Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da haɗin bakinki bane bakisan ya shigo ba toh wannan saƙon fa waya aika.?”

A hankali ta ɗago ido ta kalli fuskarsa, idonsa sunyi wani irin ja, jijiyar kansa ta tashi kallo ɗaya zakayi nasa ka gane mugun ɓacin rai dake cikin ransa,
A kasale ta mika hannu ta karɓa, sannan ta kai ɗayan hannunta ta share hawayen dake idonta tana duba sakon.

_DEEN. Zanyi miss ɗinki sosai Minal kamin ranar da zamu haɗu_

_MINAL. Na sha faɗa maka Deen ka daina damun kanka aure na da Saif na ɗan lokaci ne kuma zama na dashi ba zai yanke tarayya ta da kai ba_

_DEEN. Bazan iya hak'urin rashin ki ba har na wani lokaci Minal kinsan yadda nake sonki_

_MINAL. Karka damu duk ranar da ya ɗan daga min kafa zan rik'a kiranka_

_DEEN. ok i love you sai na jiki_

_MINAL. i love you too_

SAKON YAU

_MINAL. Deen kazo yanzu idan kana free Saif ya fita amman kayi sauri kamin ya dawo_

_DEEN. ok gani nan zuwa kiyi min kwaliya mai kyau i can't wait to see you dear yau zan zama ango nima_

_MINAL, Ka daiyi sauri karya dawo kasan ba wani daɗewa zamuyi ba_

_DEEN. Yes gani kan hanya mi zan zo miki dashi?_

_MINAL, hot kiss_


Hawayen idonta ne suka rik'a sauka saman wayar, tun tana iya ganin alphabet har ta daina saboda cikar da idonta sukayi da kwallah, yanzu kan bata da hujjar kare kanta ada tana tunani idan da nusar dashi wata kila zai fahimta amman yanzu ba taya zai yarda ba ita ta tura wannan saƙon ba, bayan gashi a wayarta amman ita tasan idan za'a kashe ta a sake sa mata rai a kashe ta ba tasan tayi wannan chat ɗin da Deen ba, hasalima tun ana sauran kwana hudu bikinta bata sake saka shi a idon ta ba, balle a waya,

“Ba ke kikayi ba.?”

Ya tambaya a tsawace fuskarsa kuma babu annuri. Yanzu kan tasan bata da wata mafita babu ta inda zata iya kare kanta, hausawa sukace gudun da ba tsira kwanciya ta fishi, Ganin haka yasa ta kalleshi fuska a raunane tace

“Nice Saif nina aikata”

Duk yadda ransa yake ɓace sai ɓacin ran yanzu yafi na ɗazin saboda ta amsa da kanta ita ta aikata, toh idan kuma bata amsa ba ya zatayi bata da wata mafita sai wannan babu ta inda zata iya kare kanta.

“Miyasa kika karyata farko ? bayan na gani da ido na”

Bata ce masa uffan ba, saboda nauyin da bakinta yayi mata sai ruwan hawaye take kamar kurma, sai kawai ta juya kamar kazar da kwai ya bashema ta ciki ta nufi kofar fita.

“Minal....-”

Cikin muryar maza yayi mata kiran muryar dake da wahalar fassara.
Cak tayi tsaya bakin kofar, ta lumshe ido tana haɗiye wani kololo daya tsaya mata a wuya,

"Thank you so much Minal I really appreciate it”

Har lokacin bata ji tana iya furta masa wata kalmar ba. Buďe idon tayi ta tattara rigarta ta nufi ďakinta da gudu,
Saman gaďo ta faďa ta rushe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, tana jan gashin kanta, sosai sosai tayi kukan nan da nan idonta ya rumburo, Zufa ce ta shiga karyo mata ta ko ina sai numfashinta ya rika fita sama-sama, da sauri ta tashi ta cire rigarta ta shiga bathroom ta tsakarwa kanta shawa.


**** **** ****

Safa da marwa Saif ya rikayi cikin ďakin bayan fitar Minal, Tunanin yake miyasa Minal tayi masa haka miyasa ma ya aureta, bayan yasan halinta kuma ta riga ta faďa bazata ta6a canjawa ba, ? _amman miye na mamaki ai daman can haka halinta yake tunda bata ďauki mu'amala da wasu mazan wani abun ba auren da nayi mata nima dai nati ne kawai dan ganin na canja mata hali,_
Wata zuciyar ta soma tunasar dashi abunda ya manta, Amman fa Minal ba karamar yarinya bace a matsayin da take yanzu yaci ace tasan abunda ya dace da wadda bai dace ba, kai Minal tasan komai da gangane take tunda har tasan ta kula wasu mazan ta 6oye ma mijinta, shiyasa Huda take burge ni nasan tana yimin ba dai-dai ba amman bata yarda ta kula wasu mazan tana kokarin kare mutuncinta tana taya ni kishin kanta sosai,

“I hate you Minal.. i hate her so much.-”

A fili ya furta zuciyarsa cike da tsanar ta, Gaba ďaya ma jin yayi ya tsani gidan dan daga ďakinsa yana jiyo kukan da take a ďakinta, Wani dogon tsaki yaja ya fice daga ďakin,
Da wani irin karfi ya buɗe Motarsa yaja ya rufe still da karfin kamar ita ce tayi masa ƙaifin, yadda ya ruƙa horn sai da ya bawa masu gadin tsoro, da gudu suka buɗe masa gate ya fice yana rike da sitarin da wani irin karfi.
.
Ya daɗe zaune cikin motar kansa jingine a sitari sai ajiyar zuciya yake saukewa, daga bisa ya fito ya nufi kofar falon hannayensa zube cikin aljihu yana tafiya guda guda, karaurawar dake gefen ƙofar ya danna ya jingina da ƙofar yana lumshe ido,
Jin an buɗe ƙofar yasa ya ɗago ya kalleta, ita kuma ta sakar masa murmushi tana faɗin,

“Ango kenan shine ƙka tsaya a waje kamar baƙo”

Baice mata komai ba sai kallonta yake fuskarsa ba yabo ba fallasa, daga bisani ya jata zuwa jikinsa ya rumgumeta, yana sauke ajiyar zuciya,

“Ina sonki sosai Huda ina sonki”

Yana faɗar hakan tayi murmushi ta ƙara ƙanƙameshi a ranta tana faɗin _Ta faru kenan_ A fili kuma sai ta ƙara shigewa jikinsa,

“Nima ina sonka sosai Saif”

Sun daɗe a tsaye gurin kowa da abunda yake saƙama zuciyarsa, zuwa can ya saketa jin wayarsa na ruri ya ɗauko wayar daga cikin aljihusa yana duba mai kiran, Nasir ne abokinsa hakan yasa shi saurin dannan picking ya kara wayar a kunne,

“Hello Nasir kana ina ne?”

“Ina majalisa naga kayi min four miss calls lafiya dai?”

“Lafiya amman ba lau ba i need to see you”

“Ok kazo ina gida ai”

“Ok gani zuwa”

Yana kashewa, ya kalli Huda

“Je ki kwanta zan leƙa gari”

Wani maraurauce fuska tayi

“Ba zaka shigo ba?”

Kai kawai ya ɗaga mata dan baya jin iya yi mata magana sosai, tsaye tayi tana kallonsa zuciyarta cike da farin ciki, tana ganin ya shiga motarsa ta rufe ƙofar da sauri ta nufi ɗakinta da ziman kiran Safiyyah,

☆ ☆ ☆

Nasir yaja wani dogon numfashi, yana tattara girarsa yace,

“Kai yanzu Saif ka tabbatar da da kanta ta kira sa?”

“Haba Nasir ga abu ƙarara na gani tayi masa tex sannan kuma ta faɗa da bakinta itacw tace yazo”

“Sai naga kamar Minal ba zata iya yi maka haka ba dan Minal tasan miye aure and..-”

“And what..?”

Saif ya katseshi yana masa wani kallo,

“Ba yaro bane ni Nasir nasan mi nake yi duk abinda ta aikata da ganganta aikata shi, kawai rainin wayo ne yayi mata yawa take son nuna min kamar bata san miye duniya ba”

“Saif ba haka bane Ya kamata ka kwantar da hankalinka ka bincika komai yadda ya kamata Baka sani ba ko wani sherin ne”

“Ba wani sheri malam kai duk yadda zakayi ka kare Minal ka iya wazai mata wani sheri kawai malam ka faɗa min abun yi tunda kace karna sake ta”

“Saki ba yi bane Saif yaushe akayi auren nan ko sati anyi da zaka cw zaka saketa ? yanzu idan ka saketa zaka jefa zuciyarta data mahaifiyarta cikin wani halin, kuma ka koma abun labari”

“Ba damuwa ta bace dan ta shiga wani halin ai ita batayi tunanin halin da zan shiga ba kadan yadda nake ji yanzu”

Nasir ya dafashi,

“Nasan kana da zafin kishi Saif amman ka kwantar da hankalinka ka koma gida yanzu gobe da safe zanzo gidan”

Tashi yayi, tsaye yana jan tsaki,

“Nifa banga wani abun da zaka zo kayi min ba malam”

“No Saif ba haka bane, kasan aba son yanke hukunci cikin fushi kayi haƙuri har zuwa gobe please”

Rausayar da kai yayi ya nufi ƙofar fita Nasir na bayansa yana bashi maganganu.



*** *** ***

Daren ranar baci ƙwara yayi daga idon Minal, ko alamun bachi ba taji ba balle bachin, a zaune ta kwana tana kuka, har aka kira sallah asuba. bayan tayi sallah ta dawo parlour ta zauna idonta sutun sutun ko gani batayi sosai, juyi ta riƙa yi saman kujerar tana jin tsanar duniyar da take ciki.
[9/13, 11:19 PM] Auntie Candy: BABBAN GORO

NA

KHADEEJA CANDY


*29*


Wasa-wasa yau kwanan Minal huɗu bata saka Saif a ido, duk tsawon lokaci ba tada abinci sai kuka iya karta ta sha ɗan ruwa tea ko shi kaɗan daman can Minal ba mace ce mai son cin abinci ba, duk wayar da suke da Mummy bata taɓa faɗa mata ba halin da take ciki ba, duk da Mummy tasha tambayar da koda wata matsalar ne saboda yanayin da take ji na muryar ta ba kamar yadda ta saba jinta ba, Minal bata taɓa nuna mata wani abun ba sai dai tace mata ba komai.

Juyi take tayi saman gado, hawaye nayi mata zuba, tunanin halin da take ciki take da kuma wadda zata shiga, miyasa Deen yayi mata haka? Miyasa Saif ya kasa fahimtarta? Tashi tayi zaune tana tunanin kodai wani aljanin ne yayi mata haka a iya saninta bata san tayi wannan chat ɗin da Deen ba, sannan tana mamakin yadda aka yi ya shigo gidan har yakai cikin ɗakinta ba tare da sanin ta ba? Ita tasan Deen ba zai mata haka ba kuma idan ma yayi mata toh wannan sak'on fa da bata san ta tura ba ya akayi hakan ya faru da ita.

“Anty Minal...-”

Kiran da akayi mata ya katse mata tunani kuma ya tsorata ta, duk da muryar maiyi mata kiran tayi kama da ta Safiyyah amman bata gama tantancewa ba tunda yanzu ta gama tunanin aljanu kuma bata ji shigowar kowa ba sai kiran sunan nata,
Tashi tayi tsaye tana kallon ƙk'ofa zuciyarta sai rawa take,

“Assalamu alaikum Anty”

Safiyyah ta kunno kai cikin ɗakin tare da sallama,
Saida Minal ta sauke ajiyar zuciya sannan ta amsa mata tana ƙirƙiro murmushi

“Wa'alaikissalam Safiyyah”

Ta amsa tare da zaunawa a kusa da ita,

“Na'am Anty Lafiya kike kuka?”

