Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan duniyar haka ta rikid’e ta koma, ba a komai don Allah, mai shi abokin mai shi ne, talaka abokin talaka d’an uwansa. Kuma daman bahaushhe yace k’warya ta bi k’warya, daidai ruwa daidai gari, ba a ganin ka da gashi wannan zamanin sai idan kana da shi. Don haka nake son ki sanyawa zuciyar ki salama. Kina jina?
D’agawa Umma Kai nayi da k’yar don kam ba ni da bakin magana.
Umma ta juya tabar d’akin, ni kuwa sake runtse idona na yi wasu zafafan k’walla suna zubo min, sosai nake jin zafi da radadin abin a cikin raina.

Tun safe na shirya don son zuwa na karb’i results d’ina a makaranta, burina tun a can baya ya ta’allak’a a kan na samu karatu mai zurfi, na tallafawa mahaifina,Akwai hakan a cikin raina da wannan burin kuma na taso.

Cikin atamfa ta k’aramar super mai k’aramin kud’i sosai, koriya na shirya na saka hijabi da zai dace da atamfar bayan na nad’e gashin kaina da ya zama kamar na sanya ribbon din a cuci maxa, powder kawai na sanya a fuskata sai man leb’e na zizara gazal a idona, don ni Sam ba ma’abociyar son kwalliya bace.
Ina Shirin fita daga gidan naji sallamarsa. Tsaki na zabga masa, don ni sam ban ga dalilin yi mana zarya a gida ba. Koda yaushe a yanzu kam na tabbatar da nagartar halayansa. Sam shi baya daga cikinsu.
Anutse na kalli umma na furta “Umma sai na dawo a yimin addu’a”
Umma tasaki murmushi ta dafa kaina ta fara yi min addu’ar da ta saba in dai zan fita ta neman tsari daga sharrikan zamani. Ta na gamawa ta saki kan ta ce “Allah yaba da saa.”
Da k’yar na kalli Yaya Hisham fuskata a d’an had’e na ce “Ina kwana?”
Shima a nutse ya ce "Lafiya” batare da ya kalle ni ba
Na fita ina tab’e baki a zuciyata na ce, kai ka jiyo..

A makaranta tun daga bakin gate duk malamin da na had’u da shi cikin farin ciki yake cewa "Saudat congrats" Anutse nake amsawa cikin murmushi duk da ban san dalilin wannan congrats da ake yi min ba.
Da sallama na shiga office din examiner. Yana gani na shi ma ya saki murmushi. Babbar “k’waruwa barka da zuwa.”
Ni dai na saki murmushi na gaishe shi, ya nuna min wajen zama yace, “Zauna mana Saudat daman ina da niyyar idan baki zo ba ni na je har gidan na sameki, saboda abin alherin daya sameki. Saudat kin lashe sakamakon jarrabawar ki duk with an excellent results, wannan dalilin ya saka gwamnati ta d’auki nauyin karatun ki a duk inda kike son karatu a fad’in duniyar nan,tare da scholarship mai nauyin gaske.”
Cikin tsananin farin ciki na d’aga hannaye sama ina yi wa ubangiji Godiya.idaniyata na kwararar da siraran hawaye. Malam Umar murmushi ya saki ya ce “Dole ki yi kuka saudat don kam abin musamman ne na farin ciki ake wa hawaye”
Na d’ago kaina cikin lumsassun idona na ce "Malam nagode, ubangiji ya fi ni yabawa, bari na yi sauri na isa gida na sanar da su Umma wannan abin alherin da ya samemu.”
Malam ya gyad’a Kai ya ce "Maza ki hanzarta kam, Amman kafin ki tafi ki biya office din principal ta ce idan kin zo na tura mata ke.”
Na gyad’a kaina had’e da karb’ar kwalin results d’ina.Na rungume shi a k’irjina cikin tsananin farin ciki.
Da sallama na isa office d’in principal, tana gani na ta mik’e tana murmushi ta ce "Welcomed gifted”
Da sauri na durk’usa na gaishe ta. Ta xagayo ta kama hannuna tana fad’in," Ina alfahari dake sauda na yi burin ina ma a ce daga jikina ki ka fito" haka tayi ta nuna murnar ta a zahiri, da zan tafi ta sanar da ni akwai taran da makaranta ta shirya min sati mai zuwa tare da fatan zan zo.
Na d’aga mata kai had’e da fad’in “Insha Allah mah”

Da gudu na shiga gidanmu na fada kan cinyar umma ina cewa “Umma na,ki taya ni murna na cinye jarrabawar duka, har gwamnati ta dauki nauyin karatuna duk k’asar da nake so a fad’in duniyar nan.
Da sauri Umma ta mik’e tana cewa “ Alhamdulillah, Allah mun gode maka sauda da gaske kike ko wasa?”
Na ce “Wallahi umma da gaske nake, na nuna mata takardar ta sake cewa "Alhamdulillah Alhamdulillah,mun godewa Allah.
Ranar har dare zancen makaranta kawai a gidan yayyena kuwa, kowa da k’asar da yake cewa in je. Abba dai yana jin su ya yi musu Shiru bai ce komai ba sai da aka gama mahawarar ya dubeni ya ce “Saudat ki na son ki fita waje karatu?”
Da sauri na d’aga kai da nufin jaddada masa ina son zuwa.

Abba yayi murmushi ya ce “Saudat a wannan karon gaskiya sai dai ki yimin hak’uri Zan tauye ki kad’an Sauda ba Zan iya barin ‘yah mace ta k’etare zuwa wata k’asar karatu ba, a cikin garin nan ma a dole zan bari,sabida haka ki za b’i d’aya daga cikin makarantun da suke nan garin na kano, ba ma wani garin ba. Dafatan ban tauyeki ba, ba zan take umarnin musulunci ba saboda burace-buracen duniya.”

Da sauri na girgiza kai don sam ni ban ga abin tsanantawa ba na ce "Abba ba komai, duk d’aya ne da nan da can d’in, fatanmu ubangiji ya bamu albarka a cikin ilimin.
Abba ya girgiza kai yana cewa Masha Allah, madallah da haihuwa y’a ta gari.”
Na ce,"Nagode Abba”Ina kallon yayyena sam ba su ji dad’in hukuncin da ya yanke ba sai dai ba yarda za su yi.

Daidai lokacin sallamar Yaya Hisham ta ratsa kunnenmu, cikin farin ciki suka tareshi ni d’in ma ba yabo ba fallasa na gaida shi. Abba ne ya rattabo masa labarin jarrabawa ta.
Da sauri ya juyo ya kalleni Yana murmushi yake fad’in”Masha Allah, ashe kina da k’ok’ari?”
Murmushi kawai na yi na mik’e na shiga d’aki haka kawai sai na ji bana son zama kusa da shi sau tari sai na ji zuciyata tana lugude a duk sanda zan ji muryarsa ko na gan shi ko na shak’i k’amshin turarensa. Sai naji yana cewa “Lallai zamu fara shirin ai na zata tsiwar ce kawai ba k’wak’walwa.
Abba ya ce Saudat kenan kowa yana fad’in wannan tsiwar ta ta,sam ba tada sauk’in hali da sau’kin zuciya.
Hisham ya ce “Lallai kam, sai dai da sau’kin ta tunda dai tana da k’ok’ari."
Ni dai ina daga cikin d’aki ina jiyo hirar ta su ban san barci ya dauke ni ba. Zuciyata cike take taf da farin ciki marar misaltuwa.


Jikar Nashe ce.


❤️❤️❤️❤️❤️🙏

08033748387


Zumuncin Zamani


7.

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

Ku karanta kyauta

(Jazakillah mai Typing Fateemah Sabi’u Dankaka, mata a gidan Isa Allah ya saka da alheri ya raya mana Meenah, ya kawo k’annenta don girman zatinsa godiya dubu.)



Da d’an takunsa isarsa ya iso ya
mikamin card d’in ni kuma na mika masa kudin.

