Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

be sa'ke ko da tari ba,su ma kuma basu sa'ke yunkurin sa'ke yi masa wata tambayar ba.
"Rameesa bakuwar na part din ku ne?" "Eh anty amarya tana can"Rameesa ta bata amsa tana kai soyayyen kwai bakinta.
Anty amarya ta ce"to mu gama,muje in ganta".





Kamar yanda na faɗa de yawan comments dinku yawan read more din da zan yi muku,infact ma in bakwayin comment Wallahi hutu zan tafi in yaso in kun shirya yin comments din se muci gaba amma bazeyu ina muku posting ace wai comment ya gagara ba.


Comment,like and share 🖋️🖋️

🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹


Page 18


*_ story & written_*

By


*_MRS 🌹 ISHAM 🌹_*
(Yar lelen Jarumai)

*The writer of ✍️*
*NIDA PATIENT DINA*


~And now~
*🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*




🔔 📚*JARUMAI WRITERS ASSOCIATION* 📚🖋️


Page 18


zaune take a cikin dakin, fatime ta shigo hannunta da tray din abincim da ta shirya, harda mini flask din tea.
"Barka da safiya ga breakfast din ki" "yawwa", ficewa ta yi bayan ta ajiye mata.
Bude kulolun ta yi taga sinasir ne da miya yasha kayan hadi ga nama acikin kamar zasu yi magana,dayan kulan kuma farfesun kifi ne a ciki,daukan plate ta yi ta zuba ta fara ci.bayan ta gama,ta haɗa tea ganin arhan madara da milo yasa se da tea din nata ya koma kamar wani kunu tana sha ta rube ido,ji ta yi koshi har wuya sannan ta kwashe plate da cup din ta sa acikin tray. ɗaukar tray ta ajiye akan mirror ta dawo ta zauna.
Shigowa dakin anty amarya da Rameesa sukayi, ɗago kai Sabriyah ta yi suka haɗa ido,a tare sukaji zuciyoyinsu ya buga kamar an buga ganga.mikewe Sabriyah ta yi,har lokacin idonsu na cikin na juna,wani irin alaƙa ta jini ne yake fisgan anty amarya harta isowa ga Sabriyah da take kallonta kamar wata bakuwar halitta daga wata duniyar,sa hannu ta yi ta shafa fuskar Sabriyah da ta zuba mata manyan idanunta, lokaci daya anty amarya ta kusan burkicewa jikinta yana bata akwai wani babban alaƙar jini a tsakaninta da yarinyar amma ta rasa wani irin alaƙa ce wannan,kuma har wannan lokacin zuciyoyinsu be dena bugawar da yake yi da karfi ba.

Da kyar anty amarya ta tattara nutsuwarta waje guda,under her breath ta ce,"ya sunanki?"
Muryar Sabriyah na rawa ta amsa mata,"Sabriyah"
"Ke din yar wata gari ce!?kuma sannan meye abinda ya kawo ki gidan nan!?"
"Ni yar Lagos ce a afafa,kuma wani mugu ne, ya kawo ni gidan nan, ga shi an sace mini yar uwata'.
Iska anty amarya ta furzar daga bakinta me zafi ta ce"Allah ya bayyana ta,bari in je se anjuma".

Rameesa suman tsaye ta yi a wajen ganin yanda anty amarya da Sabriyah suke tsananin kama,amma se wanda ya zuba musu ido sosai ze fahimci hakan,duk da tunaninta be kawo mata kan cewar akwai wata alaƙa ba,amma ta yi matukar mamakin yanda suke kama fiye da tunanin me tunani.

Da sauri anty amarya ta juya ta fice daga dakin ta nufi part dinta,bin bayanta Rameesa ta yi.ba ta cimmata s hanya ba.daki anty amarya ta faɗa, zubewa akan gado ta yi, numfashinta na fita dakyar,jawo maganinta ta yi tasha,nan ne taji nutsuwa ya fara shigar ta, cikin tsantsan damuwa ta shiga magana"ƴata Asrah kina ina ne?,ganin wannan yarinyar da nayi de naji tamkar kece a gabana,jikina yana bani kina raye.ya Allah na rokeka da sunanka tsarkaka ka bayyana mini ƴata cikin aminci".kwararo addu'o i sosai ta shiga yi.

Jiki a sanyaye Sabriyah ta zauna a bakin gado tanajin wani irin kadaicin da tunda take bata taɓa jinsa ba, fashewa ta yi da kuka me cin rai da ta rasa dalilin wannan kukan da takeyi, haɗe kanta da guiwa ta yi tana kuka me sauti haɗe da shesheka, zuciyarta ce ta tambayeta.
"To kukan me kike yi haka?"
Ɗago kanta Sabriyah ta yi,a fili ta furta "Nima bansan kukan me nakeyi ba"
"To ai ba'a kuka dole seda dalili"
"Kila kewar Asmita ne ya dameni"

Ita kadai ta dinga magana da zuciyarta,in ta yi maganar ta gaji kuma seta saka kuka,nan take idanunta ya yi ja.
Durkusawa ta yi a ƙa san tiles din, ta zauna ta ci-gaba da kukan.
A wannan halin major Marry ta sameta, cikin hanzari ta iso wajan ta tsuguna tana tambayarta abinda ya sameta cikin harshen turanci.
"Beautiful girl!why are you crying like this!?,did someone said something bad to you!?".

Ko daya daga cikin kalmomin da major Marry ta faɗa Sabriyah bata gane ba, ɓalle ta bata amsa goge fuskarta ta yi,ba ta cewa major Marry komai ba,tunda de ba gane maganar juna zasu yi ba.

Ganin Sabriyah ta ƙi kulatane yasa ta ce"okay dear sorry for bothering you, LTG wants to talk to you! let's go".

Major Marry ta yi maganar tana ɗago Sabriyah.
Rike hannunta ta yi suka fice a part din.
Su parsa suna zaune a cikin falo,suka ga fitowar major Marry rike da hannun Sabriyah, Umaisha ce ta fara magana "Sabriyah in zo in raka ku ne!?".

Kallonta Sabriyah ta yi fuska ba yabo ba fallasa ta ce"ah ah ba se kinzo ba".

Dariya sukayi banda Zoya da ko kallonta batayi ba, hasalima haushi ta ji da taga yanda Umaisha suke janta da zolaya.
Parsa ne ta miƙe ta bisu a baya ta ce"nide Wallahi sena biku". kallonta kawai Sabriyah ta yi taga tana mata murmushi, itama murmushin ta mayar mata.
Sannan suka fice garden suka nufa tun daga nesa suka hango LTG zaune akan kujerun da suke cikin garden din yana sanye da army trouser se rigar t-shirt me budeden gaba, sojoji kuma na zagaye dashi ta ko ina,ga wasu maza guda biyu da aka musu daurin huhun goro da igiya zaune akasa.
Karasowa wajan sukayi major Marry ta jawa Sabriyah kujera ta zauna.

"Ya Taj ashe kana nan dazun muka ta neman ka bamu ganka ba"ta yi maganar tana shagwabe fuska.

Wayarsa yake dannawa cikin kwanciyar hankali tunda suka iso wajen be ko daga kai ba.

With his sexy voice ya ce"yeap am here do you need anything?"
Cikin jin dadi Parsa ta ce "yes!Muna son muje mu siya ice cream, chocolate and some yogurt".
Yanda take lissafin ne ya bawa major Marry dariya...ita de Sabriyah da ido kawai take binsu.

"Give her the ATM"cewar LTG,fito da ATM da suka kusa takwas major Marry ta yi ta mikawa Parsa guda daya.

Tsalle ta yi tana"thank you sweet bro".da gudu tabar garden din,dan taje ta bawa su Umaisha labari.yau ai tunda ATM ya shiga hannunsu se abinda hali ya yi.



Ajiye wayar hannunsa ya yi,ya ɗan kalli wa'yannan mazan da suke daure da igiya, "kun san wannan!?"ya faɗa yana nuna musu Sabriyah da ido,a galabaice daya daga cikinsu ya ce "ah ah Wallahi bamu santa ba".

Gyada kai ya yi "ke kin san su?"harara ta watsu musu ta ce "Ni ban san su ba."

"Shikenan!amma shi ogansu ai kin sanshi tunda har kukayi kwanaki goma a hotel,yanzu ina so ki sanar dani aina zan sameshi!?"tunda ta ji ya ambaci tayi kwanaki goma a Hotel da wani ta gane magana yake yi akan Fu'ad.

baƙi ta buɗe da niyar zata yi magana ta ji ana mata rada a kunne,kuma ba muryar kowa bane, fa ce na Fu'ad"my Sabriyah dan Allah karki nuna musu kan cewa kin san ni,nemana suke yi,ruwa a jallo,saboda su kasheni,babu abinda na musu kawai zalunci ne irin na soja.ki taimaki rayuwata dan Allah Sabriyah"
Shuru ne ya biyo baya hankalinta ya yi gaba wajen sauraran abinda Fu'ad yake ce mata,a dayan bangaren kuwa tana mamakin taya hakan ya kasance amma wannan ba shi bane damuwarta,abinda yafi damunta jin wai nemansa suke yi su kasheshi,hakan ne ya tayar mata da hankali, tambayar kanta takeyi,shin menene abinda Fu'ad ya musu,bawan Allah da Babu ruwansa,kamilin mutum me kyautatawa mutane.
Wannan dalilin ne yasa tasa aranta ko da kasheta zasu yi ba zasu taɓa jin wani abu dangane da Fu'ad a bakinta ba.

Ganin ta yi shuru ta faɗa duniyar tunani ne yasa LTG ya da ki table din gabansun da karfi,har seda ta firgita tana kokarin mikewa.

"Zauna"
Ya yi maganar fuskarsa kamar hadari.
"Inajinki"
Cikin inda_inda ta soma magana"ni ban san akan waye kake wa'yannan maganganun ba,ka kyaleni in je in nemo yar uwata'".ta karisa maganar idonta na ciki da hawaye.
LTG dama yasan za'a rina saboda shugaban kungiyar Italian Mafia ba karamin shu'umin mutum bane zeyi fiye da haka ma.yasan ko shekara daya zasu yi yana tambayarta game da shi bazata taɓa faɗa masa komai akan sa ba,kamar yadda shugaban Italian Mafia ya yi blackmailing din ta shima dole ne ya yi blackmailing dinta saboda ta wannan hanyar ne kawai ze samu ta yi magana, saboda shugaban Italian Mafia yana kokarin juya mata tunaninta ne da karfin sihirinsa..

Kallon major Marry ya yi ya mata alamar da ta komar da ita ciki.

"Okay"

marairace fuska Sabriyah ta yi "dan Allah ka taimakeni ka mayar dani inda ka dauko ni,sun sace mini yar uwata' akan wani abun da baya wajen ta yana wajena,sun saceta bansan a wani hali take ba".tana magana hawaye na zubowa daga idanunta.

maida kallonsa kanta yayi,jin abinda ta faɗa. yana me son gasgatar da hasashen da ya keyi game da abinda Sabriyah ta ke magana yana wajenta,fatan shi ɗaya shine Allah yasa wannan ma'adanar memory card din ne a wajenta.

"Akan me kike magana meye a wajen naki!?"ya faɗa yana tsare ta da mayun idanunsa,ka war da kanta gefe tayi saboda bazata iya kallon cikin kwayar idanunsa ba,ji ta keyi kamar akwai guba me zautar da mutum acikin idanun nasa.wannan dalilin yasa ko da yaushe take avoiding din haɗa ido dashi.

"Am......amm......dama wani Barrister Lameer ne ya bawa Asmita ma'adanar memory kan cewa ko ta wani hali mu tabbatar da mun miƙa wannan abun wajen hukuma,ita kuma ta bani.shine suka kashe Barrister Lameer din,suka biyo mu har gida aka sace Asmita".

Zuba mata ido kawai ya yi,yana sauraranta,lumshe kyawawan idonsa ya yi ganin ya samo abinda suke nema har gida,domin lokacin da suka jefo da Barrister Lameer kan titi yayi dede da i sowarsu wajan nan suka fara ɓarin wuta har suka samu suka kashe wasun su wasu kuma suka kama su,anan ne Barrister Lameer ya sanar dashi kan cewa ya bawa wasu yan mata ajiyar memory din.kiran ambulance sukayi aka dauki Barrister Lameer zuwa asibiti domin a bashi taimakon gaggawa.

Ashe wa'yanda yake nema tana tare dasu.

Idonsa a lumshe kamar me bacci ya furta, "bani memory card din!"
Mikewa Sabriyah ta yi, "ban yarda dakai ba,babu dalilin da zesa in baka wannan memory ko da kuwa kasheni zakayi"tana gama maganar ta fara tafiya,zata bar garden din.cizan libs din sa na kasa ya yi,ya ce "in dan kika bani,nikuma na yi miki alkawarin nemo miki yar uwarki a duk duniyar da take".

Cak ta dakata da tafiyar da takeyi jin ya ambaci ze nemo mata Asmita,da sauri ta juyo ta dawo inda yake zaune ta ce "ni kuma muddin ka nemo mini ita zan baka wannan memory card din".tana ga fadin hakan ta sa kanta ta wuce cikin gidan,ta barsa zaune a wajen murmushi ya yi.
kawai yana binta ne cikin ruwan sanyi ta ba shi,amma in ya gadama a yanzu ze ƙarbi memory a wajanta,domin duk wani motsin mutanen gidan nan yana sane dashi,amma ze barta ya ga iya gudun ruwanta.
"Find the other girl,and kill this bastards"abinda ya ce kenan sannan ya mike,a tare sojojin dake wajen suka sara mishi.barin garden din ya yi wasu daga cikin sojojin suka bi bayan sa.


Kallon wani soja major Marry ta yi, ta ce "Khalifa! hand me the gun"miko mata bindiga ya yi,.nan take tsoro ya dira akan fuskokin wa'yanda za'a kashen suka fara neman afuwa.

Ko ajikinta ta seta kansu ta ɗa na kunamar bindigar sannan ta sake shi akan goshin na farko nan take ya fadi awajen matacce,haka dayan ma ta harbeshi a goshi.

Bindigar da ta yi amfani dashi,bayi da ƙara hakan yasa mutanen gidan basu ji kar'ar ba, ficewa ta yi itama taname basu umarnin su kwashe gawan nasu a wajen.

Birkita dakin ta yi kamar wata mahaukaciya tana neman breziyar ta,amma bata gani ba hakan ya daga mata hankali sosai,wanda yasa ta fara zargin ko wani ya shigo ya dauke ne musamman inta tuna da yanda sukayi da LTG,leƙawa kasan gado ta yi nan ta gansa yashe awajen. ashe da ta fito daga wanka ne ta yi wurgi dashi kan gado se ya faɗa bayan gadon.

Da hanzari ta shige kasar gadon kamar wata bera,daukowa ta yi ya,ta na kokarin fitowa ta ji muryoyinsu a dakin suna "to ina kuma taje?"

Fitowa ta yi hannunta riƙe da breziyar nata ta gansu dan tsuke fuska ta yi,bata ce musu komai ba.

Kallonta sukayi suna mamakin ita kuma me yasa ta shiga ƙasan gado.Rameesa ta ce"Sabriyah me kikeyi a kasan gado kuma".
Ajiyar zuciya ta yi "breziya ta na dauko" "okay!dama zamuje shan ice cream ne mukace bari muzo muce ki shirya muje".

Yatsina fuska ta yi ta ce"ku je kawai bazan samu zuwa ba".

