaninka har wani lokacin gari kan waye ban iya runtsawa ba, nasan wannan yana faruwa ne saboda irin tsantsar soyayyar da nake maka, Shin ko kaima haka ne?

Karashe mgnr tayi cikin matsanancin kuka"

Dan haka hankalin deeni ya tashi, idonshi ya kankance, karkace baki yayi sannan ya bude wannan muryan tasa yace wanne d'an ta shekiyan ne ya bata miki rai har kike kuka?

Sau sauta kukan tayi sannan tace deeni ranan juma'a za,amin aure"

Diffff yayi, zuwa can yace...... Yaseeeen karya ne, Asma'u ko sama da kasa zata hade hakan bazai faru ba"

Itadai ma'u kuka kawai take"

Jitayi ya sake cewa dawa za,ayi miki auren"

Nima bansani ba amman ina zaton Jafar ne"

Kai!!! Ina, yaseeen karya ne"









Heart Beat
*Mmn Yazeed*πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*




DedicatedπŸ‘‡πŸ»
Faty AfreenπŸ’‹πŸ€³πŸ»




4⃣1⃣to4⃣3⃣





πŸ’•πŸ’˜πŸ’žπŸ’•β€‹
Asma'u idan kika ga na barki agidan wani to ki tabbatar bana numfashi"

Zan dauki mataki agun duk wadda ya nemi ya rabani dake, ke tawa ce danni aka halicce ki"

Nisawa yayi yana huci, yaci gaba da cewa karki yadda da duk Wanda za,abaki, dan wlh zan kashe mutun"

Shi tsohon naki bashi da anhali ne, zan batar dashi yaseeen'

Kukanta ne ya Karu, cikin kuka tace......
kayi hakuri banason abin da zai taba abba na, duk abinda ka mishi ni kamawa, kuka ta tsaya tayi sosai, deeni yana sauraran ta, zuwa can tace.......
Deeeni muhakura kawai"

Diffff, yayi zuwa can yace...... Asma'u ni kike cewa muhakura? Kin manta kalaman da kika gayamin yanzu, daman yaudarata kikeyi ?

A'a ba haka bane deeni, tunanin abbana nake, banason nasa shi awani hali, tunda ya nuna baya so, dole na hakura koda haka zai zama sanadin ajali na"

Girgiza kai deeni yayi kaman yana gabanta sannan yace........
haka kika ce ko ?, tabbas zan kashe Jafar"

Iya abin da ma'u taji kenan ta kashe wayan, tare da fashewa da kuka, acikin zuciyanta tace wlh wlh duk wadda ya aure ne ya daukan ma kasan wahala, dan bazai taba samun inda yake so ba"

Kuka tayi sosai sannan ta goge no deeni, toilet ta shiga ta wanke idonta sannan ta nufi dakin mama domin ta mayar mata da wayarta"

Tana shiga mama tace idan kin gama da wayar bani "

Bata nuna tsoro ba, cikin dakewa ta mika mata tare da cewa......
Muyi hira da zainab ne, dan mun dade bamu hadu ba"

Hmmm kawai mama tace, Sanan ta karbe wayar ta tare da fadin ga zuma nan a cup zauna ki shanye shi, ki bani cup din"

Bata kawo komai azuciyarta ba ta zauna ta dauko kofin, rabon da tasa wani abu abakinta ta dade, deba tayi ta kai bakinta, wani irin bauri taji, dan haka ta mike aguje tayi toilet"

Binta da kallo mama tayi, tanajin ta tana kwara amai, zuwa can ma'u ta fito tare da fadin mama, menene wannan kika bani ?

Zoki zauna mama ta fada tana nuna mata wajen zama"

Zuwa tayi ta zau sannan mama ta dauki cup tace bude bakin ki, wannan abun da kike gani yana da muhimmaci sosai, kuma kinsan bazan baki abinda zai cutar dake ba"

Bude baki asma'u tayi tare da rufe ido mama taita dura mata zubar abaki, bayan ta gama mama ta kalleta, sannan tace..... Yanaga idonki sun kara tasawa? asma'u kodai har yanzun jikan kakan nanan zaciyan Ki ne?

