Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tamanin ya ce“To yanzu tun da sadaukai sun kasa yanzu ku kuma sai ku kar6i yakin ku yi shi da ilimin alkalumma". Nan fa bokayen nan suka shiga bokancinsu da tsafe-tsafen su sai suka fito da wata takarda suka yi mata wani siddabaru sai ta tashi sama ta shig cikin birnin Yemen ta shiga har zuwa fada a wannan lokaci Malukussaifi yana zaune akan karaga a gefensa na dama ga Sarki Afarahu ga Sa'aduni ga Sabikussalalasa a gefensa na hagu kuma ga sArki Abuttaj ga Maimunu ga Hurulwahashi sannan gaban karagarsa daga kasa ga Barnuhu yana zaune, da
shigowar wannan takarda duk sai suka sandare babu mai iya motsi a cikinsu sai Barnuhu kawai shi ya tsira a wannan fadar bai sankame ba.
Da Barnuhu ya ga haka sai ya san lallai wannan aikin mutanensa ne nan da nan ya dauko wata tasa ya zuba ruwa a ciki ya dauko wata takarda daga jakarsa ya sata a cikin tasar nan, nan da nan ruwan cikin tasar nan sai ya canza launinsa ya rika tafarfasa, yana cikin haka sai ga Shamatu matar Malukussaifi ta farko ta shiga fadar nan wani bawa ya je ya bata labarin abin da ya faru ta zubo sulkenta ta yi shirin yaki ta fito ta tsaya kusa da Barnuhu tana kallonsa yana ta bokancinsa.
Suna cikin haka sai suka ji wata tsawa, Barnuhu ya ce da Shamatu rike wannan tasar idan kinga ruwan ciki ya huce ya daina tafasa ki yayyafa musu duk zasu warke ni zan fita na yaki bokayen nan domin ga su nan sun taho zasu shigo".Shamatu ta karbi tasa ta soke takobinta cikin damararta ta Lsaya tana jiran ruwan ya huce.
Barnuhu kuwa ya fila ya tunkari bokayen nan tamanin suna jifansa da bala'in tsafi yana karewa yana jifan su shima, haka suka yi ta yi har sai da ya zamanto Barnuhu baya iya jifansu sai dai kawai kare kansa yake yi har takai ta kawo kare kan nasa ma sai da kyar yake iya yi domin sun yi masa yawa, da dai Barnuhu ya ga zai halaka sai ya kama addu'a yana mai tawassili da Ubangiji, bai gama addu'arsa ba sai ga wata tsohuwa akan wata taguwa mai fuffuke da wata mace ita kuma kan wani doki mai fukafuki sun sauka a kofar fadar birnin.
Da saukarsu sai suka shiga fada suka iske Shamatu tsaye da tasa a hannunta, da ganinsu sai Shamatu ta tambayesu daga ina, kuma suwaye ku?" Tsohuwar nan ta amsa mata da cewa "Ni ce boka Akila kuma wannan 'yata ce sunanta Damatu,kuma mun zo wannan gari ne neman Malukussaifi domin ya jc kasarmu Kaimaru neman littafin halwanu shekarun baya na taimaka mar ya samu littafin bisa alkawarin da ya yi na auren 'yata to na ga har yau bai koma ba shi yasa na biyo sawunsa domin va auri 'vata”
Da Shamatu ta ji haka sai ta ce “ai ga mijin nawa nan wasu bokaye ne suka yi masa asiri da' mutanensa duk suka daina motsi". Da Akila t ji Shamatu ta ce mijina sai ta ce “Ince ko kc ce 'yar Sarki Afarahu Shamatu?” ta ce “E, ni ce mana".Ko da Damatu ta ji ai Shamatu ce wannan sai ta dube ta ta tuna a saboda ita Malukussaifi yaki yarda ya aureta tuntuni nan sai kishi ya kamata ta zare takobi ta yi kan Shamatu nan da nan Shamatu ta ajiye tasa ta zaro nata takobin suka kama kai wa juna sara, Akila ta shiga tsakani ta sasanta sannan ta dauki tasar nan ta tambayi Shamatu ta ce “Wannan kuma meke nan?”Sai ta ce “Ai wani bokan mijina ne ya sana'anta wannan ya ce idan ruwan ya huce in yayyafa musu za su warke shi kuma ya fita yaki da wadannan bokayen domin kada su shigo su halakamu”.
Akila tana jin wannan magana sai ta fusata ta fita ta nufi wurin da Barnuhu suke yaki ta tarar sun ci karfinsa ya gaji,nan da nan sai ta sa hannu a jakarta ta bokanci sai ta dauko wasu darmomi guda tamanin ta watsa sama da suka yi sama duk sai suka kama da wuta sai kowace darma daya sai ta dira akan boka daya sai ya fadi matacce cikin kankanin lokaci duk bokayen nan tamanin suka mutu babu wanda ya tsira.
Koda Sakaradisa da Sakaradiyyuna suka ga an kashe bokayen nan duk sai suka juya da sauran jama'arsu aguje suka koma gida suka kwashe labarin duk abin da ya faru suka gaya wa Sarki Saifu'ar'adu ya ce “Ba komai ni da kaina zanje nan gaba na yake su”.
Akila da Barnuhu suka koma cikin birni yana tambayarta tana yi masa-bayanin kanta da zuwansu sai suka tarar Shamatu tana yayyafa musu wannan ruwan, gamawarta ke da wuya sai duk suka warware suka komo cikin hayyacinsu.Malukussaifi sai ya yi farin ciki da ganinta ya dubi Damatu ya yi murmushi sannan ya kwashe labarin zuwansa kaimaru neman littafi da irin taimakon da Akila ta yi masa kaf ya gayawa jama'a.Bayan da ya gama sai Akila ta ce "Yaya maganar auren 'yata Damatu?" ya ce "Ai ni wallahiina kaunar ta kwarai da gaske
kuma ina begenta a koda wane lokaci kuma ina so na aureta,to amma fa tun sanda zan-baro garin ku ta dauken hula ta wadda na samo a garin Mallam Afaladinu ta ce sai na aureta a wannan lokaci sannan zata ba ni ni kuma na yi rantsuwar ba zan aureta ba sai ta ba ni hulata"
Akila ta dubi Damatu ta ce “Ki ba shi hularsa yanzu ya aureki”. Sai 'yar ta ce ai nima na yi rantsuwa na ce ba zan ba shi hularsa ba sai ya aureni, saboda haka yanzu ya aure ni na ba shi hularsa". Suka yi ta jayayya ko wa ya ce ba zai karya rantsuwarsa ba.
Haka aka zauna tsawon wasu 'yan kwanaki, wata ranata ana zaune a fada sai Maimunu ya roki izinin a bar shi ya koma dajin nan da yake zaune domin ya musuluntar da 'yan'uwansa kuma ya debo dukiyarsa ya dawo nan. A kai masa izini ya tafi sai Sabikussalasa shima ya nema kamar yadda Maimunu ya nema shima aka ba shi izini ya tafi.
Bayen kwanaki masu dan nisa Maimunu ya dawo da dukiyarsa da mutanensa, shima Sabikussalasa lokacin da ya komo gida sai ya umarci 'yarsa da matarsa da su musulunta ya tafi da su Yemen sai uwarta taki ita kuwa 'yar mai suna Ummulhaya sai ta yarda ta musulunta ta kuma biyo ubanta suka komo Yemen. Da zuwansu sai Sabikussalasa ya wuce da Ummulbaya fada ya fadi gaban Malukussaifi ya yi gaisuwa sannan ya gabatar da 'yarsa gabansa ya ce “Gata nan na baka ka sata a cikin matayenka". Ya dubeta yaga Ummulhaya kyakkyawace ai nan take sai aka daura musu aure da Malukussaifi, nan kishi ya kara kama Damatu.
Bayan sati da gama biki, wata rana ana zaune a fada sai ga wani malami ya shigc da mace tana biye da shi ta lullube tuskarta da bakin mayani. Mutumin ya wuce zuwa gaban Malukussaifi ya tsaya ya yi mubayi'a sannan ya ce_“Ka mantani ko?” Sai Malukussaifi ya ce “Haba ya ya za'a yi na manta ka ba kai ne Malam Ihimimiddalibi ba wanda ka shiryar dani izuwa ġidan kakana Samu ba, aina gane ka". Sai Ihimimi ya ce “To yaya alkawarinmu da muka yi na maganar auren
'yata?” ya amsa masa ya ce “Ai 'yarka Jizatu babu makawa
zan aureta yanzu kuwa”.
Jin haka sai Damatu kishi ya kamata sai ta ce "Yaya a gabana mata za su rika zuwa kana aurarsu bayan ni kuma gani?” Ya nisa ya ce “Ita wannan Jizatu ubanta shi ya taimaka min na samu allon Iluru kuma na samu takobin kakana Samu kinga kuwa tana da matukar daraja a guna, nan take ya bada izini aka daura musu aure da Jizatu aka yi ta biki har tsawon wasu kwanaki.
Amma abin da ya abku ga Kamriyya bayan da ta warke daga cutar ta shi kuma danta Malukussaifi da sauran jama'arsa sun shagalta da yakinnan sai ta tura wani bawanta a asirce ya kirawo mata wani makeri ta dauko allon Iluru ta nunawa makerin nan ta ce tana so ya kera mata irinsa a girma da launi da komai da komai. Makerin nan ya kera mata daidai da wannan allo komai da komai bayan ya gama ta karba sai ta kashe su da bawan da ta aike ga makerin. Sannan ta je ta boye allon mai kyau ta dauki na karyar wanda ta sa aka yi mata ta fito fada ta durkusa gaban Malukussaifi ta ce "Abin duk da na yi maka ka yafe ni ga allonka". Ya mika hannu ya kar6i allo ya daura ya yi farin icki da nadamar uwarsa.
Daga wannan loacki sai ya kasance Kamriyya ta sake har fada take zuwa, wata rana ta zo fada a gabanta sai Akila ta tashi ta ce “Ya kai Malukussaifi na sana'anta maka wata riga .da fatan barewa wadda in kasa ta wani aljani bai isa ya ra6eka ba in ba da izininka ba, to da ba zan baka ba sai ranar da ka auri 'yata to amma yanzu na canja shawara gata ta mika masa rigar. A na cikin haka sai Mallam Ihimimi shima ya fito ya ce “Ai nima kamar yadda ta yi maka wannan riga nima na zo maka da wani zobe wanda zai maka fa'ida mai yawa”, ya mika masa ya karba. Ganin an ba shi wadannan abubuwa sai bakin ciki ya tunnuke uwarsa Kamriyya ta tashi ta fita daga fadar ta koma cikin gidanta.
Komawarta ke da wuya sai ta rika tunanin wane makirci kuma zata Rullanc tunda yanzu danta yana da masu taimako da yawa, haka ta dau lokaci mai tsawo tana tunani.
Bayan an tashi daga fadanci, Malukussaifi ya kadaita a cikin gida sai Damatu ta zo ta zauna kusa da shi ta ce da shi "Tun da kaki ka aure ni har sai da ka auri mata biyar wato in ka aurč ni nan gaba in zama ta shida kenan ni kuma na yi alkawarin bazan zo a matarka ta shida ba. Saboda haka sai na kashe daya daga cikin matanka". To saboda sanin halinta da ya yi da taurin kanta sai yasan lallai zata aikata sai ya ta da hankalinsa ya rika rarrashinta sai ta kuma cewa “Kaga ba zan kashe Shamatu ba da Manniyatunnufusi da Ummulhaya da Jizatu ba ka kwantar da hankalinka', sai ta ki fadar sunan Nahidu 'yar Sarkin Sin, Shi dai bai gushc bå yana ta rarrashinta har sai da ta yi kamar ta hakura.
Bayan an sami kimanin watan ni goma wata rana ana zaune a fada sai aka zo a kai wa Malukussaifi bishara da cewa matarsa Jizatu ta haifa masa da namiji wato dansa na biyu kenan ya yi murna kwarai aka radawa yaron suna Nasaru,wannan abu shi ma ya kara bakantawa uwarsa Kamriyya rai ta yi matukar bakin ciki ta tashi ta koma cikin gida ta zauna da abin ya damela sai la ta tashi ta dauko allon lluru ta goga ya zo sai ta ce da shi“Hluru yanzu abin da nake so da kai yanzu ka je ka cfauki Malukussaifi ka kama shi ka murde masa wuya ka kashe shi". Saiya ce “Ya shugabata ki sani fa yanzu ba ni da skon zuwa in da yake muddin yana tare da wannan rigar fatar barcwar nan da bokanyar nan ta ba shi, domin akwai dalasimai wanda in na kusance shi ba cikinizininsa ba konewa zanyi".Nan dai ya tababtar mata ba zai iya ba ta sallame shi. Bakin ciki ya hana ta zaune ya hana ta tsaye sai ta fito tana dan zagawa cikin gidan sai tayyo wajen gidan Nahidu da zuwanta sai ta shiga cikin gidan ta tarar da Nahidu tana zaune ko da,ta ga Kamriyya sai ta mike ta gaisheta ta girmamata a matsayinta na uwar mijinta, ta bata wuri ta zauna.
Zamanta ke da wuya sai Nahidu ta ce "Dama kuwa ina sO na kawo miki karar Malukussaifi domin yana fifita Manniyatunnufusi akan dukkanin mu sauran matansa musamman ma ni domin ni rabonda ya zo gidana har na manta, to shi ne nake so na gaya miki ki yi masa magana a matsayinki na mahaifiyar sa". Da jin wannan magana ta Nahidu sai Kamriyya ta yi farin ciki domin ta samu hanyar da zata Rulla makircinta.
Kamriyya ta yi murmushi ta ce “Ba komai in dan wannan ne kada ki damu yauma zan sa shi ya zo nan gidanki ya kwana in dai har kika amsa zaki aikata abin da zan sa ki". Da jin ance zai zo gidanta ya kwana sai ta ce “Mc kike so na yi miki na dau alkawarin in dai ya zo ni kuwa zan yi miki ko mene ne".Kamriyya ta cc/“Dama ba wani abu ba ne,kwana biyu ni ba ni da lafiya wata cuta cc ta shige ni, shi ne nake so yau idan ya zo gurinki ya yi barci to ki dauko min wannan rigar tasa ta fatar barewa domin na jika ta nasha ruwan ko na samu lafiya". Jin haka sai Nahidu ta ce ai wannan abu ne mai sauki sai da daddaren ki zo ki karba".
A wannan lokaci da fitowar Kamriyya daga gidan Nahidu sai taje ta samu Malukussaifi yana zaunc,da ganinta sai ya mike ya gaishcta ya girmamata ya bata wajc ta zauna bayan ta zauna sai ta ce da shi “Kai kuwa me matarka Nahidu 'yar sarkin Sin ta yi maka ka daina zuwa gidanta? Haba ai ya kamata ka rika yin adalci a tsakanin matayenka". Ya amsa mata ya ce “Ai ba abin da ta yi mini amma babu komai yasma to a gidanta zan kwana". Ta ce "Dama ni abin da ya kaw ni kcnan". Ta tashi ta fita, sai ta koma gidan Nahidu ta gaya mata “To fa ki shirya na je na same shi yau fa a wurinki zai kwana",sannan ta juya ta fita.
Dare na yi Malukussaifi ya taho gidan Nahidu kamar yadda ya fada. Da zuwansa ya kwabe kayansa ya ja mayafi, bayan sun yi hira' sai barci ya kwashe shi, da Nahidu ta ji ya fara jan minshari sai ta san lallai' barcinsa ya yi nisa, sai ta tashi la dauki rigar nan ta sa sai ta lito daga dakin ta nufo inda
Kamriyya ta ke laбe domin ta bata rigai, to a wannan lokaci Damatu ta saka hular batan 'nan ta na yawo cikin gidan kamar yadda take yi kullum to a wannan lokaci ta shigo gidan Nahidun sai ta ganta da rigar kuma ga Kamriyya tsaye nan sai Damatu ta san lallai wani makircin ne. Ba ta yi wata-wata ba sai ta sa takobi ta sare kan Nahidu ko da Kamriyya ta ga takobi bata kuma ga wanda yake rike da ita ba ta sare kan Nahidu sai ta tsorata sai ta juya aguje ta gudu bata dauki rigar ba.
Karar Nahidu yayin da aka sareta sai ta sa Malukussaifi ya farka daga barcinsa ya fito a guje yana zuwa ya tarar da gawar matarsa Nahidu da rigarsa a hannunta ya kuma ga takobi yana yawo a sama shi kadai sai ya ce “Lallai wannan duk yanda aka yi Damatu ce ta aiwata da wannan. Ko da ta ji ya gane ita ta yi kisan sai ta cire hular sannan ta baiyana a gabansa. Ko da ya ganta sai ya ce “Ke kuwa me Nahidu ta yi miki kika kashe ta?”Sai ta ce “Ai dama na gaya maka cikin matanka sai na kashe daya kuma na lissafa maka wadanda banda su ai ba ita a ciki,ba'a da bayan haka kuma laifinta shi ne dubi hannunta ka ga ni ba. Ba rigarka ba ce to hada baki suka yi da uwarka ta dauko mata rigar zata bata ta aikata maka wani sharrin, kai wai ma tsaya kai fa yanzu duk kana zaton uwarka tunda ta baka allonka ba kiyyaya a tsakaninku ko, to bari na gaya maka shi wannan allon da ta baka ba na gasken ba ne. Sawa ta yi aka kera mata na jabu ta kawo ta baka domin ka saki jiki da ita ta samu ta halaka ka”.
Nan da nan ya zaro allon nan ya goga ya goga amma bāi ga Iluru ba sai ya san lallai maganarta gaskiya ce, suka fitä suka tafi gidan Kamriyya suka neme ta kasa ko sama ba su ganta ba nan Malukussaifi ya komo ya yi wa Nahidu wanka yana kuka ya haka rami ya binne ta.
Bayan wasu 'yan kwanaki, wata rana daddare Malukussaifi yana gidan matarsa wadda ya fi so wato Manniyatunnufusi suna kwance suna hira sai ita barci ya kwasheta shi kuma dai ya na kwancc amma ba barci yake ba sai kawai ya ga wani takobi yana walkiya ya nufo kanta tana barci sai yasan Damatu
ce ta zo zata kashe ta sai ya yi wuf ya janyeta ya kifu akanta takobin ya kwanta a shimfidar gadon, sai ya ce "Haba Damatu yaya ne kike nema ki kashe min mata bayan da kin kashe min wata?”
Damatu ta cire hular, ta baiyana gabansa ta ce “Ai in dai baka aure ni ba to sai na kashe duk matanka" Sai ya ce “Ni kuwa da ki kashe min mata gara na fanshi rantsuwata na aureki gobe". Ta yi farin ciki da jin ya ce gobe zai aureta, ta fita ta je ta gayawa uwarta suka yi ta murna a wannan daren ba su yi barci ba saboda murna.
Gari na waye wa fada ta cika makil sai Malukussaifi ya ce a yanka shanu bakwai ya fanshi rantsuwarsa domin zai auri Damatu nan da nan aka je aka yanka shanun nan, sannan aka dawo aka gaya masa. Nan da nan ya yi umarni da a daura musu aure. Sai Damatu ta ce a dakata ta ce "Kafin a daura mana aure sai ka yi min alkawarin duk abin da na tambaye ka zaka ba ni a ranar da ka fara shiga dakina. Sai ya amsa mata ya ce ya yarda, sannan aka daura aure aka shiga shagalin biki.Jama'a ka yi ta shagali.
Cikin gida kuma Damatu amarya ta zauna tare da sauran kishiyoyinta ana kida kuyangi suna ta rawa, can sai Ummulhaya ta fito ta hau rawa ko da sauran kuyangi suka ga ta shigo fagen rawa sai duk suka koma gefe aka barta ita kadai ta yi rawa ta yi rawa ta koma ta zauna sai Jizatu ta fito itama ta yi rawa ta yi rawa ta koma ta zauna sai Shamatu itama ta fito ta yi rawa ta yi rawa ta koma ta zauna sai Damatu ta nuni Manniyatunnufusi da nufin ta fito ta yi rawa sai ta mike ta ce "To kusan fa ni ina da tsohon ciki saboda haka ba wata rawar kirki zanyi ba sannan ta fara rawa duk matayen da suke wajen suka dimauta da ganin irin yadda take rawa sai canta koma ta zauna,sai Damatu ta ce “Da ita amma kuwa kin iya rawa wannan rawar ta ki ta kawatar da ni kwarai sai ta ce "Ai don ma ban sa wata rigata ba ai da na sata da na yi wadda ta fi
Damatu ta ce to ki dauko wannan rigar mana ki saka ta ki yi mana rawar mu gani”. Sai ta gaya mata ta ce “Ai wannan rigar tana wurin mijinmu tun lokacin da muka zo na yi na yi ya bani amma yaki. Ko da Damatu ta ji haka sai ta tuna ai sun yi wata yarjejeniya da Malukussaifi akan duk abin da ta tambaye shi zai bata, sai ta ce “To ki yi hakuri zan kar6o miki rigarki ki yi mana rawa da ita mu gani.
Bayan kwana bakwai duk an gama biki kaf ango ya shigo dakin amaryarsa sai suka zauna suna hira, can sai Damatu ta ce “To yaya alkawarinmu yana nan?” Sai ya ce “Ai ni ba karamin mutum ba ne bana alkawari na fasa, maza yanzu fadi duk abin da kike so na rantse da Allah zan ba ki ko mene ne”. ta ce “Ba wani abu na ke so ba illa rigar nan ta Manniyatunnufusi na ke so ka bani aronta”. Ko da ya ji wannan magana sai jikinsa ya yi sanyi ya kuma tuna matsayin Manniyatunnufusi a wurinsa sai ya ji tsoron kar ya bata wani abu ya faru gareta, amma kuma sai ya tuna ya yi rantsuwa duk da haka sai ya ta shi ya je ya dauko rigar ya kawo ya ce “Ga riga zan baki to amma da sharadi. Sharadin kuwa shi ne kada wani abu ya samu matata kuma kada ki yarda ki bari ta san wannan rigar tana wajenki"Ta ce ta yarda ya danka mata riga sannan suka kwanta barci.
Bayan da gari ya waye Malukussaifi ya fita fada ana zaune ana fadanci sai aka zo aka gya amasa matarsa Manniyatunufusi ta haibu ta haifi da namiji wato dansa na uku ke nan, sai Barnuhu ya ce “Wannan dan a saka masa suna Misira domin kuwa zai gina wani birni Misira nan gaba wanda kuma shi zai jawo kogin Nil”. Nan aka radawa yaro suna Misira.
Wata rana ana zaune a fada sai Malukussaifi ya yi nishadin farauta, sai ya umarci mutane ya ce “Gobe kowa ya fito zamu fita farauta ta kwana uku. Bayan an tashi daga fada duk jama'a suka watse kowa ya koma gida da burin gari ya waye su fita farauta. Kamár yadda Sarki ya fada. Gari na wayewa kuwa sai duk jama'a suka laru a kofar fada cikin shirin su na fita farauta sarki ya filo suka dunguma suka tafi. A wannan tafiyar kuwa
har da babban dansa Damaru dan Shamatu yana dan shekara
goma sha biyu da haihuwa.
A wannan lokaci shi wannan yaron bai dade da dawowa daga wurin wani sadauki da aka kai shi domin ya samu horon yaki ba.
Jim kadan da tafiyar su sai Damatu ta fito fada ta zauna tare da kuyanginta can ma sai ga Shamatu ita mata fito da nata Kuyangin ita mata ta zauna sai ga Ummulhaya ita mata ta fito,sai ga Jizatu ita ma ta fito sanan Manniyatunnufusi ita ma ta fito. Wata Kuyanga tana dauke da jaririnta Misira a cikin wani mayafi na farin alharini an yi masa cinbaki da yakutu ta zo ta zauna sauran mata na gari duk suka taru a fadar suka zauna ana ta fadanci. Fada ta zama ta mata. Zuwa wani lokaci suka sallami matan nan duk suka watse ya zamanto sai su da kuyanginsu.
Damatu ta ce "Manniyatunnufusi yaya maganar mu ta kwanaki game da rawa kin ce in kika saka rigarki akwai wata rawa mai kayatarwa da kike yi to yaya yanzu zaki yi mana?”Ta amsa mata ta ce "To ina rigar take ai kin cc zaki kar6o mini in kin kar6o ta ai sai in yi muku". Damatu ta mika mata riga ta umarci kuyangi suka fara yi mata kida, ita kuwa ko da ta ga rigarta ta zo hannunta sai ta yi farin ciki domin ta samu hanyar gudu.
Manniyatunnufusi ta saka riga ta fara rawva tana yi tana yi har ta dauki danta Misira sai ta yi wuf ta fita waje duk suka biyo ta suna zaton ko duk rawar ce haka sai ta tashi sama ta dubo su kasa ta yi dariya ta ce da su “To ni fa yanzu kasarmu zan tafi idan Malukussaifi ya dawo ku gaya masa inya isa yana jin shi sarki ne madaukaki, to ya biyoni kasarmu”Rufe bakinta ke da wuya ta mika sama rungume da danta ta yi tafiyarta.
Damatu ta tuna dama sai da Malukusaifi ya ce karta bata rigar, kai kar ma ta bari ta san rigar tana wurinta,amma ga abin da ya faru sai hankalinta ya tashi saboda sanin matsayinta a gunsa ga shi ta gudu nan da nan ta aika aka kirawo uwarta
Akila ta zo ta gaya mata abin da ya faru, nan da nan uwarta ta yi shirin bokancinta sai ga wani aljani ya zo ta umarce shi da ya yi maza ya bita ya dawo da ita, cikin hanzari aljanin nan ya yi sama ya bita jim kadan ya dawo ya ce “Ai ina, in dai tana sanye da wannan rigar ba zan iya rabarta ba ma balle na kamo

Please Login or Register in order to submit comment