Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hajiya amina bazata shiga kitchen ba, masu aiki zataba, shikuma kisanshi da iyayi"

Dakuma shegen fadinrai ta fada azuciyarta, take zacen deeni ya fado mata wai saiyaci uwar yaya usman, tunawa tayi da yadda yake ciccijewa yana karkata hanci da baki sainaci uwassa!! kyalkyalewa tayi da dariya dan tayi nisa atunani tama manta ba ita kadai bace agurin"

Dariya take babu kaukautawa ta kurawa guri daya ido"

Daga mama har tani mikewa sukayi suna binta da kallo, afirgece mamata tace ke asmau menene haka?

Batasan sunayiba kuma har yanzun dariyar take, takawa mama tayi da sauri ta girgizata cikin sauri ma,u ta hadiye dariyarta"

Asmau kinyi gamo ne? Cewar mama tana zare ido"

a,a mama wani abu na tuna jaye hannuta tayi tare da fadin barin nayi sallah na tafi makaranta"

Tundaga lokacin jikin mama ya mutu murus har lokacin da mau taxo mata sallama xata wuce"

Ahanyama babu abinda take sai tunanin deeni dan haka yau tanajin bata iya hakuri idan bata ganshi ba"

Bata biyawa zainab ba dan yau bazatabi ta lungu ba"

Sai dai har takai kofar gidansu deeni bata ganshii ba dan haka wata zuciyar tace kii shiga gidan mana"

Takawa tayi ahankali harta isa kofar gidan idonta tasa asakon kofar ta leka babu kowa sai ummi datai zaune kan kujera ta rafka tagumi"

Gabantane
yayi mugun faduwa sakamakon jin kokan katan kare abayanta, afirgice ta juyo sukai ido 4 da karan, baki ne mummuna bashi da kyan fasali ko kadan"

Tsugawa taga karan yayi zuwa can ya dago da karfii kaman zai yago mata fuska ganin haka ma,u ta saka uhu tare da neman hanyan guduwa"

Duk inda tabi shima be yake tare da kokarin yago hajjabinta ganin haka mau ta cire hijjabin tayi titi aguje"

Jitayi anjawota atsorace ta waigo deeni ne tsaye, gawani mutun mummuna agefen shi bayanta ta waiga ta hango karan aguje dauke da hijjabinta a bakin shi"

Ai batasan lokacin da ta kadandane deeni ba tana tsala uban uhu"

Kokarin rabata da jikinshi yake yana fadin Ohh sorry gaisuwa ce fah, *Duna* kenan meyasa kin cika tsoro.......









Heart beat
*Mmn Yazeed*​
[11/29, 8:57 PM] 80K: πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*



*Na sadaukar da wannan shafin garekiπŸ‘‡*
πŸ‘‘QueenπŸ‘‘πŸ˜˜

*Nima ILove u wojuga wojuga wlh😍*🍭



1⃣5⃣ to 1⃣6⃣




πŸ“’ Jin ya ambaci gaisuwa ce yasata jan jikinta ta koma gefe, tare da karabin karan da kallo"

Haryanzun hijjabinta na bakin shi, matsowa yayi ya ajiye hijjabin akasa sannan ya koma kusa da deeni yana goga kanshi ajikin deeni"

Sai alokacin ma'u ta tuna jikinta babu hijjabi hannu tasa ta rufe kirjinta, sannan ta matsa ta dauki hijabinta ta saka"

Karan tabi da kallo har yanzun Yana gaban deeni sai shafamai kai yake alman lallashi"

Tsaki taja azuciyarta sannan tace wannan bakin karan ne duna, ganin inda yake lallashin karan abin yai matukar bata haushi, hawaye ta fara matsowa acikin zuciyarta tace yanzun akwai miyon wannan mumman karan ahijjabi na wlh Allah ya isa, bata san cewa mgnr ta fito fili ba saiji tayi deen na fadin wa kikeyiwa Allah ya isa.....

Atsora ce tace ni bada kai nake ba, da wannan mummunan karan naka nake"

Ke *duna* kike kiran mummuna kinyi na farko yariya karki kara, idan kuma kika kara zan barki dashi"

Kallo kawai ta bishi dashi har yanxun lailaya kan Karen yake, harga Allah haushi yake bata dan me xaisa hannun sa yaita shafa kare batasan lokacin da tace toh kadaina shafashi haka mana"

Inaruwan ki ko kanki nake shafawa?

Kasa tayi dakai tana cigaba da kunkun"

Tunda ta fara motsa bakinta deen
yake kallon bakin amman ya kasa gane kalma daya da take Dada dan haka yace banajin abinda kikecewa"

Turo baki tayi sannan tace ai badakai neke ba"

OK da *Duna* kike kenan?

Shiru tayi batare da tace komai ba dan haka deen yayiwa caka mgn da hannusa gani tayi ya matsa can gefe ya tsaya atsakiyan hanya"

Kallonta ta mayar kan deeni gani tayi ya dago kan *Duna* yana mai mgn da ido aguje yayo kanta tare da haushi irin na mahaukatan karnuka"

Cikin gidan su deen tashiga aguje ummi na zaune tana wanke2 tayi fatali da ruwan cikin jikita ta shige ta kwakumeta"

Kobata tambaya ba tasan karen deen ne ya biyota dan tun dazun takejin haukan sa, rungumeta tayi ajikinta tare da fadin uban gidan nasa baya wajen ne ya bari yana tsorata Ki?

Sai alokacin kuka ya kwace mata cikin kukan tace ai shine yace mai ya biyoni"

Daidai lokacin deen ya shigo yana murmushi harara ummi a zubamai sannan tace nadai hanaka shigowa da karan nan uguwar nan kaki bari ko?

Ummi nakawoshi ne yagaida wannan yariyan ita kuma sai zaginshi take"

Ai dole ta xageshi auta tunda bata saba ba ita gani take tsoratata yake, yanxun zoka rakata ta shiga makaranta"

Makaranta ? Yau bazata makaranta ba lokacima ya kure"

Bude baki ummi tayi xatayi mgn amman deen sai ya mata wani irin siririn fito tare da kada mata hannu nan danan taja bakinta ta tsuke , shiko deen dakin sa ya shiga"

Daga ma,u har ummi tsaye suke saidai jikin ummi asanyaye yake kamar tana cikin damuwa"

Zuwa can ta waigo tace Asmau dan Allah ga abincin auta nan a kitchen taimaka ki kai masa rabon sa da abinci ya dade basan me yake damunsa ba"

Shiru ma,u tayi kanta akasa acikin zuciyarta tace toh meyasa bayacin abinci? Afili ko cewa tayi ummi wlh tsoron shi nakeji"

Murmushi ummi tayi sannan tace a'a karkicemin kinajin tsoron sa keda mutumin ki kuma? bubu abinda zaiyi miki tashi maza kije"

Jikinta babu kwari ta nufi dakin da taga deeni ya shiga sallama tayi abakin kofar bayan ya amsa tashiga"

Dakine dan karami daga can gefe akwai yar karamar katifa gefen katifan ko wukakene an jigine su a jikin bango"

Gyare dakin yake tsaf ahankali ta karasa gaban katifan ta aje kwanan tana kokarin mikewa ya rike hannun cikin sauri ta dago ta kalleshi"

Ido suka tsurawa juna natsayon wanni lokaci take ma,u taji tsigan jikinta na tashi nan danan idonta yacika da kwalla amman takasa dauke idonta akanshi"

Shiko deen wani irin farin ciki yakeji wadda betabajin irinsa ba har yanajin inama su kwana ahaka"

Murmushi yasaki wadda yai matukar dacewa da fuskanshi azuciyar ma,u cewa tayi inama ace haka fiskarshi take kullum"

Kasa ta sauke idonta tare da sauke ajiyan zuciya, haka shima deeni ajiyan zuciya ya sauki sannan yasa hannun shi ya sake dago fuskanta"

Runtse idonta tayi cikin wata dashashshiyar murya taji yace *Asmau* bude idonki ki kalleni"

Koro na farko da deeni ya kira sunanta agabanta dan haka taji yafi kowa iya kiran sunanta"

Bude idon tayi saidai baxata iya kallon sa ba kamar yadda yace dan haka ta durkusan da kanta kasa"

Jawota yayi daf dashi ya zaunar sannan yace meyasa kwana 2 baki zuwa makaranta?

Ina xuwa ta fada atakaice"

A'a karya ne bayan kullum inajiran ki akofar gida amman ban ganin wucewan ki"

Wlh kullum ina zuwa bandai wucewa ta nan ne "

Me yasa ?

Shiru tayi tana tunanin tagayamai abbanta yace zaiyi mata aure ne ko karta gayamai, idan bata gayamai ba toh mezata cemai?

Tunanin me kikeyi?

Bakomai "

Shiru yayi xuwa can yasake dagowa yace yau kinji ganina kenan shine kikazo kina leka mana gida"

Turo baki tayi kaman zatai kuka zuwa can taji ya sake cewa wadda ya dauki ki a mota ranan shine babanki?

Eh tace tare da kurawa kirjin shi ido"

Shiru yayi yana kallonta zuwa can yace me kike kallo?

Kai tsaye ta nunamai sarkan dake wuyan sa"

Kina sone?

Tana wasa da yatsunta take fadin a'a kacire ne beyi maka kyauba"

Dariya yayi sosai har hakoran shi suka baiyana zuwa can yace naji tunda bakison ganina da sarka saikizo kicire da kanki"

Tana cigaba da wasa da hannunta tace kacire da kan ka ai babu kyau mace ta dinga taba namiji"

Axuciyar shi yace kina da wayo babu kaifi afili kuwa cewa yayi toh bakison nadaina sawa kenan?

Mikewa tayi tare da fadin nixan tafi kar atashi amakarata bansani ba"

Daure fuska yayi sannan yace dawo ki zauna, idan lokaci yayi zan fada miki"

Zama tayi nesa dashi badan ranta yaso ba, kanshi ya turo mata ahankali ta fara warware sarkan duguwa ce sosai, kallon sarkan take tana mamakin wai mutum da hankalin sa ya dauki wannan karfen yasa ajikin sa"

Shiko deeni kallonta yake yana murmushi yana da tabbacin yadda *ZUCIYAR* shi ke buguwa haka ta ma'u ma take bugawa, xuben da ke karamin yatsan shi yacire ya kamo hannun ma'u ya zura mata"

Harcikin zuciyarta taji dadi kallon zuben tayi sannan tace nagode"

Murmushi yayi sannan yace toni me xaki bani?

Tsintan kanta tayi da cewa me kakeso na baka?

Duk abinda kika bani zanyi farin ciki dashi"

Cikin sauri ta ciro xoben da abban ta ya saya mata ta mikamai"

Nuke kafada yayi kaman yadda yara keyi yace bazan karba ba, ni ai saka miki nayi dan me xaki bani ahannu"

Shiru tayi cikin rashin jin dadi zuwa can tace ka karba ai be dace bane ina mace kuma.. ..

Kasa karasawa taayi dan haka deen yaja tsaki ya kwatar da kanshi akan katifan"

Ganin haka yasa ma'u taji babu dadi dan haka ta kamo hannun saidai duk yatsan da ta nufa zuben baya shi, daker ya shiga karamin yatsan shi, shima be gama shewa ba"

Tagama sawa tana kokarin mikewa ya mirginota jikinsa ya rungumeta tsam ajikin shi, tare da sunbata goshinta kumatunta zuwa kan lebenta, neman rikicewa yake, dan haka ma'u tafara kokari kwace kanta take mgnr abbanta ya fado mata, hawaye taji yana zubu mata"

Daidai lokacin ummi ta dago labulen cikin sauri deen ya mirgina ma'u gefe sannan ya cigaba da sauke ajiyan *ZUCIYA*"

Cikin sauri ma'u tamike tana gyara hijjabinta"

Itako ummi kallon deen take cikin bacirai zuwa can tace auta har ka manta alkawarin dakamin?

Be iya cewa komai ba dan koya bude baki besan me zaice ba"

Yana kwance yanajiyo fadan ummi, dakanta ta rike ma'u tayo waje da ita"

Jin asmau zata tafi yasashi mikewa dasauri ya fito samu yayi daidai ummi ta budewa ma'u kafar cikin sauri ya rike hannuta tare da zuba mata jajayen idon shi sannan yace gobe zaki zo ?

Tana share hawaye tace eh"

Murmushi yayi kadan sannan ya karkata kai"

*****

Tafe take tana kuka dan daganin yanayin garin andade da tashi makaranta"

Ta saka wannan ta kwance wancen tana tunanin wata karyan zata shirya"

Taci rabin ta fiya taga motar yaya usman ta wuceta"

Innalillahi ta fada azuciyarta Allah yasa be ganeni ba"

Hango motar tayi ta tsaya tana dawowa da baya"

Jitayi 'ya'yan hanjinta na motsawa daidai saitinta yaya usman ya tsaya ya zubo mata idonta shi sannan yace ke sai yanzun kike dawowa daga makarantar?

Mutumin dake zaune agefen shi ta kure da ido, gani take kaman kunki ne domin kwata2 baya motsi, jarida ce bude ahannun shi idonshi sanye da farin glass"

Yaya usman ne yace kagamin shegiyar yariya ina mata mgn tana kallon wani guri"

Zabura tayi ta dawo cikin hankalinta ta kara matso kuka tace"

Yaya wlh kare ne ya tareni ahanya ya hanani wucewa.....

Kutumar ubanki shigiya yar iska, ni xaki rainawa hankali duk cikin daluban be tare kowa ba saiki ? A ina kika tsaya?

Cikin kuka ta tattaro hijjabinta tace wlh yaya da gsk ne kagama yadda karan ya lalatamin hijjabi"

Takaici ne ya kama usman dan haka yace Allah ya kara, dayasani ma ya ciccije ki dan ubanki, kin tsaya shashanci duk dalubai sun wuce sun barki dallah dobeki saikace doluwa, ni shiga mota mutafi"

Tashiga mota? mutumin dake kusa da yaya usman ya tambaya batare da ya waigo ya kalleta ba har yanzun idonshi nakan jaridan"

Waigawa usman yayi ya kalleshi sannan yace wannan itace kanwata *Asma'u* danake baka lbr, wlh kwata2 yariyar nan batajin mgn"

Idonshi akan jaridan yace aina ganeta, kanta na rawa, naji kaman kana cewa ta hau mota, ai kamata yayi ta isa gida kafin mu isa"

Kumafa hakane usman ya fada yana kallon ma,u zuwa can yace asmau kafin mu isa gida nasameki acan, idan har kika bari na rigaki isa gida kashinki ya bushe"

Arude tace yaya amota kake fa ?

Muryan bakon taji yace ke!!, dakaran ya yabiyoki bakiyi gudu ba?

Idonshi nakan jaridan dan haka ta murguda baki tace nayi?

Toh irinshi zakiyi, idan kuma kikabari har mukaje gida bakizo ba, zan kirga mintocin da kika kara duk minti 5 yana da bulala 15, be jira mezatace ba yace usman muje"

Figar motan sukayi kankace me suyi nisa sai kellin motar take hangowa"

Cije lebe tayi sannan tace lallai abokin yayan nan bakin mugune har yafi yaya mugunta idan ba samun guri ba daga zuwanka bakunta zakace zaka dake ni ko gidan ma bakaje ba?

Cafdin ta fada afili wlh bazan tsaya ka dakeni ba idan ko ya dakeni da abba zan hada su"

Juyawa tayi ta fara tafiya lokacin data shiga gida ana kiran mangariba"

Aharaban gidan taci karo dasu zasu masallaci"

Abokin yaya taga ya kalli agogon dake daure ahannu shi sannan yaci gaba da tafiya batare daya kalleta ba"

Koda ta shiga gida mama bata nuna fushinta ba"

Dakinta ta wuce tayi wanka sannan ta dauro alwala Riga da siket ta saka na atamfa sannan ta saka babban hijjabi. ta tada sallah"

Bayan ta idar ta wuce dakin mama"

Tana shiga mamata tace ke kuma garinyaya kare ya tareki kinason kizama ballagaza ko?

Shiru tayi dan haka mama taja tsaki sannan tace wuce Ki dauki abinci ki kai falon abban ku"


Bata kawo komai a xuciyarta ba, ganinta abba zata ajewa abinci kafin ya shigo dan haka da karfinta ta shiga falon"

Turus tayi lokacin da taga abokin yaya zaune akan doguwan kujera ya miki kafa fuwan shi"

Cikin sauri ta aje abincin ta juya zata fita taji muryan yaya usman yace"

Ke zonan?

Dawowa tayi ta tsaya tana kokarin matso hawaye".

Jitayi ya sake cewa *JAMAL* gata"

Kaman jira yake ya juyo ya sakko da kafan shi kasa sannan yace kina da bulala 30"


Kallon su kawai take dan ita gani take wasa suke zuwa can taga wadda yaya usman ya kira da suna *JAMAL* ya mike sannan ya saka hannu a aljihun gaban gaban wandon shi daidai guiwa ya ciro wata zafgegiyar bulala sannan yace daga zanin Ki.....







Heart Beat
*Mmn Yazeed*
.β€‹πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*





1⃣7⃣ to 1⃣8⃣





πŸ“™ Na daga zani ? Lailai wannan dan rainin hankali ne aiko yaya betaba cewa na daga zanina ba, bare wani katon banza"

Muryan yaya usman taji yana cewa wai bada ke ake mgn ba?

Karya murya tayi sannan tace ai ba zani bane siket ne"

Abokin yaya taji yace koma menene ki dageshi sama"

Cikin sauri ta kalleshi saidai shi ba ita yake kallo ba"

Mikewa yaya usman yayi ya fice dan haka Asmau taita zubawa abokin shi harara"

Zuwa can taga ya fara tahowa yanazuwa daidai inda take yasa kafa ya kwasheta"

Ganinta kawai tayi akasa cikin sauri ta fara kokarin mikewa amma ina jitayi kwankwasonta ya rike"

Daker ta iya dago kanta ta kalleshi daidai lokacin daya dago hannu ya sauke mata mari"

Innalillahi wa inna ilaihir rajun'un ta fada da karfin saboda zafin marin ya shigeta, zaki daga ko bazaki dagaba?

Wlh zan daga arude ta Kwaye zanin har zuwa guiwa, tare da tsiyayar da hawaye"

Bulalan ya daga sannan yace idan kinga dama ki kirga, dan ni ba kirgawa zanyi ba, kuma idan kika sosa bandashi alissafi"

Fukanta cike da hawaye ta kalleshi acikin zuciyanta tace lallai wannan bakin mugune so yake yaga karshena, nan danan taji wata dakiya tazo mata, dan haka ta tsaya cak"

Kin shirya?

Eh tafada tana kauda idonta gefe"

Bulalan ya daga yaita zula mata tuntana daurewa harta kasa taita zuba uhu"

Shiko *JAMAL* kaman kara zugashi take har wani tsalle yake yi"

Goggo tani ce tajiyo uhunta tundaga cikin gida harda gudunta ta nufi idan take jiyo sautin kukan daker ta kwaci ma,u ahannun sa"

Hargun mama goggo tani takai ma'u tanaci gaba da korafin cewa adaina mata irin wannan dukan haka kwanaki usman ya mata dan banzan duka kartaxo ta saba da duka"

Mama batace komai ba mikewa kawai tayi tabar dakin"

Nan ma,u ta kwanta tanajawowa *Jamal* Allah ya isa acikin zuciyarta"

Ko ina ajikin ma,u ciwo yake dan yau abin ya mata yawa ga wahalan da *Duna* ya bata gana wannan dan iskan abokin yayan"


*****


Washegari ma haka ta tashi batajin kwarin jikinta dan haka batace zata makaranta ba"

Misalin 11 tayi wanka ta danji dadin jikinta, falon Abba ta wuce acan ta samu mama"

Gaban abba ta zauna ta tankwashe kafa sannan ta fashe da kuka"

Nan danan hankalin Abba ya tashi, zaman shi ya gyara tare da kura mata ido sannan yace"

Mamana waye ya taba ki?

Cikn kukan tace ba yaya usman bane yacewa abokinshi wai banajin, shikuma kawai sai ya ciro bulala ya hau dokana"

Abokin nasa?

Eh Abba"

Duka fa kika ce mamana?

Xanin ta ta fara dagawa tare da fadin eh abba kagama gurin"

Babban mgn Abba ya fada bayan yaga inda jikin ma'u yai rudu2"

Mikewa yayi sosai sannnan ya daga waya ya kira usman"

Cikin Monti 15 suka iso, dukka su jallabiya ce ajikin su fara kar"

Tunkafin su zauna abbba yake fadin a'a wanake gani kaman *Jamal*"

Mumurshi kamal din ya saki yana shafa keya yake fadin nine abbba"

Bayan sun gaida abbba hira suka hauyi, dan haka ma'u ta Kule"

Mikewa tayi tana kokarin tafiya Abba ya dakatar da ita sannnan yace"

Mamana kinga wannnan sunan shi Jamal yayanki ne shima, nida mahaifin shi tare mukayi wasa, dan haka yadda usman yake da daman hukuntaki shima yana da dama kijji ko"

Tana barin falon ta fara kunkunai kai tsaye ta wuce dakin mama dan daman tuni ta bar musu falon, zama tayi tare da share guntun hawayenta sannan taci gaba da kunkunan ta"

Mama na gefe tanajinta jefi jefi tana tsintan abinda take cewa, zuwa can tace"

Kee!!!! Tashi kibani guri, haka kurun zakizo kisani agaba kinamin mita toh me kikeso nayi rama miki zanyi kome?, yariya banda fitsara ba abinda kikasa agaba ke wacece da baza'a dakeki ba?, to kici gaba kece zakisha wahala"

Dahaka mama ta fice tabarta adakin"

Itama mikewa tayi tabar dakin"

Tundaga ranan asmau bata sake zuwa makaranta ba har wani satin ya zagayo, gashi kewan deen ya dameta, dan tasan yanzun har ya gaji da zuba ido"


***



Yau ta kama asabar dan haka tunda wuri ma'u tayi sallama ta fito"

Saidai tana fitowa taci karo dasu yaya suna kokarin shigowa"

Dauke Kai tayi taja gefe sanan tace ina kwanan Ku murya ciki2"

Yaya usman ne kawai ya amsa amman jamal gaba yayi, harta kusa fita taji jamal na cewa usman, kunabin bayan yariyar nan Kuwa....

Daidai lokacin suka sha kwana dan haka bataji amsan da yaya usman ya bashi ba"

Tana tafiya tana waige dan gani take kaman Jamal zai biyo ta"

Hango deen akofar gida shine yasata ta manta komai tundaga nesa ya sakar mata murmushi itama mayar mai tayi tare da sunkuyar da kanta kasa"

Tana isa gaban shi taja ta tsaya tare da kara sunkuyar da kanta kasa"

Babu abinda deen yake banda kallonta acin tuhuma ya

Please Login or Register in order to submit comment