Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

halarci , momy tafara share hawaye.
hadiza tace kiyi hakuri yaya ki kwatar da hankalin ki kibarmi ita anan takwana biyu. momy tace
gobe fa zai dawo , kuma kiga inyadawo bata gida bazaiji dadi , yanzon kawai abinda za ayi kizo muje ki rakani gurin kawarki Dr zainab.
hadiza tace to bari nakintsa , badan ran ta nasoba ta fito suka tafi.

bayan sunje wajen Dr zainab sun mata bayani amman ba suce mata matar aure bace, ta basu wasu kwayoyi , saida suka biya suka maida mama hadiza gida , sannan suka kama hanyar gida , itako humaira batama san meke damunta ba itada kawai taji jikinta ya canza, bayan sun koma gida momy tabata magani , ta karba ta sha.

humaira ko abinci bata nemaba takwata ta fara bacci, can cikin bacci taji marar ta naciwo, tabude ido , ta mike ta zauna . tun humaira na iya jurewa har ta kasa ta fara rike cikin tana kuka, can taji wani lema nabinta, momy ce ta shigo ganin jini tayi yana bin humaira, ta iso da sauri , toilet ta nufa da ita, zuwa ni lokaci jinin ya tsaya, bayan ta bata ruwa tagasa jikinta , tafito tayi wujuga wujuga duk ta rame , akan gado momy ta kwatar da ita, momy ta nemi guri ta zauna anya cikin nan ya fita kuwa , itadai bataga wani guda guda ba , jini ne dai yadan fita dan haka ta shiga zullumi


Washe gari da safe humara na tashi tace , momy kinsan yau me nake son ci?
a ,a saikin fada. wlh dan,wake nake so.
momy jitayi kamar ta mangare ta , tace to ai ina zaki same dan,wake? tace momy yau basai a yiba.
muba shi zamuyi ba inbaza kici abinda muka dafa ba saidai ki bari. humaira ta juyo ta kalli momy, taga momy ta juyar da kanta can gefe, meena ce ta shigo zata tafi makaranta, humaira tace meena dan Allah in an tashi ki biya gidan inna kece mata tabani dumamen tuwo.
momy ta dago cikin fada tace wa meena kar kisake ki biya ko ina ,da an tashi kiyo gida, wlh naji ance kin biya wani waje sai ranki ya baci.
humaira tace momy wai yau menayi miki ne,. ba abida kika min naga dai kincika kwadayi ne.
momy ba fa dagangan nakeyi ba. mikewa momy tayi tafita.

4:25 faruk ya shigo gida . yasame mutan gidan duk a falo humaira ce kawai bata gurin bayan sun gaisa suka dan taba hira, yayita jira yaga humaira ta fito amman shiru dan haka ya mike ya nufe bangaren su, aminu ya bishi da akwatin sa , yana shiga dakin humaira ya nufa, yaji shiru, da haka yafito da sauri dan yana zatan ko taji wani wajene , yana futowa ya tsaya afalo yace banga humaira ba. hjy tace munsiyar da ita. faruk yayi dariya yace da kuwa kunje kun karbota. itama dariya tayi , tace lallai baka da kunya tana daki ba lfy.
da sauri ya shiga dakin yasame ta kwance miyau ya cika bakin ta, ya isa gabanta ya tsuguna yabude ta daga rufan da tayi , yataba jikinta yaji zafi rau yace humaira me yake damun ki . bata bashi amsa ba dan bazata iya magana ba bakinta cike yake da miyau ya tai maka mata ta zubarda ta dawo, yace meyake damunki , tace nima basan abinda yake min ciyo ba nidai kawai bani da lfy. Faruk yayi shiru can yace kina cin abinci kuwa? humaira tace ai dana ci abinci amai nakeyi . yace baki jin kina son wani abu. eh tace da shi amman azuciyar ta sotake ta kwanta ajikin shi dan ayanzun babu abinda take so ila kamshin jikinsa batassni ba turare ne ,ita koma dai meye shi take so, amman bazata iya gayamai ba. shikuwa faruk laifin momy yake gani yaya zayi yarinya bata da lfy abarta agida ta rame haka, suna haka saiga momy ta shigo , yace momy shine humaira bata da lfy haka, ba a kaita asibiti ba. momy tace waye ya gaya maka ba akaita ba, sonawa muna zuwa, sauki ne sai ahankali, shawara ce taimata mugun kamu. yace a sibitin ne sukace muku haka? nidai nace naka sun bamu magani amman basuce ga abinda yake damunta ba faruk yayi shiru ya dokar da kanshi kasa ,can yadago yace to momy anyi mata test ne, da a keta bata magani. cikin fada momy tafara magana test din me za ayi mata, tashi kafita kabani waje.
Faruk yamike cikin zafin zuciya bari naje nasami Dr mansir din saina ci uban shi yaya zayi akawo mara lfy, ba ayi test ba yakama darka mata magani, yajuya yafita da sauri ,
[6:36PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURENKI💞💞

