Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin ka aureta ake girmama lamarinta, ba zan iya ba ko da wasa Y. Hisham ko ta ina Fareedah ta min fintink’au na hak’ura da aurenka ko da sonka zai zama ajalina. Ma’assalam.” Cikin wata irin raunin zuciya ta shige gida da gudu…….



Nazeefah Nashe.


Zumuncin Zamani

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387

(Continuation. A yi hak’uri da aka ji ni shiru kwana biyu dalili mai k’arfi ne ya rik’eni. Nagode da jumurin saurare)


Cikin tsananin zafin zuciya Hisham ya dafe kai cikin ransa ya ce “Shikkenan tawa ta sameni wata Sabuwa Sauda bata son kishiya.” Ya lumshe idanunsa shi kansa bata san a dole zai had’a mata biyun don hakan baya cikin tsarinsa.


Saudat kuwa cikin gigitar Lamarin ta fad’a cikin gida ta ci sa’a Abbanta yana nan bai shiga d’akinsa ba. Da sauri ta zube a gabansa ta fashe da wani irin kuka na tayar da hankalin duk mai saurara ta. Da sauri Abbanta ya mik’e yana sake dallareta da torch light yake fad’in “Lafiya Sauda? Me ya faru?” Kukan sosai take kafin ta saki ajiyar zuciya idanunta jajir ta dubi Abban cikin sark’ewar harshe ta ce “Abba na fasa aurensa, na shiga uku Abba kuna sane Abba za ku kaini gidan da za’a kashe ni da bak’in ciki wayyo Allah…..”

Takaicinta ya sa Abban ya kasa ce mata komai illa zuba mata ido da ya yi yana tunanin irin amsar da ya dace ya bata. Don bai zaci zata yi irin wannan wautar da shirme har haka ba. Sai da ta d’an nisa daga kukan sannan ya ja ajiyar zuciya bayan ya kawar da kwanon abincin da yake gabansa ya ce “Kin gama kururuwar? Ashe zuciyarki bata sakankance da cewa duk inda kike ubangiji shine wanda ya kamata ki nufa da lamari mai girma irin wannan ba? Imanin bai kai ki gane cewa ba bu wanda ya isa ya cutar da ke ba matuk’ar kin yi rik’o da addu’a Sallah da karatun Alkur’ani da salatin Manzon Allah, kin ba ni mamaki kishiya ki ke tsoro Saudat? Kishiyar da take mace kamar ki?”

Da sauri Saudat ta girgiza kai “Ba kishiya nake tsoro ba Abba, sharrinta,kaidinta da makircinta nake tsoro, da kuma matsalar da zan fuskanta da danginsa tunda zuciyarsu ta Riga ta fifita kud’i fiye da zumunci.” Abban ya dad’e yana nazarin kalamanta tabbas ya san tana kan turba sai dai baya son ya nuna mata tasa gazawar hakan yasa cikin kwantar da murya ya ce “Kada ki manta Ubangiji da kansa yake maganin Makircin mutane tunda da kansa ya ce “Wa makaru wa makarallah Wallahu Khairul makireen, ki rik’e Allah a ranki Sauda ba abinda zai sameki In sha Allah ki tattara kaidin nata da makircin da na su gaba d’aya ki mik’awa Allah ki sha mamakin yarda ubangiji zai yi yak’i da su akan zaluntarki da suke son yi, ai shi ya fad’a idan bawa na ya rik’e ni ya kusanceni ya kuma yarda shine mai yi to shi Ubangijin zai zame masa jin sa da yake ji da shi ganinsa da yake gani da shi takunsa da hannayensa gaba d’aya sai Allah ya zama shine yake yak’i da dukkan wanda zai zalincesa ki yi rik’o da Sallah da Alkur’ani ko bayan raina zaki tuna da ni nace ba abinda zai sameki matuk’ar kin zamo mai jajirtacciyar zuciya wajen ibada. Amma ina tabbatar miki babu maganar fasa aurenku, a zuciyata ina so ki zame musu aya ki zame musu abin misali ko sa hankalta su kuma fad’aku.”

Tsaf Cikin d’akikai kad’an Sauda ta shanye kukanta, zuciyarta ta sanyaya matuk’a da gaske da kalaman mahaifinta, tabbas samun mahaifi na gari ya fi samun mahaifi mai tarin dukiya a yau kam tana alfahari da zamowarta tsatson Mustafa. Ta share hawayenta sannan ta yi k’asa da kanta tana antayawa mahaifinta godiya da ya kub’utar da ita daga sharrin shaid’an mai tunzira zuciyarta. A zuciyarta ta hak’kak’e cewa lokacin barci tuni ya k’ure mata ya zama dole ta jajirce da addu’oi da k’iyamallaili da azumi gami da nafilolin dare da rana dafatan Allah ya mata katangar k’arfe daga dukkan abin k’i da idanu ababen zargi.


Shi kuwa Hisham har tsakar dare ya kasa samun nutsuwa da sauk’in zuciya wani irin So ne yake dagargazar ransa na halitta d’aya Sauda. Ga shi duka k’ok’arin kiran wayarta da ya yi ya gaza samunta, duk bayan mintuna sai ya gwada kiranta sai dai amsa d’aya wayar take ba shi a kashe take. Yana jin wani iri a ransa duk a dalilin yanayin da ya barta ya san tana ciki matuk’ar damuwa musamman kasancewarta mace mai zafin kishi. Fatansa d’aya Allah ya sassauta zuciyarta ya saka Mata ha’kuri da juriya. Shi kansa ya san aurenta da zai yi abu ne da zai janyo mata matsaloli a rayuwa Ba daga danginsa ba masu k’wad’ayin Naira ba daga dangin kishiyarba masu tak’ama da arziki. Abu d’aya ya sani ba zai bari a wulak’anta ba zai jajirce matuk’a da gaske wajen ganin ya k’watar mata y’an cinta, zai kuma zama mai share mata hawaye In sha Allah a duk yayin da wani ya cusguna mata zuciya.



***************


Hajiya laraba sun dawo daga dubai d’auke da kaya masu d’inbun yawan gaske tamkar wanda za’a kaiwa y’ar shugaban k’asa. Shi kansa Alhaji Hamzan sai da ya yi mamakin yawan kayan, sai dai duka zuk’atansu ba su kawo tunanin a raba a bawa Sauda ba. Ita da Inna Falmata suka dinga waya had’e da sanar da shi ya zo ya ga kaya don gobe suke saka ran kai kayan. Cikin siyayyar har da mota wanda Hajiya Laraban da Inna Falmata ne suka had’a kud’in motar a matsayin ta su gudumawar mota y’ar gaske da ta amsa sunanta na mota k’irar rav 4.


Bayan gajiya da nacin kiran wayarsu ya shiga cikin gidan fuskarsa babu wata walwala. Idanunsa ya zube akan tsibirin kayan da ke gaban mahaifiyarsa tamkar wanda za’a bud’e shago. Bai dai yi magana ba ya d’an tab’e bakinsa had’e da k’arasawa ya zauna yana gaishesu. Daga haka ya ja bakinsa ya tsuke Inna Falmata ta dubeshi da murmushi “Hisham ka ga kaya Ma sha Allah ba kace komai ba.” Hisham ya mayar da idanunsa kan kayan a shagub’e ya ce “Ai ba sai na ce komai ba, in dai sun muku shikkenan, amma ina ganin kamar kayan sun yi yawa mai zai hana a raba musu da Sauda?” A zabure gaba d’aya suka d’ago suna kallonsa kamar su rufeshi da duka Inna Falmata da ta tunzira da takaicinsa ta jefeshi da filo “Ka idonka wannan kayan ya yi kama da kayan da za’a kai gidan Mustafa? Wai hauka ne a kanka Hisham, ka san adadin dukiyar da aka kashe kake cewa a d’auka a kai inda ba’a san darajarsu ba balle a mutunta su? Kayan da ko gidan shugaban k’asa aka kai sai sun jinjinawa k’ok’arinmu kake cewa a kai wannan akurkin gidan?” Mommynsa kuwa tsaki ta ja kafin ta ce “Ke kika kula shi Hajiya, yo wannan gidan ya fi a kai musu akwati uku da d’an kit, dubu d’ari uku ma tsaf zata had’a lefen gidan nan kuma a kai su yi murna had’e da zakwad’i su nunawa jama’a.” Dariya sosai Inna Falmata ta yi kafin ta ce “Wallahi kam, to dangin uwa duk talakawa ai Mustafa ya cucemu da ya auro y’ar matsiyata ko da yake kansa ya cuta ga shi nan tsiyar tana ta binsa a guje.”

Tsananin mamakin lamarin su da son zuciyarsu ya saka Hisham sakar baki yana kallonsu a zuciyarsa yake tunanin tabbas idan ka na duniya zaka sha kallo’ har ya kasa jurewa ya magantu ta hanyar cewa “Amma kuwa idan na bari aka aikata haka tabbas na tabbata mara adalci, ita wannan an mata lefen miliyoyi ita kuma sai a mata na dubu d’ari uku haba Mommy kada son zuciya ya kai ku halaka mana, su ma fa talaucin nan ba su suka d’orawa kansu ba kuma babu wanda yafi k’arfin Allah ya jarrabeshi kamar yarda ya jarrabi Abba Mustafa.” Ba wani tasiri da kalamansa suka musu cikin confidence Inna Falmata ta ce “Ai kuwa hakan ba zai zama rashin adalci ba, kuma ko tsarin musulunci ma aka bi shine daidai tunda cimarsu ma ba d’aya zaka dinga ba su ba, kowa zaka ciyar da ita ne da irin cimar da take ci a gidansu ka kuma tufar da ita da kalar ta ta tufar….” A zafafe kamar ya kai mata duka ya ce “Ba dai tsarin musulunci ba sai dai idan aka bi son zuciya” da sauri Mommynsa ta ce “Kai Hisham saurara rashin kunya zaka mata? Saboda an tab’a zuciyarka d’iyar gwal.” Ya sake b’ata rai ya ce “Ni ba rashin kunya zan mata ba gaskiya ce zan fad’a mata.” Daga haka ya mik’e zai fice daga d’akin Mommynsa cikin b’acin rai ta sake kiransa ya juyo kad’an sai dai bai dawo ba saboda suyar da zuciyarsa ta ke masa Ko Falamata baya son gani, tunani yake yau da ya na da damar da zai sake Iyaye tabbas da ya sake na sa iyayen da ba komai a ransu sai son zuciya. Ita kam sam bata lura da yanayin da yake ciki ba ta ce “Sai ka kawo dubu d’ari ukun da za’a had’awa y’ar gidan Malam Musty lefe.” Muryarsa a shak’e ya ce “Zan kawo” akwai kud’in a jikinsa amma ba zai ba su ba, zai je ya had’a da kansa akwai matar abokinsa da take siyar da komai na mata tafkeken shago ne ma da ita a can zai je ta had’a masa kuma ko k’yalli daga cikin kayan ba za su gani ba, idan sun san wata ai ba su san wata ba, ko kud’insa kaf za su k’are itama sai ya mata irin lefen da suka yi wa y’ar mai kud’in. Inna Falmata ta tab’e baki kafin ta ce “Laraba kin yi sake an gama miki da d’a tsaf kamar yarda Matar Mustafa suka tsubbaceshi a allunan almajiran makarantar Ubanta,sai kin tashin kin yi da gasken gaske Hisham ya yi nisa baya jin kira.” Hajiya laraba ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce “Ai kuwa sun yi a banza idan a tsaye suka kwana ni a tafe na kwana. Mu zuba ni da su a yi auren dai mu gani sai sun gwammaci kud’i da karatu wallahi.”




Daga Taskar Jikar Nashe.❤️❤️❤️

Zumuncin Zamani.


08033748387.

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

Daga k’ungiyar Elegant Online ✍🏽


Masu nemansa daga farko su Duba a wattpad.

@Nazeefah381 nagode.


_____________

Kunya ce sosai ta kamata jin shine da kansa yake gaisheta. Cikin wani salo na jan hankali ta yi k’asa da murya sosai kafin ta ce “Y. Hisham Ina yini?” Murmushi ya saki hankalinsa a yanzu ya d’an kwanta ganin akwai alamun sassauci a tattare da ita ya gyara zamansa sosai, yana dubanta ya ce “Lafiya lau, ya aka ji da fushi da mu? Ban yi tunanin ko mata hud’u na ce zan aura rana d’aya ba za ki guje ni saboda haka, tunda kin san ta ki k’aunar tafi ta su a zuciyata you are so special to me.” Ya fad’a yana narkar da idanunsa cikin nata, lamarin da ta ji ya fara d’imautar da tunaninta da ma nutsuwarta gaba d’aya. Amma sai ta bagarar tana d’an b’ata rai ta ce “Ka yi hak’uri na kasa danne kishina ne, ina da zafin kishi sosai da sosai, ga shi zuciyata tana bani ba zaman y’anci zan yi a gidanka ba ganin duk dangi basa bayan aurena da kai. Suna kuma ganin mu ba a bakin komai ba duk a dalilin talauci kamar mu muka d’orawa kan mu.” Tsit Hisham ya yi ya kasa ce mata komai don ya san duka zancenta ba bu tasgaro gaskiya ce tsagwaronta, bisa dole ya ce “Ya kamata wannan issue d’in ya zama labari a wajenmu kin san dai ni nake son ki ba danginmu ba, don haka ki dinga tunanin a wajena kad’ai idan kika samu farin ciki kamar kin samu duka farin cikin duniya ne tunda dai ni ne muke tare kullum ki ture kowa a ranki ki saka Hisham d’inki ni kad’ai na isa na shayar da ke tsantsar farin ciki a doron duniyar nan, kin ji ni? Bana son a sake tada wannan maganar please.”

D’aga masa kai ta yi kawai zuciyarta tabbas ta sassauta daga b’acin ran da take ciki. Hisham ya saki murmushi don ya hango yanda idanunsa suka mata dabaibayi suka hana ta katab’us shi kad’ai ya san kalar kallon da yake mata yau kallo ne mai nuna zallar muradin zuciyarsa. “Menene tsaratsaren bikin namu?” Ta jiyo muryarsa daga sama yana tambayarta don ita tuni ta lula wata duniya can, tsananin soyayar Hisham d’in ce take neman kawar mata da nutsuwa ban da tana daurewa. Ta d’an langwab’ar da kanta itama tana jifansa da madadin wancan kallon da ya kusa sanya shi ya janyota jikinsa da sauri ya ja A’uziyya ya runtse idanunsa musamman jin muryarta cikin wani salo tana amsa masa tambayarsa “Ba ni da wani tsari Y.Hisham walima kawai zan yi da zan kira Malamai su fad’akar da Mata akan zamantakewar aure sai saukar Alkur’ani da zan saka a yi da niyyar Allah ya albarkaci aurenmu da zuria d’ayyiba.” Ya dad’e yana jinjina kai don ba d’an kad’an ba ya burgeshi don samun Mace mai irin halinta a zamanin nan sai an yi mugun dace. Ta san yana da shi amma bata d’orawa kanta wasu bidi’oin banza ba albarkar auren kawai take buk’ata su kuwa bidi’oi babu abinda suke kwashewa sai albarkar aure ina ma mata duka za su koma Sauda da matsalolin aure sun ragu. Ya ce “Shikkenan Allah ya sanya mana albarka zan nema miki guri mai kyau ki yi walimar hakan ya yi?” Ta d’aga kai tana sakar masa murmushi Daga haka ya mata sallama ta fice daga motar shi kuma ya rakata har k’ofar gida inda anan ma sai da ya sake janta da hira.



————————-
Da safiyar kashegarin ranar suka wayi gari da bak’in danginsu, su Inna falmata ne da Yayyan Hajiya Laraba wai suka zo ganin lefe. Umma dai cikin farin ciki ta tarbesu duk da ta san ba alheri ne ya kawo su ba sai son ganin k’waf.

A yatsine suke kallon gidan kamar sun gama abin k’yama, Umma sam bata damu ba don gidanta tsaf yake ko tsinke babu a tsakargidan. Baya ga haka sai zabga k’amshin turaren tsinke yake kamar yarda ta saba sakawa a koda yaushe. Ta malala musu tabarma tana kallon yarda suke zama a d’ofane.

Inna Falmatan cikin isa da tak’ama ta kalli Umman Saudan ta ce “Kayan lefen Y’arki muka zo gani, duk da dai ba ki gayyacemu ba muna matsayin dangin ubanta.” Umma ta d’an yi yak’en murmushi duk da ta san ba har zuciya Falmatan ta yi maganar ba ta ce “Wallahi ko kad’an ba haka bane, da yake Hisham d’in da abokansa biyu suka kawo kayan ba ma mu san
Da zuwansu ba sai ganinsu mu ka yi da kaya, amma Allah huci zuciyarku a yi hak’uri.”

Inna Falmatan ce dai ta sake magana da cewa “Ai hakan ya yi kyau ya kyauta, ya kuma hutashshemu musamman kai lefen gida biyu ne can muka kai na kishiyarta gidan Senator Sule Jami’i yanzu ina kayan suke?”

Umma ta mik’e tana mamakin yarda ba wanda ya mata kara da kanta ta dinga janyo manyan akwatunan masu tsadar gaske tana direwa a gabansu. Baki sake cike da mamaki suke kallon kayan ko kad’an ba su san kayan za su kai haka ba. Yayar Hajiya Balaraba ce ta kasa jurewa ta ce “Kan uban can amma Balaraba ta yi sake kun shanye mata d’a tsaf irin wannan narka dukiya haka tamkar za’a kai gidan wani k’asurgumin k’usan gwamnati ko d’an kasuwa.” Inna Falmata ma jinjina kai ta ke ta ce “Ai kuma daga gani ba sai an yi tambaya ba, yarda dai aka sammace Mustafa a allon almajiran ubanta haka aka summace Hisham to Allah dai yasa ita ba jininki na tsiya ta d’auko ba ta tsiyata shi a banza da wofi.” D’if Umman tayi tabbas maganganunsu sun yi tasirin da suka haddasa mata matsanancin bugun zuciya da b’acin rai. Ta saki ajiyar zuciya ganin yarda suka mik’e suna tsallake kayan ba tare da sun gani ba idanunsu bayyane da haddasa k’iri-k’iri. Tana jiyosu suna cigaba da cilla mata bak’aken maganganu ita da iyayenta, ta runtse ido murmushi gami da hawayen takaici suna zubo mata duka a lokaci guda a fili ta furta tabbas talauci bai yi ba, don bakomai ya janyo mata wannan wulak’ancin ba sai talauci, yau da su masu kud’i da murna da zakwad’i za ‘a so auren y’ar su amma ji yarda ake gudunta yanzu duk a dalilin rashin kud’i. A fili ta ce “Allah ka fitar da mu daga wannan k’angin mu ma.” Ta fad’a tana d’aga hannayenta sama.




_______________

Shirye-shirye ya kankama daga can d’aya b’angaren na masu hannu da shuni, shiri ake gagarimi na bikin ba ga dangin angon ba ba ga na amaryar ba kowa so yake ya nuna k’aryar arzikin da yake da shi. Su Saudat dai sai dai godiyar Ubangiji suna ta kayan d’aki ma wa yake ta wani hidimar biki.




Hisham ya shiga gidan nasa mai d’auke da sassa biyu d’aya Saudat d’aya Fareedah. Murmushi ya saki ganin yarda gidan ya fara d’aukar haske da yake gidan Fareedan ya fara shiga kaya ne na goge raini ake zuba mata zubi da k’irar turkey
Komai da yake gidan kayan waje ne. Sanda ya shiga sashen Saudat sai da ya ji tamkar ya yi hawaye don babu komai sai malalan tiles sai a yanzu zuciyarsa ta tuna masa da Abba Mustafa ba shi da komai kuma bai bawa kowa ajiya ba, da kuwa sam ya manta kamar wanda aka kawar masa da tunaninsa. Cikin azama da sauri ya juya ya shiga motarsa ya figeta a guje, har mai gadin yana mamakin dalilin saurin nasa.


Isarsa gidan ke da wuya ya shiga da sallama, ba kowa a gidan daga Umman Sauda sai Abban Sauda ita Sauda a lokacin ta tafi rabon I.vn Walima.

Jikin Hisham a sanyaye ya samu gefe ya zauna cikin ladabi ya fara gaishesu. Da walwala sosai a fuskokinsu suke amsawa kai ba zaka ce akwai wata matsala tattare da su ba. Abban Saudat ya ce “Malam Hisham ya shirye-shirye? Dafatan dai ba matsala?” Cikin jin kunya sosai ya yi k’asa da kansa kafin ya ce “Babu komai Abba sai godiyar Ubangiji.” “Masha Allah!” Abban yace yana cigaba da danna counter d’in da take hannunsa. Tsawon mintuna Hisham d’in yana son furta abinda yake ransa amma yana shakkar Abban gani yake kamar ba zai amince da buk’atar da yazo masa da ita ba. Da kyar ya yi k’undunbala ya ce “Abba dama da wata magana na zo.” Abban ya mik’e yana gyara zamansa sosai, Umma ta yi nufin mik’ewa Abban ya dakatar da ita “Sha zamanki, na san babu wani abu da Hisham ba zai so ki ji shi ba ni ma kuma kin san ba ni da sirri in dai a wajenki ne, Ina jinka Hisham fad’i abinda ke tafe da kai Allah yasa mu ji alheri.”

Hisham ya shiga wasa da yatsunsa kafin ya ce “Abba dama alfarmarku zan rok’a don Allah bana son a kai Sauda da ko cokali gidana zan mata komai a aljihu na.”

Farin ciki sosai Abba Mustafan Yayi tabbas Hisham ya cika d’a na gari abin alfaharin ko wane iyaye sai dai ba anan gizo ke sak’ar ba yana gujewa Sauda gori irin na dangin miji musamman aka ce muku dangin miji masu k’arancin ilimi da tunani “Madalla da d’a na gari, na ji dad’i sosai Hisham sai dai ka yi hak’uri buk’atarka ba zata amsu ba, bisa dalilai da hujjoji masu k’arfi babban dalilina GORI bana son a dinga mata gori musamman gidan kishiya, bayan wannan kada ka manta mahaifinka ya kafa mama sharad’in duk ranar da ka sake taimakon mu bai yafe maka ba, don haka ka bar zancen a iya nan, zan kai Sauda da duk abinda Allah ya hore min, kuma a tarbiyyar da na bata ina tabbatar maka da ko da karauni na kaita kishiyarta tana da gadon diamond ba zai damu Sauda ba, ta san matsayinta ta kuma san waye ubanta ba ni da shi ban bawa kowa ajiya ba, na kuma d’orana y’ay’ana a turbar samu da rashi duka na Allah ne, don haka kada ka damu. Allah ya yi maka albarka akan kyakykyawar niyyarka na kuma ji dad’i sosai.” Hisham ransa bai so ba amma haka ya mik’e zuciyar sa cike da tunanin ta inda zai taimakawa Abban ba tare da ya san shi ne ya taimaka masa ba.

Ko da ya koma office tunanin da ya dinga yi kenan, ga shi da kud’i tamkar su kasheshi amma ba ta halin da zai iya taimakawa matarsa duk a sunan wai kada
A mata gori, Allah ya kaisu lokacin da zata tare a gidansa ya siya mata duk abinda yake so idan ya so yaga uban da zai ce masa don me? Da Abba Mustafa ya barshi ko kud’insa za su k’are duka sai ya mata irin kayan da aka k’awacewa Fareeda gida da su. Company uku gareshi banda na Atamfofi da shadda akwai companyn gine-gine da na kwangilolin titi ga kuma kamfanin yin taliya da fulawa, amma mahaifinsa ya masa karantsaye ya hana shi taimakawa bayin Allahn nan don son zuciya. Bai san sanda ya runtse idanunsa ba kawai sai ji ya yi suna zubar da hawaye. Murmushi ya kubce masa tunanin hanya d’aya jal da ta rage masa yana tunanin wannan hanyar kam babu mai ce masa don me? Don musulunci ne ya bashi dama.



___________


Ana yin sallahr Isha ya isa gidansu Saudan amma ba shiga ya yi ba, waya ya yi mata ta fito ta sameshi a waje. A gajiye take sosai don ba k’aramar zirga-zirga suka sha ita da aminiyarta ba Maimunatu.

Tana jan k’afa ta isa motarsa, shi kuwa idanu ya zuba mata yana hango yarda gaba d’aya jikinta ya nuna mabayyaniyar gajiya. Ya sake ware idanunsa yau kam yana morewa kallonsa ganin irin kyawu da k’irar jiki da Allah ya mata. Ya ja kalmar Hamdala ga Allah a zuciyarsa.

Da sallame ta bud’e motarsa ta shiga tana sakin murmushi ta gaida shi. Hisham shima murmushin yake ya ce “Ran amaryata ya dad’e. Duk na lura yau kin wahalar min da kanki.” Tsam ta d’inke fuskarta murya a shak’e ta ce “Uwargida dai.” Hisham ya tuntsire da dariya ya ce “Tuba nake da girman kujerarki Uwargida, amma kuwa a yi haka Fareeda ta ta girmeki girma ba kad’an ba.” Ta sake cono bakinta ta ce “Wallahi ko haihuwa ta tayi ni nafi son na zama uwargida akan ace ni ce amarya.” Da sauri ya kawar da zancen don baya son ya tunzirata ta sake masa fushin da ta masa wancan karan. “Amarya guda ba gyaran jiki bakomai haka za’a kai ki gidan mijin? Ke haka ake uwargidan ba zaki tambayi kud’i gyaran jiki ba, tun yaushe Fareeda naga ta fara ko so kike ta fiki haskawa?” D’if ta yi da fuskarta duk wani annurin fuskarta ya kauce ko kafin Hisham ya ce komai Hawaye sun fara zuba a idanunta…



Daga taskar jikar Nashe❤️

Zumuncin Zamani..

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387.

Wattpad
@Nazeefah381


Daga k’ungiyar Elegant Online Writers.



_______________


Ranar da za’a kai kayan lefen, gidansu Hisham a cike yake dank’am da jama’a, dangi cike kowa ya hallara tamkar gidan biki kai kace ranar ake auren, ba mamaki don ganin gidan Senator za’a kai kayan shi yasa kowa ya zo don an san za’a samu tarba mai kyau da kuma tukwuici, don haka kowa baya son a ce an barshi a baya.

Hajiya Laraba ta fito falon cikin wata shiga ta alfarma sai taku take d’aid’aya cike da izza da ginshira take musu kallon sama da k’asa. Cikin murya mai nuna zallar tak’ama ta ce “Lallai ba shakka gida ya d’au jama’a, to amma fa da sake don dole a tantance masu tafiya gidan senator da kuma masu tafiya gidan Mustafa.”

Gaba d’aya gurin ya hau tsine da hayaniya kowa a fili ya nuna zilamarsa ta son zuwa gidan Senator. Muryoyi ne kawai ke tashi da gunaguni “Aa Wallahi gidan Senator za mu, ni don haka ma

Please Login or Register in order to submit comment