Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aure asma'u, bayan d'an uwana na auren ta, daddy kayi kuskuren cewa Jamal yabar min mata, wlh na barta har abada, dan Allah abani no Jamal nakirashi ya dawo gida, zama awani waje be dace dasuba"

Kowa afalon kuka yake yi ba mazan ba ba matan ba"

Daddy ne ya share hawaye sannan yace......

Ai be tafi da waya ba, dan dana kira naji karanta adaki"

Shiru deeni yayi zuwa can yace........ .


Daddy ina son nayi aure, nabaka zabi ka zabar min mata ko ya take indai ka amince da tarbiyan ta, inaso na haifi yara na musu tar biya ba irin wacce akamin ba






Heart Beat
*Mmn Yazeed*πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*
​



1⃣0⃣4⃣





Takaici ne ya kama alhaji bashir, tare dajin bakin cikin abin da ya aikata abaya, ga dukkan alma deeni baya al'fahari da zaman su iyaye agare shi"

Itama ummi kuka take tasani tuna baya garesu abin kunya ne, suna da mummunan fenti"

Daddy ne ya share hawaye sannan yace"

Allah ya maka albarka shamsu, naji dadi daka fahimci haka, kuma nima nasan banma Jamal adallaci ba, gani nake kamar bazaka rayuba, rayuwarka taban tausayi, inason nan gaba rayuwar ka tai kyau, atunanina sai ka same asma'u ne zaka tsaya ka gane me rayuwa take ciki, duniya ba wani abubane shamsu inda kasan wasan kwaikwayo haka take, idan ka biyewa son zuciya saikakai kanka ka baro"

Nisawa yayi sannan yaci gaba da cewa.....

Shiyasa Jamal yaban mama ki daya zabi barin gida, hakan dayayi ya nunamin yana son matar shi, matsowa daddy yayi sannan ya dafa kan deeni yace....

Shamsu insha Allah matar da zan zabo maka saikayi mamaki, fatana ka kwantar da hankalin ka, kuma kaci gaba da daukan karatun ka agun malam"

Ana cikin haka momy ta mike ta shige daki bakomai ke damunta ba illah barin Jamal daga gida, ba laifin kowa bane illah na alhaji, idan kafar Jamal ta samu matsala dashi xatayi kuka, inama shika dai ya tafi, da hankalinta bazai tashi sosai ba"

Akacin wannan tunanin ummi ta sameta, dago ido momy tayi ta kalleta ta sake maida kanta"

Saida ummi ta share hawaye sannan tace zamu tafi"

Toh kugaida gida Momy ta fada fukarta daure"

***


Bayan fitan suma momy zama tai taishiru kamar wadda akawa mutuwa"

da dare daddy
ya samu momy adakinta, acikin dibara ya fara sako mata zancen shawaran daya yanke, akan cewa mezai hana ahada shamsu da nafisa"

Cikin sauri momy ta mike tare da fadin Sam alhaji, dan me zakace nafisa ta auri shamsu?, kodan kaga bakai ka haifeta ba?

Wani irin kallo daddy ya mata sannan yace....



Yanzun ne dai zaki nunamin bani na haifeta ba, dan inda ace nina haifi nafisa bazan yi shawara dake ba, tun agurin zance nabashi nafisa, ni yanzun roko nazo dan Allah kicire tunanin komai insha allahu alheri ne"

Nifa alhaji bakin shamsu nake ba, dabi,un shi neke tsoro"

Ai yanzun ya shiryu ke dajin kalaman shi na dazon kisan kura tayi lfy"

Eh tabbas ya gyara abubuwa da dama amman alhaji shamsu fah ko mgnr arziki yake sai karkace baki abin ya riga ya zamar masa jiki, sannan har yanzun inajin kyankyanin rayuwar da iyayen shi sukayi, ina musu kallon tsofaffin banza"

Kul daddy ya fada sannan yaci gaba da cewa.....

Karki zama me roko, komai me wucewa ne"

Hmmm Alhaji idan na yadda aka hada wannan aure na cuci nafisa, kuma ma ai dangin babanta bazasu yaddda ba"

Murmushi daddy yayi kadan sannan yace......

Ai bayan fitana dazon naje wajen wan babanta, mun gama mgn dashi yakuma ce sun bani wuka da nama, na yi komai idan nasa rana na sanar masu"

Shiru momy tayi zuwa can tace kuma ka gaya musu waye shamsu??

Cikin fada daddy yace.....

Nace mishi dan kanina ne, kuma ban amince kije ki gaya musu wata mgn ba, na lura so kike ki tuzarta ni, kamata yayi kiyi addu'a Allah yasa alheri muke shirin kullawa"

Mikewa momy tayi
tana share hawaye tare da fadin shikenan alhaji idan kaga dama ma kayi gunduwa gunduwa da nafisa, amman kafin kayi abinda kaga dama ka nemomin dana ya dawo gida dan baza ahada min zafi 2 ba"

Dariya daddy yayi tare da fadin wannan kicire shi azuciyar Ki, ai shiba mahaukaci bane"

Cikin kuka momy tace nifa idan Jamal be dawo gidaba hankalina bazai kwanta ba"

Tsaki kawai addy yaja sannan ya fice abinshi

Bayan kwana biyu daddy ya shiga har dakin nafisa, kwace take tana latsa wayarta ganin daddy yasata saurin mikewa"

Murmushi daddy yayi sannan yaje bakin gadon ya zauna, sannan ya kira sunanta

Ahankali ta amsa daddy yaci gaba da cewa, nasan zaki mamakin ganina adskin ki ba komai bane ya kawani illah wani alhri da muke shirin kullawa, mum yake shawaran hadaku aure keda shamsu"


Nasani ke yariya ce me biyayya, kuma nasan zaki amince da bukatata, karki yadda momyn ki ta zugaki insha Allahu zamuce gara da akayi"

Kan nafisa akasa wasa take da hannun ta, hakan nan ta tsinci kanta cikin farin ciki saidai fauskan Jamal tana firgitata lamarin shi yana bata tsoro, Allah yasani tun ranan dataga deeni ya kwanta mata arai tsoron fasifar shi yasa tayi nesa dashi"

Mikewa daddy yayi tare da fadin umarni na baki bana neman zabinki, ina fata bazaki ki jin umarnina ba"

Kai da daga ahankali, sosai daddy yaji daddy har yabar dakin yana samata albarka"

Shirye shiryen baki daddy ya hauyi gadan2 komai da ake zubawa yar gata daddy yasa anzuba agidan da yabawa deeni"

Shiko deeni bawani shiri yake ba, domin kokari yake yaga rayuwar sa ta gyaro, bema san wacece amaryar ba, kuma be damu ya sani ba, burinshi kawai yaga ya aje iyali"

Abangaren momy kuwa, kullun fuskarta daure take tam, taki gayawa kowa zancen auren nafisa, dan haka daddy da kanshi ya sanarwa dangita"

Koda yayyata sukazo lallashinta suka yi, akan tayi hakuri insha Allahu auren zai bata mamaki"

Haka shirye shiye ya dada kankama nafisa sai rawar kai take, tare da kawayenta, sosai takebawa momy haushi, saidai batace mata kala, har biki ya rage sati, kuma aranan ne Jamal yacika sati uku da barin gida"


****


Jamal da ma'u nagani agaban doctor, sai ya mutsa fuska take Jamal na tarota"

Bayan Dr ya gama rubuce rubucen sa ya dago ya kalli jamal yace"

Ranka ya dade inaganin abin da yafi kawai, ku raba makwanci har cikin yayi kwari, domin idan har zaku dinga haduwa za'a samu matsala gaskiya"

Shiru Jamal yayi zuwa can ya daure fuska tare da fadin.....

Bakomai insha allahu zan kiyaye, sai mgnr kafata?

A kafar ka Alhamdulillah ta cike saidai ansamu matsala inaganin daga Dr dake wanke maka ciwon ne tun da farko, dan gashi bata warke yadda ya kamata ba, amman bawata matsala"

Godiya Jamal yawa dr sannan ya daga ma'u suka fito"

Biyosu Dr yayi tare da fadin Oga akiyaye fah"

Bayan sun koma gida tarairayan ma'u Jamal keyi sosai baya yadda ta dauki ko kofi abinci ma abaki yake bata, cak yake daukanta ya kaita toilet yai mata wanka, cikin dare ko haka yake rungumeta tsam ajikin shi, kamar dai wani zai kwace masa ita"

Har mamakin Jamal ma'u take wai ayanzun ita Jamal yakewa bauta, duk girman kannan ya ajeshi agefe"


Bayan sati 1


Yau jamal ya tashi da tunanin gida sosai axuciyar shi dan haka yadau waya yasa no momy"

Bugu biyu ta dauka, hayaniyan mutane yaji tare da dallaman Momy"

Ahankali ya amsa"

Arikece momy tace......

Jamal?

Na'am momy kuna lfy?

Kaniyarka Jamal, kai kana da hankali kuwa?, kana inane yanzun?

Momy nakirane naji lfyr ku kuma kusan muna lfy"

Jamal ina Asma'u?

Tana toilet"

Kafarka fah?

Karamar dariya Jamal yayi tare da fadin ta warke mom......

Karya kake Jamal be isa ta warke ba"

Wlh Momy ta warke bari zan turo miki pic dinta kikani"

A'a karka turomin kadawo gida kawai Jamal, hankalina bazai taba kwanciya ba, sainaga ka dawo idan ma kai bazaka dawoba toh katuro Asma'u gida"

Kawar da zancen Jamal yayi tare da fadin momy wai baki gida ne naji hayaniyan mutane ne"

Ina gida Jamal, bikin Nafisa ake yanzun aka daura mata Aure"

Aure kuma Momy?

Fashewa momy tayi da kuka tare da fadin eh Jamal daddy ka ya matsa saiya aurar da ita"

Da sauri Jamal yace dawa?

Da shamsudeeni"

Deeni ?, momy ta yaya zaki bari adaura wa Nafisa aure da deeni?

Jamal kasan halin daddyn ka da kafiya da naso hanawa ma cewa yayi dan naga bashine ya haifeta ba, dan haka nabarshi yayi abin da yaga dama da ita"

Hakuri Jamal ya karabawa momy sannan ya mata alkawarin sunanan dawowa"

Bayan ya aje wayar ya tashi ya shiga dakin baccin su, ma'u na kwance akan gado, hawa yayi ya kwanta, sannan ya jawota jikinshi ya rungume tare da sun batanta ta, acikin kunnenta ya rada mata yau kawarki na Aure"

Zainab ? Ma'u ta tambaya"

A'a Nafisa"

Tashi tayi ta zauna tare da fadin nafisa?, naga yau satin mu 4 anan kuma banji ana mgr aurenta ba"

Eh daga baya ne"

Tabe baki tayi tare da fadin aiko banji dadiba naso ina gida za'ayi, to wa ta aura?

Kauda kai yayi sannan yace deeni"

Deeni? Yaya da gaske???

Zan miki karya ne?, yanzu nakira momy awaya take fadamin"

Guri daya ma'u ta kurawa ido, tare da kokarin danne abinda ke shirin bijuro mata"

Kallonta kawai jamal yayi sannan ya mike ya fita adakin"

Hawaye taji yana zubo mata ahankali ta fara tuno irin rayuwar da sukayi da deeni abaya"

Acikkn xuciyanta take cewa...

Haka Allah ya nufa deeni ba mijina bane bazamu zauna tare ba, duk irin soyayya da mukayi tazama abanxa abubiwan da sukaitayi ne yaita fado mata, zama tayi kamar mahaukaciya wani tai murmushi wani tai hawaye, acan karkashin zuciyanta ko bataso nafisa ta aure deeni ba taso yasamu watacan ya aura"

Tun daga ranan yanayin ma'u ya dan canza haka ma Jamal dayake lora da ita"


***

Deeni ko Sai a Wajen daurin auren yasan nafisa ce amaryan, fuskan shi babu yabo babu fallasa, abokan shi na kano duk sunzo cikin manyan kaya kamar basuba, bayan andaura aure duka suka wace caka ne kawai ya tsaya"


Lokacin da caka zai raka deeni gidan shi saida suka fara biyawa gidan alhaji bashir sosai sukamai fada harsaida abin ya bashi mamaki, bayan sun mike ummi ta kalli caka tace wlh bakuga inda kukayi kyauba, kamar baku ba, wai ya sunanka ne?

