Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallameta bayan sun tabbatar babu abunda yake damun ta, daker Mummy ta yarda aka maida da gidan mijin dan son tayi ta koma gida har sai yadda hali yayi tukuna, sai gashi Saif yakin yarda a dole ita ta hak'ura,
Tunda suka dawo ba wani aiki take yi sosai ba, ga kula da take samu ta ko ina, duk bayan kwana biyu sai tazo duba ta, a ɓangaren Abbah ma haka yake dan a koda yaushe cikin waya suke,
Bata da matsala ko ɗaya a yanzu, babu kuma abunda take zumuɗi kamar auren Abbah da Mummy, duk da a ɓoye za ayi shi,
amman hakan bai hana Kairat yin wasu abubuwan ba, haka ta rika kai kawo har aka ɗaura auren, aiko ranar farinciki gurin Kairat ba'a magana, gurin Hajiya Suwaiba kan bakinciki ne ya cika ta a nan ne Kairat ta kara tabbatar da Lallai kishi kumallon mata ne tana mamaki yadda Hajiya da ta girmi Mummy amman take kishinta,
haka tayi ta tausar ta da kalama da kuma nuna mata Mummy ba mace bace mai matsala, Abbah yaso Mummy ta tare a ɗayan gidansa ko kuma gidan da Hajiya Suwaiba take ciki amman taki ita dai tafi son gidan da take, tunda aka ɗaura aure sau ɗaya Saif ya yarda Kairat taje gidan Mummy, wai a yanzu shi ba zai yarda tana masa yawo da ciki ba ga kuma lil Minal take fama da quiya tunda aka yayeta a yanzu bata yarda da kowa daga Mah sai Pah,

Wasa wasa lamarin Safiyyah sai karuwa yake tun ana ganin kamar za a warke haran fara fidda rai, dan babu asibitin da kai ta ba ta ido tun daga nan Nijeriya har waje amman abun sai karuwa yake dan a yanzu har kaikayi suke mata,
Tana tafe yar jarorar da Momy ta samo mata tana janta har suka kawo gurin da akace bakon dake sallama da ita yana tsaye,

"Gashi nan"

Yar jarorar ta faɗa sannan ta sake ta ta juya ta basu guri, shirun da taji yayi yawa ne yasa ta mika hannu zata taɓa mutumen

"Ba mutun a gurin ne?"

"Hmmm gani ba ganki amman baki iya gani ba, duniya kenan budurwa wawa, ai ni naso kin fi haka shiga matsala, Kyakkyawan dake amman ba ido,
kin cancanci shiga ko wace irin matsala ta rayuwa, zaki iya tuno lokacin da kika ɓata tsakani na da Minal kika kira ni wawa saboda na biye miki mun aikata abunda kika yaudare ni a kai kuma kika yaudari kan ki, shin wace irin riba kika ci a yanzu?"

Tunda ya soma maganar ta fahimci wanene, wani kalar bakinciki ne ya mamaye mata zuciya lokaci ɗaya hawaye suka rika bin fuskarta wasu na korar wasu,

"Deen... -"

"Yes anything for me again?"

Bata ce komai ba har na tsawon wani lokacin, zuwa can ya kalleta up and down yace

"Nazo ne kawai na ganki kuma na fi kowa farinciki shiga halin da kike ciki ina miki fatan alheri"

Bai jira abunda zata ce ba ya buɗe motarsa ya shiga, ita ma ɗin bata ce komai ba har yaja motarsa ya bar gurin, sannan tasa hannu ta share hawayen idonta ta juyo da yar sandarta ta dafe dafehar ta shiga parlour, yar jarora na ganin ta, ta tashi ta rika ta, ta zaunar,
Ajiyar zuciya ta sauke ta tsura ma carpet ɗin ido kamar wance ke ganin carpet ɗin, wasu siraran hawaye suka zubo mata, ta fi karfi minti talatin a haka sai hawayen take, yarinyar na ganin hakan ta tashi ta faɗa ma Gwaggo, sai gata ta sauko cikin sauri ta zauna kusa da ita

"Me kuma ya faru?"

Sai da share hawayen sannan tace

"Mako mata nake tunani Gwaggo, na cuci mutane da suka yarda dani na zama mai fuska biyu har wanda bai san da zama na ba na cutar da shi"

"Har yaushe zaki daina wannan tunanin Safiyyah yaushe zaki bar zuciyar ki ta huta?"

"Sai ranar da na koma ga Mahalicci na, makoma ta nake tunani Gwaggo, idan amanar wasu ta tashi kama ni ya zata zo min, wata rana zata zo Gwaggo ke kanki zaki gaji dani ki gujeni,
ba zan auru ba Gwaggo dan babu wanda zai auri makauniya, duka kawayena sun bar ni saboda suna ganin yanzu bana iya komai, hakika hausawa sunyi gaskiya da sukace duniya ta ishi kowa ri da wando wanda bai zo ba ta shirya masa balle mu da muke cikin ta"

Gwaggo ta share hawayen idonta tana faɗin

"Babu wannan ranar Safiyyah, bazan taɓa gudun ki ba Allah dai ya baki lafiya"

"Amin amman wannan idon ka ba zan taɓa warke ba"

"Kada ki yanke kauna daga Rahama Allah"

"Kai ni ɗaki na zan kwanta"

Gwaggo da kanta ta rika ta suka nufi ɗaki ko wane zuciyarsa babu daɗi.

**** **** ****
As usual da ledoji ya shigo parlor, ganin bata parlour kuma bai ji motsinta kicin ba ya tabbatar masa da tana ɗaki, a parlour ya aje ledojin ya nufi ɗakinta, ya tura kofar ɗakin yana faɗin

"I'm back"

A wahale ta ɗago ta kalleshi tace

"Sannu da zuwa"

"Yauwa Baby na, ina ɗayar Babyn?"

"Ta raka Lubna da kawayenta rabon anko"

"Kin san ban cika son yawan fitar nan da take ba ko, bana son ta saba da yawon nan"

Ita dai bata ce komai ba nata ya ishata, sai a lokacin ya lura da halin da take ciki,

"Meke damun ki?"

"Marata ke ciwo"

Ta faɗa tana dantsar baki, karasowa yayi ya rik'a ta daker tayi zaune, a nan yaga jini, zaro ido yayi

"Subhanallahi"

Hannayensa yasa ya ɗauke ya nufi bedroom da ita, ya cire mata kayan jikinta ya gyara mata jikin sannan ya ɗauko doguwar riga yasa mata da hijab, ya ɗauke ta ta nufi mota da ita.



60

Safa da marwa ya rik'a yi a bakin kofar, yana haka Mummy ta iso

"Tana ciki?"

Shine abunda ta fara tambaya daga isowa, a natse ya gaishe ta bayan ta amsa yace

"Eh tana ciki"

"Haihuwar ne?"

"Ina jin shine ban dai tabbatar ba"

Kujera ta samu ta zauna, hankalin ta ba a kwance ba, sai Addu'a take, Saif ma ita yake a inda yakr tsaye,
Bayan kamar awa biyu da wani abu wata nurse ta fito daga ɗakin da sauri,

"Kuje ku kawo kayan jariri matar ka ta kusa sauka"

Tana faɗar hakan ta nufi wata hanyar da sauri, shi kan tsaye yayi kamar wanda bai ji abunda tace ba, Mummy ta kalleshi

"Kun sayi kayan jariran?"

Ya ɗaga mata kai

"Eh suna can gida"

"Okey ba ni keys ɗin zan ɗauko"

Mika mata yayi dan shi kan baya jin zai iya barin gurin har sai yaji ance matarsa ta haihu. Mummy na karɓar keys ɗin ta ɗauki jakarta ta fice da sauri, ba tayi minti biyar da fita ba sai ga Momy ta iso tare da Nasir, ganin Momy ne yasa shi zama a kujerar dake gurin yana karfafa ma kansa guiwa, a gurin suma suka zauna ko wanne zuciyarsa cike da zullumi, suna haka har Mummy ta dawo, kusan set set biyar tazo dasu na kayan jarirai da duk wani abun da tasan za'a bukata, isowarta yayi dai dai ta fitowar nurse ɗin tace a bata kayan jarirai, Mummy na cikin gaisawa da Momy ta juyo, ta mika mata kayan, gurin karɓa ne ta kalli Saif tana murmushi tace

"Matarka ta sauka ta haifa maka kyakkyawan kuma lafiyayyen jariri"

"Alhamdulillah"

Shine abunda ya furta ta rungume Nasir yana dariya, Mummy da Momy ma ko wanne fuskarsa ɗauki take da farinciki, suna yi ma Allah godiya,
Bayan sun gama gyara jaririn suka fito dashi daga ɗakin, Momy da Nasir suka rika rigangan gurin karɓa,

"Masha Allah"