Shiru tayi, mama nabinta ta kallo zuwa can tace niba tunanin sa nake ba"

Toh tunanin me kikayi asma' u kinga yadda kika rame kuwa, kinyi wani zuro2 dake, jifa inda wuyan riganki ke fadowa"

Kallon wuyata tayi sannan tace......

Mama toh daza'a dan daga auren ne tunda yanzun banda lfy"

Hmmm asma'u kenan, ai idan ma kina tunanin za'a daga auren nan gara ki bari"

Shiru tayi zuwa can tace mama abba fah yamin alkawarin bazai min auren dole ba, kuma gashi zaimin."

Ke kikajawa kanki asma'u ban da rashi tunani meya kaiki soyayya da d'an daba, duk wadda kika ganshi awannan harkan bayajin tsoron iyayen sa, dan duk iyaye na gari bazasu so ganin dansu cikin irin wannan harka ba"

Shiru sukayi zuwa can ma'u ta kalli mama tace......
Wlh mama deeni yanada kirki, kuma inaji ajikina idan na aure shi zai bari, cikin rawan murya ta karasa dan haka mama ta bita da kallo sanan tace........
Zuciyan Ki bata gaya miki gaskiya asma'u, ki daina asaran hawayen ki"

Shiru asmau tayi bata sake cewa komai ba, saidai lokaci zuwa lokaci tana Saka hannunta ta share hawaye"

Jamal kuwa tunda tunda yaji lbrn auren shi da asma'u ya rage walwala, baya wa kowa magana sai yaita mazurai yana cicin magani"

Yau alhamis Jamal na zaune adakin sa yana aikin da ya saba wato karatun jarida"

Ji yayi ana buga kofar, saida ya hada rai sannan yace waye?

Nafisa dake tsaye abakin kofa tace... Nice"

Shiko ya fada tare da maida kanshi kan jaridan"

Shigowa tayi sumi2 harta nufi bakin gadon, ta tuna yaya Jamal baya son ahaumai gado, dan akwai Wata rana data zauna abakin godon yaita masifa, wai dan tsabar rashin kunya zata zauna mai agado, saida Momy tasa baki sannan yabar mgn, dan haka yau ta tsaya atsaye"

Yaya Jamal ina kwana"

'Dagowa yayi fuskan shi adaure ya kalleta, wanne irin iskanci ne zakizo kimin tsaye aka"

Cikin sauri ta nufi kujeran ta zauna sannan tace, daman Momy ce tace naxo na dubaka ko lfy, wai taga tun safe baka fito ba, kuma abba na kiran ka"

Toh naji, wuce kiban waje"

Jifa yayi da jaridan hannu shi sannan ya miki yabi bayanta"

Har cikin dakin daddy ya shiga, daga nesa dashi ya zauna ya mika gai suwa"

Bayan daddy ya amsa sukayi shiru na dan wani lokaci, zuwa can yace......

Jamal jibi fah daurin aure banga gana shiri ba"

Daker ya bude baki yace.......
nasani ai daddy ni babu wani abu da zanyi ne"

Toh ai ko bazaka yi komai ba Jamal ka gayawa abokan ka, ko baka son suzo maka daurin aure ?

Shiru yayi bece komai ba"

Kallon shi daddy yayi sosai yace.... Kuma gashi har yanzun bakaje gurin yariyar ba, domin kaji bukatun ta"

Cafff ya fada azuciyan shi, afili kuwa sai yace, sai dai nayi aike daddy, dan inada aiki gobe"

A'a, ai zuwa dakai yafi sako kadaure dai kaje din kaji ko"

Toh kawai yace tare da mikewa yana kokarin fita, axuciyan shi yace.....
yaya ma za'ayi nayi zaman aure da *Husna* ai ni koda anyi aure sai dai na aure wacce ta girme ni"

***




Deeni ko tunda suka gama waya da asma'u ya shiga cikin wani hali, haka kurum yaji hawaye na zubo mai, tunda yake beta neman wani abu ya rasa ba, duk abin da yake so shi ake mishi, amman yau yaga ma'u na shirin subuce mishi"

Cikin wannan halin ummi tacimai afirgice tace.....

Auta menene haka? Meya maka zafi har kake tsiyayar da hawaye?

Hannun yasa ya share hawayen sannan yace ummi zan kashe baban Asma'u, dan naga nema yake ya rabani da ita"

Kul auta na karka soma, kana son ka tura mata kiyayyan ka ne ?, mundin ka kashe babanta toh duk son da take maka juyawa zaiyi ya koma kiyayya, kuma ina gargadin ka da kadaina kuka idan Allah ya yarda zaka Aure asma'u"

Hannusa ya shafo hawayen ya kallah ummi wlh in masifar son asma'u"

.Nasani auta tun da gashi naga kana zubar da hawaye rabonda naga hawayen ka tun kana goye"

Ummi bakomai ke ta damin hankali ba, ummi sai kalman asma'u wai ta hakura dani sabo da bata son bacin ran abbanta, ummi to idan nakashe Mijin fah"

Karka kashe kowa auta idan Allah yaso dakai za,ayi"


****


Yau ta kama alhamis, dan haka baki sun fara sauka agidan su ma'u"

Tunda ma'u taga 'yan uwan sun fara zuwa hankalinta ya tashi, tunanin ta gobe iyanzun tana matsayen matar wani, ba deeni ba" kuka take son yi amman hawayen yaki zuwa, rasa inda zata saka kanta tayi"

Da misalin karfe 11:00am yaya usman ya shigo har dakin ma'u, fuskan shi daure yace ke dauko gyalen ki kisame ni amota"

Mikewa tayi cikin sauri ta fito, ganin Anty fa'iza acikin motan yasa taji sanyi"

Tunkafin ta karaso anty fa'iza ke mata murmushi, shiga tayi ta zauna, har sukai nisa babu Wanda yace uffam"

Sunyi tafiya me nisa, sannan Anty tace, asma'u lalle zamu da gyaran kai kinga gobe dauren aure ko?

Dauke kai ma'u tayi tare da matso hawaye, wani kululun abu taji ya tsaya mata awuya"

Bata sake cewa kala ba, har sukaje akayi komai aka gama, ko ruwa aka bata bata sha"

Bakaramin kyau ma'u tayi ba, lallai ne dan uban su, dan haka tai kaman ba itaba, sai dai raman da tayi yasa idonta duk ya zurzurma"

Sun kusa isa gida wayar yaya usman ta fara kara, dauka yayi ya kara akunne sannan yace ka iso ne?, OK toh kashiga ciki mana, shiru yayi zuwa can yasake cewa toh kama ka zasuyi?, tsaki yaja sannan ya kashe wayan"

Karfe 5 da wani abu suka dawo, tun kafin ta fito ta hago yaya Jamal tsaye ajikin wata mota, gani tayi kaman ya kara tsayo dauke kanta daga kallon shi tayi, aranta take cewa shikuma wannan mugun meya kawo shi" wata zuciyar tace kika sani ko an gaiya to shine idan kinyi gaddama yaci uban ki"

Batace zata jira anty ba tayi gaba abinta, koda taje gaban Jamal bata kalli inda yake ba, harta wuce Taji yaya usman na cewa ke zonan"

Juyowa tayi afirgice tazo gaban su ta tsaya"

Zakice bakiga Jamal bane koko gaidashi ne bazakiyi ba?

Ban kula dashi bane, ma'u ta fada sannan tace ina wuni?

