Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

la.
Akila ta ce “To yanzu dai kunga dama mijinku yana fifita ta dama akan ku ya fi sonta kuma ga shi ta gudu kun huta to yanzu yadda za'a yi zan sa wannan aljanin ya juye ya koma kamarninta ya kwanta idan mijinku ya dawo sai ku ce masa ai ita ce ta mutu danta kuma ku ce yana wajena”. Duk matan suka yarda da wannan shawara ta Akila, saboda gudun 6acin ran Malukussaifii game da su.
Kwana uku na cika da yamma sai ga jama'a duk sun dawo daga farauta aka rako sarki gida sannan duk ya sallami jama'a ya shiga cikin gida. Da shigarsa sai ya tarar duk matan sun taru waje daya sun yi jugun-jugun, ya tambaya ko lafiya,suka gaya masa ai Manniyatunnufusi ce ta mutu.bayan tafiyarsa. Koda jin haka sai ya kidi me ya rasa inda zai sa kansa ya rude, suka nuna masa aljanin nan dake kwance suka ce “Ga gawar nan".Ya zo ya bude fuskar aljanin sai ya ga ai lallai matarsa ce, ya fashe da kuka ya dauki gawar ya yi mata wanka ya binneta da kansa ya zauna gindin kabarin ya yi ta kuka har dare ya yi gari ya waye rana ta fadi har kwana uku yana gindin kabarin baya zuwa ko ina. Duk irin manyan fadawansa aka yi ta kirawo su suna rarrashinsa amma ina abin ya ci tura.
Da Damatu ta ga haka sai ta zo ta same shi ta gaya masa gaskiyar yadda duk lamarin ya faru a kan ba mutuwa ta yi ba gudu ta yi. Ko da ya ji haka sai ya tashi ya fita fada ya zauna.Nan da nan labari ya bazu cikin gari ai yau Sarki ya fito fada,kan kace mene ne wannan fada ta cika makil da jama'a duk aka yi shiru ana jiran a ji abin da zai ce. Zaune dama da shi ga Sarki Afarahu ga Sa'adunizamji ga Sabikussalasa, hagu da shi ga Sarki Abuttaj ga Maimunulhinjab ga Hurulwahashi.
Ya numfasa ya ce "Alhamdullahi matata Manniyatunnufusi ba mutuwa ta yi ba komawa ta yi garinsu,saboda haka gobc kowa ya shirya zamu tafi izuwa kasarsu mu dawo da ita". Aka ci gaba da fadanci har zwau wani lokaci sannan ya tashi ya shiga cikin gida duk jama'a suka watse kowa ya koma gida ya kama shirin tafiya kamar yadda Sarki ya umarce su.
A wannan daren duk ya yi sallama da matansa, gari na wayewa ya yi shiri ya fito ya tarar duk jama'a ta hadu ana jiran fitowarsa ya yi duba izuwa sadaukai mayakansa ya ga ga Sa'aduninzamji ga Maimunulhinjab ga Sabikussalasa ga Hurulwahashi da sauransadaukai runduna ta hadu yayi duba izuwa wazirinsa ya ga ga Sarki Afarahu ga Sarki Abuttaj sannan ya kuma duba izuwa malamansa ya ga ga Barnuhussahiri ga Akila tsakiyarsu kuma ga dansa Damaru ya shiga sulke yana tsaye sai murna ta kama shi ya sabi wata waka baiti hudu sannan ya sa densa gaba suka dunguma suka tafi.
Da fitarsu bayan birni sai suka ji wata tsawa daga sama duk aka dakata sai ga Akisa ta zo, ta matso kusa da Malukussaifi ta ce“Yanzu yanzun nan na samu labarin wannan tafiyar da zaka yi zuwa garin matarka Manninyatunnufusi shi ne na yi gaggawa domin na zo na sanar da kai labarin wannan gari da ka shirya zaka”. Koda ya ji haka sai ya ce“Madallah da ke wannan 'yar'uwa tawa maza ba ni labari na ji". Sai ta ce "Ai wannan labarin saimun koma fadar ka mun zauna sannan na gaya maka domin kuwa labarin yana bukatar natsuwa". Nan da nan ya ja runduna duk aka koma cikin birni aka sauka aka shiga fada aka zauna.
Bayan da duk aka zauna sai Akisa ta fara bada labari ta fara da cewa “shi wannan gari da zaka, asali sunansa Kahur koma daga nan kasar ka zuwa wannan gari tafiyar shekara talatin ce a doki, ada can a waonan garin an yi wani sarki sunansa Sarki Kahuru, ya baifi 'ya'ya guda biyu maza. Na farko sunansa Kasimulabusi na biyun kuma sunansa Abisul'abisi, shi wannan Sarki yana da wasu bokaye su dari uku da tamanin masu
yawan sihiri wanda saboda tsananin bokancinsu a wurin nan wanda yake tsakanin sama da kasa wato babila a nan suke zuwa nazarin bokancin su kuma na tabbatar maka kowane daya daga cikinsu ya fi duk bokayenka karfin sihiri.
Lokacin da Sarki Kahuru tsufa ya kama shi sai ya raba kasar biyu ya yi birane guda biyu Kashtuk da Mantus. Sai ya nada babban dansa wato Kasimul'abusi Sarki a birnin Kashtuk. Ya kuma nada karamin dan wato Abisul'abisi Sarki a birnin Mantus, sannan kuma ya raba bokayen nan izuwa ka shi biyu ya tura kashi daya Kashtuk kashi daya Mantus. Bayan wani dan kankamin lokaci Sarki Kahuru ya mutu.
Su kuma 'ya'yan kowannen ya ci gaba da mulki a kasarsa.Bayan wani dan lokaci sai Sarki Kasimul'abusi ya haifi 'ya'ya mata guda biyu kyawawa da matarka Manniyatunnufusi da Ranwarta mai suna Nurulhuda in ka gansu kamar su daya jama'a basa iya banbancewa tsakanin su in dai ba su suka banbanta maka ba da kansu kai ko uban nasu ma kansa baya iya banbancewa, sannan kuma tun lokacin da aka haife su Sarki Kasimul'abusi ya sallada rayuwarsa a kansu bayan son abin da zai tabasu ko da kankani ne.
Shima can Sarki Abisul'abisi aka haifa masa da namiji kyakkyawa ana kiransa da suna Abbasi shima tun lokacin da aka haife shi ubansa ya sakada rayuwarsa a kansa saboda kaunarsa da yake yi.
Bayan wasu shekaru wata rana Șarki Abisul'abisi yana zaune a fadarsa ana fadanci sai wazirinsa ya ce “Ran Sarki ya dade yanzu fa ina ganin dan nan naka Abbasi ya isa aure ina ganin ya kamata mu aurar da shi”. Sarki ya ce "Wannan magana taka haka take gaskiya ne, to yanzu wace yarinya zamu hada shi da ita?”Sai Waziinsa ya ce “Ai dama yaron ya same ni ya gaya min ya ce ai shi Manniyatunnufusi 'yar dan'uwanka Sarki Kasimul'abisi yake so”. Sarki ya yi murna da jin wannan maġana, nan da nan aka ta shi 'yan aike aka tura kasar Kashtuk domin su isar da muradin Abbasi dan Sarkinsu,aka rubuta takarda aka ba su suka tafi.
Da isar 'yan aiken nan birnin Kashtuk suka wuce fada aka yi musu iso suka shiga suka fadi gaban Sarki suka yi gaisuwa sannan suka gabatar da takardar da aka aiko su. Sarki ya bude takarda ya ga an rubuta daga dan'uwanka Sarki Abisul'abisi na rubuto wannan takarda ne domin na sanar da kai muna neman auren 'yarka Manniyatunnufisi ga danmu Abbasi.Ko da Sarkl Kasimul'abisi ya ji wannan magana sai ya yi murna ya sallami 'yan aike ya ce su koma su gayawa Sarkin su zai aiko da bayani daga baya. 'Yan aike suka koma. Bayan an tashi daga fadanci Sarki ya shiga gida sai ya kirawo Manniyatunnufisi ya ce da ita "Dan'uwana Sarki Abbisul'abisi ya aiko yana nemar aurenki ga dansa Abbasi, to shi ne na kirawo ki domin na tambayi ra'ayinki domin ina so na aurar da kè ga duk wanda kike so". Ta sunkuyar da kanta ta ce "Ni gaskiya ba na so na auri dan'uwana domin kuwa shi auren zumunta mafi akasari.daya yana zaluntar daya. Ko dai mijin ya zalunci matar ko kuma matar ta zalunci mijin, saboda haka ni bana sonsa. Kada ma a soma wannan lamari”. Da ya ji wannan ra'ayi nata sai ya sallameta ta tashi ta tafi ta koma cikin gida.
A washe gari Sarki ya fito fada ya zauna bayan duk jama'a sun yi gaisuwa kowa ya zauna, sai Sarki ya gaya musu, duk yadda suka yi da 'yarsa jiya da kuma rashin amincewarta a bisa ga wannan lamarin. Saboda haka sai ya ce "Ni kuwa tunda 'yata ta ce bata so, to nima bana son wannan lamari". A wannan lokacin Sarki ya sa aka rubuta talakarda. Zuwa ga Can'uwana Sarki Abisul'abisi bayan gaisuwa da fatan alberi a gareka na ga wasikarka ta neman auren 'yata to amma na nemi ra'ayinta amma bataamince ba saboda haka wannan magana ba zata yiwu ba, da fatan wannan ba zai sa ka samu damuwa ba.Da aka gama rubuta wannan takarda sai aka ta shi 'yan aike aka umarce su da su tafī birnin Mantus sukai takardar. Nan da nan suka karbi takardar suka shirya suka kama hanyarsu ta zuwa kasar Mantus wato kasar Sarki Abisul'abisi, bayan kwana uku suka isa cikin birni.
Da zuwansu suka wuce zuwa fada aka yi musu iso, suka shiga suka fadi gaban Sarki suka yi gaisuwa sannan suka mifa sakon Sarkinsu. Sarki ya kar6a ya karanta ko da ya ga abin da 'dan'uwansa ya rubuta na game da rashin amicewa da abin da ya nema sai ransa ya baci ya sallami 'yan åike suka tashi suka koma. Da fitar 'yan aiken nan sai Sarki yasa aka karanta takardar nan a fada kowa ya ji, duk fada sai ta yi tsit kamar ruwa ya ci su. V
Can bayan wani dan lokaci sai Wazirin nan ya ce “Ai wannan wulakanci ne yanzu har mu zamu nemi aure a hana mu, ai sam bazamu yarda da wannan ba domin kuma ídan wannan labari ya bazu cikin duniya ai abin aibu ne a gare mu”Sarki cikin fushi ya ce “To waziri yanzu yaya ina dabarar yadda zamu yi mu rama wannan?” Waziri ya duka ya ce “Ran Sarki ya dade ba dai mace muka nema aka hana mu ba,to yanzu yanda za'a yi ka kirawo bokayen ka ka umarce su da su aikata wani sihiri wanda zai sa duk matan da ke garin nasa duk gaba daya su komo garin nan, sannan kuma su sana'anta wani dako wanda duk matar da ta shigo nan ba zata iya fita ba,sannan kuma wani namiji ba shi da ikon shigowa wannan garin in dai bako ne”.
