Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bani sha'wa inason yara sosai sunbatan yaran yayi tare da fadin Allah yayi muku albarka ya karawa mahaifiyar ku lafy shekara me zuwa ta sake haifo mana kalan ku, yakuma bawa mahaifin ku abinda zai ciyar daku"

Amsawa nafisa tayi da ameen, sannan tace ka manta addu'a daya da bakiyi ba"

Dagowa yayi
ya kalleta, idontshi da ragowan hawaye ga kuma murmushi akan bakin shi yace....

Wacce kenan?

Cikin murmushi tace......

Bakace muma Allah ya bamu irinsu ba"

Murmushi yayi tare da cewa a'a nafisa muruke me albarka kawai, ko mace kona miji ke duk abinda Allah yabani zan karba nayi godiya lokuta da dama abinda mukeso ba alheri bane agare mu"

Dahaka ya mikawa nafisa yaran sanan yace ta gaida asma'u"

Aranan momyn usman ta iso tare da dada"

Tunkafin ta shiga gidan take fadin you alkawari ya cika gani agidan takwara"

Koda suka shiga dakin ma'u daure fuska tayi, tare da kyauda kai, itama dada daure fuska tayi tare da fadin nima ba gurinki nazo ba"

Aranar da daddare hajiya asabe tazo ganin jarirai, farin ciki sosai ta nuna"

Acikin zuciyan Momy tace inma bakin ciki kike ke kika sani, ni baki gabana mantawa ma nake inada kishiya idan yana gidan ki gani nake kamar tafiya yayi"

Awaya deeni ya kira Jamal yamai barka, ana gobe suna ya dauki nafisa suka shiga kasuwa kayan yara yaita kwasa kala kala tare da kayan wasa kai harda keke komai iri daya ne kuma bibbiyu, mota sukaita lodawa, Wata sarka nafisa tagani tace ka saiwa asma'u"

Wani kallo ya watsamata tare da fadin awani dalilin zan saimata ?, kinason mijinta yakaini kutu ko?

Turo baki tayi sannan tace wato ka maida yaya mafadaci ko?

A'a nafisa aiko nine sai inda karfina ya kare"

Washegari akwai suna, anci ansha jama'a ba masaka tsinke da sunan su aka barsu *Hassan da Hussain* aciki waddan da sukazo suna harda zainab kawar ma'u"

Lokacin da yan waliman Jamal suka cika gidan da hayani ma'u ta jawo zainab bakin window da hannu ta mata nuni da deeni"

Tabassa deeni yayi kyau babu wadda zaice yayi rin
rayuwar da yayi abaya, Saika ma zaci yafi su Jamal roko da addini domin su dikine na zamani sanye ajikin su, yayin da deeni yake cikin jallabiya fara karrr hannun sa rike da carbi, gefenshi Faisal ne zaune"

Washegshegari duk yan suna suka watse, sai dada kadai ta rage"

Kulum abba ke kiran dada awaya tare da tambayan jikokin shi, wata rana abba ya kira dada suna cikin mgn ma'u ta kwace wayar tasa akunne tare da fadin abba kulum ni baka tambayata"

Dariya yayi sannan yace......
Asma'u ai muna waya da mijin Ki, nasan lfy lau kike, ya mutanen gidan naku?

Lfy lau"

Toh madallah, Allah ya miki albarka, yadda kika min biyya kema Allah yaba ki masu miki, akullum ina miki addu,a zama lfy tare kwanciyar hankali"

Ameen abba, idon ma'u cika yayi da kwallah, sallama sukayi da abba, hawaye kawai ma'u taji suna Zubo mata daman haka iyaye sukeji idan dan su yai masu biyyaya, lallai naso nayi kuskuren nabi son zuciyata, kome nayiwa iyya na bazan biyasu ba, addu'a ta shiga ma iyayenta Allah ya saka musu da alheri"


Haka dada taciga da kula da yaran ma'u Hassan da Hussain har sukayi arba'in aranan Jamal yakaisu Kano, bayan sati 2 ya koma ya dauko su"

Bayan wata 5

Nafisa ta haifi katon danta, murna gurin deeni ba'a mgn, ya dade rungume da yaron, yana kwalla tare da tufa mishi addu'oi"

Ma'u ma bakinta ya kasa rufuwa, shiryawa sukayi ita da momy zasu tafi, momy na rike da hassan, hussaini a hannun ma'u har sun fito harabar gidan, motan Jamal ya shigo"

Tunkafin ya fito ya daure fuska"

Ma'u ko fara'a take tare da zumudin fadamai nafisa ta haihu"

Cikin basarwa yace naji ai, ina zaki?

Sanyi jikin ma'u yayi, tare da rasa abincewa"

Momy ce ta kalleshi tace.....

Zamuje gano jariri ne"


Da sauri yace amman bada Husna ba"

Daure fuska Momy tayi tare da fadin da Husna kuwa, Jamal wai me kake nufi ne?, kiri kiri ka hana Asma'u zuwa gidan Nafisa, bata taba zuwaba, watanta 6 da haihuwa amman ka hanasu suyi zumunci, wanne irin bakin kishine wannan?

Shiru Jamal yayi tare dasa idon shi akasa"

Cigaba momy tayi da cewa toh abin ya fara damun nafisa, dan harta fara korafi akai, abinda kake nufi baxai yuwuba gara ka canza tunani, jayawa tayi ta kalli asma'u tace wace mutafi"


Acike suka samu falon, ummi na zaune rungume da d'an deeni ahannunta, bayan gaishe gaishe ma'u ta amsa yaron, dakin nafisa ta nufa, tana kokarin shiga dakin sukai karo da deeni yana fitowa"

Cikin sauri ya matsa gefe tare da fadin Ya subuhananlah"

Dago ido ma'u tayi ta kalkeshi, shima idosa nakanta"

Tafiya ta fara tare da gaidashi bayan ya amsa tamai barka sannan ta shiga dakin jikinta asanyaye"

Saida yamma suka koma gida tundaga ranan Jamal be sake barin ma'u tajeba, har ana gobe suna"

Ran momy ya baci sosai dan haka dayazo sallama zai tafi aiki ta rufeshi da fada"

Fadan momy yasa hankalin jamal ya tashi har ya yanke shawaran zuwa ya gano nafisa tare da jaririn da ta haifa"

***


Yana shiga gidan deeni na kokarin fita amman ganin jamal yasa yai saurin fitowa"

Hannu ya bashi suka gaisa fuskan deeni asake yayin da ta jamal take daure"

Har dakin baccin nafisa ya kai Jamal sannan ya juya ya fita"

Bayan sun gaisa ya rungume jaririn ya koma gefe"

Gunshekan kukan nafisa yaji, cikin sauri ya daga kai ya kalleta, sannan yace.....

Ya da kuka kuma?

Yaya Anty asma'u fah bata taba zuwa ba, gashi yanzun ma tunda tazo so daya bata sake zuwa ba"

Shiru yayi yana kallon yadda take share hawaye, zuwa can yace.....

Au saboda haka kike kuka, lallai shagwaba ta miki yawa dallah zoki amsa yaron Ki"

Juyawayi yai ficewan shi"

Daddare nafisa na zaune taji muryan asma'u kasa jira tayi ta shigo"

Cikin fara suka kalli juna sannan nafisa ta karbi yan biyu ahannun ma'u

Bayan sun zauna nafisa take tambayanta halan keda momy?

A'a yaya ne ya saukeni wlh abin yaban mamaki ina zaune yace wai nashirya yakaini Gidan Ki na kwana tunda gobe suna, wlh na dauka sunan ma bazai barni zuwa ba"

Wani farin ciki ne ya kama nafisa, mara misalantuwa"

Washegari yaro yaci suna Mashkur, aranan sunan Faisal yazo, walima sosai deeni yayi"

Washegarin sunan ne daddy ya hada Jamal da deeni, fada ya musu sosai tare da nasiha me shiga ciki, bayan ya gama ne yayiwa deeni albishirin ya budemai manyan rumfuna dazai yi kasunci aciki"

Godiya yayi sosai, nan danan deeni ya zama shararran dan kasuwa"

Tare da faisal suke gudanar da komai cikin Ikon Allah kasuwa saikara burun kasa take"

****

Jamal da deeni zuwan su baguma 3 tare dakai musu niki2 abun arziki"

Yan biyu nada shekara daya ma'u ta sake samun ciki, bayan wata tara ta haifi da namiji wadda aka sawa Aliyu, sosai yan biyu sukayi wayau tafiya suke gwanin sha'awa"

Aliyu nada wata 7 Nafisa ta sake haihuwan Jafar"

Zuwa wannan lokacin Jamal da deeni suna mgn sama sama, yadda yaga deeni na nuna soyayyar nafisa ako ina yasa jamal ya saki jikinshi, kullum cikin kara ririta ma'u yake"

Sosai Abba yakejin daddy idan ya tuna Asma'u na dakin mijinta, Jamal betaba kaimai karanta ba, kullum yaje gaida Abba idan xai tafi ya dinga godiya kenan"

Ita ko ma'u akullum suka hadu da Abba albarka yake saka mata"

Bayan ma'u ta yaye aliyu ne Jamal ya maida ma'u makaranta domin ta cigaba da karatunta"

Manyan hijjabai ya saya mata dakan shi yake kaita indai yana gari"

Bayan shekara 3

Ma'u na daf da karasa karatunta, ta fara laulayin ciki, tashin hakali ta nuna sosai, ganin haka Jamal yaita kwantar mata da hankali tare da nuna mata ai ciki bazai hanata karasa karatu ba"

Lallashinta yaita yi tana dada narkewa ajikinshi tare damai shagwaba iri iri, biye mata yai tayi, har ta saki jikinta"

Itako nafisa cikin na hudu ne ajikin ta, kulawa deeni yake sosai wajen basu tarbiya, baya wasa, beciga son kaisu gidan abbashi bashir ba, daya kaisu aranan yake komawa ya dauko su betaba bari sun kwana agidan ba, duk da yasan cewa komai ya zama daidai amman hankalin shi baya kwanciya"

Gidan momy ko aduk sanda suka samu hutu can yake kaisu har hutun ya kare, dan haka mushkur da yan biyu suka kule, wasa suke sosai"

Cikin ma'u ya tsufa dan haka Jamal ya matsa zai koma gidan shi, momy taso ya bari sai ma'u ta haihu amman ya dage"

Acewar shi tunda da tace tsoro take ji yanzun ai ga yara nan ta samu"


Sun koma da sati 2 ma'u ta haifi 'ya mace"

Kowa ya kalli yariyar cewa yake da ma'u tai kama, amman Jamal dagewa yayi wai shi ta dauko, haushi ma'u takeji idan jamal yace shi ta biyo, dan haka ta fara daure fuska"

Nafisa ce taita sintiri zuwa gidan da goyota abaya har akayi suna ayanzun yaran nafisa 4 kuma duk maza ne, yayin da ma'u keda 4 amman haihuwanta 3"

***


Yanzun Hassan da Hussaini suna da shekara 10, girma sukai na ban mamaki farare ne tas idan ba wadda ya sansuba baya iya babbaci su"

Wayon tsiya gare su, idan ka kalli ma'u baka taba cewa ita ta haife su, shi kanshi Jamal idan ya fita dasu cewa ake kannin sa ne, dan sun kusa kafardar shi"

Wata rana jamal ya kwaso duk gidan domin zuwa gidan momy, akan hanyar ne hira ta barke tsakanin Jamal da yaran shi, inda yake tambayan so idan sun gama karatu me suke so su zama?

Hassan ne ya fara cewa nidai daddy SOJA zan yi"

Kai amman ka burgeni kaifa hussaini?

Tura kanshi yayi gaban motar inda Jamal da ma'u ke zaune yace.....

Nidai daddy so nake kawaai na auri Hussaina"

Gaba dayan su dariya sukayi ban da ma'u data zafgawa Hussaini harara"

Itama Fatima wadda suke kira shikuriya zuboro baki tayi tare da matso hawaye"

Bayan jamal ya gama dariya ya waiga ya kalli Hussaini yace amman ai saika gama karatu ka samu aiki zakai auren ko?

Kafin Hussaini ya bashi amsa yaga Shukuriyya na shirin kuka dan haka ya juya ya kalli ma'u yace....

Toh fah, ita kuma wannan rigimanmar waya bata mata rai, nakula duk dabi,unta naki ne"

Juyawa yayi ya sake kallon shukuriya yace gaya min wanene ya bata miki rai?

Cikin shagwaba tace ba hussaini bane yake cewa baxai aureni ba, wai Hussaina zai aura"

Murmushi Jamal yayi kadan sannan yace wace wacece Hussaina?, rabu dashi aina zai samu Husaina ?, karya yake yi"

Hassan ne yayi dariya tare da fadin dolowa kawai, yaya za, ayi ya aureki ?, mamarmu daya babamu daya ai ba'a aure, saidai ki Aure mashkur"

Azuciye ma'u ta waga ta daka musu tsawa tare da fadin wlh duk wadda ya kara mgnr aure cikin ku saina fasamai baki, waigawa Jamal yayi ya kalli ta ya dauke Kai domin ya lura kamar ranta bace yake"

Babu wadda ya sake mgn har suka isa gidan' bayan Jamal ya gaida mikewa yayi zaifita saitin kunnen ma'u yaje yace.....

My Sweet Heart idan nina bata miki rai kiyi hakuri, idan kuma yara ne ki musu uzuri yarinta ce ba wani abuba"

Yana gama fadan haka yajuya ya tafi"

Da daddare ya dawo ya dauke su suka koma gida"

Jamal na kwace agefen gadon ma'u yake tambayan ta wai dazun menene ya bata miki rai ne?

Cikin damuwa tace....

Yaya tsoro Hussaini ke bani bashi da zance saina aure kusan kulum sai yayi mgnr, sai naga kamar babu karatu agaban shi"

Murmushi yayi sannan yace......

Ki daina damun kanki Husna yarinta ce ke damun shi, babu abin da ya sani fada kawai yake"

Washari da safe daddy ya bugawa Jamal waya cewa nafisa ta haifi 'yan biyu duk mata"

Cikin fara'a Jamal ya fadawa ma'u, shiri tahau yi cikin tsan tsan farin ciki"

Tunda Hassan da hussaini sukaji suka kama murna tare da rukon suma zasu"

Lokacin da suka isa gidan cike suka samu falon ciki harda dadddy da momy, alhaji bashir da ummi, deeni har kuka yake saboda farin ciki, kasa amsa barkan da Jamal kemai yayi sai hawaye dake zuba a idon shi, bayan shi Jamal ke bugawa tare da fadin ba kuka yakamata kayiba ka godewa Allah"

Addu'io Jamal yayiwa Hassana da hussaina sanan ya mikawa ma'u"

Kwlla cike da idonta bakinta dauke da murmushi take kallon su"

Damunta yan biyu sukayi dan haka ta mikawa husaini Hasssana girza kai yayi tare da fadin momy Husaina zaki bani"

Hararan shi tayi sannan kowanne ya dauki takwaran sa"

Kinbawa kowa su sukayi, momy ce tace, nifah 'yan biyu ban gane bane, me kuke nufi?

Dariya ummi tayi tare da fadin kika sani ko yar gida za'ayi?

Dariya daddy yayi sannan yace kudai kuce kishi na damun ku"

Tun daga ranan ma'u ke zarya zuwa gidan har akai suna, kulum idan ma'u zata tafi sai 'yan biyu sunce ashafa musu kan jarirai"

Abba da kanshi ya kawo mama suna sannan yaita sawa yaran albarka dayaga deeni be iya shaidashi ba, saida daddy yagaya masa"

Ma'u nakai ziyara kano akai akai, inda lokaci bayan lokaci yaya usman yake kai mata fa'iza da dada"

Wata rana dada ta kawo mata ziyara da gangan tajata gidan nafisa, suna shiga tsakiyan harabar gida ma'u ta juya ta kalli dadda tace......

Dada kinsan Gidan wa na kawoki?

Saikin fada takwara"

Dariya ma'u tayi sannan tace gidan me kare"

Rawan jiki dada ta fara tare da fadin La haula fisha'atillahi azubika, Allahu akkubar Allah da kirma kake, fitsari ne ya fara zubowa ajikinta, banda dariya babu abinda ma'u keyi"

Daida kokacin deeni ya fito daga gida, ganin haka yasa ma'u ta tsaya da dariya tare da kama hannun Dada tana fadin zomuje"

Tirjewa dada take tana cigaba da surutun ta"

Deeni ne
ya matso yana fadin yaya akayi ne dada?

Yauwa bawan Allah zoka tai make ni, ka maida ni Kano ya riyar nan bata kyaunata so take taga bayana, zata kaini inda za'a akashe ni"

Ganin in da dada take arikece yasa ya kama hannun ta, motar shi ya bude ta shiga, ma'u dariya take tayi badan kar dada ta sumaba data kara cewa wani abu, cikin gidan ta shige"

Shiko deeni bayan sunyi nisa yaga jikin Dada ya daina rawa, anan ya fara tambayanta meya hadata da asma'u?

Warware mishi komai tayi, kwashewa yayi da dariya acikin zuciyan shi yace sai yashe asma'u zatai hankali ta daina tsokana, daman har yanzun tana nan da halinta?



Gidan daddy yakai dada sannan ya gaya musu abinda ke faruwa, dariya sosai daddy yayi sannan yace ai ga mekaran nan agaban Ki"

Mamaki ne ya kama dada daman Abba ya gaya mata deeni ya shirru Amman batasan takai haka va"

Hira sukaci gaba tsakanin deeni da dada daddy da Momy na souraran su"

Bayan shekara 10


Soyayya ce me karfi tsakanin Hassan da Hassana, Husaini da Hussaina, tun suna kana suka taso da kyaunar juna, duk da cewa su hassana basu wuce shekara 12 ba"

Jamal da deeni zumuci suke sosai har sun yake shawaran hada inbiyun su aure, da zaran ko wannen su ya kammala karatun shi"

Ma'u tun daga shikuriyya bata sake haihuwa ba, Jamal kara shagwabata ma'u yake idan ka gansu adaki bakace suna da yara 'yan shakara
20 da duriya ba"





ALHAMDULILLAH












Heat Beat
The End๐Ÿ™‹๐Ÿป

*Mmn Yazeed*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment