Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana fadi ina abba furuk?
yace abdallah kenan kuna gida daya kuma zaka rinka tambaya na shi. yace toh ai yau bangan shi ba. toh yanzun nan zaka ganshi ,yana hanya.
samira ce takatse musu hirar daga shigowan shi kasashi gaba da surutu. yagaida Anty amarya kazauna mana.
a,a zan shiga gun momy ne samira tace inawuni yaya.lfy lau samira ya megidan.tace lfy lau. yasakai dakin momy ,ya kwan kwasa kofar ,tace shigo nura . bayan yashiga ya zauna ya gaida momy tace rike gaisuwar ka banason momy me yayi zafi ? dakai da Dan,uwanka nakusa dai amsa gaisuwar ku .
dan Allah momy karkiyi haka, inkikai fushi haka ai bazamu ga albarkan abin ba, nasan banzai wuce maganar auran faruk ba, dakata nura, nasan duk halin da dan uwan ka yake ciki kasani. yace haka ne momy ya fada a takaice .
toh naji, inaso na tambaye ka, amma kamin alkawarin zaka gayamin gaskiya .
insha allahu zanfadi abida na sani.
nura dan uwanka yana neman matan banza ne ?yace
toh nidai a iya sanina faruk baya ta ammali da mata, gaskiya.
momy ta dukar da kai tai shiru, nawasu mitina sannan ta dago tace, toh ko dai baya da lfy ne?nura yadukar dakai yace
wlh lafiyar sa lau kuma daina tunanin nan.
nura tunani ya zama dole , yanzun baban ku laifena yake gani yace kila baida lfy,banja shi ajikina ba bare ya fada min, kuma innayi tunani sainaga kamar haka ne ,
ni tunda nake ban taba jin ance you ga budurwar sa ba,, koko ace ya taba cewa yana son wance, kaga ko abin akwai kulle kai.
yace gaskiya ne momy, nima din bantaba gani ba, amman dai lfyr sa lau wlh , aure kuma yanason yayi Amman shi anashi ra,ayin yafi son karama kuma
yana so ya zaba da kansa.
waya hana shi ya zaba, yanzun kanin shi tun yana secondary za,ace yace yana son wacce ,amman wannan shiru fah. yanzun dai momy dan Allah kikwatar da hakalin komai zai wuce insha allahu, barinje wajan faruk din .
toh shekenan kunadai rike da ranar ko? eh yace da ita yana kokarin fita daga dakin

nura ya tura kofar dakin faruk ya shiga, yasame shi zaune akasa yace, meye haka kuma ? faruk yace wlh hankali na atashe yake. toh ai kai ka zabi haka .
bahaka bane, nura,bazaka gane ba, yanzon acikin yan kwanakin nan, za,ace nasamu matar aure saikace yar tsana.
gaskiya faruk nagaji da halinka , kai wai wani irin buri kaci ne haka.
ba haka bane nura, niyanzun ma tsaya, tukuna dai ,momy har yanzun kuka takeyi ? a,a batayi kuka ba, amman dai ranta abace yake, kuma bai kamata ace kamar ka kana batawa iyayenka rai ba, faruk kafa girma ya kamata ace anwuce wannan worin.
na sani nura, dazun fah momy kuka na sameta ta tanayi.
toh ina amfanin irin wan nan ,haka dai nura yayi taba faruk shawarwari

akwana atashi kwanaki nata tafiya abubawa nata faruwa gashi yau har saura kwana biyu biki gidajen ya,uwa duk ya kaceme faruk kuwa antura su abuja daga office dinsu anasa ran dawo wan shi ayau
kuma ayau ne iyayansu suka shirya zama domin tattauna agidan mahaifin su wato malam
bayan sun bude taro da ar,dua ne suka fara tattaunawa akan matsalan da faruk yakeso kawo musu acikin dangi wannan zama kuwa anyishi harda yaya sulaiman da anty hafsat yayyen faruk wada hjy safyya ta haifa

malam faruku ne yafara magana, yanzun dai takwarana banda shi kenan awannan biki. alhj usman yace to baya ga anbarshi yana abinda yaga dama ba saikace yafi karfin mu, ai yaka mata mununa mishi mune iyayen shi, saimu zauna yaro karami yana juya mu ,wlh tllh be isaba.
alhj ahmad yace saurara usman yaran zamani yanzun lallaba su akeyi, inhar akace za,ayi musu da karfin tsiya toba inda abin zaije.
hmm ku kuke sa yaran nan nama na tsayayya wlh dole sai anbi abinda yake so kenan.
sulaiman ya dukar da kai yana son yayi magana amman yajin tsoro baba usman karya dawo kanshi alhj yusuf yace nidai idai nine anemi koma wacece a aura masa kwai, malam yace haka yadace amai, ina nura? alhj usman yace bezoba ai dukkan su muna fukai ne.
alhj ahmad ne yace nidai inhar zakubi zawara ta malam aban dama ta karshe, ayi bikin nan abar faruk ni nasan yadda zanyi masa
[6:34PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURENKI💞💞

7 to 10

✍MMN YAZEED

Alhj usman ne yace nidai gaskiya ban amince da wannan shawara ba.
alhj ahmad ne yace ,yusuf kai me ka gani . yace duk yadda kuka yanke daidai ne
alhj ahmad ya dukar da kanshi kasa yayi shiru yana tunani falon yayi shiru can alhj ahmad ya dago kai yace usman ina da hujjujin dayasa nace abar nasa sai daga baya,
kaga nafarko faruk baida yarinyar da zai aura sannan lokaci ya kure balle muce zamu nemar mai wata inkuma mun samu yariyar ma toh bawani kwakwaran bunkece zamuyi ba saboda lokaci yariga ya kure, dan haka nakeson abarmin komai ahannuna nanda wasu yan sati faruk zaiyi aure ko yaki ko yaso.
malam ne yace nayarda da dalilan ka dan haka kubar maganan ahanun sa alhj usman badan ransa yaso ba .
haka akayi bikin akabar furuk

faruk dai yaga andaura aure shiko bawan da yamai wata magana nandai yafara tunanin kila zaman da sukayi sunyi shawaran abarshi sai sanda yaga dama, dan haka ya sake ranshi yanata harkan gaban shi, bayan anyi biki amare su biyar kowacce tana dakinta .

faruk ne zaune a haraban gidan su yan shan iska da waya ahannu sa yana dan dadda nawa, saiga motar alhj ahmad ta sawo kai nura ne ke jan motar faruk ya mike da sauri yaje wurin ya budewa alhj murfen motar yafuto nan yafara gaida shi ya amsa da murmushi , nura ya zagayo ya mikawa faruk hannu suka tafah , alhj yayi gaba yabarsu anan yana fadi inkugama kusame ni aciki, sundade tsaye suna cabtar su sannan faruk yaga kira daga maihaifin sa, yadaga yana fadi gamunan zuwa, ahanyan su nashiga ciki faruk yake tambayan nura wai lfy kuwa ?
yace ai kasan tatsuniyar gizo bata wuce ta koki . dahaka suka isa falon.
alhj ne yace babana manyan kasa, kagama buyar kenan ko ?
baba dama ba boyewa nayi ba aikine yayi mana yawa.
toh ai shikenan, yanzo a ina muka kwana.
faruk yayi shiru ya dukar da kai kasa . alhj yusuf ne ya kalle shi yace bada kai ake magana bane .faruk yadago ya nama nura alama da hanu, kace wani abu mana.
nura ya make kafada. faruk dai daya ga ba sarki sai Allah ,sai yace baba wlh ban samu bane . yanzun kana nufi baka samu wace kakeso ba? eh
shikenan babana yanzo umarni zanbaka, bana neman amincewan ka ,ko zabin ka , kuma yanzun ne zamu gane kafi karfinmu ne ko kuwa, yadda kuwa zamu gane kafi karfinmu shine bijerewa umarnin mu.
dan haka nake sanar dakai kashirya karban angoci nanda wasu kwanaki zamu zabama mata, ya kalli faruk da nura yace kunji ko bakuji ba ?
suka hada baki sukace munji. yace kutashi kutafi .suka tashi sukayi cikin gida. bayan fitasu ne Alhj yusuf ya kalli yayan shi yace gobe inson zanyi tafiya zanje katsena gidan alhj nasuru babban dansa yarasu gobe ne bakwai zanmai gaisuwa . au haka ne fah naji sanarwa aredio enkaje kamai gaisuwa.
yace zaiji insha allahu
alhj nasiru aminin alhj yusuf ne tare suka taso da zumunc
mai karfi tunsuna yara kanana. bayan suyi sallama alhj ya tafi. sai alhj yusuf ya mike yanufi dakin hjy aisha , momy taji mamakin ganin alhj dan baifaye zuwa dakinsu ba.n yace jeki kiramin faruk. tace yau kuma ba baban saika kira sunan gatsal haka. eh ba zance mai baba ba dan banana ba haka yake ba, d'a da mahaifi sai Allah momy bataji dadin maganar nan ba. ko .kuma ma barshi ,ki gaya mishi nace inhar alhj ya kawo mai mata yace mai baya so ,Allah ya isa ban yafemai ba, bejira mezata ce ba ya fita. wa shegari anayin sallah subahi alhj yatafi katsina bayan yayi sallama da iyalan shi. 8:00 faruk ya fito domin tafiya office ya leka dakin momy yace natafi .tace yauwa zo nan dama babanka yace nafada ma inhar baban ku yakawo maka yariyar dazaka aura, kace a,a beyafe makaba. faruk besan lokacin da yazauna ba yace momy me yayi zafi haka? oho kaika sani . momy dan Allah kibashi hakuri dan Allah. nidai sako yabani kuma nasanar ma tashi ka fitanmin adaki.

KATSINA
Bayan alhj ya isa gidan alhj nusiru yatarar da shi yata karban gaisuwa,
alhj nasiru yaji dadin zuwan shi kwarai da gaske, bayan mutane sun watse yarage daga alhj nasiru sai alhj yusuf sai kuma hirar bayan rabowa ta barke inda alhj ya tambaye shi wai faruk yayi aure kuwa?. yace inafah har yanzun baiyi aure ba , ko kunya bayaji d'an aminu fah shekar shi uku da wani abu. yace ai lefin ku ne me yasa baku bashiba acin yaran ku ba. nima naso haka amman kasan halin alhj ahmad memakon muyi sharawara atsakanin mu sai yace sai annemi zabin yara, toh shi kuma faruk anashi haukan wai shi yar secondary yake so.alhj nasiru yayi dariya lalai faruk, toh balaifi idai wan,nan ne takwana gida sauki , aini inada kananan yara badai ni da niyar aurer dasu yanzun , amma tunda dana ne na bashi ko nan da sati daya ne sai ayi alhj yaji dadi sosai yarasa wane irin godiya zaiyiwa alhaji nasiru. bayan sun shiga cikin gidan yayima matan shi gaisuwa yarako shi har gon motarsa yashiga yace gobe su yaya ahmad zasuzo. yace allah yakawo su lfy .
alhj nasiru da bai naimi shawaran kowaba ya yanke hukunci ya shiga gida ya kira matan sa guda biyu , yace dama wata magana ce ta taso ya kwashe yadda sukayi da alhj ya gaya musu .hjy rabi uwargidan alhj ce ta daka talle tace wacce yar taka kabashi, badai zainab ba. yace ita. nan tamike tafara fadin wlh wlh bazai yuwuba yama zayyi haka dandai ni baka sona kowanne tarkace ka zubomin ingaskiya ne kabashi humaira mana ko dan ita yar gaban goshin kace.alhj ya kalli ta yace kingama ta murguda baki tace eh.yace shikenan dama abinda yasa nace zainab naga humaira tayi kankata da yawa ne kinga fah zainab wannan shekarar zata gama secondary humaira fah sheranta17 ne kuma ss1take tace alhj gaskiya nifa bazan taba yarda da wannan zalincin ba alhj yamike yana fadi baki isa kihanani iko da yata ba hjy fatima wadda suke kira da anty tace alhj dan Allah kubari tunda dai kariga da kayi musu alkawari nina amence abashi humaira amman dan allah alhj kagaya masu zata cigaba da karatu.
alhj yaji dadi sosai yace nagode fatima dama ai zata cigaba da karatun ta wannan dalilin yasa nakejinki araina fiye da yadda baki zato. hjy tamike tawuce tana fadin kukusani alhj yace bari naje can gidan yaya nasanar mai tace toh yana fita tashiige daki tafashe da kuka tana tausayin yarta yayanta kenan guda biyu daga yayan humaira auwal sai ita humairan
bayan alhj yusuf ya koma kano bai sauka ko inaba saigidan yayansa bayan ya gaya mishi yadda sukayi da alhj nasiru yaji dadi sosai dan haka suka shirya tafiya washe gari basu gawa kowaba acikin matan su
nura ne yaja su kuma shima besan meye zasuyi ba , nura nata kasa kune ko zaije suna fadin inda zasu sukasha manyan kaya haka su uku ne ciki alhj ahmad sai alhj usman saikuma kanin malam sun isa gidan alhj nasiru karfe 2:24 bayan sun huta sunci abinci saiya hada su da auwal ya kaisu gidan wanshi malam buba
bayan sun shiga gidan ankarbe su da mutunci suji dadin tarbar da aka musu sanan sukafara maganar akan abinda ya kawo su alhj ahmad ne yayi magana , malam nawa zamu bada sadakin yar tamu yayi dariya yace sadaki ai baya kadan ku bada dubu talati Allah yasa su zauna lfy .alhj Ahmed ne ya mike yace ina zuwa yana fita ya daga waya yakra kaninsa yusuf ya fada masa . yace a,a ni amatsayina uban yar ,ban yarda ba dubu dari zaku bada, alhj ya koma ciki yace uban yar yace be yarda ba, yace wai dubu darine sadakin ta malam buba ya gane wasuke nufi yace a,a dari yayi yawa dakyar dai ya karbi dubu dari buyu harda kayan sarana suka tsaida rana sati daya.
suka futo suka samu nura a motar

sun kawo kano fly saida suka tsaya ahanya suka sayi dabino alewa sanan nura yakara tabatar da zargin sa azuciyar shi yace yau faruk akwai tashin hakali kenan.
gidan malam faruku suka yada zango suna shiga inna ta rangala gula nura ne ya fakaici idonsu ya harari ta.
nandai aka raba kowan ne ya wuce gida da kulin nashi nan da nan lbr ya karade dangi kowa na murna shikuwa faruk besan dawan garin ba dan tun safe ya tafi gidan kakan shi maifiyar Maman shi
[6:34PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURUNKI💞💞

