Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin wannan auren, saini za acemawa wai wani sati daya . dakata ,suda suka gaya maka meyasa baka gaya musu haka ba, koko nice marainiyar wayonka, to wlh bari nafada maka karka kaskura ka kara tarana da irin wannan maganan kuma auren nan kama daina tunanin za a daga shi, mumungama shiryawa gobe anty ku zata hadu akwati. . yace aiko wlh duk yarinyar da aka hadani da ita zata gane kuranta. momy takalle faruk, nikake gawa haka. faruk ya dukar dakai ga dukkan alamu subutar baki yayi momy ce tace ai dama alhj ya karanci bakin halinka, shiyasa yace agyara sama ka zauna.
au asama ma zan zauna, gaskiya ana cutar dani saiga hawaye yana zuba a idon faruk. momy ta lura, tace ma meena dake gefe zokifita, meena ta wuce falo. tace dashi wai kuka kake ne ? yayi shiru kawai yana share hawaye. momy tace amma wlh kaji kunya kayi asara namiji nefa kai ba mace ba , ni wlh har yariyan ma tabam tausayi, me shekara talatin da wani abu, yana kuka ita kuma me goma sha, tayi yaya. yace ba kuka nakeyi ba fah. kadaiji kunya wlh. yamike zaifita sukaci karo da meena zata shigo tadan bigeshi kadan yakai mata duka tayi bayan momy tana kuka, tazaci zaibiyu ta saitaga ya wuce. lokacin da faruk ya shiga dakinshi karfe goma shadaya saura ya hau gado ya kwata yana tunani kalakala azuciyar shi.

washe gari ya kama Sunday dan haka faruk bai fito da wuriba sai karfe tara da rabi lokaci yashiga bankare mahaifin shi domin gaida shi yacidda dakin rufe ya tabbatar ya fita, yace azuciyar shi ina abba yaje dasafe bayan yau babu aiki, ya nufi dakin momy yana dosan dakin ya fara jiwo hayaniyar muta ne adakin ya shiga tare da sallama ,nura yagani zaune da kati agaban shi daga gefe kuwa mama hadiza ce kanwar momy sai anty amarya da samira matar aminu. nura ne yace yanzun nake shirin karasowa. faruk yace mezaka min ? bakomai nazo miyi shawara ne . nikuma na rasa wadda Zanyi shawara dashi saida munafuki . mama hadiza tace faruk wai baka ganni bane ? faruk yace naganki mana, bakiji inata kawo gaisuwa bane.
tace karya kake ko nima fushin ya shafeni ne.
yace waye yace miki inafushi niba fushi nakeyi ba. tace to ai shikenan .yace mama akwai lbr fah. tace to faruk aini inanan har ayi baki. yace lallai abinnaku nayine. nan mama hadiza da anty amarya suka mike suka fita momy nace musu kodin zai isa kuwa . sukace inba bai isaba zanyi waya saiki turo meena. faruk yamike nifa wucewa yanyi . nura yace inazaka bayan yau Sunday? yace gidan malam zani .
nura yayi murmushi yace dama kabar wani kame kamen kafafuwa agidan fah aka raba alewar sunsan komai furuk yace kana nufin malam yasan za ayimin auren dole ? yace susani mana kaini nakaisu fah kai sadakin, amma basu gaya min ma idazamu ba, haka sukai ta bari na a mota kamar maigadi, saida muka shiga gidan malam naji inna anrangala buda sai wani murna take . faruk yace har inacewa zanje gunta ashe ita ta kitsa musu, yasake cewa har ina kukaje neman aure ne.
nura ya kwashe lbrn ya fada masa. faruk jikinshi yayi sayi dayaji cewa yarinyar alhj nasuru ce, yasan ma kamar anyi angama ne momy tanajin hirarsu batace komai ba.
faruk ne yace amman wlh inna zata gane kurenta bazan kara zuwa gidan ba. momy tasako baki karka kara zuwa mana saime .suka futo nura yace zo muduba masu aikin sama mana, bayan sun hau sama nura yace ka musu bayani yadda kake son ayi. yace koma yaya ne suyi kawai. .sai nura ne ya nuna musu yadda zasuyi.
bayan sun koma dakin faruk nura yamika mai katin, yaki karba, yace kaje karaba kawai nime zanyi da shi. yace to naji zanraba, amman dan Allah ka rage nuna kiyayyan ka akann auren nan ya kamata kamusu biyayya kagafa sunyi iya bakin kokarin su ka kawo mata kaki, to inbahaka ba ya kakeson sumaka, yadauko wata yartakarda a aljihusa ya mika mai wannan number tane kakirata sunanta HUMAIRA

