Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tozarta?to Wallahi tallahi ko zan yi yawo tsirara se na hana wannan cin mutuncin da kuke kokarin yi min, da rai na da lafiya ta bazan taɓa barin ɗana na cikina ya auro karuwa ba sauran da wani ya ci ya rage, budurwa sabuwa fil a leda zan aura masa yanda shine nan ze bude ta da kansa".
Runtse ido Sabriyah ta yi jin mummunar kalmar da ta jefesu dashi wai sauran da wasu suka ci suka rage,ina bazeyu ba,dole ne ma su bar gidan nan yau an musu irin wannan tereren tambadar basu san gobe wani kala za'a zo musu dashi ba.

Hajjatiye dake zaune akan kujera tana yar kuka ne ta rangwada gu ɗa"aiyiriyiri!, Ubangiji Allah ya maka albarka Isma'il na yafe maka duniya da lahira,gwara da ka gwadawa wannan mara mutuncin matar ta ka kai ka isa da ya'yanka.kuma inde da ranmu da lafiyar mu se an yi auren Asmita da Saghar sede in mutuwa za kiyi ki mutu.saghar Allah ya sanya alkairi ya nuna mana ranar auren naku mu yi rawa har da karya kwankwaso".

Ba Hajjatiye ba kowa dake falon wannan abin ya musu dadi jin Saghar ya ce yana son Asmita,su ga iya gudun ruwan ummah din.

Mutsu_mutsu take yi a jikinsa tana so ya sa'ke ta,kowa dake falon yana kallon su.
Can ciki ta yi magana.
"Ya Saghar ka sa'ke ni".
"Bazan sake ki din ba"shima ya mata rada a kunne.
Taga tabbas da gaske yake yi ,ba sa'ke ta din ze yi ba hakan yasa ta cize shi a damtsen hannunsa, sa'ke ta ya yi yana kallon idonta da har yanzu be dena zubar da hawaye ba,wajen da Sabriyah ke durkushe ga anty amarya na shafa kanta ta nufa ta zauna a ƙasa tana kwantar da kanta a kafadarta suna kuka a tare.

Folding din hannunta waje daya ta yi alamar roko.

"Ummah kiyi hakuri ba abinda kike tunani bane,ki yarda dani,baki san ainihin abinda muke tattaunawa da Hajjatiye ba,kin zagemu kin kiramu da suna ye kala_kala,tabbas mu bamu da asali bamu da ahali,amma ba laifi muna jin dadin rayuwar mu a inda muka baro din,bamu taɓa kwadayin shiga wajen da Allah be kaimu ba,duk irin azabtar da mu da ake yi amma bamu yi kwadayin shiga cikin wasu ba.gudun gori da wulakanci duk da mu din wulakantattun ne kamar yanda kika ce,amma bama yarda a tozarta mu,muna iya kokarin mu wajen kare mutuncin kan mu.
Ba ma son zaman silar haddasa faɗa ko tashin hankali a cikin wannan gida na ku,domin kun dauke mu Kamar yaranku,kun nuna mana so da kauna har abada baza mu taba mantawa da haka ba, kuma zamu ci gaba da muku addu'a har iya rayuwarmu da gode muku.kun taka muhimmiyar rawa a Rayuwar mu,kun nuna mana hanyar dede,mun san mu su waye ne a yanzu.mun gane addininmu duk ta dalilin ku bamu da bakin da zamu gode muku.
Amma yanzu lokaci ya yi da zamu bar wannan gida bawai dan kun gazaba,sedan kar mu haddasa muku fitina,kafin muzo hakan baya faruwa amma daga zuwan mu ta dalilinmu kun fara samun saɓani.ku yafe mana mun gode sosai ".
Jikinsu ya yi sanyi sosai ganin yadda suke kuka tana magana.
Anty amarya ma sosai take kuka ga idonta ya yi ja.
In su Sabriyah suka bar gidan nan ba kowa aka yi wa ba sama da ita,domin yanzu jin kanta takeyi a matsayin uwa,taya zata juri rasa wata ƴar idan kuwa suka tafi bazata taɓa yafewa ummah da ta zama silar haka ba.

Muryarsa sukaji daga bayansu yana faɗin
"Babu wacce za ta bar gidan nan"kallon shi Sabriyah ta yi idonta na zubar da hawaye ta ce "ya Taj,dole zamu tafi domin kuma ku samu kwanciyar hankali".
Kafeta da ido ya yi,yana kallonta ya dede da yin observing din Sabriyah tana da matukar taurin kai,in ta kafe akan magana to bata taɓa sauya wa musamman ma in ranta na a ɓace.
Be sa'ke cewa komai ba domin tunda ya ji ta ce se sun bar gidan yasan ko da ba'a sani ba zasu iya bari din.

Gyaran murya Abbie ya yi da gaba daya he's out of words, takaici ya gama dabaibaye shi.

"Tashi kuzo nan Sabriyah da Asmita".
Miƙewa sukayi jikinsu a sanyaye suka je wajen Abbie din shafa kansu ya yi kafin ya rike hannunsu ya zaunar da su akan kujera kallon Saghar dake tsaye kamar dutse ya yi,"zo ka mata dressing din kanta nan da ya fashe".
Ba ce komai ba ya nufi clinic ya dauko first aid box.
Ya fara wanke wa Sabriyah ciwon kanta, runtse ido ta yi lokacin da ya fara goge mata da hydrogen har cikin ranta take jin zafin kawai daurewa takeyi,gaba daya ta kosa a gama su tafi.
Bayan ya gama ne,ya bawa Asmita maganinta tasha.
"Kuyi hakuri da abinda ya faru yau din nan tabbas an ci mutuncin ku,wanda gaba dayanmu ba mu ji dadin hakan ba,umman ku ba ta kyauta ba, ɗa na kowa ne amma ku yafe mata in sha Allah bazata sake ba,kun ji ko".
Gyada masa kai sukayi.
Ya ci gaba da magana"yanzu kuna da damar da za ku zaɓi a duk in da kuke son kasancewa,kuna son komawa afafa ne"ya tambaye su yana kallon ko wacce,da sauri Asmita da Sabriyah suka gyada masa kai tabbacin suna son komawa.

Murmushi irin tasu ta manya ya yi ya ce"shikenan zaku koma,kun ji ko, tunda gobe da jibi babu makaranta se ku je ko".da zallan mamaki dauke akan fuskan ko wanensu suke kallon Abbie jin abinda ya faɗa,domin kuwa babu wanda ya yi tsammanin abinda ze faɗa kenan,to menene yasa Abbie ze ce za su koma afafa.me yake shiryawa dan haka kawai bazece zasu je su afafa ba.to kode ya faɗa hakane dan ya kwantar musu da hankali.
Murmushin gefen baki LTG ya yi domin yasan abinda Abbie yake da niyar yi,kuma tunanin su yazo daya.


Ammi ta ce"amma Abbie ta ya kuma za'a mayar dasu can din?,ko ka manta wata irin rayuwa sukayi abaaya?",daga mata hannu ya yi,shuru ta yi bata sa'ke cewa komai ba.
Duk masu son yi magana da su ka ga yanda Ammi sukayi da Abbie se suka ja bakin su sukayi shuru suna son ganin iKon Allah.

"Yawwa gwara de su tattara su bar gidan nan in ana so a samu zaman lafiya dani"cike da takaici Abbu ya juya ya kalli Hajjatiye ya ce "Hajjatiye kwanaki ba kin yi mini tayin auren Hajiya lubabatu ba?,to na amince zan aure ta ko zan samu salama da irin bakin cikin da Huraira ta ke cusa min".
Hajiya Hajjatiye abin nema fa ya samu dama tun shekaru uku da suka wuce take mishi maganar wata Hajiya bazawara da mijinta ya rasu tana da yaronta na miji guda daya tal,kuma matar na da kirki sosai ga hankali da sanin yakamata shisa ta yi wa Abbu kwadayin aurenta amma da ta masa magana se cewa ya yi shi yanzu baze iya yin wani aure ba matar sa da yaranshi zasu ga kamar ya yi hakan ne dan cin mutumci,amma yau shi da kansa ya ce yana bukatar aurenta.hakan yasa ta sa'ke rangwada gu ɗa.

"Se yau na san yarana jinina da halina suka dauko yau Isma'il ka nuna min ka haifu a cikina,ba a cikin ko wacce shegiya ba.uba da ɗa sun kusan angwancewa".ta yi maganar tana gyara daurin zanin ta.

Saghar da Sudais, Parsa ko a jikinsu da suka ji Abbu ya ce ze ƙara aure domin kuwa ummah ita ta jawa kanta da batayi haka ba babu abinda ze sa Abbu yin wannan maganar,yau ta kuresa ne,mutum me hakuri dama in aka kai sa bango to babu dadi.

Hajiya babba kam aranta ta ce "gwara a yi mata hakan ai ko zata yi hankali".

Ummah daura hannu akai ta yi tana"Isma'il ka yi kadan da ka wulakanta ni a gaban yarana,ba de aure ba to daga kai har Saghar din sede in bayan rai na ne zakuyi auren,a yi mugani in tusa zata wura wuta"ganin ta fara faɗe_faɗe ne Ammuh ta zo ta ja ta dakyar zuwa part din ta.

Parsa da idonta ya yi ja tsaban kukan da tasha ne,ta je wajen su Asmita tana basu hakuri.
"Dan Allah kuyi hakuri da abinda umman mu ta yi muku,.. tabbas bata kyauta ba,ku yi hakuri Allah yana son me yafiya,Dan Allah karku tafi please,mun riga da mun zama yan uwan juna baza mu ji dadi ba in kuka tafi kuka bar mu".
Murmushi yaƙe Sabriyah ta yi"bakomai masoyiya ummah ai kamar uwa take a wajen mu komai ta yi mana bazamu rike ta a zuciya ba,amma kam zamu tafi afafa".
Shuru ta yi tarasa me zatace musu ganin takeyi kamar laifin da umman su ta yi ne ya shafe su dayasa Asmita da Sabriyah suka dage se sun bar gidan.

Haurawa Anty amarya part din ta,ta yi tana hawaye saboda Abbie ya riga da ya gama magana,babu wanda ze sa shi ya canza se Hajjatiye ka dai,bin bayanta Ammi ta yi da sauri.

Sahil da Salim dake tsaye su basu da bakin yin wata maganar ma.

"Kuje part din ku lokacin sallah ya yi"part din su suka wuce su bakwai din.

A dakin su Sabriyah suka yada zango,kamar sune suka aikata abinda ummah ta yi haka suka hadu suna ba su hakuri more especially Zoya da Parsa.

Umaisha da ta yi tagumi kamar wata marainiya"Sabriyah tunda kin nace se kun tafi nide duk weekend se na kawo muku ziyara, Wallahi abinda ya faru yau din nan kamar a mafarki,babu wanda ya yi tsammanin haka zata faru".

"Karki damu ai komai ya wuce"cewar Asmita.

A Falo kuwa Abbie ne yake magana da Sudais da Saghar.
"Kun ji abinda Abbu din ku ya faɗa ko,ze ƙara aure fatan baku da matsala da hakan"Saghar ne ya fara magana saying.
"Allah yabasu zaman lafiya nide banda matsala"murmushi Sudais ya yi"Nima haka".

"Shikenan zaku iya tafiya, Tajuddeen ka tsaya kai".
Barin falon sukayi ya rage daga Abbie, Abbu, Hajiya babba, Hajjatiye, LTG.
Dama uncle Hameed ba ya gida duk wainar da aka soya baya nan be san abinda ke wakana ba.

"Tajuddeen nasan ka fahimci dalilin da yasa nace yaran nan zasu koma afafa gobe?"gyada kai ya yi without saying anything.
"Good,ka sanar wa Khalifa shi ze kai su a private jet din ka,daga nan kuma se ku yi abinda ya kamata".

"To shikenan Abbie dama na daɗe da son yin haka kawai wani aikin ne nakeson kammalawa amma tunda bukatar hakan ya taso za'ayi".

Abbu dasu Hajiya babba de basu fahimci inda zancen Abbie da LTG ya nufa ba shisa kawai suke kallon su.

Barin falon ya yi domin dauro alwalar sallar mangrib.

Se da suka tabbatar da babu sauran yaran da suka rage a downstairs din kafin.

Abbu ya rarrafo akan guiwowinsa yazo gaban Hajjatiye ya daura kansa akan cinyarta murya a sanyaye with full of regret ya soma magana.

"Ina me baki hakuri a madadin Huraira,naji takaicin wai yau matata ce ta tsaya tana yiwa mahaifiyata rashin kunya,dan Allah ki yafe min,in sha Allah se na dau mataki akan abinda ta aikata yau din nan".
Shafa kansa Hajjatiye ta yi ta ce "ban amince ka ce zaka dau mataki akanta ba,ni a wajena komai ya riga da ya wuce,ka dena damun kanka".
Murmushi Hajiya babba ta yi wannan dalilin ne suke sa'ke son surkar tasu,ko min irin masifar da zaka ga tana yi tofa bazata yarda wani abun ya ruguza ahalinta ba,wanda be san ta bane kawai zece tana da faɗa.

Magana sukayi sosai kafin Hajjatiye da Hajiya babba suka haura upstairs jin an kira sallah.

Su kuma suna jiran su LTG su fito su tafi masallaci.


A part din Ammuh kuwa,ummah se faman Safa da marwa takeyi tunda suka shigo ta kasa tsaye ta kuma kasa zaune.

Ita kan ta Ammuh lamarin ya girgiza ta,

"Hajiya Huraira dan Allah ki nutsu mu san mafita, wannan Safa da marwa da kike yi babu inda ze kai mu".

Zama ummah ta yi"kamar ni Isma'il ze tozarta a gaban yara da kuma kishiyoyin balbali na?".
"Calm down first wannan fa ba wani babban matsala ba ce amma duk kin bi kin tayarwa da kanki hankali,ko kin manta abinda zamu iya aikatawa ne".
"Hajiya khareema ina sane amma dole raina ya ɓaci kishiya fa?,tun da be min kishiya ba se yanzu da na girma ga yara na sun gama girma shine ze min kishiya".
Matsowa kusa da ita Ammuh ta yi dan ta lura har yanzu Ummah bata dawo dede ba.

"Ki shirya ranar Lahadi muje wajen boka mauzau,daga auren shi Abbu din harna Saghar din se mun watsar dashi".
Se sannan ne taji hankalinta ya kwanta ruwa me sanyi ta bata tasha.


Bayan sallar isha uncle Hameed ya dawo kai tsaye part dinsu ya nufa.
Tsaye a jikin window ya iske Anty amarya, kallo ɗaya ta mishi ta kauda idonta,tunda yaga haka yasan cewa akwai wani abinda ya faru ga idonta da ya kumbura tasha kukanta hatta koshi.
Wajen ta yi nufa.
"Amaryata me yake faruwa na ganki haka"murya na rawa ta sanar masa da duk abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa,kafin ya shigo din nan Hajiya babba da Ammi suka fita a part dinta bayan sun gama rarrashinta.

Jawota jikinsa ya yi yana bata hakuri shi kanshi be ji daɗin abinda ya faru ba, yasan Abbie baze taɓa yanke wannan hukuncin ba,batare da kwakkwaran dalili ba.

"Kiyi hakuri in sha Allah a wannan karon bazamu rasa yarmu ta biyu ba Sabriyah, Allah yana sane da mu,kuma ya Mubarak nasan akwai dalilin da yasa ya yanke wannan hukuncin ".
Ba ta ce mishi komai ba.

8:00pm dede lokacin cin abinci as usual ummah da Ammuh basu fito ba,haka LTG shima yana part din sa, uncle Hameed ya yi iya yin sa amma Anty amarya taki fitowa itama.

A bangaren su Umaisha ma dakyar suka sha kansu Sabriyah suka je dinning.

Kowa ka gani fuskar sa babu walwala da annuri,kawai de ana cin abincin ne,bawai dan yana shiga yanda ya kamata ba.
Kallon Asmita dake tsakuran abinci Saghar ya yi yana ajiye spoon din hannunsa,jikinta ne yabata ana kallonta haka yasa babu shiri ta dago suka haɗa ido,hararanta ya yi,dan haushi ta bashi da Abbie ya tambaye su ko suna son komawa afafa har da cewa eh.

Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi taci gaba da tsakuran abincin.
Bayan sun gama ne.zasu koma ciki Abbie. Ya ce
"Tafiyar ku da safe ne so be ready,kuma karku dau kaya da yawa saboda Monday akwai school kunji ko".
Ido kawai suka zubawa Abbie dukkansu suna tambayar kansu to me yake nufi?,kenan in suka tafi zasu dawo kenan,tunda ga shi har cewa musu yake Monday akwai school.

Ta rasa me zata ce kawai ta ce"thank you Abbie"kafin ta ja hannun Asmita suka wuce part din su,binsu a baya su Umaisha sukayi,kowa de ya rasa gane inda lamarin Abbie ya dosa.

Saghar da ya ƙasa hakuri ne ya ce"Abbie kenan zasu je su dawo ne?,Ni ban fahimta ba".

Fuskar Abbie ba yabo ba fallasa ya ce"ga shi nan de!"ya yi maganar yana fuskewa.

Be sa'ke cewa komai ba,ya miƙe yabar wajen.


Kamar yanda Abbie ya bukace su da suyi haka kuwa suka yi yar karamar trolley ta dauka ta saka musu kala biyu a ciki se dogayen hijabs.


Lieutenant general Tajuddeen


Yana nan a dakin bincike yana aiki,yaran da aka sace yau binciken sa ya tabbatar masa da Mafias ne suka sace su shisa ka ya maida hankali akan neman in da aka kai yaran,in har hasashen sa yabashi dede yaran da kuma masu kidnapping din Suna cikin garin Maiduguri kuma baze taɓa barin su bar garin nan ba se ya kwato yaran,karfe sha biyu ya kira Khalifa a waya ya sanar masa da ze kai Sabriyah Lagos gobe.



Tunda sukayi sallah asuba sukayi wanka suka shirya cikin dogayen rigunan abaya,daukan trolley din Rameesa ta yi sukayi fito falo.

Gaida kowa da suka samu afalon sukayi.dubawa ta yi taga anty amarya bata fakon hakan yasa ta haura part din ta sallama ta yi tana daga tsaye a bakin kofar,amsawa anty amarya ta yi.

"Mommy ina kwana?".
"Lafiya klau mommy's angel,how are you?".
"Am fine mommy"murmushi ta yi jin ta amsa mata da turanci,wato suna fahimtar karatu kenan duk da ma wa'yannan ƙananan words din bame wahalar wa bane.

"Mommy zamu tafi shine nazo miki sallama ki yafe min"shafa fuskarta ta yi,tana danne abinda yake yunkuro mata na baƙin ciki.

Ta ce"baki taɓa min laifi ba daughter, and in sha Allah za ki dawo wannan gidan da izinin Allah ta Allah".

Hawaye ne ta ji ya cika mata ido, hakan yasa ta rungume anty amaryan,.

Sun kusa minti uku a haka kafin ta zame jikinta ta ce"ko ma me ze faru kiyi min alkawarin bazaki taɓa komawa rayuwarki na ɗa ba?".

"Na yi miki wannan alkawarin mommy,".

Dawuwa falon tare sukayi.kowa ya hallara a falon ummah da Ammuh suna upstairs suna kallon duk wani abinda yake faruwa suna murmushi Finally burinsu de ya cika Sabriyah da Asmita sun bar gidan.

A babban filin farfajiyar gidan private jet na wajen, Khalifa su yake jira su fito,rako su har wajen sukayi suka shiga ciki.

Suna musu bye_bye a haka jet din ya tashi sama.sun tafi.



Lagos

Bayan sun isa Lagos ne motar ya zo ya dauke su ya ajiye su har cikin afafa a bakin gate din gidan karuwan da suka baro.

Duk wacce su ka haɗu a hanya se ta kallesu suna mamakin sauyawan da sukayi da kyaun da suka ƙara.

Sashen su na gidan suka nufa,suna shiga suka iske,anty Teema ita kadai tana zaune ta rame sosai ta yi baƙi ta kode kamar ba ita ba,tana daure da fallen zani.
Cikin tsoro suke kallonta a tare suka haɗa baki wajen cewa.
"Anty Teema".
Ta jima da cire tsammanin sa'ke jin muryoyin su a rayuwarta,bude idonta da bacci ya fara saceta ta yi taga dagaske yaran nata ne.
"Hot girl!, Asmita da gaske kune?,kun ga ni yanda na koma ko?, kullum addu'a ta shine, Allah yasa in gan ku kafin in mutu ashe de da rabon za mu ga juna?".

Gyara mata zama Sabriyah ta yi, tana me jin tausayin Antyn nasu,ganin yanda gaba daya ta canza ta kare.
Asmita kam ta ma gagara magana.

"Anty Teema meyake faruwa ne,,shin maganin ki ne ya ƙare?".
"Ai komai ma ya ƙare Sabriyah rayuwar bariki be yi ba ko kadan,yanzu abincin da zan sa abakina ma babu rabona da abinci tun jiya da rana.mutane biyu ne kawai suke taimaka min daga Cele se Nabiha suma tun shekaran jiya basu zo ba".
Ta yi shiru,can kuma ta sa'ke magana.
"Ku da Allah yasa kuka bar nan wani ƙaddarar ce ya dawo daku gidan nan?, kullum inna tuna bakwa s wannan gida ina jin dadi a raina domin jikina yabani kuna a hannu na gari,dubi yanda kuka yi kyau kuka canza kamar ba ku ba,cikin shiga na mutunci".

Yanda take magana ma dakyar take iya bude bakinta,se sukaji kamar basu kyauta ba na barin antyn nasu har tsawon Wannan lokaci basu san halin da take ciki ba.

Gyara mata dakin nata suka yi kafin suka dauki kuɗin da Abbie ya basu koda suna bukatar wani abu.
Suka fice, babban pharmacy suka je suka siya mata magungunanta, sannan suka tsaya a shagon trader suka siya kayan abinci.

Suna a hanya suna tafiya ne, suka hango cele na nufo su, da alamar ya ji labarin dawuwar su ne.

Yana isowa ya ƙare musu kallo sama da kasa kafin ya basu hannu suka tafa,su kansu sun yi tsananin kewar abokin nasu biye da yanda ba'a magana,sun yi farin ciki sosai da ganinsa haka shima bakinsa ya kasa rufuwa se yabon kyau da kibar da sukayi yake yi.nan ya taya su daukan kaya suka koma gida.

Asmita me girkin su ita ce yauma ta musu jallof din macaroni.ta zubawa anty Teema da yawa ta kai mata ta kai mata harda ruwa.

Kiran Nabiha a waya Cele ya yi ya shaida mata,su Sabriyah sun dawo.
Dama tana dakin su bata je ko ina ba,ai kuwa da gudu ta nufo sashen nasu.

Tana zuwa suka rungume juna cike da kewa.

Nan fa aka fara hirar yaushe gamo,suna hira a na cin abinci.
Ko da suka gama cin abincin ma baranda suka dawo suka zauna suna hira harda anty Teema,da ta ɗan warware dama har da yunwa a abinda yake damunta.

Labarin dawuwar Sabriyah da Asmita ya gama kararide gidan,tun shigowarsu dan daudu ya gansu da gudu ya je ya sanarwa boss lady cewa sun dawo, dariyar mugunta ta yi,domin dama ta dau alwashin in de suka dawo se ta yi musu abinda basu taɓa tunani ba.

Lokacin Sallah na yi suka tashi suka yi.

Bayan sun idar ne, Nabiha take basu labarin abubuwan da suka faru bayan barun su gidan,ta ƙara da.
"Amma meyasa kuka dawo?,ni de Wallahi banji dadin dawuwar ku ba,domin ko nice na samu wannan damar baza'a sa'ke kallon ko da inuwata ba, ɓalle kuma ni".

Murmushi kawai suka mata,suka ka war da maganar.
Se karfe biyar Cele ya tafi Nabiha kam ta ce yanda ta yi kewar su dole tare zasu kwana duk da katifarsu baze ishesu ba.

"My Jerry nasan wannan abin hannun nawa yana a dakin nan namu,shisa ban taɓa tambayarki ba,dubomin a inda kika a jiye min".
"Ah ah baya a dakin nan ai ranar da kika bani ban cire ba,har lokacin da wayan'can mugayen suka sace ni yana hannuna bansan ya akai ya ɓata ba".

Jiki a mace ta ce"Tom shikenan bakomai yanzu de abin Tajuju na ya ɓata,amma kinfi min abun hannun daraja".

Nabiha tana zaune tana kallonsu tsananin kaunar dake tsakanin su ne yake burgeta, bata gajiya da son kasancewa a cikinsu.

Saura jallof din su ne suka cinye, se da suka tabbatar da anty Teema tasha magungunan ta kafin suka baro wajen ta.
Sukayi sallah isha sannan suka kwanta,nan ma ba bacci sukayi ba su ukun hira kawai suke yi kamar wa'yanda suka yi shekara uku ba su haɗu ba.se da bacci barawo yazo ya sace su.

Har karfe 8:00am na safe basu tashi ba saboda babu masallaci a kusa da ze kira sallah ɓalle su ji kiran sallah su tashi.

Suna cikin bacci suka ji saukar ruwa me sanyin gaske a jikinsu.a zabure suka tashi suna rawar sanyi, musamman Sabriyah jikin ta ne ya kama rawa bata shiri da ruwan sanyi shisa take kiyaye kanta da kuma lafiyarta domin ciwon nimoniya dake tare da ita.

Boss lady ne suka gani tsaye da babban bokiti tana tsaye akan su ga kuma bulala a dayar hannun nata.

Kafin su gama dawuwa dede ta fara shiga jikinsu da bulala,duka ko ta ina, dakyar suka samu suka kwace kansu suka fito a cikin sashen nasu suna kuka.

Ga kayan jikinsu dake ɗiga da ruwa Nabiha kam guduwa dakinsu ta yi.

Suna tsakar gidan suna kuka,sanyin dake kaɗa kayan jikinsu ne ya sa'ke tsananta rawar da jikinta yake yi.

Lallabawa anty Teema ta yi ta fito ta fara bawa boss lady hakuri, amma ko saurarar ta bata yi ba.

Karuwan dake gidan gaba daya taruwa suka yi suna kallon abinda yake faruwa.

"Kun gama yawon duniyar taku da kuma guje_gujen kun dawo kenan,ai ni banso ku dawo yanzu ba,yanda kuka sani a sarar kudina da kuma bata lokaci wajen neman ku yau se kun yabawa aya zakinta".

Bata hakuri suka shiga yi, tana matsowa suna matsawa baya,har suka fita gidan a bakin gate,zagi iri da kala babu wanda boss lady bata musu ba, Cele da ya hango dandazon mutane ne yasa ya iso wajen da gudun gaske nan fa ya tarar da abinda yake faruwa bashida ikon kwatarsu a hannun boss lady hakan yasa ya koma gefe yana bata hakuri.

Ga mutane da suka yi cincirindo suna kallonsu kowa na tofa albarkacin bakinsa.
Sanyi ya gama ratsa ko wani lungu da saƙo na jikinta har wani tsuma takeyi idonta ya fara kakkafewa..
Lura da ciwonta ya tashi ne yasa Asmita ta rungumeta gam a jikinta tana kuka.

Ko damuwa da halin da Sabriyah ta ke ciki boss lady ba ta yi ba,ta daga doguwar bulalar injin da iya karfin ta, zata zafga mata,ta ji an rike bulalar ta baya, ja ta yi amma kamar ma bata motsa ba,da sauri ta juya dan ganin waye ne.

Bata iya ganin fuskarsa ba saboda face mask dake manne a fuskar tasa,hannu yasa ya dauke ta da lafiyayyun maruka guda biyu,ihu boss lady ta sa,dan tunda take bata taɓa jin marin da ya ratsata irin wannan ba,se da taji kunnenta da dayan idonta lokaci daya sun dena aiki.
Kafin ta gama dawuwa hayyacinta, yasa ƙafa ya kwasheta ta zube kasa warwas, ƙafa yasa ya take hannun nata daa take rike da bulalar da takalminsa,da ƙafarsa ya dinga dukanta kamar ya samu wani katon dabban jaki.

Ɗaukan bulalar ya yi,ya ci gaba da dukanta dashi ihu da kururuwa boss lady take yi na neman a gaji amma babu wanda ya yi gigin

Please Login or Register in order to submit comment