Nasir ya faɗa yana rumgumar jaririn a hannunsa, Momy ce ta biyu gurin karɓa bayan Nasir, sannan Mummy, Saif ne na karshe, ya rungume ɗansa kamar wanda za'a kwace ma wani irin daɗi yake ji a ransa kamar yanzu ne aka fara masa haihuwa,
Kula ta musamman Kairat ta rika samu daga gurin Momy da Mummy, da kuma Hajiya Suwaiba, kwanan ta biyu a asibitin suka salameta bayan sun tabbatar da lafiyar ta da kuma ta jaririnta,

Gidan Mummy aka dawo da ita, duk da Hajiya Suwaiba taso a barta ta koma gidan su amman Mummy ta ki yarda, babu irin kukan da lil Minal bata yi ba ganin Momie ta ta wani ɗan, hakan yasa kullum Saif yake zuwa ya ɗauke ta sai dare zai dawo da ita wani lokacin kuma a can take kwana tare da shi.
Bayan kwana uku da da dawowar ta aka kawo kayan barka, da kayan kauri, babu abunda ba a saka ba tun daga kayan jarirai har na mai jegon, tun ana kirga kayan har aka gaji, dan kowa akwatunansa daban na mai jego daban na Jariri daban abun gwanin ban sha'awa, sai labarin ake. Ranar suna yaro ya ci sunan kakansa, MUHAMMAD BASHIR aka masa lakani da Aniq. An ci an sha, babu abunda ba a raba ba,
Bayan sunan da sati biyar aka bikin Nasir da Lubna, daker Saif ya yarda Kairat taje bikin duk da tayi arba'in sai dai Mummy bata barta ta koma ba tasa ana mata shiri n musamman. anyi biki abunda ake kira biki, an zubar da kuɗi kamar ba gobe, Saif ya nuna ba jinta a gurin biki ta ko ina, yadda yake ɓarin kuɗi sai ka ɗauka bai san zafin neman su ba, ranar Asabar aka ɗaura, bayan anyi dina amarya ta tare dare da aka ɗaura auren.

Sai da Mummy ta gama shirya Kairat sannan ta barta ta koma gidan mijinta, bayan an samo mai taya ta reno. Fasalin rayuwar Saif ta canja daga marar mata zuwa mai mata har da yaya biyu, an yanzu kan shi kansa yasan ya girma, ita kan ta Kairat ta canja a yanzu dan kallo ɗaya zaka mata ka gane matar aure ce, saboda yadda ta buɗe ta zama babbar mace, daman hausawa sunce haihuwa na buɗe mace. Rayuwar suke yi ta jindaɗi da kwanciyar hankali, rayuwar da ita ko shi ba su taɓa mafarkin shiga ba.
A ɓangaren Mummy ma haka abun yake bata da wata matsala ko damuwa a yanzu, hankalin ta a kwance, Abbah yana kula da ita sosai musamman cikin nan da take ɗauke da shi ita kanta tana farinciki, sai dai wani gefen tana jin kunya wai zata yi haihuwar tsufa, hakan yasa ba kowa ne yasan tana da cikin ba Kairat ma ita kanta bata san tana da cikin ba, Allah ya taimake ta mace ce mai babban jiki hakan yasa ba a gane cikin dake jikinta, idan ba wanda ke kusa da ita kullum ba.

Komai ka shuka shi zaka gurba, in ji hausawa, kuma ramen mugunta gina shi ɗan kaɗan ba kato ba, dan wata rana kai ne zaka faɗa, rayuwa ta zamo mata ta tsanani da wahala, saboda rashin ido komai sai dai ayi mata, tun tana mafarkin buɗewar idonta har ta daina tun tana dafe dafe har ta saba, abun da yafi damunta shine na rashin auren da bata yi ba, ta tsaya bata lokacin ta akan wanda ya zama silar makantarta kuma bukatar ta bata biya ba, ganin zaman baya mata a gidan Gwaggo yasa ta tattara ta dawo gurin Momy, dan tasan duk kular da Gwaggo zata bata ba zata kai ta Momy ba, daman tayi tayi ta dawo ita ce taki ganin yanzu babu sarki sai Allah yasa ta dawo gidan, hankalinta yakan tashi duk lokacin da Saif yazo gidan ko ya kawo iyalinsa, babu irin kuɗin da Momy bata kasa ba wajen ganin ta samo lafiyarta amman ya ci tura.

Da gudu ta sauko downstairs kamar wata karamar yarinya, rike da waya a hannunta, ta zauna kusa da shi,

"Yanzu Humaira ta kira ni... -"

(Humaira matar da Deen ya aura kenan)

Kamin ta karasa ya walkato ta ta dawo saman jikinsa ta kama karamin bakinta

"Tace me?"