Sai a lokacin ta tuno da hawayen dake fuskarta, da sauri tasa hannu ta shafe tana dariyar da bata kai zuci,

“Lafiya kalau kai ido na ne yake ciwo ya su Momi”

“Lafiya ƙalau suke tare muke da Yaya Nasir ƴyana Falo yana jiranki”

Jimmm ta ɗanyi, azuciyarta tana tunanin ko yana tare da Saif ne, bata son wani yasan halin da take ciki duk da tasan bata aikata ba, amman tasan tunda Saif ya kasa fahimtar ta babu wanda zai fahimce ta, dan haka bata son wani yaji, sai ta sake sauke ajiyar xuciya sannan ta kalleta,

“Oke jeki ce masa gani nan zuwa”

“Ok”

Ta faɗa tare da juyawa tana murmushi. Da saƙe-saƙe ta fito ɗakin ta nufo falon har ta zauna bata san ta zauna ba saboda tunanin da take,

“Lafiya?”

Nasir ƴya buƙata, ta kalleshi tare ɗa faɗaɗa murmushinta,

“Lafiya ƙalau gata nan fitowa”

Kai ya ɗaga mata ya ciro wayarsa yana danne-danne. Sautin ƙarar takalminta yasa shi ɗaga kai a hankali yana kalleta,
Yadda take tafiyar kamar wata marar lafiya ko kuma nace marar lakka, ta naɗe jikinta da sari ja irin na shuwa arab, yayi mata kyau sosai kamar wata balaraba, kasa ɗauke mata ido yayi har ta zauna.

“Ina wuni Nasir”

Ta gaisheshe kanta na kallon ƙasa,

“Lafiya ƙalau Minal”

Ya amsa mata still yana kallonta, sai a lokacin yaga ramar da tayi dan har kashin idonta ya fito kamar wata mai ciyon ƙaujamau, Tausayinta ne ya shiga fisgarta ganin yadda idonta ke kwance da ruwan hawaye, kodai wani abun Saif yake mata? Tambayar taya jefa fama kansa kenan yana kallonta,

“Anty kamar akwai abunda yake damun ki?”

Safiyyah ta tambaya fuskarta na nuna damuwa kamar gaske,

“Babu abunda ƴyake damu na”

Ta amsa mata ba tare data kalleta ba,

“Amman Anty naga kinyi rama sosai kuma fuskarki na nuna akwai damuwa a tare dake”

“Babu komai Safiyyah Kinsan daman lafiya bata ishe ni ba”

“Haka ne Allah ya baki lafiya”

“Amin”

Nasir ya kalli Safiyyah,

“Tashi kije waje zamu yi magana”

Ta ɗanyi murmushi,

“Yaya Nasir kenan ba sƙon Yaya Saifu bane ai zaka iya faɗa ai”

Ya haɗe mata fuska,

“Bazan faɗa ba ke kika aiko ne ko kuma lokacin daya bani saƙon a gabanki ya bani? Kinfa san bana son iskanci ko?”

“Yaya miye abun faɗa daga magana, naga ni Ƴar'uwar Saif ce kuma..-”

Ya katse ta, a fusace

“Ke tashi ki fita nace kona ɓata miki rai shiyasa da zan fito kika ce zaki biyo kinsan bana son gardama ko?”

Ta fusata sosai, hakan yasa bata sake musa masa ba ta tashi, duk da taso taji abunda zai faɗa ɗin, amman kuma tasan halinshi zai iya yi mata tass a gaban Minal,

“Na tafi anty”

Ta faɗa tana kallon Nasir,

“Ba awaje zaki jirashi ba”

Minal ta tambaya ganin yadda take gyara gyalenta da rataya jika,

“A a daman ni gida zanje sai nace ya rage min hanya”

“Allah ya kiyaye”

“Amin”

Bata sake cewa Nasir komai ba ta fice,
Bayan kamar minti biyar da fitar ta, Nasir ya kalli Minal yace,

“Mi Saif yake miki wanda har tasaki rama haka”

“Baya min komai babu wata matsala a tsakanin mu”

Ta amsa masa muryarta a raunane,
Hakan ya ƙara karantarda shi halin da take ciki na damuwa,

“Bai kamata ki ɓoye min ba Minal Saif ya faɗa min komai, amman ni ban yarda da abunda ya faɗa min ba saboda nasan ba zaki aikata ba”

Sai a lokacin ta kalleshi, suka haɗa ido,

“Miyasa kace haka Nasir bayan ga gaskiya ƙarara na na aikata”

“Baki aikata ba Minal ba zaki aikata irin wannan abun da auren ki ba zan iya yarda kin kira Deen cikin gidanki ko kuma nace ya kawo miki ziyara amman ban yarda zaki aikata wani abun ba kamar yadda Saif yake zargi,
Bai kamata ace kin bar abu a ranki ba idan wani abun Saif yake miki ki faɗa min Minal?”

“Baya min komai Nasir hasalima tun ranar da abun ya faru ban sake sashi a ido ba, be sake shigowa gidan nan ba kuma idan na kira baƴa ɗauka in na masa text baya reply”

Tagumi tayi tana goge hawayen da suka zubo mata wanda taso ta tsaidasu suka ƙi tsaiduwa,

Wani irin tausayinta ne ya fusgi zuciyarsa, sai yaji kamar a tsokar jikinsa hawayen suke zuba haka yaji kamar ya tashi ya koma kusa da ita ya share mata hawayen ya rumgumeta,
A take tsanar Saif ya shiga zuciyarsa, miyasa yake gallaza mata har haka? dan me zai ɗauke mata ƙafa har na kwanaki huɗu, akan abunda zuciyarsa ta tabbatar masa da bata aikata ba, shi taya ma zai faɗa mata saƙon da Saif yace ya faɗa mata? Sai yanzu ya gano dalilin Saif na shirya tafiyar da yayi ba tare data sani ba, kuma har yake son tafiyar ba tare daya faɗa mata ba, ko ƴyanzu ma in ban da ya tirsasashi da ba zata sani ba,
Tunani yake yadda Saif yake amsa masa maganar duk da yayi masa ta Minal da kakkausar murya, wanda ke nuna har yanzu cikin ɓacin rai yake,

“Saif yanzu kana ganin kayi tafiyar nan da Minal.baifi ba a maimakon Huda?”

“Da huda nake ra'ayin tafiyar Nasir ban ma faɗa ma Minal ba kuma bazan faɗa mata ba sai dai taji na tafi”

“Saboda mi naga ai itama matarka ce kuma hakkinta ne idan zakayi tafiya ka faɗa mata, ka kuma tambayi ta idan tana buƙatar wani abun”

“Toh baxan yi mata hakan ba au nasan dai abinci da yake cikin gidan zai isheta har na wani lokacin, dan Allah ka daina yi min maganar Minal Nasir indai kana son mu zauna lafiya”

“Amman dai kasan Allah ne ya ɗora maka hakki haka ko”

Ya fita cikin motar yana faɗin,

“Na wakiltaka kaje ka faɗa mata kayi mata duk abunda ya dace”

Bai tsaya jiran abunda zaice ba, ya nufi bayan motar ys fiddo kayan da suka siyo ya nufi cikin gidan,
Nasir na kokarin ribas Safiyyah ta fito daga falon Huda ta nufoshi tana tsayar dashi,

“Ya akayi ne?”

Ya tambaya bayan ya tsaya ɗin,

“Dan Allah Yaya ka sauke ni gida”

“Ba gida zanje ba gurin Minal zani Saif ya ban sƙo na kai mata ne”

“Oke muje kawai”

Da sauri ta shiga motar. Cike da son ta bishi ɗin dan taji wane saƙon ne Saif ya bashi ya kai ma Minal.
Gyara zaman da tayi ya dawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi,
Ya kalleta a kasale muryarsa kuma na nuna rashin jindaɗi yace,

“Saif yace na faɗa miki tafiya ta kamashi zuwa Londom kuma gobe zai wuce duk abunda kike so ki faɗa min”

Da sauri ta kalleshi hawayen dake idonta suka ɓalle, suka cigaba da zuba, bakinta na rawa tace,

“Toh.”

Da sauri ta tashi ta nufi dan samun damar yin kukan da take haɗiyewa,
Shima tashi yayi tsaye, yana kiranta, bata amsa masa ba saboda halin da take ciki bata son juyo balle ma har ta dawo.


Ƙasan carpet ta faɗi tana wani irin kuka abun tausayi,
Ƙasa tayi mata zafi gashi kuma yanzu ƙsaman nason kama mata da wuta, Saif zai tafi ya barta bai damu da duk halin da zata shiga ba, miyasa har yanzu Saif ya kasa fahimtarta ko yayi mata uzuri?
Da sauri ta ɗauki wayarta da makulin matarta ta bar gidan. Tuƙi take tana kuka kanta babu ɗankwali jikinta ko mayafi babu daga ita sai doguwar riga ta isa gida,
Sai tayi fakin wani tunin yazo mata, shin mi zata cewa Mummy wane hali mummy zata shiga idan ta faɗa mata? Shin mummy ma zata yarda da bata aikata ba?
Ganin bata da amsoshi waɗannan tambayoyi yasa ta share hawayen dake idonta, ta buɗe motar ta fito ta nufi cikin gidan.

“Assalamu alaikum”

Ta shiga falon da ƴar far'ah kamar gaske, duk idonta a kumbure yake,
Tsohuwa ce ta amsa mata cike da mamakin abunda ya kawo ta gidan yanzu gata kuma a yamutse,

“Wa'alaikissalam Minal kece haka?”

“Nice Tsohuwa ya gida?”

Ta faɗa tana kallon Kairat dake kwance saman doguwar kujera tana bachi,

“Gida lafiya kalau Kairat ce kawai ba lafiya”

“Miya same ta”

Da sauri ta karasa kusa da ita, ta rame sosai tayi baƙi kamar ba ita ba,
Tsohuwa ta taso daga inda take ta nufo Minal tana faɗin,

“Tun ranar da kika tare washe gari ta tashi da rashin lafiya kuma Hajiya tayi tayi ta kaita asibiti ya ki ankira likita ya duba ta taki yarda a dole aka sama ta ido ko abinci kirki bata ci”

Tausayinta ne ya kamata Minal, nan da nan kukan dake tare da ita yayi kokarin dawowa, a take ta manta da nata damuwar, tana kallon fuskar Kairat, mi yake damun yar'uwata haka? Wane irin ciwo ne wannan miyasa bata son taje asibiti? bayan nasan Kairat da tsoron ciwo!
A hankali ta kai hannu ta taɓa jikinta, hawayen dake idonta suka zubar Kairat a fuska, Hakan yayi sanaɗiyar tashinta daga bachi,

Tana ganin Minal ta zabura ra tashi zaune, tana kiran sunan nata da kasallaliyar murya,

“Minal kice?”

“Nice Kairat mi ke damunki?”

“Aike ya kamata nayi ma wannan tambayar kinga yadda kika rame?”

Hannu takai ta taɓa wuyanta, sai kuma damuwarta ta dawo mata arai, tashi tayi ta nufi hanyar ɗakin Mummy,

“Minal Ina Saif...”

Tambayar ta tayi mata tasa ta juyo, ta kalleta,

“Yana gida gobe zaije London shine yace nazo gida”

“Kizo gida kamar ya?”

Kairat ta tambaya fuskarta ɗauke da mamaki. Duk yadda Minal tayi kokarin ɓoye damuwarta sai da ta bayyana a fuskarta saboda hawayen da suka shiga zubo mata, Duk da rashin kuzarin da Kairat take ji bai hana ta tashi ta rika hannu Minal suka nufi ɗakinta,

** ** **

Da kanta ta zaunar da ita saman gadon tana kallon fusakarta,

“Minal faɗa min meke damunki?”

Idonta na hawaye tace,

“Kairat jindaɗi na ragaggene, mafarkina yankanke ne a duk lokacin dana hango haske sai naga karshensa duhu ne, bansan nayi ma duniya take juya min baya ba i know rayuwata yar kaɗan ce amman naso jindaɗina na kasance dogo sai gashi ban samu haka ban Duk ƙlokacin da farinciki na raɓe ne toh bakin cikin da zai shafe ni sai ya fishi yawa”


Kukan da take yasa Kairat kuka,

“Minal ki faɗa min abunda yake damunki mi Saif yayi maki?”

Bata ɓoye mata komai ba, cikin abunda ya faru komai sai da ta faɗa mata.
Sosai jikin Kairat yayi sanyi, sai dai itama ɗin ta yarda da Minal ba zata iya aikatawa ba amman miyasa Deen ɗin yayi mata haka? Waya shirya mata wannan abun dole a kwai wani abu akasa, tausayin Minal ya kamata akoda yaushe cikin bakin ciki take Sai yaushe jindaɗin ta take mata fata zaizo mata, farincikinta a yanzu Saif ne kuma shima ya juya mata baya.
Hannu tasa ta share mata hawayenta, itama tana kuka, tace,

“Kiyi hakuri Minal zanyi masa magana kinji?”

Kai Minal ta ɗaga mata duk da tasan ko tayi masa maganar ba yarda zaiyi ba,

“Please Kairat karki faɗama Mummy zata iya shiga wani hali kinji?”

“Bazan faɗa mata ba”

Suka rumgume juna suna kuka.
Sun ɗauki lokaci a haka sannan ta taso ta fito daga ɗakin ta baro Minal.

Gardem ta nufa ruke da wayrta tana danna ma Saif kira,
Sai da tayi masa miss calls biyar ana shida ya ɗauka,

“Ya akayi.?”

Muryar Saif ta ratsa jiyoyin jikinta da kunnenta ta game ilahirin jikinta,
Wani dogon numfashi taja sannan yace,

“Dan Allah dan Annabinsa ina son kaganinka na haɗa ka da girman Allah”

“Me xanyi miki.?”

“Kazo dai yanzu ina son ganinka dan Allah da ya halince ka”

Bai bata amsar zaizo ko bazai zoba sai kawai taji ya katse kiran, lumshe ido tayi ta sauke ajiyar zuciya, ta juyo jikin a mace ta dawo falo.

Toh yanzu ya zata ɓulloma ƙlamarin ba lallai bane ya gansu da maganar ta waya sai dai kuma tasan ba zai zoba tunda ya kashe mata waya, toh kodai ta kyaleshi, wata zuciyar tace baza iya jure ganin Minal haka ba, kuma tasan Mummy ma idan taji zata iya shiga wani halin.
Tana cikin wannan tunanin mai gadinsu ya shigo yace Saif na sallama da ita a waje,
Tashi tayi da sauri bayan tace masa yace tana zuwa ta shiga ɗaki ta ɗauko hijab ɗinta ta nufi kofar fita,
Tsaye ta hangonshi jikin motar hannayensa zube cikin aljihu yana sanye da wata shadda blue colour ta karɓi jikinsa sosai ɗinki yayi masa kyau, fuskarsa babu annuri,
Ita kuma fuskar tasa take kallo har ta karasa kusa dashi,

“Na gode da kazo Sannu da zuwa”

“Ba godiya nazo kiyi min ba ba kuma tarbarki nake so ba dalilin kiran nake son ji”

Ya faɗa kamar a fusace, ajiyar zuciya ta sauke murya a kasale tace,

“Dan Allah kazo mu shiga ɗakin baki sai muyi maganar”

Baice mata komai ba sai kawai ya nufi hanyar ɗakin bakin ita kuma ta rufa masa baya, tana kare masa kallo.


Bayan sun zauna, ta kalleshi tana murzar hannunta tace,

“Saif Minal ta faɗa min abunda ya faru, nasan zakayi wahalar fahimtar ta amman ....-”

Hannu ya ɗaga mata,

“Idai maganar Minal ce toh ki hutar da kanki babu ta yadda zaki juya min kwakwawa alhalin ga gaskiya ina gani da

Please Login or Register in order to submit comment