Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga hannun Kamriyya ya komo ya fito, sannan Akisa ta shiga ta dauko Kamriyya ta fito da ita suka kamo hanyarsu ta komawa Yemen. Cikin Rankanin lokaci suka zo birnin Yemen.
Da zuwansu Akisa ta daure Kamriyya,a waje sannan suka shiga fada. Da zuwansu suka yi gaisuwa gaban Malukussaifr ya tambaye su ya ce “Yaya?" Barnuhu ya dauko allon nan ya mika masa ya ce “Ai bukata ta biya". Ya karba, sannan kuma ya ce yaya Kamriya kuma?” Akisa ta ce "Uwarka tana waje mun zo da ita, abin da ya sa bamu shigo da ita ba shi ne don kar ka ganta ka hanani kasheta." Akisa ta yi yo wuf ta fito waje Malukussaifi da duk sauran jama'ar gari suka fito Akisa ta kama Kamriyya ta tashi sama da ita.
Malukussaifi ya ce da Akisa “Kar ki kashe min uwa na gaya miki in kika kasheta ke ma sia na kashe ki duk randa kika shigo hannuna” Akisa ta ce “Ai ni kuw ako me zaka yi min sai na kashe ta domin kuwa na yi rantsuwa da hatimin Annabi Sulaimana (A.S.).
Akisa ta yi sama da Kamriyya ta sako ta ta taho kasa ya rage saura kadan ta zo kasa sai ta kuma fautar ta ta kara yin sama da ita, ta kuma sakota ta taho kasa, ko da ta kusa zuwa kasa sai Damatu ta zare takobi ta buda tana jira ta karaso ta raba ta biyu. Sai Akisa ta fusge takobin daga hannun Damatu ta sari Kamriyya ta raba ta gida biyu sannan ta rika bin barin jikin tana sassara ta gunduwa-gunduwa, kai ya fado daban hannu da bana kafa daban.
A wannan lokaci Malukussai ya rika kuka saboda bakin cikin ganin yadda aka kashe uwarsa kamriyya. Haka yna akuka ya tattara naman ta da kasna ya haka rami ya bunne ta. To wannan shi ne abin da ya gudana ga Kamriyya.
Bayan an sami wasu 'yan kwanaki sai tunaninsa ya komo kan matarsa Manniyatunnufusi da ta gudu ya zauna sh kadai yana tunani wani lokaci mai tsawo yana cikin wannan hali sia ga Akisa ta zo, ta yi masa sallama ko da ya ganta sia ya ce
ziyarce ni ma?" Akisa ta ce ai abin da ya sa na kaurace maka don na ji ka ce tunda na kashe Kamriyya kai ma sai ka kashe ni to shi ne nake jin tsoro kaga na daina ziyartarka". Sai ya ce da ita “ai wannan magana ta wuce ki manta da ita ba komai yänzu ni abin da yake gabata na kawai ki zo mu yi tafiyar nar zuwa garin mata ta Manniyafunnufusi.
Akisa ta ce “To ai yanzu sai ka kirawo Iluru don mu y maza mu tafi ko". Nan da nan ya goga allo Iluru ya zo ya kwashe labari kaf ya gayawa Iluru, kuma ya ce yana so su taf tare, "Iluru ya amsa ya ce “To ai sai mu tafi”. Ya dauk Malukussaifi suka tashi tare da Akisa suka yi sama suka kama hanya bayan sun samu sa'a tara suna tafiya sai suka sauke sh kan wani dutse domin ya huta nan da nan Akisa ta je ta zo masa da wasu 'ya'yan itatuwa iri daban-daban ya ci ya kosh ya kwanta ya yi barci. Bayan ya farka sai Akisa kuma ta dauk shi suka ci gaba, haka dai suka yi ta kar6a-karbar daukar s tsakanin Akisa da Iluru. Idan daya ya duke shi to dayan sai y tafi nemo abinci, tafiyar nan ta shekara talatin suka yanke ta cikin wata shida suka yi ta.
Suka sauka kan wani katon dutse sai Akisa ta ce da Malukussaifi “To mu fa daga ni har Iluru nan ne iyakar m domin kuwa daga nan wurin duk aljanun da suke gaba ba'karkashin ikon iyayenmu suke ba kai ba ma irin halittarm daya da su ba, sannan kuma akwai yaki tsakanin iyayenmu da su. Saboda haka ko da da taki daya ba mu da ikon matsawa gaba daga da nan. Saboda haka yanzu sai dai mu yi sallama da kai daga nan mu yi maka fatan alheri”.
Malukussaifi ya yi musu godiya yana cewa "Madallah na gode muku kwarai kuma ina mai muku fatan alheri har iya tsawon rayuwarku. To amma ina so ku zaun a nan kar ku taf har sai na dawo". Suka amsa masa. Ya kama hanya ya gangaro kasa daga kan dutsen nan.
Ya mika ya yi ta tafiya har rana ta fadi dare ya yi ya tsaya ya samu wani kogon dutse ya kwanta ya huta amma ya kasa barci saboda kaguwa da ya yi da ya kai ga bakin wadi na
farko.Haka ya kasance har gari ya waye, sannan ya fito ya kama tafiya. Bayan kimanin sa'a uku da fara tafiyarsa sai ya fara hango duhun katangar birnin, nan fa ya kara azama ya tasamma wannan katanga yana ta sauri kamar zai tashi.
Bayan wani dan lokaci ya kai gindin wannan katanga,sai ya ga ai ba katanga ba ce wani katon dutse ne ya zagaye wadin. Ya yi ta zagaye-zagaye yana neman hanyar da zai shiga amma ina ya rasa. Da ya gaji sai ya samu wani waje ya zauna domin ya huta sai barci ya kwashe shi. Bai farka ba har sai da gari ya waye, yana farkawa sai ya ga wani tsoho zaune sanye da fararen kaya kusa da shi.
Da ya tàshi ya zauna sai tsohon nan ya yi masa sallama irin ta musulunci, ko da Malukussaifi ya ji ya yi masa sallama sai ya san lallai wannan tsohon musulmi ne saboda haka sai ya saki jikinsa da shi. Tsohon nan ya ce da shi “Barka da zuwa Malukussaifi dan sarki Ziyyazanun”. Bayan da Malukussaifi ya amsa sai ya tambaye shi ya ce "Kai kuwa wa ye kai kumma me kazo yi nan kuma wa ya sanar da kai sunana?” Tsohon nan ya amsa masa ya ce "Ni sunana Nurulzaitun, Shehi na Annabi Halliru (A.S.) shi ne ya sanar da ni kai kuma ya umarċe ni da nazo na taimaka maka ka biya wannan bukata taka”. Sai ya dauko wata jaka ya bude ta ya dauko wata rigar gashi ta mata wadda aka yi mata ado da dinarai ya mikawa Malukussaifi ya ce da shi riki wannan za ta yi maka amfani”. Ya karba yana mamakin yaya wannan riga za ta yi masa amfani bayan kuma ga shi ma ta mata ce.
Tsohon ya kuma dauko wata kwarya da farin mayani ya kuma mika masa ya karba, sannan ya kuma dauko wata 'yar lailayayyiyar bal da wani dan ice mai fadi na buga wannan bal din ya mika masa ya karba, sannan ya kuma dauko wani dan lailayayyen dinari dan karami ya mika masa ya karba, ya kuma dauko wani dan karamin allo na bakin karfe da wata 'yar sarka ta azurfa a rataye.a jikin allon sannan kuma jikin allon akwai wani hatimi mai dauke da wasu dalasimai masu kwatankwacin irin na allon Iluru ya mika masa ya karba ya
tsaya. Shi dai Malukussaifi yana ta mamakin yadda wadannan
abubuwa da aka ba shi za su amfane shi.
Nurulzaitun ya yi murmushi ya ce “To yanzu zan yi maka bayanin amfanin wadannan abubuwa da na baka, na fakro dai ita wannan riga da na baka lokacin da zaka shiga birnin mata zaka tarar da su duk suna sanye da irin wannan riga. To kaga sai ka saka ta ka shiga cikin su ba za su gane ka ba. Na biyu kuma ita wannan kwarya da na baka duk lokacin da ka ke bukatar abinci ka rufa wannan mayanin a kan kwaryar ka kuma fadi nasabarka sannan ka ambaci duk irin abincin da kake so zak agan shi cikin wannan kwarya. Abu na uku kuma ita wannan 'yar bal da wannan dan iccen da na baka bayan ka shiga birnin mata ko wacce zaka ganta da su a hannu suna wasa to kaima sai ka fito da naka ka rika yi kamar yadda suke yi,sannan shi kuma wannan dan dinari da na baka amfaninsa idan ka sa shi a baki ko mai zafin rana ba za ka jishi ba, kuma ba za ka ji kishirwa ba, haka kuma idan ma san yi ne komai tsananin sanyi za ka ji yanayin ya yi maka daidai da yadda kake so, sannan kuma idan ka bukaci yin barci sai ka dawo da shi 6arin da ka ke kwance zaka ji shimfida mai taushi kana kwance a kanta.
Abu na karshe kuwa shi ne wannan allo da na baka, to shi wannan allo na Hairakana ne dan babban Sarkin aljanun wannan nahiyar, shi ne kadimin wannan allo, yanzu duk lokacin da ka murza wannan allo aljani Hairakana zai zo ya biya maka bukatarka, shi zai dauke ka ya wuce da kai wannan wadaye na wakilwaki,amma idan ka je ka biya bukatarka ya dawo da kai nan ka ba shi allonsa ya yi taliyarsa kar ka sake bautar da wannan aljani. To ka ji wannan shi ne bayanin da zan yi maka game da wadannan kayayyaki dana baka. Sannan ina mai kara yi maka wasiyya da ka dogara ga Allah a duk halin da ka ke ciki, sai an jima".
Rufe bakin sa ke da wuya sai ya bace Malukussaifi ya neme shi sama da kasa ya ga bai gan shi ba nan ya zauna yana mai godiya ga Allah har dare ya yi gari ya waye ya ta shi ya dauko
Rwaryar nan ya rufe ta da wannan dan mayanin ya fadi nasabarsa sannan ya ce yana so a kawo masa gurasa da miya da gasasshen naman barewa. Yana rufe bakinsa sai ya ji dumi jikin kwaryar da kamshi yana tashi ya bude mayanin sai ya ga gurasa take cikin kwaryar ga gasashshen naman barewa kamar yadda ya bukata, sai ya yi farin ciki ya ce “Kai madallah da wannan kwarya abinci ba tare da wata wahala ba, ai wannan tafi komai ma amfani. Ya duka ya kama cin gurasa nan yaci-yaci har ya koshi sannan ya tashi ya kuduri niyyar tafiya.
Da ya gama kintsawa sai ya daukko allon nan ya murza,nan da nan sai ya ji wata iska ta sa kura ta turnuke gurin, yana tsaye sai ya ga wani katon aljani wanda ganinsa ya so ya razana shi, domin ya fi Iluru girma ya zo gabansa ya ce “Ga ni ya shugabana me ka ke nufin na aiwatar maka na aiwatar yanzu-yanzun nan?”Malukussaifi ya dube shi ya ce “Kai ne Hairakana?”ya amsa masa ya ce “Nine ya shugabana”.
Malukussaifi ya ce “To yanzu Hairakana na zo nan ne bisa wata bukata ta, saboda haka ina so yanzu ka daukeni ka wuce da ni wadannan wadaye guda bakwai na wakil-waki domin na isar da burina”. Hairakana ya ce “To in ka shirya ai sai mu tafi”.Ya amsa masa ya ce na shirya mu je".
Hairakana ya dauki Malukussaifi ya ta shi sama da shi suka kama hanya suka yi ta tafiya, saboda tsabar sauri tafiyar shekara guda Hairakana ya rika yanketa cikin wuni daya har suka isa wadi na farko sannan ya sauke Malukussaifi akan wani dutse domin ya huta.
Bayan da ya huta sai ya tambayi Hairakana ya ce nan kuma ina ke nan muka zo?” Ya amsa masa ya ce ai nan wadi na farko ke nan” Malukussaifi ya duba ya ga' babu komai a wannan wadin banda duwarwatsu, sai wani aliamudi kato na farin karfe,nan dai suka kwana gari ya waye sannan sukaci gaba da tafi. Malukussaifi ya umarce shi da ya kara sauri ya kara shudawa da gaggawa kamar walkiya, cikin wannan wunin da azahar suka isa wadi na biyu.
Hairakana ya sauke Malukussaifi kan wani dutse. Ya gaya masa sun zo wadi na biyu,ya zauna ya huta sannan ya gangaro kasa daga kan dutsen nan domin ya dan kekkewaya ya yi ta kallo yana tafiya. Hairakana yana biye da shi a baya,yana cikin tafiya sai ya ga wani katon al'amudi na farin karfe irin wanda ya gani a wadi na farko ya tsaya ya yi kallo sannan ya wuce ya ci gaba da tafiya. Sai ya ga rinjin wasu bishiyu jikinsu ga 'yan mata nan barjak suna reto rataye jikin wadannan bishiyoyi.
Nan da nan sai ya juyo ya tambayi Hairakana ya ce “Kaga wasu'yan mata an rataye su ko wane laifi suka yi aka yi musu haka. Kai shin wane ne Sarkin wannan wadin ya aikata wannan aikin haka?" Hairakana ya amsa masa ya ce “Sarkin da ya halicci sammai da kassai ya yi duniya ya yi lahira shi ne Ubangijin Annabi Ibrahima (A.S.) shi ya aikata wannan.
Wadannan van nota da kake gani ba bil'adama ba ne 'ya'yan ita wannan itaciyar ne haka Allah ya yi su da siffar mata sak,sannan kuma kuilum idan dare ya yi sulusi na farko ya fita na biyu ya shigo su wadannan 'ya'yan bishiya suna yiwa Ubangiji tazbihi har zuwa ketowar asuba”.
Malukussaifi ya yi shiru yana mamaki ya ce to in kuwa maganar nan taka gaskiya ce to yau a nan zan kwana sai na ji irin tazbihin da suke yi haka ya zauna a nan har daresyanyi sulusi na farko ya fita na biyu ya shigo sai ya ji wadariah 'ya'yan bishiyar suna cewa “Wakil Waki Subhanal Malukul Hallaki. Ko da ya ji haka sai ya ce “Tsarki ya tabbata ga Ubangijin Ibrahima (A.S.) Ubangiji Annabi Muhammadu (S.A.W.) wannan Annabi da zai zo karshen zamani,a nan dai ya kara-inganta imaninsa ya ci gaba da tazbihi shima kamar yadda wadannan 'ya'yan itatuwa ke yi har gari ya waye.
Hairakana ya zo gabansa ya ce “Ya shugabana yanzu nasan zaka bukaci abinci to bari in ciro maka daya dage cikin 'ya'yan bishiyar nan ka ci” Ko da Malukussaifi ya ji wagnan magana ta Hairakana sai ya ce "Haba Hairakana ya yaya za a yi na ci wadannan 'ya'yan bishiya bayan suffar su ta
'yan'adam ce kuma har ga shi suna magana". Hairakana ya ce “Ai ana ci mutanen da suka wanzu a da a wannan wadi ba su da wani abinci in ba su ba, kuma sun kunshi dukkan launi na kayan marmari da ka sani".
Malukussaifi ya ce “To kawo na gani" Nan da nan Hairakana ya fusgo daya daga cikin 'yan matan nan daga'jikin bishiyar ya kawo gaban Malukussaifi ya ajiye ya duba ya ga gata budurwa sak yana al'ajabi. Hairakana ya fake cikin wannan budurwa sai Malukussaifi yaga cikin duk inibi ne jajaye a ciki daga cikin kirjinta kuwa tuffa ce da nau'in kayan marmari iri daban-daban, cinyoyinta kuwa duk curarriyar gurasa ce, nan ya kama cin wadannan abubuwa har ya koshi,ya yi wa Allah godiya ya tashi don su tafi.
Hairakana ya dauki Malukussaifi suka ci gaba da tafiya har gefin faduwar rana sannan suka sauka akan wani dutse a wadi na uku. Bayan ya huta ya tambayt Hairakana ya ce “Shi kuma wannan wadi mene ne a cikinsa? Ya amsa ya ce “Shi ma wannan wadin akwai irin wadannan 'ya'yan itatuwan kamar wancan amma su kuma wadannan siffar maza gare su. Kuma suma suna tazbihi kamar yadda na baya suma suke yi. Nan dai suka zauna suka yi ta hira har dare ya raba can sai suka ji tazbihin wadannan.Malukussaifi ya kama yin tazbihin kamar yadda nuke yi shi ma har gari ya waye sannan sukai shirin mikawa izuwa birni na hudu.
Hairakana ya sake dukawa ya dauki Malukussaifi suka mika izuwa wadi na hudu, haka Hairakana ya yi ta keta hazo cikin gaggawa har rana ta fadi. Farkon Magariba saka isa wadi na hudu, da zuwansu sai suka sauka akan wani dutse. Bayan sun huta sai ya tambayi Hairakana ya ce “To shi kuma wannan wadin fa mene ne a cikinsa?” Ya amsa masa ya ce shi wannan wadin babu wata halitta a cikisna banda wasu bishiyu wadanda su kuma 'ya'yan su siffar kawunan biladama gare su, kuma ana cinsu. Idan ka dauko zaka ci sai ka ga suna yi maka murmushi, sannan kuma idan ka ci ka rage ka yar, shi wannan ragowar da ka yar sai wani tsuntsu ya zo ya dauki ragowar ya
mayar da shi jikin bishiyar. Sai ya koma yadda yake kamar ma ba'a taba ciro shi ba, sa'annan kuma suma idan dare ya raba suna yi wa Ubangiji tazbihi kamar yadda wadancan na baya suke yi
Gari na wayewa Hairakana ya dauki Malukussaifi suka mika izuwa wadi na biyar. A wannan lokaci Hairakana ya kara hanzari irin wanda bai taba yinsa ba, tsakiyar rana suka isa wadi na biyar da suka sauka, suka huta sai Malukussaifi ya ga babu komai a wannan wadi banda rairayi da wasu kananan duwarwatsu, sannan ga wani katon al'amudi na farin karfe irin wanda ya gani a sauran wadayen baya, sai ya tambayi Hairakana ya ce “Shin wai wadannan al'amudan da nake ta gani a kowace wadi na meye kuma mene ne tarihinsu?”Hairakana ya amsa masa ya ce “Su wadannan al'amudan ai dako ne wanda wani zamani mai tsawo da ya wuce wani Sarki ya yi su”. Ya kuma tambayar sa ya ce “Meye dalilin yin su?"Hairakana ya fara da cewa:
“A wani zamani an yi wani Sarki mai suna Abidunnajami.Shi wannan Sarki ya kasance kuma boka ne mai tsananin sanin ilimin bokanci, wanda a saboda haka ne ya sa mutanesa suke yi masa tsananin biyayya saboda karfin mukinsa da bokacinsa.Shi wannan Sarki yana da wani waziri hatsabibi wanda shi kansa Sarkin shakkar juna suke shi da shi. Waziri yana shakkar Sarki saboda bokancinsa haka shi kuma Sarki yana shakkar waziri saboda makircinsa, haka dai suke zaune shi kuma wannan Wazirin sunansa Kiwanu.
Shi wannan sarki yana da wani da guda daya wanda ke kira da suna Shahudata, shi wannan da ba shi da wata dabi'a illa bin gidajen mutane ya haikewa 'ya'yan mutane da matansu,duk wadda ya gani ya neme ta taki sai ya kamata ta Rarfi ya biya bukatarsa sannan kuma ya kasheta. Wannan ala'ada ta Shahudata duk ta damu jama'ar gari amma sun rasa yadda za su yi da shi saboda tsoron Ubansa, Sarki.
Wata rana Shahudata yana yawo a cikin gari yana farautar mata sai ya ga wata kyakkyawar yarinya ta ci ado tana tafiya
da kuyanginta su uku. Ko da Shahudata ya ganta sai ya yi nufin kamata. Sai wadannan kuyangin suka gaya masa ai 'yar Waziri Kiwanu ce, da ya ji haka sai ya kyaleta saboda gudun kada ubansa ya ji labari. Ya tafi ya rabu da su.
Bayan da 'yan matan nan suka koma gida sai ita wannan 'yar waziri ta kwashe labari ta gayawa Ubanta Waziri Kiwanu abin da ya faru na nufin kamata da dan Sarki Shahudata ya yi.Ko da Waziri ya ji wannan labari sai ransa ya baci ya kuma san lallai tunda wannan yaro ya ganta to ba zai hakura ba sai ya sake haike mata, sai ya tashi ya tafi izuwa gidan Sarki, ya je aka yi masaiso ya shiga ya iske sarki yana zaune ya fadi ya yi gaisuwa, Sarki ya tambaye shi ya ce "Waziri lafiya dai na ganka ranka a 6ace haka?” Waziri ya amsa masa ya ce “Na zo ne akan ka yiwa danka Shahudata tsakani da 'yata domin' yana neman haike mata”.
Jin wannan magana ta Waziri sai Sarki ya harzuka ya tura wasu bayi ya ce su nemo dansa Shahudata, nan da nan bayin nan suka bazama cikin gari suna nemansa, can sai suka same shi kofar wani gida yana tsaye, sai suka gaishe shi suka gaya masa ya zo Sarki yana kiransa. Shahudata ya ce “Ku je ku ce da Sarki ba ku ganni ba domin kuwa ni yanzu wata yarinya na gani ta shiga nan gidan na tsaya ina dakon ta fito in isar da bukatata. Bayin nan suka ce ai kuwa lallai ne yanzu.mu tafi da kai domin kuwa kasan Ubanka yana da ilimin kasa babu mamaki yanzu ma yana ganinmu, sannan kuma mu je mu ce ba mu ganka ba ai ba zai yiwu ba. Suka taso shi a gaba suka kawo shi gaban Sarki.
Da zuwansa Sarki ya dube shi cikin fushi ya ce “Kai me ya hadaka da 'yar Waziri ka ke nufin haike mata?” Shahudata ya daga kansa ya dubi uban ya ce “To ran Sarki ya dade ka san fani a rayuwata ba ni da wani abu a duniyar nan da nake so fiye da mata, wanda ni ina ganin ba zan iya rayuwa ba,sai da mata shi ya sa idan dai naga mace har na kyasa ta to hankalina ba zai taбa kwanciya ba har sai na isar da burina gare ta, tun da
kuwa na ga wannan 'ya ta waziri labudda sai na isar da burin
gareta ba makawa".
Jin wannan magana ta Shahudata sai Sarki ya fusata ya juy wurin Waziri ya ce "To gashi nan duk ranar da ya kum bijirowa 'yarka kada ma ka yi shawara da ni kawai ka kash shi".Waziri ya ce “To ai shike nan ya tashi ya fita, shim Shahudata ya tashi ya fita aka bar sarki a zaune shi kadai. S kuwa wannan umarni da Sarki ya yi wa Waziri ya yi shi ne wai don yana nufin Wazirin ya aikata hakan ba ne, ya yi shi r kawai don dan nasa ya ji tsoro ya rabu da yarinyar.
Bayan an sami wasu 'yan kwanaki da yin wannan, wa rana da daddarc Shahudata ya fito yana yawo cikin gari yan farautar mata sai ya biyo ta wajen gidan Waziri sai ya tuna 'yar nan ta Waziri sai ya saci jiki ya shiga cikin gidan ba ta da kowa ya ganshi ba, ya wuce can cikin gida ya rika bi dak daki yana neman inda wannan yarinya take har ya zo dakin takc ya budc ya hango ta tana kwance tana barci, sai ya shi ya tsaya a kanta ya zarc takobi ya tashe ta. Ko da ta farka ganshi sai ta san abin da ya kawo shi sai ta yi tunanin idan nuna masa rashin yardarta lallai zai halaka ta sai kawai koma ta kwanta tana kallonsa.
Shi kuwa da ya ga haka sai ya cire rigarsa ya hawo k gadon ya kusance ta, ya mika hannu ya fara shafa kumatun har ya kai ga kirjinta zuwa bayanta, ya koma wasa da gash kanta ya rungumcta ya sumbaci bakinta. To a nan fa ita ma kamu ta soma shafa kirjinsa tana wasa da gashin kirjinsa.in dai takaicc maka har sai da ya isar da burinsa. Ya tashi y kayansa ya juyo da nufin zai fito sai suka yi kicibis da Wa a bakin kofa, ko da ya ga Waziri sai Shahudata ya dube shi yi dariya. Ko da Waziri ya ga haka sai ya yi taunin abin da wakana, sai ransa ya baci ya yi wuf ya zaro takobi ya sare Shahudata; ya yi kiransa wasu bayi ya ce su fita da gawar kai can bayan gari su jefar. Nan da nan suka aikata kar yadda ya umarcesu.
Gari na wayewa da hantsi ya dan daga Waziri ya yi shiri ya fita fada ya tarar da fada ta cika Sarki ya zauna, ya fadi gaban Sarki ya yi gaisuwa sannan ya koma mazauninsa ya zauna aka ci gaba da fadanci. Jim kadan sai ga wasu mutane su hudu dauke da gawar Shahudata sun shigo fada. Da zuwansu suka yi gaisuwa suka bawa Sarki labarin yada suka tsinci gawar dansa : a bayan gari.
Koda Sarki ya ga gawar dansa sai hasken da ke fuskarsa ya :koma duhu jikinsa ya kama rawa idanuwansa suka kada suka :yi jawur zuciyarsa ta rika tafasa tana kumbura. kamar zata fashe, ransa ya yi matukar 6aci hankalinsa ya dugunzuma ya ta lshi,ya daga kansa sama ya zagi tauraruwar bautarsu ya zagi Iwuta ya ce “Yau wa ya aikatawa dana wannan aiki?" Ko da 'Waziri ya ji haka sai ya yi wuf ya mike tsaye ya dubi Sarki 'cikin fushi ya ce “Ba wani ba ne nine na aikata wannan aiki”.
Sarki ya kara harzuka da jin wannan magana ta Waziri,ya yi duba izuwaWaziri ya kuma tuna ba zai iya ramawa ba saboda sanin makircin Waziri, kuma ya tuna jama'ar garin ma nasa idan ya ce zai yi wani abu ma ba za su goyi bayansa ba Waziri za su goyi baya. Sai ya.yi shiru zuwa wani lokaci, can ya nisa ya ce “Waziri me ya sa ka kashe mini dana?”
Waziri

Please Login or Register in order to submit comment