Juyowa Jamal yayi ya kalleta, sannan ya tabe baki tare da daga hannu shi, ya mata alma wai tatafi"

Koda tashiga gidan, kowa fadi yake tayi kyau, azuciyar ma'u fadi take da kusan abinda nakeji da bazakumin mgn ba"

Zuwa can Anty ta shigo, fuskanta dauke da dariya ke kuma haka akeyi, kina ganin mijinki saiki wani dauke kai"

Dasauri ta kalli Anty sannan tace waye mijin nawa ni ba wanda nagani"

Hmmm Asma,u bayan tun muna cikin mota naga kin kalle shi"

Mikewa tsaye tayi da sauri sannan ta koma ta manne da bango, hannunta dafe da kirjinta Anty kina nufin *Jamal*? Jamal ? shi abba ya hadani dashi?

Mikewa anty tayi cikin sanyin jiki tace, daman baki sani ba?

Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, wlh bana son shi, bazan aure shiba, dana Aure shi gara na kashe kaina"

Kafin anty tayi yinkurin cewa wani abu, ma'u tafita da gudu, cikin kuka tashiga dakin mama, idonta arufe ta fada jikinta tana kuka kaman ranta zai fita tace mama dagaske wai da yaya Jamal za'amin aure ?

Kai tsaye mama tace, eh, daman abban Ki be gaya miki ba?

Bana son shi mama, wlh na tsane shi, dan Allah karku hadani dashi, mugune mama, kuma azzalumi ne"

Bakin alkalami yariga ya bushe asma'u, dama ki daina bata bakin ki"

jikin bango ta koma ta dunkule hannu tare da fadin, mama wlh idan aka hadani dashi zan kashe shi, zan kashe mama"

Batasan cewa yaya usman na dakin ba, saiji tayi yace" idan har zaki iya to ki kashe shi"

Bataji tsoro ba, dan yanzu jitake zuciyarta ta bushe, da za'aita dukanta har akasheta dataji dadi"

Dakinta ta koma ta zauna tare da zubawa guri daya ido, deeni ne ya fado mata arai, inama zabar ta ta aure deeni, dataji dadin arayuwan ta, Amman me ake da wani jamal, tsaki taja sannan tace afili , wlh idan har akayi kukkuren yimin Aure da jamal dagani harshi haka zamu kare rayuwan mu cikin bakin ciki"

Tana cikin wannan tunanin taji ana kiran sallahn mangariba, mikewa tayi ta dauko dogon hijjabi har kasa ta saka"

Lekawa falo tayi taga babu kowa duk sun shiga sallah, dan haka tacire ta kalminta tarike ahannu sadaf2 ta fice agidan"

Gidan su deeni ta nufa tana tafe tana waige, harta isa gidan, akofar gidan ta tsaya ta kurawa dutsen da tasaba ganin deeni akai ido, hawaye taji yana zubo mata, ahaka ta shiga gidan, deeni na zaune atsakar gida ya zuba uban tagumi"

Tsugunawa tayi agaban shi, ahankali ya dago ya kalleta"

Mamaki baiyane afuskasa yace asma'u kece?

Cikin kuka tace nice deeni"

Yaya akayi kika fito da daddarenan ina nan ina shirya kayan yakin da zan fito dasu gobe, ina tabbatar miki gobe babu tsoho babu Yaro shara ne kawai"

Hannu tasa ta rufe mai baki sannan tace, bazaka iyaba deeni, kasan dawa za'amin aure ?

Gargiza kai yayi tare da kura mata ido"

Jamal, tafada tana share hawaye"

Wata irin muguwar dariya yayi sannan yace, jamal"?

Eh Jamal, ka kwatar da hankalin ka, bazan taba zama da jamal ba, na yake shawara adaren da aka kaini aranan zan kasheshi, karkace zaka dauki wani bataki, ka bari harsai nakasa"

A'a asma'u bazaki iya ba, insha Allahu bazakije kidan saba, ke macece bawani karfi gareki ba, ni kuma *na dad'e ina dama furata bazan so wani ya shanye min ba,* abin da yafi kawai kije gida da asuba kisan yadda zakiyi ki fito zanzo na daukeki mugudu"

Shiru tayi zuwa can tace......

