Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

humaira gani tayi bashi da niyar sauke ta dan haka tafara kokarin kwacewa, faruk kuwa kin sakin ta yayi yana da damatse ta.

duk yan falon binsu su kai da kallo, banda momy data daga kai sama , samira kuwa bakinta yafi na kowa budewa , shikowa aminu kallon su yake yana murmushi lallai yaya ya kamu.

hajiya ce tace wai faruk meye haka ne, ka sake ta mana.

momy tace hajiya bar shi ya gama tsiyaya rashin kunyar shi.
da sauri faruk ya sauke humaira yace kasa tafiya fa tayi.
humaira kuwa kusa da momy taje ta zauna.
bayan su gama gaisawa momy ta kalli humaira tace humaira me yasa me ki har kika kasa tafiya sai an dauko ki?
humaira kasa magana tayi, sai faruk ne ya bude naki yace, cewa fa tayi wani abu na mata mutsi aciki.
aminu kwashe wa yayi da dariya.
faruk ya jiyo ya kalle shi yace dan ubanka ni ka kewa dariya, ina wasa da kai ne.
Yaya ai kai ne naji kace wai cikin ta na mutsi , to ba mutun bane aciki ai dole yayi mutsi.
faruk bece komi ba mikewa yayi ya shiga bangaran su.
meena nagani faruk ya bar wajan ta fashe da dariya tace anty humaira wlh da gangan kikeyi so kike ki zarar mana da yaya.

momy tace meena ki kama bakin ki dan in ya jiki , kashin ki ya bushe agidan nan.


faruk da humaira komawa sukayi kamar sababin amare kuluma suna manne da juna.
faruk kuwa ji yake kamar yanzun ne yayi aure dan har wani kima yayi ya kara haske. ansami abinda ake so.

haka zaman su yaci gaba da tafiya humaira har bata son lokacin tafiyar faruk yayi, da zara lokacin tafiyar faruk yayi humaira zata fara kuka.
Su momy har sun saba duk ranar da faruk ya tafi humaira bata fitowa sai washe gari.
haka kwanaki suyi ta tafiya gashi yanzun har cikin humaira ya tsofa haihuwa ko yau ko gobe , humaiya da 'ker take tafiya sabo da girman da cikin yayi.

faruk ya kosa humaira ta haihu dan yanzun baya samun yadda yake so , daya taba ta Zara fara nokewa , daga tace bayan ta ke ciwo sai tace kafar ta na ciwo.
shiko faruk ya riga ya saba dan haka baya iya hakura sai yasan inda ya lallabe ta tabari.

dan haka humaira ta fara jin tsoron faruk, Dan haka a yau faruk na sakin humaira ta samu tayi wanka, ta aje mai kayan kari .
wuce wa tayi dakin momy da niyar baza ta koma ba sai dare, dan tasan indai ta tsaya to da rana ma cewa zaiyi zai kara.

humaira na shiga dakin momy ta nemi guri ta kwanta tace momy idan yaya yazo nemana kice mai bani da lfy.

momy tace humaira kenan meye kuma na karyar ciwo, yana takura miki ne dai ko?
shiro tayi bata ce ko mai ba.
humaira bata dade da kwanciya ba faruk ya fara sintiri , zuwan shi na uku kenan yace momy wai har yanzun bata tashi ba ne.

eh bata tashi ba, wai yau she zaka koma ne?
momy nifa jira nake humaira ta haihu sannan na tafi.
tace a,a gaskiya ka shirya ka tafi , data haihu za,ama waya, kabar yarinya ta huta.
momy ce miki tayi ina takura mata.
tace a,a ni ba ta cemin ba, nice dai na fada ka shirya ka tafi.

faruk zama yayi ya kasa cewa komai , har aminu ya shigo suka hau hira ,

hayaniyar su ya tada humaira , ta tashi zaune tana kokarin mikewa.
momy tace kibi ahankali mana saurin me kikeyi.
humaira zama tayi sai da ta was tsake tukuna ta mike ta fita.
cikin gida ta nufa ta neme guri ta zauna tana shan iska.
zuwa cen sai ga samira ta fito, tana ganin humaira ta ya tsina fuska, juyawa tayi ta leka hagu da dama bataga kowa ba,
Juyawa tayi ta dawo gurin Humaira tace to muna fuka uwar kisisina me kikeyi anan.

humaira shiru tayi batace komai ba.
Samira ta kara cewa tunda faruk ya kaiki garin ku ku ka bashi a abinci yaci kuka mallake shi, ya zama kamar wani mara wayau.
humaira dai har yanzun bata ce komi ba.
haka samira tai ta gayawa humaira bakaken magan ganu .

humaira mike wa tayi zata bar waja.
Samira tace ai dama baza kice komi ba, tunda karuwar uwarki ta koya miki kisisina irin na ka ruwai.
humaira juyo tayi da sauri ta dawo baya saida taje har gaban samira mamayan samira tayi ta tsuguna ta wawosu kafar samira ji kake tiibbb, ta fadi kasa , duk da haka humaira bata hakura ba, hangon wata ta barya tayi acen gefe dan haka ta nufi gurin da sauri.

Samira na kwance ta kasa tashi sai ganin humaira tayi ta kinkimo ta barya, nan da nan samira ta saka ihu tana fadin kuzo ku tai makeni zata kashe ni.
su kuwa su faruk suna zaune suna hira suka fara jiwo ihun samira aminu ne ya fara mikewa aguje suka fito.

Lokacin da suka fito humaira ta kusa isa gun samira.
da sauri faruk ya taho ya rike tabaryar yace sake, humaira kin saki tayi , takara rikewa tam.
Kowa dake gidan ya fito kowa na tofa albarkacin bakin shi.
sukowa su momy kokarin daga samira suke.
humaira ko so take kawai faruk ya saketa ta koma gurin samira.
faruk ya fara kulewa dan haka ya fara fada, yana fadi kina ganin kinfi karfi nane wlh inbaki Saki ba zan mareki, dama baki da hankali ban sani ba, sake tayi ta fashe da kuka, tafara magana yaya wlh wlh bazan yarda ba, sai dai ka kashe ni, uwata fah ta zaga rudewa tayi tana magana tana kuka wani maganar ma basajin me take cewa har muryan ta ya dashi.
faruk fadi yake to munji kiyi hakuri kibar maganar haka ya isa, faruk gani yayi humaira kamar sambatu take, dan haka yakama humaira ya juyawa su momy baya , yasa bakin shi ya rufe nata dole tasa humaira yin shiru, faruk ya dauke ta cak yayi bangaren su da ita.

su momy baya sunkai samira dakinta , hajiya taje gaban samira tace samira kece babba ki fada mana gaskiya me ya faru a tsakanin ku?
Samira tace wlh hajiya ni babu abinda na mata nidai ina ga Humaira tana da aljanu.
aminu cikin bacin rai yace samira karya kike akwai abinda kika mata , kuma inbaki fadi gaskiya ba wlh zan dauki mumunan mataki akanki, dan bazaki wargaza mana gida ba.

momy tace da aminu ya woce ya tafi baruwan shi.
haka sukayi sukayi da samira ta fada musu amman tace ita bata san ko mai ba.

faruk kuwa tunda ya dauki humaira rarrashin ta yake amman bata ma iya magana sai kuka.

faruk yace humaira wai ke kin manta halin da kike ciki ne, ciki ba gareki haihuwa ko yau ko gobe kina son ki mana asaran baby ne,

Sai lokacin ta samu bakin magana tace cikin kuka yaya uwata fah ta cewa karuwa, wlh in har nabari bani da amfani.

faruk ya mike da sauri yace samira ce tamiki wannan zagin.
to ki kwatar da hankalin ki, bazamu bar maganar ba, dole mu dauki mataki



💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞


93 to 96

FADEELA LAMIDO
MMN YAZEED



Faruk yasha wiya kafin humaira tayi shiru, fuskarta duk ta kunbura sabo da kuka, mikewa yayi ya duka daidai saitin fuskar ta, yace karki kara kuka humaira, kibar min komai ahannu na, bari naje
sallah na dawo.

lokacin da faruk ya fito yajiwo hayaniyar aminu da samira dan haka yadan tsaya, jiyayi aminu na fadin tunda bazaki fadi gaskiya ba ki tattara kayanki ki tafi gidan ku.

faruk ya daga murya ya kira aminu, aminu ya amsa tare da fitowa.
faruk yace zo mutafi masallaci , bayan sundawo suna kokari shiga gida saiga samira tafito da akwatin ta zata fita.

faruk ya kalli aminu yaga hararar ta ma yakeyi.

faruk ya juya yace ke ina zaki.
Saida ta share hawaye sannan tace cewa yayi na tafi gida.
faruk yace a,a koma gida.

Cikin fada aminu yace wlh in kika koma gidan,nan sai na karairaya ki, yaya ba ruwanka kabarta ta tafi.

Faruk ma zafi ya dauka dan ubanka ni kake cewa, babu ruwana , ni abokin wasan kane , cikin tsawa yace ke dauki jakarki ki koma gida dasauri samira ta juya dan dama bason tafiya take ba.

faruk kuwa har suka shiga gida fada yakewa aminu,bayan yagama zagin shi, sannan ya koma mai nasiha.

ganin yadda aminu yadau zafi yasa faruk jikin shi yayi sanyi.

dakin momy suka shiga suka momy zaune tana share hawaye, faruk yace momy lafiya kuwa, me yayi zafi haka.

saida ta gama share hawaye sannan tace kun tabayi matan ku me ya hadasu, tunda ni duk irin jansu da nakeyi ajikina sun gagara fada min.

faruk yace to momy wannan shine abin kuka dan Allah kidaina.

dole nayi kuka dan na tabbata indai suka ci gaba da zama haka, kuma kanku rabuwa zai yi, dan kowa cikin ku yana son matar sa .

In Allah ya yarda haka ba zata faruba, juyawa yayi ya kalli aminu daya hada kansa da gwaiwa yace aminu jeka Kira samira, shima mikewa yayi ya shiga bangaren su .

tana shiga ya sameta zaune akasa haryan zun kuka takeyi, zuwa yayi ya tsuguna agaban ta, yace waike haryan zun baki hakura bane, to yan zun me kike son ayi.

da sauri tace so nake abarni na dake ta
murmushi yayi yace yanzun ke har kika tunani zaki iya dokan samira, samira fa tafi karfin ki , yanzuma da ki kaga kin kadata Allah ne ya baki sa,a
aman ba karfinki ba,

yasake cewa yanzun ke ko kunyar mijinta baki ji, kika yar mai da mata, kina tunanin in nine na samo anyar dake akasa haka zan yarda ne.

Jijikin humaira yayi sanyi faruk ya lura da haka, dan haka yace dashi muje dakin momy duk abinda ta tambaye ki kifada mata gaskiya , inkuma ta yanke hukunci kiyi hakuri da shi ko ya miki dadi ko be miki ba.

humaira kasa tashi tayi sai da faruk ya daga ta .

lokacin da su faruk suka shigo su aminu sun dade da shigowa.

momy samira tafara tambaya tayi shuru taki magana har lallashin ta momy keyi amma ta kasa magana.

dan haka momy ta juwo kan humaira, humaira kuwa tiryan tiryan ta farawa momy bayani tun farkon abinda ya hada su, har na yau inda ta karasa magarnar cikin kuka.

momy sai da tasaki salati sanna tace samira, yanzun tsakani da Allah wani babbaci nake nunawa a tsakanin ku da har zata kai ga haka, samira batace komai ba, in banda kuka, momy taita mata fada , samira bata da yadda zatayi dan haka tamsa laifin ta.

Sannan momy ta hadasu gaba daya taita musu nasiha mai shiga jiki.

Washe gari da daddare humaira tana cikin barci taji marar ta naciwo , tashi tayi da sauri ta sauka kasa.

humaira ji take abu nadada gaba tafara tunanin kodai mutuwa zatayi.

Juya wa tayi taga faruk yana ta sharar baccin sa, tace yaya katashi mutuwa zanyi .

mikiwa yayi da sauri yana fadi meke damunki humaira, ya sauko yazo ya rike ta ganin yadda take murkusu murkusu yasa shi tashi dan yaje yakira momy, humaira rike shi tayi tam.

Yace humaira sakeni nakira momy kodai haihuwar ce, yayi yayi ta sake shi amman taki sakin shi. gashi lokacin karfe 10:47 pm.

faruk da 'ker ya kwaci kansa ahannun humaira, yama manta cewa jikin shi babu kaya , haka ya shiga dakin momy.

momy naganin faruk ya fado mata ko sallama babu , tace yaya ko haihuwar ce.

tana nandai momy ni ban sani ba.
mikewa tayi tadau maya finta.

momy na shiga taga yadda Humaira keyi,tace mutafi asibiti.

momy ta kamo humaira anty amaryace ta dauko kayan baby

suna isa asibitin aka shiga da ita labour room.

su faruk duk suna tsaye ji yake kamar ya shiga ciki.

momy ce ta juyo ta kalli faruk daga shi sai siglet da gajeran waddo, tace Kai lfyr ka kuwa ahaka ka fito , dan Allah ka rufa mana asiri ka koma gida kasa kaya.

kai momy kibarni bazan iya tafiya ba.

hararar shi momy tayi tace wlh in baka tafiba ranka zai baci.

tashi yayi yabar gun ya koma motar shi ya zauna , ji yake zuciyar shi babu dadi kamar dai wani abu zai faru.

tunani yayi azuciyar shi yanzun in humaira ta mutu yaya zaiyi , ji yayi hawaye na bin kuncin sa, dan haka yakira aminu awaya ya fadamai suna asibiti da Humaira.

aminu yace shine baku tashemu ba.
muntafi ne arude aminu ko kaya ma babu ajikina.
kaje daki kadauko min kaya na nasaka.

Faruk na zaune
aminu ya shigo asibitin harda samira da meena aminu ne kadai ya nufo gun faruk, su meena ciki suka shiga.

ya mikawa faruk jallabiyar da ya dauko masa , faruk ya karba yana kokarin sawa ke nan ya hango meena aguje tana kuka ta nufo gurin su.



💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞


97 to 100

FADEELA LAMIDO
MMN YAZEED........✍




faruk sakin baki yayi yana fadin innalillahi wa,innailaihir raju,un tana kara sowa ta tsaya ta fara haki tana fadin anty ta haihu tana fadi tana share hawaye.

ai faruk be saurari me zata kara cewa ba, rugawa yayi da gudu ya shiga ciki.

yana shiga yamu su momy sunata nurmushi anty amarya naganin shi tace to saika bani goron albishir.


Shiko fadi yake ina take .

momy naganin faruk ta hadiye murmushin ta dan tasan ba kunya gare shi ba.
yace anty me muka samu?
tace mace ce.
yasake cewa humaira dai lfy ko?
momy ce ta harare shi .
dan haka yabar maganar, bayan angama gyara mejego da jaririyar ta aka basu izinin shiga .

dukkan su suka dunguma suka Shiva har rige rigen daukan ta suke yi .

Faruk ko bata yar yake ba so yake kawai yaga humaira dan bebi ta kanta ba, ya wuce wajan humaira.

humaira ko dama jira take taga gun wa zai fara zuwa, sai taga ya nufo gurin ta yana zuwa ya kama hannun ta ya rike yana fadi sannu da kokari Humaira, ba dai inda yake miki cewo ko.

Itako humaira kunyan su momy duk ya rufeta dan haka taki yimai magana , tasa kanta cikin kafafun ta.

Shiko faruk zama yayi abakin gadon ya shiga daga mata kai yana fadin humaira me ya faru .

Meena ko na rike da jaririya sai kallon ta take tana share hawaye, ta bude baki tace yaya aminu yariyar kama take da yaya faruk.

da sauri faruk ya matso ya mikawa meena hannu ta samai yariyar.

gani tayi ya rike yarinyar a kar kace tace yaya ba haka ake rike yarinya ba, da saurin shi yace meena zoki gyara min.
baya meena ta gyare mai, tajuya tana mamaki, ita ta dauka data ce mai be iyaba dauka ba , zaginta zai yi ko kuma ya kai mata duka sai ta ga sabanin haka.

acikin daran nan suka koma gida.

washe gari da safe nura yayi sallama agidan su faruk, yana shiga dankin momy ya shiga domin suna dawowa dakin momy aka nufa da ita, faruk yaso abar humaira a dakinta amman momy taki yadda.

nura na shiga ya samu humaira anyi anyi taba ma yariyar nono amman taki, momy sai fada take , nura ya shigo, yana fadi ina yar tamu take, momy dariya ta saki tamika mai yarinyar.

nura yace ina faruk din yake ne humaira?

momy mikewa tayi ta fita , tabar musu dakin, humaira ta bude baki tace nifa yau kwata kwata ban ganshi ba, yana cen yana baccin shi.

mormushi nura yayi , ya daga waya yakira faruk , faruk daukan waya yace kana son yar nan taka kuwa?

sosai ma kuwa gata ma ahannu na, kai sauri kafito kar maman baby tayi fushi.

suna gama waya da faruk sai gashi ya shigo , saida yaje gafda humaira ya zauna yadan ruko ta, yayi murmushi yace ya gajiya.

tace ai ka manta da ni ka tafi kana barcinka. yace waya gaya miki , nifa jiya na dade banyi barci ba, inata tunanin Ku.

suna cikin haka su alhaji suka shigo gaba dayan su, har da alhaji usman.

Nura ne ya mika musu yarinyar banyan ko wannen su ya dauki yarinyar sai alhj ahmad yace to iyayen yarinya kun mata huduba ne.

nura ya kalli faruk , faruk yamike tsaye yace ba ayi ba, dama ku muke jira.

alhj yace a,a wane mu, wane suna kuka zaba mata.
faruk shiru yayi ya kasa magana , alhj ahmad yayi dariya ya mikawa faruk yariyar, yace kayi mata huduba.

bayan faruk ya karbi yarinyar shiru yayi ya dukar da kanshi kasa yana shere hawaye farin ciki wai shine yau har yana da yarinya, lallai iyaye ba karamin son yaran su suke ba, gaskiya su abba sun mai gata kuma lallai wanda beyiwa iyayen shi biyayya ba yayi asara , yau gashi an wayi gari humaira tayi kane kane azuciyar faruk,
zuwa yayi ya mikawa nura yarinyar, yace kamata huduba .
yace wane suna kukasa mata?
Kai zaka zaba mata nura yaji dadi sosai amman sai ya juya yace humaira ko akwai sunan da kike so

da sauri tace a,a

sai da ya gama sannan yace sunan ta nana aisha, kowa adakin yaji dadin wannan suna momy ta samu ta kwara.
abban yaji dadi sosai dan haka ya fara sa musu albarka, suna cikin haka meena ta shigo, nura yace abba meena fa ta girma amata aure.

abba ya kalli nura yace ba yanzun ba nura sai tayi karatu.

alhaji usman yace kasani ko shi ke so.
abba yayi murmu shi yace inshi ke so ai sai ayi ta karasa adakin ta.

Nura shiru yayi ya kasa magana , faruk ya lura da haka , dan haka faruk yace eh abba ayi yana so.

su alhj sunji dadi sosai dan haka basu bar gidan ba sai da su tsaida ranar daura auren meena da nura.

ita ko meena dake kukan farin ciki sai ya ko ma na bakin ciki, har ranar suna meena ko kwaliya batayi ba tana ta kuka tun momy na bata hakuri har ta gaji ta barta.
faruk ko aranar suna ji yake kamar yaune za a daura mai aure da Humaira , jama,ar da be tara da bikinsu ba su a yau su ya tara , walima yayi sosai
yan katsina sunzo suna sosai kwana biyu sukayi suka tafi momy ta musu tarba mai kyau ,suma sunji dadi inda suka koma gida cike da tsara ba.

taro ya tashi lfy humaira har yanzun tana dakin momy faruk yaso ta koma amman momy taki Bari.


nura kuwa yana yawan zuwa gidan wai ko zasu saba da meena , amman meena data ganshi zata shige daki bata kara fitowa sai ya tafi.

akwana atashi ba wuya gashi Humaira har tayi arba,in bayan momy ta gama gyara ta suka dauki hanya katsina aminu ne yakai su , dan faruk tunda ya tafi bai dawo ba, dan haka yace ma aminu ya kaita , shi kuma zai dauko ta.

satin ta biyu faruk ya je ya dauko su,

bayan sun dawo dakin su suka sauka suka balle sabon amarci, momy karama kuwa haka zasu bar ta taita kuka , tun da momy ta lura suna barinta tai ta kuka , tace to ni kubar min ita intana jin yunwa akwata tasha

Please Login or Register in order to submit comment