Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Asrah makurace , sa hannu tayi ta shafa fuskarta tana "wowwww! Mark aina ka samu wannan zazzafar yarinyar?" Bayanin komai ya yi mata kamar yanda su black suka faɗa mishi kuma ya faɗa mata kancewa yar Bishara family ne tsohon gwamnan jihar Borno, sannan ya sanar da ita koda ta tashi bazata iya tuna komai na rayuwarta ba , duk abinda aka faɗa mata dashi zatayi amfani , boss lady bata tabajin dadin aiki da Mark ba irin yau domin wannan yarinya mudin ta girma tasan zata samu maƙudan kuɗaɗe da ita.
Karawa Mark kudi ta yi sannan ta sallame shi ya tafi, har lokacin tagagara dena kallon Asrah, da muryanta me kama da anbuga ganga ta kwala musu kira " Teema baby da Rash baby duk kuzo nan "tana gama rufe bakinta wasu yan mata suka shigo dagasu se pant da breziya ƙafafunsu na sanye da sarka.

Teema baby da Rash baby su kansu seda Asrah ta tafi da imaninsu ga kuma Asmita itama kyakkyawa da ita.

"Kunga wa'yannan yara guda biyun?so nake tauraronsu ya daukaku sosai a idon duniya, musamman wannan kyakkyawar.duk wani salon karuwanci da damfara,sata,salon duk wani makirci da kuma salon yaudara kuyi musu training na musamman ku koya musu rawa kuma ku kula dasu domin da kudi masu yawa na siyesu, so nake su taso da farin jini na daban acikin duk wasu karuwan dake gidan nan, Teema zoki tasheta har yanzu tana bacci"tashinta Teema ta yi , tashi Asrah ta yi ta zauna tana mutsutsuke idonta alamar baccin be ishe ta ba , turo bakinta ta yi gaba fara ƙarewa dakin kallo ta yi kafin tafara kallonsu ,kallon_kallo aka tsaya yi tsakanin ta dasu, tana kallonsu kamar idonta ze faɗo ƙasa so takeyi ta tuna aina tasansu amma tagagara tuna komai , shafa mata kumatu Teema ta yi" tace yanmata meye sunanki ?" Kallonta Asrah ta yi tanason tuna sunan nata amma ta gagara hakan yasa ta ce" bansaniba" murmushi boss lady ta yi ta ce"ɗakyau Teema samo suna me dadi ki saka matashi" nisawa sukayi kafin Rash baby ta ce" asa mata Sunaya ,yayi ?"girgiza kai boss lady ta yi alamar ko kadan sunan be mata dadi ba , ganin hakane Teema baby ta ce" to adinga kiranta da *SABRIYAH* sunan ya yi ko boss lady?" murmushi boss lady ta yi ta ce"sosaima kuwa ya yi dadi" kafin ta kalli Asrah da itade kawai da ido take binsu ta ce" daga yau sunanki shine *SABRIYAH* ,faɗa inji" gyada mata kai Asrah ta yi ta ce" daga yau sunana *SABRIYAH*" murmushi boss lady ta yi da su Teema, sannan ta maida kallonta kan Asmita da tazuba musu ido tana kallonsu , boss lady ta ce "ke kuma menene sunanki"a dan tsorace Asmita ta ce" sunana Asmita"
"Ku daukesu kuje dasu sashinku ku basu daki daya su biyu,ku musu wanka ku basu abinci zan turo da kayan su, sauran yaran kuma su ma za'a zo a kwashesu" cewar boss lady , riƙe hannun SABRIYAH Teema baby ta yi ita kuma Rash ta riƙe hannun Asmita suka nufi sashin su. Wanka suka musu sannan suka basu abinci me kyau suka faraci , tana cikin cin abincin ta shaƙe tafara tari kamar zata mutu dakyar ta iya furta"wayyo Tajujuna zan mutu" ruwa suka bata tasha Teema tana shafa bayanta seda ta gama tarin kafin , Teema ta ce"Sabriyah waye kuma Tajuju ?"shuru ta yi tanason tuna me sunan amma ta manta amma daga zaran ta rufe idonta kanta take gani da wani saurayi kyakkyawa suna zane dasauri ta bude idonta ta ce "nima bansan waye ba" abincin da bata karasa ci ba kenan ta tashi tahau gado ta kwanta, ficewa adakin sukayi dan su barsu su huta, kuka Asmita tafarayi tanajin tsanan mahaifinta na shiga cikin zuciyarta, jin kukanta ne yasa Sabriyah ta ɗago kai ta kalleta saukowa ta yi akan gadon ta zauna akusa da ita ta ce"meyasa kike kuka?" Kallonta Asmita ta yi ta ce"babana ne ya siyar dani awajensu yarabani da mamana" " to kidena kuka wata rana zakije gurinsu " gyada mata kai Asmita ta yi ta ce"kema ai siyar dake akayi"girgiza mata kai ta yi tace "to aini banida kowa, Tajuju kadai nake iya gani a idona"ta yi maganar cike da yarinta kamar zatayi kuka.sannan tana me rufe idanun nata sosai rayuwarta da Tajuddeen ya dinga mata flash a ido musamman lokacin da suke zane tana hango kanta tana zanen hoton Tajuddeen komai na rayuwarta dashi tana ganin shi afuskarta da kuma shi din bayanshi kuma bata ganin kowa a ahalinta .kallon abin hannunta ta yi ta kafeshi da ido tana kallo sannan ta yi murmushi ta ce" nasan wata rana zakazo gareni tajuju"

rike hannunta Asmita ta yi ta ce"to daga yanzu munzama kawaye sosai ko"Sabriyah ta ce"eh"."to Kinga basa nan kizo mu gudu kinji"Asmita ta yi maganar tana riko hannun Sabriyah ta fara janta saboda Asmita ta tsani wajan fitowa sukayi daga dakin basu haɗu da kowa ba lokacin har duhu ya fara yi.lungu_lungu suka fara bi domin guduwa har sun kai bakin gate se suka ga an rigada an datse kofar fita din ga shi sunyi nisa da inda suka baro ga garin hadari ne ya kankama sosai nan take iska yafara tashi aka fara yayyafi suna damƙe da hannun juna tsoro ya gama kamasu ganin yanda ruwa lokaci daya ya fara sauka kamar da bakin kwarya basu da wani option da ya wuce su koma.haka suke tafiya a yayinda ruwa ke yi musu mugun duka nan take jikin su ya soma rawan sanyi musamman ma Sabriyah hatta harshenta karkarwa yakeyi domin ita yar hutu ce bata saba da irin wannan rayuwar ba tafi sabawa da rayuwar ac da air conditioner.a hanyar su ta komawa sashin da suka baro suka mance daga ina suke suka dinga dabur_dabur ga ruwan na dukansu kuma har izuwa lokacin basu samu wajen fakewa ba zubewa akasa Asrah ta yi ga ruwa dake wucewa akasan kamar karamin kogi dungulewa ta yi waje daya tana kuka da iya karfinta har muryanta ya koma dishi_dishi Asmita zama ta yi kusa da ita itama suka hadu suna kuka har na kusan minti biyar kafin daga bisani ta ji Asrah ta yi shuru . matso da fuskanta dede da nata ta yi taga idonta arufe ga shi bata motsi dake yarinya ce se ta yi tunanin Sabriyah din
Teema baby da Rash ne suka shigo dakin nasu domin dubasu ko akwai abinda suke bukata bacci ta yi.haka suka kasance a wajen su biyunsu babu kowa.
amma da mamaki se suka ga babu su a dakin hakan yasa suka dauki lema da torchlight suka fito suna dudduba su har suka hangosu da sauri suka isa inda suke bakaramin tashi hankalinsu ya yi ba ganin halin da suke ciki ba ga Sabriyah dake sume a ƙasa cikin ruwa cikin rudewa Teema baby ta ce "Asmita meya fito da ku awannan ruwan?me ya sami Sabriyah?"ta jero mata maganar a yayinda ta sa hannu ta dauki Sabriyah din ta saɓata a kafardata, Asmita dake rawan sanyi kuwa bata samu damar bata amsa ba haka suka koma sashin su kwantar da Sabriyah Teema baby ta yi akan gado ta cire mata kaya da sauri haka Rash ma ta canzawa Asmita kaya har lokacin Sabriyah bata farfaɗo ba hakan yasa Teema baby ta dauki lema ta nufi bangaren boss lady domin sanar da ita halin da ake ciki.sosai ran boss lady ya ɓaci wato yaran so suke yi su gudu ta yi asarar kuɗinta kenan jinjina kai ta yi a ranta ta ce"zan yi maganinku" kafin ta daga waya ta kira wani doctor ta sanar dashi akwai mara lafiya in ruwa ya dauke yazo ya dubata kafin ta kashe wayar ta juya kan Teema baby ta ce "ku kuna ina lokacin da su ke kokarin guduwa?nace kuna ina ?ko ba cewa nayi ku kula dasu ba kuɗi da yawa nasa na siye su da ace kudi kaɗan ne ko mutuwa sukayi Ni bazan damu ba amma bazeyu inyi asarar wa'yannan yaran ba,amma dake ku din ballagazazzu ne ga shi kun barsu suna shirin guduwa to wlh duk sanda yaran nan suka sake kokarin guduwa Teema abinda zan aikata agareki se kinyi da nasanin rayuwarki.banza kawai ɓace mini da gani ko na dauke ki da mari wa'yanda basu san darajan kuɗi ba" sosai idanun Teema baby ya cicciko da ruwa ta bar sashen boss lady da sauri tana me tausayin rayuwarta da kuma sauran da suka tsinta kansu acikin wannan halin nan ne ta sake jin kaunar Sabriyah aranta sosai domin yaran tunda ta gansu dazun taji tana mugun tausayinsu kuma ta yi alkawarin zata kula dasu sosai.