Cikin murmushi caka yace ummi sunana *Faisal*

Hannu ummi ta tafa tare da fadin sunanka me dadi ake cemaka wani wai caka, dan ALLAH auta daga yau ka rinka kiranshi da sunan shi"

Addi'oi tayimai sosai sannan suka wuce gidan deeni"

Gidane nagani nafada daddy ya mallakawa deeni tare da mota me zafi, har cikin falon suka shiga har sun nufi cikin dakin deeni ya tuna da karatun malam acikin zuciyan shi yace bazan shiga dawani har cikin dakin mamata ba"

Waigawa yayi ya kalli caka yace faisal zauna anan ina zuwa"

Bakin gado ya samu Nafisa yafe da gyalenta me tsananin shiki, hannu yasa ya yaye gyalen, cikin sauri ta sukuyar da kanta kasa, yana daga tsaye yasa hannu ya dago habarta suna hada ido ta maza ta rufe ido"


Murmushi yayi kadan sannan ya ninke gyalen ya aje agefe sannan yace kisa hijjabi ki sameni falo akwai abokina dazaku gaisa"

Kamar yadda yace haka tayi bayan sungaisa ta koma daki"

Aranan deeni be runtsaba adaren ya dama furanshi kuma yashanye ta tas"

Nafisa ta jigata sosai tayi kuka tayi magiya dan haka dasafe idonta yayi jawur bata san haka haka aure yake ba da bazata taba yadda ba"

Shima deeni tausayinta ya kamashi tsam yasata akirjinshi dare da lalabo duk Wata kallama ta lallashi yana gaya mata"

Ahankali yafarajin sonta na shigarshi, farin cikin yaji ya kamashi sosai tare da godewa Allah daya amsa addu'anshi daman ya shanye furan ne ayau Dan ya yakice burbushin son ma'u azuciyan shi"

Haka suka kwashe tsayon sati uku suna cin soyayyar su, zuwa wannan lokacin sun saki jiki da juna kuma ahankali suna kara shakuwa"

Zuwan su gidan momy 3 amman da daddare suke zuwa itama momy ta fara sakkowa domin ayanxun duk lokacin dazakaga deeni cikin farar jallabiya yake tare da carbi ahannun shi"

Har kasa yake tsugunawa ya gaisheta betaba yadda su hada ido, Nafisa ko cikin manyan hijabai take"


Tayi wani irin kiba naban mamaki"


****


Jamal ko jinyan ma'u yake, tare da kokarin cire mata kowanne irin tunani sosai takejin dadin zama da jamal, dan yi yake tamkar ya maidata ciki"

Dakanshi yake girka mata abincin da zataci, baya barinta tayi ko cangal, anacikin haka ne ya koma aiki dan haka dole yasa ya nemo me aiki"

Bayan sati 2 ma'u tana kwace afalo cikin duguwar riga, sosai cikinta ya turo kaikace cakin wata 7 ne, kyau cikin ya mata tare da Kara fari da sheki"

Daya daga cikin. yaran Jamal taga ya shigo da wusu manyan ledoji guda biyu, cikin sauri ta miki tare da mamakin meyakawo Jamal da rana"

Muryan yaya usman taji yana sallama tare da anty fa'iza"

Batasan sanda ta mike taje gaban fa'iza tana fara'a ba, amsan yariyar tayi sannan ta jawo hannun fa'iza suka zauna yaya usman ta fara gaidawa amman ke madagas yaki amsawa, ganin haka jikinta yayi sanyi gaisawa suka da anty Sannan sukaciga da hira sama sama"

Hannun anty fa'iza ma'u ta dada dagowa tare da fadin zo muje daki"

Bazataba, usman ya fada fukan shi cike da haushinta, cigaba yayi da cewa mara kunya kawai ke me miji ko ?

Kara sukuyar da kanta tayi tare da matso hawaye"

Basu dadde da zama ba taji tsayowar motar jamal tasan gayamai akayi yayi baki"

Yana shigowa ma'u ya fara kallo sannan ya koma gurin da usman ke zaune karasawa Jamal yayi tare da fadin babban yaya daman nasan kaikadai ne matsala ta tunda ka bincikoni akurgumin daji babu a inda bazaka binciko ni ba"

Wani irin kallo usman yamai sannan hace....



Yazun saboda Allah abinda kayi kan kyauta kenan?, kabar momy cikin tashin hankali"

Katseshi yayi tare da fadin haba usman ko kaine bazaka zauna ba hukuncin daddy yayi tsauri da yawa gaskiya inason matata yaya za'ayi ba acemin wani nasaketa "

Juyawa Jamal yayi yaga idon ma'u alamar tai kuka, cikin sauri ya tashi tsam, ya nufi gurinta, ganin tahowanshi yasata mikewa ciki sauri dan tasan riketa zaiyi gaban yaya"

Bayanta yabi tare da fadin.....

tsaya mana, ina daki ta shige Jamal nabin bayanta hannu sa yasa ya tarota sannan yasata ajikin shi tare da fadin usman ne ya bata miki raiko?

Guntun hawaye ta share sannan tace yaya yaushe zamu koma gida?, kaga yaya usman na fushi dani nagaida shi yaki amsawa, ina tsoron kar ace abba ma yayi fushi dani"

A'a Husna Abba bazaiyi fushi dake ba, ni mijin ki ne kuma sun san muna tare, dole ce tasa nai haka bayin kaina bane, dan haka ki daina damun kanki da tunani banza, nasan halin usman ciki dabai, zuwa dare zan kira miki abba Ku gaisa, wata kila hankalin ki zaifi kwanciya"

Sakin ranta tayi kadan, nan Jamal ya barota ya dawo falo yana zama anty fa'iza ta miki dakin ta shiga sosai ma'u taji dadi, nan hira ta barke tsakanin su, lbr yadda abba ya shiga damuwa da daddy ya gaya mushi Jamal yabar gida tabata

Cikin ido ma'u ta kalleta tace kila shima yanzun haushina yakeji?

Bawani haushi, ko jiya da mukaje ya fada mishi ya samu inda kuke cewa yayi agaida ku, kuma usman ya roki Jamal idan cikin ki ya tsufa ya dawo dake gida"

Ajiyan zuciya tayi sannan sukahau hira"

Jamal ma da usman hira sukayi sosai acikin hiran ne usman ya isar da sakon abba"

Difff Jamal yayi xuwa can yace kasan abin da yasa na kasa dawowa wlh banson ganin deeni kullum tsanarshi kaaruwa take axuciyata"

Ai kaji irin ta mutumin da yayi auren shi ina ruwanka dashi, kaifah daman kacika kishin jaraba, shiyanxun ma bata Asma'u yake ba bakaga gadda. Nafisa tai kyauba naji kanmar ma ance ciki gareta, shikanshi deeni idan ba Sanin shi sosai kayiba baka iya shaida shi"

Ker Jamal ya yadda idan cikinta ya tsufa zasu taho, anayin la'asar suka kamo hanya"

Jamal yaciga ba da lallashin ma'u harta saki ranta so daya ya taba kira mata Abba, bayan sungama waya ya kira mata momy, tundaga ranan ya kashe waryarsa"

Bayan 4

Cikin ma'u ya tsufa tafiya daker tashi daker, idan ka ganta saika tausaya mata"

Kuma lokacin ne hankalinta ya tashi sosai, cikin dare bata iya bacci tashi take ta tasa jamal agaba da kuka"

Cikin tsananin damuwa yake tashi ya zauna, tare da fadi husna kiyi hakuri mana kidaina dagawa kanki hankali"

Nina gaji yaya, ciki kusan shekara daya ajikina ni gaskiya daga wannan bazan kara ba"

Kauda fuska Jamal yayi yai dariya sannan ya juyo ya kalleta tare da fadin gobe zamu wuce gida, dan naga nema kike hawan jini ya kamaki, haba ace mutum be gajiya da kuka"

Murna ce ta kama ma'u sauka tayi wai xata hada kaya, jamal ne yahanata shida kanshi ya hada musu kaya"

Dasafe ya kira no Momy, tana dauka tace Jamal wai yaushe raini ya shiga tsakanin mu haka?, bazaka dawo da yar mutane ta haihu agida ba?, cikin watan haihuwanta fa take"

Cikin mamaki Jamal yace momy waya gaya miki?

Uwarka ce, akace maka bansani bane?, ai ina lissafi, ko ta haihu ne ma?

Sosa keya yayi tare da fadin a'a munan isowa yau"

Yauwa Jamal Allah ya maku albarka dan Allah kutaho da wuri"

Toh momy amman kafin mu tahu inason zan shiga kasuwa"

Me zaka saya indai kayan haihuwa ne nariga dana hada komai"







Heart Beat
*Mmn Yazeed*πŸ’—πŸ’πŸ’πŸ’—
​*BUGUN ZUCIYA*​
( ​Heartbeat​)

πŸ’“πŸ’πŸ’—
πŸ’—

πŸ’“πŸ’πŸ’—
​By​
πŸ’—
​​*Fadeela Lamido*




*@AM££NCI WRITER'S ASSOCIATION🀝*
​


*Sadaukarwa ga duk me karata BUGUN ZUCIYA, nagode da irin soyayyar da kuka nuna min tare da wannan lbr BUGUN HEAT, Allah yabar kyaunaπŸ’‹*



*Sakon gaisuwa da fatan alheri ga marubutan mu, wad'an da suka karamin karfin guiwa wajen rubuta wannan lbr, bani da bakin mgn, hakika kun nunamin kyauna, sai dai nace Allah yabar xumunciπŸ™πŸ»*



1⃣0⃣5⃣





βœ‹πŸ»βœ‹πŸ»βœπŸ» Karfe 3:15pm suka shiga gidan momy murna momy take sosai tana rike da hannun ma'u tare da tsareta da ido, nandan lbrin dawowan su ya zaga ko ina, tsilum saika Nafisa aguje ta shigo da cikinta daya fara tasowa manne ajikinta"

Jikin ma'u taso fadawa, momy ta tareta tare da fadin nafisa lfyr ki lau kuwa? Kewai bakijin nauyin jikin ki ?

Komawa tayi kusa da ma'u ta xauna, sannan ta shiga gaida Jamal wani irin amsawa ya mata batare daya kalleta ba,

'Daga ma'u nafisa tayi sannan ta suka nufi daki, kallon nafisa ma'u take tana mamaki wai yanzun cikin deeni ne jikin nafisa?, Ikon Allah kenan"

Hira suka barke dashi daga falo su momy sunajin dariyar su"

Sai dare deeni yazo daukan nafisa be shigo ba, waya ya mata tafito sutafi sannan tace yana gaida momy"

Daddare momy so tayi ma'u ta kwana gurinta amman taga Jamal sai zarya yake yafita yadawo dan haka tace tashi su tafi"

Dukda kwaciya kawai zasuyi tare yafison haka akan ace sunyi nesa da juna,

Washegari da safe sukaje gaida daddy abinda ya bawa Jamal mamaki daddy be nunafushi ba, sosai farin ciki ya bayyana afuskar shi, koda zasu tashi yaga ma'u na kici kicin tashi, cikin fada daddy yace haba Jamal taimaka mata mana, kunya ce ta kamashi daker ya iya mika hannu ya dagata Albarka daddy yaita samusu tare da addu'ar Allah ya sauketa lfy"

Adaren ranan ciwon nakuda ya tayarwa ma'u tunda momy taga inda take cije baki ta kira jamal, daki ta shiga ta dauko kayan haihuwa tace asibiti zamu"

Karfe 10:39pm ma'u ta haifo zarkada zarkadan 'ya'yanta guda biyu dukkan su maza ne masu kama da Jamal"

Bakaramin maki Jamal yayi ba, tunda suke zuwa asbiti babu wadda yataba cewa yan biyune acikin husnan shi"

Momy ko farin ciki ya hata mgn, adaren suka dawo gida domin ma'u lafiya lau take"

Tun asuba momy ta fara gayawa yan uwa da abokan arziki dan haka tunda safe gidan ya fara cika da baki"

Nafisa ma murna ba'a magana tare da deeni sukazo fuskanshi dauke da murmushi nafisace ta kwaso yaran ta mika mishi kallon yaran yayi gwanin ban sha'awa nan danan idonshi yacika da kwallah yasa hannu ya share tare da fadin nafisa yaran nan sun

Please Login or Register in order to submit comment