Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ya ga wani dan tafki da aka yi shi domin linkaya. Ya matsa ya je bakin Rofar gidan ya bude ya shiga da shigarsa sai ya ga gidan an shimfide shi da kilisai da kujeru da tebura na alfarma, ya hau kan wata kujera ya zauna yana mamakin irin kawatar da wannan gida da aka yi.
Ana cikin haka sai ya ji motsi sai ya tuna Akisa ta ce kar ya yarda wani ya ganshi sai ya yi wuf ya fito waje ya koma cikin ciyawa ya buya yana hangen inda wannan motsi da ya ji yake.Jim kadan sai ya ga wasu 'yan mata sun taho a sama kamar tsuntsayc suna sanye da wata riga ta gashi mai fukafukai, sai ya ga duk sun sauka akan wannan farin dutsen nan mai kujeru,kowacce ta zauna bisa kujera daya sai ya ga wata wadda duk tafi sauran kyau ta zauna a tsakiyarsu akan kujcrar da lafi kowacce girma ya dubeta ya ga lana da matukar kyawun fuska ga manyan idanuwa farare tas ga kwayar idonta mai matsanancin baki ga yawan gashin gira da gashin kai, ya yi duba izuwa kirjinta ya iske shi cike da nono a tsaitsaye, sa'an nan ya yi duba izuwa mararta ya ganta a dame kamar tsakiyar kalangu, ya kara duba izuwa kugunta ya iske mai fadi kamar wasu kididdigaggun zura'i a cike, ya kuma duba izuwa kafafunta ya gansu a tsaye car kamar mashi.
A wannan lokaci sai ya dimauce saboda tun da yake a rayuwarsa bai taba ganin mace mai kyan siffa da cikar zati irinta ba. Cikin hanzari sai ya fito daga cikin gonar ya komo wurin Akisa ya kwashe labari kaf ya gaya mata ya kare da cewa “Ke nifa naga wurin zama nifa a nan zan zauna har karshen rayuwata domin na shagalta da bengen wannan varinya da na gani". Ta ce da shi "Haba ya dan'uwana kada ganin 'ya mace ya shagaltar da kai ga barin masarautarka mana da sauran matayenka da kuma danka Damaru mana". Sai ya

nisa ya ce da ita “To, Akisa ki taimaka min mana na mallaki wannan yarinyar mana. Ni dai wallahi ina sonta". Ta ce da shi ai sam ba zai yuwu ba domin ita bata da ikon shiga wannan gonar.
Jin wannan magana ta Akisa sai ya fashe da kukan asararta da zai yi, sai ya sabi waka yana kuka yana bege. Ganin haka sai Akisa tausayinsa ya kamata sai ta ce “Yi shiru dan'uwana zan gaya maka yadda za ka yi ka dauko ta”. Jin haka sai ya yi shiru ya daina kuka, sannan Akisa ta ce “Ita dai wannan yarinya da ka gano sunanta Manniyatunnufusi 'yar Sarki Kasimul'abusi, yanzu yadda za ka yi ka koma cikin gonar a 6oye ka lalla6a ka haukan farin dutsen nan ka dauke wannan rigar tat tgashi ka sakko ka buya a wani gun da koda sunyi bincike ba za su ganka ba, domin ita wannan riga wasu bokayen ubanta ya sa suka sana'anta musu su wadda idan sun sakata za su tashi sama kuma tafiyar shekara goma suna iya yinta cikin wuni daya da wannan rigar. Sannan kuma kowacce rigarta da sunanta aka yi ta saboda haka ta wata ba taiwa wata amfani, tò kaga bayan sun gama abin da suke suka hau dutsen nan da nufin su tafi gida kowacce ta sa rigarta ita kuma zasu ga basu ga tata ba, za su yi bincike in ba su sameta ba za su tashi su tafi da nufin su dauko wata mata domin ita biyu aka yi mata rigar to da ka ga sun tafi kai kuma sai ka fito ka tsaya nesa da ita ka nuna mata rigar, da ta ganta zata yiwo kanka da nufin ta kwace kai kuma sai ka juyo a guje ka fito daga gonar da kun fito sai ka juya ka kamata domin in ka sake ta kama ka a cikingonar to tafi karfinka saboda dakon da aka yi zata halaka ka in kuwa kun fito daga gonar to bata da wani tasiri a kanka".
Ya yi farin ciki da jin wannan dabara ta Akisa nan da nan ya koma cikin gonar nan ya kama sanda da labe-labe yana addu'ar neman nasara a bisa muradinsa, sai ya hangi 'yan matan nan dukkan su sun tube kayansu sun shiga tafkin nan suna wanka, sai ya lababa ya hau kan dutsen ya dauke rigar nan kamar yadda Akisa ta gaya masa ya sauko ba tare da sun
11
gan shi ba, suna ta wanka ya samu wani wuri ya make yana
kallonsu.
Bayan da 'yan matan nan duk suka fito daga ruwa sai duk suka nufi dutsen nan kowacce ta sa kayanta ta dauki rigar gashinta ta dora sai Manniyatunnufusi bayan ta sa kayanta sai ta nemi rigar gashin ta ta rasa suka ta duba kasa ko sama ba'a samu riga ba sai ta umarci sauran 'yan mata n da su koma gida su dauko mata wata, nan da nan duk suka tashi suka tafi suka barta a nan a zaune.
Bayan tafiyar su zuwa wani dan lokaci sai Malukussaifi ya fito daga inda ya ke labe da rigar a hannunsa sai ya nuna mata sigar. Ko da ta ganshi sai ta nufo shi a fusace, sai shi kuma ya juya a guje suka rifa tana binsa har suka fito daga cikin gonar,suna fitowa sai ya juyo ya yi wuf ya danketa ta yi ta kici-kici ta kwace amma ina ta kasa har ta gaji, ganin haka sai Akisa ta matso kusa dasu ta ce “Haba ya ma'abociyar kyau yaya krke neman gudu daga zuciyar da take yawan bengenki, ki sani fa shi wannan dan'uwa nawa ba yana nufin cutar da ke ba ne,kaunarki ce ta sa ya aikata miki wannan domin in ba da hakan ba ba shi da yadda zai kusanta da ke balantana har ya yi zance da ke, kuma ki sani ya canci ya neme ki domin kuwa shi ma ya kasance madaukaki kamar ke shima sarki ne babba mai manya-manyan lamari na daga rayuwar duniya". Akisa bata gushe ba tana ta rarrashinta tana gaya mata kalamai masu dadi na yabo da kambamata har sai da zuciyarta ta yi sanyi jikinta ya mutu.
Sannan ta yi duba izuwa Malukussaifi ta gan shi kyakkyawa wanda bata taba ganin wani dan adam mai kyauwunsa ba sai ta tambaye shi ta ce “to kai yanzu mai kake nufin yi da ni da har ka kama ni?” Ya amsa mata da cewa "Na kamaki ne ba don nufin wani abu ba ne illa kawai don ina so na auręki." Da Manniyatunnufusi ta ji wannan magana ta sa sai ta natsa cikin tunani a cikin zuciyarta ta ce "To shi dai wannan mutum kyakkyawa ne kuma ba wulakantacce ba ne an ce Sarki ne, to bari na yarda na aure shi tun da na san ko daga bava
mutanen kasata sun sami labari na san idan suka gan shi ba za su aibatani bisa aurcnsa da na yi ba". Sai ta dago kanta ta ce "To ai shi ke nan na yarda
Rufe bakinta ke da wuya sai Akisa ta kwashe su ta yi sama da su bata zame ko ina ba sai kan tsaunin nan gidan bakin aljanin nan Muftadihu wanda Malukussaifi ya kashe shi ya ku6utar da 'yan matid nan su Nahidu ta sauke su. A cikin gidan, da gadaje da kujeru da shimfidu na alfarma, sannan ta kawo turaruka iri daban-daban kamar su muski da wardi da alfursan, gida ya kawata sannan aka kawo wani katon gado na jan dinari aka ajiye a dakin da suke.
Bayan haka kuma Akisa ta sa aka kirawo malaman aljanu na fadar ubanta suka daura auren Malukussaifi da Manmiyatunnufusi, nan aljanu suka barke da biki ana ta kide-kide da raye-raye irin na aljanu har zuwa wasu 'yan kwanaki,sannan aka gama biki ango da amarya suka ci gaba da zaman amarcinsu, aljanu suna ta yi musu hidima.
Wata rana Malukussaifi da amaryarsa suna zaune suna hira sai ta ce da shi “to kai ka ce kai sarki ne kai kana da kasarka to me yá sa muke zaune a nan? Ba gara mu koma zuwa kasartaka ba mu zauna cikin mutanc 'yan'uwanmu ba, amma ma zauna nan cikin aljanu". Sai ya ce “Lallai kin yi gaskiya, to bari wannar 'yar'uwar tawa ta zo ta kaimu”. Rufe bakinsa ke da wuya sai ga Akisa ta shigo, bayan sun gaisa sai ya gaya mata yanaso ta dauke su ta kaisu Yemen domin yasan yanzu mutanensa suna can suna jiransa.
Akisa ta dauke su ta kama hanyar komawa Yemen da su,suna cikin tafiya sai suka zo wani waje sai Akisa ta tsaya,jin ta tsaya sai ya tambayeta ya ce "Ya 'yar'uwata me ya tsaida ke a nan?” Sai ta ce “Ai mantuwa na yi domin ita wannan hanyar da na biyo akwai wani dako wanda bana iya ratse shi saboda haka yanzu zamu koma baya na sake hanya”. Jin haka sai ya ce “Ai kawai kada ki koma ki sauke mu kasa kawai mu ci gaba da tafiya da kafarmu domin ma na dade ban yi tafiya a kafa ba kuma yanzu ina sha'awar na yi”.
Akisa ta ki yarda saboda gudun kar ta saukc su wani abu ya same su, amma ya takura mata dole ta saukc su a gabar kogi suka yi sallama ta tafi ta barsu shi da matarsa a nan. Suka ci gaba da tafiya shi da matarsa suna bin gefen kogi sai suka z0wani waje mai sanyi ga bishiyun kwakwa ko'ina sai suka zauna a nan domin su huta, suka debo kwakwar nan, da ya fasa kwakwa daya cikinta sai ya ga nono ne madara fara tas, ya kuma fasa wata sai ya ga zuma ne a cikinta nan suka kwana uku 'ya'yan kwakwar nan suka zama abincin su.
A rana ta hudu da gari ya waye sai suka dcbi 'ya'yan kwakwar nan saka yi guzuri da su suka kama hanya suka ci gaba da tafiya..Bayan wasu 'yan kwanaki 'ya'yan kwakwar nan da suka yi guzuri da su suka karc sai suka shiga farautar bareyi suna yankawa suna ci. Tafiya ta yi tafiya har suka zo wani waje in da nan kuma rairayi nc fululu a wajcn. Gia shi ba guzuri sannan kuma rana ta bude duk rairayin nan ya yi zafi sai huci kawai ke fita ta ko'ina tsananin kishirwa da yunwa ya tsananta a gare su sai suka kara matsawa gabar kogin domin su sha ruwa da suka sha ruwan sai suka ji ruwan dandanonsa na gishiri ne maimakon ya'yaye musu kishirwa sai ya kara musu.
