Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na fito sai dai idan an dawo daga gidan Senatorn wanda ya dubi Allah ya dubi zumunci ya je gidan Mustafa fisabilillahi fa, ke ma Hajiya zance ki ke wa zai hak’ura da zuwa gidan da za’a dagargaji kaji ya tafi gidan da ba mamaki cincin da cofe za’a bayar.” D’aya daga cikin y’an uwanta ta fad’a, ai kuwa kowa kamar jira yake suka bata goyon bayan zancenta d’ari bisa d’ari.

Inna Falmata ma murmushi ta saki, ta ce “Ai na san za’a rina an saci zanin mahaukaciya sai ki kira Hisham ya kawo lefen y’ar gidan Mustafan idan muka dawo mu ma yi shahada ko mu biyar ne mu mik’a, ko bakomai ka samu ladan zumunci don dai ba abinda za mu tsinto a gidan Mustafa suna ta kansu.”

Hajiya Laraba ta d’aga waya ta kira shi. Bugu uku ya d’aga wayar don yana bayan gidan kuma duk wata tattaunawa da suke a kunnensa suke yinta, ransa a b’ace cizar lab’b’a kawai yake yi. Sai da ya bari ta gama sanar da shi sannan ya ja hucin numfashi shima ya gaya mata abinda ya girgiza zuciyarta don direct ya ce “Ai lefe ya dad’e a gidansu Saudat na hutar da kowa ba sai an je ba, su je inda suke da tukuici mai kyau…” cikin dukan zuciya Hajiya Laraba ta ce “Ka yi me ne? Kai ne ka kai lefen da kanka saboda a garin gab’a gab’a ake? Ba fa na son k’arya ko dai kud’in suka buk’aci ka basu?”
Cikin b’acin rai ya ce “Ko d’aya Mommy na ga dai hakan shi yafi cancanta.”

Kafin ya sake cewa komai ta danne makashin wayar cikin b’acin rai ta kawar da wayar a kunnenta, kada dai zancen Falmata ya tabbata da gaske an shanye mata d’a tunanin da ta dinga yi kenan, kafin ta kalli Falmata ta ce “Kin ji yaron nan wai ya kai musu lefen tun d’azu” Falmata ta d’an zare ido ta ce “To Allah ya kyauta, amma menene abin b’oyewar?” Cike da takaici Balaraba ta ce “Zai wuce dukiya ya narka musu baya son a gani, kai ni wannan wace irin k’addara ce ta auren y’ar nan?” Caraf k’anwar Laraban ta ce “Kwantar da hankalinki Yaya, ai ya yi a banza za muje har gidan mu ga abinda ya sa ya k’i ya kawo mana lefen idan kuwa dukiya ya narka mata tsaf za mu rago su mu dawo miki da su.”


_____________________

K’arfe biyar daidai na yamma masu kai lefen suka bayyana a tanfatsetsen filin gidan Sule Jami’i, haka aka dinga d’iban kayan ana shiga da su, su kuma suna tururuwar shiga babban falon na gidan. Dama dai an ce gaba da gabanta tuni kallo ya koma sama. Haka suka cika falon nan taf.

Hajiya Sa’ar na zaune a hakimce saman Babbar kujera, gefe da gefenta kuwa manyan Aminanta da suke take mata kaya sun sha adon gwalgwalai a jikinsu da laces masu uban kud’i. D’ayar kujerar kuwa Yayyan Alh.Sulen ne su biyu suma a hakimce cikin tasu shigar su kenan masu karb’ar lefen, amma su sun yi uban gayya. Tsaf Hajiya Sa’a ta dinga musu kallon d’aya bayan d’aya tana nazarinsu a tak’aice. D’aid’aiku ne a cikinsu ta san sun kai daidai yarda take son surukan yarinyarta su kasance irin su Hajiya Falmata, sauran kuwa duk daga yanayin surutun da suke jikinsu ta tantance a level d’in da zata ajiye su. Ta yamutsa fuska tana mamakin irin ayarin da suka yiyo wai kawo lefe a zuciyarta ta dinga ayyana masu shegen son abin duniya, dubi haukan da suka yi wai kawo kayan lefe kawai da sannu duk zan yi maganinku.

Bayan an gama gaisuwar kowa a d’arare Hajiya Falmata cike da Izzarta itama da nuna bajintar da suka yi wajen had’a kayan lefen ta gabatar musu da kayan tana nazarin fuskarsu ta ga wani irin kallo za su yiwa kayan. Ganin ko kallon kayan ba su yi ba ya sa Inna Falmatan ta dubi Sadiya K’aramar k’anwarsu ta ce “Bubbud’a kayan nan su gani mana.” Da sauri dangin amaryar suka dakatar da ita d’aya daga cikin Aminanta ta ce “No need ta bar shi ma menene bak’o a wajenmu za mu gani later.” Gaba d’aya gwiwoyin Inna Falmata dana sauran wad’anda suka san ciwon kansu suka yi sanyi, don dole suke dariyar yak’e. Inna Falmata ganin ba arziki ta mik’e ta ce “To mun barku lafiya, idan aka saka lokacin bikin a aiko mana.” Saura kuwa sai godiya suke, godiyar da ta k’ular da Inna Falmata ta shiga wurga masu harara. Har sun kai k’ofa Hajiya Sa’a ta kalli wata budurwa a cikinsu ta ce “Ke zo nan.” Yarinyar ta juya Hajiya Sa’a ta nuna mata wata leda mai d’an girma “Gashi nan, maza ki d’auka ki kai musu tukwucinsu ne don ni ba ni da wani lokacin saka orderr snacks.”