14 to 16

Shirye shirye nata kankama komai angama shiryawa yau saura kwana biyu biki, kuma yau aka kawo akwati gidan su humaira an musu tarba na musaman kayane na gani nafada hjy fatima da yan uwanta suji dadin ganin yan uwan faruk, saboda sunga alaman karamci atatare da su , sadai sun lura angon beyi na am da yar tasuba danbe zoba kuma beyi waya ba, yayar hajiya fatima ce tafara yin wannan korafi suna ganin laifin fatima da tayadda da wannan abu , yaya zaki dauki yarki guda daya kimata wani irin aure ,ai koma za amata irin wannan aure yakamata a fara turo yaron su daidaita da yarinyar, hjy fatima tace nidai Allah kadai yasan abinda ya shirya kawai mubar ba Allah, to shikenan Allah yasa haka shine mafi alheri.
itako hajiya rabi tunda taga akwatin humaira hankalinta ya tashi tanata dana sani ,bakin ciki nacinta idan ta tuna manya manyan gwala gwalan da tagani acikin akwati dazaran tatuna irin maya mayan mutocin da yan kawo akwatin suka shigo, ai ita tazace duk wasu abubuwan al ada humaira bazata samu ba, intai la,akari da karancin lokacin da a kasa.

hakama gidan su faruk anata shirye shirye biki yan uwa duk sun halara nura ko bazama abubuwa sunmai yawa faruk kuwa yaki gaiyatan kowa daga cikin abokan shi, sai nura ne yakaima wada yasani kati
nura ne yazo yadauki faruk zasu fita saiga alhj yadawo zaishiga gida yace inazuwa haka nura yace zamu dan fitane jyace bazakuyi aski bane nura yace zamuyi dama yanzun can zan kaishi, to kayan da zaisa fah kun tanaza ne ? nurane yasake magana, nasa wani zaikawo anjema.
yace kushirya da wuri ,alhj yaji dadin yadda nura yakeyi yawuce yana fadi Allah yayi muku albarka. tuni kayan amarya suka iso da yan uwanta guda uku bayan sugama gyara dakin suka koma katsina.

Tofah rana bata karya yaune za,a daura auren faruk tunsafe suka fara shirye sheyen tafiya daura aure gidan duk ya hargitsi faruk ne ya fito ko wanka beyi ba yatarar da yaya sulaiman a falo yasha manyan kaya yace yaya harka zo ? kai mekakeyi baka shirya ba, har yanzo kana kan bakan ka kenan, kaidaiyi ahankali kar wata rana muga kana yar murya. yace habadai Allah ya kauta yar tatsitsiyar yariyar zanwa haka.yaya yasake cewa kataba kiranta kowa? a,a nakirata nace mata me, niban kirata ba. yace lallai faruk nan gaba akwai aiki wlh kare cika baki, yanzu jeka shirya .
bayan faruk yayi wanka yadauko wani yadi daga cikin kayan shi zaisa kenan saiga nura da Ismail abokin faruk suna shigowa suka fara tsokanan faruk nura ne yace cire wannan kayan gawanda zaka sa nan yamika mai leda hunnushi yakarba ya futo da kayan yadine me kyaun gaske fari tas da hula da takalmi da agogo aciki. faruk ya kalli nura yace kaidai wlh dan wahala ne, kanata kashe kudin ka abanza. yace nidai ko me zakace kace,amman kai sauri kasa kayan. bayan yasa kayan ne suka fito, da fitowan shi yan,uwa suka hau fadi kaika kaga angon har wani haske ya kara lallai angoci yayi. yace bawani angoci dama da haskena. lokacin duk su alhj suntafi su faruk ne kawai da abokan sa. ya leka dakin momy nanma cike yake da mutane bayan ya gaida su ne ya tsaya abakin kofan yayi shiro can ya dago yace momy zamu tafi. itama tadanyi shiru na wani lokaci sannan tace haka zaka tafi daura auran a murtuke fuska ba fara,a to dan Allah inaneman alfarma kasake ranka bece kome yasake cewa na tafi. momy ma kasa cewa komi tayi amma tamai andua azuciyar ta sai yan dakin ne sukace Allah ya tsare yakuma sa adaura asa,a bece komi ba ya fita. bayan sun futo harabar gidan ya tarar da friends dinshi da yawa awaje harda yan office dinsu, mutoci kuwa ba,a magana wannan na wane waccen yana futowan suka hau yimai shakiyan ci irin nasu na abokai. shedai faruk ba baka saikunne sun isa katsina lfy inda nanma sun tarar da mutane makil, nan da nan muroka sukayo kansu sunata kirari wani abokin faruk ne ya nuna musu ango suko isa gareshi, faruk dabesan hayaniya yabude aljihu yanata basu kudi duk dandai su barshi ya huta nandai dubban mutane suka shaida auran faruk yusuf faruk matawalle, da amaryarsa aisha humaira nasir. faruk yatuna maganar momy dan haka yafara ya'ke. mutane sunmai ca kowa kokari yake sugaisa anata mai Allah yasanya alheri yana ameen ameen nura ne yalli faruk yaga yasake yanata fara,a ya matsa kusa dashi yamika mai hannu yace inatayaka murna, faruk yace zaka fara ko. bayan muta ne sufara wucewa ne saiga aminu yana tahowa wurinsu yace baba yace kuzo ku gaisar da baki nan suka kama haya da wasu daga cikin abokansa bayan sun gaisar da sune suka fito . su alhj ma sunfuto da tawargar su sun tafi, wasu da cikin abokan faruk ma suntafi sauran kowa sunajira afuto musu da amarya nura ne yaga shirun yayi yawa yace bari dai nashiga naga mesuke jira ne har yanzo. faruk yace nifa nagaji zan wuce . nura yace ina zuwa yasakai ciki , ya cidda su mama hadiza zaune afalon yace wai ina amaryan ne yamma fa nayi saiga wata dadtijuwa ta fito da wata kyakyawan yarinya tasha ado da zanan fulawa ahanu da kafafuwan ta mama hadizya tamike ta mikawa yarinyar hannu takama tana kuka me tsuma zuciya nura yace amarya tamuce kai masha allahu yadafa azuciyar shi bayan sudauki amarya da yan uwata suka kama hanya, a mota nura yace ma faruk ba kaga yarinyar ba wlh ta hadu tanada kyau sosai . yace to ni meya dameni da kyanta, kaima inaruwan ka da ita zakazu kana cemin wani tana da kyau kaje ka kare ma yariyar mutane kallo nura ya kwashe da dariya yace kace dai nakare ma matarka kallo. yace niba haka nace ba
motar amarya ita tafara isowa baayan anshiga da amarya dakin momy. momy taga yariya nata kuka fuskarta arufe tace taso kizo nan humaira. humauira tamike taje gaban momy ta tsuguna , momy ce ta jawo ta jikita tace kidaina kuka nan ma gidan kune ki kwatar da hakalinki, bude fuskarki kisha iska, tasa hannu da kanta taja mata gyalen.
bayan sauran mutocin sun karaso ne suka. dauki amarya akakaita dakinta gaskiya anshirya daki ,nera tayi kuku .
washe gari yan rakiyan amarya nata shirye shiyen komawa amma yan uwan hjy fatima sunason ganin faruk
kafin suwoce, dan haka suka je dakin. momy suka suna son ganin furuk, momy ta daga waya takira shi, yace gashi nan zuwa sunan zaune sunata dan hirarsu, saiga furuk ya shigo, momy tace zoka zauna .tamike ta fita , bayan sungaisa daya daga cikin matan tace dama humaira ce dan Allah gatanan amana kaiyi hakuri da ita yarinya ce karama bata da wayo sai anyi hakuri da ita. yace bakomai dayar tace muma mugama shiryawa. yace to dama yanzun motocin zasu karaso .
haka suka dinga dauko jakarsu da daya baya daya suta fita batare da sani humaira ba , can humaira taji tashin motoci ta leko ta window taga wasu mutocin har sun wuce, tasaka kara tafito da gudu dankwali ahannu da gudu ta sakko faruk da abokan sa suna tsaye bakin motar data rage su momy ma suna gefe sunrako baki saiganita kawai sukayi ta fito aguje tarike motar . samira ce tafara kokari riketa amma ta kasa nura ne yace ma faruk kaje ka kamata mana. yace caf ninema zan kamata. dakyar suka samu suka maidata ciki tana kuka maiban tausayi momy ma kuka take tausayin yarinyar ya kamata dan haka ta turamata meena ta tayata hira
[6:34PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURENKI💞💞

11 to 13

✍MMN YAZEED

Bayan faruk ya baro gidan kakanin shi yana kan haryar sa tazuwa gida, yaji kira daga alhj ahmad. yayi kamar karya dauka saida, takusa katsewa ya dauka.
tare da sallama. alhj ne yace kana inane? yace ina hanya zanje gida. gashi kuma, inason ganinka? faruk yayi shiru na dan wani lokaci, yace ganinan zuwa. bayan sunkare wayan faruk yayi zurfi atunani, waisu wadan,nan ina suke son nasa kaina ne, kullum magana daya ko gajiya basayi, ni wlh nagaji da maganar nan, nifa inhar suka takura min, kararsu zankai gun malam.
dawan nan tunani ya isa gidan, kofar dakin nura ya buga . nura ne yace waye ?
gafara malam zoka bude min. ai nura najin muryar faruk da sauri ya taso dan ya dauka maganar yazo yamai, yana budewa yafara fadin ango kasha kamshi.
bafa nason irin wannan wasan. bayan yashiga ya zauna ,yace ina madam ?tana cikin gida, lfy? yace ruwa zata kawo min . bari na kawo ma mana bayan suyi hira sama sama nura ya fahimci faruk besan dawan garin ba, dan haka yaja bakin shi ya tsuke. faruk ne yace zomu je ka rakani gun baba . a,a nikam bazani ba ai wan,nan ganawar takuce, bani cikinta. faruk yasake cewa zomuje kana kara batamin lokaci fa. nifah wlh baxanje ba, zanjira ka awaje, ko murfen mota ne na bude maka,inkuma abin ya gagara nakaika gida.
faruk be gane me nura yake nufiba, yace saikace wani mara lfy, banaso je ka kwata kawai wawa da kai .
nura yace kadai bini ahankali, in bahaka kuwa zaka gane kuranka.faruk yayi tsaki ya shiga cikin gidan .ya tarer da alhj yana tattara takardu, bayan sungaisa alhj yafara jan faruk da hira, tun faruk na dari dari harya sake jikinshi sonata hira can alhj ya dauko ledan dake gefenshi ya mikawa faruk ,yasa hannu buyu ya karba. yace gashinan ko kana da wanda zakaba alewan sa ranar kace.
gaban faruk ya fadi nandanan gumi ya fara fesu mishi, yace ansa ranar ne? eh rana itayau ne.
yace baba gaskiya yayi kusa da yawa,aiban shirya ba, kuma bani da wajen da zan zauna.
alhj yace baka gama gininka na abuja ba? a ,a ban karasa ba.
yace to karka damu dama koka karasa ma ba acen zaka zauna ba, za abaka wanjen zama .faruk dai ya sunkuyar dakai idon,nan jawur bashi da sauran dama, duk ta inda ya bulowa alhj sai ya kauce , ya zauna yakasa tashi .hjy ce taga shirun yayi yawa. tace kaci abinci kuwa ? banajin yunwa ya fada kansa akasa. tace waikai lfyr ka kuwa, kaifa namiji ne ,ba macce ba, to kai kanayin haka mace kuma tayi yaya. alhj yace rabuda shi, tashi kabani waje. yamike ba magana yayi dakin momy tana ganin shi gabanta ya fadi fuskar nan ba rahama ,ya zauna ,meena na zaune agefi tana danna waya yace momy dama nazo na miki magana dan Allah ki roki su baba adan kara lokaci, lokaci nan yayi kadan kuma duk agidan nan wa,akayima

Please Login or Register in order to submit comment