"Ta haihu ta samu Ya mace"

"Masha Allah Allah ya raya, yaushe?"

"Wai yau kwana uku ranar Litinin za'ayi suna"

"Toh Allah ya raya sai ki samu abunda zaki bata"

"Ai dole zanje gobe nayi mata barka"

"Yeah, cox jibi zanje wani business trip kuma kila dake zanje"

"What?"

Ta tashi zaune,

"Wasa dai kake ko?"

"Aa nima ɗazu Daddy yake sanar min, kuma yace yana da muhimmanci dole naje indai har an tabbatar da abun"

"Gaskiya ni ba zani ba"

Ta faɗa tana kukan shagwaɓa,

"Saboda me?"

"Yaushe muka dawo, ni gaskiya ba zan kara fita waje ba sai na yaye Aniq"

Dariya yayi dariyar da sai da ta fitar da Beauty point ɗinsa

"Amman yarinyar nan kin raina mutane, oh ke abarki kije kina yawo a gari kina matsu ko baki son shayarwa kar ace kin haihu"

"Eh mana ai yana takura min kuma ni gaskiya, ina son naga bikin Anty Fareeda yau fa sauran sati biyu"

"Whatever, ni dai ba zan je ni kaɗai ba tun da kinsan ba wata matar ni dani ba"

Kuka tasa masa ya rungume ta yana murmushi, kamin ya ɗaga ta daga jikinta yana mata kiss

"Bari ma naje gurin Daddy na kara tabbatar wa"

"Allah yasa an fasa"

"Ba Amin ba"

Ya faɗa yana smirking.

Da Sallama ya shigo parlour, Momy da Nasir suka amsa masa,

"Ango ango ango kasha mai"

Ya faɗa yana zaunawa saman kujera

"Kai wane irin ango watan mu nawa da yin aure bana son shashancin fa"

Dariya yayi

"Au gaban uwata zaka kira ni shasha?"

"Uwata dai kai kana da uwa ne"

"Aa sama na faɗo"

Dariya sukayi har Momy,

"Auto naga uwata ce sai ka nemo wata uwar kuma"

"Sarakuwar ka dai"

"Aa ni ba wani sarakuta uwata ce kawai kaga tafiyata"

Bai bari Saif ya kara cewa wani abun ba yayi ma Momy sallama ya wuce, suka bishi da kallo suna murmushi.

"Ya gidan ya kowa da kowa?"

"Lafiya kalau, tana gaishe ki"

"Ina amsawa Abbah ka yayi maka maganar tafiyar ko?"

"Eh daga gurin shi na fito yanzu yace min Saturday zan wuce ya za a shirya min komai"

Kamin Momy tayi magana Lil Minal ta fito da gudu ta rumgume masa wuya,

"Oyoyo Bah Babyn Mah"

Hararar ta yayi yana satar kallon Momy, Momy kan ɗauke kai tayi ta mai da hankalinta gurin Tv,

"Bah ina Momie Aniq"

"Ke ba Momie ki ce ba"

"A a tunda ta haifi Aniq ni ba Momie na bace"

Momy ta juyo ta kalleta tana dariya

"Ai na manta tace na zama Momy ta wai tunda taga bana da yara, wai Aniq ta bar masa wacan yayi ta kaya"

"Har da Ni kin bar masa?"

Saif ya tambaya, she's nodded her head

"A a wallahi ai kai ba kai ka haife shi ba"

Duk dariya sukayi, banda ita data yatsine fuska

"Ina kika shafo wannan?"

Yana taɓa ink ɗin take Hannunta

"Ɗakin Anty Safiyyah"

"Toh je kice ina gaishe ta"

"Toh"

Da gudu ta sauka ta nufi ɗakin, Momy ta kalleshi

"Amman kan ba zaka faɗa mata tafiya zaka yi ba, dan zatayi kuka kuma kaga ba hutu suka. Samu ba balle kaje da ita"

"Aa ba zata sani ba ma, ai kinga tafi son zama nan"

"Eh tace fa ku ba iyayenta bane"

Dariya yayi yana amsa kiran da aka masa a waya.

**** **** ****
Kamar yadda Daddy yace masa Ranar Saturday ya bar kasar zuwa Paris, duk yadda Kairat taso ya barta bai yarda ba a dole ta hakure suka tafi tare, tafiyarsu da wata daya Mummy ta haifi kyakkyawar yarta, aka rada mata suna AMINA sai dai Meena suka kiranta, babu yadda Kairat bata yi ba dan tazo bikin amman Saif ya tsaya kai da fata yaki yarda wai shi ba zata barshi can shi kaɗai ba, sa'arta ɗaya ya kusa kammala abunda yazo yi, bayan suna da sati biyu suka dawo, a gidan Mummy Kairat ta sauka, ta kama jaririyar ta rungume sai zumudi take kamar zata haɗe ta, kamar su ɗaya da Kairat sai dai fari na Mummy ne, Mummy kunya take ji sosai wai tayi haihuwar tsufa ita tana haihuwa Kairat. Na haihuwa, a boye take bata nono ko kuma ta saka hijab,sai dai a can kasan zuciyarta farinciki fal aciki dan gani take kamar Minal ce ta yi dawo.

BAYAN WADANSU SHEKARU

Tsiren gudu suke, kowa so yake ya wuce ɗan'uwansa, daga karshe dai Aniq yayi nasara, aiko da gudu yayi gurin Safiyyah yana faɗin

"Anty. Ni nayi na ɗaya"

"Sai wa kuma yayi na biyu?"

Safiyyah ta tambaya tana tataba kansa,

"Ni nayi ta biyu"

Lil Minal ta faɗa tana smirking,

Dariya tayi,

"Good ina Amir ta nawa yayi?"

"Amir yayi na karshe"

Sweets ɗin dake hannunta ta ɗauko ta tana mika musu, duk suka rungume ta suna dariya da yi mata godiya, kansu ta rika shafawa tana hawaye.

Kairat dake tsaye a windo tayi murmushi tana rungume hannayenta, bata sarar ba taji an jama kumatu, tana juyowa ya ɗaga mata gira ya kashe mata ido, mur tasha

"Zaka fara ko bafa gida muke ba"

"Gida muke kan Da nan da can ai duk ɗaya ne"

Ya faɗa yana kara motsowa kusa da ita,

"Dan Allah ka daina kar fa Momy ta fito ta gan mu"

"Toh idan ta gani fa Haramun nayi? Bari ma ki gani"
Dukawa yayi ya ɗauke ta Cak, ita kuma ta shiga cuku cukun ganin ta bar jikinsa har suka faɗa saman kujera still bai sake ta ba,
Yana kokarin kai hannu ya cire mata ɗankwali yaji alamar motsin fitowar Momy, ba shiri ya sake ta ta nufi kofar fita da sauri, ita kuma ta tashi zaune tana gyara jikinta da murmushi a fuskarta.

ALHAMDULILLAH!!!

Godiya ta tabbata ga Allah madaukaki sarki mai kowa mai komai, wanda ya bani ikon kammala wannan littafin, oh Allah i hope for your mercy don't leave me for myself correct all my affairs for me,

Komai yayi farko zaiyi karshe, na gode sosai da irin bibiyar da kuke ma wannan littafin, ina son so na tsakani da Allah,

Mom shuraim
Naffsy
Sadiya sale
Yar fulani
Da feenah
Suby jukus
Zainab ta House of novel 2
Da duk yan Khadeeja Candy novels da taskar khadeeja Candy,da duk grp ɗin da nake ciki duka ina godiya,

My wattpad readers
Ina godiya sosai da irin kaunar ku, ba zan iya lissafo sunan ku ba, ina son ku fisabilillahi
Kairat
Gaudiya
Onmyyasmin
Da ghosts readers duka thank you

Facebook readers
Ina godiya sosai da sosai Allah bar zumunci,

My writers
Miemiebee
Phartiemaerk
Safiyyah Mrs j moon
Kamala Minna
Thank you all

Nagarta Writers Association
Nagartacciyar kungiya mai Nagartaccen suna daga Nagartattun shugabanin da Nagartaccen aiki Kungiyata abun alfarina, Allah kara haɗa kan mu Amin

Sadaukarwar taki ce
Anty Maijidda musa maman biyu ina sonki fisabilillah

Tukuici ne
Ga duk wanda ya jure karanta wannan littafin daga farko har karshe i love you

daga karshe ni Khadija Abubakar Alkali nace muku saduwar alheri, ina rokon gafarar duk wanda na taɓa ɓatawa rai cikin kuskure ko ganganci ko rashin sani, ku yafe min nice taku Khadeeja Candy 2 +2

Stay bless all the best one heart one love 😍

Khadijacandy44@gmail.com
In case



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment