Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka yi hak’uri”
" Ba xan iya ba Saudat,
Yana daga dalilin da ya sa zan sake jajircewa har na ga na cimma burina na auranki, saboda ina so nuna wa dangina kuskuran su, a yau ma zan samu Abba akan maganar saboda tafiya zan yi next week, ina so in ga matsayar zancen” hawaye ne ya kwaranyo daga idona cikin tsananin rud’ewa nace. “Dan Allah Y Hisham ka taimake ni” k’ura min idon ya yi kafin ya ce “Saudat bakya so na ne?"
Kallon sa sosai ya gigita ni don haka na kasa katab’us, sai murza yatsun hannuna nake.
Murmushi ya saki ya ce “Saudat kina so na, wani banzan dalilin ne zai saki k’warar kanki," daga haka ya tayar da mota bai sake magana ba sai dai jefi_jefi yakan kalleni ya saki murmushi.
Ko da daddre ina jin sallamar sa na shige d’aki. Na ji yana gaisar da Abba, sannan duk su Yaya sa'eed suka gaishe shi kuma, yayi k’asa da muryarsa sosai ya ce “Abba na zo ne yau a kan wata magana."
Gabana ne ya fadi sosai na yi saurin mik’ewa zaune ina zare idanuna. “Me Y.Hisham yake nufi ne?”
Abban yace "Ina jin ka Hisham menene ya faru?”
Tsit ya yi har sai da na ji Abban ya sake ce masa “Kai nake saurare Hisham, ka yi magana mana ka ke sosa k’eya, kada fa ka manta kai da su sa’eed d’aya na dauke ku fad’ ko ma mene ne ina sauraron ka.”
A zuciyata na ce "Ai dole ya ji kunya, shi kansa ya san ba abu Mai yiwuwa zai fad’a ba, sai kuma naji ya ce, “Abba dama a kan saudat ne, don Allah Abba aurenta nake so ka bani.”
Tsit na ji kowa yayi shiru a wurin, da alama dai Hisham ba zai yi sa’a ba,hakan ya sa farin ciki ya ratsa zuciyata.



Abba ne ya yi gyaran murya ya ce “Hisham ba zan hanaka auren Sauda ba saboda ina alfahari da kai kuma uba nagari zai so ‘yarsa ta samu miji nagari kamar ka. Matsala d’aya nake tsoro, ba kowacce matsala ba ce sai matsalar danginmu masu fifita kud’i fiye da zumuncin, don haka abin da zan ce maka ka je ka gama da mahaifanka, idan har sun amince maka auren Sauda, to ni a shirye nake na aura maka ita”

Hisham ya saki ajiyar xuciya ya ce "Shi kenan Abba, zan je na same shi amma ina so ka yi min izini na ci gaba da neman auren ta, kafin mu ga abin da hali zai yi”
Abba ya ce “Bakomai ai Sauda “yar uwarka ce Kai mai iya d’aura mata aure ne, fatanmu dai Allah ya tabbatar da alheri.”
Hisham ya ce “Shikkenan Abba, bari na je gida”
Gaba d’aya farin ciki ya ratsa ni, saboda na san ba yadda za’ayi Babansa Hamza ya yarda da wannan auren.
Yayanmu na ji yana cewa “Ai kuwa a gidan su da kyar za’a yarda da wannan had’in su da ba sa auren kowa sai yar wane, yanxu ya je yace saudat yake so ai B. Hamza sai ya kusan kashe shi.”
Y Sa’eed ya ce “Hmmn kai dai Allah ya kyauta amman dai za’a b’allo ruwan bala'i a dangin mu
Abba ya ce “Ni kam zan so ba shi aure don Hisham nutsattsen yaro ne, Abu d’aya nake tsoro, sam sauda ba zata iya jurewa bak’in hali irin na danginmu ba, don kuwa ba ta da sanyin hali kwarai, zuciyarta tana da zafi.
Umma dai cewa ta yi “Allah ya kyautaa, ya kiyaye fitina.”
Nidai na yi lamo kan katifata, can na ji Ya sa,eed ya ce “wallahi Abba ba ma za su yarda Hisham ya aureta ba saboda yadda yake tashen naira yanzu ba zancen wanda ake yi a dangin nan da ya wuce Hisham, don kuwa ya tako arziki.
Abba yace "Wai ina saudat d’in ne?”
Umma tana murmushi na ji ta ce “wacce saudat? Ai ita tuni ta yi barci”
Yayanmu yace “Wa ya gaya mata karatun jami'a irin na secondary ne? Musamman ita da take medicine karatu ma sai nan gaba”
Abba ya ce “wace irin magana ce wannan? Madadin ka yi mata addu’a, Allah sarkiii auta Allah ya ba da sa’a”



Jikar Nashe

Zumuncin Zamani
Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387

Pg. 9

(Sannu da jumirin typing Fad’ima Sab’iu Dankaka jazakillahu Bil jannatil Aaliyah.)



Da asussuba muka ji abba yana ta zabga "Innalillahi wainnah ilaihirrajiuna" A hanzarce muka fito daga d’aki kusan tare da Umma fad’i take “Lafiya Abbansu?”
Abba yace “Ina fa lafiya, yanzun nan Hisham ya yo waya ya sanar da ni mutuwar H.Amarya”
Umma ta saka salati ta ce "Allahu Akbar ubangiji Allah ya jikantaa.”
Ni kuwa sam ban ji mutuwar a cikin raina ba. To ina ruwa na? Ta yi ta mutuwar mana. Matar da ba ta so sam ta ga y’ay’anta sun yi alheri don bak’in hali, ita duk ta koya wa y’ay’anta rashin kyauta da rashin alheri, to don ta mutu har abin damuwa ne? Ai ga shi nan za’a je kabari a girbi abinda aka shuka, idan ka aikata alheri kaga alheri, idan sharri kuwa ka aikata kaga sharri cikin kabari.
Kwanciya na sake yi akan gado, dama ina fashin sallah. Har aka idar da sallah ina jin su maimaita zancen mutuwar kawai ake yi, kuma ban ji wanda ya yi wa Abba waya ya sanar da shi zancen mutuwar ba tun bayan Hisham duk dai ba don komaii ba sai don an san ba shi da shi.


Umma naji tana kwala min kira.
Nayi saurin amsawa na kuma fito. Bi na ta yi da kallo "Yi ki d’auko hijabinki mu tafi gidan mutuwa nan su Abbanki har sunyi gaba kada mu rasa jana’iza.
Na zumb’ura baki ina cewa “Umma ban yi wanka ba fa?”
Bi na tayi da kallo ta saki baki ta ce "Wanka! Wanka fa ki ka ce? Sai kin yi wanka za ki je gidan mutuwar.? Matsayin uwa take fa a wurin babanki.”
Na sake Zumb’ura ba ki na ce "Umma don Allah ki je zan taho idan gari ya yi haske,su ma da idan sune ko Abba ne ya mutu babu mai zuwa gidan nan da asuba.
Umma ta hade rai ta ce “To uwata, gaya min abindaa ya dace na aikata ki ke,ke ma ai kin zama su wallahi ba ku da banbanci ko ki d’auko hijabin mu tafi ko ranki ya yi matuk’ar b’aci.
Ganin yanayin fuskarta ya sa babu shiri na tafi d’aki na zira hijabi harda nikab na saka muka tafi.
Gidan mutuwar dank’am yake, a d’inke da mutane kai da ganin wasu ba don Allah su ka zo ba,ana ta kuka ni dai na ja nikab na rufe fuskata. Ina daga gefe cikin ya ku bayi, jiga - jigan kuwa suna cikin k’aton falon. Abinda ya ba ni mamaki ganin kafin asuba aka yi mutuwar nan amman kafin kiftawar ido har gidan ya cika damkam da jamaa tun kafin garin ya yi haske. Kowa ya shigo da kukansa burinsa dai a ce ya zo
Hajiya amarya ba ta da y’a mace duk y’ay’anta maza ne su Baffa Umar. Ba a samu fita da gawar ba sai k’arfe goma saboda ana jiran manyan baki da za su zo daga garuruwa daban- daban, tamakar idan babu su Allah ba zai mata rahama ba.
Bayan an kai ta kuwa nan gidan ya zama gidan party don dai lemuka iri iri aka dinga shigo dasu katan _katan da ruwan roba. Abincin breakfast kuwa doya da kwai, dankali da kwai sai dangin su farfesu da waina masa, funakaso da su sinasir. Tabbas wanda ya mutu shi ya mutu.
A gidan mutuwar ma sai an banbance tsakanin talaka da mai kud’i domin kuwa gurin zaman masu kud’i daban ne tamkar yadda cimar su take daban, ya illahi me wannan zamani yake son ya zama mutane sun makance sun kurmance saboda kud’i? Kowa zancensa kudi!!! Kudi!!!kudi¡!!!! Babu abinda yafi kud’i daraja da k’ima a idon jamaa.
Duk zaman gidan ya gundire ni, ba don komai ba sai don yadda ake ta Hira, duk wanda aka gani kuma da wata irin shiga kallon banza ake yi masa, amman naga alama Umma ba ta da niyyar tashi mu tafi, sai ma tattre kwanuka suke yi wai za su wanke ita da wasu ya ku- bayi y’an uwanta A xuciyata nace "Ya ubangiji Allah ka azurta mu ko iyayenmu muma sa zama masu daraja tamkar kowa.
Sai bayan magariba sannan umma ta ce na mik’e mu tafi, zuwa lokacin na galbaita da yunwa don banci komai ba sakamakon wariyar launin fatar da na ga anyi a wajen rabon abincin.
Y.Hisham yana ganin mu ya taso da saurinsa daga rumfar da ake zaman makokin, har k’asa ya gaida Umma, sanann ya ce “Gida za ku tafi ne?”
Umma tace “Wallahi,dare ya fara yi gwara mu tafi gidan.” Y Hisham ya ce “Gaskiya kam, bara na sauke ku dama ni ma tafiya zan Yi"
Umma ta girgiza kai kafin ta ce, "Ba mu takura ka ba kuwa Hisham?”
" Ba komai umma, wallahi daman ni ma zaman ya gundire ni"
Yana sauke mu gida na fad’a don ba na k’aunar ya yi min magana, hasali ma kunyar sa nake ji.
Ko da muka shiga su Abba tuni sun dawo, su ma maimaita zancen budurin da aka sha kawai suke yi. Ni dai kicin na shiga na dafa abincin . Ko fitowa ban yi ba daga kicin din sai dana xauna na take cikina da abinci sananan na sami nutsuwar kaina.
Kashe gari kuwa tun safe Umma ta tafi ni dai rok’on Allah na yi ta bar ni a gida na ci saa kuwa ranar ta barni babu mamaki ita ma ta hango babu alfanun a zuwa na zaman makokin.
Hakan ce ta ci gaba da kasancewar har aka yi sadakar bakwai, zuwa na biyu kad’ai gidan mutuwar.
Tun bayan ranar aka yi mutuwar ban saka Hisham idona ba sai bayan sati guda. Ko makaranta direban kamfaninsa ne yake sa wa ya kai ni ya d’auko ni.
Da yammah ya shigo gidan cikin shigar k’anann kaya da suka amshe shi sosai, fuskarsa a dan had’e idanunsa a kaina ya na gaida Umma ta mik’e ta shiga d’aki, ni kuwa daman ina daga gefe gyran farcena nake yi.
Ya matso daf da ni ya zauna , kamshin daddadan turarensa ya ziyarci hancina. Muryata ta yi k’asa sosai na ce Y.Hisham ina wuni.”
Wani kallo ya jefe ni da shi, wanda ya saka jin bugun k’irjina ya tsawaita. “kin kyauta Saudat, yanxu fisabillahi abin da kika yi ya yi daidai? Kwana nawa ba ki gan ni ba Amman ko ki neme ni duk a dalilin rashin so.”
K’asa na yi da kaina sosai,don kam ban san amsar da zan ba shi ba sai na ce “kayi hakuri Y.Hisham ban san hanyar da zan bi na neme ka ba, saboda ba ni da number wayarka.”
Kura min ido yayi sosaii,kafin ya ce “Saudat wanann ba hujja ba ce, saboda su khalil duk su na da number ta.” nayi murmushi kawaii don babu abin cewa.
Y Hisham ya ce “shi kenan nagode sosai daman sallama na zo yi miki, gobe zan yi tafiya ne sai na ce sai na dawo." Ya fad’a yana mik’o min wata babbar leda mai tambarin ShopRite cike take taf da kaya,daga haka ya juya ya fice.
Na lura jikinsa a mace yake sosai, na mik’e nima jikina a sanyaye Umma na kai wa ledar, har zan juya ta ce "Zo ki bud’e mu ga abinda ya ke a ciki, shi baya gajiya da hidima duk da na tabbata iyayensa ba bari za suyi ya aureki ba.”
Kayan kwalliya ne designers masu d’an karen kyau, sai turarika da wata shegiyar waya umma ta ce “Ban da matsalar danginku Hisham mijin kwarai ne kowacce mace za ta yi murna da farin cikin samun sa a matsayin miji abu d’aya ake guje miki matsalar danginku, da ba sa ganin talaka da k’ima da mutunci.”
Na saki ajiyar xuciya bayan na mik’e na koma d’akina, kwanciya na yi sosai a kan katifa cikin zuzzurfan tunani, don so kamm yanxu na hak’kake wa raina ina son Hisham amman na san aurenmu da shi na mai yiwuwa ba ne.


Daga nan labarin da na karanta wanda ta mik’o min a wani dogon littafi ya tsaya,na d’ago ina duban ta, kafin na ce”Saudat labarinki ya d’auko dad’i sai dai banji k’arshensa ba"
Tayi murmushi kafin ta ce" Anty Nazeefah ba ni da jumurin rubutu ne, zan gaya miki da wanda na sani da wanda ni ma labari aka bani.” Na d’aga kaina kafin na ce, “Ni ma hakan zai fimin sauki”
Sauda ta gyara zama, sanann ta miko min takarda da biro,ta kuma ci gaba da ba ni labarin***************


Jikar Nashe ce!


Zumumcin Zamani.

Na

Nazeefah Sabo Nashe


(Typing: Fad’ima Sabi’u D’ankaka. Ku mata addu’a Allah ya saka da alheri yasa ta koma saudiya kwana kusa.😊❤️❤️ burinta kenan a gareku.)


08033748387

(Kyauta ne.)

Gabadaya suka hada baki wajen fadin "innalillahi wainna ilaihir raji’un"
Y Mahmud ya ce "Abba garin ya ya?l
Abba ya ce "Allahu a’alamu Mahmud, mu k’arasa mu gani.”
Sauda na jin haka ta zira hijab d’inta haka nan Umman Sauda Abban ne ya watso musu wani kallo ya ce “Ku kuma ina za ku?”
Cikin rawar murya umma tace, “Zuwa za muyi mu gani”
Abban ya girgiza kai kafin ya ce "Ku je ku ga me? Ku ga tashin hankalin, bayan haka ma da mutane dank’am a wurin ku koma ba na son shirme da shiririta”
Jikin Umma a salub’e ta juya ta zauna. Haka nan Sauda ta bi bango ta rakub’e tana hawaye. Umma tace “Sauda yi kukanki ba zan hana ki ba wallahi, don dole ne abin kuka ya samemu innalillah wainnah ilaihir raji’una!”



Mata ne mak’ota suka shishshigo kowa fuskarsa d’auke da taysayi, ya ku bayi ne kamar gisansu Sauda. Kuma suna zaman mutunci da su suka zauna suna taya su jaje. Inna Sahura ta fara zuwa da danginsu, sananan Inna maryma. Sai sha biyun rana sauran suka fara zuwa, duk wanda ya zo kuma ba ya zama sai dai ai jaje a tafi hakan ya tunzura zuciyar, Saudat saboda ta tabbata da wani ne haka ya same shi da wuni Ummanta zata ce su je su yi.


Jajen kawai ake zuwa a yi ba tare da an miko ko sisi an ce ga shi a bawa Abba ba, duk da babbar asarar da ya tafka. Sai yammah Y.Hisham ya zo gidan afujajen ya shigo a lokacin yake fad’a musu ba ya gari sai sha biyu ya samu labari ya je Abuja.
Yayi musu jaje sosai, sannan ya dauki naira dubu dari (#100,000)ya ba Abbansu, ya ce kuma insha Allah zai mayar masa da kayan shagon.
Sosai akayi godiya har da Saudat, don bai tab’a burge ta kamar yau ba, ya kara k’ima da mutunci a idonta.

A nan yake sanar da su Y. Mahmud duk sanda ba su da karatu su dunga zuwa kamfaninsa, ba zaa rasa inda za a saka su ba, Sa’eed da Sa,ad kuwa ya ce su tsaya tare da Abba a shago.
Bai bar gidan su ba sai dare, yana tafiya kuwa suka dira faifan yabonsa tare da matuk’ar girmama k’ok’arinsa, Abba kuma yayi alk’awarin aura masa Sauda da son iyayensa ko babu. Don ya yaba da k’ok’arin sa matuk’a da gaske, tunda abin ya faru babu wanda ya d’auki ficika ya bashi daga danginsa duk da bai ba wanda bai sani ba, amma bai sani ba ko sai nan gaba.
Sauda ta shiga d’aki ta d’auki waya ta kira shi karo na farko a rayuwarta ,don kam yanzu ta aminta da shi kuma ruwa da iska babu mai hanata auransa. Bugu d’aya wayar ta yi Hisham ya d’auka cike da farin ciki yau Saudat ta kira shi. Cikin murmushi ya ce "first in life, yau Saudatuna ta kira ni da Kanta.”
Murmushi ta saki ta ce “Y. Hisham ya ka je gida?”
Shiru ya yi yana sauraren tattausar muryarta,ya saki ajiyar zuciya ya ce "Sweety, please! ba na son Y.Hisham d’in nan ki dinga kirana da Dear Hisham.”
Lumshe idonta ta yi ta ce 'wannan sunan ya fi k’arfin bakina yanzu.”
" Sai yaushe?” Ya cillo mata tambayar
Tsit ta yi
"Sweety,ba kya ji ne?”
Yace, “ok, fad’a min sai yaushe?”
Can k’asan makoshinta ta ce, “sai mun yi aure.”
Ai ji yayi tamkar ya nutse don tsananin taushin muryarta “Hello!” sai ya ji d’if, ta kashe gaba d’aya hakan ya tabbatar masa da kunya ta ji ya saki murmushi ya tura mata sako
"Ina son ki sweety"
Da kyar ya samu ya yi barci saboda tsananin soyayyar sauda. Hakan ya sa ya kudurce a ransa gobe zai samu mahaifinasa a yi wacce xa ayi, shi kam babu abinda zai Hana shi auren Saudatunsa.....


A dining room ya samu mahaifin nasa Yana zaune Yana cin abincin kala-kala wanda Hisham ya tabbatar sun fi ‘karfin cikinsu,A nutse ya gaishe shi shima cikin kulawa ya amsa wa Hisham, don kam yana ji da shi a cikin y’ay’ansa saboda dollars d’in da suke hannunsa.
“Hisham ya aka yi yau ba ka fita da wuri bane?”
Hisham yace, "Wallahi kuwa sai kuma ka ji abinda ya faru.”
Abbansa ya d’aga kai cike da rud’ani ya ce, “Na me fa?”Hisham ya ce , “Na gidan Abba Mustafa, wallahi Daddy na matuk’ar tausaya masa.”
Tsaf Alhaji ya gintse fuskarsa ya ce” Eeeh haka ne, Allah ya kyauta, ita rayuwa ai ta gaji haka, samu da rashi”
Hisham ya ce. “Haka ne." Bayan d’an shiru ya ci gaba “Daddy Dama nazo sanar maka wata magana tare d amincewar ka.”
Ya d’ago Yana kallon sa, “Ina jin ka Hisham”
"Daddy daman so nake a yi min izinin auren yar gidan Abba mustap ....”
Da sauri Alhaji Hamza ya d’ago har cokalin hannunsa Yana fad’uwa, cikin matuk’ar mamaki yake kallon sa, “Hisham ban ji me ka fad’a ba, ba tare da fargaba ba, Hisham ya ce “Izinin auren ‘yar gidan Abba mustapha.”

"kaiiii dakata!! Wane Mustafan kake nufi!!?
Hisham ya ce. "Abba mustapha k’aninka nake nufi”

Alhaji hamza ya girgiza kai had’e da cewa "Cab’ amma kuwa Hisham yau na tabbatar ba ka san ciwon kanka ba. ‘Yar Mai k’ashin tsiyar za ka aura?Wanda duk abinda ya tab’a ba ya albarka kowa ba yaso ya rab’e shi saboda ba shi da k’ashin arziki? To wallahi ba ka isa ba!! Ka sake ka rab’e shi komai naka sai ya tsiyace ban da abinka yanxu zamani ne da kowa ya sani Mai kud’i sai mai kudi, talaka sai talaka d’an uwansa zamani ne da auren soyayya a wajen masu kud’i ya zama tarihi sai na wanene Ubanki? Ina hankalinka yaje Hisham? Muna nan muna Neman maka aure gidan manyan mutane ka b’ige da neman d’iyar Mustafa toh ba zai yiwu ba wallahi, ka sake zance.”
Hisham ya lumshe idonsa yace, “Dan Allah Daddy ka duba batun nan, Abba mustapha fa jininka ne, wannan kuwa bare ne.”
"Kai rufe min baki yaron banza kawai. To akwai wani bare a wajen mai kud’i yanzu da ya wuce talaka ko uwarku d’aya ubanku d’aya da mutum,yanzu wa yake ta zuminci?Kawaii inda za ka huta zaka nema, shi ma Mustafan da ba ka da shi ba zai ce zai ba ka d’iyarsa ba. Kuma wallahi zan same shi sai ya san ya shigo gonata.”
Hisham ya d’ago da kyar ya ce “A’a Daddy ni ne na ce Ina sonta ba shi ya bani ba"
Cikin matuk’ar fushi Alhaji Hamza ya ce, “Tashi ka bani wuri ba na son maganar banza yanzu haka mustapha asiri ya yi maka, ni ban san yaushe kuka d’inke da shi har haka ba. Kowa yana gida sai kai kana lik’e masa, idan ya tsiyata ka kai ka sani, waye bai san k’ashin tsiya ne da Mustafa ba. A can danginsa uwarsa ya gado kashin tsiya, saboda haka ka fita idona, Kuma maganar aurenka zan dawo da ita nan da wata d’aya. Zan samu honourable muyi maganar, shashashan banza me aka yi akayi mustapha bare d’iyarsa gadon tsiya da talauci, garar arziki ba samunta za kayi ba idan ka auri y’arsa sai dai su kwashi nasu rabon a jikinka.”




Daidai lokacin hajiya laraba ta shigo falon tana fad’in “Ni Alhaji fad’an me kake ne ana jiyo ka fa tun daga can k’asa”Alhaji Hamza ya ja tsaki ya ce "To fad’an me zan yi Hajiya ban da ni da wannan shashashan d’an naki wanda arziki yake binsa shi kuma yana bin tsiya da gudu? Wai d’iyar Mustafa yake so.” Hajiyar ta zaro idanu tace "Me? A,a wallahi wasa yake Alhaji ka san Hisham da tsokana.”
Alhaji hamza ya ce. “Bilhakki da gaske yake gashi nan ki tambaye shi...”
Mommy laraba ta juyo ta karewa Hisham kallo ta ce "Hisham da gaske ne?”
Hisham ya d’aga kai “Haka ne Mummy"
Ta kuwa girgiza kai tace “To baka isa ba wallahi in dai ina raye ba ka isa ka aure taba shashanshan banza kuma na sake jinka ka je gidan ma sai na sassab’a maka, Allah ka rabamu da mugun ji da mugun gani auren yar gidan Mustafa ai tamkar siyan talauci ne da kud’inka.”




Jikar Nashe! Mai tak’ama da ikon Allah.


Zumuncin Zamani..

Na

Nazeefah Sabo Nashe.


(Typing: Fad’ima Sabi’u D’ankaka, ina godiya da k’ok’arin ki gareni jazakillahu bil jannatil firdausiya uwar gidan Isa Dankaka.)




Hisham shiru kawai yayi tare da tsananin mamakin iyayen nasa, tamkar dai Abba mustaphan shi ya d’orawa kansa talaucin. Allah alhakimu, Al’amarin kyamar talauci ya ta’azzara kwarai a zuciyar iyayensa Yana dago Kai ya ga wajen wayam sai shi kad’ai a falon.
Jikinsa a salub’e ya mik’e ya bar wajen, don zuciyar sa tayi nauyi sosai yana tunanin menene mafita kuma?



Kashegari duk da ba ya jin dad’i haka ya mik’e ya tafi gidan Abba mustapha, babu mutane ko kad’an sai dangin Umma da Inna sahura, bayan ya gaishe su waya ya yiwa Sauda ya ce Yana jiranta a waje.
Doguwar riga ce a jikinta, hakan yasa mayafi kawai ta nad’a ta nufi k’ofar gidan wajen Hisham, yana cikin mota ta bud’e ta shiga, alamar damuwa ta gani k’arara a Fuskarsa, hakan yasa ta gaishe shi had’e da fad’in “Y.Hisham, meke damunka?”
Murmushi ya dan yi yana sakin ajiyar zuciya ya ce “Babu abinda yake damuna Saudatuna illa tsananin soyayyar ki,Saudatuna please ki tayani addu’a mahaifina ya amince min na aure ki.”
D’if ji da ganin ta suka d’auke, jikinta a sanyaye ta dube shi ta ce “Y. Hisham na san za a rina shi ya sa tun farko abinda nake jiye maka tsoro kenan ka kasa fahimtata, na sani a danginmu mun fi kowa bak’in jini duk a dalilin talauci da Allah ya jarrabi mahaifinmu da shi, Y.Hisham dan Allah ka janye daga batun aurena”
Wani kallo ya wurga mata, ya dakatar da ita daga cigaba da magana “Saudatuna za ki iya hak’ura da ni? Ashe akwai abinda zai sa ki janye daga aurena? ki kalleni nan, duk rintsi duk wahala,ni babu abinda zai sa na janye daga zancen aurenki.Ina so ki san haka,kuma ki janye daga ranki duk rintsi duk wahala ba zan fasa auren ki ba, ban fara neman aurenki don na bari ba, zuciya da ruhi gaba d’aya muradinsu aurenki, ba ki san yarda nake son ki a cikin raina bane, da ba ki kawo min maganar na hak’ura da ke ba.” Shiru ta yi don kam ita ma yarda ta fad’a cikin soyayyar tsamo tsamo,ba ta jin zata iya rabuwa da shi, a hankali ta ce”Y.Hisham, ka yi addu’a”
Zuwa wani dan lokaci ya sallame ta, yaja mota ya yi gidansu.
Da safe ko da ya yi wanka kamar yadda ya saba karyawa a cikin gidan su, k’a’idarsa ce, ya shiga falon gidan Gaba d’aya iyayensa suna zauna har k’asa ya durk’usa ya gaishe su don kam Hisham yaro ne mai matuk’ar biyayya da sanin darajar iyaye.
Har zai mike Alhaji Hamza ya dakatar da shi ta hanyar cewa “Kai zo mana"
Hisham ya koma ya zauna
Daddy ya sha mur ya ce,”Kamar yadda na sanar dakai, munyi magana da honourable ya amince da dawo da bikin nan da wata d’aya, haka sai ka bada kud’i mummyn ka taje dubai ta had’o kayan lefe Muryarsa can k’asa kai daga ji ka san ba ya son auren, ya ce "Daddy kamar nawa zaa bayar?” Alhaji hamza yace “Ga tanan ka tambayeta, ita ta san kan harkar kayan mata, abu d’aya na sani aljihunka zai yi kuka sosai, don ‘yar gidan manya ce.” Hisham a zuciyasa ya ce

Please Login or Register in order to submit comment