Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

se wata zuciyar ta ce mata karfa ki manta bawai laifi daya ne kikayiwa Tajuddin ba ,manyan laifi guda biyu kikayi mishi ta ina za ki fara neman afuwarsa? Sosai jikin Ammi yayi sanyi se saƙa da warwara takeyi , shigowa falon Hajiya badiyya tayi tundaga nesa data hangi Ammi tasan akwai abinda ke damunta zama tayi kusa da ita,tsabar yanda Ammi tayi nisa cikin tunani batasan ta shigo falon ba, taɓata Hajiya badiyya tayi ta ce " Hajiya hamdiyya lafiya naganki cikin damuwa? ko dayake nasan be wuce tsakanin ki da Tajuddin ba " kallonta Ammi tayi ta ce " Hajiya babba wallahi bansan yazanyi in shawo kan Tajuddin ba, abu ne me matukar wuya " ta kare maganar tana zare medicated glass din idonta tana fuskantar kishiyarta ta, ɗan nisawa Hajiya badiyya tayi ta ce " kuskure an rigada anyishi amma duk da hakan kema danaki laifin duk wani ɗa yana bukatar mahaifiyar shi ta jawoshi ajikinta amma Tajuddin be samu haka daga gareki ba ga laifin da kikaso tabkawa tun kafin yazo duniya bayan wannan kinsake yin wani laifin da haryanzu Taj dashi yake kallon ki. Hajiya hamdiyya ke Mahaifiyarsa ce haryanzu kinada damar da zakije ki neme afuwarshi nasan Taj yanada zuciya me kyau idan kikayi mishi bayanin komai dakuma dalilin haka nasan ze fahimceki , kiduba kiga yaron nan tunyanzu yanaso yarikoɗe yakoma boss wannan dalilin ne yasa Abbie dinsu yake tsoron zuwanshi makarantar sojoji domin a yanzu ma ya'ya? Ya muka ƙare da Taj inaga yatafi yaje yayi shekara goma yana daukan horon sojoji. tun kafin yasa ƙafa yabar kasar nan Yakamata muyi kokarin sassauto mishi da zuciyar shi yayi sanyi yasan kedin uwarshi ce bawai maƙiyarshi bace domin khareema tarigada data gama poisoning zuciyarshi da tsanarmu , har kullum cigaba da cusa mishi ƙiyayyar yan uwanshi da iyayenshi takeyi " tunda Hajiya badiyya tafara magana Ammi ta mayar da hankalinta gaba daya kanta domin maganar ta hakane dolene tasan hanyar da zata ƙwato ɗanta daga sharrin Hajiya khareema domin tanason juyawa Taj ne tunaninshi akansu bude baki tayi zatayi magana sega Hajiya khareema tafito tana nufo inda suke, tsayawa tayi akansu ta riƙe kugu ta ce " naji kamar gulmata kukeyi to adeji tsoron Allah adena gulma da munafurci in an girma asan an girma , duk wani kulle_kullen dakuke kullawa agidan nan ina sane daku yanzu muka fara muzuba mugani kaff senayi maganin ku" tana magana tana kallon Asrah dake wasa acan gefen su mugun kallo ta watsa mata cike da tsananin tsana , Hajiya babba da Ammi de acikinsu babu wanda ya kulata balle tacigaba dayi musu rashin kunya hakan yasa taja doguwar tsaki tayi gaba tana kokarin shiga part din Taj.
Girgiza kai kawai Ammi da Hajiya babba sukayi kafin sukaci gaba da tattaunawar dasukeyi.

Tana daf da zata shiga part din Taj ta hango anty amarya tafito malalacin murmushi ta sake da ita kadai tasan ma'anarshi , ka war da kai anty amarya tayi kamar bata gantaba , bangaje anty amarya Hajiya khareema tayi dayasa saura kadan ta fadi , sannan tayi gaba abinta kamar babu abinda tayi .
afusace anty amarya tabi bayanta tasa hannu ta jawo hannun rigarta ta dawo baya sannan itama ta hankaɗeta ta fadi ƙasa warwas kafin ta nunata da yatsa " wallahi khareema ki shiga taitayinki dani acikin gidan nan karki ga idan kinayiwa su yaya suna ƙyaleki ni to bazanyi shuru kice za ki takani ba , ah ah baki isa ba munafukar banza munafukar hofi" yanda anty amarya take magana ranta amatukar ɓace ya isa yanuna kancewa tabbas akwai babbar yar tsama a tsakaninsu.dafa kujeran dake kusa da ita tayi ta mike ta ce....



Comments, like and share for more...

*🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹*



*_Story & written_*


By

*MRS🌹ISHAM🌹*
( Yar lelen Jarumai)




*THE WRITER OF 🖋️*
*NIDA PATIENT DINA*


~And now~
*🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*



📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️



Page 03


Da fa kujerar dake gefenta ta yi ta mike ta ce " Abida kenan , duk wani kule_kulen munafurcin da kuke yi dake da wancan munafukar ya'yar ta ki Hajiya hamdiyya dakuma ɗayar munafukar taku Hajiya badeeya ina sane daku kuma nafi karfinku , karkuyi tunanin zan zuba muku ido , ina nan ina bin duk wani takun ku !" Magana takeyiwa anty amarya hade da makirar murmushi dauke akan fuskarta,anty amarya kuwa binta kawai takeyi da kallon tsana saboda duk duniya babu irin mutumin da ta tsana sama da munafiki kuma makiri.
Batare da anty amarya ta ce mata komai ba ta juya tana kokarin barin wurin riko hannunta Hajiya khareema tayi tazo dede kunnenta tafurta mata " hankalina baze taba kwanciya ba sena raba ku da Tajuddeen sannan kuma in mai dashi karkashin ikona se yanda nayi dashi bayan hakan ya faru kuma zan raba shi da farin cikin rayuwa . wannan alkawari ne dani Hajiya khareema na daukawa kaina " tana gama fadin hakan tasaki hannun anty amarya ta wuce tabarta awajan ta shige part din Tajuddeen, kamar wacce aka shuka awajen anty amarya ta ka sa koda kwakkwaran motsi kirjinta se bugawa yakeyi da karfi domin kuwa ba ta raba dayan biyu tasan abinda Hajiya khareema ta faɗa tabbas zata aikata, saboda tun farko ita ce ainihin musabbabin cusa ƙiyayyar kowa acikin zuciyar Tajuddeen aciki kuwa harda Ammi.
"Ya Allah ka shiga tsakaninmu da wannan makirar baiwar ta ka da ta shigo rayuwarmu da muguwar nufi , Allah karka ba ta Sa'a akanmu ." Anty amarya ta yi maganar azuciyarta jiki asanyaye.
ji ta yi an rike hannunta tasan ba kowa bace fa ce Asrah , kai dubanta ta yi zuwa kanta , ƙakulo murmushin dole ta yi ta sawa fuskanta ta tsuguna agaban Asrah ta ce " Asrah din mommynta ya akayi har kingama wasan naki ne ?" Ganin ta tsuguna ne yasa Asrah zagayawa ta hau bayan anty amarya,
ta ce" mommyna ki goyeni muje gun daddy " tashi anty amarya ta yi da Asrah din dauke a gadon bayanta suka isa falo anan ta iske Ammi ( Hajiya hamdiyya ) da kuma Hajiya babba ( Hajiya badeeya ) suna tattaunawa.

Tun kafin anty amarya ta karaso Hajiya babba take watsawa Asrah dake goye abaya hararan wasa tana fadin " gaskiya Asrah kinji kunya, shame on you ahakan kikeso in aura miki ɗana Tajuddeen? Kin girma bakinsan kin girma ba no!no bazeyu ba , jibeki katuwa dake abayan mamanki gaskiya bazaki auri Tajuddeen ba" dariya Ammi da anty amarya sukayi banda Hajiya babba da ta danne nata dariyar ta koma serious face dan tasan yanzu zasu ɗibi adashen tsiya ita da Asrah.
Kokarin sauka tafarayi abayan anty amarya ta name kwabe fuska jin abinda Hajiya babba ta faɗa, sauketa ƙasa anty amarya tayi . Wajan Hajiya babba Asrah taje ta tsaya ajikin kujerar datake zaune, ido tabb da hawaye ta ce " adiya babba dan auri tajuju ko " girgiza mata kai ta yi ta ce" no bazaki aureshi ba ,cos he don't loves you" da karfi ta ce" he loves me " ta faɗa tana goge guntun hawayen idonta sannan ta ƙara da fadin " kuma ! Kuma seya aureni din " ta karishe maganar tana murguda dan karamin bakinta , tabe baki Hajiya babba ta yi ta ce" to ai se ya aurekin mugani " anty amarya de da Ammi yan kallo suka zama domin kuwa sun san mudin Asrah ta shaqa tofa gidan nan yau ba zaman lafiya dan rigimarta ma kadai seya hanasu bacci , saboda tasan me ake nufi da kalmar love duk da kananun shekarunta , tunda tashin turai ce. yara tun suna ƙanana zakaga wai sun san meye soyayya,shisaka duk ranar da akace Tajuddeen baya sonta ko kuma baze aureta ba tofa ranar akwai chakwakiya agidan.
Kuka tafarayi a hankali tana " tajuju loves me and we will get married tomorrow" bakaramin dariya Maganar ta yabasu ba hakan yasa suka sa dariya dukkan su harda Hajiya babba dake tsokanar nata , dariyar da taga sukeyi mata ne yasa ta sake hassala ta fashe da kuka da karfi .

Tun bayan rabuwar ta da anty amarya ta shiga part din Tajuddeen bude kofar bedroom din ta yi ta zuba mishi ido , yana kwance yabawa kofar baya.
idanunshi a rufe amma jikinshi yabashi ana kallon shi , murmushin mugunta Hajiya khareema ta yi aranta ta ce " Tajuddeen Mubarak Bishara kaida samun farin ciki arayuwarka sede bayan na mutu amma mudin ina raye , sena rabaka da kowa " cikin kissa da kisisina ta shigo bedroom din ta zauna a bakin gadon shi tasa hannu ta yaye bargon dayake rufe dashi " my son bacci kakeji ne ? gaskiya bazan barka ka kwanta haka ba, tashi ka zauna bari in sa akawo maka abinci ka ji?" tana magana hade da kallon fuskarshi da babu walwala a cikinta ,mikewa ya yi ya zauna yana facing dinta, riko hannunta ya yi murya akarye ya ce " Ammuh duk faɗin gidan nan ke kadaice kika damu dani kuma kika damu da damuwata, duk da ci miki mutunci da ake yi akaina amma hakan besa kindena sona ba" yana magana yana sauke ajiyar zuciya saboda be saba magana me tsayi ba , murmushin samun nasara ta yi kafin ta koma kalar tausayi kamar wata mutumiyar kirki ta ce" ɗana Tajuddeen, banida burin da yawuce inga yan uwanka da iyayenka sun fara sonka narasa wace iriyar tsana sukayi maka , karkaga laifina idan nace hakan yasamo asali ne daga wajan Amminka , ɗan da ace ta nuna maka soyayya dakuma janka ajikinta tofa da kowa ze so ka, amma ah ah ta fifita sauran yan uwanka akanka , kullum kokarina shine inga na nunawa Hajiya hamdiyya abinda takeyi bata kyautawa ita da Hajiya babba amma daga nafara faɗa musu gaskiya sesu fara zagina da cin mutuncin hade da faɗin ina ruwana dakai , nikuma wallahi Tajuddeen bazan iya juya baya akan rayuwarka ba. Allah ya samun sanka tun daga ranar da kazo duniya na mayar dakai ɗana" ta karishe magana tana hawayen munafurci tasaka gefen gyallenta ta goge hawayen, kallonta yakeyi cike da tausayawa saboda Tajuddeen shi gani yakeyi ita kadaice masoyiyarshi acikin gidan daga ita se anty amarya se kuma Asrah da ya mayar da ita wani bangare na rayuwarshi.
Ci gaba ta yi da magana tana nuna mishi hannunta da ya gurje lokacin da anty amarya ta hankaɗata ta fa di ƙasa ashe ta gurje a hannu , yana fitar da jini kadan_kadan dake farar macece se wajan yayi jawur " kaduba ka ga abinda Amminka dakuma Abida suka aikata agareni" rai abace ya ce " Ammi ce tayi miki haka ita da anty amarya?" Cikin salon makirci ta ce" su sukamin haka Tajuddeen saboda naje nasamesu inayi musu magana akanka ,shine sukamin koran kare danaƙi tafiya kuma shine su biyun suka tureni nafadi aƙasa.
Amma bawai na faɗa maka hakan ɗan in tayar maka da hankali bane kokuma in shiga tsakaninka dasu ba kayi hakuri karka musu magana ,in sha Allah wata rana se labari komai ze wuce ." Tana magana ne hade da satan kallonshi ta ƙasan ido .

Tunda ta fara magana yake kallonta jikinshi duk ya yi sanyi jin wai ta dalilinshi akayi mata hakan lumshe idanunshi yayi ya makasa cewa komai saboda shi ba ma'abocin so da kuma yin dogon magana bane,shisa yarasa wata kalma zeyi amfani wajan bata hakuri akan abinda Ammi da anty amarya suka mata , kamar yanda ta faɗa .

Mikewa ya yi slowly yanufi toilet ze dauko first aidbox domin yayi mata treatment din ciwon da taji . Ya riko first aidbox Yana kokarin fitowa yaji kamar kukan Asrah dinshi, ka sa kunne ya yi dan ya tabbatar shin dagaske ita ce din take kuka ko kuwa, sake ji yayi hakan ya tabbatar mishi da antabo mishi Asrah fitowa yayi daga toilet din da sauri batare da ya dauko first aidbox din ba ɗan hankalinshi ya koma kan Asrah da take kuka , be ko kalli inda Hajiya khareema ke zaune ba yanufi hanyar barin bedroom din.
da mamaki take binshi da kallo ganin irin saurin da ya keyi kamar wanda ze tashi sama ,yana daff da barin bedroom din ya tsinkayo muryanta ,tana fadin " son saurin me kake yi haka " amsa yabata da" kukan Asrah naji shine zanje in daukota " beko jira abinda zata faɗi ba ya fice , afusace ta ce " bazeyuba dole in fara ka war da Asrah domin ita ce zata hanani cika burina akan wannan yaro saboda ba karamin so yake mata ba ,in banyi wasa bama zata iya wargaza min aikina danayi shekara da shekaru inayi . Dole indau mataki akanta" ta faɗa tana huci.




Comments, share and like 🥰🥰

Share fisabilillahi
🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹



*Story & written*

By


MRS🌹ISHAM🌹
( Yar lelen Jarumai)



*THE WRITER OF 🖋️*
*NIDA PATIENT DINA*


~And now~
🌹*ASHE ZAMUGA JUNA*🌹



📚📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚📚🖋️



Page 04


" Se tajuju ya aureni ! se munyi aure ! and we love each other" kalmomin da tadinga faɗa kenan tana kuka , tun suna mata dariya har suka koma lallashinta ƙin sauraransu ta yi , ta ci gaba da kukanta jikinta har rawa yakeyi lokaci daya ta haɗa zufa saboda kuka , daukanta Hajiya babba ta yi ta daurata akan cinyarta tana lallashinta amma sam taki shiru.
Abbie, Abbu , uncle Hameed suna zaune suna tattaunawa suka ji ihun kukan Asrah dafe goshi uncle Hameed ya yi. murmushi Abbie ya yi ya ce" to yanzu kuma wa ya taɓo wannan rigimammiyar " ya faɗa yana mikewa yar dariya sukayi su ma suname bin bayanshi , su iklas dasu Abbas duk suna part din Hajiya babba gaba dayansu , yaran matan sun duƙufa suna homework Hafiz na gyara musu in basuyi dede ba , saghar tun da suka shigo be kula kowa ba ɗan har iya zuwa lokacin fushi yakeyi ,yakoma gefe aranshi kuwa yana aiyana irin mugun dukan dazewa Asrah aduk lokacin da Tajuddeen yatafi U.S.A , idan ya tuna Tajuddeen zeyi nesa dasu ne yake jin ranshi nayi mishi sanyi ɗan hakan ne ze bashi damar cin zalin Asrah yanda yaga dama.
Kukan Asrah suka faraji da rigimarta kallon juna Abbas da Ahmad sukayi sukasa dariya , Ahmad ya ce" tabb dijam ! Yau anya zamu yi bacci kuwa? gaskiya Asrah akwai shegen rigima " " ni wallahi kukan yara dagamin hankali yakeyi , Allah de yasa Tajuddeen na gida , ɗan kuwa inde baya nan banajin akwai wanda zesa yarinyar nan ta yi shuru" cewar Abbas .
Dogon tsaki saghar yaja ahassale ya ce " wannan iskancin da yarinyar nan takeyi guri ta samu ,aikin banza " ya mike yabar musu part din,girgiza kai kawai Hafiz ya yi bece komai ba.

" zoya,parsa,umaisha,rameesa kuzo muje gurin Asrah kunji tana kuka ko " cewar iklas da ta mike tana jiran sauran yan uwan nata su tashi suje, mikewa sukayi su ma suna kokarin tafiya, daka musu tsawa sahil ya yi ya ce" common ku zauna babu inda zakuje, ta yi kukan jini ma ina ruwanku " duk tsilli_tsilli sukayi da ido kamar wasu marasa gaskiya, basu zauna ba kuma basu tafi ba . sake daka musu tsawa ya yi yana kokarin mikewa suka zura aguje sukayi part din Tajuddeen ɗan saboda suna kyautata zaton Asrah na can.
Kwafa sahil ya yi ya ce" zamu haɗu ai duk senayi maganin ku " Abbas, Ahmad,Hafiz de basu ce musu komai ba karshema tashi sukayi suka bi bayansu parsa zuwa part din Tajuddeen din.

" Ohhh no! wa ya taba Asrah ne haka, meyafaru yar lelen Abbie" Abbie ne ya yi magana a yayinda yake sa hannu yadauketa akan cinyar Hajiya babba suka zauna akan manyan kujerun da ke zagaye a falon.
Rarrashin ta Abbie yakeyi ko zasu samu ta yi shuru amma ina ,kamar ana zugata ga har kanta yafara daukan zafi , uncle Hameed ne ya kalli anty amarya ya ce " nikam Abida wa ya taɓo wannan rigimammiyar" dariya anty amarya ta yi ta ce" ita da Hajiya babba ne , ce mata ta yi bazata aura mata Tajuddeen ba shine ta ke wannan kukan " dukkansu dariya sukayi harda su Abbas da su ma suka shigo, ga su parsa atsaye sunyi carko_carko duk jikinsu ya yi sanyi sosai ganin irin kukan da yar uwarsu Asrah keyi , ɗan kuwa ba karamin so sukeyi mata ba shisa kullum se sunje wajanta duk da ita bata wani shaƙu dasu ba ,saboda ba kasafe take zama a cikinsu ba.
" Haba Hajiya babba ! kinsan halinta inde akan Tajuddeen ne tofa seta hanamu bacci agidan nan " cewar Abbu fuskarshi dauke da murmushi .

Shigowa cikin falon ya yi idonshi akan Asrah da ke zaune akan cinyar Abbie tana kukanta , sake tsuke kyakkyawar fuskarshi ya yi babu annuri a fuskar, ko kallonsu beyi ba yakarasa tsakiyar falon ya tsaya , tunda ya fito , cak kukan nata ya tsaya kamar anyi ruwa an dauke tafara dariya kamar ba ita ce take wannan kukan ba da kururuwa , hannu ya mika mata ya ce" let's go Asrah" cikin hanzari ta sauƙo akan cinyar Abbie ta riƙo hannun nashi hade da rungume shi, duk zuba musu ido sukayi babu wanda ya ce mishi uffan , ɗan sun san wani inya mishi magana acikinsu ze iya basu amsar da bazeyi musu daɗi ba , domin Tajuddeen inda kunya yabi ma be biba , riko hannunta ya yi yajata zuwa part din shi suka barsu afalon.

Ajiyar zuciya Ammi ta yi kawai taname bin bayan Tajuddeen da Asrah da kallo, kallon Abbie ta yi taga shima ita yake kallo, alama yamata da ido ,ta kwantar da hankalinta, gyada mishi kai ta yi sannan ta mike ta bar falon ta nufi nata part din ,hadaddiyar bedroom dinta tashiga na alfarma dayasha dukiya, zama ta yi akan gado. wasu abubuwan da suka faru shekaru sha takwas abaya ne yake dawo mata acikin kwakwalwar ta , bedside table takai idonta ,yar karamar hoton enlargement ne me kyau ita ce acikin hoton da wani kyakkyawan yaro ajikin hoton sa hannu ta yi ta dauki hoton , shafawa ta yi hawaye na fita a idonta " am sorry my Tajuddeen, ɗana ka yafemin ninasan me laifi ce agareka amma ban cancanci haka daga gunka ba, wallahi bantaba jin bana sonka ba kawai ,abinda ya faru sharrin shaidan ne " ta faɗa tana kuka ta rungume hoton a kirjinta , haka ta kwanta da hoton rike ahannunta , shigowa bedroom din Abbie ya yi yabiyo bayanta domin yasan inde tashiga daki setayi kuka hakan ya rigada ya zame ma ta jiki, tana jin motsi , da sauri tasa hannu ta goge hawayen fuskanta, zama Abbie ya yi a kusa da ita yasa hannu ya ɗagota ta zauna , ganin idonta ya yi ja ne yasa ya ce " sarauniyata kuka kika yi ?" girgiza mishi kai ta yi" ah ah kuka kika yi mana ga idonki ya yi ja ! nasan abinda yake damunki nikaina abun na damuna, wallahi nafara zargin kode sihiri akayi wa wannan yaron , da nayiwa malam baba gana magana ya ce babu sihiri ajikinshi . bansan meye matsalar shi ba "
Kwantar da kanta Ammi ta yi akan kafaɗar Abbie ta yi shuru tana sauraranshi.
Cikin tsigar lallashi ya ce" sarauniya ta , ki kwantar da hankalinki in sha Allah zanyi iya kokarina inga Tajuddeen yadawo kamar kowa " bata fuska ta yi domin ji ta yi ranta yafara ɓaci ta ɗago ta kalleshi ta ce " ka fa riga da kasan matsalar kasan wacece ta shiga tsakanina da ɗana, amma narasa wani daliline ya hanaka yarda da hakan" murmushi Abbie ya yi ya cire glass din idonshi sannan ya ce" bansan meye matsalarku da Hajiya khareema ba , ko da yaushe ita kuke kallo amatsayin me laifi , bayan ita tsakani da Allah take son Tajuddeen. babu mugun nufi aranta amma kun ka sa fahimtar hakan ! to gaskiya banason irin haka " yagama maganar shi yana me janyeta daga jikinshi sannan yafita yabar dakin nata babu walwala atare dashi .
Ammi kam bakin ciki da bacin rai ne ya hanata magana se ma bin bayanshi da takeyi da kallo harya bacewa ganinta .ta rasa dalilin da yasa Abbie kwata_kwata ya tsani akawo mishi aibin Hajiya khareema, kallon mutumiyar arziki yakeyi mata ,domin duk inda makira algunguma take tofa inde akasamu Hajiya khareema magana ya ƙare.
Kwafa Ammi ta yi azuciyarta tafurta " ina sha Allah sena kwato ɗana da mijina daga sharrinki khareema".


Shigowa bedroom dinshi sukayi yana rike da yan dugui_dugui din hannunta, yanda yafita yabar Hajiya khareema ahaka yadawo yasameta sede wannan karon yanayinta babu yabo babu fallasa, zaunar da ita ya yi akan gadon ,tun kafin yakai da zama akan gadon,zazzakar Muryar Asrah kamar wanda aka barbaɗawa suga ya dira musu akunne tana faɗin" my tajuju ai zamuyi aure ko" bece mata kala ba face gyada mata kai da ya yi, dan tun ahanya ta cikashi da surutu hade da bashi labarin abinda yahadata da Hajiya babba cike da yarinta gwarancinta. nan ne ya gane asalin musabbabin kukan nata da yajiyo , har cikin ranshi yaji dadin yanda Asrah take matukar kaunar shi da har yakai in ance bazata aureshi ba kokuma baya sonta take kuka kamar wacce taci duka , duk dakuma kananun shekarunta, shisaka yake jin duk fa ɗin duniyar nan bashi da mata sama da Asrah domin son dayake mata tun tana cikin mahaifiyarta yakamu da sonta , hakan yasa yasanyawa ranshi duk dadi duk wuya yana tare da ita baze taba barinta ba .
muguwar kallo Hajiya khareema take bin Asrah dashi domin yanda ta tsani yarinyar ma aranta to bazata iya faɗa ba domin tsanan yawuce misali , duk wata hanya dazatabi wajan ganin ta ka war da Asrah tagama shirya komai kawai lokaci take jira tarusa farin cikin anty amarya da uncle Hameed da sauran mutanen cikin gidan.mikewa ta yi ta ce" my son nafarajin bacci bari inje in kwanta sannan zanbawa parsa abincinka ta kawo maka " lumshe mata idanunshi dasuka kasance masu daukar hankali ya yi. kan nan tafice a part din nashi tana tafiya tana sake_sake na ganin bayan Asrah in bahaka ba kuwa zata bata mata aikinta ne.

Dawo da kallonshi ya yi kanta yaga ta dauki headphone dinshi tasa akunne , kokari takeyi wajan ganin ta kunna ƙida amma takasa , girgiza kai ya yi dan yasan yanzu zatace seya kunna mata ,aikuwa hakan ce ta kasance datayi iya yinta ta ka sa budewa ta miko mishi " tajuju play a song for me" karba ya yi ya ajiyeshi ya ce" not now , ke bakyajin bacci ne karfe 9 fah " turbune fuska ta yi zata mishi kuka ya ce" karma ki fara ɗan drygon zan kira miki " nan take tayi shuru kamar ba ita ba ,saboda tana matukar tsoron wannan karen nashi da yasa mishi suna drygon hakan yasa cikin tsoro_tsoro ta ce" tajuju ka kaini wajan mommyna zanyi bacci" ta yi maganar tana hawa bayanshi . har part din su yakaita abakin bedroom din anty amarya ya ajiye ta da gudu ta shige ciki ɗan gani takeyi kamar ze iya kiran karen.


Washe gari 6:00am

Yawan comments dinku yawan read more din da zan muku ah to.
Se mun haɗu gobe in Allah yakai da rai da lafiya.




Comments,share and like

🌹🌹 *ASHE ZAMUGA JUNA *🌹🌹


Page 05


*_ story & written_*



Please Login or Register in order to submit comment