Suna gama ficewa ko k’arasawa falon ba su yi ba na zauna falon suka tintsire da dariya, Hajiya Sa’a ta ce “Makwad’aitan banza, su nan sun zata wata tsiyar suka kawo da zamu dinga Rige-rigen gani ko menene abin burgewa a akwatina sha takwas, ga can in da ake abin arziki ana kai akwatina dozen biyar dozen goma.”

Yayar Senetorn ma tsaki ta zabga kafin ta ce “Shima dai Sule ban ga dalilinsa na d’aukan santalar y’a ya bawa d’an yaronsa ba, fisabilillah ina laifin ya samar mata y’ar shugaban k’asa ko d’an mataimakinsa, amma wannan mai na sama ya ci balle ya bawa na k’asa idan banda suma su dinga harin arzikin shikkenan ka siyar da akuya ta dawo tana ci maka danga…” Hajiya Sa’a ta sake tunzira ta ce “Ke ma dai kya fad’a Hajiya, ana harkar arziki shi yana rakitowa kansa tsiya da kud’insa, dubi don Allah tururuwar da suka yi tamkar gidan biki, sam bana farin ciki da wannan auren duk da dai yaron yana tashin kud’i amma ai ba kud’i irin wanda mu za mu yi zakwad’in ba shi y’a saboda shi bane.”

(Tirk’ashi shi dama lamarin duniya haka yake, idan kana ganin ka fi wani to shi fa wani ganinka yake kamar yaron gidansa don haka ba’a son tutiya da arziki.”

Haka suka koma gida gwiwoyinsu a sage, sai dai babu wanda ya furta kalmar ‘a’ a cikinsu ba don komai ba sai don mak’udan kud’in da aka shak’a musu a matsayin tukwuici miliyan biyar cif ai ko ta rufe bakin surutu tsaf. Madadin k’orafi ma jinjina k’ok’arinsu suke ta hanyar yamad’id’i da cewa an musu harkar girma wad’annan kud’in ai sun fi mana tarkacen soye-doyen da za’a ba mu. Kai Hisham ya yi dace da gidan k’warai ya tako arziki wannan gida na su ai ko a aljanna aka baka shi sai kace Falillahil Hamdu.


Mhmmn! Kud’i kenan k’are magana!



_________________

Gidansu Sauda kuwa fal ya cika da y’an uwan Umman Sauda da y’an unguwa masu ganin lefe. Akwaninta goma sha biyu cif kuma komai a ciki mai tsada ya saka mata. Kowa fad’i yake son barka a dangin Abbansu kuwa y’ay’an Inna Halima da Inna Haliman ne kawai suka zo wanda suke uwa d’aya uba d’aya da Abba Mustafan. Zance guda ake Sauda ta tako arziki Ma sha Allah.

Da Abban Sauda ya dawo ya ga kayan fad’a ya dinga yi yana fad’in siyar masa da y’ar zan yi zai zo ya sameni Shi Hisham d’in.

Ita kuwa Sauda ba zata ce ba ta yi farin ciki ba, sai dai ta ce farin cikin nata ragagge ne, don tunda ta samu labarin su biyu zai aura gaba d’aya gwiyoyinta suka yi sanyi da maganar auren don ta san tarin matsaloline zata fuskancesu jingim. Tun ranar bata sake ganin Hisham ba don ko yazo barcin k’arya take Sam bata son had’uwarta da shi. Kishi ne yake nuk’urk’usar zuciyarta.

Da daddare Hisham d’in ya sake zuwa kamar kowane lokaci baya gajiya zai zo ko ba zata fito ba.

Shigar k’ananan kaya ne a jikinsa sun yi matuk’ar amsarsa. Sai zabga k’amshin turaren Lulu yake. Ya yi kyau sosai zatinsa ya kammala ya kuma nuna cikakkiyar haibarsa da kamalarsa ta mazantaka.

Saudat ta sake lafewa a katifarta kamar mai barci, duk da tana jin Ummanta na kiranta. Tsam Umman ta mik’e ta shige d’akin. Duka sosai ta d’aka mata a cinya ta ce “Mik’e y’ar banza , ai na san idonki biyu wallahi ki kiyayeni akan wannan banzar d’abi’ar da kika d’auka, me kike nufi ne yanzu duk halarcin da yaron nan ya miki ke k’ok’ari kike sai kin zuba masa k’asa a ido? Zaki ta shi ko sai na ba shi izinin shigowa?” Da sauri Saudan ta mik’e tana turowa baki ta ja mayafinta ta nad’e kanta da shi. Ta fice daga d’akin fuskarta a had’e. Tuni ya fice daga tsakar gidan hakan ya sa ta bi shi wajen. Cikin motarsa ta shiga gidan baya ta zauna madadin gidan gaba da ta saba zama.

Wata irin ajiyar zuciya Hisham ya sauke ganin ta fito ta saurareshi ya dinga kallonta ta cikin mudubi yarda take murza hannunta fuskarta a had’e. Farin ciki ne sosai ya kamashi ganin da gaske Saudan kishinsa take ya dinga sakin murmushi shi kad’ai ji yake tamkar ya jata jikinsa ta ji yarda zuciyarsa take bugawa kuma ko wane bugu da zuciyar za ta yi da gurin soyayyarta take yi.

K’amshin turarensa ya bi ya addabi Saudat ta dinga jin wani irin feeling na saukar mata, har bata san sanda ta dinga jin b’acin ranta yana sauka daga zuciyarta ba, ta lumshe idanunta kawai kafin ta bud’esu su sauka cikin nasa k’wayar idanun. Wata irin kunya ce ta dabaibayeta ta yi saurin saukar da kanta. Da murmushi sosai a fuskarsa ya shafa sumar kansa murya can k’asa ya ce “Saudatuna Ina yini?”




Daga taskar jikar Nashe.❤️🙏

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment