Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zauna dukkan su kai akasa dan sunsan alhj ya gansu , alhj yace kutashi kuje ka wai , nan suka mike sumi sumi suka fita.

Suna fita alhj ya daga waya ya kira momy , da sauri ta shigo tace gani alhj lfy ? yace nakira ki muyi shawara ne.

to inaji alhj .
Alhj yace dama cewa nayi faruk ko dai za,a nemar mai wata ne ya kara.
saboda me kace haka alhj.
gani nayi kamar yana takura mata da yawa. momy ta gano inda alhj ya nufa , amman ita tasan matalar dan haka tace alhj kabar maganar wani aure , baya wani takura mata ita dama bata dakin. alhj yace kina nufin bata kwana adakin ta,
garin yaya akai haka. to ai kaga bata da lfy , kuma fada ma sukeyi. dakata bana son maganar banza , tun yaushe humaira bata dakin ta.
Momy tace tun tafiyan da yayi bata koma ba.
alhj ya fara fada momy na bashi hakuri daga karshe yace tai maxa ta tura mai matar sa. momy tace to naji zan turata amman ina naiman alfarma daya aban nan da sati daya kafin ta koma kuma dan Allah karga gaya mai . alhj bece komai ba ya mike ya fita.

bayan kwana biyu , faruk ya kira humaira awaya yace tazo ta same shi adaki . Kashewa tayi ta gayawa momy .
tace inkinga zaki kije ni babu ruwa na. nifa ba zuwa zanyi ba, nadai gaya miki ne kawai .
inma zaki kije niban hanaki zuwa ba.
humaira bata kara maganar ba shima faruk be sake kiranta ba ,
saida daddare wajan 8:30 ya shigo yasha shadda taji aiki yana zuba kamshi ,
ya durkusa saitin kanta yace natafi wajen budurwa ta . ko kallon shi batayi, amma jitake kamar ta rikeshi ta hanashi fita.
shiko mike wa yayi , yace momy bari naje zance na dawo. momy ta Kallin humaira tayi, murmushi to ka gaida ta .ya juya ya fita da sauri . humaira ta kule haushi ya kamata momy na lura da ita , ta fara shere hawaye. momy yi tayi kamar bata gani ba,
ta juya ta fita , humaira kwanciya tayi ta fara kuka , dan yanzun haushin momy take ji,
me makon ta hana shi fita ,har tana ce mai ya gaishe ta. meena ce tashigo tana dariya, ta dafa humaira daker meena take magana saboda dariya, anty humaira menene kike kuka?
mikewa tayi tace meena wlh idan dai yaya faruk yayi aure wlh, bazan zauna ba,
meena ta da da kwashewa da dariya. au dariya ma kike min, mikewa tayi ta sauri ta ture mina ta dauki wayar ta.
abban ta takira yana dauka ta fara kuka , abba dan Allah kazo ka dauke ni.
cikin tashin hankali yace me yake faruwa? nidai dan Allah kazo ka dauke ni.
Yace to naji zanzo amma saikin gayami me ya faro? abba yaya faruk fa aure zaiyi.
tsaki yayi cikin fada yace to menene inzaiyi aure , dama wannan ne kike ma kuka,
karki kara karan banin kiran wani agida na akan wannan maganar kibarshi yayi auren shi yaga zai iyane, kashe wayar tayi taci gaba da kukanta ,meena taita rarrashin humaira tai shiro taki dan haka taje takira momy , momy tana shigowa taga humaira ido duk sun kumbura ,
tace meye haka kuma,
kina so me sunan malam yayi miki dariya ne ,
ga meena nan ma tana miki dariya. maza share hawayan ki,
jimin wawiyar yarinya ai yana dawowa ya ganki ahaka dadi zaiji tsokanan ki yake fa , duk kinbi kintada han kalinki tace momy bake kika bari ya tafi ba.
momy tayi dariya tace ashe nima nayi laifi , kuma in ance kina sonshi kice ba sonshi kike ba.
ni ba sonshi nake ba . to kwanta kiyi baccin ki ko yadawo karki bari yaga fuskar ki,
humaira kwanciya tayi amman babu bacci a idonta, faruk sai karfe 10:12 ya shigo dakin momy yace humaira ya jiki momy tace ai humaira ta dade da bacci. Yace momy wlh idonta biyu ba bacci takeba ya nufi gadon . momy tace kai wlh inbaka wuceba ranka zai baci.

Usaida faruk yajera kwana biyu yanama humaira haka, koda momy ta gaya mata tsokananta yake amma hankalin ta yaki kwanciya , ta tsani taji yace yatafi zance, yauma suna zaune sai gashi shi da nura yayi kwalliya sosai yayi sai dai yau kana nan kaya yasa . nura yace humaira jiki ? yayi sauki , nura yace nifa yau hira nazo, faruk yace wani irin hira kuma ,kazo mutafi kasan fa tana cen tana jirana.
nura yace jeka ni bazani ba .
mikewa yayi zai fita , humaira ta juya tadauko ragowar miyan da momy taci tuwo ta watsa mai
[6:36PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞


63 to 65

✍MMN YAZEED
07014197556


Faruk tsayawa yayi yana kallon kayanshi shi ko nura kwashewa yayi da dariya.

Yace amman gaskiya humaira ta iya tsiya, yanzon ai sai kaje tadin mugani .
humaira kuwa sai ka rantse da Allah ba ita ta aikata ba.
faruk yace kuna dai ganin abinda tayi min ko.
momy tace Kayi hakuri bata sani bane.
Wlh momy tana sane .
Kuma wlh ke zaki wanke,
fita yayi da zafin shi dan yaji haushi,
Koda dai yayi ne dan yaga yadda zata yi,
amman be zaci, zata mai haka ba.
Yaje ya cire kayan ya dawo ya watsa Mata.
mikewa tayi da sauri tace wlh bazan wanke ba.
baza ki wanke min ba ko?
eh bazan wanke ba, aini ba jakar ka bace.
Kaje ka kai ma budurwar ka ta wanke ma.
momy ma dariya tayi sosai, tace humaira zoki kwata rabu da shi dama abinda yake so kenan. humaira bayan momy ta kwanta zuciyar ta na tafarfasa .
shikuwa faruk juyawa yayi yace na tafi.
momy ta kirashi yadawo
tace gaski abin ya isheka haka kabari, idai ba so kake wani,abu ya faruba,kaga ba ita kadai bace , kabari kawai.
yace momy yanzon sabo da humaira nada ciki saina fasa neman aure.
na dai ce maka kabari ko? wlh zan hada ka da baban ka.
yace to na bari na hakura.
nura yace momy ya kamata asa ranar tafiyar humaira katsina.
ai ku muke jira.
nura ya juya yace ma faruk mai zai hana inza ka tafi jibi ka kai ta, saika wuce daka dawo sai ka biya ka dauko ta.
haba dai ahaka zata je arame, ai sai ace wahala take sha, ina humaira, sauko muyi magana,.
saukowa tayi ta zauna.
yace humaira kiyi hakuri kidan warware sai mutafi.
aini nariga na warke.
to kibari innatafi nadawo sai mutafi kiji wlh namiki alkawari, kin amince?
eh na mince amman sai ka gaya min idan kadawo da kwana nawa zamu tafi.
koda kwana biyu ne sai mu wuce , amman kiyi kiba kafin lokaci.
momy da nura suna jinsu .
momy tace nura mune sheda.
nura yace kwarai kuwa,mutun ya karya alkawari ya gani.

washigari momy da meena suna ta shirye shirye zuwa bikin yar kawar momy.
humaira tace momy nima zani.
tace humaira kisan me sunan malam ba zai bariba.
ai inkika ce zani bazai ce komai ba.
momy tace wa din ai da aminu ne, amman me sunan malam kiri kiri zaice a,a inkina son zuwa ki tambaye shi.
humaira ta kira shi taji wayar shi kashe, dan haka tacewa momy bari naje na tamba yoshi.

lokacin da tashiga yana dakin shi yana barci , taje ta fara buga kofar.
yace waye? nice
yace shigo mana.
yana kwance ya rufa da bargo.
ta zauna bakin gado, tace momy ce tace na tambaye ka zamu biki.
biki kuma keda baki da lfy.
nifa naji sauki.
yace to naji zaki, amman kizo kidan kwanta, na dan ji dume sanyi nake ji.
humaira batayi musuba domin tunda ta samu ciki babu abinda tafi kauna, illa taji ta kwance jikin faruk, kuma har yanzun bata same wannan damar ba, dan haka ta daga bargon ta shiga ciki ta kwanta.
shikuwa faruk tashi yayi yasa ma kofar key, ya shiga toilet yayi wanka ya fito, baya ya gama gyara jikinsa ya fesa turare ya haye gadon.
humaira ko tuda ta hau kan gadon faruk tafara shakar kamshin sa, bacci yayi awon gaba da ita.
dan haka sanda faruk yahau, yasamo tayi bacci , shiko ya hayo ne da shirin shi, sai dai rungume ta yayi tam a jikin sa, ji yake kamar ya hadiye ta .
humaira bata tashiba sai wajan 10:45 farka wanta ne ya ta she shi.
yace kin tashi, dama kina jin bacci zaki biki.
aini ma ban san inajin baccin ba, bari na tafi kar su tafi su barni.
kiyi zaman ki ,bayanzun zasu tafi ba, sai anjima, janta yayi ya kara matseta akirjin shi.
humaira lamo tayi a Jikin shi, ta tura hancinta cikin kirjin shi.
faruk yaji dadin yadda humaira tayi dan haka yafara dan wasannin shi da ita.
humaira ta fara kokarin yin gaddama ,amman faruk yabita ahakali cikin lallama da dabara ya biya bukatar shi da ita.
humaira har yanzun kwance take ajikin shi ,taki tashi.
shiko faruk yana son yaje ya tsarkake jikin shi, amman ya lura humaira taji dadin kwanciyar dan haka ya kasa tashin ta.
[6:36PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞


66 to 68

✍MMN YAZEED


Bacci ne ya debe su gaba dayan su sai kiran sallahn azahar ne ya farkar da faruk a hankali ya zame jikin shi, ya shiga toilet.

bayan wasu yan mintoci ya fito, ya tada humaira.

zabura tayi tana fadin waiyo momy na shiga uku.
ta fara lalibe hijab din da ta shigo da shi, bayan ta gama laliben ta bata gani ba, tace ina hijab di na?
yace kije kiyi wanka saiki dauko wani adakin ki.
a,a ni gsky tafiya zanyi tsoron nake ji.
ba wani tsoro , indai momy ce baza tace komi ba, nifa mijin kine, muje na tayaki.
tashi yayi ya rike mata hannu, yakaita toilet yaso yataya ta amma taki bari dan haka ya fito yaja mata kofar.
bayan ta fito ta gyara jikinta tafara tunanin fita ya zata yi ta hada ido da momy.
faruk ya lura humaira kunyar fita takeyi, dan haka yace muje na raka ki.

lokacin da suka fito gidan ba kowa, hjy babba taje gai da inna , itako anty amarya tare dasu momy suka tafi harda samira.

humaira naganin gidan ba kowa ta fara kuka, kaga ni suntafi sunbar ni ko, kuma kaine kajamin.
murmushi yayi yace to humaira meye abin kuka, nima ai zani daurin auren, yi sauri ki shirya kinga lokaci ya kusa, bari naje sallah na dawo.

cikin sauri ta hau shiri bayan ta gama shirya wa ta zauna tana jiran faruk ya shigo , sutafi.
ba a dade ba sai gashi ya shigo ya shirya tsaf .
yace to tashi mutafi.
mikewa tayi ya kalleta ya kashe murya yace Humaira gyalan nan beyi karami ba.
Itama cikin shagwaba tace beyi ba fa.
nidai gsky ki can za.
humaira bata yyi musuba ta dauko wani ta yafa suka kama hanya.

lokacin da suka isa kofar gidan sun tarar da mutane cike akofar gidan maza yan daurin aure .
har cikin gidan ya shigar da ita dan bata taba zuwa gidan ba.
suna shiga yaga meena zaune ita da wasu yan mata, ya kirata yace ta kaita wajan su momy, faruk har ya juya ya waigo yace meena karfa ki barta anan ki shiga da ita ciki, humaira ko kunyar haduwa da momy takeji dan ko meenar ma kuyarta takeji.
bata bari sun hada ido da meena ba, duk da cewa meenar tana ta janta da hira.
momy na zaune cikin kawayen ta taga meena da humaira suna shigowa.
momy ta sake fara,a ta fara miko ma humaira hannu. humaira bata kalli momy ba kanta akasa ta mika hannu ta, ta zaunar da ita kusa da ita.
takira hjya baturiya tace to ga sirikar ki.

da sauri ta taho ta daga kan humaira
tace tubar kallah Ina faruk din shiya kawoki ? Eh yana waje.
ai na dauka ya hanaki zuwa ne, ki saki jikin ki kiji ko, bari akawo miki abinci.

humaira na cikin cin abinci faruk ya shigo ,bayan ya gaida mutane dake dakin yace humaira inkingama kizo mutafi.
humaira batace komi ba, tana gamawa momy tace tace humaira tashi, kutafi yana can yana jiranki.
humaira kanta a kasa tace momy gidan fa ba kowa.
ba kowa .
me sunan malam din fa?
shiru tayi.
momy ta sake cewa tashi ku wuce, kinga shi gobe da safe zai wuce, gara ku rabu lfy ko.
mikewa tayi badan ranta ya so ba.
koda suka koma gida be barta ta koma dakin momy ba kamar yadda taso
Sai dare su momy suka dawo taji motsin su dan haka ta matsa mai sai ta je.
tare suka fito suka shiga dakin momy. momy tace yau dai humaira munbarki da yunwa, nasan dazun bawani cin abincin nan kikayi ba.
Momy naci sosai fa , bana jin yunwa.
ni bacci ma zanyi.
to tashi kije ki kwanta.
furuk ya gaji da jiran humaira ta tashi ,kuma gashi yau wani irin kunyar momy yake ji, dan haka ya fara zungurin ta abaya,
haka ya gaji ya tafi ya barta, duk da cewa itama Humaira tana son ta kasance da mijinta kunyar momy kawai takeji .
momy ko tana lure da su , tace Humaira tashi ki tafi.
momy ni anan zan kwana.
a,a tashi kawai ki tafi, ke ahaka ake auren.
mikewa tayi tace saida safe.

faruk yaji dadin zuwan humaira, dakin shi suka kwanta suna makale da juna.

Washe gari faruk na tashi ya fara shirye shiryen tafiya, humaira naganin
yafara shiryawa hankalin ta ya fara tashi.
tace yaya da gsk tafiya zakayi.
au da kin dauka wasa ne.
to yaushe zaka dawo.
sai kun ganni, keda baki damu dani ba.
Juyar da fuskar ta tayi, ta bata rai.
faruk ya juya ya kalleta, yace humaira me ya faru kuma?
shiro tayi bata kulashi ba, dan haka ya isa gareta ya dagata yasata ajikinsa
yace Humaira baki son na tafi ne, kina son na tsaya atare da ke ne?
tace ba haka bane, ka tafi , ta kara yin kasa da murya tace amman in ka tafi karka dade, kuma karkaje gun wata.
murmushi yayi yace humaira kenan, ashe kina sona amman ko kuyar momy baki ji ,kike ce mata baki son danta.
ai ba mamar ka bace, katon ka da kai.
yace to naji mamar waye?
mama ta ce.
dariya yayi sosai, yace ashe shi yasa kike mata shagwaba ita kuma take biye miki, to naji na bar miki, aman saidai in zaki barmin ummin katsina.
eh nabar maka.
yace to shikenan.
mikewa yayi yaci gaba da shir yawa, bayan ya gama ,yace to ni zan wuce.
mikewa tayi ta zauna a bakin gadon, ranta ajagule.
faruk yaje kusa da ita ya zauna, yace humaira karki damu, ni budurwata nan garin take ,ba acen ba ,
agidan malam take, kuma tunda baki so bazan kara zuwa ba, dama ni basonta nake ba itace ta manne min, sai da ya gama lallaba ta ya baro daki, tare da tabbartar ma kanshi humaira bataso ya tafi kawai dai bata son ya gane, ne.

dakin momy ya shiga bayan ya gaida ta yace nafito zan tafi.
tace baka fito da wuriba gashi har baban ku ya tafi aiki.
Wlh kuwa saida zankira shi a waya.
tsayawa yayi, yayi shiro, momy na kallon shi, can ya aje jakarshi yace Ina zuwa, momy nayi mantuwa.
to ,tace da shi ya juya ya fita.
yana shiga bangaren su ya fara jiwo kukan humaira, da sauri ya karasa dakin ,tana zaune akasa yaje gabanta ya tsuna.
koda da humaira ta ganshi bata fasa kukan ba.
yace Humaira kukan me kike yi, ba mun gama magana ba.
bata ce komai ba , ita dai sai share hawaye takeyi..
ya sake cewa ko za mutafi tare ne?
nan ma bata ce komi ba, haka ya gaji da magana ya tashi ya fito jikin shi a sanyaye idon shi sunyi ja.
dakin momy ya koma , tace yau dai ta fiyar taka ta rana ce.
durkusar da kai yayi, ya dan sosa keya yace momy wai bazan iya tafiya da humaira bane? tace zaka iya tafiya da ita mana, amman ai badai yauba ko?
wai da yau , momy kinga humaira fa kuka takeyi kuma nalura tafiyan nan ne bata so.
momy tace ikon Allah ita humaira take kuka zaka tafi, kiramin ita.
be jima da fita ba saiga shi da humaira, momy ta kalli humaira taga idonta duk sun kunbura, ta daga murya takira hjy , tace kuzo kutaya ni kallo wai humaira ke kuka mijinta zai tafi
[6:36PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURANKI 💞💞

69 to 71

✍FADEELA LAMIDO
MMN YAZEED


Anty amarya ce ta fara shigowa tace kukan lfy.
humaira ta tura kanta cikin kafafuwan ta.
hajiya ta tashigo tana fadi , sai dai in dukanta yayi, kallon faruk tayi taga idon shi jawur, au ashe abin da gsk ne , kaima kukan zakayi ne?
haba dai ni ba kuka zanyi ba.
momy tace shifa wai a haukan shi zai wuce da ita ne , yanzun.
hjy tace Allah nagode maka da ka nuna min wannan lokacin, ina son girman naka yake, duk ka mata cika nakin da kayi, ni wlh duk yarinyar da aka aura min saita gane kuranta, amman shine dan baka da kunya zaka ce wani zaka tafi da ita.

faruk yace dan Allah hjy ku daina irin wanan maganar, lokaci na tafiya fa .

momy ce ta jawo humaira tace humaira dgsk zaki bishi?
bata ce komi ba tayi kasa da kai tana share hawaye.
hjy tace kai in zaka tafi ka tafi, kaima kasan yazun bazaka tafi da itaba baban ku besan maganar ba .
faruk dagewa yayi sai ya tafi da ita.
dan haka hjy tace mai ya tafi inhar alhj ya yarda za,asa aminu ya kawo mai ita.
har ya juya zai fita yadawo yaje gabanta ya tsuguna.

momy mikewa tayi ta fita suko su hjy dama tuni sun fita.
yana tsuguna wa ya rikota yace humaira karki kara zubar da hawayen ki, ki kwantar da hankalin ki in aminu be kawoki gobeba jibi zandawo na dauki ki
gani yayi humaira bata da niyar magana ya tashi ya tafi.
su momy na zaune a falo yazo ya wuce su fuuu, daker ya bude baki yace na tafi.

Sukuwa su momy sun dai amsawa faruk ne dan ya tafi amman sunsan alhj bazai bari ya tafi da humaira ba.

humaira kuwa shiru tayi ta daina kukan, tayi tagumi tana tunanin koma wacece budurwar faruk agidan su malam sai tayi maganin ta, tana cikin tunanin momy ta shigo tayi murmushi tace humaira manya to zaki iya cin abinci kuwa yau?
ahan kali tace zan ci, bayan ankawo mata abinci tana cikin ci sai ga aminu ya shigo meena na binshi abaya , aminu ya kalli humaira , yace anty mu lfy kuwa.
tace lfy lau kaina ke ciwo.
momy kallon humaira tayi ta danyi murmushi , itadai abin nan yana bata mamaki wai humaira ce takewa tafiyar faruk kuka.
aminu yasake cewa yaya ya tafi ne ?
momy ce ta bashi amsa ya tafi itama humaira in alhj ya yarda gobe zaka kaita.
yace gobe kuma, me yasa basu tafi tare ba.
be fadawa baban ku zai tafi da itaba, kaga zai iya yin fada.
humaira tace momy nifa ba binshi zanyi ba , karki gayawa abba.
humaira ai dama bake kika fada ba mijin ki ya fada, kuma ai ba lefi bane ma dan kuntafi tare.
humaira ta fara rantse rantse ita ba binshi zatayi ba.

bayan alhaji yadawo an gaya mai sakon faruk , cewa yayi sam bazai yi wuba , in yaga zai matsu ya kara aure ,amman bazai bashi humaira da ciki yatafi da ita ba , yabari ta haihu .
su hjy suyi taba shi shawara ya barsu tunda duk su biyun suna san tafiya.
amman alhj be yarda ba.
ya kafa huja da cewa faruk be da hakuri ga saurin kai hannu , karta je tayi mai wani abu ya bigeta.

shiko faruk tunda yatafi yarasa sukuni dan haka yace bari ya kira abba yaji ko ya yarda.
alhj na zaune yaji kiran faruk , ya daga bayan sun gaisa faruk kasa magana yayi , alhj ya gane faruk ya kasa magana ne dan haka yace mai naji sakon ka , amman nace kayi hakuri inta haihu saiku tafi , inkuma kana ganin akwai matsala kanemi aure.
faruk shiru yayi bece komi ba, amman azuciyar shi gani ya keyi an takura shi.

humaira kuwa tun tana jin kewa mijin ta har tadan war ware saidai kulum suna waya, dan haka humaira tasake jikinta sosai.

akwana atashi ba wuya yauga shi faruk wajan watan shi biyu da tafiya amman yaki dawowa ,kulun tamai magana daga yace antura su wancen gari sai yace antura su wancen gari, gashi ita tana ta jiran shine yadawo ya kaita katsina, kulum insukai waya sai yace mata taci abinci mai yawa tayi kiba kafin yadawo dan daya dawo sai tafiya, dan haka tayi ta cin abinci, tako yi kibar cikinta kuma ya fara fitowa.

humaira tagaji da jiran faruk dan haka yanzun inya kirata tana dagawa saita fashe da kuka, dan haka ya rage kiranta.

humaira da meena suna zaune afalo suna hira saiga nura ya shigo .
yace au ashe da gangan kike mai kuka in ya kiraki dakin gama wayar kuma kici gaba da hirar ki, shi kuma ki daga mai hankali.
tace to bashi bane yaki dawowa.
ba asan ranshi bane humaira shima fa ya kosa ya dawo.
humaira tace yauwa dama inason na tambaye ka .
nura yace ina jinki.
tace dama budurwar yaya faruk a gidan malam take?
nura yasa dariya , meena tace duk ma wadda ya gaya miki karya yake gidan Inna ba wata budurwa.
tace ke yayane fa ya gayamin da kansa.
nura yace ke meena waye ya gaya miki babu budurwa, akwai budurwa agidan mana zarka dediya, ita faruk yake nema .
meena tace to shikenan ki tsaya su yita shigar da ke.
humaira tace wlh yaya nura sai naje har gidan nasame ta.
nura yayi dariya yace gaskiya da kin birge ni , ni inzaki ma zan rakaki , dama haushi take bani.
meena ko haushi yasata ta mike tashige dakin momy.
nura yaji dadin tashin meena, yace humaira dama ina son muyi wata magana dake .
tace ni kuma ?
yace eh, humaira nifa son meena nake, dan haka nayi kamun kafa dake, nataba yima faruk magana da dadewa yace wai zanja ta raina shi, nakasa hakura ne , ki taimake ni kishgar dani agun meena tunda naga kawar kice.
humaira ta gama kallo nura da mamaki a idonta tace anty bilkisu zakawa kishiya da meena.
to me nene Humaira?
mikewa tayi , yaya gsky meena bazata aure kaba, yaya za,ayi kama anty kishiya ai wlh bazai yuwo ba .
shigewa gefanta tayi tabar nura zaune afalo.


nura na zaune jikin shi asan yaye, yamike ya shiga dakin momy, ya gaisar da momy, meena tace yaya nura ka gama zura anty humairan ne?
nura yayi dariya yace faruk ne ya zurata bani ba.
meena tace momy wai yaya faruk ne yace mata yana da buduwa agidan malam.
momy tayi dariya tace me sunan malam bashi da kunya wlh inna fa yake nufi .

humaira ko tunda ta shiga daki tunanin take dole tadau mataki shiryawa zatayi taje gidan inna tame yariyar da faruk ya nema tayi maganin ta.

washe gare da safe faruk na taye ya gama shiryawa damin yau zai dawo gida kuma be gayawa kowa ba dan yana son yama humaira dirar bazata.
Itako humaira ta shirya tsaf dan tafiya gidan Inna bata tambayi faruk ba dan tasan kota tambaye shi ba bari zai yiba , sai dai tai tunanin bari ta Kira shi ta tambaye shi sunan yariyar, lokaci da ta takira shi yana mota yaci rabin tafiya yaji kiran humaira da sauri ya yadaga, bayan ta gaida shi tace yaya yasunan budurwar ka, ta gidan inna?
sai da yayi dariya sannan ya ce sunanta zee baby .
da sauri ta kashe wayar tafito.
dakin momy ta shiga tace momy zanje gidan inna .
wani irin gidan inna kuma kibari mijin ki ya dawo mana.
momy nafa tambaye shi yace naje.
ayho to saikin dawo tajuya ta tafi.

✍07014197556
[6:36PM, 11/6/2016] ‪+234 701 419 7556‬: 💞💞ZAKI GANE KURANKI💞💞


72 to 74

✍FADEELA LAMIDO
MMN YAZEED


Humaira ta isa gidan Inna tana ta haki saboda yanzun koya ta danyi tafiya sai taji haki na taso mata.

Inna tace ke kuma daga ina .
humaira tace Inna bakiyi murna ganina bane ?
ko kadan ni tausaya miki nakeyi, ga ciki gashi ke abu ba au ki ba. ,
inna kenan ina dan tsohon mijinki .
Inna tace ahaka kuma kuka manne mai.
Allah ya kiyaye

Please Login or Register in order to submit comment