Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta bude kofa sai ta ga wata kuyanga ce ta zo ta tambayeta ta ce "Yaya lafiya cikin tsohon daren nan?" Kuyangar nan ta fadi tayi gaisuwa gaban Murjanatu ta ce "Ranki ya dade Sarauniya Nurulhuda ce ta ce maza-maza yanzu ki zo tana neman ki cikin gaggawa”.Ta ce “To jeki kice ina zuwa”.
Murjanatu ta koma cikin gida-ta ce da Kaukabu "Maza ki koma can kurkuku domin yanzu Sarauniya ce ta aiko na jë ina zargin ko wani abu ne ya faru”. Kaukabu ta koma kurkurku,ita kuma Murjanatu ta nufi fada suka bar Malukussaifi da Manniyatunnufusi a cikin gidan.
Murjanatu da zuwanta ta iske sarauniya Nurulhuda zaune ita kadai, ko da ta ganta sai ta ce “Yauwa dama ke nake jira”.Murjanatu ta zauna ta ce Yaya aka yi lafiya kike nemana cikin wannan daren?”Sarauniya ta ce “Na kirawo ki ne domin na bayyana miki wani mafarki da na yi wanda ya razana ni a wannan daren cikin barcina. Na yi mafarkin wai ga ni a daure kuma ga 'yar'uwata Manniyatunnufusi kan wani farin doki ta zare takobi ta nufo ni sannan kuma bayanta ga wani mahaukacin zaki yana gurnani, can kuma sai wannan zakin ya zo ya banke ni na fadi kasa, ana cikin haka sai na faka a gigice hankalina ya tashi shi ne na aika a kirawo min Bokanya Kaluhata domin ta zo ta fassara mana wannan mafarki nawa".Kafin ta rufe bakinta ta sai ga bokanya Kaluhata ta shigo. Da zuwanta ta fadi ta yi gaisuwa ta ce "Gani ranku ya dade".Sarauniya ta ce “Na kirawo ki ne domin ki fassara min wani mafarki da na yi, ta kwashe labarin mafarkinta ta gayawa bokanya.
Bokanya Kaluhata ta baje kayan tsafinta ta fara buga tsafi ta yi ta yi har zuwa wani lokaci sai ta dago kanta ta dubi

Sarauniya ta ce "Na gano miki fassarar mafarkin". Sarauniya
ta ce maza gaya min na ji".
Bokanya ta ce "Wato abin da ya faru shi ne mijin wannan
'yar'uwa taki Manniyatunnufusi an shigo da shi garin nan
kuma an kai shi wurin matarsa ya kwance ta ya fito da ita,
kuma ba wani ne ya aikata duk wannan aiki ba illa waziriyarki
gata nan kusa da ke, kuma shi wannan mutumin in ba da gaske
ki ka yi ba zai halaka mu ya kama ki ya raba ki da mulkinki.
Kuma ya daure ki kamar yadda ki ka gani a mafarkinki. Kin ji
wannan shi ne fassarar mafarkin ki kuma yanzu ma zancen nan
da nake miki suna gidanta mą ita wannan waziriyar ta ki".
Ko da Murjanatu ta ji wannan magana ta bokanya sai ta cc
"Ai wannan ma zancen banza ne yaya za ai namiji ya shigo
garin nan bayan duk dakon tsafin da ke garin nan. Ai sam ma
wannan magana karya ce kawai". Sarauniya ta sallami
bokanya ta tafi, sannan ta juyo ta ga ran Murjanatu ya baci sai
ta ce da ita "Haba Murjanatu me ye za ki damu kanki da
wannan maganar ai ke ma kin san na san babu yadda za a yi ki
ha'ince ni. Ai ke ce mafiya yarda daga cikin yardadduna ai
babu komai". Murjanatu ta ce "To shike nan ni zan tafi”. Sai
Sarauniya ta ce to ai ni yanzu ba zan iya barci ba domin na
razana kwarai saboda haka yanzu ki zauna ki taya ni hira har
zuwa wayewar gari".
Haka suka zauna suka yi ta hira har gari ya waye. Sai
Sarauniya ta ce "To yanzu ke sai ki fita fada yau ki zauna
wajen fadanci ni zan kwanta na huta a gida". Murjanatu ta tafi
fada ta zauna wajen fadanci ita kuma Sarauniya ta fita ta tafi
kurkuku ta duba ta ga Manniyatunnufusi bata nan, sai ta fito ta
tafi gidan Murjanatu ta kwankwasa kofa, sai kuyangin gidan
suka amsa mata suka ce "Waye a nan". Sai ta ce kuyangar
Manniyatunnufusi a da, kuma na tambayi Waziriya Murjanatu
ta gaya min tana nan gidan ita da mijinta". Su kuma kuyangin
da suka ji haka sai suka san lallai wannan magana babu wanda
ya santa illa Murjanatu da Kaukabu da kuma su da suke gidan,

sai suka san lallai wannan ba karya take ba Murjanatu ce ta
turo ta, sai suka amsa mata suka ce "I,suna nan".
Da sarauniya ta tabbatar da hakikanin lamarin suna nan sai ta koma fada, da zuwanta ta yi umarni aka kama Waziriya Murjanatu, ta ce “Na amince miki amma kika ha'ince ni ki ka kawo min namiji kasata ko?".Murjanatu ta ce “To ai ni yin wannan da na yi na yi ne domin na shirya wata dabara na kama shi cikin yaudara, domin kuwa shi wannan mutumin ba za mu iya yakar sa ba. Amma ni dai na gaya miki kada ki kuskura ki ce za ki yake shi". Sarauniya ta ce “Ba wani nan karya ki ke munafuka ya ya duk yawan nan namu mutum daya zai gagaremu,da sannu za ki ga yadda zan kama shi na kashe shi”.Murjnatu ta ce "Ai karya ki ke yi wannan magana ta ki ki ma daina ta zancen banza ne”.
Nan da nan Sarauniya ta hada sadaukanta mata su dubu ashirin, ta umarce su da su je su yaki Malukussaifi,duk suka dunguma zuwa gidan Murjanatu, ko da suka kusa, can daga cikin gida sai Malukussaifi ya jiyo hayaniyar su sai ya sha jinin jikinsa ya san abin da ya faru, sai pa ce da Manniyatunnufusi ta tashi mu fita mu gani me yake faruwa".Ya zare takobinsa suka fito waje da fitowar su sai ya hango rundunar mata nan tafe cikin shirin yaki, da isowarsu sai suka kaure da yaki ya riki baryar dama ita kuma ta riki baryar hagu,suka yi ta gabzawa duk in da ya juya sai kawuna ke zuba kasa kamar ganye. Cikin kankanin lokaci sun yi musu muguwar barna.Ganin haka sai Sarauniya ta san lallai idan har aka kara natsawa zai karar da su sai ta aika aka kirawo bokanya Kahulata ta ce da ita "Maza taimaka mana daga cikin irin hikimominki na tsafi mu kama wannan mutumin".
Cikin hanzari bokanya ta dauko wani kasko ta rura wuta garwashi ya hadu ya yi ja jawur ta saki gashin kanta ta rika wasu surutai tana hura wutar nan da bakinta, can kuma ta dauko wani dan karfe mai tsini ta saka shi cikin wutar nan ya yi ja sannan ta dauko shi ta nuni Malukussaifi da shi tana sambatu. Kan ka ce meye wannan duk sai ya ji ga6obinsa
kamar an daddaure masa su kuma ya ji ya gaji, saboda haka sai ya samu rauni wajen yin yakin suka rufo masa za su kama shi yana kai musu sara da kyar.
Da Manniyatunnufusi ta ga haka sai ta ciro danta daga baya ta rike shi a hannuwanta ta daga shi sama ta fara addu'a tana ce "Ya Ubangiji ina rokon ka domin girmanka da sirrin da ke tsakaninka da Annabinka Ibrahima Halilullahi (A.S.) da Annabin Muhammadu (S.A.W.) ka sababa sababin ku6utar mu daga wannan bala'i”. Bata rufe bakinta ba sai Annabi Halliru yazo wucewa ta wannan wuri ya kuma tarar ana wannan yakin ya kuma san me ake ciki sai ya daga kansa sama sai ya gani rubuce a allon lau'ulmahafuz ai kubutar Malukussaifi daga wannan yaki tana hannunsa. Nan da nan sai ya tafi kasar Dawariza, ita kuma wannan kasa tana karkashin wani babban Sarki mai suna Shahazzaman shi ne Sarkinta kuma daga wannan kasar zuwa ita waccan kasar tafiyar shekara talatin ce,amma Amabi Halliru (A.S.) ya yanke ta cikin 'yan-dakiku.
Da zuwa ya musuluntar da Sarki Shahazzaman da duk jama'ar kasar sannan kuma ya gaya masa tunda ya musulunta yanzu lallai ya wajaba kansa ya shirya ya debi sadaukansa su tafi izuwa birnin mata su taimakawa Malukussaifi. Ba musu nan da nan Sarki ya hau da sadaukai dubu hamsin,Annabi Halliru (A.S.) ya wuce gaba suka bisi cikin kankanin lokaci suka isa birnin mata da zuwansu suka abka musu da yakI,kakin azahar sun yi wa matan nan kaca-kaca,Manniyatunnufusi kuma ta lala6a ana cikin yaki ta kama 'yar'uwarta Sarauniya Nurulhuda ta daure ta, shi kuma Malukussadi tuni ya kashe ita wannan bokanya Kahulata.
Ganin haka sai duk sauran matan suka daina yaki suka mika wuya suka sallama. Bayan an daina wannan yaki Sarki Shahazzaman ya zo wurin Malukussaifi ya yi masa jinjina ya ce “tunda yanzu yaki ya kare ni da jama'a ta yanzu zamu tafi mu koma zuwa birninmu". Malukussaifi ya ce "Madallah da kai wannan Sarki mai yawan kyautayi,amma yaya za a yi har ka ce zaka koma baka tsaya mun dan yi zance da kai ba na
tambaye ka labarinka kuma da yadda kai ka sanni har ka zo ka taimaka min". Sarkin ya yi murmushi ya ce Ko da yake yanzu ba lokacin zance ba ne amma ni ninc Sarki Shahazzaman Sarkin Kasar Dawariza,kuma Sheihinka Annabi Halliru (A.S.)ya musuluntar da ni ya kuma bani labarinka kuma shi ya umarce ni da nazo na taimaka maka. Amma sauran bayani sai ka zo kasata ka ji domin daga nan zuwa Rasata tafiyar shekara talatin ce amma Sheihinka ya kawo mu cikin lokacin da baifi rabin sa'a ba, sannan kuma ya ce da mun gama wannan yaki kada mu tsaya mu fito ya yi mana jagora mu koma. To ka ji wannan shi ne dalilin rashin tsayawata sai ka zo.
Sarki Shahazzaman da jama'arsa suka fito bayan bisni Annabi Halliru (A.S.) ya wuce gaba suka bi shi kafin sallar magariba Sarki Shahazzaman da jama'arsa suka isa kasarsu Dawariza.
Nan shi kuma Malukussaifi da Manniyatunnufi da Murjanatu da Kaukabu sun kame birnin mata. Ita kuwa Sarauniya Nurulhuda tana can daure. A wannan lokaci Malukussaifi ya musuluntar da duk matan garin nan sannan ya sa aka kawo Sarauniya Nurulhuda daure cikin sarka ya zare takobi zai sare ta, sai Manniyatunnufusi ta ce “Karka kashe ta ka yi mata rangwame ka tuna fa 'yar'uwata ce".Jin wannan magana sai ya fasa kasheta ya kwance mata marin da ke kafarta.