Wacece humaira
humaira yariya ce kyakya sonkowa farace tas matsakaiciya ce itaba ba duguwa ba itanaba hajeriya ba , batada kauri sosai saii uban gashi hargado baya, bagaren halaye kuwa tana da ladabi da biyayya ga nagaba da ita, saidai inkatabo ta bata da kuya ga shagwaban tsiya da surutu , lokacin da tasami labari za, amata aure tayi kuka kamar ranta zaifita acikin kwana biyu duk tafita haiyacinta, hjy rabi kowa ansame abinda akeso dama babban farin cikinta taga fatima da iyalanta cikin bakin ciki inbanda shewa ba ,abinda take, itako hajiya fatima tana ta shirye shiryen auren yarta take ,amma fukarta babu walwala dan tausayin yarta da take ji
[6:34PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURENKK💞💞

15 to 17

✍MMN YAZEED


Meena nata jan humaira da hira harta dan sake jikinta da ita, har dare meena na dakin har sukayi sallah sukaci abinci tare , bayan sunkare saiga anty amarya ta shigo, tace sunnuku kuta hira, tawoce toilet din dake cikin dakin , bayan wani lokaci tafito tace, humaira tashi kije kiyi wanka, tamike tacere kayan jikinta ta daura towel tashige toilet, anty amarya tabude akwatin humaira taciro wani yadi maikyau ta aje agefen gadon, tace da meena inta fito tasa wadan kayan, tajuya ta fita.
meena tana dan latsa wayarta saiga humaira tafito, bayan tagama shafan ne meena tadauki kayan ta bata tasaka, meena tace kai Anty kinga yadda kikai kyau kuwa. humaira tayi murmushi tace nagode. meena ce tasake cewa bari na tashi natafi karsu yaya su sameni. ta waigo ta kalli meena tace ina zaki kuma ba anan zamu kwana ba. a,a ba anan zan kwana ba amman gobe da sassafe zan shigo. tace wlh indai zaki tafi nima binki Zanyi. meena ce tamike tace to bari naje nadawo. to kiyi sauri karki dade.
meena nafita tayi dakin momy tagaya mata abinda humaira tace. momy tayi shiru tace gashi mijinta ba hankali gareshi ba bare yalallashe ta.suna cikin haka saiga faruk da abokan shi sun shigo nura ne agaba duk suka tsuguna furuk na gefe ya dukar da kai kasa nura ne yace momy munkawo miki ango ne kiyi mashi fada. tace nime zance mai aida gun hajiya kuka kaishi Allah dai yasa su zauna lfy kuma yaji tsoran Allah. daganan kuma sun kaishi hargun alhj shimdai fadan da yayi mishi kenan yaji tsoran Allah.

lokacin da suka shigo bacci yafara daukan humaira haniyar sune ya farkar da ita tadau gyalanta tarufa. sun shigo harciki suka zauna suta shakiyancin su , ita dai humaira ba fahimatan su takeyi ba ita bata masan waye mijin ba kuma badamu tasan shi ba. haka suka gama surutun su suka fita gaba dayan su. tana ganin sun fita tamike tayi daki momy, tatura kofar ta shiga bataga momy ba, sai meena dake bacci akan gado, danha tadau filo takwata akasa momy kuwa tana dakin alhj dan
yau itake da girki shikuwa faruk da yadawa daga raka abokan shi yarufe kofar falon su bekoma dakin humaira ba ya nufi dayan dakin yayi kwanci yarshi.

da subahi bayan alhj yatafi massala ci , momy ta nufi dakinta tatura kofar sai kawai taga yarinya kwace akasa tai salati ta sanar da uban gije ta matsa kusa da ita ta tashe ta, tashi kiyi sallah ta matsa ta tashi meena itama taji mamakin ganin humaira adakin. bayan alhaji yadawo daga sallah momy ta koma tagayawa alhj abinda ta gani.alhj yaji mamaki, yace turo min ita bayan tazo tagaida alhj yace matso nan ,yata taje kusa da shi ta zauna, yace faruk koroki yayine ? tace a,a nidaice nafito. yasan kinfito ? a,a ai lokacin sunfita . alhj ya girgiza kai yace ikon Allah kuruci dangin hauka
momy ce tace bari nakira shi . yace karki kirashi barni da shi kawai.
faruk ko tudda yadawo sallah yashige dakin shi yana sharar baccin shi saida gari ya waye yatashi yayi wanka yafito ko kallon dakin beyi ba yafice be nufi dakin momy ba falon alhj yanufa , yatar da alhj ya kishingida ya zauna yace abba ina kwana. fly lau yace dashi ya iyali .
faruk ya durkusar da kai yace lfy lau . ya baku fito tare ba jeka kirata . faruk yamike yafita, yayi sallama adakin yaji shiru yasa kai dakin bega Kowa ba, ya bude toilet bakowa , be tsora taba saida yaduba dakin momy beganta ba.
momy ce tace lfy kashigo bako sallama kana mana dube dube . yace yariryar nanne abba yana kiran ta. wace yarinya mu bamuga wata yariya ba anan. .yace momy kingane fa wadda nake nufi . bata da suna ne? ni sunan shige min yakeyi . to jeka bata shigoba .
faruk ya fara rudewa yarasa yazaiyi amma baiyarda da maganan momy ba, kasa koma yayi ya zauna afalo.
alhj yagaji da jiran faruk ya fito yasame shi afalo , kaikuma inajiran ka kazo ka zauna .
abba bangata bane adakin, kuma naje dakin momy tace wai fata shigo ba. alhj yace inataje to tun yaushe ne bata daki ? yayi shuru dakai fa nake magana, tun yashe rabonka da ita ? daddare ne ni ina daki basan sanda tafita ba.
ok irin rukun da zaka mata kenan gara da ka nunamin ban isa ba tunda da dai kai bakayi niya ba mu kuma bamu isaba to shikenan kayi duk abinda kaga dama kuma kaje duk inda take kanemo min ita. faruk yamike ya shiga dakin momy yace momy dan Allah kibar irin wannan, nasan tana wajenki karkisa Abba yayimin baki . nace maka ban gata ba, kawuce kabani waje. zabura yayi yanufi dayan dakin dake gefe , momy na fadin karka shiga min daki. ina ko sauraran ta beyi ba yana shiga ya ganta ita da meena zaune suna ta hira harda dariya yamika hannu ya kamata karo na farko da humaira ta fara sashi a idonta shima kuma haka dan haka da ya riketa itakuma ta rike meena tana kuka, ya daka mata tsawa ,saketa kukanta ne ya karu tana kira momy. yafara janta harya fito da ita yana rige da hannun ta momy ta tare hanyar tace saketa karfa kaji mata ciwo. be saurari taba saida yakaita gaban alhj ya saketa shikuma ya tsoguna yace abba dan Allah kayi hakuri ka yafemin kuma in Allah ya yarda haka bazata kara faruwa ba. yace to naji amman karka kara barita adaki ita daya daga yau .yace to nagode alhj yayi musu nasiha bayan ya kare faruk yamike yace mata tashi muje tamike suka fita, tana gaba yana baya kallonta yakeyi yariyar ba laifi yafada a zuciyar shi ga hannunta tunda yake betaba jin me taushin shiba suna shiga ban garen su yasake rike ta ke munafuka ce ko me aka miki kike kuka ya kama kuneta ya murde waye yace miki kifita, kinaso kihada ni da iyaye na ne ? tace a,a tana gargiza kai, dan kwalinta ya fadi , faruk naganin gashi yace yauwa yau zaki gane kuranki yasake kune ya kama gashin ya murde, saida tayi wujiga wujiga tafita haiyacin ta tukun ya saketa yace daga you karki kara fita daga dakin nan batare da kin gayamin ba
[6:34PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞

18 to 20

✍MMN YAZEED
Lokacin da furuk ya fahimci ta firgita da shi ,ya saketa ta tashige dakinta ta kwata tana ta kuka.
meena ce ta shigo dauke da abinci ta aje a falo, ta shiga dakin humaira tace ga abincin ku cen na aje a falo, tace anty humaira kuka kikeyi. humaira ta dago kai tace meena wlh yayan ku mugu ne.
meena takalli fuskar humaira data kunbura saboda kuka tace dukan ki yayi ? kinga yadda yake jamin gashi kamar zai kasheni ni wlh bazan iyaba zan kira abbana na fada mishi. meena ta rufe mata baki dan taji motsi a falo, tai kasa da murya tace mata karki gayawa abban ki, momy ya kamata ki gayawa wa xatamai fada zai bari, kiji.
kitashi kije kizoba mai abinci naji kamar ya fito.
nigaskiya bazanje ba meena tayi tayi da humaira ta fita tace bazata fita ba.
haka harta gaji da magana ta tashi ta tafi.
faruk ko yasaba dakin momy yake cin abinci gashi kuma yau anbiyu shi da shi. kuma masifar yunwa yakeji yarasa yarda zaiyi, hakadai ya daure , yace ke zo nan . afirge ce tafito ta manta ma kanta babu dankwali, tace gani. zuba min abinci . nanta tsoguna ta fara budewa. yace ahaka zaki ban abincin kanki ko dan kwali babu ke kazamiya ce wlh inhar naga gashi acikin abincin nan zaki gane kurenki.ta koma ta dauko dankwali tadaura sannan ta zuba mai . tamike takoma daki . yana cikin cin abincin aminu ya shigo shi da abdallah suka zauna suna ta hira da faruk abdalla ko dama yana shigowa ko gun faruk bejeba ya wuce dakin humaira , aminu ne ya gaji da jiran fitowan ta ya daga murya yace anty kifito mugaisa mana. tafito rike da hannun abdallah, hanun kujeran da aminu ke kai taje ta zauna ina wuni yaya yace lfy lau antymu. faruk ne ya dago ya kalleta yace waike baki da hakali ne zakizo kan mutun kizauna, da sauri ta sauka kasa ta zauna, aminu yayi ta jan ta da hira harta manta akwai faruk awajen sukaita hira suna dariya har abdallah ko kallon faruk basuyi ba shiko furuk hararar su yakeyi amma azuciyar shi cewa yake yarinyar nan dariya tana mata kyau . bayan aminu yayi musu sallama yatafi tamike tace zanje gun meena . yayi kamar bejita ba tagaji da magana takoma daki tayi tagumi .

hakadai zaman su yaci gaba da tafiya in dare yayi zaije dakin humaira ya kwana shi yana kujera ita tana gado inbanda tsangwama abinda yake shiga tsakanin su ,duk ta rame ta lalace dan haka aka maida ta makarantar da meena take zuwa drive ne yake kaisu ya kuma dauko so , humaira ta saki jikinta sosai ta saba da kowa agidan indai kaganta bata walwala to faruk na wajen ne har yan gidan suka fara ganewa da sungan shi saisu ce ga dodon humaira nan dan haka yafar dan sakar mata fuska agaban mutane anacikin haka tafiya ta kama faruk zuwa naija zaiyi wata uku bayan tafiyan shi humaira ta kara sakin jikinta duk inda meena tasa kafa sai tasa tata dakinta marufe shi tayi tadawo dakin momy ta tare, momy bata hana taba saima suje gidan inna su kwana buyu gidan yan uwa kuwa ba inda meena bata zaga da itaba humaira dai ta goge tayi kiba mulmul da ita faruk ya cika wata uku harda sati daya da tafiya suna waya da momy amman baitaba cewa aba humaira ba ko ya tambayi lfyr ta ba, meena da humaira suna zaune afalo meena tace tunda yau ba makaranta zo muje mutambayi momy sai muje gidan baba, to nima kafata kaikayi take. sun gayawa momy tace kuje amman karku dade, suka hau shiri yarda meena tayi shigar ta itama haka tayi baza ka taba cewa matar aure bace harma tafi meena haduwa, suka fito falo su hjy babba suna falon hjy tace sai ina kuma , gidan baba zamuje hjy tace amma dai humaira wannan gyalan yayi kadan . hjy beyi kadan ba nattare shine, to adawo lfy basu nemi drive ba suka wuce suka hau ta haya lokacin da suka shiga gidan nura da abokin shi suna zaune aharabar gidan suka karasa wajen suka gaida su suka wace ciki ,abokin nura ne yabi humaira da kallo ya nuna humaira yace nura wanan yariyar fa? kannai nane, eh nasan dayar ba meena bace kanwar faruk , dayar nake magana , kaifa kacika son matan to matar aure ce, nura wlh ba wasa nakeyi ba inasota wlh zan aure ta , nace maka matar aure ce matar wanin dan uwana ne , kai amman mijinta wawa ne wlh yana da mata haka yabar ta tana yawo ahaka, su kuwa su humaira tunda suka gaida mutan gidan suka dawa dakin bilkisu matar nura suta hirar ,suna cikin haka saiga nura ya shigo, yace ke shine kika biyewa meena kuna yawo, ke da meena fa kwai banbaci ke matar aure ce, yanzo da kika biwo ta wa kika tambaya ? wazan tambaya kuwa yaya banda momy, momy ce mijin ki, a,a mamata ce ni ai bani da miji, nura yayi dariya ba laifinki bane humaira to yanzu yaushe faruk zaidawo? ni bansani ba nama manta da wani faruk, lalai kinci ganye.
sai gurin mangariba suka baro gidan suna shiga Layin suka hango faruk da aminu zasu shiga masallaci faruk ne ya waigo ya kallesu yace da aminu dama su meena basa gida, eh suje gida baba baikara cewa komai suka shiga, itako mena tunda ta hango faruk ta rude tace mun shiga uku yaya yadawo, ni ina ruwa na da shi basai na koma dakin zaimin muguntan ba, suna shiga momy tace haka mukayi da ku ba nace muku karku dade ba, momy wlh wahalar mota ake , kun kyauta ke humaira je kishare dakin ki mijin ki ya dawo tayi kamar bata jiba ta shige daki, faruk ne ya dawo sallah dakin momy suka zauna har aminu dama abicin su na aje a gefe suka fara ci, ya waiga ga kalli su meena da suke cin abinci, yace ku baku ci abinci bane a inda kukaje gantalin, meena tace gidan baba fa muka je, ya daka mata tsawa ina magana kina mayar min, ya mike yayi fataili da abincin yaciro wayar redio ya fara tsula mata tana ihu aminu bece komai ba ,tayi waje da gudu tana kiran momy, faruk kuwa kan humaira ya koma ya fara tsola mata ta fasa kara da karfi yake dukan ta dan yafi jin haushin ta kuma ya tare hanyar bare ta gudu dan haka tayi bayan aminu ta rikeshi tam tana ihu shi ko faruk ganin inda ta rike aminu ranshi ya kara baci,
momy ce ta shigo aguje ,ta rike wayar tace sake .yaki saki jikin shi na rawa kamar mazari, dakai fa nake magana kasake min bulalar nace ko kasha kwaya ne. ya saki wayar yana huci, ita kuma humairar meta maka kake jifgarta kamar kasamo jaka, yawo taje kuma ai bai kamata adinga barin ta tana yawo a haka ba.
ubanta ne kai, kodan kana mijinta kuma sai kasa bulala ka zaneta ?
ai itama kanwa tace kamar yadda zan hukunta meena itama haka zan hukunta ta.
karya kakeyi ba kanwar ka bace matar ka ce karka sake fakewa da meena ka daketa akwai banbanci meena ta saba da bakin halinka ka tsaya kanta.
humaira ta sake alone tayi bayan momy tai kasa da murya tace kuma Allah ya isa.
faruk yayo kan momy gadan gadan kamar mahaukacin zaki yana fadi , ni kikewa Allah ya isa ni abokin wasanki ne, dan kinga ana daure miki gindi kina iskanci da kikaga dama wlh zanga wadda zai hanani dukanki yau.
momy na kokarin tare shi amma ina idon shi yariga ya rufe
[6:34PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURENKI 💞💞

21 to 23

✍MMN YAZEED

Da momy taga ya nufi gurisu gadan gadan yasa ta daga hannu ta wanka mishi mari.ya tsaya cak yarike gurin.
momy harda duka kuma. eh kadan ma ka gani watarana ma tabarya zansa maka, bakai kana ganin kafi karfin kowa ba to muzuba dani dakai karyan rashin kunya kake.
yadade tsaye ya dukar da kai yayi shiru sannan ya juya ya fita. aminu ne ya durkusa yana kwashe abincin da faruk ya zubar .momy tace aminu barshi jeka wajan iyalinka zan kwashe bayan tagama gyara wurin tashiga toilet ta hadawa humaira ruwan waka ta fito tace humaira jeki ki gasa jikinki, zaki iya kuwa dan naga jikin ya tashi da yawa? zan iya, bayan ta fito tadau wata riga mara nauyi ta saka nan da nan zazzabi ya rufeta duk jikinta shedan bulala ne rudu rudu, momy ta dauko magani ta bata tasha ta kwanta, bayan alhj ya dawo ne momy ta shiga ta same shi da hjy babba da anty amarya tafara gaya musu abinda ya faru, alhj yace wani irin duka, wlh alhj inda kasan yana dukan yar shi, alhj ya daga waya ya kira faruk, momy ce ta mike zata fita, alhj yace ina zaki kuma , zanje na kwanta ne danni ko ganin shi bana sonyi, hjy tace matsala ta dake baki iya fushi ba nan sukai ta mata nasiha, faruk ne ya shigo tare da sallama, momy na ganin shigowan shi ta fita , alhj ne yace me ya faro ne naji ance kadaki humaira? yayi shuro kanshi akasa, ina sauraron ka, abba ita da meena ne, yawo suka je sai dare suka dawo , alhj ya rufeshi da fada ta inda yake shiga batan yake fita ba, faruk yau yaga bacin rai agurin alhj wadda betaba gani ba, nan ya tsuguna yayi ta bashi hakuri, saida su hjy sukasa baki tukuna alhj yabar fadan, tashi ka fita kuma kaje kaba mahaifiyar ka hakuri, lokacin da faruk yaje ya tarar ta riga ta rufe kofa dan haka ya wuce ya kwanta amman bacci ya gagare shi ya shiga dogon tunani , yaya akayi na bari yariyar nan ta rainani yariyar da batafi sa,ar meena bace take min Allah ya isa, kuma an hanani na hukunta ta itakuma momy harda mari na agaban ta hmm tunani da yayi tayi kenan besan sanda bacci ya dauke shi ba, washegari faruk ko wanka beyi ba, yatafi dakin momy domin ya bata hakuri , yasa meta itada su meena suna hira momy na ganin shi ta daure fuska, humaira kuwa mikewa tayi ta shige ciki, ina kwana momy, tayi banza da shi yaga kamar bata jiba yasake gaida ta nanma yaji shiru , itama mina mikewa tayi tabi humaira, faruk yaji dadin fitan meena dan haka yazo gaban momy ya tsuguna, momy dan Allah kiyi hakuri naga kindau abin da zafi bazan kara ba, har yanzo bata tanka ba, yayi ta surutun shi tayi banza da shi, haka ya gaji ya mike ya koma daki, kanshi yaji yana juyawa, dakar ya daga waya ya kira nura, nura na dagawa yace mishi akwai matsala.Allah yaraba mu da ita, menene ya faru daga dawowan ka jiya? nura komai ma ya faru , kadai zo dan Allah. a,a nikam ba inda zani yau ranar hutu ce gida zan zauna in huta da iyali na. wai inace ma matsala kana cewa zaka huta dan Allah kayi sauri kazo, nura ya fahimci tashin hankali atare da muryar faruk dan haka cikin hanzari ya taho, saida yafara shiga ya gaida muta nan gidan sannan ya woce gurin faruk ya same shi kwance a falo akan kujera ya rike kai, baka da lfy ne? a,a lfy ta lau ya kwashe duk abinda ya faru ya gayawa nura, gaskiya tsakani da Allah faruk abinda kakeyi be taceba yariyar nan tunda tazo kake nuna mata kiyayya ni banga laifinta ba tun tanaji tsoronka ga shi har ta iya mayar maka da magana ina amfanin irin wannan.
ai wlh bawai nabarta bane zan kama ta saita gane kurenta akanta fa momy ta daga hannu ta mareni tunda nake da wayo na momy bata taba sa hannuta ajikina da sunan duka ba sai akan wannan wawuyar yariyar, kuma ita momy da take cewa ba kanwa ta bace wai matatace to da izinin wa ta fita, kaga ma shigar da tayi ne .
to lefin waye lefin ka ne , ka nuna mata auren nada daraja agurin ka, kai da kayi biyayya da yanzu in robo ne ma ansamu.
wanne irin rabo kuma wannan yar tatsiyar yariyar ya zatai da ni.
ikon Allah kai dai mutun bazai taba gane kanka ba, bakai kace karama kake so ba.
ai da nace karama bance sa,ar meena ba.
to

Please Login or Register in order to submit comment