Deeni wacce fura ce wannan?

Kau da idon shi yaye gafe, tare da fadin bazaki gane ba"

Cikin sauri tace nagane deeni, ummi na nan ne ?

Daker iya cewa taje anso min magani"

Shiru ta sake yi zuwa can ta kalle shi tace toh me zai hana kashanye furan taka yanzun"πŸ™†πŸΌ




πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*
​


DedicatedπŸ‘‡πŸ»

*Firdausi Sodangi*πŸ’‹




4⃣4⃣to4⃣6⃣




πŸš”πŸš”πŸš”



Da saurin shi ya mika hannun shi kan kafadan ta, ido ya zoba mata, itama kallon shi take cikin ido"

Sun kwashi tsoyon lokaci ahaka, zuwa can ya sake shigota"

Asma'u nasha kika ce?

Kai ta gyada masa sannan tace indai hakan zaisa ka yadda dani.....

Bata gama rufe baki ba, ya rarumo bakinta, sunbatan ta yake kaman zai cinye ta"

Sun dauki tsayon lokaci haka, deeni duk ya fita ahaiyacin shi"

Acikin wannan hali ummi ta riske su, babu abin da take ban da salati"

Cikin sauri ma'u taja jikinta, deeni ko ya kasa sakinta sai kara binta yake yana rokota"

Hannu ummi tasa ta rike ma'u, tare da fadin ke asma'u meya fito dake da tsohon daren nan"


Ma'u bata iya cewa komai ba, kanta ta sunkuyar akasa"
Kanta ta maida kan deeni daya rike hannun ma'u daya da kyau"

Ta dade tana kallon cikin idon shi sannan tace, auta haka mukayi dakai"

Jan ma'u ya fara, yana kokarin shiga dakinsa da ita, batare dayace wa ummi komai ba"

Dan haka ummi tabi su, fadin take kai auta kana hauka be?, saketa mana"

Ummi ina zuwa mana, akwai sakon da zan bata"

Runtse ido tayi tana fadin bana so auta, kasake yariyan muta ne, ta wuce gida karka jawo mana abin mgn"

Daramm gaban ma'u ya fadi, muryan Abba taji yana mata Yawo aka, lokacin da yake cewa.... da kijwo mana abin mgn gara namiki aure, cikin sauri ta zame hannunta ta fara kokarin tafiya"

Binta deeni yayi ya sake jawo hannun ta, sannan ya matsa daf da ita, hannu yasa aljihu ya ciro wata yar karamar wuka acikin dan gidanta, ya mika mata, cikin rada yace ki rike wannan koda anyi nasaran kaiki gidan wannan danta shegiyan, inason ta zama filonki, ma'ana akarkashin filonki, kara cije baki yayi, ya dage shi sama, sannan yace, daya neme karban wani abu awajen ki, ki kaddamar mass"

Kuma kisan yadda zakiyi kifito daga gidan tun kafin akiran asuba"

Idan ban ganki ba zansan baki zamu daman fitowa bane, kuma washeri za'a daura miki aure, idan haka ta faru Asma'u, banason ki wuce kwana 3 banji lbrn mutuwan Jamal ba, idan kuma kin kasa kina da no zamuyi waya"

Kuskus sukai mgnr dan haka babu mejinsu"

Ummi ce tarako asma,u, tame cigaba da mata fadan ditowa da daddare"


Tana isa kofar gidan ta cire takalminta ta rike ahannu, bakinta dauke da addu,ai"

Allah ya tai make ta me gadin benan, hakane ya bata daman shiga gidan cikin sauki"

Harta shiga bayi tai wanka ta fito tai sallah babu wadda ya nemeta"

Dan haka tai zaune ta fara aikin nata wato kuka"

Hayaniyan mutane taketaji cikin raha suna wasa da dariya, azuiyarta tace dafa haka kawai ne da yanzun ina cikin su ina kasan dariya"

Zuwa can tafarajin ana cewa wai ina amaryan ne ya kamata asata alallai dare nayi"

Cikin sauri ta juya ta haye gado ta kudunne kanta"

Wata kanwar mama ce ta shigo ta yaye bargon ta fesheta da turare, sannan ta rangada guda"

Ba ma'u kadai cikinta ya karta ba harda na jamal, jin wannan gud'a ya tabbatar mai auren nan babu fashi"

Dare ya tsala kowa yayi shirin bacci amman banda ma'u, zau ne tayi ta rafka uban dagumi"

Da misalin karfe 4:30am ta fara jin wani dan siririn fito, haka ya tabbatar mata deeni ne, dan haka tafara kokari meman yadda zatayi ta fice"

Waigawa tayi ta kalli Anty fa'iza dake kwance akan gadonta, tare da yariyar kanwar mama Khadija, bacci su suke kashir ban, dan haka ta mike, daman hijjabin ta, na jikinta ahankali ta bude kofofin tayi waje, a harabaan gidan taji gabanta na faduwa dalilin tunawa datayi, ai get din kwado ake samishi yanzun yaya kenan?, dan dakatawa tayi, zuwa can Wata zuciyar tace mata maza kisan duk yadda zakiyi kibar gidan nan, idan ba haka ba gobe Aure za,amiki da jamal"

Guiwanta taji ya kara kwari dan tana ganin duk duniya babu wadda yakaita tsanan jamal"

Karasawa tayi bakin get din, abin da yayi matukar bata mamaki, abude gidan yake, ahankali ta bude karamar kofan ta fita"

Cikin Sauri deeni ya karasu ya riketa da duk hannun wanshi guda biyu ido ya zuba mata zuwa can yace muje ko?

Jikinta taji yayi sanyi ko wani hali Abba da mama zasu shiga idan suka wayi gari basu ganta ba, amman kuma bazata iya tsayawa ba, haka kurum ahadata da Jamal, dan haka ta gyada masa kai, tafiya suka fara amman ma'u saitaji kaman anfito daga cikin gidan"

Waigawa tayi ta kalli get din, bataga komai ba, saboda duhu, dan haka ta juya sukaci haba da tafiya"

Sunyi kaman taku 5 sukaga andallare su da filan mota mai tsananin haske"

Gaba dayan su suka juya, ganin Abba tsaye abun yayi matukar razanata ahankali ta zame kasa tare da daura hannuwan ta aka, tana fadi na shiga uku na"

Deeni ko fadi yake tashi muje asma,u karki yadda suyi nasara akan mu bazan iya rayuwa babu ke ba, kinsa ni ina tsananin sonki"

Karasuwa Abba yayi cikin tsananin tashin hankali yace"

Asma'u tashi Ki bishi, ai bansan cewa ni ban isa dake ba sai yau, dan haka bazan hanaki Ki bishi ba, amman kisani idan kika Saka kafa kika wuce nan wajen Allah ya isa takanina dake, sai yanzun nake dana sanin saka miki sunan mahaifiyata danayi, baki cancanci sunan nan ba"

Deeni ne ya karkace baki shi sama sanan yace toh saika goge sunan, maza sa ruwa ka goge sunan sunan tsuhuwar taka"

Zare ido ma'u tayi abba ko kokarin karasawa gaban deeni yake, saida yaje dafda shi sannan ya bigi karjin deeni tare da fadin zakamin rashin kunya ne ai daman na sani kai d'in fitsararre ne"

Murmushi deeni yayi sannan ya kalli ma'u yace tashi muje"

Kuje Abba ya fada yana nunawa ma'u hanya tare da fadin tarihi ne zai maimaita kan shi, kallon deeni yayi cikin ido, sannan ya cigaba da cewa haka ubanka yayi Wa uwarka"

Dan zaro ido deeni yayi tare da zuba su akan abba"

Dan haka Abba yace, eh kaje ka tambayi uwarka saratu, ta gaya maka yadda tayi ta zame ka"


Runtse ido

Please Login or Register in order to submit comment