Wannan kenan,bayan ruwa ya dauke likitan da boss lady ta kira yazo ya duba Sabriyah kuma ya gano ta kamo da (pneumonia) nimoniya hakan yasa ya rubuta mata magani sannan Asmita ma ya rubuta maganin mura sannan ya kara musu da kar a dinga barin Sabriyah tana mu'amala da ruwa sosai musamman ma me sanyi Sannan ya tafi abinshi.

Washe gari se karfe goma Sabriyah ta farka daga bacci Teema baby ne a dakin se Asmita ruwan wanka ta daura ta mata wanka da ruwan zafi ta haɗa mata shayi da biredi yanda Asmita ta karya.

Bayan ta gama ne tabata magani ta sha haka Teema baby ta dinga kulawa da Sabriyah hatta warware.
Bayan sati daya su Asmita, Sabriyah sun shaƙu sosai da Teema baby da Rash kamar da can sun san juna haka suka koma kiran su da anty Teema da anty Rash,dake sun samu masu ɗebe musu kewa har sun fara sabawa da wajan kuma har zuwa lokacin boss lady ba ta zo ba.

Yau ma suna zaune Sabriyah na gaban anty Teema tana yi mata kitso amma dake gashinta yanada tsantsin gaske se yaƙi kitsuwa haka ta gyara mata gashin,agefe daya kuwa anty Rash ne da Asmita suna kwance suna baccin rana akan katifa,basuyi tsammanin zuwan boss lady ba kawai ganinta sukayi akan su"ke Teema baby tashe min Rash da wancan yarinyar"tashi anty Teema ta yi taje ta tashi Anty Rash mikewa sukayi suna gaisheta ta amma sannan ta maida kallon ta kan Sabriyah da Asmita ta ce"wato naji kuna kokarin guduwa ko? warning nazo muku duk sanda kuka sake yunkurin gudu karnuka zan sa su biku su cije ku,su cinye naman ku har se kun mutu.kun ga wannan gidan duk wanda ya shigo gidan nan baya fita har abada sede ko in mutuwa ya yi,to nan gaba in kuka sake yunkurin guduwa mutuwa zakuyi kunde jini ina?."cike da tsoro sukace mata to sannan ta ce wa Anty Rash"kizo ina neman ki."

Bayan fitan su ne Anty Teema ta sake musu faɗa ta ce kar su sake kokarin guduwa.

Haka su Sabriyah da Asmita suka ci gaba da rayuwa a gidan karuwai tare da yaran da aka kawo su tare har an fara musu duk wasu training din da boss lady ta ce ayi musu salo kala _kala ana koya musu tun suna ganin abun wani iri har ya bi jikinsu.





Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.


Comment,like and share 🖋️🖋️
https://chat.whatsapp.com/DuXNzdLkDfm1U0dZg9YE73



🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹


Page 12


*_ story & written_*

By


*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)

*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*


~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*




🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️



Page 12


*This is just the beginning*

AFTER TEN YEARS OF LIFE (bayan shekaru goma na rayuwa)



Gidan rawan cike yake da mutane maza da mata ga manyan mutane masu zuwa daukan yanmata suje su kwana dasu,in banda filin da za'ayi rawan babu wani space aciki ko ina damke yake da mutane kowa so yakeyi yaganta yakuma ga rawanta na musamman da takeyi me daukan hankali,shisa duk karshen sati suke biyan kudi suzo su ga rawanta,kamar yadda aka saba yauma karshen sati ne ranar Lahadi kenan karfe 8 nadare, duk sun zauna ita kawai ake jira ta karaso.
Kunna wata wakar India akayi wanda nora fatehi tayishi me suna kusu_kusu.
Cike da yanga take tafiya jikinta se juyawa yakeyi kamar wata macijiya,tundaga tafin kafarta nafara ƙare mata kallo har sama.

Kalar fatarta fara ce irin farin nan mai kyau da tafiya da hankali babu mis ko ta ina fari sumul ga jikinta da se sheki yakeyi , doguwa ce amma ba can sosai ba matsagaiciya ,Siririya bata da jiki sede akwai shape sosai tana da hips ga kirjinta dake cike taf da tula_tulan dukiyar fulani suna atsaye se daukan ido suke ,cikinta a shamule yake sosai kamar wacce batacin abinci, komar da kallona nayi izuwa fuskanta, innalillahi wa'innailaihi rajuun tsarki ya tabbata ga Allah Ubangijin talikai, kyakkyawa ce ta ajin farko tana da ɗan dogon fuska me dauke da dogon hanci kamar anzana pencil,kumatunta kuwa na dauke da dimple aduka biyu bangaren, wanda ko murmushi tayi se sun lotsa balle ace ta yi dariya ko kuma ta yi magana,tana da manya_manyan idanu masu jan hankali cikin idon din nata na dauke da oiling eyeballs ga dogayen gashin idonta dasuke ajere reras kamar wacce tasaka eyelashes sunyi gazar_gazar, bakinta dan karamine sosai pink color yanayin suffan bakinta kamar heart aka zana mata,gaban goshinta na dauke da lallausan saje dake kwance luf_luf gashin kanta ya zubo tundaga kanta har izuwa kusa da kugunta yanada tsayi da kuma cika sosai ,duk inda za'a sako kyakkyawa tofa wannan ita ce zatazo a farko domin makura ce wajan kyau, jikinta na sanye da wasu tsinannun kaya wanda dasu da babu duk daya , irin kayan da nora fatehi tasaka a wakar kusu_kusu , irin kayan nan na yan rawa da India ko larabawa ke sawa , dogon skirt ne wanda ya kasance a rabe biyu gefe da gefe ga ya matseta sosai hips dinta sun fito kayan se daukan ido yakeyi yana walwali rigan skirt din kuma bashi da maraba da breziya sede yadan fi breziya girma kadan tula_tulanta duk suna waje kadan ne acikin rigar , tsayin rigar ko cibiya be kaiba se wasu chain ne da aka musu kwalliya dashi ,hannunta na dauke da abun hannu kalan kayanta baƙi se kuma wani abun hannun da ya kasance silver color me kyau da design din suna ajiki yazauna dass a hannun, yarinya ce yar shekara goma sha bakwai.

Tunda ta shiga cikin filin nan aka fara kururuwa ana kiran sunanta , rawa tafarayi tana lankwasa kugunta kamar babu ƙashi ajikinta , ga kuma kirjinta da take jujjuyawa kamar wata yar India haka take rawa duk wani bangare na jikin na juyawa kamar ba mutum ba ,haka ta dinga rawa baji ba gani cike da kwarewa tanayi tana tauna chew gum din dake bakinta su kuwa mutanen da suke wajan se ihu suke mata ana watsa mata kudi ana kiran sunanta"*SABRIYAH*!*SABRIYAH*!*SABRIYAH*".
Se karfe goma dede ta gama show din rawan. nan take akafara zafga mata tafi raf!raf!raf jama'ar gurin se yabonta sukeyi da kuma zuzuta kyawun da Allah yamata sukeyi,tana kokarin barin filin wani saurayi yazo yasameta"Sabriyah wani ne ya ce yana son magana dake"zuba mishi idanunta masu daukar hankali ta yi cike da tsiwa ta ce" cele kaje kace mishi bazanzo ba" "Sabriyah karki yi haka babban mutum ne kuma daga gani za'a samu kuɗaɗe a hannunshi ki biyoni kawai idan be miki ba sekiyi tafiyarki"ganin inbatayi yanda yaceba ze bata ma ta lokaci kuma akwai wanda tabari yana jiranta sunyi dashi akan zasu hadu.
Bin bayanshi ta yi suka kutsa cikin mutane ko ajikinta,abakin wata mayyar motar kirar corolla s black color ya tsaya , juyawa ya yi yabarta atsaye awajen ,yar tsaki ta yi kadan kafin ta kwankwasa glass window din budewa ya yi hamshaqin attajirin me kudi ne zaune acikin motar murmushi ya yi mata ya ce "shigo mana hot girl" batare da ta bashi amsar tambayar da ya mata ba ta rankwafo ajikin motar kirjinta da fuskanta na ta cikin motar tana tauna cingum ta ce" ya! Lafiya ka sa akirani?"murmushi kawai ya yi dan ya lura yarinyar akwai zafin kai da tsiwa hade da rashin kunya ya kwantar da kai ya ce "ni baƙo ne a garin nan na kama hotel zan kwana biyu kafin in tafi !to sede bana iya kwana batare da na ji ni akusa da mace ba , shisa nakeso muje ki tayani kwana ko nawa kikeso zan sallame ki dashi"dariyar renin hankali ta yi ta ce"sede kuma kayi rashin Sa'a akwai wanda nayiwa alkawari zamu kwana , ga shawara akwai wasu matan anan kaduba su kawai se anjuma"ta faɗa tana juyawa ta tafi bin bayanta ya yi da kallo yanda shape din kugunta yake juyawa nan ne yaji ranshi ya sake biyawa da ita harta ɓule mishi sannan yaja motarshi.


Duk inda ta wuce setaga mace da na miji sunata alfasha ko kuma mace da mace ko kallonsu ba tayi ba ta ci gaba da tafiyarta hankali kwance har takai bakin kofar da zata shiga ta hango rabin ranta na tsaye jikinta da wata yalolon riga yar karama, hannunta rike da kwalban piscup tana sha kadan_kadan rai abace Sabriyah ta nufeta , tana isowa wajan tasa hannu ta fisge kwalban totoline din a hannunta tayi wurgi dashi, ɗago kai Asmita ta yi ta kalli Sabriyah ta dan sosa gashinta ta ce" kiyi hakuri my Tom bazan sa ke shan wani abu ba"watsa mata harara Sabriyah ta yi ta ja hannunta sukayi kofar da tazo zata shiga ta ganta , tana mata masifa"wlh my Jerry zan fara ja miki Allah ya isa in kika sake bari naganki da kayan maye,ke bakisan illar shi bane . kinaso ki mayar da shaye_shaye abin ado awajanki to zamu samu matsala ta kan haka"murguda mata baki Asmita ta yi"nifa karki takuramin maganar illa kam ai rayuwata yadade da samun illa tun lokacin da ubana ya siyar dani akan dubu dari bakwai,ga shi yanzu na zama karuwa karfi da yaji , kidena min yawan wannan fadan naki banijin dadi.so nakeyi in tara kudi sosai ta yanda wata rana in na hadu da mahaifina zan wasa masa su afuska kuma in dauki mahaifiyata in siya mata gida da duk wani kayan more rayuwa"dakatawa da da jan hannunta da takeyi Sabriyah ta yi suka tsaya kallon fuskan Asmita tayi taga kuka takeyi hakan yasa ta rungumeta tana faɗin"ki godewa Allah ke kin ma san iyayen ki nifa bansan kowa ba bana tuna komai na yarintata kawai mutum daya nake iya tunawa Tajujuna shi kadai nake iya zana hotonshi kuma in inya tuna fuskarshi, yanzu mu bar wannan maganar zo ki rakani akwai wanda ya ce zan tayashi kwana yana ciki" goge hawayenta Asmita ta yi ta yi dariya jin abinda Sabriyah tafada wai akwai wanda zasu taya kwana.

Cikin dakin su ka shiga suka sameshi yana kwance daga shi se gajeren wando ya zubawa kofa ido da alamu ita yake jira.suna shigowa ya mike ya zauna yana murmushi , kallon tumbin shi Sabriyah ta yi tana yamutsa fuska" yan mata kindawo kenan ai tundazun ke nake jira zo mufara,nakosa in farajin dadinki" matsowa kusa dashi Sabriyah tayi ta ce "gaskiya ni bazan kwana dakai ba"dasauri ya ce"haba hot girl karki min haka wallahi ke kadai nake da bukata ko nawa zan baki ko 30mint muyi"girgiza kai ta yi "ni kudinka be dameni ba kawai de saboda wannan abun naka ne yasa bazan yarda kayi komai dani ba maganar gaskiya kenan"ta yi maganar tana tuttura baki Asmita dake gefe kam babu abinda takeyi da ya wuce aikin dariya dama wallahi tasan za'a rina kadan daga iya shegen Sabriyah kenan, ƙare wa kanshi kallo ya yi yana neman abinda take magana akai ,"hot girl saboda me kike magana akai ?"da kyawawan hannunta ta nuna mishi tumbinsa ,ɓata rai ya yi ya ce"ke banason iskanci saboda tumbina ne zakice bazaki yarda ba? ke da kike karuwa har sekin zabi da wanda za ki yi mu'amala?"gyara tsayuwarta tayi ajikin bangon dakin tana girgiza kai kamar wata me jin waƙa ta ce"eh naji ni karuwace ka faɗa da karfi ka ƙara da ihu kuma karuwar ma me lasisi, amma bazan bar me shegen tumbi kamar wanda ya haɗiyi tukunyan giya ya kwanta ajikina ba atoo kaje ka rage wannan cikin naka wasu insun ganka ma zasuyi tunanin cikin wata tara ne dakai"tunda yake ba'a taɓa ci mishi fuska da mutunci ba irin yau ba a harzuke ya kai hannu ze cakumeta ta gauce ta bude kofa ta fice a ɗari Asmita dake dariyar mugunta itama tabita abaya suna gudu suna dariya hade da tafawa "wallahi my Tom bakida kirki bawan Allah ya gama saka rai zaku kwana shine zakici mishi mutunci"far_far da idonta ta yi ta ce"to ai ina zan tsaya ma wannan katon mutumin" "to inya kai ƙaran ki gurin boss lady fah?"kwashe gashinta ta yi ta dauresu da daya daga cikin abun hannunta ga kayan jikinta ma sun fara takura mata "oho ina ruwana seta san yanda zatayi dashi"haka suka koma sashinsu suna tafe suna hira.suna shiga suka hangi anty Teema na zaune ga kwalin sigari agabanta da laita sede bata kunna ba alama ta tafi duniyar tunani ne domin ko shigowar su ma ba ta ji ba.
Zama sukayi Asmita ta ce"anty Teema mun dawo"se a lokacin ne ta fahimci cewa su Asmita su shigo girgiza kai ta yi murya a sanyaye ta ce"dama yanzu nakeson zuwa in kira ku na ji ku shuru kuma nasan in kunyi wasa bakwa daɗe wa" Sabriyah de tunda suka shigo ba ta ce komai ba se nazartan antyn sun takeyi"anty Teema dan Allah meyake damunki ne gaba daya kin canza ba kamar yanda muka sanki ba tun bayan mutuwar anty Rash gaba daya kin koma wata kala Wallahi ni gaskiya banajin dadin ganin ki ahaka"murmushin takaici anty Teema ta yi ta ce"ku haryanzu yarane amma abun da kullum nake faɗa muku shine karku yarda boss lady ta turaku wajan da za'a kwanta da ku domin daga za ran kun shiga wannan harka na karuwanci da take saka yara Wallahi rayuwarku ya lalace kamar yanda nawa rayuwar ya lalace nasan kusan abinda ya kashe Rash ciwon ƙanjamau ne ya yi ajalinta nima kuma ina dauke da wannan cutar.kullum cikin nadaman wannan rayuwar nake ina so inga iyayena bansan ko suna raye ko sun mutu ba, guduwa nayi daga gida saboda za'a min auren dole ashe a hannun boss lady zan faɗa na bijirewa iyayena nazo na shiga duniya.inde da raina da numfashina bazan taba barin boss lady ta mayar da ku karuwai ba yanda take buri duk da ta yi rabin hakan duk wanda ze ganku se ya kira ku da Wannan suna na karuwa se de ko in ba'a garin nan ba.rawa,damfara,shaye_shaye domin Asmita ke naga kin fara mayar da kanki yar shaye_shaye to dan Allah ki raba kanki da kayan maye domin ni nasan illar su.duk kun rigada kun faɗa wannan harkan yanzu jira takeyi nan da kwana biyar akwai manya_manyan masu kuɗi da zasu zo diban wa'yanda zasu kwana da su daga nan ne kuma zata fara safaran ku"tabe baki Sabriyah ta yi ko ajikinta ta ce"nifa anty Teema haryanzu ban ma ga na mijin da zan iya bashi jikina ba sede ko boss lady kasheni zatayi amma Wallahi bazeyu tasani inje wajan wani banza ba, wasar rawar da nakeyi ma kadai ya isheni shi dinma dan kawai innayi inajin nishadi ne amma badan haka ba babu abinda ze sani inyi yawwa"duk zuba mata ido kawai suka yi saboda sun san halin Sabriyah sarai akwai taurin kai bana wasa ba in ta faɗa magana tofa ko me ze faru ba zanjawa takeyi ba in ma zata canza se ankai ruwa

Please Login or Register in order to submit comment