Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuce, dan ta fahimci faruk akwai abin da ya shirya .

tashiga ummi tace maganar abinci ne, shinkafa muka da fa, wata kila shi baya so, me aza,a dafa mashi.
humaira tace ummi zai ci shinka far ai kome su momy suka dafa shi yake ci.
tace kina nufi abincin gidan kuke ci baki mai girki.
Sai alokacin humaira ta tuno kuskurenta, tace ai baita cewa namai girki ba.
Lallai nagano irin zaman da kikeyi , tarbiyan da aka baki kenan, haka kikaga inawa baban ki, to bari baban ki yadawo zan fada mai halin da ake ciki.
humaira idon ta ya cika da hawaye tace ummi karki fada mai na Bari.

taje ta dauko abincin ta ajiye agefen shi tabude ta zuba mai, faruk ya kalla fuskar Humaira ya tabbatar fada aka mata, bayan yagama cin abinci ,ummi ta dawo ta zauna , tace ashe humaira bata maka girki, su kuma su hajiya aisha suka sa mata ido.

faruk ya sosa keya yace ummi ai yar lelan momy ce, ita ke shagwa bata.
tace lallai kuwa zama ki bari ne bari baban ki ya dawo.
faruk yace ummi inason na koma yau ne kuma gashi baba baya man.
to ka bari sai gobe mana saika wuce, yaka mata ku gaisa da shi, kuma sai anyi mangariba zai dawo , ai yan zon yamma tayi 5:48 in katafi dare zai maka a hanya.

Itako hajiya rabi tunda suka shiga bara yin su basu fito ba, bakin ciki ke cin su da dana sani, inama ta bari zainab ta aure faruk.

hakalin su be kara tashi ba saida su kaga ana shigo da tsarabar humaira, atanfufine masu kyau da turaruka masu tsada


sai bayan sallah mangari ba alhaji ya dawo tundaga waje lbr ya zo mai cewa humaira tazo, dan haka yaji dadi azuciyar shi yasan yanzun hakilin mahaifiyar ta zai kwanta.

humaira najin ance alhaji ya dawo ta mike da sauri zata fita , ummi ta dakatar da ita tana fadin karki kuskura ki fita.
bayan alhaji ya shigo yaji dadin ganin faruk sun gaisa cikin farin ciki, ya tam baye shi muta ne gida , faruk ya tabbatar mai suna lfy.

alhaji yakalli humaira yace humaira angirma tayi dariya ta dukar da kai tace bayan kun manta dani.
alhaji yace aini na hana kowa yazo gara abarki ki natso.
Ummi dake gefe tace kuma sai gashi bata natsun ba, tunda a inda nalura humaira bata kula da mijinta kwata kwata, dai dai da ruwa dungura masa take.
alhaji yaji mamaki yace humaira haka kika koma kuma, kai kuma kasa mata ido kana kallon ta, baza ka bata kashi ba.

faruk ya dukar da kai yace ai su momy basa bari, shi yasa take yi.
alhji mikewa yayi cikin bacin rai, yace ina zuwa , zaki gane kuranki.



_*💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞*_


_*84 to 86*_

_*FADEELA LAMIDO*_
_*MMN YAZEED........✍*_


Humaira kuka ta fara dan ta tabbatar dukan ta zaiyi ,dan abba baya wasa, ummi dan Allah kibashi hakuri wlh na daina, bazan kuma ba.
faruk ko atunanin sa alhj firgita humaira zai yi, dan shi aganin shi humaira ta wuce duka, koma ko za abige ta, ai baza a bigeta da ciki ba, dan haka da yaga humaira ta firgita yaji dadi zociyar shi.


sai ganin alhj su kayi ya fito da wata sharbebeyar durina sai huce yake ya nufi humaira gadan gadan , ya zuba mata ta sake kara.

faruk ya zaro ido ya mike da sauri, humaira ma mikewa tayi da gudu tayi bayan faruk ta cukuikuye shi tanà kuka alhj be barta ba biyota yayi ya kuma daga bulalar zai gara mata, faruk yace baba dan Allah kiyi hakuri ka bar ta , ko sauraran shi beyi ba ya zuba mata ganin da faruk yayi da gaske alhj keyi.yasa shi rudewa , juyawa yayi ,yama humaira runfa, yana fade baba bafa ita kadai bace.

alhj bebar dukan humaira ba sai da yaga ba ita yake samu ba, faruk kawai yake samu sannan ya bari.

humaira sai kuka take yi dan ma Allah ya tai make ta befi bulala biyu bane yasame ta, amman sauran duk ajikin faruk ya sauka.

bayan faruk ya sake humaira taje gaban alhj ta tsuna tana rokon gafara, sài da yayi mata nasiha me ratsa jiki sannan yace taje taba mijinta hakuri.

zuwa tayi gaban faruk ta tsuguna duk da cewa shima akasa yake, tace yaya kayi hakuri na daina bazan kuma ba.


har ga Allah humaira tabawa faruk tausayi besan haka baban humaira yake da zafi ba da be fada ba.

dan haka yace ba komi humaira ya wuce.

mikewa tayi ta shiga dakin ummi, dama ummi tuni ta bar wajen, tabar faruk da alhj suna hira.
koda humaira da shiga dakin babu abinda ummi take mata bada nasiha, kuma tabas nasihar ta shegeta dan jikinta yayi sanyi sosai.

faruk ne ya kalli agogon hannun sa karfe goma saura dan haka yace baba bari na tafi naga dare yayi.

alhj yace kana tunanin ina garin nan zakaje wanne waje ka kwana.

faruk yace ba haka bane baba , akwai wani abokina da zanje wajensa da safe saina tafi.
alhj yace sam bazai yiyu ba, ba in da zaka.

daga murya yayi ya kira auwal yayan humaira, bayan auwal ya shigo alhj yace kaishi dakinka.

auwal yakai faruk dakin sa yadan zauna suka dan taba hira duk da cewa auwal karami ne, befi shekara biyu ba tsakanin sa da humaira dan ko aminu ya girmi auwal nesa, amman haka be hana faruk yayi hira dashi ba.

zawa wani lokaci auwal ya mike yayi wa faruk sallama ya fita.

humaira tayi shirin kwanciya ummi tace ta tafi gurin faruk, badan ranta yasoba tafita .

tana shiga ta same shi ya fara barci mutsin ta ya sashi ya tahi, zama tayi agefe batace masa komi ba.

gani yayi humaira bata da niyar tashi dan haka yace humaira tashi kije ki kwanta.

ummi ce tace nazo nan na kwana.
faruk yace humaira bazan iya ba ki koma dakin ummi ki kwata, yaya za ayi na kwana dake daki daya agidan nan, ban so ma nakwana ba wlh dan baba yaki yarda ne.

humaira tace yaya gaskiya bazan koma ba, innakoma ummi fada zata min.

to muje na raka ki, da sauri humaira ta mike dan dama baso take ba.

suna shiga bakin kofar yace mata saida safe, ta bude dakin ta shiga, yana jiwo fadan da ummi kewa humaira , au dawowa kika yi.
tace shine yace nadawo.
faruk dake bakin kofar yace ummi ni nace ta kwanta anan, ummi ta girgiza kai .

bayan faruk ya wuce ummi tace Allah ya baki miji me natsuwa ga kunya amman ke baki sani ba, idai bak gyare halinki ba sai asamo mashi wata, kinga lokacin saiki zama yar kallo.

humaira jitayi haushi ya kamata dan ta tatsana taji ance faruk zai kara aure duk da dai ba wani son shi take ba.

washe gari faruk da wuri ya gama shirya wa, yana kokari fitowa sai ga humaira da kayan kari niki niki.

yace nifa bazan tsaya cin abinciba tafiya Zanyi.
saboda me tace da shi, yau fa baranar aiki bace balle kace zaka aiki

eh amman inason nakoma gida da wuri.
to ai in baka ci abincin ba ummi bazata ji dadi ba.
faruk yace hakane kuma, zubamin to.
waina ce lafiyayya da kunun tsamiya, ta tura mai gaban shi, yaja ya fara ci, tas ya cinye shi sannan yace humaira idan akwai karamin ,gaskiya ummi ta iya girki.

humaira dake kokari juye wa faruk ragowar wainan tace to malam ba ummi bace tayi nice niyi.

faruk dake kokari kai waina baki yace kai humaira anya kuwa, ban son karya fah.

tace to katam baye ummi kaji.

saida fatuk yaci ya koshi sannan ya musu sallama ya fito humaira na biye dashi har gun mutar sa

ya bude ya shiga yace to natafi sai na zo kenan .

eh tace tana yake hakora, faruk yace kinata murna makiyin ki zai tafi.

tace yaya wlh ba haka bane.
tsayawa yayi ya kare mata kallo ya hada rai yace koma ciki nina tafi


faruk haka yakoma gida jikin shi babu kwari shifa ko humaira bazata mai wani abuba yana son yaganta kusa da shi.

su momy na zaune sukaga yashigo wani iri.
momy tace lfy kuwa ko wane abu ya sami humair ne?

yace lfy lau momy kaina ke ciwo.
tace Allah ya kawo sauki, ya ka baro su?
yace lfy lau.

mikewa yayi ya shige daki, cikin dare kasa bacci yayi sai juyi yake akan gado, dan haka washi gari yana mikewa yadau waya ya kira number humaira , harta katse ba adaga ba, faruk ya kara kulewa.

itako humaira lokacin da faruk ya kirata, bata daki sai da ta shigo taga kiran dan haka takira shi , har so shida amman be dauka ba.

dan haka humara tayi tunanin ko yayi fushi ne, nan tafara neman number momy dan ta gaya mata, momy tace a,a kila dai baya kisa da wayar ne

bayan momy ta kashe wayar saita kirashi bugu daya ya dauka, tace mai inka tashi kazo, lokacin 8:35 na safe.

yana shigowa momy tace me yasa humaira takira baka amsa ba.
momy kiran ta nayi taki dauka, kuma ni gaskiya bazan iya barin ta tayi kwana biyar ba nan gaba, gobe zanje na dauko ta.


07014197556✍



***RABUWAR BAZATA***
(10)

ASALIN LABARIN

Cikin kankanin lokaco Iman ta fita hayyacinta, domin wani irin zazzafan zazzabi ne ya rufeta.
Abin da ya kara dagawa su Mina hankali shine, duk abinda taci ko tasha sai ya dawo, ga wani matsanai cin ciwon kai da jiri da yake damunta, wanda ko iya mikewa tsaye bata iya yi sai dai a riketa.
** ** **
Muhib ya kasa zaune ya kasa tsaye, labarin da yaji su Mahmud na bayarwa dazu ya tsaya masa a rai mutuka, dan wani irin tsorone da fargaba suke shigar shi, domin yasan duk abun da ya sameta shine sila.
Tausayin yarinyar da dana sani yake yi, domin shima tun daga ranar da abun ya faru yake cikin tashin hankali mara misaltuwa, saboda rashin dacewar abin da yayi, musanman ma ta fusakar addini, yasan ya sabawa Allah mutuka.
A kullum istigifari yake yi amma sai ya rinka jin laifin shi kamar dada karuwa yake. Yana ganin ya dauki fansar abinda tayi masa.
Sai kuma washe gari ya tashi da matsanaicin damuwa da bacin rai, saboda wannan shine laifi na farko da yataba aikatawa makamancin wannan a rayuwarshi.
Yana cikin wannan tuna nine su Munnir suka zungure shi.
''Lafiya over tun dazu muna ta magana baka jimu ba?''
Ya dan waske yace ''Sorry, ban ji bane shiyasa''.
Mahmud yace ''tuna nin mi kake hakane?''
Ya dan sosa keya yace, ''i am just thinking about some thing (kawai ina tuna nin wani abune)''
Muzaffar ya kalle shi yace, ''Nifa na fahimci wani abu''
Muhib ya ce '' me kake nufi kenan?''
Ya karasa saman sit din da suke ya zauna yace, ''Ina nufin tun da abun nan ya faru a social night kake cikin wani hali, kana dai boye mana kawai bayan kuma ka san bama haka a tsakanin mu, saboda duk damuwar dayan mu taruwa muke muyi maganinta gaba dayanmu''.
Munnir ya amshe da cewa, ''Ni ban ma ga abun damuea ba, tunda ka samu ka dauki fansar abinda tayi maka''.
Mahmud ya ce, ''Yanzu dai duk ba wannan ba, kayi mana bayanin abinda ke damun ka''.
Muhib yayi ajiyar zucia ya nisa yace, ''Na san za ku yi mamakin abinda zan fada, to amma har ga Allah ni iya gaskiyata kenan, domin abinda nayiwa yarinyar nan na mutukar damuna, musanmanma rashin lafiyar da takeyi a yanzu''.
Munnir ya ce, ''To ina ruwan mu, ba ita ta jawa kanta ba, kuma ma in ban da gulma mene ne abun rashin lafiya''.
Muzaffar yayi saurin dakatar dashi ya ce, ''Ba wannan maganar ya kamata mutsaya mu tattauna hanyar da zamu taimakawa Muhib kawai''.
Mahmud yace ''gaskiya ne, to yanzu mai yadace muyi?''
Munir ya ce, dazu a daining hall na ji wasu 'yan class dinsu na cewa, wai gida za a kai ta saboda magungunan da take bukata sunfi karfin hukumar makaranta''
Mahmud ya ce ''Ya ya za mu taimaka mata da magani, ai ina ganin sai dai mu nemi wata hanyar''.
Muzaffar yayi ajiyar zucia ya ce, ''Ni ina ganin bamu da wata hanya bayan wannan, ko ba haka bane Muhib? Anata magana kayi shuru.
Yadan sauke wata kasalalliyar ajiyar zucia ya ce ''To ni me kuke so in ce?''
Mahmud ya ce ''Kaima sa baki zakayi ayi shawarar da kai''.
Muhib ya nisa ya ce, ''Eh to , ni ina ganin shawarar da munir ya bada ta yi a matakin farko''.
''kana nufin bayan wannan taimakon nan gaba sai mun kara wani?'' in ji Muzaffar.
Muhib yayi wani dan murmushi mai ciwo yace ''idan ma ita ba zaku kara taimaka mata ba, ni kam ina da yakinin ni sai kun kara taimaka min a kanta''.

Via
¤Sman U.K




_*💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞*_


*87 to 89*

_*FADEELA LAMIDO*_
_*MMN YAZEED........✍*_



momy tace to madallah Allah ya tai maka, kana da wuyan sha ani babu uzuri kenan, dan ka kira ta bata amsa ba, bakasan meye dalili ba, amman kace zakaje ka dauko ta, to ba dai haka babba ya keyi ba, suna cikin haka yar momy ta sake yin kara, miko mai wayar tayi, ya karba dan ba yadda zaiyi da momy.

mikewa yayi ya fita yana kokari wayar kunnen sa, muryar humaira yaji tana fadin yaya ina kwana, murya kasa kasa ya amsa .

ta sake cewa kayi hakuri bana kusa da wayar ne shi yasa.
cikin fada yace ai dama bazaki zauna kusa da waya ba, tunda ba damuwa kikayi dani ba.

humaira ta marai raice tace haba yaya me yasa kake cewa haka.

saboda na tabbatar jiya kinyi bacci amman ni kasa bacci nayi , humaira sai juyi nakeyi akan gado, humaira nafison na ganki agida ko zakiyi min komi ba, humaira wai me yasa baki sona ne?

humaira hankalin ta tashi yayi jin yadda faruk ke magana kamar zaiyi kuka, tace yaya nifa ba na kinka kuma nima jiya ai banyi baccin ba.
faruk da sauri yace kina nufin kice kema kinyi kewa ta?
kasa tayi da murya sannan tace eh mana.
faruk murmu shi yasaki yace humaira zan tambaye ki dan Allah ki gaya min gaskiya tsakanin ki da Allah.

tace to ina jinka.
yace humaira da gaske kina sona?
tace yaya ai kai ma baka taba cewa kana sona ba .
to indai wannan ne abune me wahali awajena ba, humaira ina mutuwar son ki, sai yanzun nake gane su abba ba karamin gata suka yi minba
humaira kece irin matar da na dade ina mafarki samu, sai dai naga kamar bana gabanki.

humaira tace yaya ba haka bane kariga ka nunawa kowa baka sona sabo da a auren so kayi ba, sai yanzun kuma kadawo kace kana sona, bayan kowa yasan ba sona kakeyi back.
karki la akari da haka humaira Allah yana iya juya al a mura, ba abun mamaki bane, dan Allah ki watsar da duk wani tunani dake zuciyar , murun gumi juna.

haba yaya bayan kowa agidan yasan ba sona kake ba, har ana min guri , wai baka sona nikuma na manne maka.

ki daina saura ran irin wa dannan magan ganu wannan zancen mata ne , amman su momy ai sunsan ina sonki.
ba wani nan, ni dai idai kana son nasake jiki na sai ka nuna wa kowa kana sona.
humaira kina son rashin kunya ta tai yawa ne, baki ganin yanzon ma su momy cewa suke yi bani da kunya, akwai wata ma a office din mu sabo da lbrn ki da nake basu harta fara cewa bani dan kunya.
Cikin bacin rai humaira tace wacece ita, kuma ya sunan ta
faruk yayi murmu shi yace sunan ta indeeeyanah.
humaira tace wlh da zan ganta sai ta gane kuran ta.😜

basu suka bar hira ba saida kudin wayar ya kare.

humaira kullum da ta idar da sallah subahi zata kira faruk su sha hira wannan hira da suke yi ta kawo sha kuwa agurin faruk da humaira , yadda in ba sunyi wayar ba basa jin dadi, dukkan su biyun.