"Sabriyah kin ka sa sakin jikin ki damu,kingan mu nan ko kadan bamu da matsala Please ki saki jiki,mu zama Kamar yan uwa"Umaisha ta gama magana tana riƙe hannun Sabriyah, kamar zatayi kuka ta ce"kaina ciwo ya ke,bazan iya fita ba"
"Ayyah sorry my dear Allah ya ƙara sauki bari inje part din ya Saghar in dubo miki medicine"Iklas ta faɗa tana fita daga dakin dan zuwa part din Saghar dubo mata maganin.
Zama sukayi tare da ita suna dan magana sama_sama,ba su san hakan damun Sabriyah yake yi ba,bazasu taɓa gane halin da take ciki ba ,gani take su basu da wata matsalar komai din su yana tafiya dede a rayuwarsu,amma ita daga lokacin da tasan kanta ta fara gwagwarmayar rayuwa komai sede ta yiwa kanta,da Asmita harta rawan da takeyi tana yine dan su dinga samun abinda zasu ci,da kuma abinda zasu sawa jikinsu, lokacin da Anty Teema ta fara jinyan cutar ƙanjamau nan ne nauyin ya sake ninkuwa mata, maganin Anty Teema duk yana kanta,haka take damfaran maza domin ta biya musu bukatunsu na yau da kullum,domin Asmita rawa kawai take yi wani lokacin ma bayi takeyi ba,saboda bataso .sede Sabriyah ta wakilce ta.
Musamman Asmita da take da babban ciwo a rayuwarta wanda inde bata cika wannan buri nata ba na watsawa Mamman kudin da kullum shine maganarta, har ya zamana wannan shine mafarkin da in ta kwanta barci se ta yisa,ga kuma shaye_shaye da take son mayar dashi jiki a wajenta.
Gaba daya bata san jin dadi ba daga wannan se wannan ga shi ita kanta ba isheshen lafiya ne da ita ba,ciwon nimoniya dinta in ya tashi kamar zata mutu.
Tagumi ta yi kawai ta zuba musu ido bawai dan tana fahimtar su ba, ankara da ita Rameesa ta yi "yan mata ya da tagumi".
"Hmmm!bazaku gane bane,babu bukatar sanar da ku". Sabriyah ta bata amsa tana cire tagumin.
"Sede in ba ki faɗa mana ba amma zamu gane..."cewar Iklas da ta shigo hannunta riƙe da sudrex da kuma glass of water.
Karba Sabriyah ta yi badan taso ba tasha ta kwanta ta juya musu baya kamar bacci zatayi saboda tana so su dan ba ta guri,ga breziyar a hannunta taki ajiye wa.
"To iyayen shegen surutu let's leave her alone to rest"cewar umaisha,gyada kai suka yi sannan suka fice.

Se da ta tabbatar da sun fice sannan ta mike ta garkame kofar da key ta dawo ta zauna tana buɗe zip din breziyar nata,sannan ta fito da memory card din ,ganin yana nan ne yasa ta sauke ajiyar zuciya tana "yauwwa,yana nan".mayar dashi cikin breziyar, ta wurga breziyar kasan gadon domin gani take yi se yafi samun tsaro a wajen.kwanciya ta yi tana jin ranta duk babu dad'i,mutane uku ne suka tsaya mata arai da bata san halin da suke ciki ba,mutum na farko farin cikin ranta wato Asmita na biyu kuma anty Teema,mutum na uku kuwa shine Fu'ad tana son sanin yana ina kuma meyasa wa'yannan mutane suke farautar rayuwarsa.aranta ta ce"Allah sarki Fu'ad kai din mutumin kirki ne Allah ya tsare ka da sharrin wannan mugun".

Haka ta dinga saka da warwara tana kwance,har bacci barawo ya yi awon gaba da ita.



Duk wani abinda takeyi,yana zaune ya yi relex a cikin dakin binciken dake cikin part dinsa yana kallon ta yana shan coffee cikin kasaita, murmushi ne ya subuce akan kyawawan libs din shi.ganin in da ta wurga breziyar na ta, kwantar da kansa akan kujerar da yake zaune ya fara juyawa dashi ahankali_hankali.
wato shi wannan yarinyar zata gwadawa wayo,shi da ya dauki tsawon shekaru goma yana karatun bincike da kuma karantar mutane da sauran abubuwa shine zata gwada masa tana da wayo.shafa lallausar sumar kanshi da ke da yawa ya yi,sumar ne ya shige cikin ɗan karamin ɓulin dake cikin abin hannunsa,da dabara ya shiresa, ya dawo da hannun fuskarsa yana kallon abin hannun nasa,kasa janye idanunsa yai akan abin hannun,ya daura hannun akan kirjinsa yana lumshe sexy golding eyes dinsa yana jin wani nutsuwa na shigarsa ta ko ina.
A lokacin da yake USA ko da yaushe cikin binciken Asrah yake ba ji ba gani ta dalilin nan ne ma yasa ya gagara dawuwa Nigeria,seda binciken nan ya dawo hannunsa ya dawo.
Amma a yan kwanakin nan yana mamakin kansa da ya dena neman inda Asrah take ,domin yana jin kusancinsa tare da ita,ji yake yi kamar yana a tare da ita,tunda ya shigo Nigeria yakejin wani kwanciyar hankali da nutsuwa.
Ajiyar zuciya ya yi wanda ya fito da sunanta"Asrahhhhh...".
Tunaninta ya fara lokacin da take yar karama da ita,wani wurin in ya tuna ya ɗan girgiza kai wani wurin kuma ya ɗan sa'ki yar karamar murmushi.
"My little stubborn girl!am feeling your presence in everywhere".
Yana gama faɗar haka ya mike cike da jarumta ya fice daga dakin binciken ya koma bedroom dinsa,ko minti biyar be kai da zama ba kira ya shigo cikin wayarsa be yi picking ba,seda wani kiran ya sa'ke shigowa, mika daguwar kyakkyawar hannunsa kan filo ya ɗauki wayar.
se da ya kusa katsewa kafin ya daga yasa a handsfree"assalamualaikum! Tajuddeen fatan kuna lafiya!?".
"Alhamdulillah! Abbu ya aiki?"
A bangaren Abbu dake kusa da Abbie shima wayar a handsfree yake,"Alhamdulillah mun gama duk wani abinda yakaimu, we're expecting to be back within next week in sha Allah".
"That's good,ina Abbie my regards to him, tell him I missed his jokes and ......"kasa karasa maganar ya yi sakamakon jin bakinsa ya gaji da maganar saboda ta yi tsayi sosai bayan haka kuma yau ya yi magana me ɗan yawa....
Daga can bangaren su jin ya carke yasa suka fahimci cewa ya gagara karasawa ne,saboda da gajiyar da ya yi.
Abbie ne ya karbi wayar"Son don't stress your self!you need to rest,inna dawo zan koya maka doguwar magana okay?".
"Uhmmmm"kawai LTG ya ce sannan ya hanging phone din.


"Kaga wani ikon Allah ko Isma'il!?,yanzu har Tajuddeen ne ze iya wannan maganar lallai nasha mamaki'.cewar Abbie,yana faɗawa Abbu.
"In sha Allah addu'ar mu na tare dashi babu wani mugun mutum ko aljani da zeyi nasara wajen ruguza rayuwarsa, ba ma shi kadai ba duka yaran namu".
"In sha Allahu!da yardar Ubangiji", Abbie ya yi maganar yana kiran number Ammi.

Ammi dake zaune akan gadon ta tana gyaran farcenta ne taga kiran Abbie ya shigo da sauri ta daga tana murmushi.
"Sarauniyata fatan kina cikin koshin lafiya!?". dariya Ammi ta yi tana jin farin ciki na mamaye ta har cikin ranta, duk da yanzu sun manyanta amma hakan be hana Abbie kiranta da sunaye masu dad'i ba sede in suna gaban ƴaƴansu ne.
"Lafiya klau alhmdllh,ya aiki ya abbu duk kuna lafiya?".gaisawa sukayi da juna kafin ta bashi labarin yarinyar da LTG ya ɗauko,shima Abbie ya yi mamaki duk da,basu san meye dalilin sa ba, amma yana addu'ar Allah yasa alkairi ne.
Sosai suka sha hira kafin ya sanar da ita sun kusa dawuwa.a haka sukayi sallama.



"Hajiya khareema!ina so ki faɗa mini meye kike nufi dani tunda burukan ki suka fara cika,kika yasar dani agefe wato amfani na ya ƙare ko!?,na gama miki amfani shine za ki cire ni daga lamarin ki.bari kiji in faɗa miki Wallahi muddin kikayi tunanin yi mini butulci tofa zan tona mana asiri kowa ma yasan abinda ya faru tunda kince ke butulu ce"cike da ɓacin rai ummah ta ke faɗawa Ammuh maganganu,ita kuma zaune take tana kallon ta hankalinta kwance.
"Am sorry Hajiya hurairah,bawai na cireki a kan wannan shirin bane,ko dan saboda kin gama mini amfani, ah ah!na ɗan janye jiki dake ne saboda na lura Abida tafara zargin akwai wani abu tsakaninmu ko kuma muna da wani manufa.to wannan ne yasa nafara nunawa kamar bama shiri sosai, amma ke kin sani,kinsan yanda nakeji dake,kece ginshikin wannan aikin namu.kiyi hakuri kin ji?".se a sannan ne ta ji hankalinta ya kwanta,yanda Ammuh ta cireta a plans din ne yasa ta fara shirya yanda zata tona musu a siri.
"Se yanzu naji hankalina ya kwanta, yanzu aina muka kwana".
"Ko kefa Hajiya Huraira abinda nakeson ji kenan,yanzu shirina na gaba shine dawo da Tajuddeen karkashin ikona,zan haɗa shi aure da yar autarmu,Naziya, Wannan shine shirin gaba".
Murmushi ummah ta yi"kina ganin Naziya zata iya janyo hankalin Tajuddeen!?".wani shegen murmushi Ammuh ta yi"Naziya is a very innocent and kindhearted girl,da ita zanyi amfani ".
Suna tsaka da tattaunawa Tajuddeen ya shigo part din,shuru sukayi suna tunanin kode ya ji tattaunawar da suke yi,tsayawa ya yi a kusa da Ammuh"Ammuh! i need fryed egg"
"To ɗana bari in soya maka"ta faɗa tana mikewa ta nufi kitchen ummah kuma ta fice daga part din.



Zaune take a kan kujerar karfe, an haɗe hannunta da ƙafafunta an daure a jikin kujerar ga bakinta manne da gam,gashin kanta duk ya hautsine kallo ɗaya zaka mata kasan cewa bata cikin hayyacinta musamman yanda idanunta suka gagara tsayawa guri daya bata iya rufesu haka kuma bata iya buɗesu.
Cikin wani ɗan karamin daki madaidaici babu komai acikin dakin se kayan karafuna,ko fulasta babu acikin daki ɓalle kuma fenti.
Wasu ƙartan maza ne masu ji da karfi suka shigo dakin kallonta sukayi suka ga haryanzu bata dawo hayyacinta ba.
"Yarinyar nan fah ta ƙi faɗan inda ta ajiye memory nan,dole mu sa'ke shaƙa mata cocaine din nan ko zata yi magana".
Cikin takaici dayan ya mishi kallon banza"Samuel kai wani irin mugu ne kam,ita din fa macece ba wai na miji ba,yau kwana biyu kenan safe da yamma kullum se an shaƙa mata haba abin ya yi yawa ze iya mayar da ita mahaukaciya".
"Yeeeeeeeh!tahhh shut up you dey craze? kana son mu a kashe mu kenan?, wannan yarinyar dole ta yi magana in ta ƙi kuma tabar duniya".
Shide be ce mishi komai ba yasa hannu ya ɓare mata gam din bakinta.
Kamar me koyan magana tana hado kalmomi dakyar ta iya furta"sab......ri..........yah......"
Oho sude basu fahimci me take cewa ba,suka sake rufe mata baki suka barta.
Fita sukayi a wajen,aka barta ita daya a dakin.



After one week

Tunda ga wannan ranar da Anty amarya ta sa Sabriyah a ido ta ji son ta ya shiga zuciyarta,haka uncle Hameed ma.Sabriyah bata fitowa cikinsu amma,anty amarya zata zo su zauna suyi hira ta yi ta zolayar ta kafin a ankara shakuwa me karfi ya shiga tsakanin Sabriyah da anty amarya, Ammi, Hajiya babba, Umaisha, Parsa, Rameesa, iklas.shirinta da Zoya ne har yanzu jininsu be haɗu ba,haka Ammuh ta rasa dalilin da yasa ta tsani Sabriyah kuma duk sa'in da suka haɗu se ta jefeta da mummunar kalma ta na hantarar ta,dake Sabriyah dinma fitsararriya ce bata raga mata bata shakkar fadawa Ammuh duk maganar da yazo bakinta, ummah kam dama tun lokacin da aka kawo Sabriyah gidan magana ko wani kallon banza be taɓa haɗa su ba.
Duk kayan da aka kawo mata haka ta zauna ta dinga reɗesu da almakashi tana rage musu tsayi, saboda bata saba sa kaya masu tsayi ba,in ta sakama takura mata yake yi.
A bangaren LTG Taj kuwa tun ranar da yasa major Marry ta fito da ita ya fara mata bincike,har yau bata sake sakashi a idonta ba, sede yasa major Marry ta ci-gaba da bincikar ta amma basa fahimtar juna ko kadan domin Sabriyah batajin turanci ita kuma major Marry batajin Hausa, wannan dalilin yasa Khalifa ya dawo shine me mata binciken, duk sanda aka tambayeta meye alaƙarta

Please Login or Register in order to submit comment