“Mayar mata da kudinta” ya fada yana kallon k’wayar idona har na fara tafiya naji yace, “Ina yarinyar da na bari anan?”
Na girgixa kai, “Wallahi bansan inda tayi ba.” Ya shafa kumatunsa Yana murmushi. yace “Ok jeki.”
Na sake tafiya sai kuma naji ya sake cewa “Sauda”
Na sake juyowa.
" Karfe nawa za ku tafi?”
Nace, wallahi ban sani ba"
Ya girgixa kai, sannna ya juya ya fice.
Koda na shiga falon na hango bakuwar Hisham kusa da Inna falmata gabana ya fadi,sai da na karasa na mika mata kati da kudin
Tsaki tayi Kafin ta ce “To mara kunya,haka kike mikawa ubanki Abu a tsaye k’ikam?”
Sosai na zuba mata ido don kam na ji zafin furucinta.
"Ko zaki dake ni ne fitsararriya.?”
Girgiza Kai nayi kawai.
“Uban waye yabaki wannan katin naga kin maido min da kud’in?”
Sai da na had’iye Wani yawu mai matuk’ar d’aci sannna nace "Ya Hisham” a zabure naga sun had’a Baki wajen cewa “Hisham fa kika ce? Meye had’inki da shi?”
Cikin matuk’ar had’e rai da gajiya da tambayoyin rainin hankalin na ce "Bakomai” Don na ga an fara yi min tambayar rainin hankali.
Tab’e baki tayi tace. “Ko da yake me ma Zai yi da ke ga d’iyar arziki wacce tayi gadon arziki gaba da baya iyaye da kakanni ubanta senator ne, kuma shi da kansa Hisham d’in ya ce yana sonta, don haka idan ma da wani abu a ranki ki batar da shi don Hisham mijin ' Y’ar manyan mutane ceeee---------“
Ban k’arasa jin sauran zancen ba na yi saurin b’acewa daga wurin,Ina ji ‘Yan matan wurin suna yi min dariya. Zuciyata kam a kufule take sosai
Wannan wacce irin rayuwa ce?don ba ka da shi k’annenka ma su rainaka?
Sai dana share kwalla, sannan na koma gurin Ummata don ba na son na b’ata mata rai sam. Koda ta ganni kallo kawai ta bi ni da shi da alama ta fahimci damuwa karara a tare da ni, ba tace komai ba kasancewar tana tare da masu aikin abincin biki ta saje a cikin su, kai ka ce ba ta da alaka ko kad’an da masu Taron bikin.
K’arfe 4 :00 na yammah aka fita harabar gidan don gudanar da yinin bikin.Umma ce ta lallab’ani ta sakani na fita, koda naje wajen rakab’ewa na yi acan Wani gefe ina kallon masu rawa da yadda ake watsar da kud’i tamkar ba a so, kai ko nace tamkar mabukata sun k’are a duniya. Mhmn rayuwa kenan!
',ya'yan inna sahura na gani sun taho gurina da yake su ma ya'yan yaku bayi ne don Inna sahura ba ta da wadatar arziki, kuma mijinta ya mutu . Dama can kuma ba mai wadatar ba ne,ita take bin babanmu a d’akinsu daga ita sai Inna maryam, ita kam mijinta yana da rufin asiri, don haka ita ake damawa da ita a danginmu don ko ba komai an san idan anyi mata tana da abun mayarwa.,babu laifi tana d’an kula da mu ita, dai sam ba kamar yadda ya dace ka yi wa jininka ba.
Da fara' arsu suka tare ni su ma sun ci kwalliyar su kamar ni irin ta yaku bayi,Zainab ce tace “laah saudat ashe kin zo?”
Ni ma din cikin murmushi na ce “Yaushe kuka zo?”
Asma’u ce ta tab’e baki tace “Yanzun nan shigowar mu, kinsan ni ba kasafai na fiye son shiga Taron Dangin nan ba”Yanzu ma don umma ta kafe tace sai mun zo ne, Ina Ummanki?
Na d’an tab’e baki tare da cewa, Tana kicin gurin aikin abincin biki.
Zainab ta yatsine baki da cewa"Wallahi Umma tana son wahalar da Kanta gurin wad’annan matsiyatan mutanen da ba su san tana Yi ba yanzu fa da muka hadu da inna falmata baki ga wani kallon banxa da ta watso mana ba,da kyar ta amsa gaisuwar amma tana ganin wata k’aramar yarinya ‘yar gidan B hamxa yarinyar ko gaisheta ba tayi ba,ta tare ta tana fad’in “Zahra,Zahra, yanzu Ku ka zo? Ina Ummanki?. Amman yarinyar nan ko kulata ba tayi ba duk da k’ok’arin cusa kanta da take.”
Dariya muka tuntsure da ita sosai ganin yadda Zainab ta dage tana kwaiwakyon maganar Inna Falmata nace. “Har yau Zainab,ki na nan ashe da d’an banzan halinki?”
Asma u ta ce "In dai Zainab ce sai abinda ya k’aru.”
Daidai lokacin na hango motar Y Hisham ta nufo inda muke da yake dama a parking space muke zaune d’an matsawa kad’an muka yi ya yi parking.
Cikin shan k’amshi ya fito daga motar. Idanunmu suka had’u sai na ga ya sakar min wani murmushi, su Zainab kuwa da sauri suka gaishe shi ya amsa musu cikin matuk’ar walwala a fuskarsa, sannan ya ce, “Ku me kuke yi a nan ba ku shiga cikin Y’an uwa ba?”
Asmau tace "Yanzu muka zo YHisham” Ya zuba narkakkun idanunsa kafin ya ce “Yanzu ku dai kuka zo ita kuwa ai tun d’azu tana nan” Murmushi kawai suka masa muna mik’ewa don barin wajen.


Ranar litinin da safe nayi shirin makaranta,saboda a ranar ne nake shirin fara d’aukar lakca a makaranta B.U.K, inda zan karanci fannin likitanci b’angaren medicine. Tun daren lahadi Y.Hisham ya zo ya kawo min dogayen riguna kala- kala goma masu kyau da mayafansu, sai plat shoes guda shida da jakunkuna guda hud’u don haka nayi kwalliyata a cikin wata doguwar riga peach color mai adon baki da golden,na yane kaina da mayafi baki. Daman gashin kaina gammo nayi da shi ya xamana tamkar na saka a cuci.
Zuciyata fresh nake jinta da tsananin farin cikin fara xuwa makaranta,
Don kam karatuna masomi ne na cikar burina na son tallafawa iyayena. A tsaitsaye na sha kokon da k’osai na yi saurin mikewa ina cewa umma, “Bara nayi sauri na tafi kada na yi late.”
Umma cikin murmushi tace “oh, sauda duk zumud’in ne haka? To Allah ya ba da saa.ga #150 ki shiga tasi yayanku ya ce ita ta fiyewa yan makaranta sauki.”
Na saka hannu biyu na karb’a had’e da cewa. To Umma sai na dawo” ta girgiza kai kafin tace
" To don Allah sauda ki kiyaye mutuncin ki jami’a ba kamar secondary bace, banda b’ata garin k’awaye da za su saka ki a hanyar b’ata, su ma muna musu addu’a ubangiji ya shirye su na ce “Ameen Umma.” na sa Kai na fita daga soron gidan namu
Adaidai lokacin na hango motar Y. Hisham ta yi parking a k’ofar gidan, tsawon mintuna na jira ya fito in gaishe shi amma bai fito ba, hakan yasa na saka Kai na fice ji na yi Yana danna min horn, na juya babu shiri.

Ya sauke gilashin motar Yana k’are min kallo cikin k’ayataccen murmushi ya ce sauda kin yi kyau sosai shigo na sauke ki makarantar.
Da sauri na girgixa Kai na ce “lah Y.Hisham ka bar shi kada na wahalar da kai. Ina fita titi zan samu mota.”kallona yayi ya hade rai yace “Sauda ba na son gardama, shigo kawai abin da na fito yi kenan.” Don tilas na bud’e motar gidan gaba na zauna wani sanyin Dad’i ya buge ni ga daddad’an k’amshinsa da ya xauna a motar.
Tunda muka fara tafiya bai ce komaii ba illa muna sauraran wani tattausan music har muka je makaranta na saka hannu zan bud’e motar ya kira ni cikin tausasa murya "SAUDAT"
Cak na tsaya.
"Dago ki kalleni”
Na dago ina duban idonsa
" Please, ki taimake ni ki tsaya ki yi karatu, ban da kula samari barkatai please.” Yadda yayi abin ya bani mamaki,tamkar mai magana da budurwar sa. “Baki ce komaii ba saudat?” D’aga masa Kai kawai nayi
"Promise?”Ya fada yana sake tsare ni da Ido.lumshe idona yi kawai saboda wani abu da naji ya tsarga min cikin raina.

Shi d’in ma jingina kansa ya yi a kujera ya lumshe Ido kafin naji muryarsa idanunsa a rufe na ji ya ce “Zuciyata da ruhina sun kasance a wani Hali tun a lokacin da na fara sanya kwayar idona a kanki All what I mean saudat l lo------------
Da sauri na d’ago ina kallonsa hakan ya saka shi gimtse maganar babu shiri.cikin dasasshiyar murya nace “Y Hisham me kake so ka ce?”
Ya daga gira Yana kallo na kafin ya ce "SO" na ce Ina sonki saudat.”
Da sauri na bud’e motar na fice saboda wani kuka da yake son ya sub’uce min. “Wane bala'i y Hisham yake son dauko wa gidanmu? Wanann wace irin magana ce? Na ja innalillah wa inna ilaihirraji’una” ya fi a k’irga da kyar na iya controlling din kaina natafi gurin lacture din.
Babu mutane sosai a hall din sai dai da yawansu masu nutsuwa ne, ko da aka tashi da sauri na fita na samu mota na wuce gida don ba naso Y. Hisham ya riskeni
A gida kuwa ganina wurjanjan Umma ta ce “Duk gajiyar ce haka Saudat?” Na d’aga kaina don haka tace "oh,sannu yau daya kin ga yardda kika koma? Maxa dauko abincinki a kicin ki ci”
Cewa nayi, “To Umma bari na yi sallah tukunna” fatana kada Allah yasa y Hisham ya sake tayar da maganar ubangiji kada ka kaddarar min auren sa, Allah ka fi ni sanin masifar dake cikin danginmu, Allah ka sa ya janye xancen nan.” Addu’oin da bake ta yi a raina kenan.
Abincin ma tura shi kawai nake yi da xarar na tuna kalmar "ina son ki sauda" sai na ji gabana ya fad’i ,umma kuwa cewa take,”’Maza ki ci kije ki kwanta,duk da rashin barci ma kin riga kin saba da shegen barcin safen nan.” Ita a zatonta duk gajiyar ce ta firgitar dani haka.
Ai kuwan ina gamawa na mike naje na kwanta lamo, ba barcin nake ba sai tsabar tunanin da ya cushemin kwakwalwa.
Sallamarsa na jiyo na tsakr gida gabana ya sake yankewa ya fadi.ina jin yana tambayar Umma “Saudat kuwa ta dawo?”
Umma tace"ta dawo,gata can a daki a kwance ko ma tayi barci. Yar nema duk a gajiye ta dawo likis.”
Yace, “Hmmm Saudat kenan.
Wa ya gaya mata karatun sauki ne musamman karatu irin nasu na likitanci”
Daga haka yayi mata sallama ya fita.

Ku karanta kyauta.


08033748387

📄6


Da safe ina d’aki a kwance nake sai dai ba barci nake yi ba. Waya muke da wani saurayina Bashir da nake matuk’ar so. Anan bayan layin mu yake trader ce dashi yana siyar da kayan masarufi. Mun dad’e mu na soyyah da Bashir ba tare da kowa ya sani ba hakan ya sa sam ba na kula kowa da sunan soyyah, duk da samarin da suke matuk’ar so na.
Bashir d’in ne ya Hana ni fad’awa kowa saboda ya CE so yake sai ya yi diploma ya samu aiki, sannan ya bayyanawa Kowa. Shi yasa ko zance ba ma yi da shi daga waya sai ko text message.
Umma ta d’aga labule ta shigo. Ba ki tashi ba ne?”
Da sauri na kashe wayar tawa kirar Nokia 3310 na ce " na tashi Umma."
"To maza ki shirya za muje bikin Nafeesa y’ar gidan Inna shukra.
Da sauri na ce" umma biki kuma? Dan Allah ki barni a gida ki je ke kadai."
Umma ficewa tayi kawai ba tare da ta sake yi min magana ba. Hakan ya sa na san na b’ata mata rai matuk’a da gaske. Don haka tsam na mike na fito tsakar gida na shiga toilet. Wanka na yi, sanan na dauro alwalar salllar wahala.


A gaggauce na shirya, ganin umma har ta fito kofar d’akinta tana jira na. Wata shadda na sa pink color a sallar da ta gabata aka dinka min ita. Adon zaren dinkin blue aka yi mata. Don haka na yafa mayafi na blue.
Sosai na tsaurara kwalliyata don gudun kada a raina ni.yau ni ce har da eye shadow da jambaki.
Ko da na fita umma ta kalle ni fuskarta d’auke da murmushi take “Ko ke fa? Baki ga yadda kika yi kyau kika fito sosai ba, dan Allah idan munje kada ki yi k’uncin ran da ki ka saba musu ki saki jiki ki gaisa da kowa da fara’a kin ji?”
D’aga kaina nayi kawai ina mamakin sanyin hali irin na Umma ita kam taji dad’inta sosai, ba ta kullatar kowa a ranta. Zuciyarta fresh take akan Al,amarin duniya. Gata da son zumunci.
Adaidaita sahu muka tafi da yake gidan da nisa tsakaninmu chairman d’in hotoro take aure.
Kofar gidan dankam da mutane don ranar ne ake daurin auren, ga shi ba halin mu juya, da sauri na ja mayafina na rufe fuskata tamkar Zan fad’i haka k’afafuna suke harhard’ewa.
"Sannu da zuwa Umma.” Muryar Y. Hisham na ji Yana gaishe da umma,bayan mun shiga farfajiyar gidan na d’an zame mayafina fuskata ta bayyana na d’an dubi inda yake caraf idona ya had’u da nasa. Ban tab’a ganin ya yi min kyau kamar na wannan lokacin ba.
Murmushi ya sakar min ya ce," kin gama boyon fuskar ta ki?”
Nayi murmushi sannan na gaishe shi
Umma ta ce "Har an d’aura auren kenan?”
Y Hisham ya d’aga kai idanunsa a kaina na rasa wani irin kallo yake bina da shi. Umma ce ta katse kallon ta hanyar cewa “To saudat mu shiga”
Na bi bayan umma muka tafi.
Koda muka shiga harabar gidan ba bu wanda yayi mana kallon arxiki bare mu samu kalmar sannu da xuwa. Da kyar muka samu muka ratsa babban falon gidan duk yayye da kannen mahaifina ne a gurin, sai y’ay’ansu da surukansu, masu ido da kwallli. K’alilan ne suka amsa sallamar mu, daga gefe muka durk’usa kan dole na gaishe su don gudun fad’an Umma.
Da kyar suka amsa kamar wad’anda aka yi wa dole babu wanda ya sake kallon mu muna daga gefe, sai can uwar bikin ta kallemu tace da Umma “Don Allah je ki baya gurin masu aiki ki taimaka musu "
Tsam umma ta mik’e muka nufi kofar da ta nuna mana. Aiki ne jingim don tuwo ne ake yi da shinkafa da jallop da alama abincin ya ku bayi ne, don dai jiga jigan na san sai dai ayi musu order hotel.
Nan da nan umma ta fara aiki ba ji ba gani.ni dai ido na zuba musu, don ban ga dalilin yi wa wad’annan matsiyatan bauta ba.
Ina gefe game nake a wayataa inna falmata ta shigo ta xabgan harara.”To matsiyaciya, kina nan kina fama da shegen girman Kan tsiya ke ba y’ar kowa ba”
Sunkuyar da kai kawai na yi ba tare Dana tanka mata ba
Ta watso min kudi #2500 d’auki ki fita titi ki siyo min recharge card na min.”
Na d’au kud’in ba don komai ba sai don ba na son b’atawa UMMA na rai, idan ban da haka duk ga k’annena a gurin ba a aika ba saboda su iyayensu suna da shi, ni kuwa da nake, y’ar fuk’ara’u dole na zama yar aike kamar yarda uwata ta zama y’ar aiki, madadin ta zauna cikin faccaloli y’an uwanta aka had’a min ita cikin masu aiki.
Jikina a salube na fita harabar gidan can gefen mota na hango Ya Hisham a tsaye da wata tsaleleliyar budurwa suna magana cikin nishadi har na gifta su na ji ya ce “Ke sauda.”
Mamaki ya kama ni, don sam bai tab’a ambatar sunan ba. Na juyo da hannunsa ya min nuni da alamar na zo na k’arasa gurinsa don kuwa shi ma yana girmama iyayena.
"Baki lura da mu bane kika wuce?”
D’aga kai na yi kawai
"Ina za ki je to?” Ya sake jeho min tambaya.
Nace “Recharge card zan siyowa Inna falmata.”
Ya d’ago kai ya dubeni kafin ya ce “Recharge card?duk ina yaran da suke aiki a gidan nan za’a aiko ki siyo recaharge card? Ke kuma ki ka fito siyowa ga maza haka za ki ratsa su?”
Cikin rawar murya na ce “To ya Hisham ya zan yi?”
Sak yayi Yana kallona.sannan ya zabga tsaki "mts:::::: wani layi take amfani da shi?
"Nace MTN "
Ya kalli bakuwaraa yace" bani two minute dan Allah " ya fice yana cewa" ke kuma ki tsaya ki jira ni anan, da ina da numberrta ma sai na mata vtu.” Ya wuce bai lura da hararar da budurwarsa take zabga min ba……




Jikar Nashe ce✍🏽✍🏽


❤️❤️❤️❤️❤️

Zumuncin Zamani
Na

Nazeefah Sabo Nashe

Typing Fad’ima Sabi’u D’ankaka

8



Daga ranar da ya yi min wannan maganar, Y.Hisham bai sake tunkara ta da xancen ba, duk da koda yaushe muna had’uwa don kuwa shi yake kaini ya kuma d’auko ni, Ko ya sa direban office d’insa ya d’auko ni, saboda ya rok’i Abba kuma yayi masa wannan alfarmar don yaji dad’i sosai.
Tsahon sati biyu bai sake tada maganar ba. Yau ma da wuri na tashi saboda 7:30 zuwa 8:00 muke da lecture, yaluwar riga na saka, kamar koda yaushe da addu’ar umma na yi sallama daga gida. Ina fita na tarar da motarsa na bud’e gidan gaba na shiga fuskata a had’e na ce "Ya Hisham ina kwana"?
Ajiyar zuciya ya saki kafin yace "lafiya lau sweetheart" yarr naji wani iri a jikina, na ce “Ya Hisham dan Allah ka bar maganar nan"
Murmushi ya saki bayan ya juyo ya dubeni yana tsare ni da ido har da d’aga gira d’aya ya ce “Me yasa zan bar ta? Ko ba kya so na ne Saudat?”
Na d’ago da kaina ina dubansa. Kafin na ce “Ya. Hisham ba wai maganar so ba ce, maganar masalaha ake, kai kanka ka san tarin bak’in jinin da muke da shi a family d’in nan duk a dalilin rashi. Ka sani ba yarda za su yi da wannan ba, idan ba so kake tsananin kiyayyar da ake nuna mana ya sake ninkuwa ba dan Allah

Please Login or Register in order to submit comment