da haka kwana kin humaira suka cika faruk Allah Allah yake gari ya waye yaje ya dauko matar shi.

washe gari faruk da ker ya bari tara tayi , ya fito cikin shirin shi na tafiya.

yana shiga dakin momy yaji momy nawa meena fada.

faruk yace me tayi momy ?

momy tace wai kamar meena ce take hira da samari, ba damar na aiketa sai ta dade in nayi magana tace wane ne ya tsayar da ita.


faruk ya daure fuska ya rufe meena da fada sai kuka takeyi, daga karshe yace ta tashi ta fita.

bayan ta fita faruk yace momy to amata aure mana.

tace wannan yar kankanuwar za,ama aure.

yace momy bata yi kankata ba, in tayi aure sai ta karasa karatun , kamar yadda humaira keyi.

tace ina sam ai bata ma da samari yanzun ne naga tana neman tasa wasa.

faruk shiru yayi ya dukar dakai, sai can yace momy meena fa zata girmi humaira dan Allah amata aure.

cikin fada tace wai kai meya dame kane da ita , da kake rokon amata aure.

faruk yayi murmushi yace yace momy amini na ke so.
cikin faduwan gaba momy tace wa kenan?

faruk yace nura.

momy tace nura, nura kuma to dan Allah karka kuma tada maganar nan, ban san alhj yaji dan yanajin lbrn nan to ta zauna kenan, kace ma nura nace yayi hakuri, ya bar maganar , yana zaune lfy da matar shi, me zai jamasa aure yanzun.

faruk yace momy nura fa da gaske yake yi , da zai bar maganan nan da tuni ya bari, ba ida banyi da shi ba amman ya dage.

tace kace mishi nace yayi hakuri ya bar maganar.

faruk yace to , dan sauri yake yaje ya dauko Humaira, amman shi dai yanzun yana son abawa nura meena.

faruk yayi sallama da su momy ya kama hanya zuciyar shi ciki da farin ciki.

aguje yake tafiya dan haka nan da nan ya isa , yana faka motar sa saiga auwal ya taho da sauri yana cewa sannu da zuwa yaya.

yace yauwa sanu auwal tare da shi suka shiga ciki , ya zauna a falo, auwal yace bari na fada musu ka iso.

humaira ce tafito da sauri, faruk naganin humaira ya mike ,ya bude hannu wanshi, dan haka humaira ta rufe idon ta tafada kirjishi, da sauri ya maida hannuwan shi ya matsata ajikin shi, yafara kai mata simba ta ko Ina, ummi ce ta sawo Kai da sauri ta juya.

ummi bata Kara marmarin fitowa ba sai da humaira ta shigo tace ummi naga biki fito bane.

tace ganinan fatowa kin dai gama hada kayan ki ko?

tace nagama sai dai anty hasana tace na aiko akarban min sako.

to ai kowa sai dai ki hakura da sakon , tunda ya riga yazo, ummi mikewa tayi ta fito falo .

lokacin da ummi ta fito auwal ne zaune shida faruk suna hira , faruk ya sauka da sauri ya zauna akasa yana gaida ummi.

humaira ta fito taje gaban auwal tace yaya auwal dan allah kaji gidan anty ka amso min sako.

auwal kallon humaira yayi yace dan ubaki ni sa,anki ne.
faruk yace kai Humaira kuma kake zagi
yace yaya baka jine wai ni zata aiika
faruk yace to meye dan ta aike ka ai yanzo ta girme ka ta shi ka tafi.

bayan auwal ya karbo sakon ya dawo sukayi sallama suka kama hanya , humaira sai kuka take a motar, faruk yayi rarrashi har ya gaji.

har suka isa gida humaira na kuka idonta duk sun kun bura.

faruk ya bude mata murfen mutar yace ta fito.

cikin kuka tace ni bazan iya tafiya ba.
saboda me?
wani abune aciki na yake min sukur sukar da karfi a ciki na.

da sauri ya sun gumi humaira da gudu yayi cikin gida ita.

07014197556✍



_*💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞*_

*90 to 92*


_*FADEELA LAMIDO*_
_*MMN YAZEED..........✍*_


Sukowa su momy suna zaune a falo duk yan gidan suna zaune a falo , har aminu da matar sa samira.

sai ganin faruk su kayi ya shi go dauke da humaira.
suka fara fadi oyoyo humaira.
Itako

Please Login or Register in order to submit comment