Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya amsa mana ya ce “Na kashe shi ne bisa umarnin ka, domin kuwa kai ka ce duk lokacin da kuma bijiro wa 'yata ka da ma na yi shawara da kai na kashe shi, ni kumana je na ske shi a cikin gidana tare da 'yata ya kuma mai da ita gida ga nazaje.Shi ne ni kumana kashe shi".
Sarki ya yi shiru kimanin sa'a guda sannan ya ce “To yanzu Waziri ka dauki 'yarka ku fice ku bar mini kasa ta kuma ka je ea tsine ma”. Waziri ya tashi ya fita daga fada ya nufi gida ya Iwashe kayansa da shi da 'yarsa suka bar kasar.
A kwana a tashi har Waziri ya kai kasar wani Sarki wanda 'ke kira da suna Haris. Da zuwan Waziri ya karbe shi hannu ibbiyu domin dama ya san shi kuma a wasu shekarun baya arki Abidunnajami ya tabacinsu da yaki ya kama shi, to a annan lokacin Waziri ne ya yi masa hanyar da ya gudu ya
komo kasarsa. Ya sa aka bawa Waziri da 'yarsa gida aka yi ta
yi musu hidima har tsawon mako guda suka huta.
Wata rana Sarki Haris da Waziri suka kadaita domin ya ji abin da yake tafi da shi, suka zauna Waziri ya kwashe labarinsa kaf ya gayawa Sarki Haris. Ko da ya ji wannan labari na Waziri Kiwanu sai ya ce "To ai shike nan faduwa ta zo daidai da zama dama watan gobe nake so na shirya na tafi na yaki kasar ku domin na dauko fansar abin da Sarkin ku Abidunnajami ya yi min. Tunda kuma ya yi maka wanna abu,to zan je na kashe shi kai kuma na nada ka sarautar wannan birnin naku”. Waziri ya yi shiru da jin wannan kalami na Sarki Haris domin shi yana ganin Sarki Abidunnajami ya fi Rarfinsa.
Waziri Kiwanu ya tambayi Sarki ya ce “Ka sani fa shi Sarki Abidunnajami yana da karfin runduna ta mayaka sannan kuma masani ne wajen ilimin bokanci. Ka ga kuwa yakarsa abu ne mai wahala, yanzu me ka taka har ka.ke ganin zaka iya cim masa?” Sarki Haris ya yi murmushi ya ce “To in runduna ce nasan rundunarsa duka duka ba ta wuce sadaukai dubu ashirin ba,to ni kuwa yanzu ina da rundunar sadaukai masu tsananin taurin kai su dubu tamanin, sannan kuma wajen sha'anin bokanci, ina bokan nan da labarinsa ya bazu cikin nahiyar nan mai suna Baganishu to na jawo shi yanzu muna tare da shi kumayana biyayya bisa ga umarnina”. Waziri ya ce “I to yanzu lallai na san zaka iya da shi.
Nan suka sa ranar tafiya yaki. Suka yi ta shiri dare da rana.Kowane lokaci Sarki Haris da Waziri Kiwanu sai su fito bayan gari a kafa musu tanti su zauna Sadaukai kuma bisa dawaki su yi ta gwajin yaki gabansu. Waziri Kiwanu ya kara gasgata karfin rundunar Sarki Haris.
Shi kuwa can Sarki Abidunnajami tun lokacin da ya kori Waziri bayan ya tafi sai ya rika tunanin irin makircin Waziri saboda haka bai sake ba ko da wane lokaci sai ya rika buga kasa yana ganin halin da Waziri yake ciki. Saboda haka ya gano shriin da Sarki Haris da Waziri Kiwanu suke yi na zuwa yakarsa, ya kuma duba ya ga irin sharinsu ya san lallai in aka
gabza babu nasara,sai ya zauna ya yi shiru yana tunani zuwa
wani lokaci mai tsawo.
Bayan wani lokaci Sarki Abdidunnajami ya tashi ya shiga dakin tsafinsa bai fito ba sai da ya samu mako biyu yana ciki yana tsafi ya sana'anta'wadannan al'amudai guda bakwai, ko wanne al'amudi daya sai da ya saka masa aljanu saba'in,mariddai saba'in ya gewaye birninsa da wadannan al'amudai,sannan kuma ya tattara duk sirrin wannan tsafin nasa ya dunke shi a cikin wata 'yar jakar fata ya sa aka rataye a can saman katangar birnin, kai ya zamto dai ya tsafe garin babu damar shiga.
Sarki Haris da Waziri Kiwanu lokacin da suka diba ya yi suka yi shirin yaki da rundunar Sadaukai dubu tamanin ga kuma boka Baganushu da bokaye arba'in suka kama hanyar zuwa kasar Sarki Abidunnajami, suka yi ta tafiya har suka isa bakin birnin suka yi suka yi amma ina suka kasa shiga birnin nan fa Sarki ya dubi Waziri Kiwanu ya cc “Ka ga aikin bokanci ko?” Sai ya dubi boka Baganushu ya ce "Garcka Baganushu a lalata wannan kafin da ya yi”.
Baganushu ya umarci bokayen nan da ke karkashinsa ya cc “Ku lalata wannan sirrin”. Nan da nan bokaycn nan suka dukufa suka kama 'tsafi ba ji ba gani amma ina suka kasa karya tsafin Sarki Abidunnajami, suka yi suka yi, har suka gaji amma ina suka kasa da suka ga sun kasa sai suka gayawa shugabansu Baganushu sun kasa. Baganushu ya harzuka ya bugi jakarsa ta tsafi ya kama kiran aljanu yana kakaji sai da ya tara aljanu dari uku da sittin sannan ya tambayi aljanun nan ya ce su gaya masa yadda sirrin wannan tsafi na Abdidunnjami yake, sai suka gaya masa duk sirrin wannan tsafin sannan kuma suka gaya masa samun makarin wannan kafin. Sai a taskar Kaushu ďan Kan'ana za a samo shi.
Baganushu ya umarci aljanun nan da su dauke shi su kai shi wannan taskar kafin kiftawa suka kai shi da zuwansa aljanun dake gadin taskar suka tambaye shi me ya kawo shi ya gaya musu ya kuma yi sa'a suka yarda zasu ba shi. Suka dauko wani
dan mayani da farin yashi a cikinsa da wani kwari na harbi da kuma kibiyoyi guda uku suka ba shi suka ce da shi idan kaje ka watsa wannan yashin kan al'amudi na fakro duk aljanun da ke jiki za su gudu, sannan ita kuma wannan kwari ka yi amfani da wadannan kibiyoyi ka harbo wannan fatar da ke rataye,kan katangar birnin. Idan ka harba kibiya ta farko baka samu fatar ba to kasa zata kama ka iya gwiwa, idan ka kuma harba ta biyu baka samu ba kasa zata kara kama iya kugu, amma idan ka harba ta uku baka samu ba shi ke nan zaka nitse cikin kasa.Sannan kuma muna gargadinka da in bukatarku ta biya ka dawo mana da wannan kwarin idan kuma baka dawo da ita ba duk abin da ya faru gareku kai ka jawo muku”.
Baganushu ya yadda da wannan sharadi ya kar6o ya tawo aljanun nan suka kara dauko shi suka dawo da shi inda sansanin su yake. Da zuwansa ya kwance mayanin nan ya watsa ya shin nan kan al'amudi aljanu da mariddan nan duk suka gudu sannan ya zaro kibiya ya auna jakar fatar nan ya tabe kyauro ya saki amma ina sai ya kuskure bai samu ba, sai ya ji kasa ta kania shi iya gwiwa, ya kuma zaro wata kibiyar ya kuma auna wannan jakar ita ma ya kuskure ya kuma ji kasa ta kama shi iya kugunsa sai ya yi nadama hankalinsa ya tashi ya yi kamar ba zai kara na ukun ba sai ya tuna to ai in ma bai kara ba kasar nan ba sakinsa za ta yi ba haka zai ta zama annan har ya mutu.
Nan fa ya sake harzuka ya yi wuf ya zaro kibiya ta uku ya auna wannan jaka sai ya yi sa'a ya sami jakar ta fado kasa.Fadowar jakar ke da wuya kasa ta sake shi duk kofofin birnin suka bude hanhai. Sarki Haris da Waziri Kiwanu da rundunarsu suka dunguma cikin birni, cikin kankanin lokacin suka rinjayi Sarki Abidunnajami da duk jama'ar kasar.
Waziri Kiwanu ya hau gadon Sarautar kasar sannan shi kuma sarki Haris da jama'arsa suka zauna a kasar domin su yi 'yan kwanaki su huta a nan, sannan su koma zuwa kasarsu.
Shi kuma boka Baganushu ya manta da alkawarin da ya dauko a wurin aljanun taskar Kaushu dan Kan'ana na cewar da
zarar bukata ta biya zai mayar da wannan kwari da baka da suka ba shi. Har tsawon wasu kwanaki bai mayar ba ya manta,saboda haka suna cikin wannan hali sai wadannan aljanu suka zo suka yake su suka halaka duk wani mahaluki da yakc wannan wadaye guda bakwai, to ka ji wannan shi nc cikakkcn tarihin wannan wadayen da ka gani”.
Malukussaifi ya yi al'ajabin wannan labari kwarai sannan ya ce da Hairakana tun da gari ya wayc ai sai mu yi aniya zuwa wadi na shida." Hairakana ya daukc shi suka mika da tafiya izuwa wadi na shida. Nan da nan cikin wani dan lokaci suka sauka a wadi na shida. Kafin azahar suka dan huta a nan sannan suka ci gaba da tafiya, daf da magariba suka sauka a wadi na bakwai suka kwana a nan.
Gari na wayewa sai Hairakana ya cc “To ai sai mu yi aniya maza mu tafi". Hairakana ya ce “Ai ni nan shi nc iyakata ba ni da ikon matsawa gaba daga nan. Kai yanzu a nan zan zauna na yi jiranka har ka dawo". Ya mikawa Malukussaifi jakarsa wadda kayayyakinsa da Nurulzaitun ya ba shi. Ya karba suka yi sallama ya kwama hanya ya tafi.
Bayan da ya samu kimanin sa'a uku yana tafiya sai ya 70wani katon fili wanda babu komai a cikinsa illa rairayi fari kal ga wata korama mai gudana. Ya nufi gindin koramar nan ya sha ruwa ya koma gefe ya zauna yanahutawa. Jim kadan sai ya rika jiyo hayaniya da motsi na mutane, sai ya yi wuf ya koma bayan wani dutse ya buya ya tsaya yana kallon hanya can sai ya hango wasu mata kungiya guda sun taho suna sanye da riga iri daya, kuma ya ga rigar irin wadda Nurulzaitun ya ba shi din nan ce amma kuma launin tasu da tasa ya banbanta sai ya rika rayawa a zuciyarsa ko ya saka tasa rigar ya shiga cikinsu ne,sai kuma ya ga to ai in ya shiga shi tasa launinta ya banbanta da nasu saboda haka ai nan da nan za'a gane shi sai ya fasa ya bisu da kallo kawai har suka zo tsakiyar filin nan.
Ana cikin haka sai ya kuma hango wata kungiyar matan sun taho, sai ya ga su kuma launin tasu rigar ya banbanta da ta na farko kuma shi ma ta banbanta da tasa, haka suma suka zo
wannan fili. Nan da nan sai ga wata kungiyar nan ta taho suma yaga launin rigarsu ya banbanta da tasa da ta sauran matan.Kai bai gushe ba matan nan suna ta zuwa kungiya-kungiya har sai da suka cika filin nan taf amma ba babu masu launin rigarsa, nan fa ya dimauce ya kama addu'a ta neman dacewa,kafin ya rufe bakinsa sai ya hango kungiyar wasu matan ta taho sai ya ga ai duk irin rigarsa ce a jikinsu ita kuma wannan kungiyar ita ce wadda sarauniya take cikinta. Ganin haka bai wata-wata ba ya sanya rigarsa ya sadada ya shiga cikinsu suka tafi har zuwa wannan fili.
Bayaun da suka shiga wannan fili sai ya ga kowacce ta dauko 'yar lailayayyiyar bal irin wadda aka ba shi. Shi ma nan da nan sai ya dauko tasa·ya rika wasa da ita kamar yadda ya ga suna yi. Haka ya yi ta wasa a cikinsu babu wadda ta gane shi,suna cikin wasan sai wata daga cikin kungiiyar da yake ta yi shela ta ce “Ya ku 'yan mata Sarauniya tana yi muku umarni da ku daina wasa haka a tsaya a ci abinci, sannan a ci gaba da wasa. Sai duk 'yan matan nan suka zauna kungiya-kungiya aka kawo abinci da kayan marmari iri-iri suka ci suka sha sannan duk suka koma wasa.
A wannan lokaci ai kowacce ta rika tsalle tana dafe 'yar uwatta suna wasan goyo, ganin haka sai ya komo gefe gudà ya tsaya yana kallon su. Can yana tsaye sai wata ta ce da shi “Ke ya naga kin tsaya kurum ba kya wasa lafiya". Kafin ya budi baki ya yi magana sai ta yi wuf ta dane bayansa ko da ta dira a gadon bayansa sai ta ji duk jiki a mummurde ba kamar yadda ta saba jin jikin sauran mata 'yan'uwanta ba ta shafa kirjinsa ta ji shi tikirkir sai ta duro ta komo gabansa ta yaye fuskarsa sai taga gashin baki ta tabbatar lallai namiji ne ba mace ba cc sai ta ce da shi “Kai kuwa yaya aka yi ka shigo kasar nan kuma me ya kawo ka?” Ya amsa mata ya ce “Ikon maiduka nc ya shigo da ni kuma na zo nan ne neman matata”. Da ta ji haka sai ta ce “Matarka ai mu nan kasar babu namiji ko daya kuma wadannan 'yan matan duk da ka ke gani mafi yawancin su babu wadda ta taba sanin wani abu wai shi namiji balle har ka
kira wata daga cikinsu matarka karya kake, kuma yau ka kawo
kanka ga halaka yanzu zan ma ihu su halaka ka.
Ta yunkura ta bude baki zata yi ihu ya yi wuf ya danke bakinta ya jata gefe daya ya ce "Na roke ki na kuma mika amanata gareki ki rufa min asiri kuma ki taimakie ni” Ya yi ta yi mata kalamai masu karya zuciya da sanyaya zuciya sai jikinta ya yi sanyi tausayinsa ya kamata ta ja shi gefe ta ce"To shike nan na yadda zan taimake ka na dauki amanarka amma yanzu abin da za a yi zan fita da kai zuwa kungiya-kungiya ta matan. nan zan rika kiran sunan ita wannan matar taka idan masu wannan sun fito zan kalli sukarka idan da ita a cikinsu sai ka yi min inkiya da ido, idan kuma ba ita ba ce sai ka girgiza kanka, amma fa kar ka sake ka yi yadda za su gane abin da muke ciki, idan kuwa ka ga matarka zan yi iyaka bakin kokarina na taimaka maka ka dauketa ku tafi”. Malukussaifi ya yi matukar farin ciki da jin wannan magana ya ce "Madalla da ke wannan ma'abociya kyautayi da yawan tausayi. Ke kuwa yaya sunanki kuma mene ne matsayinki a wannan garin naku?”
Ta nisa ta amsa masa ta ce “Ni sunana Murjanatu kuma ni ce Waziriyar Sarauniyar wannan garin namu". Nan dai ta bayyana kanta gare shi, sannan suka komo cikin mata ta rika yawo da shi cikinsu. Da suka shiga cikin wata kungiya sai Murjanatu ta ce “Maniyatunnufusi sai 'yan mata biyu saka amsa suka zo gabanta suka gaida ita sai ta ce da su yaya tun dazu ban ganku ba shi ne na ce ko lafiya?” Sai ta dubi Malukussaifi sai ya girgiza kai sai suka wuce zuwa wata kungiyar ta kuma cewa "Manniyatunnufi". Sai wata ta fito ta dubi Malukussaifi ya kuma girgiza kai, suka wuce zuwa wata kungiyar, kai haka dai suka yi ta zuwa kungiya-kungiya, har suka gama zagaye matan nan kaf amma baiga matarsa ba.
A nan sai Murjanatu ta ce da shi “To kaga yanzu duk mun zagaye matan nan bamu ganta ba to yanzu babu wasu mata sai matan da suke fada yanzu can zamu je idan baka ga matarka a nan ba to matarka bata wannan gari namu" Şuka juya suka
nufi inda Sarauniya da 'yan majalisarta suke, Da zuwansu sai duk matan da suke fada suka mike domin girmamawa ga Waziriya Murjanatu, ta wuce ta zauna kusa da Sarauniya,shi kuma Malukussaifi ya samu waje ya zauna ba tare da wata fargaba ba, domin kuwa rigarsa irin ta duk matan da ke fadar ne.
Bayan da magariba ta kawo kai sai duk matan nan suka dunguma zuwa cikin birni tare da Malukusssaifi. Da shigar su aka raka Sarauniya gida sannan aka rako Waziriya Murjanatu gida suka shiga tare da ita da Malukussaifi. Ya shiga cikin kuyanginta aka shiga gidan tarc da shi. Sannan duk sauran matan kowacce ta tafi izuwa gidanta.
Murjanatu ta ja Malukussaifi wani daki da ke can cikin gidanta suka zauna aka kawo musu abici suka ci suka sha suka huta sai ya ce da ita “Ai da muka je fadar nan naga matata".Sai ta tambaye shi la cc “wace ce daga ciki?” Sai ya amsa mata ya ce "ai wannan sarauniyar ita ce matata babu shakka domin kuwa lokacin da muka gamu da ita a wata gona kafin na aureta ta gaya min ita sarauniya ce. A haka dai na aureta har muka haihu da ita sannan ta hilace ni ta karbi rigarta ta tashi ta gudo min da dana", Ko da Murjanatu ta ji haka sai ta ce “Ko kai ne Malukussaifi dan Sarki Ziyyazanun?”
Ya amsa mata ya ce “Ai ni ne, yaya aka yi kika samu labarina ke kuwa?” Murjanu ta ce.“Ai na sau labarinka a wurin matarka-wadda ka taho nema, ai ita wannan sarauniya da ka gani ba ita ce matarka ba kanwarta ce, ita kuma sunanta Nurulhuda. A da matarka Manniyatunnufusi ta kasance ita ce Sarauniyar wannan birni to a lokacin da muka je gona hutawa bayan mun gama abin da za mu yi, za mu komo gida sai aka nemi rigarta aka rasa sai muka komo domin mu daukar mata wata rigar. Da muka koma sai muka ga bamu ganta ba muka yi ta neman ta har muka gaji ba mu ganta ba, sai muka komo gida sannan muka rubuta takarda game da batan Sarauniya muka aika wa ubanta dake can birnin Maza wato Sarki Abisul'abusi.
Da Sarki Abisul'abusi ya ga wannan takarda ya yi matukar bakin ciki da batan 'yarsa ya tara bokayc daga kasa-kasa akan su binciko masa inda 'yarsa takc, nan fa bokaycn nan suka dukufa suka yi ta bokanci ba dare ba rana har tsawon kwana arba'in sannan suka zowa da sarki labari suka gaya masa ai 'yarsa tana hannun wani sarki mai girman sha'ani wanda shi wannan Sarki shi ne wanda zai zo ya mulki duniya kuma a tun yanzu ma yana da iko a kan aljanu da mutane. A yanzu shi ne Sarkin kasar Yemen wata babbar kasa a yammacin duniya,wadda daga nan zuwa wannan kasa ta Yemcn tafiyar shckara dari uku da tamanin ce a kukwane bisa ingarman doki. Sannan kuma shi wannan Sarki sunansa Malukussaifi dan Sarki Ziyyazanun kuma ya riki 'yarka ne ba kuyanga ba, ba baiwa ba ya auréta ne ta zamo daga cikin matayensa.
Da Sarki Abisul'abusi ya ji wannan magana ta bokayc sai ya yi shiru har zuwa wani dan lokaci can sai ya dubi Wazirinsa, ko da Waziri ya ga haka sai ya ce, “To ai wannan mu abin farin ciki ne ma, mu a wajen mu Sarki mai girman sha'ani irin wannan, ai yau a ce wani talaka ne ko kuma shi ya riketa ne a matsayin kuyanga ko baiwa shi ne abin damuwa amma wannan ai babu komai. Da Sarki ya ji wannan kalami na Waziri sai zuciyarsa ta yi sanyi bakin cikinsa yajuye izuwa farin ciki, ya sallami bokayen nanduk suka tafi izuwa garuruwansu.
Bayan da aka kwana biyu sai ya aiko mana da wasika ya bayyana mana duk abin da ya faru sannan kuma ya umarce mu da mu nada kanwarta ita wannan Nurulhuda din ta zama Sarauniyar wannan birni namu, shi ne muka nada ta ta hau gadon mulkin wannan birni namu na mata.
Bayan wani lokaci mai tsawo wata rana muna zaune a fada sai kawai muka ga Manniyatunnufusi rungume da jariri ta sauka a kofar fada, ko da ganinta duk saj muka yi ta murna ta dawo, amma ita kuwa 'yar'uwarta Sarauniya Nurulhuda sai ranta ya baci domin/tana gudun idan ubanta ya samu labari ta dawo to zai aiko a sauke ta daga mulki a mayar da 'yayarta
kan mulkinta. Ita kuma ga shi ta dandana giyar mulki ta ji dadi. To a saboda wannan dalili sai ta sa aka kamata aka saka ta da ita da dan jaririn ta a kurkuku aka kulle ta, a yanzu baka matarka tana can a kulle".
De Malukussaifi ya ji wannan labari na Murjanatu saiya Ragauta da ya ga matarsa Manniyatunnufisi sai ya ce“To yanzu yaya za ai na ganta?” ta ansa masa ta ce “Ai so nake dare ya natsa sawu ya dauke za mu je ka ganta a yau din nan.Suka ci gaba da hira har dare ya -raba, sannan suka fito su biyu suka nufi gidan kurkukun, da zuwansu suka tarar da dogarawa mata masu jiran gidan kurkukun. Da suka ga Waziriya Murjanatu duk sai suka zube suka yi gaisuwa gabanta sanoan suka bude musu kofa suka shiga suka yi ta wuce soraye sannan suka isa wajen wata katuwar kofa ta karfe wadda daga ita sai cikin kurkukun.
A wannan kofar kuma a nan ne shugaban masu gadin wannan kurkukun take wadda ake kira da suna Kaukabu. Da zuwan su Kaukabu ta fadi ta yi gaisuwa gaban Murjanatu,sannan ta ce “Ranki ya dade ke ce kike tafe cikin daren nan,wannan kuma wace ce kuke tare da ita?”Murjanu ta amsa ta ce “Na zo ne naga Manniyatunnufuisi, wannan kuma da kika ganmu da ita wata tsohuwar kuyangar Manniyatunnufusi ce ta roki alfarma a wajena da na kawo ta ta ganta shi ne na taho da ita domin na cika mata burinta”. Kaukabu ta matso kusa da Malukussaifi ta bude mayafin da ya rufe fuskarsa sai ta ga gashn baki sai ta ja da baya ta dubi Murjanatu ta ce “Yaya aka ki ka shigo mana da namiji kasarmu ai wannan cin amana ne.Kuma yanzu zan sanar da sarauniya bisa ga wannan'aibu da kika aikata”.
.Koda Murjanatu ta ji wannan magana ta Kaukabu sai ta waiwayo a fusace ta ce da Kaukabu “Ke bari ma na gaya miki na ma daina 6oye miki hakika wannan ba mace ba ce namiji ne, kuma shi ne mijin ita Manniyatunnufusi. Saboda haka na kawo shi ne domin ya ganta kuma ya tafi da ita ko kinso ko ba ki so"ba”. Da jin wannan sai Kaukabu ta ce “Ko shi ne
Malukussaifin nan da muka samu labarinsa a wurin bokayen nan na Sarki Abisul'abisi?' Ta amsa mata ce ai shi ne mana”.
Kēukabu ta zube kasa gaban Malukussaifi ta yi masa kirari fana fadar nasabarsa tana ba shi hakuri tana cewa ka yi hakuri bisa ga abin da muka yi maka na daga tsare matarka da aka samu muka yi, kuma yanzu ina mai baka tabbacin goyon baya da taimaka maka da duk wata hanyar da zaka yi ka kubutar da matarka daga nan wurin”. Nan da nan ta zaro makulli ta bude Rofa suka shiga cikin kurkukun suka iske Manniyatunnufusi tana kwance. Malukussaifi ya ganta ta rame duk ta fita daga haiyaeinta. Ganin haka sai idanuwansa suka cika da hawaye sabođa tausayi. Ya matsa kusa da ita sai ya sabi wata waka irin ta ma'abota bege bati hudu. Yana cikin wannan waka tasa ita kuma Manniyatunnufusi ta na kwance sai ta jiyo sautin muryar sa sai ta ji abin kamar a mafarki sai tà tashi zaune ta bude idonta, tana bude idonta sai taga Malukussaifi a tsaye a gabanta ta gasgata ganinta da shi, sai suka rungume junansu,take duk suka suma saboda shaukin bege suka dan jima cikin wannan hali, sannan Murjanatu ta yayyafa musu ruwa suka farko daga suman da suka yi. Suka samu kamar rabin sa'a suna kallon junansu, sannan can Malukussaifi ya numfasa ya ce “Ke kuwa me ya rude ki har kika aikata min wannan aiki kika gudo min, na rasa ki, kuma na rasa dana kika wahalar da ni wajen yawon nemanki?”
Ita ma ta nunfasa ta ce "Ina neman rangwame gareka bisa ga wannan laifi da na yi maka kuma na gode Allah da kazo ka tarar da ni a cikin wannan hali na muzanta wanda ya afku gare ni sakamakon wannan aibu nawa”. Cikin raurawar murya ya ce “Babu komai na yafe miki wannan abu ma ai kaddara ne babu komai”
Daga nan sai Kaukabu ta kwance mata marin da ke kafarta suka fito duk gaba dayansu suka komo gidan Murjanatu ba tare da kowa ya sansu ba. Da zuwansu Malukussaifi ya dauko kwaryar nan tasa ya lullubeta da mayani ya fadi nasabarea sannan ya ce yana so a kawo gurasa da zuma da dabino, yana
rufe bakinsa ya bude kwaryar sai ya ga abubuwan nan kamar yadda ya lissafa su cike da kwarya. Dukkan su suka ci suka sha suka zauna suna hira yana ba su labarin irin abubuwan da ya gani kafin zuwansa garin. Suna cikin wannan sai suka ji ana buga kofar gida.Murjanatu ta tashi ta nufi bakin kofar gida

Please Login or Register in order to submit comment