Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaisheshi, Bana son sake ganin fuskarsa da ta rikid’e ta koma min tamkar ta bak’in kumurci. Bana marabtar duk wani zuri’a ko jinin danginmu musamman d’iyoyin gidan Baba Hamza da basa daraja da martaba iyaye na. Abin haushi da saka takaici su Yaya Khalil na ji suna ta murnar dawowar ta sa da rawar jiki da shi.
Alk’alamin Jikar Nashe


Zumuncin Zamani


Daga k’ungiyar Elegant online✍🏽✍🏽

Ku karanta kyauta..

3

Ina ji Umma na sake yi masa murnar kammala karatu lafiya. “Oh, Hisham tun da ka tafi sai yanzu ka waiwayo gida? Tun fa kana k’aramar sakandire.”

Ban ji amsar da ya bata ba, saboda muryarsa ta yi k’asa da yawa. Na ji dai Umma na fad’in “Masha Allah, sai aure kenan ko ka yi auren ne ma babu labari?”

Ji na yi ya ce, “Haba Umma, ya za’ayi na yi aure ba ku sani ba? Khalil ya yi aure ne,”
Umma ta saki dariya ta ce, “Ina fa, shi ko niyyar auren ai ina ji babu shi a zuciyar Yayan Sauda.” Kasancewar haka Umma take ce masa.
Ina jinsa ya tintsire da dariya mai d’an sauti kad’an ya ce “Umma ai shi aure lokacine da zarar lokacin sa ya yi ba sai ance ma ya yi ba. Ni kuwa da a gidan nan akwai wata y’ar bak’ar yarinya mai tsiwar tsiya tana ina ne? Ko an mata aure?”

Umma da su Khalil suka tuntsire da dariya kafin Umma ta ce “Sauda kenan ai kowa ya santa da wannan tsiwar da rawar kai tun tana yarinya, ba’a yi mata aure ba, tana uwar d’aka tana jinka.”

Ina cikin d’akin na ji tamkar na fita in k’unduma masa zagi. Da gaske naji haushin halin da ya jingina ni da shi. Na runtse ido kin Umma na k’walla min kira na tabbata cewa za’a yi na fito na gaisheshi. Murya a ciki-ciki na amsa.

Daga bakin k’ofa na tsaya fuskata a had’e rik’e da k’ugu na ce “Ga ni Umma.” Da sauri na ga ya d’ago kai ya zuba min dara-daran idanunsa.

Umma fuskarta a had’e alamar ba wasa ta ce “Ba kiga Yayanki Hisham ba ne?” Ta fad’a tana zabga min harara da take nuni da gargad’inta gareni. Hakan ya sa a dole na kawar da kai na kuma gaisheshi murya a cunkushe.

Murmushi ya saki yana amsa gaisuwata. Ya kalli Umma ya ce “Lallai girman y’a mace ba wuya tamkar ba ita na tafi na bari tana kukan wanka, wasan k’asa da shan majina ba.” Da sauri na saki labulan na koma d’aki don ina ji a raina tabbas na cigaba da tsayuwa zan iya k’unduma masa zagi.

“Amma Umma ya aka yi na ga kun dawo nan gidan? Bayan ba a nan na tafi na barku ba? Yau fa har tsohon gidan ku na je na can k’asan layinmu sai aka ce min yanzu ba nan ne gidan ku ba, na zata ma Wani cigaba ne ya samu Malam ya sake Gina muku wani gidan, sai da na dawo na tambayi Mami ta ce min bata san inda kuka koma ba, Yanzu ma Idi driver ne ya rako ni ya koma. Umma wai me ke faruwa ne?” Ya fad’a yana sake k’arewa gidan kallo da alamar yana mamakin yarda muka tsinci kan mu a halin rayuwa irin wannan da muke ciki yanzu.

Umma murmushi kawai ta yi ta ce “Hisham Kenan, shi lamarin ubangiji da kake gani izzar sa da mulkinsa duk ya fi gaban haka, yanzu idan ya ga dama duk sai ya shafe babinmu, ba ma dukiya ba, duk ikonsa ne, mun gode masa ma da ya ba mu lafiya da wadatar zuci, abubuwan da suka yi k’aranci kenan a wajen mutane, bawa ba shi da ikon canja duk wata k’addara da jalla ya hukunto masa Alhamdulillah ala kulli halin.” Daga haka ta kawar da maganar ta hanyar tambayarsa wai yaushe za mu sha biki ne Hisham, tunda dai da rai da lafiya da wadata ya kamata ka angwance haka.”

Ya sunkuyar da kansa yana shafa k’eyarsa ina kallonsa ta cikin labilai ya ce “Muna nan muna dubawa Umma, kin san y’an matan yanzu ne sai a hankali Umma su ba k’warya ba balle ka k’wank’wasa ka ji ta gari.” Umma ta ce “Haka ne kam, to Allah yasa a yi gam da katar da ta garin.” Tsaki nasa a raina na ce “Shegen iyayin tsiya, sai kace shi na garin ne.”

Ina jiyo sallamarsa yana cewa Yaya Khalil Sai yaushe?” Ya ce “Zan shigo gidan naku ai, Insha Allah ranar da ba lectures.”

“Kada ka ce min har yanzu baka gama makaranta ba?” Y.Khalil ya d’aga kai cikin son tabbatar masa da haka ne. “Ka san abubuwan ne sai a hankali ina HND 2.” Bai sake cewa komai ba ya juya had’e da furta Allah ya taimaka” suka fice tare da Yaya Khalil.

Umma ce ta d’aga labilan d’aki na na ga ta jijjiga kai kafin ta ce “Y’ar banza mai taurin kan tsiya, zuciya kamar ta mutanen farko, sam babu lislama a zuciyarki, wallahi idan ba ki jingine wannan bak’in halin naki ba tsaf zan jingine lamarinki a gefe, ko kuma na samu wani a dangin na ba shi auren ki, sai na ga ya za kiyi shashashar banza mutuniyar kawai.”

Da sauri na zaro ido na ce “Wallahi kuwa Umma da na kashe kai na...”

“Kashe kanki? Kin san kuwa furucin da bakinki yake furtawa? Me kika d’au duniya ne? To Allah ya kyauta ya yi mana maganin masifa lamarinki kuma sai addu’a tabbas.” Daga haka ta saki labilan ta juya ta fice daga d’akin tana sake jinjina kai. Na tabbata mamakin furucina take ni kuwa Iya zallar abinda yake raina na fad’a, Gaskiyar kenan, saboda yarda nake sake jin tsanar dangina a zuciyata. Kwatankwacin k’iyayyar rai da mutuwa. Me zan yi da mutanen da basa kallon iyayena da k’ima da martaba.



*************
Ba kowa a gidan ni kad’ai ce, hakan ya bani damar sakewa Abuna, ina ta wak’e-wak’ena da raye-raye na, na ware wak’a a radio mai Bluetooth, Yau kam da farin ciki na tashi zuciyata fresh na ke jinta tamkar ta yaran da ba su wuce shekara uku a duniya ba, saboda yanayin yarda nake tsalle-tsalle na. Har igiya na samu ina y’ar tsalle bayan na gama gyaran gidan tas na d’ora abincin dare tuwon shinkafa ne miyar zogale. Kasancewar gawayi ne ba ci yake sosai ba, ya sa nake ta tsallen y’ar igiya. Sam ban san da mutum a tsaye a bakin k’ofa ba, ina juyowa na yi arba da shi yayi holding hannayensa a k’irji. Sanye yake cikin farar shadda gezner da ta sha aikin brown d’in zare. Da sauri na had’e rai don sam ban san dalilin zaryar da yake yi gidanmu ba. Ba ya kwana biyu bai zo ba. To yau dai mutanen gidan basa nan, na ga da wanda zai yi hirar tasa. Na raya hakan a zuciyata.

Ban sake kallonsa Ba an burma kaina cikin d’akin. Ina jin takun takalmansa a tsakar gida ban yi aune ba na ga ya d’aga labulen d’akina. Ya kuma zuba min tsumammun idanunsa da suke lumshewa da kansu ko kuma iyayinsa ne oho. Don na lura hakan kamar ya zame masa al’ada, ko naturally haka yake oho masa.

“Ke, ya ma sunanki? Mutanen gidan ba Sa nan ne?”

Duban cikin tsakiyar ido na yi masa jin ya ce bai san ma sunana ba. Na lura k’warai mutumin d’an rainin hankali ne. Na gyara zamana sosai, na kuma sake bud’e littafina ina karantawa ba tare da na sake masa magana ba.

“Ba kya ji ne?” Wannan karan muryarsa a kaurare ya yi magana. Na lura kamar ma a kufule yake. Na d’an tab’e bakina cike da tsiwa na ce “Kai baka lura ba?”

Sake harzuk’a ya yi ya ce. “Idan na luran ai Ba Zan tambayeki ba, ke me yasa ba ki da kunya ne? Wallahi za ki gane kurenki idan ki ka k’ure malejin hak’urina.” Ya fad’a yana murza yatsun hannunsa. Sannan ya fice.

A harzuk’en nima na ce “Babu abinda kurarinka zai yi min.” Na tabbata kuma ya ji ni ban damu Ba sam don burina ya fita sabgata.


Ko da Umma ta dawo ban sanar da ita da zuwansa ba don na ma manta da babinsa.


Bai sake dawowa gidanmu ba sai bayan kwana biyu. Ranar ma ba kowa ni kad’aice a gidan. Ummana haihuwa aka yi mata take suntirin zuwa gidan mai haihuwar, k’anwarta ce ta haihu. Ina wanke-wanke ya shigo, sam ba ni da juriyar aiki duk da aikin gidan namu ba wani yawa bane da shi amma yana gajiyar da ni, kasancewata mace mai son jiki.

D’akin Umma ciki da rumfa ne, su ma ba wasu manya ba bane, sai fallen d’aki d’aya da ya zama mallakina da kichin da band’aki a can gefen tsakar gidanmu. Sai k’aramin d’akin su Yaya Khalil da yake zauren gidan. Sai soro d’aya jal shima k’arami.
Tsakargidan malale yake da fasassun tile wannan dalilin yasa kullum sai an wankeshi. Sabida Umma na mace mai matuk’ar tsafta.

Riga ce a jikina brown colour, sai bak’in siket gashina kuwa a ranar raba shi biyi na yi na tufke shi gefe da gefe, kamar wata yarinya ya kuwa sauka a saman kafad’una kasancewata mai yalwar gashi ina kuma matuk’ar son gyara shi.


K’amshin mayataccen turarensa da ya bad’e tsakargidanmu ne ya sanar da ni zuwansa. Don haka na had’e rai na juya da sauri shi d’in kuwa na gani a tsaye yana k’are min kallo sama da k’asa. Haushin kaina ya kamani da kuma yanayin shigar da take jikina. Ya yi kyau Ba kad’an ba don shigar bak’ak’en kaya ya yi na english wears da suka sake haske masa farar fatar jikinsa.

Daga kallo d’aya da na masa na had’e rai, shi d’in ma bai Yi min magana ba can gefen tsakar gidan ya nemi waje ya zauna. Tsawon mintuna yana daddanna wayarsa a hannunsa ba tare da ya yi min magana ba. Sai can ya wurgo min tambaya “Ke Yau ma Umma bata nan ne?” Kamar da iska yake magana haka na sake d’auke kai na zumb’ura baki kawai na shige d’akin girki.


A k’ufule na ga ya taso ya tsaya a k’ofar kitchen d’in. Shi d’inma kallon banzan ya wurga min kafin ya ciji bakinsa ya ce “Ke wai me ki ka d’au duniya ne da kike wulak’anta mutane? Kin san kuwa illar wulak’anta d’an Adam?

Na sake watso masa manyan Idanuna kamar na ce masa “A je a tambayi tsoho wato mahaifinsa, sai dai na ja bakina na had’iye maganar ba tare da ba bashi amsa ba, na cigaba da iza wutar gawayi na. Daga baya ma sai na mik’e na rab’a ta gefensa na shige uwar d’aka.

Ina jin takun takalminsa alamar ya fita daga gidan na saki tsaki a bayyane na ce “Ka ji min kinibibi uban wa za ka yi wa wa’azi, aje a yiwa magabata su suka fi cancanta ba ni ba.”

Sallamar yara ce ta sa da sauri na mik’e na d’aga labulen ina fad’in wanene nan? Yara na gani d’auke da kayan abinci suna jibgewa a tsakar gidanmu. “Kai ku tsaya wannan kayan daga ina?” Na fad’a cike da mamaki don Abincin yau ma auno shi mu kayi a kantin iliya.

Ba su ba ni amsa ba na jiyo sallamrsa ya shigo hakan yasa na ja bakina na tsuke don na fahimci daga inda kayan suke.

Umarni ya bawa yaran akan su sauke kayayyakin a can gefe daga haka ya juya ya fice. Ina jiyo tashin motarsa alamar ya tafi. Na bi kayan da kallo don kaya ne aka jibge masu yawan gaske kamar za mu bud’e shago. Komai biyar taliya shinkafa macaroni kuskus semovita, golden vita, indomie. Sai su maggi da dangin kayan shayi rankatakaf. Har da sabulu da omo. Na tab’e baki jiki a sanyaye na shige d’aki. Tabbas na ji kunyar rashin mutuncin da na gama yi masa shi kuma ya bi iyayena da alheri.


Jikar Nashe taku ce✍🏽✍🏽


❤️❤️❤️❤️❤️🙏


Zumuncin Zamani

Na Nazeefah Nashe

08033748387


Page 4

Adaidai lokacin umma tayi sallama, ta shigo tadawo daga unguwar. ji na yi tana "wannan kayan fa daga ina?” Na fito daga d’akin ina bin umma da kallo.Ita ma ni din take kallo, tana jiran karin bayani. “Ba tambayar ki nake ba?”Na d’an tab’e baki na ce “wannan mutumin ne da yake zuwa ya kawo.Ta sake bina da kallo, "Waye wannan mutumin?” ‘Dan jim na yi ina tunani,sannan na ce,"Mtsw Hisham ko hashim?”Umma ta girgixa kai had’e da murmushi ta ce "Saudat kenan hashim din ne kike kokwanton sunan sa? Yaro d’an albarka kenan, wannan yaro sam bai yi halin uwarsa da ubansa ba Wannan kayan haka jimgim? Allah ya yi masa albarka”
Tsit nayi mata ta dube ni,kafin tace "Yana ganki wani sukuku dake?”
Na gyara tsayuwar kafin nace" “Bakomai”
Ita din ma tabe baki tayi tace,"Allah ya kyauta ta shige dakinta.”
Koda malam din yadawo ta nuna masa kayan,murmushi yayi yace"Allah kenan mai fitar da rayayye daga cikin matacce, shi kuma Hisham sam baiyi halin iyayensa ba.to Allah ya saka masa da alkairi,yakuma sa shine silar shiryiwar iyayensa”umma “Amin _Amin”kawai take fada
Xuwa can abba yace gobe ma ku shirya ke da sauda kuje gidan yaya falmata ku dubata,an ce tayi fama da jinya duk da dai ni ma ban sami kallon arxiki ba. Amma ya wajaba ka sauke hakkin musulunci a kanka".
Umma tace,"haka ne kam"
Ina daga cikin daki ji na yi kamar na xunduma ihu,gidan inna falmata? Na shiga uku! matar da ta tsane mu muguwar tsana,ba ta mana kallan arziki, ita ce za mu je gidanta? Gaskiya gwanda na kwanta ciwon karya akan naje gdn inna Falmata.


Tun dare na fara nuku - nuku na cutar karya. Umma na hankalce da ni ba tace dani ‘’kala ba.
Koda safe kallo na kawai ta yi ina daga kwance tace," baki tashi bane?ko ciwo ne?”
Na daga kaina.
Fita tayi daga dakin zuwa mintuna ta dawo da cup din ruwa da paracetamol a hannunta ,ta miko min." Tashi ki sha maxa ki shirya mu je dubo Innarki."
Na langwabe murya na ce ."Umma ba zan iya xuwa ba
Dariya ta yi ta ce" Ai kuwan xuwa ya xama dole yarinya,ina kula fa da take - takenki tun jiya da Abbanki ya yi maganar xuwa gidan Innarki kika langwabe ki ka fara cutar k’arya. To duk wani lagonki na gane sarai kuma xuwa dubiya ko da jan ciki sai kinje."
Ai ban san lokacin da na d’ora hannu a ka na runtuma ihu ba. Umma kuwa ta doke bakina ta ce "Wallahi,kina tara min mutane ranki xaiyi mashahurin b’aci."
Don dole na ja baki na yi tsit.Sai hawayen bakin ciki da yake malale akan k’uncina.
Ban wani shirya ba da kayan jikina na mike na xura xumbulelen hijabi, da sauri na fita Jin umma na zabga min kira. A tsaye take fuskarta a hade ta nuna min hanyar zaure, na zira takalmina na ja k’afata muka fara tafiya
Ko a mota ban yi wa kowa magana ba, har muka Isa kofar makeken gidan mai kama da gari guda.k’ayatuwarsa ma fad’a b’ata baki ne. Mai adaidaita sahu yayi parking, umma ta fito ta biya shi kud’insa,sannan muka nufi kofar shiga gidan.
Sojan da yake gidan ya dube mu sama da kasa ya watsar, to ba dole ba ya gan mu a adaidaita sahu ba a irin manyan motocin da suka saba shiga gidan ba.
"Malamai daga ina? ba fa yau bane Alhaji yake raba sadakar,sai ranar jumaa,
Fuskata na hade ita kuwa umma murmushi tayi ta ce “Bawan Allah matar gidan mukaxo dubawa”
Ya sake kallon ta a wulakance yace " matar gidan wacce daga cikin"?
Da sauri umma tace , " hajiya falmata. Ni matar kaninta ce."
Ba tare da ya yi magana ba ya wangale kofar, yana fadin “Haba malama ki ce dai kawai kin zo maula amma ta ina kika yi kama da matar k’anin Hajiya k’annen Hajiya fa duk na sansu
kuma ba talaka a cikinsu, Matansu kuwa a galla -galla motoci suke zuwa”
Umma tace"Haka ne, mun gode da alfarmar shiga da aka bar mu mukayi "
Hakimar a hakince a falo muka sameta. Tana kishingide tana danna remote ga masu yi mata hidima nan sun kewaye ta suna mata tausa. Wasu kuma suna yanka mata kayan marmari tana sanyawa abaki tana taunawa cike da nishadi tana lumshe Ido.

Ko sallamar da mukai ba ita ta amsa ba sai daya daga cikin barorintace ta amsa mana. Umma ta samu gefe ta durkusa ta gaisheta ta,da kyar take amsawa.ni kuwa daga tsaye fuskata a matukar had’e
Hajiyan bude baki tayi tana min kallon mamaki."ke tsagera wani irin iskanci ne yasa ki ka yi kikam ba kya gaisuwa?”
Fuskata a hade na russuna na gaidata.
Ba ta amsa ba sai sake tunxura datayi tana zabga masifa."ke wallahi ki kiyayeni,don ana yawan fadar rashin tarbiyyar ki, To ni ba zan d’auka ba. Uban waye yace kixo gidana? Me zuwan na ku zai k’areni da shi?ban da ya rageni? Don ko ba komai idan za ku tafi tilas na ba ku kudin mota, don nasan k’ila bashi ma kuka ci kuka taho shegiya ke ba y’ar kowa ba sai fadin ran tsiya. To ki kiyayeni ehe don ni ba kanwar lasa bace kin yi na farko kuma wannan ya zama na karshe” Umma ce ta shiga bata hakuri, ta mik’e tana fadin kin bata hak’uri ko sai nayi kasa-kasa da ke?”
Murya shake na ce ."Allah yabaki hakuri”
Bata amsa ba ta shige daki tana cewa masu aikin ta "ke kawo musu pure water,ki kuma basu #500 idan xasu tafi”
Mai aikin ta ce “To”
Zata mik’e umma tace.”Yarinya barshi kinji tafiya ma za mu yi kuma wallahi muna da kudin mota mungode Allah ya saka da alkhairi."
Mai aikin ta tab’a baki ta ce “kun yi wa kanku.”

Cikin jan k’afa ni da Umma muka fice daga gidan, muna barin gate d’in gidan umma ta dubeni cike da masifa ta ce “To ishasshiya mai bak’ar zuciya ,saiki tafi naki wuri do ni ba zan jera dake ba don kece uwar yanzu, Ni na zama y’ar tunda ke ba za’a fad’a miki ki ji ba.Kuma wallahi sai nasa yayanki ya yi miki dukan tsiya shashashar banza da wofi kawai.

Kuka na saka ina ba ta hakuri don na san dukan yayyanmu ba bu sauk’i, amma umma tayi burus dani haka muka dinga shan tafiya a k’asa don sam layin babu ko adaidaita sahu, kasancewar layin shahararrun masu kud’ine.
Wata bakar motace ta dinga reverse (baya) tana yi mana horn alama anaso mu tsaya, Amma babu wanda ya tsaya a cikinmu ganin haka mai motar ya yi parking ya fito k’amshin turarensa shi ya sanar da ni shine. Ai kuwan ina juyawa nayi arba da shi.
Cikin sakin fuska umma take amsa gaisuwar da ya russuna yake mata. Ni kuwa da yake ina son mu shirya da umma da Dan hanzarina na ce "Ya Hisham ina wuni?"
Ya juyo yana min kallon mamaki, bai ce komai ba baya ga amsa gaisuwata da ya yi a can k’asan makoshinsa ya mayar da hankalinsa akan umma." Umma daga unguwa kuke ne?”
Umma ta daga kai tace"Wallahi daga gidan innarku falmata muke,munje duba ta an ce ta Dan kwanta cuta kwanaki."
Hisham ya gyada Kai hade da fadin,"Exactly " nima chan xanje amma umma kun wahalar da kanku don nan unguwar ba a samun mota sai dai private car da kin sani kin gayamin sainaxo na kai ku.”
Umma tace"Hisham kenan menene abin wahalar dakai a sadar da zumunci?,banda samun dinbin lada"Hisham ya gyad’a kai yace haka ne umma ga mutum mai hasashe da tsinkayen tunani mai kyau irin na ki kenan,ammn don Allah ki yi min uxuri na fara biyawa na duba inna falmata"
Umma tace"bakomai Hisham daka bar mu mun karasa kada mu dora maka wahalar”
Hisham din da sauri ya ce,"Haba, umma daina fadar hka wace wahala ce a aikin iyaye banda d’imbun samun lada?”
Ni dai ina tsaye a gefe tamkar an dasani a wurin.Hisham ya budewa umma mota gidan baya yana cewa "Bismillah umma tashiga motar, sannan ya juya ya dubeni "Malama shiga mu tafi" ya bude min gidan gaba.
Fuskata ba yabo ba fallasa na shiga na zauna, wani sanyi da kamshi dadi ya shiga bugata. Hisham ya kunna karatun Alkur’ani cikin suratul bakara, kira'ar Sudais mu ka sake komawa gidan inna falmata.


Ai da sauri maigadin ya wangame mana gate yana kai wa Hisham gaisuwa.

Hisham ya zura hannu aljihu yafito da hannu a dunk’ule ba wanda xai ce ga abinda yake Cikin hannun irin kyautar da annabi yakeso hannun hagu bai san abinda dama ta bayar ba. Ya mannawa mai gadin
Koda ya tsaya da motar sake russunar da kai yayi yace"dan Allah umma ki yi hak’uri yanxu zan fito idan ya huce ynxu ba zan samu damar zuwa ba don gaskiya bani da lokaci, amma ki bani minti biyar kacal"
Umma da sauri ta ce “Haba Hisham wallahi bakomai kaje ka xauna ku gaisa a nutse mu ba bakin xafi bane.” fita yyi Yana cewa “Nagode umma”
Na bishi da kallo na ce “ NAGARI A BAYA MUGU.”
Umma ta ta watso min harara tace “kinga dan arziki kenan irin Al barka, ke ynxu don Allah wannan bai zame miki ishara ba? Ai ba duka aka taru aka zama daya ba.”
Gum nayi da bakina don kam bani da bakin magana.
Mintuna biyar d’in daya fada kuwa cif ya fito har kofa Inna falmata ta rakoshi don ina hango ta ta cikin duhun gilas din motar, sai dai ita bai xama lallai ta gan ni ba. Da sauri har da sassarfa ya k’araso daidai lokacin da barorin hajiya suka biyo shi d’aukeshi da wasu manyan kwanuka masu siffar kwalba. Kusa da umma suka ajiye ina kallon su suna mana kallon mamaki.
Hisham yaja mota muka tafi
Koda muka isa gida,shi ma fita yayi daga motar ya d’au flask din nan biyu na taimaka na dauko masa biyun, don dole na dauka ba don komai ba, Saboda daga gidan falmata ya zo.
A tsakar gida yace na ajiye na samu plate na zuba masa kad’an tamkar na kwarara ihu haka na ji, don tilas dai na nufi kitchen. Umma ta ce, “ki d’auko masa a fararen plastic din nan"
"Tom" nace na burma kitchen.
Kawo masa na ya ce,"Bubbud’e ki zuba min, rigimar Inna ce daga ta yi min tayin abinci nace sauri na ke ba zan samu ci ba, duk da ina jin yunwa, shine ta biyo ni da wannan tulin abincin.”
Umma murmushi ta yi kawai daga gani kasan na yak’e ne ta ce"Ai ta taimaka ka kuwa baka ce rigimarta ba.”
Na taso ba don na so ba a’ a sai dan ganin idon umma na bubbud’e flask d’in na farko farfesun dakwalen kaji ne,na biyu kifi ne,irin manyan kifin nan da ake kira ragon ruwa, sai na uku shikuma sinasir ne da waina masa, na hudu kuma hadaddiyar basmati rice ce
Abincin kam ya hadu,na fara xuba masa.
“Kad’an _kad’an, za ki zuba”ya ce da ni cikin wata salon murya".


Zumuncin Zamani.

Na

Nazeefah Sabo Nashe

Littafin kyauta ne

📄 5
(Sannu da jimirin typing Fateemah Sabi’u Dankaka. Ina godiya k’warai da gaske, ubangiji ya fi ni yabawa.)





Kad’an- kad’an d’in na zuba masa, na mik’e na bar wajen, d’akina ma na shige kwanciyata nayi sosai flat, ina tunanin irin wula’kancin da muka sha wai k’iri-k’iri da d’an uwan ka sai ka na da shi sannan yake kallanka da daraja da k’ima. Sosai zuciyata take bugawa, yanzu dai dubi mu da muka je muka sha uwar rana, wai da pure water aka sadamu. Shikuwa da yaje a cikin mota mai AC an sada shi da garar abinci da na tabbatar ba zai iya cinye wa ba, duk a dalilin shi mai kudine zai rama abinda ake yi masa ko ma fiye da haka. Mhmn! Duniya kenan makaranta ce!

Ina ji da zai tafi umma tana cewa bari ta kira ni na kai masa ragowar abincin mota. Ya ce “Haba Umma me Zan yi da shi? yau dai kin huta da yiwa gwaurayen gidan girki.”
Umma dariya tayi tana sake zuba masa godiya.
D’aga labulen d’akina ta yi ta ce “Ke sai ki zo ki d’ebi abincin kici don nasan kina jin yunwa.
Da sauri na girgiza kai ta ce, “ke kika jiyo, wallahi Sauda ina raba ki da wannan shegiyar bak’ar zuciyar, ba inda Zata Kai ki don kuwa ynzu

Please Login or Register in order to submit comment