Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallon kanta,seda ta ja baya tana mamakin kanta,gani take yi kamar ba ita ba gaba daya kayan sauya mata kamani ya yi, tsananin kyaun da kayan ya mata ya sa ta fara juyawa tana karewa kanta kallo kamar ba ita ba,gashinta dake zube a bayanta ta fara kokarin daure su waje daya,dakyar ta iya daurewa,ta dau dankwalin kayan ta fito,tun da anty amarya ta daura idonta akan Sabriyah ta gagara daukewa kallon fuskar yar karamar ƴarta da ta rabu da ita take yi a fuskarta, fuskar Asrah take gani lokacin da tana karama a fuskarta,ta kasa janye idonta akanta bata ma san ta iso kusa da ita ba tana mata magana amma ina hankalinta ya yi nisa.

"Mommy ki daura mini dankwalin ban iya ba"shiru anty amarya ta yi tana kallonta, taɓa hannunta ta yi tana sa'ke cewa"mommy ki daura min"se sannan ne ta dawo tunaninta,da sauri ta ce"sure kawo in daura miki "miƙa mata ta yi batare da ta yi tunanin komai a ranta ba.

Daurin dankwali me kyau ta mata ta saka mata sarka da ɗan kunnen gold me kyau simple design,ji ta yi kayan yana muskulinta tasa hannu zata dan ja zip kasa kadan,rike hannunta ta yi tana tambayarta "meye zakiyi haka"shagwabe fuska ta yi da iya gaskiyarta ta ce "mommy Wallahi muskulina yakeyi"dama ta yi tunanin za'a yi haka duba da babu irin wannan kayan a rayuwarsu bama su taba sawa ba.
"Karki cire ki daure kidinga sakawa a s haka zaki saɓa,ke bakiga yanda kika yi kyau a cikin kayan bane,kamar wata amarya"tsadadden murmushinta dake ƙara mata kyau ta sakarwa anty amarya"mommy dagaske na yi kyau sosai!?"ta tambayeta with excited face,kai ta gyada mata alamar ta yi kyau sosai,itama da murmushi akan fuskarta nan ne dimples dinta suka bayyana,dan yatsa ta saka a ciki ta taɓa kamar wata karamar yarinya ta langwabar da kanta gefe tana kallon kyakyawar fuskarta anty amarya da za'a iya cewa photo copy dinta ce.
"Laaah mommy kema kina da dimple guda biyu iri daya da nawa,kuma ma a waje daya suke"hararan wasa ta mata"ke dama baki taɓa gani bane se yau".
"Allah ban taba lura ba,se yau.mommy kin san meye!?"girgiza kai ta yi kawai ba ta ce komai ba.
"Mommy ke kyakyawa ce sosai ko fa murmushi kikayi se kin ƙara kyau,kalli idanunki Wallahi kamar akwai wani abu kamar man gyada_man gyada a cikin su"rike haba ta yi tana kallon Sabriyah da mamakin ta,kenan itama surutacciya ce rashin sabo da kuma rashin wanda zaka zauna ka sa'ke dashi har ka ta yi masa surutun ne ta rasa shisa a ke mata kallon bata wani magana sosai.
Yanzu da ta samu anty amarya kuma ta dauketa tamkar uwa shisa take ta mata surutu.kuma ita ta ji dadin hakan sosai yanda ta ji free da ita babu wani shuru_shuru ko kuma wani kunya,ta fito tana ta mata surutu da shagwaba hankalinta kwance.
Tunawa ta yi da Asrah,duk lokacin da ta yi kwalliya se ta shafa fuskarta ta ce "mommy kinyi kyau sosai, you're so beautiful mom".

Ruko hannun Sabriyah ta yi "Tom Nagode babyn mommy, yanzu kije palour,in kije ki gaishesu daya bayan daya bawai yanda kika saba yi ba"gyada kai ta yi ta mike da niyar tafiya.
"Sabriyah zo nan"dawuwa ta yi,ta tsaya,dauko gyalen shantali ta yi ta yafa ma,akai.

Fita ta yi a part din ta nufo main part da tabar su.
A hankali take taka stairs da takalmi me madaidaicin tudu,kamar wata hawainiya take tafiya kai kace tsoron taka kasan takeyi,ita kuma ji takeyi in ta yi tafiya da sauri to skirt dinta ze rabe gida biyu duk da kamatan da ya yi ba sosai bane kawai rashin sabo da irin kayan ne yasa takejin wannan sabon a al'amarin.
Jin ƙaran takun takalmi ne yasa suka maida idon su wajen dan ganin waye haka.
In badan sun santa ba to babu abinda ze hanasu cewa wata shuwa arab mix with Hausa ce,yanda ta atamfar ya yi fitting din jikinta se ya zamana kamar tun asali shine suturanta.
Saukowa downstairs ta yi idanunsu duk a kanta musamman su Umaisha da su Ashman,kallonta suke yi babu ko kyaftawa.
Yanda anty amarya ta sanar ita hakan ta yi wajen Abbie ta fara zuwa ta gaisheshi.
"Abbie ina wuni!?".
"Lafiya klau Sabriyah,ya mommy ki!?".
A hankali ta ce
"Mommy na lafiya"
Ta je wajen Abbu shima ta gaisheshi.
"Abbu in wuni!?".
"Lafiya klau alhmdllh yarinyar kirki"
A marairace Jaleelah ta ce "Abbu mu ba yaran kirki bane!?".
Gwalo Sabriyah ta musu
"Eh din,kun ji haushi ne?"
Hararan wasa Rameesa ta mata ta mike ta dawo wajen abbu ta zauna cikin shagwaba ta ce
"Abbu mu ma ai yaran kirki ne ai ko?".
Dariya abin na su yaba kowa wai kishi suke yi,gyada kai Abbu ya yi kafin ya samu damar cewa
"Dukkan ku yaran kirki dan Allah ku barni haka"sa'ke kwashewa da dariya sukayi harda Sabriyah dake tsaye kusa da Ammi.
Seda ta gaisar da duk wa'yanda suka girmeta a falon,kafin ta lura akwai wa'yanda basa nan. Hajjatiye ma ba ta nan, uncle Hameed, saghar, Dawood,sun tafi da Asmita asibiti.se kuma LTG da tun lokacin da ya tashi be sa'ke dawuwa ba.

Jan hannun Parsa ta yi tana"masoyiya zo muje ki rakani part din Hajiya babba in ga my Jerry"ta kira Parsa da masoyiya kamar yanda ta ji kowa na gidan yana kiranta.

Kame_kame suka fara mata sun rasa ta wani hanya ne zasu hanata zuwa part din Hajiya babba.
Abbie ya ce "Sabriyah bari in ta tashi daga bacci se kije gudun kar ki tasheta"
Murmushi ta yi,cikin farin cikin da bata taba tsintar kanta a ciki ba ta ce "Abbie ka yarda dani,ko motsi na bazata ji, kallonta kawai zan yi in fito".
Ta faɗa tana kuma jan hannun Parsa din.
"Sabriyah bazaki samu ganinta yanzu ba"Sahil ya faɗa yana kallon su.
Kallon tuhuma ta fara binsu dashi jikinta ne ya fara bata akwai wani abu da suke boye mata.
Slowly ta ce "meyasa ka faɗi haka ya Sahil akwai abinda kuke boye mini ne!?"ta tambayashi tana kallon su gaba daya.

Daga bayanta ta ji muryarsa yana faɗin.
"Bazaki samu ganinta yanzu ba kamar yanda Sahil ya faɗa miki saboda yanzu keda su anty Sameera zaku fita siyayya ita kuma Asmita,ba ta tashi ba tukun nan bana son musu"ta kasan ido take watsa mishi harara,yana sanye cikin ka'kin uniform dinsa da ya sake fito zallan madaran kyawunsa.

Sarai ya ga hararan da ta yi mishi amma dake yana da important issues da yakamata ya yi clearing dinsu ya sa be bi ta kanta ba,saboda yasan tunda ya ce bazata shiga ba to,babu yanda za'a yi ta shiga sede in taurin kan nata yana kusa.komawa sukayi daga ita har Parsa suka zauna.shi ma zaman ya yi akan kujerar dake facing na Abbie.
Ganin shi cikin uniform ne yasa Hajiya babba cewa"Tajuddeen ina zuwa haka".
"Zamu je wani dan karamin aiki ne".
Ta ce "Allah ya taimaka"ya amsa mata da"Ameen".
Kallon Ammi ya yi yaga idonta na kansa.
"Ammi zan fita".
"Allah ya taimaka yabaka nasara".
Har cikin ransa ya ji dadin wannan addu'ar da Ammin sa ta mishi,.ya amsa da"Ameen".

Kallon yan matan anty Sameera ta yi ta ce" to maza duk ku tashi muje a yi shopping,Sahil da Sudais ku tashi muje ku zaku kaimu".

Hajjatiye da fitowarta kenan ta ji tattaunawar da suke yi ta ce"kayya! dan Allah kwashesu kaf ki tafi dasu ni dama sun isheni,gwara su je su dede ta kansu a yi tuwona mai na".

Yar dariya kowa ya yi, Sahil ya ce"Tabb waya gaya miki Hajjatiye ni zan yi auren gida!?,ai ina da budurwata a kano to kuma me ze sanya ni in yi auren gida ". "Ah ah babu kam se ka kawo mana ita ai mu ganta"cewar Hajiya babba tana dariya domin duk sun fahimci ya yi hakan ne dan raha.

Tunda ya furta wannan maganar murmushi da walwalar dake kan fuskar Parsa ya dauke cak, idanunta suka cika da hawaye,zufa ya fara tsatssafowa wuyanta da goshinta, sunkuyar da kanta kasa ta yi bata san kowa ya fahimci halin da take ciki.ji tayi komai ya dena mata dad'i,kenan dama duk dakon soyayyan ya'yan nata da ta jima tana yi yana da budurwa ba ta sani ba?,duk da tasan ita kadai take san shi,be ma san tana yi ba shi kallon kanwa ya keyi mata,kuma babu wanda ya fahimci hakan a gaba daya ilahirin gidan se Salim,shine ya fahimci ta fadawa soyayyan dan uwanshi amma ko da ya fahimci hakan be sa ya nuna mata kan cewa yasan wani abu ba.

A duk lokacin da ta yanke shawarar taje ta samesa ta sanar dashi irin son da take mishi ko da Allah ze sa ta samu waje a cikin zuciyarsa,amma kunya da gwarjinin da yake mata se ya hanata tabuka komai.ga shi yau kunnenta ya jiyo mata abinda bata taɓa tunanin jin sa ba a wajensa,ashe ita haukanta kawai take yi.(hmmmm,ni ko nace matsalar soyayyar bari daya kenan ".

Salim da ya lura da yanda mood dinta ya sauya ne yasa ya ji wani iri a ransa, yarinyar da babu wanda ze ce ya taba ganinta a cikin wannan ɓacin ran,ko da yaushe murmushi dauke akan fuskarta se gashi yau ta kan abinda ya kasance ba gaskiya ba,ta shiga wani yanayi,yanke shawara ya yi ze samu Sahil din ya sanar da shi Parsa na matukar kaunar domin shi yafi kowa sanin babu wata mace a cikin rayuwa Sahil kawai yanxu ma ya faɗa ne saboda rashin sani da kuma raha.


LTG dake jin hiran na su ne ya ɗan yi tsaki,shi gani yake yi ja musu reni za'a a wajen wa'yannan kananun yaran.

"Ku tashi mu tafi ko,kar yamma ya yi, Sakeena zakije ne!?"ta tambayi anty sakeena dake magana da Hajjatiye,se kus_kus suke yi.
"No sekun dawo kawai"
Ta faɗa mata haka sannan suka ci gaba da maganar su.

"To Allah ya tsare ya kuma kare ku da karewarsa"can kasan makoshi ya amsa addu'ar da Abbie ya musu sannan ya mike ya fice,yana fitowa yaga rundunar sojojin sa shi kadai suke jira,duk a tare suka sara masa gyada musu kai ya yi Khalifa ya buɗe mishi ya shiga yana kokarin rufe motar major Marry ta fito ita ma cikin shirinta tana sanye da uniform.
Dasauri ta iso tana kokarin shiga.

Kallon ta ya yi irin kallon me kike kokarin yi din nan.
Ta fahimci abinda yake nufi hakan yasa ta ce "Please LTG I want go along with you".
Cikin harshen turanci ya ce mata bazata je ko ina ba,se jikinta ya gama yin sauki.
Babu yanda ta iya tunda bazata tsaya jayayya da lieutenant general ba uban gidanta.
Ta na ganin su suka fita a gidan ko kadan ba ta ji dadi ba,raunin hannunta nan ne ya kwafsa mata saboda tana son ta ganta a bottle field ana fafatawa da ita.

Komawa ciki ta yi babu yanda ta iya haka take ta kwanta.

Fitowa packing space sukayi, Jawan, Sudais, Sahil suka fito da motocin su dan kai su kasuwa.
Jaleelah ce ta yi hanzarin zama a gaban motar tana murguɗawa Iftisan baƙi.
Kallonta Jawan ya yi,ya kuma ga hararan da Iftisan take yi mata.
"In kin gama neman tsokanar seki fito min a motar"tura baƙi ta yi can kasa _kasa ta ce "baza'a fito din ba".
"Rike kugu Jawan ya yi yana mamaki wato wannan rashin kunyan da ya sansu da shi musamman ma ita Jaleelah da tafi Iftisan sangarcewa yana nan.

Hannu yasa ya buge bakinta.kuka tasa ka tana kama bakinta, karasowa bakin motar anty Sameera ta yi jin kukan Jaleelah,kallon Jawan da kukan nata ko ajikinshi ta yi ta ce "meye kayi mata Jawan!?".
"Zagina ta yi shine na buge bakin"ya bata amsa yana yiwa Umaisha alamar ta zo da hannu.
Cikin kuka ta ce "Wallahi anty Sameera ni ban zage shi ba sharri ya min"hannu yasa ze sa'ke buge bakin anty Sameera ta yi saurin rikesa.
"Yi hakuri,kidena kukan.kai kuma Jawan ka kyaleta please".
Bude murfin motar ta yi ta ce "kuma,ma na fasa tafiyan".
Galla mata harara ya yi,ta shige da gudu tana kuka.
Dariya Iftisan ta yi taji dadin yanda Jawan ya yiwa bakin rashin kunyar Jaleelah.
Sabriyah motar Jawan ta shiga ita da anty Sameera da kuma Iftisan din.
Yayinda Umaisha,Zoya, Rameesa suka shiga motar Sudais.
Baya Iklas ta shiga,Parsa dake tsaye a bakin motar bata ma da niyar shiga,fuska a ɗan haɗe.
Kallonta Sahil ya yi "masoyiya zo shigo Mu tafi".
Maƙe kafada ta yi, ta ce "Iklas ki dawo gaba ni abaya zan zauna"with full surprise a fuskarsa yake kallonta,gani ya yi Kamar ba Masoyiya Parsa ba,da duk lokacin da zasu fita inde har dashi tofa tana gaban motar amma yau ita ce take yin tayin zaman gaban motar.
"Yau kuma!,nikam get in don't waste my time"sa'ke maƙe masa kafada ta yi a karo na biyu.
Da ya fuskanci dagaske ta ke ne yasa ya haɗa rai ya daka mata tsawa da yasa ta shige babu shiri.
"Za ki wuce ki shigo ne ko sena shigo dake da kaina!"zama ta yi fuskarta babu walwala,shima da yaga yanda ta yi kicin_kicin da rai ne yasa shima be bi ta kanta ba,duk da yana mamakin meye haka ya samu Parsa da yau ya ganta a haka.
Shi da Iklas ne suke ta hiransu,ita kam ko tari bata yi ba tunda ta shiga motar.

A motar Sudais ma su na nan suna ta surutu gaba daya sun cika wa Sudais kunne, musamman Umaisha an fi jin muryarta.
Juyowa da kansa ya yi ya watsa musu harara,ai babu shiri duk sukayi shuru.
Har aka isa shopping mall din babu wanda ya sake cewa komai.

Ciki suka shiga suka bar mazan suna waje suna jiran su.

Sosai sukayi wa Sabriyah da Asmita shopping kaya na ban mamaki masu yawan gaske da kuma tsada,kama daga kan kayan sawa,kayan make up, perfumes, shoes, bags,hijabs,gyale, jewelrys,sari(lufaya), shower items, lotions,duk wani abinda aka san mace zata yi amfani dashi seda aka siya musu,wajen pad suka je,anty Sameera ta fara ɗiba musu tana sawa a basket,daukan guda daya Sabriyah ta yi ta matsa kadan taji da laushi.
"Anty Sameera meye wannan din?, amfani me ake yi dashi?"anty Sameera ta ce mata "wannan din pad ne ,ana amfani dashi ne lokacin period".
Sa'ke je fa mata wata tambayar ta yi domin bata fahimci abinda take nufi da period da kuma pad ba.
"Anty Sameera su din meye su to"se yanzu ne anty Sameera ta kalleta da mamaki,dazun da ta mata tambayar menene pad ko kadan bata yi mamaki ba saboda wasu basa amfani dashi,da tsuma suke amfani shisa bata kawo komai a ranta ba.
Danne mamakinta ta yi,ta ce "idan kina al'ada da me kuke amfani ke da Asmita"nisawa ta yi kadan domin anty Sameera ta sa ta a duhu bata fahimci abinda ta ke nufi ba.
"Ban san me kike nufi ba anty Sameera"kallon yan matan ta yi taga babu wacce hankalinta yake kansu kowa tana ɗaukan abinda take so ne.
Ta jawota gefe kadan ta ce "Sabriyah idan karshen wata yazo,in kuna jinin al'ada da me kuke amfani!?", girgiza mata kai ta yi,kamar wata wawiya ta ce"jini?, karshe wata? ni haryanzu bangane ba jini aina!?",ta jefa mata tambayoyi uku at one time.
Jinjina kai anty Sameera ta yi wato de in ta fahimta Sabriyah na nufin ta ce mata,daga ita har Asmita babu wacce ta taɓa yin period a cikinsu,tunda ga shi bata ma san ni ba,ta yi mamaki sosai.ta ce zasu karasa maganar a gida.

Bangaren wayoyi suka je,nan Anty Sameera ta dauka musu waya iphone 12 normal su biyu ita da Asmita,irin na hannun su Umaisha.

Layi me register suka karba guda biyu.komai sun gama siya,an je wajen bill anty Sameera ta bayarda ATM guda daya.
Duk hankalinsu nakan wajen bill suna hira.

Ji ta yi an rike hannunta an cusa mata takarda a hannu da sauri ta juya dan ganin waye haka, bata iya ganin fuskarsa ba se bayansa yana tafiya harya yi nisa.
Kallon takardar ta yi kafin ta bude,suna ne a jiki da kuma number waya.suna an rubuta Fu'ad.
Amma bata iya karatu ba ɓalle ta fahimci sunan.
Chukuikuye takardar ta yi da niyar ya sarwa,se zuciyarta ta raya mata da ta kira number ta ji waye.sake kankame takardar a hannu ta yi tana mamakin to waye haka,kuma aina ya santa.

Yaran shopping mall din ne suka kwashi kayan suka kai musu zuwa motar.

yanda suka zo haka suka koma, yanzu kamar dazun har suka dawo gida Parsa batayi magana ba.ita kanta Iklas seda ta yi mamaki kowa yasan ba halinta bane wannan amma ta yi shuru kamar me tunani.

Fita a motar Iklas ta yi ta barsu su biyu.kokarin bude motar ta yi taji taki budewa ta fahimci sarai Sahil ya saka lock ne a motar.
"Masoyiya meya sameki gaba daya kika sauya kamar ba ke ba!?"ya tambayeta yana tsareta da idon sa da takejin kunyar kallo.
"Bakomai"ta ba sa amsa a hankali.
"Karya kike, kowa yasan ba haka kike ba so tell me is something wrong?"girgiza mishi kai ta yi.
Haɗe fuska ya yi "kalli idona da kyau"ka sa dagowa ta yi.
Ya sake maimaita mata a karo na biyu.
"Kalli idona Parsa".
Dakyar ta iya masa kallon da be fi na second biyu ba.
"Tom sanar da ni meke faruwa".
Hawaye ne ya gangaro daga fuskarta,ya ɗigo akan hannunta.
Da mamaki ya sa'ke kallonta.
"Bazakiyi magana ba!?".
Tana sheshekar kuka ta ce "to ai ya Sahil kai ne".
"Ni ne meye Parsa"
Share fuskarta ta yi ta ce "to ba kai bane kace kana da budurwa a kano ba,kuma shine baka sanar damu kana da budurwa ba, ko a waya fa baka taɓa haɗa mu da ita ba ɓalle mu san antyn na mu,for God sake hakan ya yi ya Sahil.kasan yanda muke so a sha biki a gidanmu kuwa musamman na aurenka se yafi na kowa dadi,se munyi event goma a matsayin mu na ƙannen ango". lokaci daya ta canza magana domin bata da karfin guiwar da zata iya faɗa masa tana san shi, wannan dalilin yasata sauya maganar kawai.

Tunda ta fara magana yake kallonta,be yarda da Abinda ta faɗa ba,kawai ya ji ta ne, murmushi ya yi ya bude mata kofa yana murmushi.
Ya ce"shikenan yau din nan zan haɗa ku waya da ita".
Yaƙe ta yi ta fice a motar.
Bin bayanta ya yi da kallo har ta shige ciki.
Ajiyar zuciya ya yi, ya ce "nasan abinda yake cikin ranki masoyiya".

Yana fitowa daga motar yaga su Abbu sun fito duk sunyi alwala zasu je masallaci binsu ya yi.

"Saghar sun dawo ne,ya aikin nata?"
Ya tambayi Ashman.
"Alhamdulillah an yi aiki successful.se gobe za'a fara ganinta".
Shima "Alhamdulillah"ya faɗa.

Suna shigowa Sabriyah ta nufi part din Hajiya babba ta ga ko Asmita ta farka daga bacci,sannan ta yi mata albishiri da an siya musu sabbin wayoyi.ga kuma takardar da har lokacin yana rike kam a hannunta.

Haɗuwa da Hajiya babba ta yi a mahayan ƙarshe,ta ce"har kun dawo kenan?!", "Eh mun dawo Hajiya babba zan je in duba Asmita ne "riƙo hannunta ta yi ta ce"ya'yan ku Tajuddeen yace kar abar kowa ta shiga part din se bayan ya dawo".
Ba dan ranta yaso ba haka suka dawo main part da Hajiya babba,


Anty sakeena ta ce "ku je kuyi sallah"miƙewa sukayi banda Sabriyah dake zaune ta saba duk sanda zasu je yin Sallah tana zaune abunta.
Kallon ta anty sakeena ta yi.
"Sabriyah tashi muje muyi sallah" "to"
ta bi bayanta.
Ta ce mata ta shiga ta yi tsarki.bayan ta yi ne,ta koya mata yanda zata yi alwala.itama ta dauro nata alwala.
Sannan ta ce mata duk yanda ta yi a sallah itama ta yi.
Haka sukayi sallah tare suka idar.

Uncle Hameed ya dawo gida.ya sanar da mom Rumanatu da Abbie,an yi nasara a aikin da aka mata,ba za'a jima ba zata farfaɗo shisa Saghar be dawo ba yana can.

Lokacin dinner ma gaba dayansu sun hallara,a dinning an yi saving din kowa abincin da yake so, Ammuh de bata fito ba dama can ita bata cin abincin su akan dinning se lokaci zuwa lokaci da Abbie yaga bata so se be ce lallai dole se tazo ba,haka ummah ma duk da ita tana fitowa amma bako da yaushe ba.
Fatime na gama serving din su takaiwa Ammuh da Ummah nasu part din su.

Ita de Sabriyah ta gama fahimtar akwai wani abu da ake boye mata,ba sa son ta sani,amma tunda LTG ya ce se ya dawo zataga Asmita to ita kuma ko karfe ɗari na dare ze dawo seta jirasa.

Bata wani ci abincin sosai ba,ta cire hannunta ba wani yunwa take ji ba.
"Ya kika cire hannunki"cewar Parsa.
"Masoyiya na koshi Wallahi".
Anty amarya dake gefenta bata ce mata komai ba, tasan dalilin ta be wuce rashin ganin Asmita bane.
Dawood ne ya miko mata wayarta.
"Yawwa ga shi na seta miki komai,daga icloud har updating din wayar na miki.
Wayarki za ki iya fara amfani da ita.akwai kati a ciki sannan data kuma daga zaran kin kunna WiFi shikenan,bakya bukatar data gidan nan kowa WiFi dinsa yake budewa".

"To na gode ya Dawood".
"Don't mention ".

Kallon wayar ta yi.tana Allah_ Allah su watse anan taje ta dauko takardan da ta boye,ta kira taji waye ne.

Hira sukayi kafin Hajjatiye ta ce ita fa surutun ya ishe ta,ta barsu a falo taje ta kwanta.


9:00pm na dare ta fara motsawa alamar zata farka.dakyar ta samu ta daga hannunta da ya yi mata nauyi ta ɗan da fa kanta,ji tayi kan akwai bandeji gaba daya an zagaye sa dashi,ga wani uban ciwo da kan yake mata.
Runtse idonta ta yi,tanaso ta tashi amma jiri ya hanata.
Ta riga da tasan a inda take,domin lokacin da suka iso asibiti ta farfaɗo nan uncle Hameed ya sanar da ita yanzu za'a shiga da ita operation,allura akayi mata na bacci fuskar Saghar shine fuskan wanda ta gani kafin ta faɗa bacci.

Hakan yasa a hankali muryanta baya fita sosai ta soma kiran sunan sa.
"Me kyau!me kyau!me kyau"yana bakin kofa suna magana shida wani doctor ya ji kamar ana magana a cikin dakin.

Shigowa ya yi ya sameta tana kwance idonta abude.

Murmushi ya yi ganin ta farka.
"Sannu ko,yanzu ina ne yake miki ciwo".
Bata ba shi amsar tambayar da ya mata ba ta ce"Sabriyah ta zo ne!?". girgiza kai ya yi.
Murya a hankali ta kuma cewa"meyasa batazo ba to me kyau !?",jin sunan da ta kirasa dashi ne yasa ya kalleta da kyau,wato wancan memoryn yarintar da ta shiga ba duka bane ya gushe ba,tunda ga shi still bayan ta dawo hayyacinta tana kiransa da me kyau.
Ya ce"bata ma san an yi miki aiki ba saboda zata iya tayar da hankalinta amma gobe duk zasu zo dubasu da jiki"gyada masa kai ta yi.
"Kai na!,na mini ciwo sosai kuma ina ganin jiri"zama ya yi a gefen gadon ya ce "ehh wannan normal ne,nan da wasu kwanaki za ki dena jin haka".
Shuru ne ya biyo baya daga ita har shi babu wanda ya sa'ke cewa komai.

"Me kyau ban san sunanka ba"batare da ya kalleta ba,ya amsa mata da "Saghar".
Nan ma shuru ne ya sa'ke ratsawa, miƙewa ya yi ze fice,dan ya rasa meyasa duk lokacin da yake tare da ita se ya ji wani iri.

"Ya Saghar tafiya zakayi ka barni ni ɗaya!?"ya tsinkayi muryarta tana tambayarsa.
juyowa ya yi idonshi ya sauka cikin nata narkakkun idanun ta kafesa dashi tana kallonsa.
Komawa ya yi,ya zauna yana kallonta.
"Asmee dama kema matsoraciya ce!?".
"Ah ah naga zaka tafi ne ai to"
"Ke kuma bakya son in tafi?",sun kuyar da kanta ƙasa ta yi.
"Kina bukatar hutu ne za'a miki allura,za ki yi bacci ba'a son ki dinga magana sosai"gyada masa kai ta yi.

Yanda suke yiwa juna magana duk wanda ya kallesu ze yi tunanin sun daɗe da sanin juna,ko kuma akwai shakuwa sosai.

Se karfe goma ya bar dakin nata se da ya tabbatar da ta yi bacci kafin ya fito.yana kashe mata light.

Tana part din anty amarya idonta biyu ba tayi bacci ba tana jiran dawuwar LTG.
Anty amarya ma idanunta biyu,ita kanta jiran LTG takeyi ya dawo, saboda duk sanda ya fita ya yi dare ita da Ammi in ba sunji dawuwar sa ba tofa basa iya bacci.

Suna zaune tana ta koya mata wasu abubuwa.idanunsu biyu har sha biyu ya gota,nan ma shuru be dawo ba.
Wayarta ta dauka ta kira layinsa sede switch off.hakan yasa anty amarya ta dinga addu'a Allah de yasa lafiya.

Karfe 1:00 na dare motocin suka diro cikin gidan,anty amarya da Ammi da Abbie da suka kasance idon su biyu suna jiran dawuwar su sukayi hamdala.

Dama ya saba duk sanda ya yi dare ita yake kira a kawo masa coffee.

Suna zaune kira ya shigo wayarta ganin shine yasa ta daga.

"Anty amarya coffee please"haka kawai ya ce ya kashe wayar.

Miƙewa ta yi ta shiga kitchen din part dinta,cikin mintuna ƙalilan ta haɗa masa coffee, tunani ta fara zuwa ta tashi fatime ko kaltume,se kuma taga in ta

Please Login or Register in order to submit comment