Ganin haka ita kuma Nurulhuda sai ta fashe da kuka tana cewa 'yar'uwata yanzu duk da izayar da nasa aka rika yi miki ashe har yanzu kina Kaunata, ina rokon ki yafe ni duk abin da na yi miki a baya nima dama ba yin kai na ba ne babanmu ne yaiko ya umarce ni da na rika yi miki haka domin ya zamto hukuncinki bisa laifin da kikai wa shi wannan miji naki na daga gudo masa da dansa da kika yi".Manniyatunnufusi tausayi ya kamata ta rungume ta tana cewa "Na yafe miki"
Bayan da gari ya waye aka fito fada Manniyatunnufusi ta dare gadon sarauta rungume da danta a gefenta na dama ga Malukussaifi da Nurulhuda a gefenta na hagu kuma ga
Murjanatu ga Kaukabu duk sauran mata na gari suka zo suka yi mubayi'a aka zauna ana fadanci. Can sai Malukussaifi ya ce “To ni fa yanzu ba zan bar garin nan ba sai na karya wannan tsafin na garin nan da na garin mazan can. Maza sun shigi an zauna maza da mata kamar yadda sauran garuruwa suke”.
Manniyatunnufusi ta ce “Ai wannan abu ne mai sauki domin kuwa na san in da sirrin wannan tsafin ya ke”. Jin haka saiya ce a ina yake?" Ta amsa masa ta ce “Shi sirrin wannan tsafin yana karkashin wannan karagar da nake zaune idan ka daga ta zaka ga wani rairayi ka share shi zaka ga wata kofa ta farin karfe ka jawo ta ka bude ta; zaka ga wata matattakala ta yi kasa cikin ramin sai ka bi wannan matattakalar, idan ka shiga ramin zaka ga gumaka na bakn karfe a kowace kusurwa sannan kuma zaka ga wani mutum zaune a tsakiya na farin karfe, sama da shi akwai wani mizani na tasa dama da hauni.Idan ka ga tasar nan ta hagu ta rinjayi ta dama to ka komo ka fito wannan sirrin ba zai karyu ba, idan kuma ka ga tasar da ke dama ta rinjayi ta hangu to akwai nasara wannan sirrin zai karyu, sai ka duba daga barin yamma zaka hango wata guduma da kulki a rataye to karka batasu daga kasa zaka ga wani tsuntsu na jan karfe sai ka dauki tsuntsun ka nuni wannan mutum na tsakiya da shi ka gewaya shi sau uku sannan ka mai da tsuntun ka ajiye, ka dauko wannan gudumar ka ajiye a gaban wannan gunkin mutumin na tsakiya. Sannan kuma ka dauko wannan kulkin ka dora shi akan gudumar nan ka koma 6arin kudu ka tsaya bayan wani dan lokaci zaka ga wannan guduma da kulkin nan sun rufe gukin nan da duka har sai sun rugurguza shi,To shi ke nan sirri ya karye”.
Rufe bakinta ke da wuya ta tashi,ya janye karagar ya share yashin nan ya bude kofar kamar yadda ta gaya masa ya sauka ya bi mattakalar nan ya je ya aikata duk kamar yadda ta gaya masa ya dace ko ya karya sirrin tsafin nan ya fito.
To a wannan lokaci fa sai matan kasar duk suka komo cikin hayyacinsu sai kuma sha'awa ta fara damunsu da tunanin maza. Da Malukussaifi ya ga haka sai ya rubuta takarda zuwa
ga Sarkin birnin maza Sarki Abisul'abisi ya shaida masa cewa ya karya tsafin birnin mata shima ya karya tsafin birninsa na maza domin su zo ya aurar da su.
Ana cikin wannan hali sai suka jiyo hayaniya da hargowar mutane, nan da nan Malukusafi ya zare takobi ya fito duk matan nan suka biyo bayansa ya nufo bakin kofar birni ya tsaya ya hango wata runduna ce ta nufo birnin. Ya tsaya ko da rundunar nan suka matso kusa sai ya daka musu tsawa ya ce "Ku tsaya a nan kada ku karaso nan". Duk sai jama'ar nan suka tsaya. Sai Sarkin ya ce “Karka damu ni ne Sarki Abisul'abisi Sarkin birnin maza kuma uban matarka Manniyatunnufusi,bokaye na ne suka sanar da ni cewa ka bata sirrin wannan birni shi ne nima na saka suka bata sirrin nawa birnin muka taho domin mu sadar da junanmu".
Malukussaifi ya ce “To madallah to kai Sarkin ka fara zuwa nan kai kadai” Sarki Abisul'abisi ya taho ya zo ya sauka.Manniyatunnufusi da Nurulhuda suka zo suka rungume shi har zuwa wani dan lokaci shi kuma ya yi mubayi'a ga Mulukussafi ya kuma nemi ya yi masa izini da shi da jama'arsa su shigo cikin birnin. Sai Malukussaifi ya ce "To ai haduwar wadannan mazan da wadannan mata ai a yanzu zai kawo abkuwar wani abu. Saboda haka yanzu ni na zamo waliyin duk wadannan 'yan matan duk namijin da zai shigo wannan birnin sai ya biya sadakl na aura masa daya daga matan nan sannan zai shiga.
Sarki Abisul'abisi ya yarda da wannan sharadi ya ce “To ina neman auren Murjanatu a wajenka." Malukussaifi ya ce “To sadakinta dinari dubu ashirin, nan take sarki ya biya sannan ya daura musu aure. Daga nan sai duk mazan nan suka yi ta biyan sadaki ana daura musu aure da 'yan matan nan.
Bayan kimanin wata guda gari ya koma daidai kamar yadda yake ainihi, sai Malukussaifi ya yi shirin tafiya ya ce da Sarki Abisul'abisi “To ni yanzu zan dauki matata da dana mu tafi kuma ina so zan tafi tare da Nurulhuda ita ma domin na aurar da ita ga wani daga cikin sarakunan da suke karkashina."Sarki Abisul'abisi ya ce “Ai babu laifi ai ba zan haa ka tafiya da
60
matarka da danka ba haka ita ma kanwar matarka Nurulhuda kai har ma da dukkan kuyangin matarka masu rigar tashin nan duk ka hada ku tafi da su su raka ku daga baya sa dawo da rigunan su na tashi".
Gari na wayewa Malukusafi da Manniyatunnufi da dansu da Nurulhuda da 'yan rakiyar su 'yan matan nan masu rigar ta shi cikin su kuwa har da Murjanatu da Kaukabu suka yi sallama da Sarki Abisul'abisi suka kamo hanya suka fito daga bimi suka mika da tafiya har tsawon sa'a hudu. Sannan suka iso farkon wadin nan inda Hairakana yake zaunc yana jiran dawowar Malukussaifi. Da zuwansu suka sauka a nan da saukar su Malukussaifi ya ciyar da su daga kwaryar nan tasa duk suka koshi.
Bayan sun gama cin abinci ya dauko allon aljani Hairakana ya goga nan da nan Hairakana ya bayyana gabansa ya cc "Barka da zuwa uban dakina”.Malukussaifi ya dubc shi ya cc “Hairakana yanzu ina so ka gaggauta ka nemo wasu aljanun su taimaka maka ku dauke mu ku mai damu inda muka fara haduwa da kai ka dauko ni da farko”. Hairakana ya yi dariya ya ce “Ai ko kun ninka yawan haka sau hamsin zan iya daukar ku ba tare da na nemi taimakon kowa ba domin ina iya daga gari guda na kifar da shi, ni kadai kawai yanzu abin da nake so idan na mai da ku ka cika min alkawarin mu da ka yi ka banj allona na tafi”. Ya amsa masa ya ce “Ai babu abin da zai han8ni na cika maka alkawarinka in dai ka mayar da mu”.
Nan da nan Hairakana ya kawo wani bakin karfe mai fadi ya ajiye ya kafa rumfa a kan sa ya ce dukkan ninsu su shiga cikin wannan rumfar, suka shiga Hairakana ya dauke su,kafin wayewar gari Hairakana ya yanke tafiyar wadayen nan bakwai ya sauke su a gindin dutsen nan wanda Iluru da Akisa' suke zaune suke jiran dawowar Malukussaifi. Ko da ya sauke su suka fito sai Malukussaifi ya dankawa Hairakana allonsa ya sallame shi ya yi tafiyarsa.
Bayan sun huta Malukussaifi ya dauko kwaryarsa ya ciyar da su abinci. Suna cikin cin abinci sai ga Iluru da Akisa sun zo
-
gabansa suka gaishe shi, ya yi matukar farin ciki da gann su ya tambaye su labari Akisa ta ce “Ai tun lokacin da ka tafi ka barmu a nan muna zaune a nan . Da muka ga zama ya tsawaita baka dawo ba sai muka kasa hakuri muka je muka samu Sheihin nan Nurulzaitun wanda ya baka allon Hairakana da wannan kwaryar muka tambaye shi labarinka. Shi ya gaya mana kana nan lafiya kuma ya gaya mana yau din nan ma zaka dawo shi ne muka taho kuma muka same ku a nan"Malukussaifi ya kwashe labarin tafiyarsa kaf ya gayawa Akisa da lluru sannan kuma ya ce "Su raka shi inda Sheihi Nurulzaitun yake domin ya sanar da shi ya dawo kuma ya yi masa godiya bisa taimakon da ya yi masa. Haka suka dunguma har zuwa wani kogon dutse kato, sai lluru ya ce "Ai a nan shi wannan sheihin yake".
Malukussaifi da shauran 'yammatan nan duk suka dunguma zuwa cikin wannan kogon, da shigarsu sai suka ga duk an shinfide cikin kogon da wadansu irin kilisai masu taushi ga kuma bangon kogon duk an kawata shi da adon jan dinari da lu'i-lu'i da jauhari da nau'o'i irin na kayan dukiya iri daban-daban daga tsakiya kuma sai suka ga Sheihi Nurulzaitun a Zaune a kan wata kujera ta jan dinari..Malukussaifi ya durkusa gaban Sheihi Nurulzaitun ya gaida shi ya yi masa godiya ya kuma kwashe labarin tafiyarsa kaf ya gaya masa sannan kuma ya gabatar da matarsa Manniyatlunnufusi da sauran matan gare shi.
Shehi Nurulzaitun ya dauko wasu sarkokin wuya na mata ya rarraba wa dukkanin matan nan kowacce dai-dai, su wadannan sarkoki an yi su ne da jan dinari kuma an yi musu kananan kwaduna na lu'i-lu'i da jauhari wanda ko wacce daya daga cikin sarkokin kimar darajarta daidai take da baitulmalil wata babbar kasar mai arziki. Sannan Shehin ya ce "To yanzu ka saka kadimin ka ya dauke su ya tafi da su izuwa Rasar Abokinka Sarki Shahazzaman Sarkin Rasar Dawariza wanda ya taimaka maka wajen yakin matan nan, amma kai tare da ni da kai zamu tafi". Da Malukussaifi ya ji haka sai ya rika
rayawa a zuciyarsa yana tuna nisan tafiyar amma sai ya hakura
ya kan ne ya amince da wannan maganar.
A wannan lokaci lluru ya dauki Manniyatunnufusi da danta da Nurulhuda su kuma sauran matan suka saka rigunansu na tashi suka tashi suka kama hanyar zuwa kasar Dawariza. Shi kuma Malukussaifi da shi da Sheihi Nurulzaitun suka kama hanya suka tafi. Bayan sun dau wani lokaci mai tsawo suna tafiya sai suka zo wani fili mai yanayi mai dadi sai suka sauka anan domin su huta, sai Sheihi Nurulzaitun ya bugi kasa da sadansa sai wani dan dabino ya tsiro ya umarci Malukussaifi da ya ci 'ya'yan wannan dabinon.
Malukussaifi ya,ci 'ya'yan dabinon nan har ya koshi,sannan Sheihin ya umarce shi da ya debi kwallayen dabinon nan ya warwatsa shi ko'ina da ko'ina. Ya rika dibar kwallayen dabinon yana warwatsawa kamar yadda Sheihin ya umarce shi.Bayan ya gama sai Sheihin ya ce da shi kaga wannan wurin, da wazirin babanka Waziri Yasariba ya taba gina wani birni a nan. Kuma har yanzu ana kiran wannan wuri da sunansa,kuma shi wannan wurin nan gaba zai zama birnin, jama'a za su sake zama a cikinsa, kuma-wadannan kwallayen dabinon da ka watsa ko wane daya zai haifar da bishiyar dabino dari kuma su mutanen da za su zauna a wannan birni nan gaba shi wannan dabibo zai zamo daya daga cikin arzikinsu kuma har wannan lokaci za'a rika kiran garin da sunan shi wannan Wazirin baban naka, wato birnin Yasariba inda daga baya kuma za'a canza wa birnin suna a rika kirasan da birnin Madina wanda kuma a wannan birnin Annabin karshen zamani Annabi Muhammadu (S.A.W.)zai baiyana”.
Daga nan suka wuce suka yi gaba suka yi ta tafiya har zuwa azahar sai suka zo gindin wani katon dutse sai suka ga wata Taeduna ta mayaka bila'adadun sun yi wa katangar wani birni kawanya. Ganin haka sai Malukussaifi ya tambayi Sheihi Nurulzaitun ya ce “Wadannan fa?”Sheihi ya amsa masa ya ce "ai wannan birni da ka ke gani ai shi ne birnin Dawariza din
birnin Sarki Shahazzaman wanda ya taimaka maka wurin
yakin mata:
Wannan runduna kuwa ta wasu manyan sarakuna ce su biyar wadanda suke da makwabtaka da ita wannan kasa sun sami labarin Sarki Shahazzaman ya musulunta ya bar bautar wuta shi ne suka samo izini daga wani boka suka yi hawa domin su yake shi. Saboda haka kai yanzu ya zama wajibi ka taimake shi wurin wannan yakin sai an jima”. Shehin ya 6ace a nan wurin ya tafi.
Malukussaifi yana tsaye a nan wurin sai ya jiyo ana kiransa.Sai ya waiwayo sai ya ga ai Akisa ce take tahowa tare da Iluru,suka zo gabansa, sai ya tambayesu ina matarsa da sauran mata sai suka gaya masa ai suna kan wannan dutsen, ko da ya ji haka sai ya umarci Akisa da ta koma ta tsaya wajensu, nan da nan ta koma. Sannan ya umarci Iluru da ya je cikin rundunar nan ya samo masa labari, nan da nan ya tafi.
Jim kadan Iluru ya dawo da labari ya ce "Ai wadansu sarakuna ne su biyar suka zo za su yaki wannan sarkin da ya taimaka maka a baya. Dalilin su kuwa shi ne a da dukkaninsu suna karkashin shi wannan Sarki Shahazzaman ne kuma suna bin addinin wuta wanda suka karbo daga wurin wani babban boka mai yawan sihiri da shu'umanci ana kiransa da suna Boka Sha'asha'ana, shi wannan boka duk sarakunan wannan nahiyar tsoronsa suke yi domin yawan shu'umancinsa. To a lokacin da labari ya iske sarakunan nan na cewa Sarki Shahazzaman ya mulunta sai suka ji tsoron kada boka sha'asha'ana ya dauka ko suma sun musulunta sun bar addinin wuta da ya basu sai sukahadu suka je suka gaya masa ai Sarki Shahazzaman ya musulunta. Ransa ya baci da jin wannan labari domin bakin cikin kubucewa daga addininsa da Sarki Shahazzaman ya yi.
A wannan lokaci boka Sha'asha'ana ya umarci sarakunan nan da lallai su zo su yaki Sarki Shahazzaman,shi ne yanzu suka zo su dubu tamanin domin su yake shi. To ka ji wannan shi ne cikakken bayani”. Rufe bakinsa ke da wuya sai
Malukussaifi ya ce “To yanzu abin da nake so da kai Iluru yanzu ka je kazo min da ingarman doki da mashi da garkuwa da sulke na bakin karfe". Iluru ya bazama jim kadan ya dawo da duk wadannan kaya da ya bukata.
Malukussaifi ya shiga sulken nan ya yi tigijim ya rataya garkuwar naħ ya hau dokin ya rike mashi a hannunsa na hagu,sannan ya rike takobinsa a hannunsa na dama. Iluru ya riki mashinfidin dokin ta barin hagu ya gangaro daga kan dutsen nan ya zaburi dokin ya tasam ma sansanin nan haikan. Koda ya kusa da su sai ya tirje ya tsaya

Please Login or Register in order to submit comment