Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

inaganin gaskiyar momy ce da tace baka da lfy, ga dukkan alama baka da sha,awa.
wlh inada ita nina ma fika lfy kawai dai ina danne wane.
a,a ni baka fini ba wlh da kafini da baka kawo yanzun baka da mata ba.
mubar wannan maganar yanzon kaje kaba momy hakuri, bana son ganinta ahaka. nura yamike yace amman gaskiya kana sani a uku.
nura ne yayi sallama dakin momy ya shiga. nura dama kana nan ai nadauka katafi. a,a bantafi ba inagun faruk, momy ya gayamin abida ya faro kuma ya amsa laifinsa dan Allah ki yafe masa.
nura kenan , kadai amsa masa laifin.
a,a momy shi da kansa yace inzo na baki hakuri.
to shike nan ya wuce amman da na dauka dambe zaiyi dani. a haba dai wane shi aibe isaba yayi kadan.
ya sake cewa ina humaira. momy da kanta ta daga murya takira humaira.
yaya nura dama baka tafi ba. eh ai ina dakinki inata jira kikawo mana abici naji shiru. caf na shigo ya bigeni.
saikace wani mahauka ci bazai bige ki ba, magana tariga ta woce karki kara tada ta, kuma ko wani abo ya faru atsakanin Ku karki kara cemai Allah ya isa. to shima kace mishi ya daina shiga harka ta. bazai daina shiga harkan taki ba, dama haka kike yanzu ne ma zai shiga harkar ki, daga yau karki kara zuwa ko ina , saikin tambaye shi. ta kwashe da dariya, au dariya na baki wlh ba wasa nake ba, momy kizama sheda wlh faruk be yadda ta fita bada izzinin shi ba. momy tace ku kuka sani niba ruwa na. bayan nura ya koma dakin faruk ya kara bashi sha warwari sannan ya nuna mashi mahim mancin kula da matar sa in kana mata haka nan gaba zaka iya kamuwa da sonta ita kuma ta bijire maka. nine zan kamo da sonta Allah ya kiyaye wlh. to shikenan tunda baka sonta, dama abinda yasa nace ka kula da ita wani abokina ya ganta jiya ya nuna yana sonta shiyasa nace.
kabari fa bana son irin wannan wasan ya fada a fusace. wlh faruk ba wasa na keyi ba inzaka kula da ita ka kula ni babu ruwana inhar baka bariba nan gaba karka kirani. bar wanan maganar wani dan iskan ne yace yana sonta, idon nan jawur
[6:34PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURENKI💞💞

24 to 27

✍MMN YAZEED

nura ya kwashe da dariya, kace baka sonta kuma gashi naga duk ka wani rude. ba rudewa nayiba amma yaya za ayi yaga martar aure yace yana so .
to ai baka kula da ita ba in bakason ace anason ta to ka kula da ita, kana son yarinya kana wani basarwa. wai wa yace maka sonta nake. nura yayi murmushi ga kishin ta nan a idon ka. niba sonta nake ba, amma ai akwai aure na akanta . zama ka kadawo hanya ne, ni zanta tafi.
da daddare humaira tashigo dakin tana zunbura baki ta wuce faruk yana kwance rike da kai dan har yanzun kanshi bai daina ciwo ba , ta shige dakinta ,faruk nason ya shiga daki shi ya kwanta kuma yana tsoron karya shiga itakuma ta fita, tajamai wata maganar dan haka yatashi ya shiga ciki
washegari da wuri ta fara shirin makaranta , tana dakinta ta na kokarin sa rigar makaranta, taji anturo kofar ,ta sake kara da karfi. juyawa yayi yana fadin meye haka. to ya zaka shigo ma mutun daki ba sallama. yayi tsaki ya fara tafiya in kun gama shiryawa kimin magana na sauke ku, bejira yaji me zata ceba ya wuce itako humaira cewa take azuciyar ta wannan yana so yafara takura mana.bayan tagama shiryawa ta fito tasame shi zaune a falow ya juwo ya kalleta ya dauke kai, yasake juwowa ya kalle ta sosai, dama ahaka kike zuwa makarantar. eh
dawan nan dan siket din, karya kikeyi.tace nizan wuce zamu makara. kije ki canza ki sako wando kisame adakin momy. toni wani wando zansa haka fa kayan yake. to wlh saidai in bazaki makaratar ba yajuwa ya fita. bin ubayan shi tayi tana zunbura baki, momy ce tagan su sun shigo kowa rai abace meena ya hango itama da irin shigar humaira. ke kmeena kayan makarantar ku ba riga da wando bane.tace ancanza ne fa yaya. ya tsaya yayi shiru momy dai ido tabishi da shi can ya dago yace ke meena taso muje na sauke ki. momy tace humaira fa. ita zauna zan canza mata. me zaka canza mata, kana nufin zakiyi mata wasa da karatu , tana gaban iyayeta tayin karatun ta aka katseta kuma yanzun ta fara asake katseta wlh baka isaba. momy aiba lokaci zan jaba. kaidai wlh fitinanne ne bakaso kaga anzauna lfy, ni idai ba barin gidan kayi ba hankalina bazai kwanta ba. faruk rai abace yace jeki dauko hijab ki daura akai. yaceni bani da hijab. ko kallota beyi ba ya juya ya fita. momy tace ke humaira jeki dauko hijab din kizo kutafi. momy wlh bazan saba haka kawai ba me sawa saini. kidaina sauri rantsuwa humaira mijinki ne yafi kowa karfi akanki tashi maza. ai bani da shi. momy tayi murmushi meena dauko mata hijab dinki. meena ta dauko ta mika mata, takarba ta bude ta fashe da kuka momy yayi nmin yawa fa. kash kema taurin kan zaki min meena tariga humaira futowa dan ita tsoro yaya faruk takeji baya ta shiga tazauna humaira ta fito gaban motar tashiga dan shi ta gani abude bata daina kuka ba har sukai nisa, yajowo ke karki damemu tai banza ta shi tacigaba da kukanta harsuka kawo bata daina kuka ba, kukan humaira yafara dagawa faruk hankali ji yake kamar ya rungume ta ya lallasheta, dan haka yace meena jeki abinki, da saurinta ta fita ta shige makaranta. ya juya ya kalli humaira yana son yakara taba hannuta amman yana gudun karta raina shi gaskiya inbai taba ba hakalin shi ba zai kwanta ba dan haka ya wayance ya mika hannun shi yarike mata hannu , yana dan matsawa. ta dago da kanta tana kicikicin kwacewa tana fadin ka sake ni niba yar iska bace.tsaki yayi ya kara matsa hannun .tasake kara akwai zafi fa . haka ya saketa bawai dan ya gaji da taba hannu ba.

faruk fa ya jawowa kanshi dan tunda ya taba hannun humai hakali shi yaki kwanciya da taimakon Allah ya isa office ko da yaje be iyayin komai sai tunani yake shidai yasan basanta yakeyi ba amman ayau yaji yana son yadan taba jikinta kuma baya son ta raina shi in ma ya daure yasan yariyar ba yadda zatayi ba dan haka yafara tunani yadda zaiyi yabar gidan da ita dan haka yana tashi office ya woce gidan alhj ahmad, nura ya fara kira yace mai zomuje karakani, ina zan raka ka? gurin baba nura bai kawo komai aran shiba dan haka ya bishi suka shiga bayan sun zauna alhj yace babana kwana biyu shiru
wlh baba abu buwa ne sukayi min yawa .
inna ma tace fushi kake da ita, rabon da ta ganka ta manta, ina sane da ita ai zanje ne baba. bayan sudayi hira faruk ya fara magana baba dama inason na tare a gida nane. to ka shirya tarewa kenan to amma maizai sa bazaka bari tagama karatun ta ba.
baba ai zatayi acan .
yace to kabari zaga baban naka tuda shi yake zaune da ku .nura ne ya sako baki baba karku yadda ya tafi da ita wlh be natsuba . alhj yayi dariya yace da gaske ne wai baka natsuba . yace karya yakeyi baba. yaushi zaka tafi? jibi yafada atakai ce. kaje zakira shi zamuyi magana.

washegari da safe yaji kiran alhj , saida gaban shi ya fadi yana me ardu,a azuciyar shi Allah yasa abba ya yarda bayan ya isa dakin abba yace naji ance wai zaka dauki matarka ka kai abuja to kama cire wannan tunanin azuciyar ka , inka manta ni ban mance ba yau kwana nawa da ka zaneta acikin gidan nan adakin mahaifiyar ka, shine dan bamu da hakali zamu baka ita katafi da ita wane waje inkana son ka tafi da ita ka gyara halinka. haka ya koma jiki ba kwari . lokacin da ya shi ya samo humaira ta waya , tanata murna tana fadin ai zanzo suna. tana kashewa tamike da gudo tayi dakin momy , bata dade ba ta dawo, yaya faruk momy na kiranka, bece komi ba, ya tashi ya tafi, yana shiga yace gani.
ni ba nemaka nakeba waye yace ina kiranka? humaira baitaba kiran sunan humaira ba sai yau. tace au ita da nace ta tambaye ka shine ta turo ka, wai matar yayansu ce ta hai hu takeson taje suna, Kuma kaga ya kamata taje tunda tazo bata taba zuwa gidan bab. momy dan Allah kidaina cewa ya katama ba ruwan ku karma kusa baki.
ai baza abaku shawara ba? bahaka bane yanzun in taji kina fadan haka saitaga kamar dole ne.
da daddare banya suyi shirin kwanciya tana gado shiya na kujera yace yaushe ne sunan matar yayan ki ? da sauri ta sauko tace yau ta haihu , yaya zanje ne . ke da kike min rashin kunya baki jin magana ta. wlh yaya na bari bazan kara ba. duk abinda nace kiyi zakiyi ?eh tace dashi da sauri batare da tayi tunanin komai ba. to dama yau agajiye na dawo zo ki dan min tausa
[6:35PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURENKI💞💞

28 to 31

MMN YAZEED


Mikewa tayi ta ja da baya , yaya dan Allah kiyi hakuri wlh ban iyaba, ta nufi kofa. ke ina zaki kuma ,zo kiji. ta kara matsawa, yaya wlh ban iya ba .
to naji baki iyaba zoki yi baccin ki. taki zuwa tamakale wa kofar, yata shi ya matsa kusa da ita , ba za kimin ba ko, ashe baki shirya zuwa gida ba. ni ashirye nake .to tunda bazaki yi min ba zoki kwata amma karki kara cewa zaki gida ,dan wlh bazaki ba . ni bazan kwata ba sai ka fita adakin . saina fita , saboda me zan fita? tsoron ka nakeji. wlh bazan fita ba ,bake kika sa akace dole sai na rinka kwanan ba, kuma yanzun dan munafurci zakice wai tsorona kikeji ,mezan miki , ko kina tunanin wani abu nake nema awajanki me kike da shi, yamike yafara takawo kusa da ita. tana ganin ya nufuta ta ruga da gudu tayi waje . dawowa yayi ya zauna yafara ganin laifin shi meyasa ma har ya mata magana, wannan yariyar da bata da sirri , yanzo ma kila harta gayawa momy.

momy na kwance taji anshigo aguje tana daga kai taga humaira na haki. ke lfy kuwa ? bakomi .
momy tamike tazo ta riketa ta , meya faru ? bakomi momy nazone na kwanta anan. a,a bazai yiwoba yazaki baro mijinki adaki kizonan ki kwata, ai ba haka akeyiba , yanzun kintaba ganin samira ta kwana adakin nan ? to momy zan koma amman kice ma yaya faruk ya koma dakin shi . momy tayi shiro can ta dago tace humaira kitashi kikoma dakin ki niba ni da damar da zance mai karya kwana adaki matarsa, ke meyasa bakice mai yakoma nasa ba. nacemai fa , yaki ta fiya ne. momy tayi murmushi ta kalli humaira tace bake kikace kinajin tsoron kwana ke daya ba ? ai yanzo na daina ji. suna cikin haka saiga faruk ya shigo, ya tsaya bece komi ba, momy tace tashi ku tafi . momy nifa inbai tafi dakin shiba saidai na kwana anan.
wai humara meyasa bakijin magana ne nace miki kitashi ku tafi, ba gobe zaitafi ba in ya tafi saiki dawo nan kitare . faruk ne yace momy rabu da ita , ki tashi kitafi dakin naki, kuma ko natafi ki zauna can ban yarda kidawo nan ba, yajuya ya tafi.
washegari da wuri faruk ya bar garin. humaira taji dadin tafiyan faruk taci gaba da har kokinta yadda ta saba , sadai yanzo momy ta takura mata da yawa bata barinta fita sai tace ki tambaye mijin ki , ni babu ruwa na ita kuma ko number sa bata dashi shima bayi da nata dan betaba kiranta ba, haka ta hakura da fitan dan bata da yadda zatayi da momy. shi kuwa faruk kulum da tunani humaira yake bacci sai yaji kamar ya kirata ko rashin kuyar ne tayi mishi sai kuma ya tuna bayi da number ta kuma abinda kunya yakira wani agidan yace abashi number matar sa. humaira ko tana ta shirye shiyen tafiya gida dan yau saura kwana biyu suna amma momy batai mata maganar tafiya ba dan haka taje ta same momy tace momy na hada kayana gobe zantafi ko sai ran suna.
momy ta ce yaushe kukayi da mijinki ?
bemin maganar ba har ya tafi. to ke me yasa bakiyi maiba?ni yanzun banda damar da zance ki tafi , yanzo sadai ki kirashi kiji me zaice. momy dan Allah ke ki kirashi. nikam bazan kira shiba. hakalin humaira ya tashi bata da yadda zatayi dole ta kira shi, dan haka ta nufi bangare samira tasame ta ita da aminu, yauwa yaya aminu dan Allah ka kira yaya faruk kace mai gobe zantafi suna. yace caf ai kunfi kusa, ke ya kamata ki kirashi.
nifa bani da number sa ne ,ya karbi wayan ya sa mata. samira ce tace ikon Allah mutun da mijin shi amman baki da number sa .aminu ya mike yana fadin ai wannan soyayyar ta manya ce, ya juya ya fita samira ce ta juwo ta kalli humaira tace dama inason naganki . tace to ai gani. wai faruk be taba kiran kiba ne ? anty me yasa kikamin wannan tanbayan .
tace naga tunda kika shigo gidan keki shishige ma momy duk kinbi kin likewa dangin miji har su meena duk an mallake mikisu amman ankasa mallake miki mijin yana can yana sheke ayarsa da yan matan sa, to dan Allah bari na baki shawara ki dan rage shishigi , tana maganar tana ya tsina baki . humaira ta gama sauraron samira, ta rasa me zata cewa samira dan magan ganu sun bata haushi mikewa kaiwai tayi ta fita tana kuka , dakinta ta nufa ta fada gado ta fashe da kuka saida tayi me isarta sannan tayi shiro sannan ta dauki alkawari duk ranar da samira ta kara yi mata irin wannan saita ji mata ciwo, bayan tayi sallah mangariba taji zuciyar ta tayi sanyi kuma har yanzo tunanin tafiyan ta gobe yanan azuciyar ta dan haka ta dauki waya ta dan, na number faruk, can aka daga. ina wuni tace da shi.
lfy, ya dauki muryarta amma sai yace waye ? humaira ce . yaya akayi ? momy ce tace na gayama gobe zantafi. kina da hakali kuwa ? ni lfy ta lau ,wata na 8 fa banjeba. to ni dai ban yarda ba, ko kofar gida bance kije kuma wlh inkika fita zaki hadu da bacin ran da biki taba ganin irinshi ba. kuka ta fara, faruk najin ta fara kuka ya kashe wayar . momy taji shiro humaira bata zoba tasan ba lfy ba dan haka ta nufi dakin humaira da kanta kuma wanne karo na farko data fara shiga ban garen su tana shiga ta sameta kwance fuska duk ta kunbura, subuhanallah humaira me yayi zafi haka . nan tara kuka ta fada mata yadda sukayi da faruk . momy ta lallashi ta takyar tayi shiru.
har washegari humaira bata hakura ba ta dinga kiran faruk yaki dauka har yamma kira takeyi amman be dauka sai can dare ya turo mata message da sauri ta bude. *ke kika jawa kanki da kibi umarni na da yanzu kina can*.
haka taci gaba da kukanta can tayi tunani bari ta kira nura ta dauko wayar ta ta danna number sa .ya daga da fara,ar sa. humaira ya akayi ne ? nanta fara kuka. ya sake cewa ya salam humaira kiyi shiru kiyimin bayani , faruk ne ko ? tace eh.
to kidaina kuka share hawayan ki ki gayamin me ya faru. nan ta fara gaya mishi abinda ya faru. to shikenan zan kira shi, amman meyasa inya ce kimai abu bakiyi ? yaya nifa ban iyaba ne , cewa fa yayi wai na mai tausa . nura ya toshi bakinsa yace to kiyi shiro karki kara gaya wa kowa . baya ya kashe waya
yayi dariya yace wlh faruk dan duniya ne. yasake daukan wayar ya fara kira faruk bugu daya ya dauka yana fadin sai yau ka tuna dani? shiko nura cewa yake yau asirin ka ya taunu, wato dan kace wa yarinya tama tausa taki shine ka hanata zuwa taga iyayenta. faruk yayi dariya, badai ta gayawa momy ba . oho ni ban saniba, yanzu dai koma mai kake ji dole ka ajeshi sai ta koya , muna fiki kawai. faruk ya kwashi da dariya wai kiran ka tayi ne ? ina ruwanka, yanzun dai zata tafi gobe. ai wlh ba zataba in kaga taje garin nan to haihuwa tayi
[6:35PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURENKI💞💞

32 to 35

✍MMN YAZEED

Nura ya yace amma dai wlh baka da kunya, da wanne dan iskan zata haihu? mata ta ce fa.
ba wani matar ka kai dai kawai kace ka kamu da sonta. dama nasan haka zaka ce amman ni ba wai sonta nake ba, kasan me ne ne ? saika fada. daki daya fa muke kwana kuma kasan nifa ba dutse bane. au she ba dutse bane ni na dauka dutse ne , yan zundai ina neman alfarma kabarta taje. nura nariga narantse , ka rabuda ita wani lokaci zan kaita da kaina . nura yace to shikenan ka kirata ka bata hakuri, wlh ta ban tausayi tana ta kuka . to zankira. bayan yajiye wayar yafara tunanin yanzu yariyar nan haka zamuyi da ita ba sirri, yanzun har tagawa nura, Allah yasa bata gayawa momy ba" tsiyar karamar yarinya kenan babu sirri .

itako humaira har ranar suna tana jiran tsammani saida taga 3:00 sannan ta cire rai tare da alwashi wlh sai ya gane kuranshi haka taci gaba da harkokinta ba walwala atattare da ita ga bacinran abida samira ta mata gakuma bakin cikin faruk, dan haka ta rage sakin jiki agidan duk da dai momy na nuna kolawa kwarai agare ta ,haka sauran yan uwa sai yan kadan wa edda ba a rasa ba, faruk be kira humaira ba kamar yadda sukayi da nura sai ana gobe zai dawo taji ankira ta a waya , ta isa ta dauki wayar, MUGU ta gani kamar yadda ta daura akan number sa. saida tayi Kamar karta dauka , tadai daure ta daga, tana dagawa ko sallama bataiba tace, to me nene ? au ko gaisuwa ma bazan samu ba. akan me zan gaishe ka. matsayi na mijin ki. Allah ya kiyaye me zanci da tsoho" ke ni ne tsoho, barina na dawo zaki gane kuranki "kadawo din kaima zaka gane kuranka wlh " ni din ko ? eh kai. faruk da sauri ya kashe waya yace rashin kunyan yariyar nan babba ne, saina bita ahankali.

washe gari faruk ya kamo hanya bawanda yasan da zuwan shi agidan dan be gayawa kowa ba, humaira kuwa yau tasaki jikinta tayi kwalliya kamar me shinrin zuwa gidan biki tunda ta gayawa faruk magana taji zuciyar ta ta mata sanyi . tana zaune Itada meena , momy na gefe ta kishin gida , meena tace anty humaira wai fly kuwa naga kwana biyu baku cika magana da anty samira ba. bakomai meena kawai da yan maganan basanan ne" meena bata sake cewa komai Amman bata yadda da maganar ba , sai ta dauko wani zance , suna cikin haka sai suka ji muryar faruk yana gaida hjy babba"humaira zabura tayi ,tabi bayan momy tace meena kamar naji muryar faruk. tace ba kama bace shine. faruk yayi sallama ya shigo ya yauna , sallaman shi ya tada momy taga humaira rakube agefeta. bayan ya gaisar da mahaifiyar shi meena ta gaida shi tamike ta fita, humaira kuwa ko mutsi ta kasa yi , shikowa faruk ya kosa humaira tayi magana yaji zazzakar muryarta amman shiro harya gaji da jira yace , ke ba gaisuwa ? tayi banza da shi, momy tace humaira dakefa yake . ta waigo tace ina wuni . yace saida na roka, yamike ya fita .
momy tace je ki kai mai abinci tamike tana zunbura baki. lokacin da humaira ta isa bangaren su ta same shi a falo yayi wanka ya canza kaya taje ta aje abincin ta fara zubawa yayi maza yarike hannuta yace to gani na dawo , koda yake kince zan gane kure na ko? tayi shiru batace komi ba. me nayi miki kika daina gaishe ni? nan ma bata kulashi ba, nan yafara tunani wannan yariyar innayi wasa ko muyar da nake dan samo saiya zama aiki , shi ko rashin kuyar ne ma tayi mi shi yana so dan haka ya mike ya zagayo kusa da ita ya zauna yana rike da hannun ta. saida taga yayi kusa da ita sosai sannan tace ni wlh ka sake ni. yakara rike hannun yace kwantar da hankalin ki, niba wani abu zan miki ba, magana kawai zamuyi kinji, kisan me Nene ? ko kalloshi batayi ba , humara kiyi hakuri nasan nayi miki laifi ba nayi bane dan na bata miki rai bane, ni bana son kitafi ke daya ,ki bari da zarar na samo lokaci zan kaiki da kaina amma kema kidaina min abida kike yi min ki dinga bin umarni na nifa mijin kine, ko bikisa hukunci matar da take yiwa mijinta haka ba" yana maganar yana kara shigewa jikinta. tace nidai kasake ni. kuma wlh idai sai nabi umarnin ka zaka kaini gidan to na hakura da zuwa. haba humaira me yayi zafi haka. tafara ciki cikin kwace hannun ta, da taga bazata iyaba tasa bakinta ta gantsara masa cizo da karfi amma ko gezau beyiba saida wurin ya fashe harya fara jini sannan ya saketa . ta ,kwasa da gudu ta nufi hanyar waje , shima tashi yayi aguje ya tare ta, ta fashe da kuka tana ganin kashin ta ya bushe.
zo ki zauna ba abinda zan miki kinji, yanzo fa saikice dakin momy zaki ko, dan Allah humaira ki daina haka yanzun ba dama muyi abu adaki sai kinje kin gayawa momy, zoki zauna bazan miki komi ba. biyoshi tayi suka zauna sannan ya saketa , yace bari na wanke hanuna na dawo, ta kalli hannuta taga jinin faruk sosai ya fita har a kasa , dan haka tamike tace so yake ya dawo ya zaneni babu me cetona.

futowa yayi be ganta ba , beji dadiba dan beso momy tasani ba dan haka ya kasa zuwa dakin, yaneme guri ya zauna. zuwa can anjuma saiga anty amarya ta shigo da sallama, tasamu faruk yana shafa man zafi ahannu shi ga digon jini akasa, tace faruk wai me yafaru ne, ga humaira can taki magana sai kuka take. ya daure fuska kukan munafurci take anty , cizo nafa tayi . cizo kuma, kai humaira itama bata jin magana, ta juya ta fita, saiga momy rike da humaira tashigo tace karka sake kace zaka tabata yanzun haka mugunta kaje yi mata . momy magana fa kawai nake mata ta kamo hannuna ta ciza. to naji abar maganar ke humaira zoki bashi hakuri. tace Allah ya baka hakuri bece komiba ta shige dakin.
washe gari da safe nura yayima faruk waya bilkisu matar shi bata da lfy. dan haka yaje dakin momy yagaya mata sannan yace tama humara magana su tafi tare. bayan momy tama humaira waya bata bata lokaci ba, ta fito suka dau hanya, suna cikin tafiya ya waigo yace, baki cemin ya jiki ba kuma jiya da

Please Login or Register in order to submit comment