Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya umarci Iluru da ya daka musu tsawa mai firgitarwa, Iluru ya daka musu tsawa wadda ta sa kasa ta rika girgiza duwatsu suka rika tartsatsin wuta,duk rundunar mayakan nan suka rude guri ya yamutse, can kuma aka natsu sannan Málukussaifi cikin sautin muryarsa ya ce “Kaicon ku marabkana 6atatttu gafalallu. Ina fadakashshe ku da yaki. Ko da rundunar nan süka ji haka sai maġanar nan ta tunzura su suka yi kansa gaba daya.
A wannan lokaci Malukussaifi ya harzuka ya yi kuwwa ya yi hamhama ya yi dandama gashin jikinsa ya mimmike idanuwansa suka kada suka yi jajawur ya bugi dokinsa shima ya yi kansu a fusace Iluru kuma yana tare shi. Koda haduwarsu ya fadamusu da sara, suma suka kifo a kansa da sara da suka da mashi, a wannan lokaci duk saran da aka kawo masa da suka sai Iluru ya kare ya maida makamin kan mai shi haka ya yi ta kashe su. Cikin sa'a guda ya halaka kimanin mutum dubu shida, a wannan lokaci Malukussaifi ya kasance yana jin dadin wannan yaki da yake har sai da ya sabi wata waka yana yi yana yaki.
Bayan sun samu sa'a hudu suna yaki sai korar Malukussaifi ta yi nisa har ya kai ga inda Sarki Shahazzaman yake. Ya dube shi ya yi masa jinjina. Koda Sarki Shahazzaman ya ganshi ya kuma ga irin yadda yake yaki da irin korar da yake kaiwa sai ya yi farin ciki da shi da rundunarsa sai suka kara samun kwarin gwiwa suka kara matsanta yaki. A ka yi ta gwabzawa har tsawon mako guda yi ake ba a daina ba.
A rana ta bakwai,lluru ya koma kan dutsen nah ya iske ARisa tana tare da Manniyatunnufusi da danta da Nurulhuda da Murjanatu da Kaukabu da saurna kuyangin nan masu rigar tashi ya ce da ARisa “Na zo ne domin na gaya miki kinga dan'uwanki ba zai bar wannan yakin ba sai ya ga ya kare wadannan kafuran kuma ga shi suna da yawa zail dade bai gama da su ba, kuma ga shi mu duk mun kosa da mu koma gida, shi ne to ni yanzu abin da nake so ki zo mu je ke ki rika fesawa mutanen nan wuta ni kuma zan rika jifan su da manyan duwatsu duk mu halaka su yaki ya kare kin ga sai ya hakura ya zo mu tafi”. Akisa ta yarda da wannan shawara ta Iluru suka taho wurin yakin suka baro Manniyatunnufusi da Kaukabu da Sauran kuyanginnan a kan dutsen nan.
Da zuwansu Akisa ta rika yi musu feshin wuta shi kuma Iluru ya rika jifansu da duwatsu suna mutuwa, cikin wani dan kankanin lokaci duk suka karar da mutanen nan sai kalilan daga cikinsu ne suka gudu suka sha da kyar.
Bayan da aka natsa sai suka shiga cikin birnin Dawariza tare da Sarki Shahazzaman da mutanensa suka wuce zuwa fada Sarki ya zauna, Malukussaifi yana zaune kusa da shi, sai Sarkin ya ce “Kai madallah da wannan taimako da ka yi mana domin ba don kai ba da bamu kaiba duk gaba dayan mu nan,kuma wannan ya kara tabbabtar min da gasgatawa bisa ga labarin girman lamarinka da na samu a baya, kai yakin ka yana da ban mamaki domin naga kawai mutane na faduwa matattu ba tare da ka kusance su ba ma".
Da Malukussaifi ya ji haka sai ya yi murmushi ya ce “Ai wannan dá ka gani aikin wasu kadimai na ne aljanu guda biyu ya yi kiran Iluru da Akisa suka zo gabansa suka tsaya ya tambaye su ya ce “Ina su Manniyatunnufusi suke?” lluru ya amsa masa ya ce “ai suna can bayan birni kan dutsen nan”. Ya umarce su suje su taho da su, cikin hanzari Iluru da Akisa suka nufi kan dutsen nan. Da zuwansu sai suka tarar duk ba sa nan suka neme su kasa ko sama babu ko daya daga cikinsu,sai suka dau oulo sauo Molukuecaifi ko da va ji wannan
labari sai hankalinsa ya tashi ya rasa abin da yake yi masa dadi, ya sunkuyar da kansa kasa ya yi shiru har zuwa wani lokaci sannan ya dago kansa ya dubi Sarki Shahazzaman ya ce yanzu ni zan tafi duk inda wadannan suka shiga sai na ncmo su in yaso daga baya na dawo kasarka". Ya tashi ya fito daga fada Hluru yazo ya ce “Ya shugabana ai ni yanzu muma bamu ga ta zama a nan ba ai duk inda zaka nemansu tarc zamu tafi".
Ya dubi Iluru ya ce “To ni yanzu ma ina zamu bi mu ncmo su?”Iluru ya ce “ai yanzu mu koma can kan dutsc nan muga ko maga no takin sawayensu". Iluru ya dauki Malukussaifi,Akisa tana biye da su suka koma kan dutscn nan suka yi laluben takin sawunsu basu gani ba. Suna cikin haka sai ga Sheihi Nurul'zaitun ya keto dutse ya fito ya zo gaban Malukussaifi ya tsaya. Koda Malukussaifi ya ganshi sai ya gaida shi ya kwashe labarin batan su Manniyatunnufusi ya gaya masa.
Sheihin ya dube shi ya ce "Matarka Manniyatunnufusi ubanta ne Sarki Abisul'abusi ya sa bokayensa suka turo wani aljani ya dauketa zai maida ita birnin matan nan da ka baro,su kuwa su Nurulhuda da Murjanatu da Kaukabu da sauran matan bokan nan Sha'asha'ana wanda ya turo sarakunan nan biyar su yaki Sarki Shahazzaman shi ne ya kama su". Yana gama wannan bayani sai ya bace.
Malukussaifi ya yi shiru yana tunanin yadda zai yi ya koma garin nan ga shi kuma ya riga ya bawa aljanin da ya kai shi wato Hairakana allonsa ya tafi.
To mai karatu sai ka yi hakuri damu domin shi wannan labari yana da yawa da gaske. Sai a nemi littafi na hudu (4)domin jin ci gaban wannan labari. Zai fito nan·ba da dadewa ba.
SANARWA
Jama'a akwai wani sabon littafi mai suna FAIRUZASHSHAHA zamu fito da shi nan ba da dadewa ba.
Shi wannan littafi ya kunshi labarin wani sarki mai suna Sarki Fairuza wanda yake haduwa da manya-manyan lamura na soyayya za jarumta da sauran ma'amiloli na rayuwar duniya.
ANA IYA SAMUN WANNAN LITTAFI A
GARBA MOHAMMAD BOOKSHOP
KASUWAR SABON GARI KANO
KOFA MAI KALLON BATA CAN CIKIN
KASUWA

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment