Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nabinshi abaya rike da kayan da momy ta hada akaiwa mama"

Daidai lokacin Deeni ya fito ya wuce su ma'u ya angaje Usman"

Saura kadan usman yakai kasa cikin zafin nama ya jawo wuyan rigar deeni tare da shake shi da ita"

Kallon shi yayi sai ya ga kamar ya taba ganin wanna fuskan amman ya rasa ina ya santa"

Cikin fada usman yace waye kai?

Wata irin dariya deeni yayi , nafisa ce ta ruga cikin gida ta kira momy, itako ma'u tuni cikinta ya burga"

Cikin wata irin murya deeni yace sakarni"

Daidai lokaci Momy ta fito aguje deeni tarike tare da fadin haba shamsundeen menene haka?, sirikin ka ne fah yayan matar jamal y kawo mana ziyara"

Tsaki yaja sannan ya fincike rigarshi ya fita"

Hakuri momy ta bawa usman cikin bacin rai yabar gidan"

Har yayi nisa atafiya ya tsaya ya fara neman no Jamal domin yaji wanne dan rainin hakali ne agidan su"

Ya dade yana gwada duk layikan shi amman duk akulle suke, haka ya hakura"

Tundaga ranan deeni ya daina ko kallon inda ma'u take, amman kullum fuskan shi murtuk"

Wani lokacin d'aki yake shiga yaci kukan shi ya kushi domin zuciyar shi na gayamai Asma'u amanar shi zataci"

Akwai wani abu da ya kudura aranshi dan haka yabarta ta gama haukanta"

Dama kawai yake nema domin ya nunawa asma'u ba'a hada soyayyan shi data kowa"

Ganin yadda deeni keyi ya fara tsorata ma'u ayanzun babu wadda take son gani banda yaya jamal, dan haka ta yanke shawaran kiranshi ta gayamai, ko zata samu saukin halin da take ciki"

Tun safe take neman no Jamal har dare bata shiga ba"

Tsayon sati biyu kenan kulum saita neme no Jamal Amman bata samun shi kullum dakin Momy take kwana bata iya sakewa acikin gidan gada daya atakure take"


Ranan da Jamal yacika wata biyu da tafiya , abun ya fara damun ma'u tun daga ranan da yaya usman yazo bata kara samun no Jamal ba, dan haka yau ta yanke shawaran samun momy da zancen"

Afalo ta same momy ta rafka uban ta gumi gefen idonta hawaye ne kwance"

Zama ma'u tayi jikinta asanyaye tare da fadin momy lfy kuwa?

Zabura momy tayi domin ita batasan da shigowar ma'u ba nan danan ta kakaro murmushi tare da fadin lfy lau asma'u"

Shiru tayi zuwa can, tace momy kulum na kira wayar yaya Jamal bana samun sa"

Adaburce momy tace wata kila network ne amman ni kullum muna waya, akwai abinda kike sone?

Girgiza kai tayi tare da fadin nagadai kwana biyu be kira bane"

Gefe ta koma ta takure gsky tanaso jin muryan Jamal sannan ta gayamai deeni nacikin gidan su" tasan kome yake har yaji deeni na gidan nan zai bari ya dawo"

Tanacikin wannan tunanin wayarta tayi kara, no usman ta gani cikin sauri ta dauka"

Tana dauka taji usman na fadin Asma'u Jamal ya canja no ne?, wadda nake dashi yafi wata akashe"

Take taji gabanta ya yaken ya fadi kafafuwanta rawa kawai su, muryanta na rawa tace"

Yaya nima rabon da muyi waya tun randa kazo"

Me ?, Taji ya fada atsorace, tare da kashe wayarsa"

Hakanan taji hawaya na zubo mata, anya kuwa lfy amman momy tace yana kiranta, shiru tayi zuwa can tace"

To meyasa naga momy na share hawaye kai Jamal babu lfy"

Mikewa tayi ta shiga cikin dakin momy, agado ta sameta tana zaune sai share hawaye take idonta jawor"

Ji tayi kafafuwanta sun kasa daukanta zamewa tayi tai zaman dirshan akasa daidai lokacin nafisa ta shigo itama idonta jawur, dan haka ma'u ta fashe da kuka"

Daga momy har nafisa kan ma'u sukayo tare da kokarin boye hawayen su"

Cikin kuka tace momy ku gayamin abin da yake faruwa ku cireni aduhu, ina yaya Jamal yake ? Idan wani abu ne ya sameshi agayamin "

Jawota momy tayi ta rungume sannan tace, Jamal na nan lfy lau....

Umm umm momy ba lfyrsa lau ba wayar sa tafi wata bata aiki"

Waye ya gaya miki, ki kwantar da hankalin ki, yanzun inda suke ne babu daman waya, kuma ai wata 7 yace zaiyi dukka fa wata 2 kenan da tafiyar sa memene abin damuwa?

Daidai lokacin daddy ta alhaji bashir suka shigo ko wanne hankalin shi atashe"

Ganin momy rungume da ma'u daddy yace yaya aka yi?

Yake momy tayi sannan tace tafara damuwa darashin kiran mijinta ne"

Shima yake yayi sannan yace ai yanan lfy, Meye abun damuwa, juyawa sukayi suka fita cikin sauri momy ta zame ma'u tabi bayan su"

Ma'u naganin fitan momy ta bude jajayen idonta ta kalli nafisa sannan ta riketa katam tace"

Hardake ake boyemin ko?, dan Allah ki gayamin gsky menene ya same shi?

Bakomai nafisa ta fada tana kallon cikin wayarta"

Cikin kuka ma'u tace shikenan amman nasan ba gaskiya kuka fada ba, bayan naga momy tana kuka kema kina kuka.....

Wayarta ce tayi kara tana kallah taga yaya usman cikin sauri ta dauka"

Ba momy wayar abinda yaya usman yace kenan, cikin sanyin jiki ta nufi hayar falon kamar me koyon tafiya







Heart Beat
*Mmn Yazeed*πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*




​7⃣4⃣to7⃣7⃣




πŸ’πŸ’πŸ’ Momy ni yau adakin ki zan kwana"

Da mamaki momy ta kalleta sannan ta danyi murmushi kadan tace"

Halan Nafisa na takura miki da shegen surutunta?

Kin kallon inda deeni yake tayi tace a'a bahaka bane, akwana biyu inayin mafarkai idan na farka ina kasa bacci tare da tsoron dakin"

Shiru momy tayi zuwa can tace"

Asma'u kinayin addu'oi kuwa?

Inayi momy"

Tsakin da deen yaja ne yasa duk suka kalleshi"

Momy ce ta lura harara yake zafgawa ma'u, dan haka ta kira sunan shi sannan ta nuna ma'u tare da fadi"

Wannan itace Asma'u matar jamaludeen dan uwan ka, nasan baku san juna ba ko?

Wani haushi ne ya kama Jamal wadda yasashi mikewa batare da yasan lokacin ba"

Kallon shi momy tayi tace wani abu ne? Naga inakan maka mgn ka mike"

Daker ya iya sarrafa kanshi ya koma ya zauna sannan ya hura iskan dake bakin sa yace"

Naganta momy gsky yayi dacen mata kuma sunan ya dace da ita"

Murmushi momy tayi tare da fadin wlh kuwa nima ina farin ciki da kasancewan ta matar jamal, kaima Allah ya baka yariya me hankali kamarta"

Ma'u banda dukan uku uku babu abunda kirjinta kemata, duk atsorace take, kin yadda tayi su hada ido da deeni duk da ta lura abun da yake so kenan"

Muryan shi taji yana cewa ameen momy amman nima inada yariyar da nakeso itama sonanta Asma'u tana da kyau sosai kamar waccen Asma'u"

Ma'u jitayi hanjin cikinta na tsintsinkewa addu'oi take karantowa acikin zuciyarta, tare da kerman jiki"

Itama momy haka kawai taji bataji dadin zancen deeni ba, amman dama tuni ta lura lamarin shi akwai gyra, juyawa tayi tace asma'u shiga dakina ina zuwa"

Mikewa tayi badan ranta yaso ba dan batason tabar deeni da momy dan tana gudun karyaje ya fadi wata mgnr da zata jawo illah arayuwarta"

Tana daf dashiga dakin taji muryan deeni yana cewa"

Allah yasa yadda kuke sonta itama tana sonku haka"

Wani irin kallo momy ta masa sannan tace"

Meyasa kace haka?

A'a na fadane kawai momy, momy kinsan menene?

Saika fada"

Kwantar da kanshi yayi ajikin kujera sannan yace"

Yariyar da nakesonta take sona babanta baya kyaunata yaki bani ita sannan ya gayamin wasu kalamai da suka girgizani, duk da cewa duk abin da ya fadin haka ne, amman naji zafin sa sosai soboda kalmar da yayi ammafani da ita wajen mgnr sa"

Nisawa yayi kadan Momy na sauraron sa, sannan yace gaba da cewa"

Wlh tsohon nan kawai yaci darajan son 'yarsa da nake amman wlh dasai na zubar masa da hakora"

Baki momy ta rike tare da fadin shamsudeen abin naka har yakai haka"

Wani irin bazawaran murmushi deeni yayi sannan yace Momy kenan, wlh ina tsananin son 'yarsa banajin zan iya barinta jinina da nata gauraye yake, banzan iya barinta ba momy rasata na nufin tsayawar numfashina


Duk abinda deeni ke fada ma'u na makale tanaji innalillahi wa inna ilaihir raju'un kawai take ambata tare da fadin wacce irin masifa ce wannan Allah ka kawo min mafuta"

Muyar Momy ta tsinkaya tana cewa Shamsundeen inason na fahimtar dakai wani abu guda daya, ka dauka kamar kana mgn ne da mahaifiyar ka wacce ta tsuna ta haifeka"

Maida hankali deeni yayi gurin Momy"

Tana kallon cikin idon shi tace Shamsudeen waye ya gaya maka anaja da iyaye? tunda mahaifinta yace bazai bakaba toh kayi hakuri kabar masa 'yarsa"

Cikin sauri yace momy bashi da wani dalili, bakinciki kawai yake min, ya dauki laifin da banawa ba ya daura min, momy daman laifin wani nashafar wani?

Tuni momy ta dago inda zancen deeni ya nufa, dan haka taji tausayin sa ya kamata"

Shima nan danan idon shi ya kankanci ranshi ya dada baci jikin shi har wani rawa yakeyi"

Mikewa momy tayi ta koma kusa da deeni ta zauna sannan ta jawoshi jikinta kamar yadda takewa jamal idan ta kula yana cikin damuwa"

Shafa kanshi take tare da fadin....
Laifin wani baya shafan wani shamsudeen amman na saratu dana bashir dole ya shafe ka"

Cikin mamaki deeni ya daga kai ya kalli momy"

Nasan komai deeni Saratu da Bashir sun aikata babbab kuskare, Idan su ya rufe sunbar mummunan tarihi, sannan bayan wannan tabo da suka maka aduniya, basu baka tarbiya yadda ya kamata ba"

Kallon deeni tayi da hawaye suka fara zubowa kan kuma tunshi sannan taci gaba da cewa"

Shamsundden bazan boye maka ba, gsky daya ce, duk mutumin da yake da mutunci ba zai haifi 'yarsa ya mata tarbiya maikau sannan ya dauka ya baka ba"

Haryanzun kallon Momy deeni yakeyi hawaye shabebe a idon sa"

Kafadar shi Momy ta kama sannan tasa idonta cikin nashi tace,

Ba'ina gaya maka bane dan nabata maka rai ko kuma na tunzuraka kaji haushin iyayen ka a'a abinda ya faru ya riga ya faru, ina gaya maka ne domin kasan inda zakasa gaba, ma'ana ka gyara halayen ka da kanka"

Yau koda ace kana da cikeken asali amman kana cikin rin wannan rashinji, duk da haka babu wadda zaiso yaba ka yarsa, saboda babu mutum me mutunci dazaiso ka zama sirikin sa"

Da ace kuma bayan haihuwarka iyayen ka sunyi nadama suntsaya sun baka tarbiya tare da ilmin addini tare dana zamani sosai, koda wani zai nemo asalinka wani bazai nemo ba, koda ace anbinciko ma idan wani be maka uzuriba wani zai maka, hawayen dake idonshi ta fara sharemai tare da fadin dan Allah ka gyara dabi'un ka kuma idan yariyar rabon kace zakaga ka sameta"

Gargiza kai yayi tare da fadin indai hakane momy sun cuceni, kuma idan sukai sular rabani da asma'u bazan yafe musu ba har abada"

Karkace haka shamsundeen"

Jikin deeni har rawa yakeyi wajen fadin wlh momy ina masifar sonta, banaso na rasata, wlh momy daga ranan danaga anyi nasara rabani da ita zan kashe Kaina.....

Kaji irinta ko ?, meyasa zaka nuna kai bakasan kaddara ba, Allah yana jarabtan bawan sa ne domin ya gwada imanin Sa.....

Bebari momy ta rufe baki ba yace"

Toni meyasa za'a jarabani ta wannan hanyar yaseeen bazan iya dauka ba......

Cikin sauri Momy tasa hannunta tarike bakin deeni sannan tace toh ya isa haka mubar zance, zan tayaka addu'a idan yariyar alheri ce agareka Allah ya baka, idan....

Taren numbashinta yayi da fadin, momy bar addu'an ki yaka daidai nan"

Kallo kawai momy ta bishi da shi sanna tace Allah ya yaye maka abin da ke damun ka, akwai wani malami daya ke mana karatu da, gobe zai dawo ya fara mana karatu ni dakai"

Kai kawai ya daga sannan ya mike ya fita"

Duk hirar su ma'u taji, tun bata fahimta ba, hartazo ta fahimci inda zancen yasa gaba, daki momy ta shiga ta zauna tare da tsananin tausayin deeni acikin zuciyar ta tace inama zan aure deeni da na mantar dashi bakin cikin dake cikin zuciyar shi"

Share hawaye tayi sannan taci gaba da cewa"

Tayaya hakan zai faru? Yaya zanyi insami deeni? Dakanta taba kanta amsa sai Jamal ya sake ni"

Hawaye ta sake sharewa sannan tace anya kuwa Jamal zai sake ni, wata zuciyar ce tace shifa ya fada, yace bazai iya rayuwar aure dake ba, sannan yace shida yaya bashir basu da babbaci harcewa yayi shi mata basa hawa gadon sa"

Toh meyasa shi yahau naki gadon ? Kuma har yayi wasu abubuwa, wannan yanuna abinda Jamal ya fada ba gsky ba ne, kuma kafin tafiyan shi ya jajjada min karna mai wasa da aure"

Shiru tayi zuwa can tace zaiyi wahala Jamal ya sake ni, hakika da anba mace damar auren maza biyu dasai dai jamal yaji na kara aure da deeni"

Daidai lokacin Momy ta shigo, bin ma'u tayi da kallo sannan tace Asma'u daga yau idan zaki fita falo kisamu karamin hijjabi ko mayafi ki riga sanyawa, dan kinga yanzun gidan bamu kadai bane"

Saida gabanta ya fadi jin kalaman momy, saitake ganin kota fahinci wani abune akalaman jeeni?

Tokawai tace sannan ta dada share hawayen dake makale a idonta"

Adakin momy tai zamanta, momy ma bata kara ce mata komai ba, daddare nafisa ta biyota da abinci, bayan sun gama ci tace toh tashi muje mukwanta"

Kememe taki zuwa nafisa tai nacin ta har tagaji ta fice"

Kashe kawayarta tayi gaba daya dan gudun kar deeni ya kirata"

Ganin yadda ma'u ke firgice daga taji motsi kadan ta kalli kofa dan haka Momy taje ta rufe daki"


*****


Washegari ma batace zata fitaba tana nade adaki"

Dafisalin karfe 1:12pm Momy ta shigo takalli ma'u tace Asma'u taso maza kinyi bako"

Atsora ce ma'u ta mike tare da fadin waye?

Cikin ido momy ta kalleta sannan tace wai Asma'u meke damunki? anya kuwa kinayin addu'oi?

Inayi ma'u ta fada tana kokarin saka hajjabi"

Harta fara tafiya Momy tace bakon yana part din Ku"

Gabanta taji ya fadi sosai, Allah yasa ba deeni bane"

Tana tafe tana addu'oi, tura kofar tayi tare da sallama tana raba ido"

Yaya jamal ta gani zaune cikin kaki, da alama ya dade da zuwa, wani farin cikine ya kamata harta sake murmushi batare da tasan lokacin daya fitoba"

Dama yaya Usman ya damu dani? Daman yaya usman na sona? Hawaye taji ya cika mata ido"

Fuskar usman dauke da murmushi yace karaso ki zauna mana"

Cikin sanyin jiki ta karasa ta zauna, tare da matso hawayen dake makale a idonta"

Bayan hannunta tasa ta share hawayen sannan ta shiga gaida usman tare da tambayan shi mutanen gida"

Cikin sakin fuska ya amsa tare da tambayar lfyr ta"

Kula yayi ma'u kuka take dan haka ya tsareta da ido tare da fadin"

Asma'u yaya haka?, ko bakiyi farinciki da zuwana bane?

Bahaka bane, naga baka taho da dada ba, kuma yace min tare zakuzo?

Murmushi usman yayi kadan sannan yace waye yace miki tare zamuzo"

Idonta akasa tace yaya Jamal"

OK eh da tare zamu taho amman tace bazatazo ba"

Hawaye ne yaki tsayawa a idon ma'u zobowa kawai yake tare da ajiyan zuciya"

Kallon ta Usman yayi acikin zuciyan shi yaji tausayinta dan haka ya daga wayan yana kiran dada"

Mika mata wayar yayi tare da fadin ga dada"

Amsan wayar tayi ta kara akunnenta muryan dada taji tana fadin Usman katafi gidan tame karan ne koko kaima ka fasa"

Dada? Ma'u ta fada ahankali"

Wiiii !! , takwara ce?, kice harya iso"

Hawaye ta share sannan taja majina eh, meyasa kikaki biyo yaya bayan angayamin zakizo kuma harna sarai"

Wa? ni ? Allah sunturu bukui, ai idan kika ganni alahira kaini aka yi, haka kurun, ku hada baki dame kare ku kasheni ? aini har yanzun ban yadda dake ba takwara, saina ganki da tsohon cikin Jamal"

Guntun tsaki ma'u taja sannan ta kara share hawaye tace"

Dada me kika maidani?, dan Allah ki daina irin wannan mgnr ni mahaukaciya ce?

A'a da hankalin ki amman idonki ya rufe baki ganin kowa sai me kare"

Hmmm dada yanzun yashe zakizo?

Sai ranan da kika haihu zanzo namiki wankan jego"

Wani haushi ne ya turnuke ma'u, dan haka tace toh kibarshi karkizo ma, kuma ni kidaina cemin tame kare, ko mun hadu ahanya ma karki nuna kin sanni....

Batajira me dada zatace ba ta kashe wayar sannan ta mikawa usman"

Dariya ce cike da cikin Usman Amman ya dake bakace abin ya bashi dariya ba"

Amsan wayar yayi tare da fadin yau kwanan Jamal nawa da tafiya?

Dogowa tayi ta kalli yaya usman sannan tace,
Zaikai sati 3"

Jinjina kai yayi sannan yace"

So nawa kika kirashi awaya?

Guntun hawayen ta share sannan tace aiko ankira ba samun shi"

Shiru usman yayi zuwa can ya fara mata nasiha cikin kwaciyar hankali"

Jikin Asma'u yayi sanyi sosai sabo da yadda usman yake xayyano mata girman miji agun matar sa, duk da duk abinda ya fadi ta sansu amman ya kara farkar da ita"

Babu abin da take tunawa sai yadda Jamal yaita mata magiya adaren da zai tafi, yanzun kenan mala'ikun Allah sun tsine min?

Hawaye ne suketa zubomata babu kyaukyautawa"

Bayan usman ya sarara sai ya shiga neman layin jamal"

Saidai babu sa'a domin wayar sa kashe take dan haka ya fara neman dayan layin"

Saida ta kusan katsewa sannan ya dauka, cikin dariya taji suna gaisawa sannan ya gayamai gashi agidan su"

Gani kawai tayi usman ya miko mata waya, dan haka adaburce ta karba tasa akunnenta"

Gaidashi tayi saida ya dade kafin ya amsa sannan yace ya bakin, kiji sauki?

Eh kawai tace idonta akasa"

Shiru sukayi dukkan su zuwa can Jamal yace *Husna* ?

Saida Asma'u ta lumshe idon saboda muryar da Jamal yayi amfani da ita wajen kiran sunan ta"

Daker ta iya amsawa sabo da yadda muryansa ya kashe mata jiki"

Ahakali yace sanyin nan fa har yanzun inajin shi, wanne shawara zaki sake bani?

Kasa mgn tayi dan haka ta kashe wayar, Cikin sauri ta mikawa usman, saidai kafin wayar taje hannunsa Jamal ya sake kira"

Janye hanunsa yayi dan haka ta maida wayar kunnenta"

Husna meyasa zaki kashemin waya?, ko kina kunyar usman ne? Idan kunyarsa kikeji tashi ki koma daki"

Kallon inda usman yake tayi ganin tayi hamkalin shi nakan wayar da take hannusa, dan haka tacewa Jamal a'a

Toh kina jina nacemiki sanyi na damuna, da daddare bana iya bacci sosai sai naji gadon yamin fadi, wani lokacin saina rungumi filo nakejin dadi"

Sai yanzun ta fqra dago inda yasa gaba, shiru tamai dan batasan mezatace ba"

Husna ya kikayi shiru?, wlh na kosa na dawo, Husna anya kuwa bazan ajiye aikin nan ba"

Shiru yaji dan haka yasashi fadin Husna kinajina kuwa"

Ummm ta fada tare da kallon yaya usman"

Jamal ne yace meye ummm?, to shikenan tunda bazaki min mgn ba sai an jima, amman ki shirya idan na dawo akirjin Ki zan rinka kwana"

Cikin sauri ta kashe wayar domi mgnr Jamal ta girmi kunnuwanta, wai meyasa maza basu da kunya?

Da misalin karfe 4:34pm usman yayi sallama fitowa yayi nafisa da asmau nabinshi abaya rike da kayan da momy ta hada akaiwa mama"

Daidai lokacin Deeni ya fito ya wuce su ma'u ya angaje Usman"

Saura kadan usman yakai kasa cikin zafin nama ya jawo wuyan rigar deeni tare da shake shi da ita"

Kallon shi yayi sai ya ga kamar ya taba ganin wanna fuskan amman ya rasa ina ya santa"

Cikin fada usman yace waye kai?

Wata irin dariya deeni yayi , nafisa ce ta ruga cikin gida ta kira momy, itako ma'u tuni cikinta ya burga"

Cikin wata irin murya deeni yace sakarni"

Daidai lokaci Momy ta fito aguje deeni tarike tare da fadin haba shamsundeen menene haka?, sirikin ka ne fah yayan matar jamal y kawo mana ziyara"

Tsaki yaja sannan ya fincike rigarshi ya fita"

Hakuri momy ta bawa usman cikin bacin rai yabar gidan"

Har yayi nisa atafiya ya tsaya ya fara neman no Jamal domin yaji wanne dan rainin hakali ne agidan su"

Ya dade yana gwada duk layikan shi amman duk akulle suke, haka ya hakura"

Tundaga ranan deeni ya daina ko kallon inda ma'u take, amman kullum fuskan shi murtuk"

Wani lokacin d'aki

Please Login or Register in order to submit comment