Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

Zumuncin Zamani

Na Nazeefah Sabo Nashe


(Ku karanta kyauta. Zai dinga zuwa muku a group d’in Sabon littafina Ya Abin Yake? Riba biyu kenan! Ku biya kud’insa ku karanta Kyauta.)

08033748387

A sunkuye kaina yake a tsakar gida, ina d’auraye kwanuka. Da sauri nake tayi don na san muddin Ummata ta dawo ban gama wanke-wanken nan ba tabbas kashi na ya bushe. Ai kuwa sallamarta na ji hakan ya sa ni saurin janyo ragowar kwanukan.


Umma dake tsaye a bakin k’ofa ta rafka salati “Sauda me zan gani haka? Yanzu da tun safe da na fita ba ki k’arasa wanke-wanken nan ba har yamma sakaliya? Anya Sauda ba zaki nutsu ki yi hankali ba, duk da gama secondary School da kika yi?”

Muryata cikin shagwab’a na ce “Umma wallahi wuni nayi kaina na ciwo.”

Ta zabgo min harara ta ce “Haka kika iya, ba ki da zance sai na cuta, shegen son jiki kamar mage, wallahi ki kiyayeni.” Ta bankad’a labule ta shiga cikin d’akinta.

Ni ko na saki ajiyar zuciya. A zuciya ta na ce “Umma kenan.”


A daidai lokacin wani yaro ya kwad’a sallama, na amsa masa ina nazarin inda na san fuskar yaron. Sai can na tuno d’an maigadin gidan Baba Hamza ne haka yasa na had’a rai na kuma bi shi da harara, don ko magen gidan na ga ni wallahi zan harareta. Na tsani ahalin gidan gaba d’aya. Wannan tabbas haka ya ke.

“Ina wuni?” Naji ya ce dani.

Ko kallon sa ban yi ba balle na amsa masa. Umma ce ta fito daga d’aki tana tamabayar “Waye mai sallamar ne?”
Da sauri yaron ya amsa, ko don ya fuskanci ni d’in ba zan amsa ba ne oho! Ya gaishe da Umma sannan ya mik’o mata chewing gum guda uku. Ta ce “ Na menene?” Ya gyara zamansa, sannan ya ce “Wai na sunan munirat ne gobe. kuma wai ta ce don Allah ki zo da wuri akwai aiki a can gidan.”

Umma ta amsa ba tare da wata damuwa ba. Ni kuwa zunduma ashar na yi na ce, “Gidan uban wa za ta zo? Saboda sun mayar da ke jakarsu, babu mai nemanki sai irin haka ta taso, saboda sun san za ki je ki wahalar da jikinki a wajen yi musu bauta da aikin banza aikin wofi.......

Wani kallo Umma ta wurga min ta kuma cillo min wani mafici cikin b’acin rai ta girgiza kai, ta kalli yaron da ya yi sugud’i yana yi min kallon mamaki da alama tijarata kawai ya ke ta’ajjabi. Ta ce “Kai yaro, ya sunanka?” Ya ce “Najibu”
“Yauwa Najibullahi, maza kaje ka ce Allah ya raya, sai mun zo insha Allah.” Ya mik’e ta mik’a masa Naira Ashirin, “Ungo wannan ka sha alawa kayi maza ka wuce gida.”

Ai yana karb’a na fisge cikin tsawa na ce “Wannan matsiyacin cingam d’in da suka kawo shine zaki ba shi har Naira Ashirin?”
Wannan karan cikin jin haushi Umma ta zabga min dundu a gadon baya na, tana salati ta ce “Sauda ina raba ki da wannan bak’in halin ba kya ji ko? Kin ba shi ko sai na mare ki shashashar yarinya har abada ana gaya miki amma kan ki ba ya d’auka? Wanda ka bayar har abada shine naka, zaki ba shi ko sai na mangareki?”

Fuskata a d’aure cike da k’unk’uni na mik’a masa Ashirin d’in idanuna har suna tara ruwan k’walla.

Shi kuwa ya karb’a ina kallon fuskarsa yana min dariyar mugunta. Hararar da na zabga masa ce tasa ya k’unshe dariyar da alama mamakin masifata ya ke.

Yana fita kuwa Umma ta hau kaina da masifa da bala’i tana cewa “y’ar banzar yarinya mai bak’in hali. So kike tilas sai kin yanke zumuncinmu da mutanen nan tamkar yarda suka yi, to bara na sanar da ke, ke ma kun zama d’aya da su. Ina ruwanki idan ma wahalar na musu, na yi d’in jikin ki ko nawa? Shashashar banza. Kuma ki sani, ki kwana da shirinki ke ma tilas sai kinje sunan tabbas! Sai dai ki kashe kanki don haushi.., shashashar yarinya mai d’abi’ar mutanen banza, duk mai yanke zumunci ai mutumin banza ne..”

Wai! Ai zuciyata tamkar ta fashe don tsananin zafi. Ba fad’an bane ya b’ata min rai sai cewa da ta yi ni ma sai na je gidan sunan. Ni ko da zuwa na wani sha’ani na danginmu wallahi gwara ta kwana tana yi min fad’a. Me za’a yi da danginmu Ko Dangin masifa da jaraba.


Har dare ina ta rok’on Umma a kan ta kyaleni da batun gidan sunan nan, amma Umma ta yi burus da ni. Kuma fuskarta babu alamun sassauci don ta d’inke tsaf ta had’e rai kamar hadarin kaji. Hakan yasa ko da na kwanta barci da batun na kwanta na fara tunanin su wanene Dangin mu?



***********

Alhaji Usman mai shadda shine sunan kakana da ya haifi ubana, mai kud’i ne a yadda tarihi ya nuna. An ce yana daga cikin k’irgaggun masu kud’in zamanin da.
Matansa uku da y’ay’a goma sha uku. A wancan lokacin shi kad’ai ne mutumin da aka san yake shigo da shadda daga waje.

Matarsa ta farko ita ce Hajiya tana da y’ay’a biyar biyu mata uku maza. Inna falmata, Inna Shukra, sai Baffa Hamza, Baffa Lawal, da Baffa Shu’aibu.

Matarsa ta biyu ita ce H.Saudatu. Ita ta haifi Babana, Malam Mustafa da k’annensa mata biyu. Inna Sabuwa, da Inna Mariya. Sai Hajiya Amarya, ita kuma y’ay’anta biyar, Baffa Amadu, Baffa Sa’idu, Baffa Umar, Baffa Nura da Baffa Iliyasu.

Wad’annan su ne zuriyar Alhaji Usman Mai shadda kakana, kafin mutuwar mahaifinsu, sam babu y’an ubanci a tattare da su, amma bayan mutuwarsa aka raba gado, sai zumuncinmu gaba d’aya ya koma ZUMUNCIN ZAMANI da wanda yake da shi ake yi don ni mahaifina a gefe aka saka shi sanadiyyar karayar arziki da ta samu mahaifinmu. Don kafin hakan ta sameshi suna zumuncin da shi sosai, tunda babu abinda zai nema a hannunsu. A lokutan baya shi ne, ya wahalta musu har da d’iyoyinsu don sam shi mutum ne ba mai raba d’aya biyu ba, ba ya y’an ubanci kuma sam abin hannunsa bai rufe masa ido ba.Koda yaushe hannunsa a bud’e yake, yana mi’kawa akwai kyauta atare dashi, sam bai zama igiyar giginya ba, kamar yadda wasu masu dashi d’in su ke yi.
Bayan anraba gadone karayar arzik’i ta same shi, ‘yan fashi suka yi masa tatas a hanyarsu ta tafiya kwatano wajen saro kaya, a zamanin baya mutane basu waye da yin transfer d’in kud’i ba idan zasuyi tafiya. shikkenan silar rukurkushewar arzik’in kenan da kad’an-kad’an komai yaja baya yana kwasar kadararsa yana sayarwa, yana jan jari amma rabon samun nasa ya k’are babu mamaki iya arzikin da ubangiji ya ‘kadarto masa kenan.

Tun muna private school(makarantar kud’i) har hakan ya zo ya gagareshi, sai da mu ka yi zaman shekara guda a gida, sannan ganin babu yadda zaiyi ya mayar damu makarantar gwamnati, duk fa ga ‘yan’uwansa nan sunxama gawurtattun masu kud’i don kam suna rik’e da manya -manyan kujerun gwamnati, amma sukayi burus damu, yakuwa za’ayi na manta?
Manyan makarantu suke saka ‘ya’yansu, wasu har ‘kasashen waje suka fitar dasu, mukuwa dagamu har yayyena ta gwamnatin ma wani lokaci nema take ta fi ‘karfinmu. Ta ya ya Umma take zaton zan manta da wannan bak’ar rayuwar da muka shiga?
Zamanin baya, bana fatan ko mak’iyina ya fuskanci irin halin da muka shiga na babu da Ta yi mana dabaibayi. sau tari muna wuni ba muci abinci ba, ko kuma garin kwakwi yazama abincinmu wuni guda tamkar ‘yan bursina. Wani lokacin garinma ko ‘kasa ko sama nemansa muke ruwa a jallo duk da a wancan lokacin store d’in ‘yan’uwana cike yake da kayan abinci. Yaushe ni sauda zan manta? Kada allah ya maimaita mana don wani abun ba shi fad’uwa.
Amma alhamdulillah, don kuwa Allah ya bawa mahaifina zafin nema da jajirtacciyar zuciya mai tsananin juriya,tak’awa da tawakkali. sam baya girgiza, duka lamarinsa yakan mik’ashi ga Allah, ba lallai ma Ka fuskanci halin da yake ciki ba idan ba ya fad’a maka ba, kai ko ya fad’a bai zama lallai a yarda ba. dalili, za ka ganshi tas, fuskarsa cike take da annurin k’aunar ubangiji.
Komai ya fara lafawa bayan mahaifinmu ya fara ‘yan buga bugar sa, ya kuma samu ya bud’e shagon siyar da kayan abinci anan k’asan layin mu. A yanxu kam babu abinda zamu ce sai godiyar ubangiji. Alhamdulillah.
Sai dai duk da haka bawai anayi damu a dangibane, a’a, ina! Ai karanmu bai kai tsaiko ba su danginmu ba sa zumunci da kowa sai mai naira. Ba sa alheri ga kowa sai wanda suka san zai ninka musu abinda suka yi masa. Haka yanzu rayuwa takoma zukatan al’umma sun mutu murus ba a kyauta don Allah sai na san zaki iya biya na.
Ga misali, a danginmu suna yin abin nan da hausawa suke cewa, dai-dai ruwa dai-dai tsaki Idan talaka na biki dari biyar, shima ana san ran zaibiya. zokisha kallo idan ana bikin mai kud’i a danginmu, yadda ake karawa mai ‘k’arfi, k’arfi saboda an san zai iya biya.
Fisabilillahi ina amfanin hakan, ga wanda zaka yiwa ya ji da’di’, Allah kuma yayi farin ciki da abin da ka yi, sai ka je ka yi a inda sam kud’in da ka bayar ba burge su zaka yi ba. Dalili? Suna da ni kin ba ninkin naka ka ga ka tashi a tutar babu ba lada ba gwaninta. Kai Allah ya kyauta! Ubangiji ka cika zuciyarmu da imani.
Mu biyar ne a wajen mahaifiyar mu, ina da yayye uku, maza biyu suna FCE biyu kuwa a management suke. Nikadai ce ‘diya mace, nida yaya sa’eed munfi kowa tsanar danginmu a gidan nan. Ni ko yawon sallah ba na zuwa, A kullum nasihar umma garemu mu yayyafa wa xuciyarmu ruwan sanyi, komai mai wucewa ne wata rana sai labari. Jin Ta kawai nake, Allah ne kad’ai yasan yadda nake ‘kinsu, K’iyayyar su ta zauna daram a raina.
Ko ‘ya’yansu babu wanda nake Huld’a dashi sai d’aya, itama sama-sama kawai ne tsakaninmu, ba wani mun sha’ku bane.

*** *** ***
Kashe gari tun safe nake ta nu’ku-nu’ku na ‘ki shiryawa don nasan Umma tace tun safe zamu tafi, ita kuwa sai mita take yi Koda nayi wanka, powder kawai na mitstsika wa idona , dama ni ba gwanar kwalliya ba.
Mutane da dama suna yimin kirari da kyau zalla, haka din ne duk da nidin ba fara bace, haka nan ba za’a sakani a layin bak’ak’e ba. Girar idona tana da yalwa,sannan tana da lan’kwasa, ina da dara daran ido masu yalwar gashi da rumfar ido. Hancina na da tsayi da tudu kad’an. Bakina kuwa ba k’arami ba ne ainun, haka kuma ba za’a kira shi babba ba, yana daga cikin tsaka tsaki dai. Jikina a murje ya ke ba rama babu kuma k’iba. Dogon wuya ne da ni wanda ya fallasa asirin tudun k’irjina. Haka nan ina da cikakken k’ugu a dire nake sosai, k’afafuna kuwa zan iya cewa sun fi komai kyau a jikina kasancewrsu luwai-luwai kamar na fatar jarirai don fatata mai kyau ce duk da ba fara ba ce ni sosai amma k’afata fara ce tas kamar ka latsa jini ya fito.


Da sauri na zira wani bak’in takalmina flat shoe half cover, nayi saurin ficewa daga d’akin jin Malam Mahaifina yana k’wala min kira.
Wani kallo ya bini da shi, kafin ya yi k’wafa ya ce “Wato ke uwata har yanzu zuciyarki ba za ta rusuna ba ko? Kin k’ullaci y’an uwana a zuciyarki. To ko ni da suka yi wa abin ban k’ullacesu ba, idan ma sun yi min d’in ina ruwanki ba tare ki ka gan mu ba? Shashashar banza. Ke ma kin zama su tunda kin yanke zumunci da su. Za ki wuce ki tafi ko sai na sab’ar miki. Sakaryar banza kawai.”
Tamkar na rusa ihu haka na ji, jikina babu laka. Haka na bi Ummanmu zungui-zungui a baya, fuskata a had’e tamkar an yi min bushara da mutuwar mahaifina. Na ayyana duk shegiyar da na je ta yi min kallon banza a gidan sunan nan wallahi sai ta kwashi hannunta a hannunta, don sai na lakad’a mata uban duka, don sun iya yiwa mutane kallon k’ask’anci da kallon baka isa ba, wanene kai?

Gidan ba kowa don san da muka je ba a cika ba, zan iya cewa ma mune farko-farkon zuwa. A zuciyata na ce na san kallon azarb’ab’i ake mana mun zo cin ta tsotse. Kamar kowane lokaci ba mu samu wani kallon maraba da
Manyan bak’i ba. A madadin haka ma kallon daman ku muke jira, ga aikinku can, shi aka bi mu da shi.
Umma kuwa dai washe baki take. Ba don uwa ba ce Allah ji na yi kamar na rufe mata bakin.

A hakimce uwargidan B. Hamzan take a kan kujera, ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya, ta bi Umma da kallo tamkar ba faccalarta ba, kai kace uwargijiya ce da mai aikinta. “Sa’ade, dama ke nake jira, ga kullin waina can a tsakar gida, suyar wainar za kiyi sai kin d’an hanzarta don da yawa kwano goma ce.”

ALK’ALAMIN JIKAR NASHE




Zumuncin Zamani

Na Nazeefah Nashe.

(Ku karanta kyauta. Abokin hira na dare)


📄 2


Umma ba abinda ya dameta da umarnin da aka bata, madadin b’acin rai ma a fuskarta sai fara’a take tana jaddada Allah ya raya d’iyarki Munira ya yi mata Albarka, alfarmar annabin Rahma.

Cikin shan k’amshi mai jegon take amsawa da kyar sai wani muzurai take tamkar Umman sa’arta ce sai kace Umman bata haifi wad’anda suka girme mata ba, kawai don dai ba ta da kud’i shi yass bata da wata daraja da k’ima a idanunsu. Ganin Umman ta mik’e sai ni ma Na mik’e na bi ta a baya, har na kusa k’ofa na ji muryar Muniran cikin gadara tana cewa “Ke Sauda ba kya gaisuwa ne? Saboda rashin mutunci kina ganin mutane ba za ki gaishe su ba?” Na juya na zuba mata wani kallo kafin na ce “Shi yasa naga kin gaida tawa uwar.. uwa ai ba tafi uwa ba..” A fisge ta d’ago ta zuba min na mujiya “Kan uban can ashe fetsararki da rashin mutuncinki yana nan? Shegiya kina y’ar talaka sai girman kan banza, ciki fal yunwa..” Na jiyo zan bata amsa a zafafe don har wani turirin b’acin rai nake tsabar tunzira da zuciyata ta yi. Ji na yi kawai Umma ta damk’i hannuna da sauri don ta san ba zan furta mai kyau ba, muka fice duk da turjewa da na ke. Aljihun rigarta ta zira hannu ta d’auko Naira d’ari wanda ba na haufi ita kad’aice da ita ta manna min a tafin hannuna “Maza wuce gida kada ki tsaya a ko ina, kuma ki yi ta jan matayassara minal k’ur’ani daga zuciyarki zaki samu sauk’in nauyin da zuciyarki ta yi.” Idona jajur na d’ago na zube su akan fuskar Umma “Amma Umma.....” “Kada kice komai Sauda wuce maza ki je Allah ya yi miki albarka wata rana sai Labari, babu wani abu da yake dawwama a duniya, komai na cikinta hudusin fana’un ne, fararre k’ararre haka manzon rahma ya ce, da kin d’auko irin zuciyata da ta ubanki da duka abubuwan nan ba su dameki ba.” Cikin sauri kawai na juya na fice daga gidan hawayen takaici yana zuba daga ido na.


******

Sai dare bayan magriba sannan Umma ta dawo, kai daga ganin ta ka san a wahalce take sai haki take saukewa da ajiyar zuciya, hakan yasa na mik’e na kawo mata ruwan cikin randarmu mai sanyi. Na dubi hannunta da take karb’ar ruwan har rawa yake tsabar gajiya ko take away d’in bikin na san basu bata ba, k’iri-k’iri suke bawa masu ido da kwalli ko kunya a hana ya ku bayi. Tsaki na ja a fili na ce “Kin gani ko? Haka kawai kin je kin wahalar da kan ki a banza don ba gani za suyi ba matsiyata.” Umma ajiyar zuciya ta yi kafin ta ce “Ba burina dama su gani ba, Umarnin Manzon Allah (S.A.W) Na cika da ya ce a sadar da zumunci, da dukiya da jikinka, tunda kuwa ba ni da dukiyar da zan bayar, dole ne na yi da jiki na Allah yasa mu dace.” Ta kafa bakinta ta sha ruwan sosai sai da ta kusa shanyewa sannan ta dire kofin tana fad’in Alhamdulillah, Sai bayan da kika taho na tuna gudar d’arin kenan na baki ba ni da kud’in mota, don haka da sayyadata na tako.” Na tab’e baki don na tabbatar wasu daga cikin su sun zo wucewa da mitocinsu kuma sun gan ta, don sun saba su gan mu muna tafiya a k’afa su bad’e mu da k’ura su wuce..
Hmm, duniya kenan idan kana cikinta zaka sha kallo.

Umma ta dubeni tana kama hannuna ta matsa shi sosai kafin ta ce “Sauda ki nutsu ki san duniya makaranta ce, ki daina sakawa kan ki b’acin ran mutanen nan a banza a wofi.”
Na d’ago idanuna jajur suna kwararar hawayen bak’in ciki na ce “Don Girman zatin Allah Umma ki rabu da mutanen nan, ki daina shiga sabgarsu mu tsaya iya matsayinmu kawai tunda ba sanin mutuncinki suka yi ba.”

Murmushi ta saki kawai kafin ta ce “Sauda kenan! Cewa za ki yi Umma ki daina bin Umarnin Manzon Allah (S.A.W) ki dawo bin umarni na, kin ji Uwata haka ya kamata ki ce, to ba ki isa ba, har abada kuwa. Me za’a yi da mai yanke zumunci? Ke ma so nake ki yayyafa wa zuciyarki ruwan sanyi, don Allah ki dinga sakin ranki da fuskarki idan kin shiga Dangi.”

Na yi tamkar na ji nasiharta, amma ina! Sam ni na san irin bak’in cikin da yake rura wuta a zuciyata. Na lumshe ido sai ga wasu siraran hawaye sun zubo min.

Umma ta saka salati had’e da rungumeni a jikinta tana buga bayana alamar rarrashi “Kuka kuma Sauda? Yanzu kuma ki ke fisabilillahi menene abin kuka anan? In dai kika ce za ki dinga saka irin wad’annan damuwoyin na duniya a zuciyarki to tabbas ciwon zuciya zai kama ki.”

Sunkuyar da kaina kawai na yi a cinyarta ina sakin wata irin ajiyar zuciya akai-akai.

Maganar Umma ce ta sake katse ni da na ji ta ce “Bayan tahowarki kuwa da kad’an sai ga Yayanku Hisham ya dawo daga k’asar da ya tafi karatu. Tsawon shekaru sha biyar fa Kenan, sai yau ya waiwayi gida duk ya canja ya yi kyau sosai ya sake fari da kyau tamkar d’iyar larabawan Qatar.”

Tab’e baki kawai na yi ba tare da na furta komai ba, na shige d’aki a zuciyata ina mitar “Ina ruwana da Wani Hisham, ban ma San shi ba, duk wani jinin Baba Hamza ni cikakken mak’iyi nake d’aukansu balle wannan da ban sani ba.
Umma dai ba tabi ta kaina ba tana daga zaune ta cigaba da laziminta tana sakin d’an murmushi da alama zallar rigimata take tunani.


*******

Da y’ar wak’a ta na shigo gidan. Dawowata daga islamiyya kenan. Yaya Khalil ya zabga min harara “Wai ke shashashar ina ce? Ki shigo ko sallama babu kuma kina tafe kina wak’a kamar matan k’auye sun dawo daga dandali.”

Raina na had’e dama shi kullum ba ma shiri da shi, mun fi shiri da Yaya Sa’eed. Na cire hijabi na na sak’aleshi akan igiyar shanyar da take tsakar gidanmu, sannan na na shige d’an d’akin girkinmu na langa-langa da yake gefe. Abinci nake nema don dama gwanace ni a wajen ci.

Yaya Saeed ya dubi kwanon da na zubo shinkafa Manja da yaji sai salad daga gefe, yau murna ce ta cika ni musamman da naga har salad aka saka mana a abinci, tsaki ya ja ya ce “Acici kenan, ke ba ki da aiki sai cin abinci kuma a rasa ina abincin yake tafiya a jikin ki.”

Na kuwa zunb’ura baki don idan da sunan da na tsani a kira ni da shi to wannan sunan da Yaya Saeed ya saka min ne. Ina Shirin ba shi amsa wani sassanyan k’amshin turare ya doki hancina, kafin sallamarsa ta bayyana, cikin murya mai tarin kamala da nutsuwa.

Da sauri na juya don son ganin mamallakin muryar “Wai! Subhanallah! Fatabarakallahu Ahsanul khalik’een..” shine kawai abinda na samu damar fad’i a zuciyata, don ganin tsananin kyau da kamala gami da Haiba da cikar zati na wannan bawan Allahn tamkar shi ya halicci kansa da kansa.

Ban san shi ba, ina kuma mamakin yarda ya shigo mana gida kai tsaye.

Yaya Khalil na ga ya saki murmushi ya kuma mik’e da sauri had’e da fad’in, “Hisham saukar yaushe?”

Wani k’ayataccen murmushi ya saki, da ya sake k’awata fuskarsa amma madadin in ga kyawunsa, sai naga duk wani kyansa da nake gani yana dushewa ya koma muni. Tun daga lokacin da Na ji an ambace shi da Hisham na san shine wanda jiya Umma take bani labarin dawowarsa. Da sauri na d’au kwanon abincina na shige d’aki don kada ma ace na

Please Login or Register in order to submit comment