Nan da nan Sarki ya yi umarni aka kirawo masa bokayen nan nasa su dari da tamanin suka zo gabansa, bayan da suka yi gaisuwa sai Sarki ya umarce su da su je su aiwatar da sihirin da duk macen da take birnin Kashtuk wato birnin dan'uwansa ta taso ta komo nan garin domin mun nemi auren yarsa ya hana mu, sannan kuma bayan kun aikata wannan kuma ku yi wani kafi wanda in mace ta shigo bata da ikon fita, kuma wani namiji bako ba shi da ikon shigowa.” Bokayen nan suka amsa 'umarnin Sarki suka tashi suka koma zuwa hurumin bokancinsu suka kama aiki babu ji babu gani har tsawon'kwana arba'in sannan suka fito sun sana'anta wasu gammazai na tsafi wanda in dai suna nan namiji bai isa ya shigo birnin ba, aka sassaka su a duk Cofofin birnin. Kai ba ma mutum ba koalias: batisa
sannan kuma da dare ya yi sai suka dauko wani dan mutummutumi na bakin karfe suka daura masa igiya a wuya suna jan igiyar.
Koda suka fara jan igiyar nan sai duk matan kasar Kashtuk manya da yara har da ita kanta Manniyatunnufusi da kanwarta Nurulhuda duk suka dungumo suka komo kasar Mantus. Su kuma mazan aka jefesu da barci har duk matan suka fita ba su sani ba.
Bayan duk sun farka sai suka duba ko ina suka nemi matansu suka rasa, sai duk suka taru a fada, can shima Sarki bai ga 'ya'yansa ba da Manniyatunnufusi da Nuruluda ba sai ya fito fada ya zauna ana ta al'ajabin yadda wannan abu ya kasance haka, ana cikin haka sai Sarki ya aika aka kirawo masa shima nasa bokayen suma su dari da matanin. Da zuwansu Sarki ya nemi su sanar da shi yadda wannan abu ya kasance haka. Nan da nan bokayen nan suka buga tsafin su, sai suka gayawa Sarki suka ce “ai wannan aikin 'yan'uwan mu ne na-garin dan'uwanka Abisul'abisi shi ya umarce su da su aikata wannan aiki. Suka kwashe labari kaf suka gaya masa game da aikin bokayen Mantus.
Ko da sarki Kasimul'abusi ya ji haka sai ransa ya baci ya fusata sai ya ce da bokayen sa “To nima yanzu ina so ku aikata min kishiyar duk abin da dan'uwana ya aikata min". Nan da nan suma suka tashi suka koma hurumin bokancinsu,suka sana'anta gammazai wadanda duk namiji da ya shigo cikin birnin ba shi da ikon ya fita, kuma mace bata da ikon shigowa birnin, sannan kuma suka sana'anta wani kuge na bakin karfe,dare ya yi sai suka dauko kugen nan suka rika buga shi. Da fara bugawar su sai duk mazan da suke garin Mantus gaba daya har da Abbasi ďan Sarki Abisul'abisi suka dungumo suka koma kasar Kashtuk aka bar Sarki Abisul'abasi shi kadai da mata a kasarsa.
To bayan wani dan lokaci da Sarki Abisul'abisi ya ga duk garin sa sai mata, sai ya ji sam mulkin nasa baya jin dadinsa sai ya dauko babbar 'yar dan'uwansa Mannivatunnufusi
wadda a dalilinta ne duk wannan abu ya abku sai ya nada ta wakiliyarsa ita take gudanar da mulkin a bisa mata 'yan'uwanta.
Can kuma a kasar Kashtuk Sarki Kasimul'abusi ya samu labari daga bokayen nan cewa dan'uwansa ya nada 'yarsa wakiliyarsa, shima sai ya nada dansa Abbasi ya zama wakilinsa a wannan kasar. Da lokaci ya tsawaita Sarki Kasimul'abusi sai ya damu a bisa rashin ganin 'ya'yansa, sai ya kirawo bokayen nan ya gaya musu shi dai yana so ya samu hanyar da zai rika ganin 'ya'yansa. Sai bokayen suka ce “To yanzu zamu sana'anta wata gona mutsafeta can nesa da wadannan birane namu sannan zamu sana'anta musu wasu riguna na tashi wadda za su rika tashi suna zuwa can kuna ganawa da 'ya'yanka duk lokacin da kaso”. Sarki ya yi farin ciki da jin wannan, ya kuma umarce su da su aikata.
Bokayen nan suka tashi cikin dare tafiyar shekara goma suka yanke ta cikin wannan daren suka je suka sana'anta gonar cikin wasu 'yan kwanaki sannan suka kafeta da asirinda babu mai shigarta in ba wadanda aka yi ta domin su ba, sannan suka komo suka aikata wani sihiri suka samo sunayen kuyangin Manniyatunnufusi su talatin da bakwai suka sana'anta riguna guda arba'in da daya suka debo rigunan suka kawowa sarki suka ce “Wadannan rigunan idan suka saka su tafiyar shekara goma zaku yi ta a kwana uku sannan kuma kowace riga mun yi ta da sunan wanda zai yi amfani da ita, daya mun yi ta da sunanka biyu kuma mun yi su da sunanan babbar yarka Manniyatunnufusi daya kuma mun yi ta da, sunan karamar 'yarka Nurulhuda. Sannan kuma sauran mun yi su da sunan kuyangin su". Ko da Sarki ya ji an yi wannan gonar kuma ga wadannan rigunan sai ya san talai ya samu hanyar 'ganin 'ya'yansa, saí dai kuma sai ya yi tunani yaya za a yi a kai wa 'ya'yan wadannan rigunan kasar Mantus sai nan da nan ransa ya baci ya tambayi bokayen ya ce "To yanzu kuma yaya za a yi wadannan riguna su tarar da 'ya'yana?" Bokayen suka ce “Ai kar ka damu lokacin mu na tafiya nazari Babila ya yi zamu
hadu da 'yan'uwanmu bokayen Rasar Mantus mu tafi to a wannan lokaci za mu ba su rigunan su kai musu". Sarki ya yi farin ciki Rwarai da wannan lamari.
A wannan lokaci shi kuma Abbasi dan Sarki Abisul'abisi sai ciwon begen rashin auren Mahniyatunnufusi ya tuke shi ya mutu nan da nan labari ya iske ubansa can a kasar Mantus, jin wannan labari nan take bakin ciki ya tuke shi, shi ma ya mutu.Manniyatunnufusi ta dare kan gadon sarautar kasar sosai ta rika shimfida mulki son ranta.
Yayin da lokacin tafiyar bokayen nan wurin nazarin su ya yi sai suka yi shiri suka fito daga cikin birnin Kashtuk suma can na bimin Mantus sun fito suka hadu suna ta labarin irin aikin da suka ka yi wa biranen nan guda biyu. A wannan lokaci sai suka bada rigunan nan ga bokayen kasar Mantus suka ce "Kafin mu tafi Babila wurin nazarinmu ku kaiwa sarauniya Manniyatu wadannan rigunan”. Sannan suka yi musu bayanin amfaninsu da duk dalilan da ya sa aka yi su, suka ce su gaya mata. Nan da nan daya daga cikin bokayen kasar Mantus ya kar6i rigunan ya koma ya kaiwa sarauniya ya kuma yi mata duk bayanai game da rigunan ya komo suka tashi su dari uku da sittin suka nufi Babila wajen nazarinsu.
Ita kuwa Sarauniya da ta ga wadannan riguna ta ji amfaninsu sai ta yi farin ciki da samun hanyar da zata rika ganin ubanta nan ta sa aka kirawo mata kuyangin nan nata wadanda aka yi rigunan nan da sunansu ta raba musu rigunan ta kuma gaya musu amfaninsu, sannan kuma ta mikawa Kanwarta tata. Ita kuma ta kwashi nata guda biyu, sannan aka ci gaba da fadanci.
Gari na wayewa ta umarci duk kuyangin nan kowacce ta saka rigarta duk suka saka ita mata ta tata kanwarta ma tasa suka ta tashi suka nufi gonar nan ta tsafi wadda bokaye suka basu labarinta. Suka je kuwa suka iske gonar kamar yadda aka ba su labarinta suka shiga suka yi ta zagawa cikinta ta kawatar da su kwarai. A ranar da suke shirin barin gonar su koma gida,sai ga ubansu Sarki Kasimul'abisi shi kadai yana sanye da
rigarsa ya zo gonar shima. Da ganinsu sai farin ciki ya kama shi na ganin 'ya'yansa bayan rashin ganinsu na tsawon wani lokaci, suka sake zama tare da mahaifinsu da kuyanginsu bar wasu 'yan kwanaki sannan suka rabu shi ya koma garinsa suma suka koma garinsu. To haka dai wahnan gona ta zamar musu mahada. Kuma wannan gona ita ce wadda na zo wucewa da kai ka sa ni na sauke ka har ka ganta ka dauko ta”.
Akisa ta kara da cewa “To kaga kuwa kai da mayakan nan naka zuwa wannan kasa ya yi muku nisa kuma koma kun je ta yaya zaku yi ku shiga garin? Kuma wadannan bokayen naka sanin ya wuce na su. Saboda haka ni dai ina baka shawarar ka hakuura da wannan tafiyar”.
Duk fada ta yi tsit da jin wannan labari na Akisa,Malukussaifi ya yi shiru yana tunani. Can sai ya dago kansa ya dubi Akisa ya ce “Mutanena zan barsu a nan amma ni kan babu makawa sai na tafi wannan gari Mantus kuma kema ban dauke miki ba da ke zamu tafi ki rakani”, Saboda sanin halinsa na kafewa akan abin da ya sa kansa Akisa sai bata musa ba ta ce “To na yarda zan raka ka, to amma mu bari sai gobe mu tafi domin na koma gida na yi yo sallama da iyayena.” Ya amsa ya sallameta ya ce “Sai goben je ki”. Ta tashi ta tafi.
Gari na wayewa Malukussaifi ya fito fada ya zauna.Zamansa ke da wuya sai ga Akisa ta zo ta yi masa sallama ya amsa mata ya ce “Har kin zo?” ta ce “I”. Ya ce to bari na yi sallama da mutanena mu tafi ko?” Sai Akisa ta ce “To ai yanzu ma ina allonka yake ka dauko shi ka kirawo Iluru domin mu tafi tare da shi ya taimaka mana”. Sai ya ce ai allona tuni uwata ta rabani da shi ta yaudare ni ta bani wani na jabu ta gudu da shi bayan ta jazo sanadiyyar kashe matata Nahidu yanzu ban sna inda ta ke ba”.
Koda Akisa ta ji wannan lahari sai ta yi bakin ciki ta ce “To yanzu kafin mu yi wannan tafiya zan fita neman uwarka kuma a duk inda na ganta na rantse da dalasiman da suke jikin hatimin Annabi Sulaimana(A.S.)sai na kashe ta”. Sai ya ce “A a ni dai ban ce ki kashe ta ba ki kamota kawai”. Akisa ta ce
ka tuna fa ita wannan uwa taka ba fa kaunarka take yi ba, ko yaushe tana jefa ka halaka, tana wahalar da ni wajen kubutar da kai. Sabo haka ni dia yanzu ko kana so ko baka so ni dia sia na kasheta”. Ya ce “Ni dai na gaya miki kada ki kuskura ki kashe min uwa”.
A wannan lokaci Akisa ta bazama ta yi ta yawo kasa-kasa tana tambayar labarin Kamriyya wurin aljanu, amma bta smau ba.Can tana cikin wannan hali sai ta gamu da wnai tsohon aljani ta tambaye shi, ya gaya mata ai Kamriyya tana birnin Sin. Akisa ta sake bazama ta nufi birnin Sin, da zuwanta ta smau aljanun wannan kasa ta tambaye su suka kwashe labarin Kamriyya kaf suka gaya mata.
A wannan lokacin Akisa ta dawo Yemen ta iske Malukussaifi yana zaune a fada da jama'arsa ta yi masa sallama ta ce “Nazo maka da labarin uwarka, amma ba zan gaya maka ba sai ka lamince min da na kashe ta in na kamata”.Koda ya ji ta ce ta samo labarinta sai ya ce “To maza gaya min labarinta”.
Akisa ta cè “Uwarka dai tun a daren nan da aka kashe Nahįdu ta dauko allon nan ta goga Iluru ya zo ta umarce shi da ya dauke ta ya kai ta birnin Sin wato kasar Uban Nahidu Sarki Samsamu. Iluru ya dauketa ta kaita, da zuwanta ta wuce zuwa gidan Sarki cikin daren, ta tarar da duk kofofi a kulle, sia ta sake gogo allon Iluru ya zo ta umarce shi da ya shigar da ita ya kaita kuma cikin dakin da Sarki Samsamu yake kwance, nan danan ya dauke ta ya shigar da ita ya kai ta kuma cikin dakin da Sarkin ke kwance, sanan ta sallame shi. Motsin shigowarta ya farkar da Sarki Samsamu daga barci ya tashi zaune ya ga Kamriyya ya zuba mata ido yana kallonta. Ya ganta gata kyakkyawa kuma ya yi mamakin yaya a kai har ta shigo dakinsa, sia ya tambayeta ta ce “Ke kuwa mutum ce ko aljana,kuma me ya kawo ki nan wurina a daidai wannan lokaci?”Kamriyya ta amsa masa ta ce ni mutum ce ba aljana ba ce ni kuma suna nan Kamriyya, kuma ni mutuniyar kasar Yemen ce,kuma na zo ne domin na cika burina, kuma na gaya maka
Sarkin garin mu wato Malukussaifi wanda ya taba zuwa nan gairn ya yi wa 'yar Nahidu magani ta warke daga makanta ka aura mas aita to yanzu ya ci amanarka ya kashe wannan 'ya laka Nahiru.Bukatata kuwa ni ita ce tun wnai zamani mai Isawo nake samun labarin ka da irin karfin mulkinka da kasaitarka a wurin fatake to ni kuma sia begenka ya mamaye zuciyata na ji ni a duk duniyar nan babu wanda nake so na aura in ba kai ba, saboda haka yanzu ina rokonka da ka cika mini burina ka aure ni.
Bayan ka aureni kuma ina so ka shirya ka tafi izuwa Yemen domin daukar fansa wurin Malukussaifi, ni kuma zan taimaka maka duk.duk wani irin taimako da zaka bukata wajen yakar Malukussaifi. Kai/zan ma nemar maka taimako daga wurin babban Sarkin yankin mu wato Sarki Saifu'ar'adu Sarkin Habasha gaba daya.
Sarki Samsamu ya yi shriu ya dubi Kamriyya ya ga duk irin zati na kyau da ake nema game da mace na Kamriyya ya wuce nan, nan da nan sia shima ya shagala da begenta. Ya ce da ita "To na yarda zan aure ki, to yaya akai har kika iya tahowa daga Yemen zuwa nan cikin wannan dan kankanin lokaci?"Kamriyya ta ba shi labarin allon lluru ta gaya masa shi ya kawo ta kuma ta ce mà zata ba shi allon idan ya'yi shirin lahowa daukar fansar 'yarsa Nahidu. To ka ji wannan shi nc labarin uwarka”.
Malukussaifi ya yi bakin ciki da jin wannan labari. Barnuhu ya ce da shi. “Kwantar da hankalinka yanzu ni zamu tafi da ni a Akisa zan sato wannan allon a yau din nan”. Malukussaifi ya yi musu izini da su tafi, nan da nan Barnuhu ya hau taguwar nan tasa suka tashi sama shi da Akisa suka tafi kasar Sin ciikin gaggawa cikin wasu 'yan sa'o'i suka isa kasar, suka zauna a bayan birni har sai da dare ya yi ya rába sannan suka shigo cikin birni suka shigo gidan Sarki babu wanda ya gansu suka wuce har zuwa dakin da sarki suke kwance shi da Kamriyyar suna barci nan da nan Barnuhu ya yi musu wani siddabaru ya rikide va zama macjii va shiga cikin dakin ya nuti inda
kwance ya mika hannu ya kwance allon Iluru

Please Login or Register in order to submit comment