Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara amman na rasa me zan dunga sayarwa
Sauda ta dan yi jim kafin tace duk layin nan umma babu mai awara da safe ina ga ita za ki dinga yi,
Umma ta daga Kai tace haka ne, ke ma kin ce wani abu bari abbanku ya dawo na sanar dashi idan ya amince shi kenan sai na fara don gashi bikinki ya matso tunda sunce jibi xaa kawo kudin aure.
Da sauri sauda ta dago kai tace biki kuma umma.

Umma ta dan saki fuska tace to ya zaayi sauda kana taka ne Allah yana yasa abbanki ya amince wa Hisham aurenki saboda takanas ya dauko baffan wudil,kuma ba komai yaron nan Hisham ya cancani a bashi aurenki don ya yi mana halacci,ke kanki kin sani sai dai ki bawa wani labari don haka don Allah kada ki sa komai a ranki ki yi addaua Allah yasa hakan ya zamo alkairii a rayuwarki...
Turus sauda tayi,hawaye male_male a fuskarta yanzu shi kenan ta tabbata Hisham zata aura? Ta sani shi kenan tayi sallama da farin ciki a rayuwarta matukar ta shiga cikin danginsu inda ba a son su ba a san darajar da kimarsu ba.

Umma ta xuba mata ido ita kanta tana tausayawa yarta tata sai dai babu yadda za tayi ba kuma abinda za tayi mata da ya wuce ta bita da addaua kiyi shiru sauda inshallah hakan alheri zai zamo miki.
Sauda mikewa kawai ta yi ta shige daki,duk da zuciyar ta tana son Hisham amman sam ba ta burin aurensa.




Senator sule Jami,I ya dubi Hisham bayan ya gama koro masa jawabin yadda suka yi da Abba mustapha sannan yace to Alhamdulillah,abu ya yi kyau zan sanar da mahaifanka a kai kudin aure gobe ba na so kai ka yi masa magana ka barni da shi.
Hisham ya rusunar dakai Yana zuba godiya.
Senator ya dafa bayansa yace kada ka damu Hisham ni da na dauke ka, don haka ka godewa Allah kawai

Hisham ya mike yana yi masa sallama,daga haka senator ya dau wayar sa ya danna kira alhaji hamxa.
Bugu daya ya dauka tamkar wanda yake Jira,bayan gaisuwa a tsakaninsu senator yace yana son ganin sa alhaji hamza bai dauki wani dogon lokaci ba ya bayyana a office din sule Jami,I
Senator ya dubi shi fuskarsa babu alamar wasa yace Hamza an gama da maganar mustapha,ya amince da bawa Hisham auren yarsa......
Hamza da sauri ya ce ba dole ya amince ba,tunda mu zai mora.
Dakata!!! a fusace senator ya dakatar dashi ba wannan maganar ce ta sani na kira kaba maganar aure nan da wata daya tana nan babu fashi,don haka a gobe nake so ka aika a kai kudin neman auren zuminci Allah ne idan kaga dama ka rike shi kai ka sani idan ba ka rike ba kai da Allah aure ne dai babu fashi kaji ni da kyau.

Alhaji hamza shi ma ya dan hade rai yace shi kenan Àllàh ya kaimu goben A zuciyarsa yace ya fara gajiya da wannan mulkin mallakar na sule Jami,I tamkar wani ubansa,amman akwai lokaci

Daga nan alhaji hamxa gidan kaninsa lawal ya tafi don ya sanar dashi yaci saa kuwa ya same shi a gida bayan doguwar gaisuwa alhji hamza yace lawal gobe za ka kai kudin auren Hisham.
Alhaji lawal ya dago kai yace ban gane ba yaya banda wanda aka Kai?
Alhji hamza ya yi tsaki kai dai bar Hisham da shegen jajibe _jajibe wai yar gidan mustapha zai hada ya aura ita da yar wajen honorable din

Alhaji lawal ya zaro ido Yana kallon alhaji hamxa yace wane ne mustapha kuwa? Shi Kuma Hisham ina zai Kai mata biyu a lokaci dan hadama?

Kai ma dai ka fada,babu yadda ba muyi da yaron nan ba sam ya kekashe kasa ka rabu da shi wanda bai ji bari ba ai bazai ji hoho, kafirin taurin kai ne dashi wai yar gidan mustapha namu yake so
Alhji lawal ya sake zaro ido yace kai haba yaya kai Kuma kana ne ka amince masa siyan tsiya da kudinsa?

Alhji hamza ya sake zabga tsaki yace barshi kawai har hadi ni yayi da honourable shi kuma ya rantse idan ban amince ya aure su biyu bato shima ya fasa ba da yarsa, don dole na amince amman a zuciyar ta fa akwai wani kuduri na daban, na amince ne ya aure ta bayan auren kawaii sai na saka ya sake ta,ta dole Kuma tun kafin ya shafo mun tsiya, don haka yanzu na yi wa adamu waya ga #20000 a kai kudin auren.

Alhaji lawal yace shi kenan ka dai yi kokarin raba su tun kafin ya goga maka tsiya,ana murna ya taso da kashin arxiki zai jinginu da masu kashin tsiya, bar ni da shi na san maganinsa alhaji Hamza ya fada yana sake girgiza Kai.




Sauda a hankali ta amsa kiran umma,ta fito daga daki duk wannan kazar_ kazar din babu shi idonta kozai _ kozai alamar taci kuka ta koshi
Umma ta dube ta tadan bata rai, yanzu sauda haka da kike yi fisabillahi ya dace duk kinbi kin kwarzabi kanki a kan karamar matsala? Sai kin janyo wa kanki cuta? Ai shi kenan,kiyi ta yi idan kina ganin hakan ya fimiki, ki wuce kije Hisham ne ya Aiko yana kiranki, saura kije ki nuna masa bakin rai. Umman ta fada tana shigewa daki.

Saudat bata yi jinkirin fita ba saboda ta lura umman ta dau xafi da yawa.
Yana cikin motar sa,don haka ta ja ta tsaya a kofar gidan, fuskarsa ta a hade, kasancewar da wuta hakan yasa Hisham ya gano ta, murmushi ya saki ya fito daga motar dan ya san Mulki ne ya motsa mata kenan Hisham sai lallashin.
Yana Isa gabanta ya hau leken fuskarta yana sakin murmushi yace ran gimbiya ya dade,ba a yi farin cikin da gani na bane.
Kicin_ kicin ta sake yi da ranta tace ya zaayi na yi farin cikin da ganin ka bayan kana shirin rusa min nawa farin cikin?
Hisham ya nuna kansa yace NI SAUDA "
Ta murtuke fuska hade da fadin kai din y Hisham dan Allah ka janye daga maganar neman aurena!!!

Ni gaskiyah baxan iya ba,sauda Naga samu naga Rashi ya fada yana kwaiwakyon salon muryarta.
Hakan yaja sauda ta saki murmushi, don kam ya bata dariya, Shima murmushi ya sake kafin yace koke fa my angel har na ji Dadi.don Allah ki zo mu shiga mota akwaii maganar da zamu tattauna.
Sauda ta makale kafada ka fadi maganar ka kawai anan ina jinka..
Ya zuba mata ido yanzu sauda ba zan nemi alfarma ki yimin ba? Shi kenan many thanks to you daga haka ya juya.
Tunanin tayi sam ba ta kyauta ba, don haka tabi shi.

Har ya shiga motar ita ma ta bude murfin motar ta shiga ya dan dade bai juyo ya kalle ta ba,sai can ya juyo ya kura mata ido tsawon mintuna har sauda din ta dan tsargu ta sunkuyar da kanta sai can ya ja ajiyar xuciya ya ce ina murna sauda na kusa mallakar ki a matsayin matata,sai Kuma ki nuna min ke ba ki so hakan ba? Sauda kin san wahalar dana sha kuwa kafin a amince min auranki amman kiri kiri ki nuna min ke baki so ba, kin kyauta kenan?

A hankali ta dago ta kalle shi, gabadaya sai ta ji ya bata tausayi,ta tabbatar Kuma ba ta kyauta ba, Hisham mutum ne da ya cancanci a soshi ko ba komai a kafatanin masu kudin danginsu shi kadai ne ya ba su kulawa,ba kyamace suba,duk da takaucinsu idan yazo gidansu abincin da suka ci shi yake ci, ruwan da suka sha shi yake sha, mutumin da ya yi maka haka anya ya kyautu kayi masa butulci? Ta tabbatar ba laifinsa ba ne na iyayensa ne, Kuma ko ba komai ta tabbata tana son Hisham,son da ya tsaga kashin ta yake zagaya wa cikin jininta.

Ta lumshe Ido ta bude tar sai taga su akan Hisham ta san saki murya tace y Hisham ka yi hakuri don Allah. Ba wai.bana farin ciki bane,ina tunanin rayuwar da zan fada ne har ga Allah,amman ya wuce kawai ka yi hakuri.
Sai a lolacin Hisham ya saki murmushi Yana leken fuskarta,yace sauda,kalle ni
Sam kasa kallon sa tayi I
Ina so ki sani,ni zaki aura ba dangina ba,kuma na yi miki alkwari duk rintsi duk wuya, babu abinda zai sa na juya miki baya!!!

Sauda ta saki murmushi tace ni ma nayi maka alkawarin kyautatae maka fiye da zaton ka, fatana daya ka bani gamsasshiyar kulawa.
Bayan hakan bai dade ba yayi mata sallama tare da alkawarin kashegari zaizo da yammah su tattauna tsare tsaren bikin mu!!!


Koda ta koma gida dakinta ta shige,sai a lokacin take jin tsananin farin cikin na samun damar mallakar burin ranta. Tana son Hisham son da sam baya misaltuwa.ta rintse ido tana tunanin ta kusa amarcewa da mijinta tunanin ta,ya tsaya cak da ta hasasho waye zai mata kayan daki, kasancewar ta sani iyayenta basu da shi kuma basu bawa kowa ajiya ba,gashi biki wata daya zaa saka.!!ta lumshe ido a hankali ta furta Allah ka fitar damu daga wannan bakin talaucin ta sani Allah Mai jibintar lamarin mutane ne, ubangiji ka jibinci Al,amuranmu.


A kashe gari umman sauda ta fara awarar siyarwa duk da ba son ran Abban sauda ta fara ba, ta bashi hakuri hade da sanar da shi alfanun haka,ga misali zaa gayyace ta biki,zata so ta mikawa uwar bikin dan hasafi yara xasu ziyarce ta, akwai bukatar ta basu kudin mota don haka a nata hasashen sana,a ta zama dole,saboda kuwa duk wadatar mijinka akwaii lokacin da zai gaji da bani bani idan kuwa kina sanaar kin wuce wulakanci namiji komai shine balle marar shii

Sauda dinma da wuri ta tashi kasancewar lahadi ce ba ta da lecture, ita ce take suyar awara a soron gidan.karfe9:00 na safe ta ji tsayuwar mota a kofar lungunsu ba tayi kokarin mikewa ba, don daman hijabintaa a jikin ta,tana jin muryar sallamar ta tabbatar b.lawal ne kanin mahaifinta ilai kuwa tana daga Kai ya sakar mata wani mugun kallo ya tabe baki yace ke kuma me kike wanann tallah, shi kuwa Hisham a hakan yake son ki

Sauda ta sake sunkuyar dakai kawai ta yi abin kam yayi mata ciwo ba ta gama sanye wanan bakin cikin ba b amadu yace " ba shi ya jiyo ba tunda an gaya masa ya kiji,sai a rabu dashi wanda baiji bari ba ai bazai ji hoho ki shiga kiyi mana sallama da mustaphan.

Ta wuce tana jin lokacin da suke cewa lallai tsiya takai tsiya ko yaushe ya dawo wannan kwarabebben gidan? Allah yq kyauta
Jikinta a salube ta shiga gidan tana kokarin goge kwallar da take kokarin zubo mata. Ta dubi umma tace wai su b lawal suna sallama da Abba.
Umma ta mike tana cewa" to bari na gaya masa kin gama awarar ne?
Ta kare!! Kawai tace, tana shigewa daki, kuka ne ya kwace mata sosai ta kunshe bakinta cikin matukar bakin cikin ba ta son umman ta taji kukan.

Abbanta yafito yana fadin oh yanzu don bani da shi a rasa mai karbar kudin auren yata duk a dangin sai ni da kaina.
Umma tace,kayya malam, Kai ma ka sam ba za su karba ba,don kawai basai don kada a dora musu wahala
Abba yace ai shikenn ya sa Kai yaefice daga gidan

A tsaye ya gansu gabadaya cirko_ cirko nan ya dan saki fuska yana cewa,sannunku da xuwa ya fada yana shimfida musu tabarma.
Babu wanda ya amsa har suka zauna Abba ya sake cewa muntashi lafiya alhaji lawal?

Duk da yake kaninsa yayi kokarin daraja shi don daga shi har amadu ya girme musu sosaii lawal fuskarsa a gimtse yace mustapha dama ba wani abu ya kawo muba sai don kawo kudin auren yarka" tare da sanar da kai an yanke biki nan da wata daya,kuma shi Yaya hamza yace a sanar da kai baya bukatar a Kara lokaci.
Mamakine ya kama Abba sabida kiransa da mustapha gatsal da ya yi, amman ya kira Hamza da Yaya hamzaa duk da shi din ya girmi hamza tsaf ya Shanye mamakin sa yace ubangiji ya kai mu

To Fa!


Zumuncin Zamani

Part 2 free book

08033748387

Na Nazeefah Sabo Nashe. ✍🏽

1



Alh. Amadu ya zura hannunsa a cikin aljihu ya zaro kud’in y’an dubu-dubu ya zari guda ashirin ya ajiye masa a wulak’ance alamu suna nuni da tilashi aka masa. Murya a shak’e ya ce “Ga kud’in neman aure nan Naira dubu ashirin, wannan kuma Naira dubu talatin na saka rana idan ka had’e su jimilla za su baka dubu Hamsin kenan cif. Tunani muka yi gwara a kawo kud’in za su fi muku amfani akan kayan da ku wasu ne ma lefen ma kud’insa za ku karb’a. Kwa siya mata kayan d’aki da su tunda dai mun san baka ajiye ba ba ka bawa wani ajiya ba.” Abba Mustafa kuwa murmushin takaici ya dinga jefa musu zuciyarsa cike da mamaki da lamari na duniya mai cike da rud’ani iri da kala. Kafin ya yunk’urin cewa wani abu tuni sun mik’e kamar dama akan k’aya su ke. Ahamdun yana cewa “Alh. Lawal sai mu wuce ko? Don ni ina da abubuwa masu muhimmanci fiye da
Wannan d’in da aka min tilas.” Shima Alh. Lawal d’in mik’ewa ya yi yana sab’a babbar Riga yana cewa “Ai nima haka Ahmadu banda abinka zaman me za muyi anan d’in da dai wani gidan ne sai mu tsammaci tukuici amma nan mai na sama ya ci ma balle ya bawa na k’asa.” Suna fita Abba Mustafa ya bisu da kallon mamaki kafin murya a sahhale ya ce “Jalla ya kyauta.” Ya kwashi kud’in a hannunsa ya shige cikin gida, zuciyarsa fal da tunanin rashin son auren banda Yana ganin girma da mutuncin Baffan Wudil da bai amince ba to k’aunar da yake wa mahaifinsu ce ta koma kan Baffan, yana kuma jin ba zai iya k’in yi masa biyayya ba matuk’ar zuciyarsa zata dinga hasasho masa waccan wasiyyar ta mahaifinsu a bigire mafi girma a zuciyarsa.

Ko a cikin gida zancen da suka dinga yi kenan, k’iyayyarsu ga auren sam bata kwatantuwa. Ita dai Sauda na jin su bata da bakin amsawa amma zuciyarta tafi tasu zafi da tafasa idan ta tuna tarin matsalolin da suke tunkaro ta, wala Allah ta ta jarrabawar kenan, sai dai fatan ta amsa ta da kyau tare da taimakeni addu’a da ta tabbatar itace takobin da ta rik’e.
Abba Mustafa cikin b’acin rai ya ce “Ficika ba Zan ci a kud’in nan ba, wajen mai kayan gado zan je na fara bashi wani abin kafin mu ga abinda Allah zai yi. In sha Allah yarda suke son na ji kunya Ubangiji ba zai jiyar da ni kunyarsu ba, shi lamarin Jalla ai girma gareshi matuk’ar zaka sakankance da cewa shi zai maka zai kuwa shayar da kai mamaki. Mu yi ta addu’a Allah ya fitar da mu kunyarsu duk da dai ba mu da arzikin da za mu basu mamaki amma za mu yi mata hana gori ko bakomai bahaushe ya ce “Da Hannau gwara Mannau kuma sandan da yake hannunka da shi ka ke kai duka.”
Saudat runtse idanunta ta yi tana jin wani irin zazzafan tausayin iyayenta yana zagwanya a k’irjinta yana haifar mata da wata irin k’una tausayin su take ji sosai bata san k’addarar da ta kawo Hisham cikin rayuwarta ba, ba burinta bane auren mai kud’i tafi son talaka d’an uwanta inda ba yarda zata je a mata gori amma ya ta iya da k’udirar Rabbani. Ta san yanzu Babanta zai d’aga hankalinsa duk da ta san shi ba mutum bane mai sanya damuwa a ransa shi yasa ko hawan jinin nan na zamani ba shi da shi, yana da kyautayi da tawali’u yana maraba da duk abinda Allah ya bashi yana kuma rok’ar Jalla arziki mai amfani kamar yarda yake neman tsari da arzikin da zai zame masa masifa arzikin da zai kasa taimakon mai neman taimako Arzikin da ake kira daga k’auri sai cinya. Ko bashi mahaifinta baya ci koda kuwa za su rasa abin kaiwa baka ya kan ce ku yi hak’uri mu d’ora da azimin tunda dai ku ba yara bane.

Ranar sukuku ta wuni, Umma na hankalce da ita, sai dai hats furta mata komai ba tana son hasasho mai ya addabi zuciyar d’iyar tata.

Da yamma Hisham cike da zakwad’i ya yi mata waya cewa ga shi a k’ofar gida kunyar Umma da Abba yake ji shi yasa ba zai shiga ba. Da tana cikin sukunin zuciya da ta zolaye shi sai dai ba wannan damar a ranta. Ta zura hijabinta kawai ta sanar da Umma yana waje yana jifanta Umma ta rik’e hab’a tana cewa “Yau kuma Hisham wani sanaben ya samu? Shi da gidansu zai rakub’e a waje sai Abbanku yazo yana fad’a kice masa ya shigo ciki ai ba shi da maraba da y’ay’an gidan har kullum Abbanku yana fad’a.”

Garin a lumshe yake da tausasahiyar iska mai gauraye da k’amshin k’asa kasancewar ba a dad’e da d’auke ruwan saman ba.

A jingine yake a jikin motarsa Mercedes benz GLK fara tas da ita. Ya yi kyau sosai cikin wata dakakkiyar shadda getzner Sky blue fuskarsa sai fitar da wani irin murmushi yake da yake k’ara zagwanyo kamalarsa da
Cikar haibarsa akan fuskarsa. Kansa babu hula ya barta a cikin mota hakan ya bawa kyakykyawan gashin kansa bak’i sud’ik damar fitowa da sajensa da ya kewaye fuskarsa. Yana ganinta ya lumshe idanunsa ya dunk’ule hannunsa waje guda ya kai mata jinjina murya a cike da farin ciki ya ce “Ga gaisuwarki ta amare manya.” Saudat murmushi kawai ta saki tana k’ok’arin kawar da abinda ke ranta saboda bata son ta b’ata yanayin walwala da farin cikin da yake ciki, don haka ta ware ta tata cunkusashshiyar fuskar. Yana k’ok’arin bud’e motar ya kalleta “Bismillah Madam yau nima zancen y’an gayu zan tab’a zance a mota.” Da sauri Saudat ta girgiza kai “Gaskiya Y. Hisham ba zan shiga ba bana son zancen mota.” Sosai ya k’ank’ance idanunsa a kanta yana kewaye fuskarta da wani irin narkakken kallo ji yake tamkar ya janyota jikinsa.
Murya a cunkushe ya ce “Why? Baki yarda dani bane ? Ko ki na zaton zan cuceki?”
Da sauri ta girgiza kai “Ba kai nake tsoro ba Y. Hisham shaid’an da muk’arrabansa na ke tsoro mu tsaya dai anan kada mu tsallake fad’ar Manzon Allah da ya hana Keb’ancewa tsakanin namiji da mace inda ya tabbatar na uku su shaid’an ne.” Sassauk’ar ajiyar zuciya ya saki yana sake jaddada kalmar Alhamdulillah ko yanzu ina alfahari da Umma da ta tsaya tsayin da ka akan tarbiyyarki ba tare da la’akari da cewa ke d’in jal ke ce y’arta mace ba. Am really proud of your Behaviour My sweet.” Murmushi ta saki tana wasa da yatsun hannayenta murya k’asa-k’asa ya ce “Kwana nawa ne zan mallakeki sai yarda na yi da ke. Ba wanda zai ja min aya ko Hadisi akan ki.” Saudat bata san sanda murmushi ya d’an sub’uce mata ba, ya shagala da kallon yarda murzazzun kumatunta suka lob’a kad’an baya gajiya da kallon fuskarta musamman idan tana murmushi sai ya ji kamar ya sunkuceta ya b’oye don yana kishin maza su ga k’ayataccen murmushin akan fuskarta. Ya saki ajiyar zuciya da murmushi lokaci guda ya ce “Ba dai kunyata ki ke ji ba? Wai ma su Baba Lawal sun zo ba ki bani labari ba?” Saudat tsit ta yi masa saboda bata san tuna ko Sunan su B.Lawal balle har ta ambaci sunan da bakinta. Hisham ya gyara tsayuwarsa kafin ya sake karantar yanayinta ya ce “Gaya min ya kika yi shiru? Ko kud’in ne suka miki kad’an na k’ara?” Saudat ta waro idonta kafin ta ce “Ni a suwa da dubu Hamsin zata min kad’an ai iya matsayina kenan a tunani ma murna ya kamata na yi. A matsayina na y’ar Malam Mustafa ba honourable Mustafa ba.” Sakar baki Hisham ya yi yana kallonta fuskarsa d’auke da matsanancin mamaki ba wai na maganarta ba sai jin da ya yi ta ce wai dubu Hamsin aka kawo. A matsayinsa ne zai kai kud’in aure da sa rana dubu Hamsin kacal kamar na wani mai k’aramar sana’a, tsawon lokaci zuciyarsa na zurfafa tunanin kafin ya ce “Ban gane me kike nufi ba? Dubu Hamsin fa kika ce?” Saudat ta d’an yi murmushi ta ce “Haka suka kawo sannan suka biyo Abba da bak’aken maganganu da habaice-habaice, wallahi Y. Hisham don ka nace ne da mun hak’urcewa juna don tsakaninmu da kai akwai nisan banbanci.” Hisham tsaf ya gintse fara’ar sa ya dinga futar da wani irin zazzafan huci ransa a hassale yake sosai ga Sauda na neman sake hassalashi da maganar rabuwa abinda ba ya son ji kenan ko a mafarki. Mamaki da al’ajabin danginsu ya dinga girgiza tunaninsa komai sake tab’arb’are musu yake kamar wad’anda ubansu ya ce ku je kwa gani. Dubu d’ari uku cus ya bada a kawo shima d’in ba haka yaso ba dubu d’ari biyar yaso amma iyayensa suka
K’i shine yanzu za’a ce masa dubu hamsin sai kace zai auri y’ar tsana a matsayinsa da tarin arzikinsa, wannan idan wasu ma suka ji ai dariya za su masa. Lokacin da ya bada na gidan su Fareeda ai rai nawa suka yi da ya kafe ba zai cika ba Daddynsa
Da kansa shi ya cika kud’in yana jaddada
Gidan girma ne da mutunci Hisham ba zaka ba kunya ba miliyan guda za mu kai. K’wafa ya ja mai sautin gaske, wanda
Hakan ya ja hankalin Sauda da sauri ya kalleshi ta ce “Y. Hisham lafiya kuwa?” Hannu kawai ya d’aga mata cikin takaici ya ce “K’yaleni kawai Sauda, ban san me mutanen nan suke son su zama ba, dubu d’ari biyu da Hamsin na basu ta yaya ta koma dubu Hamsin sai kace zan auri bazawara, to ko bazawara a matsayina na mawadaci ai bai kyautu na
Kai kud’in aurenta haka ba, kuma ni kud’in zance kawai na bayar ban ce musu da na saka rana ba, kayan saka rana a
Cikin kayan lefe za’a kawo. Wato suna so tun yanzu su fara nuna banbanci tsakaninku tohm ba zan amince ba ba su san ni ke zuciyata take so ba, ke na ke jin zan iya kashe last kobo na a
Kanki saboda son da nake miki.”

Tuni duk wani b’acin ran Sauda ya zagwanye ta dinga jin wani farin ciki na ambaliya a cikin k’ok’on ranta. Don haka zuciyarta tas ta d’ago ta kalleshi tana jin son sa na k’ara ninkuwa a ranta. Sai dai zuciyar ta ta buga ras jin ya ce tun yanzu za su fara nuna banbanci tsakaninsu me yake nufi? Ba dai su biyu zai aura ba. Cike da tsoron jin amsar sa ta ce “Y. Hisham ban fahimceka ba, kana son kace min mu biyu zaka aura? Ban fahimci kalmar banbancin da ka ambata ba? Banbanci tsakanin ni da wa?”

Tsit Hisham ya yi don sam ya sha’afa bai sanar da Saudat zancen su biyu zai aura ba, k’irjinsa ya shiga bugu yana tsoron tawayen Saudat don ya san daga ganinta zata yi kishi. Wannan fa shi ne ana wata ga wata.
Cikin wata iriyar muryar firgita ta sake cewa “Y. Hisham tambayarka fa nake?” Ta fad’a muryarta na rawa tun kafin ta ji amsar ta ji gaba d’aya yanayin sauyin bugun zuciyarta ya sauya. Tsoron jin furucinsa take yi tsoron ta ji ya ce ‘eh Ku biyu zan aura take yi’

Jikinsa a sanyaye ya d’ago yana kallonta murya a tausashe ya ce “Ki yi hak’uri Sweet na zata na sanar miki ku biyu zan aura da Fareedah rana d’aya za ku tare, amma wallahi Sauda Ina son ki fiye da son da nake wa Fareeda.” Cikin wata irin razana tana masa wani irin kallo ta d’aga masa hannu “Ya Isa Y. Hisham, wallahi ba zan aureka ba, don ba zan iya zama da
Kishiya ba musamman kishiyar da kowa a dangi ya shaida sun fi son ta a kaina so kake bak’in cikin tarin banbancin da za’a nuna a tsakaninmu da ita ya bugar min da zuciya? So kake y’ay’ana su zama barori a cikin dangi? So kake su tashi ba soyayyar iyayenka Daga haka takaici ya kar ni na mutu? Ba ni da k’wanjin da zan iya kishi da Fareeda yarinyar da tun

Please Login or Register in order to submit comment