50 to 53

✍MMN YAZEED
07014197556

Momy ta ce da abdallah ya bi faruk da gudu ya kirashi, momy har yanzo bata fahimci komai ba ,ta fara tunanin ko dai faruk ya ganu humaira nada ciki ne yanzo ta ina zata bullo wa, al amarin ne, be jima da fita ba saiga shi ya dawo shi da nura , dakin momy suka shiga baya sun gaisa da nura , ya tambaye ta me jiki, tace da sauki, yasa ke cewa wani asibiti aka kai humaira ? tace au yaje ya dauko ka ne ku tsareni ? nura yace haba dai ai munyi kadan ,dama faruk ne yace, Dr mansir yace mai, ba gunshi aka kaita ba . tace eh banan mukaje ba kuzo kumin abinda za kumin. ta mike ta fita. faruk ya juya ya kalli humaira tana ta bacci . su kuwa kowa da abinda yake sakawa acikin zuciyar shi, suna haka abdallah yashigo da gudu yace , abba faruk alhj na kiran ku, faruk yace yanzun haka kila momy ce tace mun mata rashin kunya, na rasa abinda ya ruda momy wlh duk ta rikece ko inna da take tsohowa batai rike ce haka ba. lokacin da suka shiga falon cike yake da ahalin gidan, samira ce kawai babu. suna ko shiga alhj yafara fadin me yasa baku da kunya ne, mamar ku tana iya kokarin ta akan humaira amman ku kuna rainawa . faruk yace ba rainawa nayi ba, abba amma ai gara asan abinda yake damun ta.alhj yace kuma fa da gaskiyar shi, aisha akaita asibiti yan zun nan, momy tamike da sauri dan bata saba ma umarnin shi, nura ne yaja su , shikuwa faruk alhj yace ya dauki shi suje su gaida alhj usman da beda lfy ,faruk beso hakaba yaso atafi da shi asibitin.
bayan suje gidan alhaji usman sun fito , sai alhaji yace da faruk yawuce dasu asibitin suga me jiki. alhj da kansa ya kira momy yace kun gama ne? tace , ai gado ma aka bata. wane asibiti kukaji ta gaya mai sunnan asibitin alhj yaso akaita wadda suka saba zuwa amman , besan dalilin da yasa momy tayi haka ba .
lokacin da suka shiga dakin da aka kwantar da humaira suntarar da Dr zainab na kanta tana kara dubata, dan haka furuk ya matsa kusa da ita , yace yariyar nan kun gwada ta ne kunga meyake da munta ? Dr zainab tace yanzun dai za ayi mata test. maganin da kika bata da na meye ?Dr zainab ta rasa me zatace , ta juya ta kalli momy tace wannan wanene? momy tace rabo da shi kiyi harkar gaban ki. faruk najin haka hankali shi ya kara tashi idon shi jawur matsawa yayi yasha mata kwula yana fadin ke wacce irin mahaukaciya ce? baki da hankali ne wlh wlh inhar wane abu ya faru zaki gane kuranki,
Alhj dake gefe yafara dakawa faruk tsawa , momy ce ta lura faruk baji yakeba dan haka ta fara kaimai duka, sakinta yayi yana fadin wlh inhar ciki take da shi ya zube bazan yarda ba , sai nayi maganin ki , yafara kokarin komawa wajen Dr zainab, nura ya tareshi, momy ko tsayawa tayi tana kallon faruk tana son ta dada tabbatar da abinda taji faruk ya fada .
bayan Dr zainab ta gama gyara rigarta tace dama yariyar nan tanada miji, yanzun hjy aisha kin kwauta min kenan. momy tarike hunnun Dr zainab suka fita. Shikuwa alhj cigaba yayi da fadan da yake yi . basu dade da fitaba momy ta dawo jikinta asanyaye ta nemi guri ta zauna ta dukarda kai dan bataso ta hada ido da faruk dan ya bata kunya , ta fara ardua Allah yasa cikin be fita ba, bayan Dr zainab ta dauki humaira domin doba lfyr cikita dansu dama tuni sunsan tana dauke da cikin , bayan wani dan takai tattan lokaci tadawo da humaira tare da tabbatar musu tanada cikin dan sati hudu , ta matsa gaban furuk ta mika mai takardan ya karba yana mata godiya tayi murmushi tace fada ya kare , mun shirya ko, shima murmushin yayi tare da mikawa momy takardan. tace je karike abinka me zanyi da shi , munafuki kawai . juyawa yayi ya mikawa alhj ya karba ya duba yace to Allah ya rabata dashi lfy . momy takalli faruk ko zai amsa, amsawan kuwa yayi saida yayi kasa da murya yace ameen. momy na kallon shi cike da mamaki lallai tsakanin mata da miji sai Allah duk wanda ko yashiga yana tare da kunya dan haka ta yanke shawarar in zaitafi kafarshi kafar humaira tama gode ma Allah da ya tsayar da abin ahaka bayan faruk yatafi maida alhj gida nura ma ya musu sallama yatafi , ya rage saura momy kadai adakin . humaira ta fara kiran momy da sauri ta tashi ta isa gareta humaira me kike so ,ganin idonta tayi duk sun kunbura , tace au dama kuka kike? momy dan Allah a cire min cikin ni bazan iya haihuwa ba wlh . to ai saiki gayawa mijinki ni babu ruwana . kukanta ya tsananta momy tace dakin bari karki jama kanki wani ciwon

Da daddare faruk ya shigo shida meena ya samo momy naba humaira tuwo abaki taki tana kwauda kai. yace momy tunda bataso ki barta mana. banza tayi da shi. Yajawo kujera ya zauna abakin godon. bayan momy ta gama bata tabar wajen faruk ya riko hannunta yace yanzun inane yake miki ciwo? Ni babu inda yake min ciwo nidai kawai acire min ciki . yajuyo yace me kikace acire miki cikin saboda baki sonane ko kuma me kike nufi ?momy najin haka ta kira meena suka bar dakin . humaira tace da faruk ,ni dama nataba cemaka ina sonka ne. zuciya ta tasomai dan haka ya mike ya fita a fusace ya buga kofar, momy dake bakin kofar tace kai lfyr ka kuwa? lfy lau, na tafi . har zakatafi na dauka nan kwana. yace a,a kwanan humaira uku aka salameta ,aminu ne yazo daukan su humaira taji sauki saidai dan abinda ba arasaba, babu abinda take so yanzun ila tasa faruk a idonta. shi kuwa faruk tun ranar da humaira ta mai maganar zubda ciki be sake zuwa asibitin ba. Suna shiga gida dakin momy suka zauna , har yanma faruk be shigoba humaira ta gaji da jiran faruk tace meena yaya faruk ya koma ne ? meena tace yana nan a daki dazun nakai mai abinci. shiru humaira tayi saida meena tabar gurin ta kira abdallah tace je kace ma yaya faruk wai dan Allah ya karbo min dan wake gidan inna
[6:36PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURENKI💞💞

54 to 56

✍MMN YAZEED
07014197556

Faruk na zaune abdallah ya shigo ya bude mai hunnu ya fada ya rungume shi, yace yau bakazo ka gaida ni ba, abdallah ya bata rai yace momy nace ta hanani fitowa. Akan me zata hanaka fitowa? wai na cika yawo. faruk yace to shikenan shareta . abdallah yace anty tace wai ka karbo mata dan wake agidan inna. faruk da mamaki yace wai dama aiko ka akayi, wacce antyn ? Anty humaira . faruk yayi murmushi yace kace mata tazo da kanta. Abdallah ya juya ya futa. faruk kuwa mikewa yayi ya shiga toilet dan yadan watsa ruwa. lokacin da abdallah ya koma ya tarar da momy ta kawo ma humaira fate sai sha take, yaje kusa da ita yace wai yace kizo da kanki. momy ta waigo tace ke baki da zuciya tun ranar da aka kaiki asibiti bai kara zuwa ba ai ya kamata ki nunamai bacin ranki tunfa da muka shigu gidan nan yana daki amman be fitoba tunda yaga kinsamu ciki dole yamiki wulakan cin da yaga dama ba yaga kina sonsa ba. momy nifa ba sonsa nake ba, cewafa nayi yace mai ,ya amso min dan wake agurin inna. Ke kika sani . humaira ta fara kuka ta tura faten gefe. faruk ne ya shigo yasame ta tana kuka. yace itakuma wannan me aka mata take kuka, ko dan waken takema kuka. momy tace bashi bane, jeka abinka. ya kalli momy yace bawani guri zaniba dama nan nazo . banza tayi dashi , yaje daf da humira ya zauna yace bakison shan faten ne . girgiza Kai tayi yace to dauka kisha, ta dauka ta fara sha. dai dai lokacin momy ta fita yaji dadi fitan momy dan haka yacewa humaira me momy tace miki naga kina kuka. ba kome, yaya dan Allah ka kaini gida. Kash ke matsalan ki kenan baki bari ayi hirar arziki saiki dauko zance tafiya gida, yanzo bakiga kina da ciki bane kibari saikin haihu , saikije kiyi sati . tabdijan wlh baka isaba yaya za ayi kace saina haihu sannan kuma kace sati daya wlh bazan yarda ba saina gayawa momy ai kaine kamin alkawari. Karki gayawa momy wlh inkika gaya mata saikin gane kuranki. fashewa tayi da kuka .bazaki bar kukan ba sai momy tadawo tasameki haka. bazan bariba kayi duk abinda zaka yi ,mugu kawai. Inkika kara cemin mugu saina fasa miki baki , mara kunya kawai . mikewa tayi ta nufi fita sannan tace kaine dai mara kunya ta fita agoje dan ta zace zai biyo tane . karo sukaci da momy da tazo shigowa riketa tayi tam tana fadin kun fara muna funcin naku ko , tu kudai shiga hankalinku wlh ko kuma kutafi dakinku ai acan ba haka kukeyi ba, dakin nane wajan fada inkun shiga daki kuma lfy lau . faruk yace momy ba fada mukeyi ba ita kadai take rashin kunyarta ni ai nafi karfin nai fada da wannan kwailar saidai na zaneta ya mikewa zai fita . humaira ta matsa ta cikuikuye mai riga , momy tana kallon su tana girgiza kai. Yace momy kice mata tasakeni. momy tace ke humaira sake shi ku tafi dakin ku, kuyi acan. humaira ta fara kuka momy alkawari fa yayi min kuma yaki cikawa ni wlh bazan yarda ba . momy tace ashe baka da gaskiya shiyasa ka kwantar da kai, alkawarin me ka mata? karya takeyi ni bawani alkawari da mata. wlh momy da gaske ne . faruk yasake cewa ke karya kike saidai in mafarki kikayi.

momy tace a,a humaira ba karya takeba nafa san halinta, ke humaira alkawarin me yayi miki? humaira har yanzun rike take da faruk tace kwanaki da daddare yace min na hada kayana gobe da safe zaikaini katsina , shine yayi min wayau yaki kaini ,yace wai nabari yayi tafiya ya dawo, kuma yanzun namai magana yace wai saina haihu tana manar ta share hawaye.

Momy ta fahimci humaira wato faruk yawau yayiwa humaira ya rude ta da zaikaita gun iyayenta ya biya bukatar shi, humaira ta kara ba momy tausayi, shikuwa faruk kunyace ta rufeshi kokari yake humaira ta sakeshi ya fita kuma baya son ya fincike dan ba kwari gareta ba. momy tace ma humaira to naji sake shi . tace guduwa fah zaiyi. Ki sake shi unace duk ma inda yaje ai zai dawo. bhumaira tasake shi ya juya zaifita . momy tace dakata malam , yazun ya muke ciki ? name kuma. alkawarin da kamata ko kana nufi kaci bulus? Yace a,a tayi hakuri inta haihu zan kaita.
Momy tace wlh wlh baka isaba saika kaita inma kai bazaka ba to kaba aminu izzini ya kaita amman zancen kace saita haihu bata taso ba kai ko tausayi ta baka ji . faruk ya tsaya yayi shiru kashi akasa, sai share gumi yakeyi ranshi bace ya juya ya fita. humaira ko dadi taji, momy tace zo ki kareshe fatenki kodai dan waken kike so ayi miki? momy nifa na inna nake so. humaira rigima ke damunki innan tace miki dan waken zatayi . ai wata rana muna zuwa musamu tayi. to aikinji kice watarana ba lallai bane asamu.
shikuwa faruk gidan inna yanufa yana cikin tafiya yakira nura , nura nadawa yace yame jikin? Kai dai fari kawai yarinyar nan saita samin hawan jini yariya bata da sirri komai saita fada, ya kwashe yadda sukayi duk ya gawa nura ,dariya nura yayi sosai yace tamin daidai wlh . Yanzun momy ta dage waisai na kaita gida, kuma ni gaskiya saina gama cin angoncina zankaita. ai kawai ka bari inkundawo kwaci angwanci, kasan me nene cikin nanne yayi saurin tauna ka. Wlh kuwa itama yarinyar ce ana tabata sai ciki. ahaka kumadai kayi fada akan cikin. to dama nace maka bana sone, ba abinda bazan iyaba akan cikin, yanzuma gidan Inna zani na karbo mata dan wake. Nura ya kwashe da dariya yace Allah ya taimaka.

koda faruk ya isa gidan inna be samu abida yaje nema ba saidai tace gobe da rana yazo ya karba.
bayan kwana biyu faruk ya gaji da jiran momy ta turo mishi humaira yaji shiru gashi ya kusan tafiya , da haka yaje sami momy itada humaira da meena. zama yayi yanajira meena ta fita dan daya shigo take fita yauko yaga bata da alamar fita dan haka yace meena tashi ki fita da sauri tamike ta fita, tana fita yace momy humaira har yanzun bata ji sauki bane ? tace meka gani ? naga har yanzun bata dawo daki bane . ai bazata komaba sai kakaita gun iyayenta ta dawo inama saita haihun ne duk daya. haba dai momy karkiyi min haka mana , sai nai ta zama ni daya .
[6:36PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞


57 to 59

✍MMN YAZEED
07014197556


Momy tace dacen dawa kake zama. amman dai momy gaskiya haka be dace ba naji zan kaita amma a dan bari ta kara warware wa sai mutafi .

to ai naji babu matsala kaje inta warware saiku ta tafi. dan Allah momy.ki daina irin wannan , ke humaira kiyi hakuri zan kaiki kinji .
banza dashi tayi.
yace humaira baki jina ne , nace kiyi hakuri kinji. gumaira ko dagowa batayi ta kalleshi ba bare yasa ran zatayi mai magana.


A katsina kuwa babu irin gorin da hjy rabi batayi wa hjy fatima ba akancewa ta bada yarta anyi sadaka da ita gashi nan ganin ta ya gagara shekara daya da watanni ko leke , hakalin hjy fatima ya fara tashi dan itama azahiri tanason taga yarta dan haka tafara damun babanta da zance tanaso taga yar ta alhj yakance mata tayi hakuri tanan lafiya ,ai lfy ke boya

yau abun yakai makura hjy fatima zaune tayi tana ma alhj kuka. alhj yace fatima meye haka ne, saikace wata karamar yarinya, nagaya miki aisha tana gidan mijinta lfy meye na tada hankaliki, kuma ba kuna waya da itaba. cinkin kuka ta fara magana nifa ba muryarta nakeson jiba ganinta nake son nayi azahiri , nidai gaskiya na yanke shawara ni zanje na dubata har rashin lfy fa tayi. alhj yace a,a ba idda zaki, ni bana son rashin hankali, tashi ki bani waje, tunda yauzon bajin magana kikeba. azuciye ta tashi tafita alhj ya bita da kallo tunda yake da fatima bata taba mai musuba sai yau, abinda hjy fatima bata saniba shima kanshi ya kosa yaga yarshi dan duk cikin yayan shi yafi son humaira . Itako hjy fatima lokacin ta tafita same hjy rabi a falo da a lama ta saurare su dan tana ganinta ta kwashe da dariya harda shewa .

shikuwa faruk daya gaji da zama mikewa yayi ya fita harabar gidan yaje ya zauna zuciyar shi cike da haushi. shifa gaskiya yada bukatan matarsa yadawone cike da bukatan matarsa ya samu kuma batada lfy kuma taji sauki sai ahana shi matarsa gaskiya haka bazai yuwo ba, yana nan zaune sai ga meena da gaiyar yan makarantar su, maza da mata sunzo zasu shiga gidan, binsu yayi da kallo har suka shiga gidan , zuwa can yaga sun fito harda humaira tana baya itada wani daga cikin su sai dariya suke meena kuwa sunyi gaba ita da sauran , faruk mikewa yayi ya daka mata tsawa ke humaira koma gida. tace momy ce fa tace na raka su , tahowa yayi , Humaira naganin tahowan shi tayi ciki da gudu, su momy zaune afalo ta shigo tana haki, tunda momy taga haka tasan faruk ne, tace maza wuce wajen babanku yanan yau dai yaga abinda kukeyi, shigewa tayi da sauri, tashiga kenan faruk ya shigo yace ina humaira anty amarya ce tace tana gurin alhj , me tayi ne? bece komi ba ya nufe wajen alhj.
hjy tace kinga ko zuwa zaiyi , momy tace to ai ba kunya gareshi ba, wlh me sunan malam ba shida kunya ko kadan , nina rasa yadda ayi ya raina ni amman zanyi maganin shi, ya maidani saikace wata kakarsa, ina fadi magana yana bani amsa nan da nan. hjy babba tace bahaka zakiyi ba nu namai yamata kiyi inyayi ba daidai ba ki nuna masa, Kazan nan be taceba, kaza ya kamata kayi, saikiga a hankali yana gyarawa. momy tace ai inda nalura dashi inranshi ya baci kowane ne zaimai magana baji yake ba, shiyasa nacewa alhj ,ya bashi matarsa su tafi insunje gidan su bayi zasuyi ba, inma sunyi ,sagaji subari , amman alhj yace wai sai mai sunan malam yayi hankali, wannan dirke ken mutumin beyi hankaliba yanzu sai yaushe zaiyi.

alhj na zaune yaga humaira tashigo tana haki yace lfy ? tace abba yayane ya biyu ni. saiga faruk ya shigo .alhj yace waikai yaushe zakayi hakali ne, tayaya yarinya nada karamin ciki zaka rinka binta aguje, ashema karya kake da kake cewa inzumar maka da ciki baza ka yadda ba tun da gashi kai zaka zubar da kanka. shiru yayi ya naimi guri ya zauna ya kasa yin fadan da yakawo shi. Meta maka to da kake binta. Yace fita waje tayi. Shine ka biyo ta aguje , to Allah ya shiryeka. wayar alhj ce tayi kara dan haka yamike yace kujirani ina zuwa. Faruk yaji dadin fitanshi dan ya dade yana jiran dama irin wannan ta zomai, tashi yayi ya matsa kusa da humaira , tace wlh kataba ni saina maka ihu.
kiyi hakuri karki ihu ba abinda zan miki , ya tsuguna agaban ta ,
ya kama dukkan hunnuwan ta biyu ya sunbace su daya bayan daya , yace humaira meyasa kike beye wa momy, yanzo ke baki son komawa dakin ki. Kasa magana tayi domi tunda ya nufota , kamshin shi ya dake hancin ta batama fatan yabar wajan , dan haka ta rasa me zata cemai, saijin hannun shi tayi acikin rigarta yana kokarin taba marar ta, da sauri ta rike hannun tace yaya dan Allah ka bari, abba fa yana nan . yace karki damu abba bayan zun zaidawo ba, inason naji dumin baby mune , saida yagama shafa mararta sannan yayi sama da hannun shi ya fara futar da numfashi sama sama🙈 humaira kasa hana shi tayi saida taji yana kokarin zarcewa sannan ta tureshi tamike, tana kokarin gyara rigarta binta yayi ya riketa yace humaira kibari nadan tabaki mana ki tausa min ina cikin wani hali wlh.
[6:36PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞


60 to 62


✍MMN YAZEED
07014197556


Salaman alhj suka ji tare da gyaran murya, da sauri faruk ya sake humaira ya dawo inda ya tashi ya zauna, itama ma humaira dawowa tayi

Please Login or Register in order to submit comment