Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uncle wata yarinya ce haka!?",ya ce "Asrah!ita ce farin cikin Tajuddeen yana sonta sosai yarinyar da yake da burin aure in ta girma,so ne me karfin gaske a tsakanin su".jikinta ne yafara rawa ta rasa dalilin da yasa duk sanda aka ambaci sunan Asrah se taji tsigar jikinta ya tashi,Wannan shine karo na biyu da taji wanann sunan a yau yanzu jikinta rawa yake yi.da mamaki uncle Hameed ya kalleta ya ce"Sabriyah lafiya ko de baki da lafiya ne!?"yana taɓa wuyanta ya ji ko zazzaɓi ne amma jikin babu alamar zazzaɓi.rasa amsar da zata bashi ne yasa kawai ta ce"babu komai uncle". "Kin tabbata?"ya tambayeta yana kallon ta,gyada masa kai ta yi.
"Ya jikin yar uwar taki ta samu bacci ko?",nan ma gyada masa kai ta yi, murmushi kawai uncle Hameed yake aikinyi,be san meyasa inde yarinyar tana a tare dashi se yaji kamar yana tare da yarsa ta cikinsa wacce ya haifa,se yaji yana sha'awar ya ta janta da hira.
Bude baki ya yi da niyar yin wata maganar ya ji horns din motoci sun shigo gidan, murmushi ya yi,ya ce "madallah sun dawo kenan,tashi muje ki rakani tarbo baƙi"bata iya masa musu haka ta mike yana rike da hannunta suka sauko main part,da mamaki matan su ya Abbas suke kallon uncle Hameed da yarinyar da yake tare da ita suna tambayar kansu wannan kuma wacece kuma daga ina?,maye hadin ta da uncle Hameed da har yake rike mata hannu baya tsoron matarsa ta gansu?,Ammuh da mugun kallo ta bisu har suka fice, tana me aiyana abubuwa aranta kallo ɗaya tayiwa Sabriyah tun zuwanta gidan ta ji ta washi yarinyar ta tsaneta,se kuma labarin da ummah ta kai mata wai anty amarya tana son adopting dinta ta zama yarinyarta,dole ne ma tasan yanda zata yi ta kora Sabriyah ta bar gidan.


Fitowa waje sukayi shi da ita suka tsaya suna jiran su abbu su fito daga motar.bubbude musu akayi suka fito,sauka idon Abbie da abbu ya yi akan uncle Hameed dake tsaye riƙe da hannun Sabriyah,basu yi mamaki ba saboda duk tunanin bakuwarsu ce,kila acikin surkansu ne wata tazo da ita. su ya Ahmad suma suna mamakin wannan bakuwar fuskar da suka gani, cike da farin ciki suka rungume juna uncle Hameed na musu sannu da zuwa,raba jikinsu Abbie ya yi yana kallon Sabriyah dake tsaye a gefen su sanye da riga da wandon jeans babu ko dankwali a kanta.
Kallonta ya yi sannan ya kalli uncle Hameed "Hameed Wannan yarinyar fa?,yar waye!?"abinda Abbu yake shirin tambayarsa kenan se Abbie ya rigasa.shima uncle Hameed din kallonta ya yi cikin zolaya ya ce "ƴata ce"da alamar tambaya suke kallon shi cikin tuhuma.dariya uncle Hameed ya yi ganin irin kallon da suke binsa dashi ya ce"just kidding!, bakuwarmu ce, shikenan?",dariya suma sukayi.

"Yarinya ya sunanki!?"Abbie ya tambayeta" "Sabriyah"ta basa amsa cike da kunyar da bata san tana dashi ba.
Murmushi Abbie da abbu sukayi.
Kafin ya sake cewa"to Sabriyah ina dankwalin ki!?ba ki san babu kyau yawo babu dankwali ba!?"girgiza mishi kai ta yi alamar bata sani ba,kallon juna abbu da Abbie sukayi,katse zancen Saghar ya yi,ta hanyar faɗin"Abbie mu karasa ciki".shiga ciki sukayi ,kafin su zauna su Rameesa suka zo dukkansu suna musu oyoyo,yanda su duka suka kam kame abbu da Abbie ne yabawa mutanen falon dariya.
Abbie ya shafa kansu"oyoyo!yan matan Abbie"cikin shagwaba Parsa ta ce "munyi missing din ku sosai kunje kun daɗe" "we missed you too masoyiya,yanzu kam ai mun dawo".

Zama sukayi gaba dayansu,ana faman gaishe da su Abbie da kuma yi musu sannu da hanya,ganin sun shiga rububi ne yasa Sabriyah ta fece zuwa dakinsu.ita bata cusa kanta cikin abun familyn duk da familyn na burgeta sosai yanda suke da son junansu da girmamawa.

Shigowa dakin ta yi ta ga wayam babu Asmita da tabarta akan gado tana bacci dubata ta yi a toilet nan ma wayam bata nan shiga dakunansu Umaisha ta yi nan ma bata ganta ba.hankalinta ya tashi tafara tunanin ina Asmita kuma ta shiga daga ɗan fitan ta da ta yi din nan.


Book one ya kusa karewa remain some few pages,na yi wa mutane 20 na farko discount din 200,zasu biya 300 kenan.idan mutum ashirin na farko suka gama biya ze koma 500 domin wannan shine standard price dinshi.luckiest 20 people ku hanzarta biyan naku.😍😍😍😍😍💝


Comment,share and like.

*🌹🌹 ASHE ZAMUGA JUNA 🌹🌹*


Page 23&24


*_Story & written_*


By

*MRS🌹ISHAM🌹*
( Yar lelen Jarumai)




*THE WRITER OF 🖋️*
*NIDA PATIENT DINA*


~And now~
*🌹ASHE ZAMUGA JUNA 🌹*



📚📚 JARUMAI WRITERS ASSOCIATED 📚📚🖋️



Page 23&24


Da gudu_gudu ta fito daga part din tsaban ta rude ma bata san wani part ta shiga ba, ita de tasan neman Asmita take yi,a tsawace ta ce "ke meya kawo ki nan!?,za kizo ki shafa min najasa ko to fice tun kafin na lahira yafiki jin dadi"mugun kallo ta watsawa Ammuh,"Mtsssw!ni in banda tsautsayi meze kawani wajen ki,je kiji da matsalar dake gabanki tsohuwar banza kawai"a harzuke ta kai hannu zata mare ta, tayi gaggawar rike hannunta ta ce "Wallahi ko a mafarki ki ka ga kin mareni to kiyi gaggawan tashi daga wannan mafarki domin murde hannunki zan yi ya koma baya,babu ruwana da girmanki,ki kalli cikin kwayar idon nan tawa in kinga kunya a ciki, to ki dau mataki akaina,yanda kika tsane ni ,haka na tsaneki kuma ina da tabbacin nawa ya ninka naki"ta sake mata hannu ta fice dan neman Asmita ne a gabanta bata da lokacin ɓatawa.
Suman tsaye Ammuh ta yi tana ta nanata maganar da Sabriyah ta gaya mata,ji take kamar an watsa mata garwashi a kirji,lallai dole ne ta dau mataki akanta saboda taga alama yarinya nan in ta samu guri zatayi abinda yafi haka.kwafa ta yi "za ki shiga hannu".

Ta duddubata a bangaren sama bata ganta ba hakan yasa bata da wani zabi da yawuce ta dawo downstairs.
Kusan yawanci ma basa nan,matar ya Hafiz ce a falon se Zoya da kuma yara.

Bata tambayi ko daya daga cikinsu ba. da taga de bata falon kawai ta fita,a waje ne ta tambayi securities ko sunganta,dayan su ne ya sanar da ita tana garden ,yana gama faɗa mata ta nufi garden din da sauri,tun kafin ta iso ta hangota zaune akan lilo dake cikin wajen.girgiza kai ta yi, ta karasa wajenta ta baya batare da tasani ba ta rike lilo ya tsaya ,juyawa ta yi tana ɓata fuska "my Tom ki bar mini lilo na" "Asmita meyasa kika baro can ki ka barni ina ta nemanki gaba daya hankalina ya tashi,banason sa'ke rasaki a karo na biyu".
Tasan abu ne ma wuyaci ta fahimci me take nufi.hakan ya sa ta ci gaba da turata a lilon,ita kuma tana dariyar farin ciki,haka suka kwashe mintuna Ashirin a haka.

Dakatawa Sabriyah ta yi,gaba daya ta gaji tana riƙe ciki ta ce"My Jerry zo mu tafi se anjuma mu dawo ko?",gyada mata kai ta yi ta sauko akan lilon.ta rike hannunta suka bar garden din suka koma ciki.

Muryar Ammi sukaji tana musu magana ."Sabriyah kuzo ku nan dama ku nake nema"karasawa wajenta sukayi ,kallon Asmita Ammi ta yi kafin ta maida kallon ta kan Sabriyah "tun dazun!,su Rameesa suke neman ku,Abbie yabada naku tsaraban abaku,ki dena yawo da wannan kayan sun matse miki jiki sosai Zoya ta faɗa mini cewa duk kayan da aka kai miki rage su kikeyi.nasan baki saba sa irin wa'yannan kayan ba amma ki daure ki dinga sawa ke macece,mace kuma an santa da kamun kai da kunya ,suturta jikinta"shuru Sabriyah ta yi,jikinta ya yi sanyi ba'a taba tsayar da ita an faɗa mata haka ba.

Murmushi karfin hali ta yi wanda kana gani kasan cewa be kai zuciya ba"Ammi!,na taso ne a inda babu me ce mini dede nakeyi ko kuma akasin haka, wa'yannan kaya masu nauyi kuma ban saba da su ba bana iya samun nutsuwa a cikinsu.Ammi yanda nake rayuwata bazance inajin dad'i ba kuma ba zance banajin dad'i ba".sosai Ammi take kallon idon Sabriyah domin iya gaskiyar ta take gani, tabbas an yiwa rayuwar yaran nan illa me muni ma kuwa.

"Bakomai Nasan in kina tare damu duk za ki saɓa da hakan"gyada kai kawai ta yi,ta ja hannun Asmita dake wasa da flowers din kan table.da tun tsayawar da Sabriyah ta yi wajen Ammi ita kuma ta tsuguna ta fara wasanta.


Suna haurawa stairs Asmita ta ce "my Tom" "uhmm"
"Ni banga me kyau ba ina yaje,nayi lilo shi be yi ba"bata amsa mata ba, suna ci gaba da tafiya ne ta ce"yau yana aiyuka sosai,ba zaki samu ganinsa ba"bata rai ta yi da alamu bata ji dadin maganar Sabriyah ba,ita tana son ganin me kyau suje su yi lilo kuma ya bata chocolate.
Har suka shiga daki bata sake magana ba se da Sabriyah ta ce "my Jerry ki dena fita batare da nasani ba,kina tsorata ni in naga bakya nan,kinji ko"gyada mata kai ta yi alamar "to".

Wanka ta shiga tayi yau duk bata samu ta sake yin wani wankan ba,tun na safe da ta yi ga shi yanzu har yamma ya yi.

Bayan ta fito daga wanka ta bude wardrobe din kayan kallon kayan da aka saka musu, ita da Asmita zuba musu ido ta yi tana tunanin wanne zata ɗauka,ga maganar Ammi da taji yana mata yawo a tsakar ka.

Runtse ido ta yi tasa hannu ta dauko wando falazo da riga.sakawa ta yi ta gyara gashinta kawai ko mai bata shafa ba.

Hawa gadon ta yi wajen Asmita da ta kwanta kamar me bacci amma idon ta biyu ta zubawa bango ido.
"My Jerry tashi kiyi wanka"maƙe kafada ta yi,"yi hakuri shalelena tashi kiyi wanka kinga dare ya kusan yi, sa'ke make kafadar ta yi.
Dafa goshi ta yi"haba my Tom ki tashi mana meyasa kike da taurin kai ne ?,"da karfi ta ce"banason wankan banaso "ta yi maganar tana bubbuga ƙafafunta akan gado,tuna maganar da Saghar ya gaya mata yasa ta kyaleta domin ya ce bata da buƙatar a dinga takura mata, lallabata yakamata a dinga yi.



Ya Abbas suna falon Abbie ana hira, matansu kuma suna wajen su Ammi suma.

"Tajuddeen be san mun dawo bane?"Abbie ya tambayi Sudais dake zaune kusa dashi.
"Ehh gaskiya ba lallai ne yasan kun dawo ba"ya basa amsa.
"Shikenan ni zanje ai in same shi".
Se da aka kira sunan Tajuddeen ne ma Saghar ya tuna da ya sanar dashi cewa yana son ganin sa da, Sudais da kuma Jawan.

Taɓa Jawan ya yi "kaga na manta ko, LTG ya ce yana son magana da mu, da ya Sudais".
"Shikenan se dare se muje "cewar Sudais.
Abbie yana matukar son ganin Tajuddeen se zuba ido yake yi ko ze zo amma shuru babu ko alamar sa,ana hirar ma shuru kawai ya yi burinsa kawai yaga Tajuddeen yazo masa sannu da zuwa ya rungumesa,amma tunda yaga har zuwa yanzu be zo ba tofa baze zo din ba.

"Yawwa nikam Hameed yarinyar waye naganku tare dazun!?"Abbu da ya kasa hakuri ya sa'ke tambayar uncle Hameed.
"Ita ce wannan yarinyar da Tajuddeen ya kawota gidan nan yana bincike akanta".
"Ikon Allah, lokacin da kuka tsaya tare se tayi kamar ƴarka"abbu sake faɗa domin shi yaga kamar Sabriyah da uncle Hameed.
Dariya kawai suka yi. Saghar da ya manta da allurar Asmita da zeje ya mata, seda a ka kira sunan Sabriyah ne ya tuna da ze mata allura.
Gyaran murya Abbie ya yi sannan ya soma magana "gobe Hajjatiye zata zo,kun san Allah wanin ku ya kuskura ya ɓatawa uwarmu rai tofa ba babu ruwana da girman da kukayi jikin ku ze baku labarin shekaru sha daya da yawuce tam"yar darawa sukayi, Ahmed ya ce"duk sanda Hajjatiye zata zo se anyi mana warning yanzu fa mun girma yakamata a dena maimaita mana Abbie ".
Cikin harshen shuwa abbu yace"da yafi muku".
Yaron ya Hafiz ne ya shigo dan shekara biyar hannunsa rike da bindigar wasa,ya zauna a kusa da Abbie"ah ah Ameer kar de mu za'a harbe da bindigar nan"Abbie ya tambaye sa cikin wasa, maganar cike da gwaranci irin na yara ya ce "nooo!terrost za'a halbe ko kaka"dukkansu dariya sukayi,"naga alama babanninka Tajuddeen ko Sudais ko kuma Jawan zaka ga'do "uncle Hameed ya faɗa yana shafo kan Ameer dake wasa shi da bindiga.

Sosai suka sha hira,ganin har lokacin LTG be shigo bane yasa Sudais ya kirasa,3missed calls ya mishi amma beyi picking ba daga karshe ya turo mishi da text,bude sakon da LTG ya turo masa ya yi.
"Bro!call you back,am in important meeting right now can't talk".
Murmushi Sudais ya yi,shi dama yasan zeyi wuya in LTG na gidan.
Shima ya rubuta mishi message kamar haka.
"Okay,Kayi sauri ka dawo Abbie is eager to see you".
Har bayan 5mint bayi mishi reply,yasan yaga message din.
"Abbie LTG baya gida yana meeting shisa ka ji shi shuru"Sudais ya faɗa masa,se yanxu yaji sanyi a ranshi,domin tunda suka dawo yakeson ganin sa it has been a while rabon da ya gansa.


"Ammi Tajuddeen fa tunda nazo ban ganshi ba"Anty Sameera ta tambaya,anty sakeena dake sawa karamin ɗanta pampas ta ce"Nima abinda nakeson tambaya kenan,ko baya nan ne" "ehh ya fita,nikam bazaku koma gidajenku bane dare fa yanayi"Ammi ta tambayesu ,tana bin ko wacce su da kallo dariya Anty amarya ta yi "haba Ammi yakike korasu ne"hararanta ta yi ta ce "to ai naga dare ya fara ne ai,kuma banga alamar zasu tafi ba, ko kuna nufin haka zaku bar mazajen naku su kadai a gida!?", marairace mata suka yi "ayyah Ammi dan Allah ki bar mu mu kwana, Wallahi seda muka sanar musu zamu kwana kafin muka taho kuma sun yarda"cewar anty sakeena.
"Se kuma kuyi ai,yanzu nan ko wacce ta shirya ta wuce gidanta,babu wacce zata kwana",Hajiya babba tana zaune tana jinsu bata sa musu baki ba.
"Ammi kiyi hakuri ki barsu tunda sun tambayi mazajen nasu,kuma kinga Hajjatiye da Rumanatu duk gobe zasu zo,su Abbas ma duk anan zasu kwana"anty amarya ta roki alfarma..
"Shikenan Allah yakaimu "suka amsa da Amin.


Yau su Umaisha ana wajen Abbie da Abbu,a wajensu suka tare se surutu suke musu,rabonsu da part dinsu tun karfe biyu basu sake komawa ba.

Sabriyah bata sake jin d'uriyarsu ba,kuma hakan be dame ta ba,tana tare da Asmita suna ta shirmensu, knocking aka yi ta ce "a shigo".
Saghar ne ya shigo hannunsa rike da kwalin chocolate din da yace ze bada a kawowa Asmita ya manta.
Tana jin muryar sa ta mike ta tsaya akan gadon tana ihun"me kyau!me kyau!me kyau"murmushi ya mata,tana daga kan katifa ta rungumoshi a jikinta kamar wani ɗanta,wani shock ya ji tundaga tafin ƙafar sa har cikin kwakwalwarsa da sauri ya raba jikinsa da nata beyi taba kawo tsammanin zata rungumesa ba.
Tura masa baki ta yi"me kyau na hau lilo babu kai"se ta nutsuwarsa ya yi kafin ya ja hannunta ya kaita gaban mirror ta zauna Sabriyah na zaune tana kallonsu,komawa ya yi wajen da ya ajiye kwalin ya bude ya fito mata da chocolate ya kawo.
Buɗe mata chocolate din ya yi,yabata raba chocolate din gida biyu ta yi tabashi rabin girgiza mata kai ya yi alamar bazesha ba.
Fara sha ta yi idonta akanshi,kawar da kansa ya yi, ya haɗa allurar ya mata cikin dabara,se da ya gama ze tafi tukun ta ce baze tafi ba se yasha chocolate din,karba ya yi gudun kar tayi kuka,yasha ya ce "shikenan!?", "Ehh".

Sabriyah ta ce "my Jerry ni baza'a ban chocolate din ba?",sake raba chocolate din ta yi tasa mata abaki.

Fita Saghar ya yi adakin yana dariya.abincin darensu Fatime ta kawo musu fuska a sa'ke suka gaisa.


Bude kofar bedroom din ya yi yaje ya zauna akan gadon Abbie yana jiransa,daga wanka ya fito beyi tunanin zega mutum a ciki ba,da mamaki yake kallon LTG dake zaune akan gadonsa.

Miƙewa ya yi yaje ya rungume Abbie yana faɗin "i missed you so much Abbie" "nayi missing dinka nima sojana "zama sukayi akan gado.
"Nayi tunanin bazaka zo ka ga Abbie dinka ba"LTG ya ce"nope ina meeting ne sorry for the delay".
"Is okay ya aiki,banyi zanton dawuwanka nan kusa ba se gashi ka dawo, amma Jawan ya sanar min bincike ne ya dawo dakai", gyadawa Abbie kai ya yi.
Sun bata kusan two hours tare suna hira,kafin ya yiwa Abbie se da safe.

Yana shiga part din sa ya tarar da Jawan, Saghar, Sudais suna jiransa.
"Very good guys,na ɗauka baku zo ba ai"ya faɗa yana wucewa dakin binciken,bin bayansa sukayi ciki suna shiga kofar ya rufe.

Suna zaune suna kallonsa ya fito da memory card din ya jona a babban system, connecting ya yi sannan ya dawo ya zauna suka fara kallo.

Fuska Barrister Lameer ne ya fara bayyana ajikin video din.yana magana murya kasa_kasa da alamu yana tsoron kar wani ya ji shine.

"Sunana Barrister Lameer muktar.ni mazaunin garin Kano ne,na samu sakon sirrine kan cewa wasu mugaye kuma hatsabibai yan ta'adda sun shigo kasar Nigeriya,wanda kasashen waje ma basu iya kawo karshen ta'adda cin su ba.sun shigo Nigeria ne da nufin kashe rayuwaka masu dimbin yawa.
Wannan dalilin yasa nasa rayuwata a cikin hatsari domin haɗa bayanai akansu nasan ba lallai in rayu ba,rayuwata dakyar ne in zan iya fita daga sharrinsu amma Allah ya fisu".
Yana gama wannan jawabin duhu ya bayyana akan screen din,duk shuru sukayi hankalinsu yana kan screen din, musamman LTG yana son yaga abinda suke shiryawa.

Mutane ne kusan su goma sha biyar zazzaune akan kujera ga tarin makamai,da bindigu,a gaban su ba iya bakaken fata bane harda turawa a cikin su.
Ogan dake zaune akan kujerar tsakiya fuskansa na sanye da mask baki irin wanda barayi suke sawa,in zasu je fashi.

Magana ya fara da turanci"babban abinda nake muradi shine zubar jini,ko da wasa wani acikin ku ya bata mana aikin da mukayi watanni goma muna shiryawa to dashi da familynsa makomarsu lahira ne,asibitoci guda ashirin ne acikin Nigeria wanda zamu dasawa boma_bomai,da Masallatai,da kuma churchs, kasuwanni,makarantu,ko ina za'a dasa bom,bayan nan kuma zamu kwashe samari mu karasu akan dakarun mu,zamu yaƙi sansanin sojaji da yan sanda,babu wa'yanda zamu kyale da rai.yan mata ɗari da daya zamuyi garkuwa dasu duk wanda yazo kawo fansar su a kasheshi,yara matan kuma zamu maida su namu,ta border za'a shigo mana da manyan makamai,da kuma sauran mutanen mu duk ta jirgin ruwa zasu zo".cikin jinjina wa da girmamawa suka fara zuba mishi tafi,hannu ya daga musu ɗan su dakata.cak suka tsaya.
"Ku tabbatar da a cikin ku duk wanda ya bata mana aiki komin muƙaminsa a cikin Italian Mafia dole ze mutu,mutuwa kuma mara dadi".
A tare suka mike tsaye sunawa kansu kirarin ƙungiya su.
"we are the mafias!, blood shed blood!,we stand with our words!,the world is ours!,we choose who to live, and we choose who to die!, mafias are the most strongest union".suna gama anthem dinsu suka fara shan giya ana shagali.
Barrister Lameer ya ce"innalillahi wainna'ilaihi rajuun,to kunji abinda wa'yannan azzaluman suke shiryawa.sunan location din da suke shine,okir......."buge wani karfen ya yi ya fadi a ƙasa yabada sauti da seda suka ji.
Da karfi" sukace waye a wajen" ku duba ko waye sannan ku kashe shi,nan take Barrister Lameer ya fara salati domin yasan tunda suka ganshi kam na shi yazo karshe.fita a inda ya buya ya yi ya fara gudu yana son barin wajen,yana cikin gudun ya cire memory cikin wayar ya jefasa cikin bakinsa.nan ne video din ya dauke gaba daya.

Ransu ya matukar ɓaci lokaci daya kuma ya tashi,suna son kashe rayuwakan al'umma da basu ji ba ,basu gani ba.
Da Karfi LTG ya daki table din gabanshi da karfi ,idon sa ya yi jajir.
Furzar da iska me zafin gaske ya yi daga bakinsa.
Sudais shafa gashin kansa ya ce"wa'yannan sun riga da sun gama shirin su,babban abin takaici shine bamu san ya kamanin sabon shugaban nasu yake ba, yana da wayo yaƙi yarda a san fuskar sa,ba musan a wani lokaci ne zasu tayar da bom din ba yakamata mu dakatar da su".
"Duk wayon sa baze taɓa kaucewa tarkona ba,koma wanene shi se na kamosa na mishi hukunci dede da Abinda yake aikatawa"LTG ya faɗa yana miƙewa tsaye.yana kallonsu"Sudais dakai zan fara, suna kokarin shigo da mutanen su da mugayen mukamai ta border,you're comptroller General,nauyin dakatar dasu ya rataya a wuyanka kabada umarni duk wani abinda za'a tsallakar dashi border daga yanzu zuwa end of this month, ka sa a rufe border babu abinda za'a shigo dashi har se da sa hannunka,saboda you're comptroller General Sudais"jinjina kai Sudais ya yi.
Maida kallonsa kan Jawan ya yi "kai mataimakin commissioner of police ne,ka zuba jami'o'i ta ko ina bama iya garin nan ba da duk sauran state. communicate with your co assistant commissioner of police".

Gyada masa kai Jawan ya yi.pointing din Saghar da hannu ya yi"Saghar make sure ku ankara a hospital daga zarran kaga wa'yanda baka yarda dasu ba don't hesitate to inform me".

Yaci gaba da magana"bana son kowa yasan da shirin da muke yi so becarefull".

"In sha Allah LTG,zamuyi nasara akan su" "very good,nasanku bakwa wasa da aikin ku, rayuwakan al'umma shine muka shiga wannan aikin akai with any cost we have to save their life's"ya ƙarishe maganar yana rike kansa dake sara mishi.yana jin kan ya fara ciwo,amma bayanin da zeyi yana da matukar muhimmanci hakan yasa yaci gaba da maganar ba tare da ya dakata ba,amma shi kadai yasan yanda yake ji,abun a jininsa yake rashin dogon magana in ba ya zama dole ba,baya dogon magana.

Kallo ɗaya suka mishi suka fahimci kansa ya fara mishi ciwo.hannu Saghar ya sa a aljihunsa ya fito da maganin ciwon kai ya basa karba ya yi ya jefa abaki ya haɗiye.

"LTG!,make sure you drink water saboda maganin ya yi melting "hararansa ya yi"ba zan sha din ba,kufa doctor's din nan ko..."ya yi shuru yana zama,dariya sukayi Jawan da Saghar suka tafa.
"Ku de anyi yan air,yanzu de kunji maganar da LTG ya yi so concentrate"
"In sha Allah ".

karfe goma na dare kafin suka bar part din nasa cike da tunanin yanda zasu kawo karshen Italian Mafia.

Se 11:00pm suka baro wajen abbu nan ma seda Hajiya babba ta korasu,kafin suka tafi.

Basu shiga bedrooms din su ba suka
shigo nasu Sabriyah suna kwance suna bacci.
"Ayyah yau nasan sun yi missing din mu"gobe se mu haɗu.
Suka faɗa yana barin dakin, Parsa kashe musu wuta ta yi kafin ta bi bayan yan uwanta.


Washe gari bayan sun karya babu wanda ya fita aiki saboda su mom Rumanatu ana hanya sun kusan sauka.

Duk wani abinda ya dace da za'a karbesu an yi sa.

Karfe sha biyu na rana suka shigo gidan,bayan yan gaisa ne suka wuce masaukinsu, Ashman da Dawood a part din Sudais suka sauka.jaleelah da Iftisan part din su parsa suka sauka.

Sauka sukayi sukayi sallah sannan suka huta,bayan sun gama cin abinci ne aka dawo falo ana hira.
Hajjatiye da a jirgi tazo ba'a motar ba amma se bala'in ta gaji takeyi,su Hajiya babba suna mata sannu,Ammuh dake hakimce akan kujera tunda suka zo sannu da zuwa ta yi musu ba ta sake ce musu komai.

"Bak'ar annamimiya,dama nasan tsinannen bakin halinki be ze bari kice mini sannu,yau da zan faɗi in mutu da kin fi kowa murna,ke kam khareema kin yi asarar rayuwa.babu yanda kika iya dani nan gidan ƴa'ƴa nane se in sa ya sake ki inga tsiyar tsinantakar da ze faru,ni maye ma haka yaganni ya barni,bare kuma ke yar adama,mara mutunci kawai". shuru wajen ya yi babu wanda ya isa yace ta yi hakuri ta hakura, mutum na sa baki zata dawo kansa.
Su Ammi de ido suka zuba musu,tun lokacin da Abbie ya auro Hajiya khareema haka kurum basa shiri saboda girman kan Hajiya khareema.shisa Hajjatiye bata santa.

"Hajjatiye wai Ni kadai kika tsana a gidan nan ne!?,duk lokacin da kika zo se kin kwashemin albarka meye na miki da zafi haka ga su hamdiyya da Badeeya,ga Abida su baƙi tsane su ba se ni!?", Bude baƙi Hajjatiye ta yi alamar mamaki"lahaula wala quwata illabilah!, khareema yanzu zagina kike yi saboda ni ba uwarki bace shine zaki za ge kina zagina ko, tabbas Mubarak yau ni matarka take zagi saboda lalacewa yakai lalacewa"ta fashe da kuka,abinda suke gudu kenan da ace Ammuh ta yi shuru batace mata komai ba da Hajjatiye shuru zatayi in ta gaji dan kanta.
Dawuwa kujerar da take zaune Abbie ya yi ya hau bata hakuri,mom Rumanatu da abbu, uncle Hameed suka sa baƙi suka bata hakuri, dakyar

Please Login or Register in order to submit comment