Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Waiwaigawa yayi ya zabi kujeran dayaga tamishi ya zauna"

Yayin da karnukan shi suka kwanta agefe"

***

Ma'u tunda taji sani yana gayawa mama ta shiga damuwa tare da addu'an Allah yasa deeni manyan kaya ya saka, kuma Allah yasa ummi ta gargade shi ya gyara harcen sa"

Addu'oi da tai tayi kenan, har zuwa lokacin da taji fitowan abba da baba"

Cikinta taji ya kada dan haka ta tashi ta shiga bayi"


Alhaji musa ne agaba abba na binsa abaya dan haka alhaji musa na tura kofar yayi to zali da duna"

Tsayawa yayi cak sannan ya juya ya kalli abba tare da tambayan shi, Gamo nayi ne?

Atare suka maida idon su cikin falon, tare da karasa shiga ciki, ko wanne su bakin shi dauke da addu'oi a bakin shi"

Wani irin BUGAWA ZUCIYOYIN su yayi atare ganin matashin saurayi zaune, karnuka kewaye dashi, cikin bin bango abba ke kokarin shiga ciki hannun shi daya dafe da saitin ZUCIYAR shi"

Alhaji musa ne yayi karfin halin karasawa gaban deeni tare da fadin.... Daga ina?

Deeni cike da kwarin guiwa yace nine bakon da Asma'u ta sanar muku da zuwan shi"

Runtse Ido alhaji musa yayi tare da dafe kirjin sa yana sauke wani irin nufashi, ja yayi da baya ya nemi wata kujera ya zauna"

Abba kuwa yana rike da kirji shi acikin zuciyar shi ko fadi yake Allah Yasa yazamto mafarki ne"

Ganin inda Abba ya sandare aguri guda, yasa alhaji musa dakewa, ya fara kwalawa Asma'u kira"

Tunda asma'u ta jiyo irin kiran da baba yake kwalawa tasan akwai Marsala, dan haka jikinta narawa tafi falon abba"

Tagaban Abba ta wuce haryanzun yana nan a inda yake"

Gabantane yai wani mummunan faduwa ganin duna kwance atsakiyan falon mahaifinta"

Ganinta kawai tayi ta daura hannuwanta 2 aka, tare da zubar da hawaye"

Sauke hannun ki taji Abba yace, bashiri ta sauke su kasa sannan tabi Abba da baba da kallo"

Deeni ko ma'u yake kallo fuskan shi dauke da murmushi"

Ahankali Abba ya nemi guri ya zauna, alhaji Musa ko, kallo yake bin ma'u da deeni dashi"

Abba ne ya kalleta sosai sannan yace.... Asma'u wannan shine yaron da kikace kina so ?

Eh, tace batare dajin kunya ba, dan ita ganinta wannan itace daman ta na karshe"

Girgiza kai Abba yayi tare da fadin yayi kyau, shiru yayi zuwa can ya sake cewa.......Asma'u kikace wannan shine wadda kika amince ya zama uban 'ya'yan ki ?

Kasa mgn tayi hawaye na zuba a idon ta"

Shiko deeni, wani irin kallo yake yi Wa abba dan ya rasa inda mgnr abba ta nufa be amince bane, koko so yake ya tabbatar?

Inajin Ki abban ya sake fada"

Ahankali ta daga kai alamar eh"

Abba komawa yayi ya kwanta ajikin kujera"

Alhaji Musa ne yayi ajiyan zuciya sannan ya juya ya kalli deeni yace......... To kai Yaro bamu gaisa ba bare musan sunan ka"

Cikin murya nan da kukasan deeni da ita ya karkace baki yace..... Sannu ku dai, ina kwanan ku?

Alhaji musa ne kurun ya amsa Abba ko inbanda binshi da kallo ba abin daya ke"

Cigaba yayi da fadin...... Ni sunana shamsundeeni amman anfi sanina da shamsun duna"

Yayi kyau alhaji musa ya fada, sannan ya kara da cewa...... Kai dan gidan waye ?

Murmushi deeni yayi sannan yace...... Ni jikan isa kaka ne"

Isa kaka ? Abba ya fada yana zare ido"

Eh, deeni ya fada"

Isa kaka ai 'ya daya ya haifa, kananufin kai dan saratu ne?

Eh deeni ya sake fadi"

Toh, toh, abu yayi na fahimta, cewar abba yana kokari mikewa tsaye, kanshi ya daga sama sannan yacewa alhaji musa shike nan, sallame shi"


Ma'u alhaji musa ya kallah, sannan ya kalli deeni yace...... Shikenan kaje zamu neme ka"

Mikewa deeni yayi yanabin ma'u da kallo ya fice waje, yan rakiyan shi nabin shi abaya"

Mikewa asma'u tayi zata fita, alhaji Musa yace koma ki zauna"

Jikinta na bari ta zauna, abban najin fitan deeni ya kalli ma'u idon shi jawur yace..... tirrrrrr Asmu'u, kinyi asara, dan yatsan shi daya ya daga sama sannan yace wlh wlh Asma'u ko zaki mutu asma,u bazaki aure yaron nan ba"

Alhaji musa ma mikewa yayi cikin tuhuma yace...... Asma'u kisan waye shi?, kinsan waye ubanshi?,
meye abin sha,awa?, me kika gani ?, meye ya rudeki ?

Kan asama'u akasa kuka kawai take, kaman ranta zai fita, tasani dabi'un deeni basu da kyau amman tamai fatan shiriya, dan haka acikin zuciyarta take addu'an Allah ya karkato da hankalin su abba su bata zabin ranta"

Muryan Abba taji ashake yana cewa..... Sabo da wannan abon kika kora mutane masu mutunci ?, Atunanin ki nizan daukeki inbawa wannan katon Dan iskan ? Wlh kinyi kuskure, baki isaba kinyi kadan, wato ina nan ina tufka wani na warware min" wan nan yaron da kike gani daga uwar shi har uban shi ba mutanen kirki bane"

Yadda abba ke daga murya yasa mama shigowa tsaye tayi tana sauraran su, harta fahimce akan abun da suke mgn"

Ma'u tabi da kallo hawaye ciki da idonta, Abba ko banda tsiyaya fada babu abinda yakeyi"

Alhaji musa ne ya tsaidashi ta hanyar fadin......barta haka, yanzun mgn ta kare, bazamu zuba mata ido ta zubar mana da mutunci ba, ko kina so ko baki so da yardan Allah bazaki wuce sati 2 agidanan ba, za'a daura miki aure da duk wadda Allah yasa shine Mijin ki"

Rikecewa ma'u tayi da kuka harta fara fita cikin hayacin ta, cikin kuka tace baba, dan Allah kumin rai, wlh Abba shi nake so, idan ban aureshi ba mutuwa zanyi, dan Allah karku rabani dashi, Allah ne ya dauramin sonshi bani nadaurawa kaina ba"

Hawayen takaici ne suka fara zobowa a idon Abba, mikewa tsaye yayi azafafe ya fara takowa gabanta tare da fadin zakiyi fito nafito da ni ne ? yau zan gani tsakanin ni dake waye ya haifi wani, duka ya rufeta dashi kan kace me abba ya kece da amai"

Alhaji musa arude ya nufeshi ya rike shi, amman duk da haka abba dukan ma'u yake tare da wani irin tari sai lokacin Alhaji musa ya lura kanin nasa aman jini yake"

Daker ya rabashi da jikin ma'u duk jikinta jinin abba ne, haka yasa hankalin shi ya kara tashi"

No Usman alhaji musa ya kira, ya gayamishi halin da ake ciki"

Da taimakon Sani drive suka saka Abba amota suka nufi asibiti dashi"

Shiko usman lokacin da akirashi suna tare da Jamal a Abuja, suna tsakiyar aiki"

Ganin inda hankalin shi ya tashi yasa Jamal be bashshi ya taho shi kadai ba"

Sun iso Kano dafda magariba, kai tsaye asibitin suka wuce"

Lokacin da sukazo abba baya cikin Hankalin sa, kwance kawai yake, komai na jikin shi baya motse, bakin shine kawai yake motsawa, ahankali yakai kanshi saitin bakin abba, jiyayi yana fadin Asma'u, fadi yake baya kyaukyautawa, dan haka ahargitse ya kalli mama tare da fadin duk yadda akayi asma'u ce sanadin ciyon nan na Abba, bakin shi sunanta kawai yake kira"

Sallaman dada ne ya katse musu hanzari, arikece ta wuce usman tana leka fuskan abban, ganin shi haka yasa ta fara tofamai addu,io"

Usman ne yaci gaba da tambayan mama ma'u tayi wani abu ne ?

Mamatana share hawaye take gaya musu halin da ake ciki, ai ganin dada kawai sukayi ta zame kasa, tare da fadin yanzun nan yariyar nan bata bar mgnr yaron nan ba?

Duk abinda suke Jamal na gefe yana kallon su, rungume hannun shi yayi akirji tare da lumshe ido kamar besan me ake cewa ba"

Nan danan jikin dada ya rikice, haki ta fara babu kyau2 tawa dan haka usman yaje ya kira likita, cikin mintocin da basu wuce 7 ba, dada ta fita cikin hayyacinta dole tasa aka bata gado"

Mama da momy ne suka kwana akan dada yayin da Alhaji Musa da su Jamal suka kwana akan abba, babu bacci dan Abba sai kusan asuba ya samu bacci"

*****


Washegari Abba ya tashi jikinshi yayi dama dama bakaman jiya ba, saidai jikin dada sai kara rikicewa yake"


Da misalin karfe 1:23pm Alhaji inuwa manga ya iso duba jikin abokin shi"

Bayan gaishe2 tsanin alhaji inuwa manga da alhaji musa, matsawa yayi gurin Abba"

Mgn suke ahankali abba da kanshi yabawa alhaji inuwa lbrn halin da ake ciki"

Nasiha yamai tare da tare da kara bashi shawar wari, nan Abba yadan ji sanyi aranshi"

Zuwa can abba yaji bacin rai ya sake taso mai, dan haka ya kira jamal da usman yace musu..... Maza kuje gida kutaru Ku karya min asma'u"

Kaman jira suke suka fita cikin sauri, Alhaji inuwa nakiran su ina, sun riga sun fice"

Bayan fitan su alhaji inuwa yakalli alhaji musa yace inason ganin ka"

Waje suka fita sun dan juma sannnan suka dawo fuskan su dauke da murmushi"

Abba kallo ya bisu dashi, koda besan me suka tattauna ba, ya san magana ce me mahimmanci"

Ganin inda yake kallon su, yasa alhaji musa cewa......rana ita yau za,a daura auren *Asma,u* da *Jamal* mahaifin shi ya neman mai aureta aguri na kuma na bashi"

Cikin farin ciki Abba yace Allah ya nuna mana"


*****


Ma'u ko yadda taga rana haka taga dare ba abun da yake damunta ban da tunanin abban ta, kasa komai tayi nan danan ta rame tai zuro2 goggo tani ce taita lallashin ta ruwa kawai take iya sha"

Misalin karfe 3:00 goggo ta matsa mata tai wanka, dan haka ta mike ajikinta babu kwari tacire kaya ta dauko towel ta daura, toilet ta shiga harta tube ta murza kunfa, tafarajin ana kwala mata kira, cikin hargagi, muryan yaya usman ta gane aciki, hayaniya irin nasu na sojoji"

Arikece ta mike ta dauki towel dinta ta daura, daidai lokacin taji an banko kofar daki"

Saida ya kira sunanta so uku ajere sannan asma'u ta amsa adabur ce"

Fito dan uban ki"

Cikin rawan murya tace yaya wanka nake yi"

Idan kika bari nashigo bazan miki da wasa ba"

Kara rikicewa asma,u tayi, sannan ta rushe da kuka, batai aune ba taga yaya usman acikin bayin, mari ya wanka mata, kafin ta ankara take karajin saukan wani, dan haka ta riki ce tayi waje rike da towel dinta dake kokarin warwarewa"

Mutum take gani dishishi kamar yaya Jamal zaune agefen gadonta cikin kakin sa, yana danna waya"

Gani tayi ya rabun mata kashi2 duk inda ta waiga shi take gani, daga can ta hango yaya usman yayo kanta, Dan haka aguje ta tayi kan abin da take ganin shi kaman gizon yaya jamal






Heart Beat
*Mmn Yazeed*💗💝💝💗
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

💓💝💗
💗

💓💝💗
​By​
💗
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🤝*




Dedicated👇🏻
*Miss xoxo*
I love u, so much😘
*Kaunarki gareni daga Allah ne*



3⃣8⃣to4⃣0⃣



🤺🤺🤺



🤺 Duk da cewa Jamal yayi kaman beganta amman yana ganin inda ta nufoshi gadan2 yasa ya ajiye wayar shi agefe sannan ya miki cikin sauri"

Itako asma'u tanazuwa ta fada jikin shi ko da tajita jikin shi ma, bata tsaya ba, kara kadandane shi take dan tasan idan tayi haka dole yaya usman yabarta, dan haka hannunta tasa guda 1 ta bayan sa yayin da dayan ta danne towel dinta dashi"

Ganin haka hankalin Jamal yayi mummanan tashi kokarin rabata da jikin shi yake tare dasa hannushi ya rike mata towel din kamar yadda yaga tayi, saboda gudun kartayi tsirara, cikin tsawa yake fadin usman bari, bari, menene haka ?"

Usman natada jijjiyan wuya yake fadin..... kasan Allah wlh saina sumar da yariyar nan"

Shima cikin tsawa yace naji ko ka shetama zakayi zaka iya amman ka bari tasa kaya ajikin ta"

Usman fah ranshi ya riga ya bacci banda jijiyoyi kan shi baka hango komai, dan haka jamal ya dauketa cak ya nufi toilet da ita, tare da kare dukan da usman yake kaimata"

Ciki ya sakata sannan ya jawo kofan tare da tsawa abikin toilet din dan usman har yanzun be hakura ba"

Kallo Jamal yabi usman dashi sannan yace dallah jin inda kake tada jijiyan wuya, mace ce fah, macen ma yar ficiciya"

Juyawa usman yayi yana huci, ya fice"

Usman na fita jamal yaja tsaki sannan yace ke kuma dallah karki cikawa mutane kune da kuka, nan dan ma'u ta kunshe bakin ta"

Zuwa can ya sake cewa fito ki saka kaya, ki fito falo ki same ni"

Sai da taji ta dainajin motsen sa sannan ta fito, tayi zuro2 da ita"

Saboda tsabar rudewa riga daban siket daban ta Saka, sannan ta daura Karamin hijjabi akai"

Afalo ta same su, Usman har yanzun bebar huci ba, Jamal ko kallo ya bita dashi, Sannan yace tsuguna kisa guiwar ki akasa"

Tsugunawa tayi kamar yadda yace tare da sunkuyar da kanta kasa"

Daga hannun ki sama sannan ki rufe idon ki"

Innalillahi, ta fada sanan ta miki tana dan bubbuga kafa alamar tsoro"

Mekewa jamal yayi tare da fadin eh lallai baki dakuba, rawa ma kike min ?

Cikin kuka ta tsuguna tana fadin wlh na daku, hannu nama ciwo yake min dan Allah kuyi hakuri"

Usman ne yace nagaya maka duka ne ya dace da yariyar nan, kace ba haka ba, mikewa yake kokarin yi Jamal ya tare shi tare da fadin banni da ita, karyan rashin kunya take"

Dasauri ma'u ta tsuguna tayi kamar yadda yace, idonta arufe amman hawaye na zuba a idonta, bayan kusan minti 30 taji daya daga cikin su ya fita, saidai bata san ko wanene ba"

Gaba daya jijjiyoyin hannunta ya sake, kuma hakan takejin kamar kallonta ake dan haka tayi saurin bude ido"

Jamal ta gani ya ya kurawa guri daya ido, bin inda yake kallo tayi da idonta, nan ta gane ashe sanadin daga hannunta sama rigarta ta daga dan haka cibiyanta baiyane yake, kuma indai idonta ba kizo ya mata ba' Jamal gurin yake kallo"

Cikin sauri tasa hannunta ta jawo siket dinta sama, zabura Jamal yayi tare da fadin ke!! Waye yace ki bude idonki"

Mayarwa tayi ta kulle, tare da kara tsanan Jamal, tsine mishi taitayi azuciyanta tare da mai fatan bala'i kala2, bata san abin da yasa ba, duk abin da yaya usman zai mata kadan yake bata haushi, amman na jamal yana mata kuna"

Saida Jamal yaga tana tangadi kamar zata fadi sannan yace zauna"

Zama tayi tana share hawaye da hijjabinta, idon nan luhu2

Wuce kiban waje kuma duk ranan da kika sake Tayar da zancen me kare sai kinci kaniyar ki"

Tafiya ma'u tayi harta shege daki tana jerawa jamal Allah ya isa, tare da addu'an Allah yasa yana fita mota ta begeshi ya mutu"

Har Washegari su mama basu dawo ba, dan haka taji bazata iya hakuri ba, Sani ta samu ya dauketa suka tafi"

Tunda sani ya sauketa gabanta ke faduwa ba komai ke damunta ba sai haduwanta da Abba da mama, tasan suna fushi da ita"

Tana tura kofar dakin sukai idon 4 da mama, daga can gefen gadon ko, wani Mutun ne, me tsananin kama da Jamal sosai kamar harta baci"

Mama na ganin ma'u ta mike tana fadin.....

Me kikazo yi ?, menene ya kawo ki?, kinzo ki karasa su ne ?....

Sakin kofar ma'u taso yi, karafff taji anriketa, wannan mutumin ne me kama da yaya Jamal"

Hannnuta ya ruko suka shigo cikin dakin, sannan ya kureta da ido, zuwa can yace a shema yariya ce karama, rashin wayo ne yake damunta, kallonta ya karayi sannan yace..... Yi shiru kinji 'yata? Ki daina kuka"

Ta gaban mama ya wuce da ma'u agaban gadon da abba yake ya saketa sannan yace...maza ki tsuguna kibawa mahauifiki hakuri, nasan kinje makaranta kuma kinsan girman iyaye agare ki, daga yau kar akara ce miki ga abinda zakiyi, kice a'a, domin duk abin da babba ya hango yaro ko rimi yahau bazai iya hangowa ba, kuma wani lokacin zuciyarmu nason abu, wata kila ba alheri bane, dan haka kiyiwa iyayenki biyayya, ko kinason wani abu ya samu mahaifin ki ta dalilin Ki,?

Gargiza kai ma'u tayi hawaye na sauka aidonta"

Toh ki maida hankali Ki, gatan da uba zaiyiwa yarsa shine aure, kuma wada duk ya rasa wadda zai masa fada yayi asara"

Sosai maganga nun suka shiga jikin ma'u, cikin kuka tafara rokon Abba gafara, tare da nuna masa yayi yadda ya gadama da ita"

Koda abba bece mata kallah ba Amman yaji dadin kalamanta"

Alhaji inuwa kan mama ya juya yaita nuna mata mahimmanci jawo 'ya'ya ajiki, tare da nuna mata ta daina kyaran ma'u"

Bayan ya gama da mama ya sake jawo hannnun ma'u ya kaita har dakin da dada take, saidai dada naganin ma'u ta fara fadin Innahu Sulaimana Wa innahu Bismillahir Rahimu, Kalu lahaula, Lahaula wala kuwata, kufita min da ita , gata nan, gata nan"

Momy ce ta rike dada tana fadin dada Asma'u ce fah, takwaranr ki, ki kwantar da hankali ki mana"

Karasawa daddyn Jamal yayi ya kamo hannun dada ya hada dana ma'u, sannan yace mata ta bata hakuri"

Cikin kuka ma'u ta rike dada tace dada kiyi hakuri dan Allah nina bari bazan kara ba"

Arikece dada tace kikace kin bari, kin hakura dame karan?

Kai ma'u ta gyada mata"

Ke takwara da gsk kincire me karan azuciyar ki?, nidai indai kinsan baki hakura ba' to ki fada min, dan nasa amai dani mahaifata"

Hannu tasa ta share hawaye sannan tace nahakura dada"

To ko kefa, yanzun kinga ran juma'a za'a daura miki Aure"

Gabanta taji ya fadi rasss, sakamakon jin zancen dauren aure, amman yaya zata yi indai tana son zaman lfy, dole tabi umarnin iyayenta"

*****

Kwanan su uku a asibiti suka dawo gida, Allhamdulillahi jiki yayi kyau sosai, kuma aranan abba ya sanar da ita ranan juma'a zai mata aure"

Tadade zaune agaban abba tana kuka, ganin inda take kuka ya hana ya gaya mata waye mijin nata"


*Abuja*


*Jamal* ne zaune agaban daddyn sa, gefensa momy ce, duk kansu fuskan su babu wasa, hakan ne ya tabbatar masa mgn ce me mahimmanci daddy ya kira sa akai"

Rubuce rubuce daddyn keyi akan wasu takardu, zuwa cen daddy yayi gyaran murya yace Jamal yau yaushe ?

Tuesday ya fada yana kallon fuskan daddy"

Batare daya kalleshi ba, daddy ya sake cewa toh ran Friday za'a daura maka aure"

Azabure yace Aure kuma daddy? aini nace muku bazanyi aure ba"

Bazaiyiwo ba Jamal Aure ibada ne, Allah Ta’ala da ya tashi ni’imtar da bayinsa daga rahamarsa, sai ya ni’imtar dasu da Aure, domin aure daya ne daga cikin ni’imomin Allah, wanda Allah ya ni’imtar dashi akan bayinsa gaba daya'
Kuma Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace“ Idan bawa yayi aure, hakika ya cika rabin Addinin sa, sai yaji tsoran Allah asauran rabin,
Kuma ya kara cewa“ Duniya rayuwa ce mafi alkhairin rayuwar duniya mace tagari

Jamal ka duba mafi yawa daga cikin wadan da basuyi aure ba, kuma suna da ikon yin auren, zaka ga tunanin su gaba daya kan Zina yake, kuma zina tana nisantar da mutum a yanke daga imani"

Shiru Jamal yayi domin bashi da bakin mgn"

Zuwa can daddy yace..... Jamal baka ce komai ba"

Shiru yayi kaman bazaiyi mgn ba, zuwa can ya bude baki cikin fushi yace... daddy nifa raini ne bana bana so"

Murmushi daddy yayi kadan, sannan yace..... kana bani dariya Jamal, ai ba kanka aka fara ba, bakuma kanka za'a kare ba"

Shiru yayi zuwa can ya miki zuciyar shi cike da tunani kala2, babu abin da yake bashi takaici irin ace wai shine zaije yanawa yariyar daya girma karamar murya"

Muryan Abba yaji yace baka tambaye ni amaryan taka, ko kunyi mgnr da usman ne?

Cike da mamaki yace daddy usman yasanta ne?

Murmushi abba yayi, sannan yace kanwar sa ce, Asma'u

Afirgice Jamal ya daura 🙆🏼‍♂ tare da fadin haba daddy ya zakamin haka, sabo da Allah, daddy karasa yariyar da zaka hadani da ita sai asma'u, yariyar da bata da kunya, kuma ma ai ma ba tsarata bace, shekara ta 30 harda wani abu, ita kuma 10 da wani dan kwayoyi, haba daddy me zan da ita, inbanda ta raina ni.....

Gani daddy yayi bashi da niyar shiru kamar ma sambatu yake, dan haka ya mike sannan yace..... nidai nagaya maka, idan ka gaji da surutun ka bari"



*Kano*


Tunda ma'u ta dan saki ranta, mama take dan sakan mata fuska, dan haka yau ma'u ta mamayi mama ta dauki wayarta"

Dakinta ta shiga ta kulle ko ina, sannan ta fara shigar da no deeni"

Kaman jira ya ke ya daga tare da fadin haba asma'u
Yazaki share ni kunsan kwana nawa kinsan halin dana shiga kuwa ?

Kuka ne ya kwace cikin sauri tasa hannuta ta rufe bakinta dan gudun kar yaji kukanta"

Marairaicewa ya sakeyi yana fadin asma,u bari na kwatanta miki yadda nakeji"
Asma' na kasance tamkar kifi a cikin ruwa, idan nayi gabas sai kuma na dawo nayi yamma, idan nayi kudu, sai kuma na dawo nayi arewa"

Shiru yaji, dan haka ya sake cewa asma'u me yasa kikai shiru ?

Hannun ma'u dafe da bakinta, ta kasa cewa komai, tausayin deeni, tare da tsananin kyaunan sa takiji acikin jikin ta, hawaye da majina ne suka hade afuskanta"

Shiru yayi zuwa can ya sake cewa..... Asma'u nasan kinaji na, yau kuma wani sabon salo kika fito dashi?

Shiru ya sakeyi zuwa can yaji shirun yayi yawa, dan haka yace....


Please Login or Register in order to submit comment