A nan fa daya ga zasu halaka sai ya daga kansa sama ya sabi wata waka yana addud'ar Allah ya fitar da su daga wannan hali, bai gama addu'arsa ba sai ya hango wasu manyan jiragen ruwa guda uku sun nufo inda sukc. Da isowar jiragcn nan sai ya ga daya cike yake da dawaki daya kuma kayan abin cine kawai a ciki daya kuma sai ya ga mutanc nen maki a eiki,ko da jiragen suka zo kusa sai ya ga ashe Sarki Abuttaj nc da sadaukansa, sai ya yi farin ciki ya kama hannun matarsa suka shiga cikin jirgin da shigarsu duk jama'ar nan da shi kansa Sarki Abuttaj suka yi gaisuwa a wurinsa aka ba su waje suka zauna.
Sarki Abuttaj ya ce “Ai tun a ranar da muka ta shi muka ga bamu ganka ba sai muka je wajen Barnuhu muka shaida masa sai ya ce kowa ya zauna shi zai kiyaye jama'a daga makircin Kamriyya, sannan ni kuma ya umarce ni da na taho da runduna
mu shigo jirage mu yi gabas zamu gamu da kai shi ne m taho muke ta tafiya sai yau ga shi kuwa AMah Ya hada mu".Shima ya kwashe labarin duk abin da ya faru gare shi da auro Manniyatunnufusi da ya yi ya gaya musu sannan suka juya jirage suka koma izuwa gabar birnin Yemen. Bayan wasu 'yan kwanaki suka zo gabar Yemen aka fito da dawaki suka hau suka kama hanyar tafiya cikin birnin Yemen, daga nan kuma zuwa birnin tafiyar kwana uku ce.
A wannan rana kuma 'yan aiken babban Sarki Saifu'ar'adu wato bokaycn nan guda biyu Sakaradisa da Sakaradiyyuna da sadaukan nan guda uku Maimunulhinjab da Sabikussalasa da Hurulwahashi da hokayen Ashhas su tamanin da rundunar mayaka dubu goma suka iso kasar Yemen, da zuwansu sai suka iskc garin kogi ya zagayc katangar birnin ba damar shiga,ko da suka ga haka sai, bokayen nan tamann suka ce"Wannan duk aikin Barnuhu nc, amma cikin daren nan duk zamu lalata shi.
Nan da nan bokayen nan suka dukufa kan bokancin su sai suka yi wasu alluna guda bakwai, sannan suka zana wasu dalasamai guda arba'in akan takardar sai suka jefa wadannan allunan cikin wannan ruwan da ya gcwayc garin sai duk ruwan ya kafc,sannan kuma suka jcfa wannan takardar ta tashi sama.
Can kuma a cikin birnin labarin tuni ya je da kuma abin da suka aikata, Barnuhu da Sa'aduninzamji da Sarki Afarahu da sauran jama'ar gari duk aka yi ciko-cirko. Barnuhu ya ce “Ai kuwa da nasan za su bata wannan kafi nawa da na yi wani daban bayan shi, na san yanzu babu shakka wadannan suna tarc da irin mutancn kasarmu". Sa'aduninzamji ya ce “Ai kar ka kuma wahalar da kanka wajct yin wani abu ka kyale mu da su kawai gobc mu yakc su mu shayar da su gidauniyar halaka kawai”.
Giari na waycwa Sa'aduninzamji ya yi shiri ya zuba.sulkensa aka kawo masa wani ingarman doki dan gaskc ya hau jama'arsa da Barnuhu da Şarki Afarahu suma suka yi shirin yaki suka fita bayan birni suka kafa sansani Sa'aduninzamji ya
fito tsakiyar filin daga ya ya yi kwuruwa ya yi gunji ya yi wa kansa kirari ya nuna su ya ce mai jin kansa ya fito sai Maimunu bisa toron giwarsa ya fito yana hamhama yana gurnani suka zabura suka yi kan juna sai da suka kusa haduwa sai dokin Sa'aduni ya ji tsoron giwa ya juya. Haka dai suka yi ta zagaye-zagaye har dare amma basu hadu ba sannan kowan nen su ya koma sansanin su ya sauka.
Da Maimunu ya koma sansaninsa sai boka Sakaradisa ya ce “Ya maimunu ai ka yi hanzari yaya daga zuwa zaka fara fita bayan kuma kai duk kai ne gaba da duk sadaukan nan da muka zo da su, ai yanzu ma idan ka kama shi su wadannan sauran sadaukan da muka zo da su sai su cika mana baki su ce ai suma da an barsu sun fita da za su iya kama shin, saboda haka yanzu gobe ba kai zaka fita ba ka zauna har sai in sabikussalasa da Hurulwahashi sun kasa sannan kai sai ka fita". Haka suka tsaida wannan shawara.
Can su kuma yayin da Sa'aduni ya koma sai barnuhu ya ce “To kai Sa'adupi sai ka zauna gobe Sarki Afarahu ya fita fagen fama.”Sa'aduni ya ce “Ai na rantse da Ubangijin mu Allah in dai har'ina numfashi ba zan bar daya daga cikinku ya yi yaki ba in dai na fito na fito ne ni zan fita ku kawai ku yi kaHo tsaron rayukan ku yana wuyana." Da Barnuhu da Sarki Afarahu suka ji ya yi rantsuwa sai suka kyale shi suka yarda akan haka.
Wayewar gari ke da wuya Sa'aduni ya fito fagen fama kai inka ganshi ka ce wani shaidani ne ya yi kuwwa ya ce ina wai wanda kwanansa ya kare ya fito, sai wani sadauki ya zaburo ya fito Sa'aduni ya kifo a kansa nan da nan ya sarekansa, wani ma ya sake fitowa sa'aduni ya kashe shi goma gaba daya suka sake fito wa ba tare da bata lokaci ba suma ya gama da su kai kafin dai ran ata fadi sai da Sa'aduni ya kashe mutum dari uku da saba'in sannan ya juya ya koma sansaninsu.
Su kuma can sai boka Sakaradisa ya ce “Kai ai in kuwa muka ce daya bayan daya zamu rika shiga to ba makawa
wannan mutumin zai yi mana barna, ai gobe ku shigar masa
gaba daya ku kama shi”.
Gari na wayewa Sa'aduni ya fito ya tsaya fagen fama sai duk jama'ar nan su dubu tara da dari shida ta talatin suka yiwo kansa gaba daya. Bokayen nan biyu da Maimunu da SabiRussalasa da Hurulwahashi da bokayen nan tamanin suka tsaya suna kallon yadda za su yi da shi.
Da Barnuhu ya ga sun nufo shi gaba daya sai suma suka danno gaba daya aka hadu wuri ya yamutse kura ta turnuke Sa'aduni duk inda ya juya sai kaga kawunan mutane na zuba kasa. Aka yi ta yaki har dare ya šhiga ba'a rabu ba a wannan lokaci sai boka Sakaradisa ya umarci Maimunu da Sabikussalasa da Hurulwahashi da su shiga yakin suma, nan da nan suka ishiga suka yi ta barna ganin haka sai hankalin Sa'aduni ya tashi saboda irin barnar da ya ga wadannan maune guda uku sunai musu, kuma ga shi ya yi yaki ya gaji a wannan lokaci sai ya rika yaki yana wata addu'a ta neman nasara. Bai gama addu'arsa ba sai suka hango wata kura ta tokare sama,jim kadan sai suka hango wata runduna ta mayaka sun nufo wajen.
Ita wannan runduņa kuwa Malukussaifi ne da Sarki Abuttaj da jama'arsa suka Raraso da suka kusanta sai suka rika jin sautin muryar Sa'aduni yana kuwwa,sai Malukussaifi ya ce “wannan muryar Sa'aduni cé lallai babu lafiya mu yi gagawa mukai masa dauki nan suka sau linzamin dawakinsu suka kutso suna kabbara da zuwansu suka shiga yakin suka hau abokan gaba da sara, sabóda dadewar da Malukussaifi ya yi bai yi yaki ba sai ya rika murna yana yaki cikin nishadi duk in da ya juya sai jikkunan mutane ke faduwa kasa kawai ya sa6i wata waka yana yi yana yaki,
Haka shima Sarki Abuttaj ya yi ta sara yana yanke kawunan abokan gaba. Ko da Sa'aduni ya jiyo muryar Malukussaifi sai ya san lalai ya dawo kuma yana wannan yakin, sai ya ji duk gajiyar da ya yi ta sake shi ya ji wani sabon karfi ya zo masa ya kuma kifuwa akan abokan gaba, cikin dai wannan dare sai
da suka kashe mutum dubu hudu da dari biyu sannan aka rabu kowa ya koma sansani. Bayan da suka koma Sa'aduni da Barnuhu da sarki Afarahu suka zo suka yi mubayi'a wajen Malukussaifi ya kwashe labarin sa kaf ya gaya musu sannan kuma ya nuna musu matarsa da ya auro wato Manniyatunnufusi.Haka suka yi ta hira,can sai Sa'aduni ya ce “Kai amma kuwa akwai wani sadauki a cikin mutanen can kai amma ina ma zai musulunta ya komo daga cikinmu”. Da Barnuhu ya ji wannan magana sai ya ce to in haka ne daga yanzu daga cikin manyan sadaukan can nasu duk wanda muka kama kada mu kashe shi, ku kamo shi mu sanar da shi musulunci in ya karba ya tsira in kuma bai kar6a ba to sai mu kashe shi. Suka yarda da wannan shawara ta Barnuhu.
Su kuma a wancan sansanin boka Sakaradisa ya ce “Duk yanda aka yi a mutanen nan da suka zo suna taimakawa wadancan akwai Malukussaifi cikinsu domin na ji muryarsa.In kuwa ya zo to gara mu canza salon yaki na daya bayan daya domin kuwa in dai zamu fita gabaki daya to zasu karar da mu nan ba da dadewa ba, saboda haka gobe yakin daya bayan daya za'a yi”.
Wayewar garj ke da wuya sai wasu daga cikin rundunar bokayen nan su goma suka fito filin daga nan kuma Sa'aduni ya fito nan da nan ya gama da su sai Sabikussalasa ya yi hamhama ya yi tsawa mai razanarwa ya yi kuwa ya yi kururuwa ya yi wa dokinsa kaimi ya fito ya yo dauki a kan Sa'aduni, Sa'aduni shi ma ya kifu a kansa suka hadu suka yi ta soke-soken jnansu har masunan su duk suka karairaye suka zare takubba suka yi ta kai bara da sara sai karar haduwar karafa da tartsatsin wuta kawai ke ta shi har magariba ta doso.Da Sa'aduni ya yi wata kuwwa ya ciro wani kulki daga damararsa ya kaiwa Sabikussalasa bugu da shi sai ya fado Kasa tik daga doki, Sa'aduni ya duro a kan kirjinsa ya daure shi tamau ya hau dokinsa ya ja shi izuwa sansani.
A rana ta biyu ma Sa'aduni ya kuma fitowa suka kara da Hurulwahashi shima ya kama shi, a rana ta uku kuwa da
Sa'aduni ya fito su kuma can sai Maimunu ya fito yana gurnani kai kace wani mahaukacin zaki ne, ya shiga sulkensa na dutse ya tasowa Sa'aduni suka hadu kowannensu yana ta kururuwa da haduwarsu kowanne ya zaro mashi suka yi ta kawa juna suka har duk masun suka lalace suka juya takubba nan sauran mayaka suka tsaya suka zubawa sarautar Allah ido,domin suna kallon haduwa irin wadda ba su taba ganin irinta ba da salo-salo da hikimomin yaki iri daban-daban haka aka yi ta gabzawa har duhun dare ya shiga sanna aka rabu kowa ya koma sansaninsa.
Da Sa'aduni ya koma sansani sai Malukussaifi ya tambaye shi ya ce “Yaya ka ji abokin yakinka?” Sai Sa'aduni ya amsa masa ya ce “Kai ai wannan shege ne domi kuwa tunda nake ban taba haduwa da mutum kakRarfa kamarsa ba da iya yakin,amma babu komai in Allah Ya yarda gobe zan kama shi”.
Can ma da Maimuni ya koma sai boka Sakaradisa ya tambaye shi ya ce “Yaya ka ji abokin yakinka?” Sai Maimunu ya ce “Ai lallai wannan babu mamaki ya buwayi Sarkinku ai ni tunda nake ban taba haduwa da mutum mai karfi da kafirin taurin kai da iya yafi irin wannan Sa'aduni ba, amma ba kome gobe da Ikon Zahlu zan kama shi.
Gari na wayewa Maimunu ya fito fagen daga Sa'aduni ya yunkura zai fita sai Malukussaifi ya yi wuf ya riga shi fita,ya yi kabbara ya bugi dokinsa ya yi kan Maimunu,ko da Maimuni ya ganshi sai ya ce a zuciyarsa to shi kuma wannan wane mai tsautsayin ne yana ganin yadda mukai da babbansu jiya amma shi kuma yau ya fito nan da nan Maimunu ya fusata ya yi kan Malukussaifi yana huci yana hamhama da haduwarsu suka kama yaki da sokekeniya da bugaiya can Malukussaifi ya yi wata tsawa wadda har sai da duwatsun dake kusa suka girgiza. Tsawa ce irin wadda kansa mace mai ciki ta haife, na tsaye ya kwanta. A wannan lokacin duk jama'ar da ke wurin sai da suka razana da jin wannan tsawar suka kai suka kawo suna kuwwa da sukan juna, Maimunu ya kaiwa Malukussaifi sara ya goce sai ya samu wuyan dokinsa dokin ya yi lau zai
fadi kafin ya je kasa shima ya sari kan giwar Maimunu suka
fadi gaba daya.
Duk suka mike suka ci gaba da yaki a kasa har ai da duk makamansu suka lalace, sai suka kama kokawa da naushc-naushe da duka da kafa, can Malukussaifi ya fusata ya yi wata kara ya kifawa Maimunu mari ya gigice ya yi wuf duk da girman Maimunu ya sure shi ya dora shi akan dantsensa sannan ya buga shi da kasa ya hau kirjinsa ya ga danne shi ya igiya ya daure shi ya ja shi kasa har zuwa sansaninsu.
Koda bokayen nan biyu da sauran jama'arsu suka ga an kama Maimunu cikin daren sai suka gudu. Da gari ya waye suka ga ba su gansu ba sai Malukussaifi da jama'arsu suka dunguma cikin birni aka wucc zuwa fada aka zauna sannan ya sa aka kawo Maimunu da Sabikussalasa da Hurulwahashi gabansa ya sa aka kwancc su sannan ya ce musu ina so na yi muku nasiha in kun yarda kun tsira in kuma ba ku yarda ba in kashe ku". Maimunu ya ce “Kai ai yanzu mu muna karkashin ikonka ne domin yanzumu bayi ne a wajenka fadi abin da kake so na rantse da Zahlu ba za mu kara sabawa umarninka ba”.
Ya ce "Nasiha ta a gareku ita ce ina mai muku bushara da ku bar wannan addini naku na bautar taurari ku komo addinina domin shi ne gaskiya". Sai duk suka amsa gaba daya da cewa “Gaya mana yadda za mu yi mu zamo daga addininka mana”.Nan ya gaya musu kalmar Shahada suka maimaita suka musulunta da gaskiya.
Can kuma boka Sakaradisa ya dubi bokayen nan

Please Login or Register in order to submit comment