Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mummy waya faɗa miki?”

“A shanun talla naji ina mai gidan naki?”

“Ya fita tun ɗazu Mummy ina Abbah na”

“Abbah ki? ai kinsan inda yake”

Murmushi tayi

“Haba Mummy ya kamata ace kun wuce wannan gurin tuni tun yaushe ake abu ɗaya dan Allah! haba Mummy ki amince masa mana Mummy yanzu ko dan karamcin da Abbah yayi miki ba zaki yarda ki aure shi ba”

“Yayi min ne saboda Allah dan Allah ki rufe min baki ko ruwa baki kawo min ba zaka ɗauko min wani shirme”

“Haba Mummy Abbah fa ko ke ko bake ba ya riga ya shirya aure a yanzu da aje a ɗauko mana wanda bamu sam halinta ba fa ao kara ke kuma kinga Hajiya ma da kanta ta roke ki miyasa kike son watsa musu kasa a ido ne? wallahi mummy sam bana jindaɗi in kina cewa Dr. Isma'il zaki aura ko dai dan yafi Abbah kuruciya ne?”

Mummy ta zaro ido

“Kairat zaki tashi ki kawo min ruwa ko sai na bar miki gidan ki?”

Tashi tayi tana dariya ta mika mata lil minal ta shiga kicin ta ɗauko mata  drinks da yan kayan ciye ciye ta dire mata.
   Sunyi kusan awa biyu suna fira, Mummy na batun tashi Saif ya shigo, yaji daɗin ganinta sosai dan rabonta da gidan har ya manta duk rashin lafiyar da Kairat take yi bata leko gidan ba har taji sauki,  Cikin mutumci da girmamawa suka gaisa Mummy take tambayarsa ya mai jiki

“Jiki da sauki”

“Ta warke kuwa?”

“Aa har yanzu tana nan abunda dai sai dai hamdala”

“Allah ya sauwake amman da kun gwaɗa gurin Deen ko Allah zai sa a dace”

Kairat ta mere baki

“Wallahi Mummy nayi ta masa magana yaki yarda shi har yanzu yaki ya manta abunda ya faru”

Mummy ta kalleshi,

“Saif ba a son musulmi da riko, ka amanta abunda ya faru kuma ai ba wani abun zaka je nema ba sai lafiyar yar'uwarka kuma ba kyauta zai maka ba”

Kasa kasa ya watsa ma Kairat harara,

“Shi kenan Mummy zan gwada insha Allah”

“Toh Allah ya sa a dace ni kan bari na tashi kar baki da zanyi suzo ba su tararda ni ba”

Sallama tayi ma Saif, Kairat kuma ta rakata har gurin mota tana mata maganar Abbah ta, Mummy dai bata ce masa uffan ba taja motar ta ta rufe.


YAU MA SAI NACE VOTING AND COMMENTING?


55

Sai da taga ɓacewar Motar Mummy sannan ta juyo, tana shigowa Saif ya cafkota ya wani walkato ta ta juya ta juyo ta faɗo korjinsa, hannunta ya ɗan matse fuskarsa na kan kafaɗarta yayi mata magana kamar mai raɗa

“Wa yace ki daɗe?”

“Ba kowa ba”

Ta faɗa da dariya tana son kwace hannunta dan taji zafin rikon da yayi mata, shi kuma yaki sakinta sai kanshin turaren wuyanta yake shaka, suna haka Lil Minal ta rarrafo tazo ta kama kafan babanta hakan yasa ya saki Gimbiyar ya ɗauki yarsa yana murmushi, dariya tayi ta rika zallo Kairat kuma ta nufi kicin tana ɗan turo masa baki.

            Bayan sun gama cin abincin dare Kairat take kara masa maganar Safiyyah, ta damu da ita a yanzu tsaɓanin baya da ba ruwanta da ciwonta ko dan yanzu taga abun yana damun Momy da Saif ne oho! Ita kanta Safiyyah yanzu ta zama abar tausayi bata magana kuma komai bata iyawa sai idan gwaggo ce tayi mata ko kuma yar aikin da ka ɗaukar mata, wani. Lokacin kuma bata komai saikin kuka, ga magani anyi nema har an gaji har yanzu shiru. Kansa ya shafa ya ɗan gunɗe baki

“You know how much I hate him”

War tayi da ido

“Oh my dear, kar wannan ya dame ka ai ba cewa nayi ka so shi ba lafiyar Safiyyah zaka nema ba wani abun ba ko dan Gwaggo da Momy and Kalbi babu abunda zai iya mana yanzu abunda yayi maka a baya zafin son ta yasa yayi maka haka tun da yana tunani zaka iya sakinta shi ya aure,

  Kuma abunda ya faru a baya ai ya zame maka darasi yanzu wani ba zai kawo maka wani abun ka rufe idonka ka cutar da kanka ba”

Iskar bakinsa ya busar

“Fine amman shine zai zo ya same ni a nan”

Dariya tayi

“Haba dai wanda keso ba shi ke biya kuma wallahi kasan Deen ba xai kawo kansa gidan nan dan matsalar Safiyyah ba, karka manta yanzo ka hana n ganshi kuma ni yanzu ko number sa bana da”

“Me kike Nufi ke nan mune zamuje?”

“Idan mun je ai ba yada kai bane, kuma ka samu Momy ku tattauna”

Tashi yayi ya rika hannunta,

“Mu rufe babi wasu muyi na mu babin zo muje mu kwanta”

    Tashi tayi tana wani irin yauki da jiki ta ɗora kan ta saman kafaɗarsa, hannunsa sarke da nata suka nufi upstairs.

         
Washe gari bayan ya tashi daga aiki ya biya gurin Momy,  sai da yayi kamar yana yi sannan Momy ta sake dashi, dan fushi take dashi wai yau kusan kwana nawa bai leko gidan ba, shi dai hak'uri kawai yake bata yana dariya yasan ba dan komai bane sai dan Safiyyah zata ce ya daina kula da ita ne,

“Ya mai jikin?”

Ya tambaya yana kallon yadda zata amsa masa,

“Jiki yana nan yadda yake  jiya Gwaggon ku tazo ta ɗauke ta wai zata kai ta wani gurin a gwada a gani”

“Wai ita bata gajiya da na hausar nn ne, ni da har nace ko mu kai ta gurin wani mai kula da masu irin ciwon mu gani”

“Toh ni ai lamarin ne yanzu na rasa gane ma kansa kullum abu ɗaya”

“Jarrabawa ce idan Allah ya kawo ma bawa sai hak'uri”

“Sai ka bari idan sun dawo sai muje gurin da kace ɗin Ya Kairat da lafiyar jiki?”

“Taji sauki sosai yanzu ai”

“Allah ya kara sauki amman nace Ba zata yaye Lil Minal ba? Kar tazo tasha ciki abu ya zama biyu gata tayi jikinta”

“Toh wai Momy Lil Minal bata saba da shan komai ba banda nono kuma kinga cikin ai wata huɗu ne yanzu kin ga akwai sauran lokaci”

“Aifa sai ka yi, wato har yanzu baku fara bata komai ba ko! Ko yar madarar nan ta yara ai kwai saba mata da ita”

“Za a bata”

Ya faɗa yana ɗan sosa kai, Momy ta taɓe baki

“ku dai kuka sani, idan ba a sharar masallaci ba ayi ta kasuwa”

Shi dai dariya kawai yake. Sai kusan la'asar ya bar gidan, Yana ɗaukar hanyar gidansa gabansa ya soma faɗuwa, sai jikinsa yayi masa ba daɗi cikin wani yanayi ya isa gidan, bayan yayi parking ma sai da ya ɗan daɗe cikin motar sannan ya fito ya nufo cikin gidan,

Da sallama ya shigo jin ba'a amsa masa ba yasa ya zauna saman kujera yana

“Mom Lil Minal I'm back”

Shiru nan ya tashi ya leka kicin bai ganta ba, kai tsaye ɗakinta ya nufa yana tura kofar ɗakin da faɗin

“Madam ko bachi kike ne?”

Nan ma ba kowa a ɗakin sai Lil Minal dake bachi tana sauke ajiyar zuciya, da ala kuka tayi har ta gaji bachin ya ɗauke ta, bathroom ya buɗe nan ma bata ciki a nan ne hankalin sa ya fara tashi

_Toh ina ta shiga.?_

Ita ce tambayar da yayi ma kansa, a nan ya juya ya shiga ɗakinsa nan ma bata nan cikin sauri ya dawo parlour yana tunanin gurin da zata shiga ya dai san bata fita bata faɗa masa ba to ina ta shiga?, gurin mai gadi ya nufa yana tambayarsa, nan shima yace shi dai bai ga fitar ta ba, dawowa yayi cikin parlour ya danna mata kira sai kawai yaga wayar saman kujera tana ringing, ɗaukar wayar yayi yana dubawa  can kuma ya aje ya nufi hanyar da zata sada shi da Garden,

Kwance ya hango ta kasa dafe da ciki, cikin sauri ya k'arasa yana kiran sunan ta, durkusawa yayi yana girgiza ta ganin bata motsa ba yasa ya ɗago ta ta ɗora ta saman kafafunsa,

“Lafiya mi ya same ki?”

Cikin firgice ya tambaya, hawaye ne yake mata zuba bata iya magana sai cikin da ta sa hannu ta dafe, hannu yasa gurin cikin yana dubawa

“Miya faru ciwo yake miki ne?”

Kai kawai ta iya ɗaga masa sai hawaye take, da sauri ya ɗauko ta ya nufo parlour da ita, saman jikinsa ya rungume ta, ita kan kallonsa kawai take tana hawaye, ganin abun banayi bane yasa ya ɗauke ta ya nufi asibiti da ita, yana isa aka wuce da ita Emergency taimakon gaggawa aka shiga bata, a waje Saif ya tsaya hankalinsa a tashe ya ciro wayarsa ya danna ma Mummy kira ya sanar da ita, bayan ya kashe ya kira Momy ita ya faɗa mata, yana kokarin zama Lil Minal ta faɗo masa a rai, cikin sauri ya ciro wayarsa ya saki kiran Momy, bugu ɗaya ta ɗauka

“Hello Momy na manta na baro Lil Minal gida a tura Lubna ta kula da ita yanzu Please”

“Okey gamu nan zuwa”

Bayan ya kashe wayar ya dafe kansa yana tunanin abunda ya samu matarsa haka, ba ayi minti goma ba sai ga Mummy ta iso gurin hankalinta a tashe,

“Ina take Saif?”

Shine abunda Mummy take tambaya cikin tashin hankali, gaishe ya fara yi ta amsa masa sama sama, tana kara tambayar sa ina take,

“Tana ciki Basu fito ba har yanzu”

“Toh wai miya same ta ne? ”

Bakin abunda ya sani ya faɗa mata dan shi kansa bai da takai maimen abunda ya same ta, zaunawa tayi a ɗayan kujerar tana kallon kofar ɗakin Kairat da take ciki. Bayan kamar minti arba'in likintan ya fito ɗaga ɗakin tare da wasu nurses guda biyu mata, da sauri Saif ya tashi da Mummy suna tambaya likitan ba'asi,

“Gaskiya ba mu gano ko minene ba a yanzu amman dai ko minene a cikin cikinta yake yanzu za muyi mata hoto ne sai mu bincika cikin nata”

Ya faɗa bayan ya sauke ajiyar zuciya,

“Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un”

Shine abunda Mummy ta faɗa ta faɗi zaune saman kujera, Saif kuma yasa hannu sa aljihu yana kallon Momy da ta iso a yanzu,

“Lafiya miya same ta ne?”

Babu wanda ya iya amsa mata daga Saif har Mummy, likitan ya kalli Saif yana faɗin

“Ina son muje office kayi mana bayanin abunda tace tun daga safe zuwa yanzu”

Kai kawai ya ɗaga masa ya bisa  baya jiki ba gwari, wani file ya karɓa hannun nurse ɗin bayan sun zauna Saif ya soma masa bayani

“Tea kawai muka breakfast da shi da safe da bread sai egg shima bana jin tace dan tun da ta samu cikin nan bata son kwai sosai sai, ni dai daga nan na fita ban sani ba ko a kara cin wani abun bayan fita na”

Bayan ya gama rubutawa ya mika masa file ɗin,

“Zaka sa mana hannu a nan”

Bayan yasa hannun ya kalli likitan yace

“Dan Allah kayi duk abunda ya dace Please”

“Insha Allah zamu yi duk abunda ya dace”

Juyawa yayi jiki ba gwari ya fice daga office ɗin.
   
Haka likitoci suka wuni akan ta suna bincikar ta, amman basu gano mike damunta ba dan ko hoton da kayi mata basu ga komai ba, abu ɗaya suka sani shine ko minene a cikin cikinta yake.
   Sai dare Mummy ta kira Hajiya Suwaiba ta faɗa mata, ba ɗauka lokaci ba suma suka iso tare da kannen Kairat da kuma Nafisa yayar Kairat,
Abunda likitan ya faɗa musu shi Mummy ta faɗa ma Hajiya Suwaiba, babu wanda hankalinsa bai tashi ba ganin irin halin da take ciki kuma gashi likitocin sunce basu gano abunda yake damunta ta,

Duk yadda Mummy taso Saif yaje gida kiyawa yayi a dole suka kyale shi ya kwana asibitin tare da ita, lokaci lokaci ta kan buɗe idonta ta kalleshi sai kuma ta rufe kamar mai bachi duk maganar fa yayi mata ba zata buɗe idon ba, balle ta motsa ko tayi masa magana, a yanayinta ma kamar bata san inda take ba,

Har gari ya waye Saif ba rumtsa ba, a masallacin asibitin yayi sallah asuba, sannan ya sake dawowa ɗakin, kujera yaja ya zauna ya haɗa hannunshi da nata ya rik'e idonta taf da hawaye, ji yake kamar rasa ta zai yi,

“Allah ya baki lafiya i Love you so much”

Ya faɗa yana lunshe ido yana sauke ajiyar zuciya yana haka Mummy ta shigo, bayan sun gaisa ta tambayi shi jikin, yace mata da sauki hawayen da taga a idonsa yasa ta ɓoye nata hawayen, tana kokarin yi masa magana likita ya shigo ɗakin,

Bayan ya duba ta ya kalli Saif yace

“Za mu canja mata ɗaki kuma ba bukatar wani ya shiga ɗakin idan ba likita bane sai dai zaku iya ganinta ta windo ina fatar zaku bamu haɗin kai”

Ajiyar zuciya Saif ya sauke,

“Doctor ko dai mu fitar da ita waje?”

“Eh to ba zan hana ku fitar da ita waje ba amman da kun bar ta muyi mata irin na mu mi gani tunda kaga abun daga jiya zuwa yau ne wannan ɗakin da za'a kai ta za'a kula da ita sosai ka kwantar da hankalinka zata samu sauki insha Allah matsalar kawai mu gano abunda yake cikin ne”

Cikin zafin rai yace

“Dr ya za'ayi na kwantar da hankali na bayan kun kasa ku gano abunda yake damunta, tun jiya yarinya ba ta san inda take ba amman kun kasa yin komai”

Likitan ya dafa shi

“Muna kokarin ganin mun gano haka sai dai kuma ina son kasan lafiyar ta da ciwonta a hannun Allah yake ba a hannun mu ba, kuma kun fa ya kum sai Allah addu'a kawai ya dace kayi”

Buge masa hannu yayi ya tashi a fusace ya fice daga ɗakin, tsaban zafin rai ko Hajiya Suwaiba bai tsaya gaidawa ba ya nufi harabar asibitin, tsaye yayi gurin motarsa yana shafa kansa zuciyarsa na bugawa da karfi, oho me zai yi shi kanshi yasan addu'a ce kawai mafita tunda baya iya bata lafiya sai abunda Allah yayi,

“Innalillahi wa innaa ilaihi raji'un”

Shine abunda yake ta maimaitawa yana son haɗe kukansa, buɗe motar yayi ya zauna ya haɗa kansa da sitarin ya rufe ido,
  Jikin Ringing ɗin wayarsa yayi yawa yasa ya ɗago ya ciro wayarsa daga aljihu daf da zata katse ya danna picking

“Hello Momy”

Yanayin muryarsa ya tabbatar mata yana cikin damuwa,

“Na'am ya mai jikin?”

“Alhamdulillahi”

“Idan ka fito kazo gida”

“Toh Momy”

Ya daɗe kamin ta kashe wayar, key yayi ma motarsa ya soma tafiya a hankali, lokaci lokaci yake shafa gashin kasa zuwa wuyansa ya sauke ajiyar zuciya, gida ya nufa kamar yadda Momy tace masa, bayan yayi parking ya daɗe cikin motar sannan ya fito ya nufi cikin gidan.
   Kallo ɗaya Momy tayi masa ranta ya kara ɓace sam bata son taga ɗanta cikin damuwa dan tafi kowa shiga damuwar,

“Momy ina kwana”

Ya faɗa yana kokarin zama, sai da ta zauna sannan ta amsa basa

“Lafiya kalau dan Allah karka sa kanka a damuwa da yawa zata samu sauki”

Kai kawai ya daga mata yace

“Ina lil Minal?”

“Tana can ɗakin Lubna muje dinning kaci abinci”

“Momy bana jin zan iya cin wani abu”

Bata matsa masa ba ta tashi ta nufi ɗakin Lubna bata daɗe ba ta fito ta nufi dinning. Ba a jima ba Lubna ta fito ɗakinta ɗauke da lil Minal ta nufo shi, lil Minal na ganin Abban ta ta fara zillo

“Pah pah pah”

Haka take faɗa tana kokarin mika kanta ya dauke ta, hannu ya mika ya karɓe ta cike da tausayinta ya rungume ta ya lumshe, wani irin tausayinta ne ya lulluɓeshi,

“Karɓi ga tea ka sha”

Maganar Momy ce tasa ya buɗe ido sai ya sauke su kan kofin tea, daga bisani yasa hannu ya karɓa, kaɗan ya kurɓa ya ajeye, Momy ta zauna kusa dashi cikin damuwa ta kalleshi

“Ita fa rayuwar duniya komai ɗan'hakuri ne jarabawa kala kala akan yi ma bawa da sannu sai kaga komai ya wuce, ni banga abun ɗaga hankali a wannan ciwon nata ba insha Allah zata ji sauki”

Iskar bakinsa ya busar

“Momy baki san yadda nake ji Kairat bane, na rasa Huda na rayu na rasa Minal na rayu Kairat kan dana rasa ta nima za'a rasa ni, Momy tun jiya yarinyar nan bata san inda kanta yake ba gashi su kuma sun kasa gano mi yake damunta”

“Kayi ta addu'a Allah zai bata lafiya”

“Ina fatar hakan amman Momy har fa ciki ne jikinta ina tsoron lamarin nan”

“Ka bar komai a hannun Allah shi zai maka magani zata samu sauki insha Allah”

“Allah yasa”

“Amin”

“Ba zaka ci abinci ba ka daure ka ci ko kaɗan ne”

“Ba zan iya i ba Momy bana jin yunwa”

“Da dai ka daure”

“Ba zan iya ba Momy”

Duk yadda Momy taso ya ci abincin ki yayi dan sam baya jin yunwa baya ma sha'awar wani cin wani abu,
   A wunin ranar haka ya wuni in banda ruwa babu abunda ya kai bakinsa, a ɓangaren lil minal ma haka ne dan bata sha komi aka bata sai ruwa sabo da nono gashi ba a koya mata shan komai ba, bai koma asibitin ba sai dare ba kuma komai yasa haka ba sai dan baya son ganin halin da matarsa take ciki. A hankali yake tafiya lil Minal na lafe a kirjinsa tayi lamo kamar wanda tasan abunda yake faruwa.
   A bakin kofar ɗakinta ya tararda Doctor tare da wasu, fuskarta ba yabo ba fallasa ya mika ma doctor hannu suka gaisa,

“Idan ka shiga wannan shi ne shiga na karshe da zaka kuyi dan anjima kaɗan zamu fara aikin mu idan kuma mun fara kuda ganinta sai a window”

Likitan ne yake faɗin hakan yana kallon Saif fuska da fuska, kai kawai ya iya ɗaga masa ya sauke ajiyar zuciya ya tura kofar ɗakin ya shiga jiki a sanyaye, Mummy ya gani zauna saman kujera ta saka Kairat a gaba tana kallonta sai hawaye take wasu na bin wasu, Hajiya Suwaiba da Abbah na daga gefe suma ita suke kallon ko wannensu fuskarsa ɗauke da damuwa dan Hajiya Suwaiba kaɗan ya rage hawaye bai zubo mata ba, cikin kararriyar murya ya gaishe su, Abbah kawai ya iya amsawa dan Mummy bata ma shigo ba, Hajiya Suwaiba kan tana buɗe baki tasan kuka ne zai fito,
   Karasawa yayi kusa da ita ya zagayo ɗayan ɓangaren, bai kula kowa ba ya mika hannu ya riko hannunta ya ɗago shi yayi masa kiss, sannan ya sake kai hannunsa ya shafa fuskarta, Mummy kan sai surutai take mata kamar wanda ke son zautowa,
“Dan Allah ki tashi Kairat kinji Mummy ba zata iya rayuwa ba ke ba, komai kike so zan miki ke kaɗai kika rage min”

Da kuka ta karasa maganar ta jingina kanta saman gadon, Abbah ɗauke fuskarsa yayi Hajiya Suwaiba kuma ta gumɗe baki kar kuka ya fito mata, Hannu Saif ya kai ya sake rike hannun nata gam tana dantsar baki, lil Minal kan sai bachinta take dan tun yana tsaye bakin kofa bachi yayi gaba da ita daman jikin nata kamar a mace yake, jin ta matsa hannunsa yasa ta kalleta da sauri sai ko yaga idonta a buɗe tana kallonsa, bana jin yasan lokacin daya risina a gurin yana kiran sunan ta, hakan ne ya hankaltarda su Mummy da Abbah suma suka kalleta, kallo Mummy tayi tare da kiran sunan ta murya kasa kasa kamar wanda aka taushe ma sheɗa,

“Mu.. mmy...”

“Na'am Kairat na'am na'am”

Da sauri Mummy take amsawa har bata iya tsayawa ta sauke numfashi, ɗauke kai tayi ta kalli Abbah da Hajiya Suwaiba sai kuma ta rufe ido kamar mai bachi, ta ɗauki kusan minti talatin a haka bata sake yin koda motsifa balle ta sake buɗe idon, ga dai numfashi tana yi amman ba magana ba alamunta, duk sukayi tsit kamar ba kowa ɗakin. Bayan kamar minti biyar likitoci suka shigo ɗakin tare da Nurses, ɗayan likitan ne ya nemi su Abbah da su fita, Hajiya Suwaiba ce ta fara fita Abbah ne na biyu sai Saif, Mummy kan daker ta fita daga ɗakin. 

A cikin Mota Saif ya rik'a rusa kuka kamar wani mace, har kukan nashi ya tashi lil minal daga bachi ta soma masa kuka, rarrashinta yayi daker ya samu ta koma bachin,

                         ***              ***               ***
Washe gari, bayan ya dawo daga sallah asuba, ya hau gado ya kwanta kasancewar jiya baiyi bachi ba kwana yayi nafisa yana nema ma matarsa lafiya gurin Allah, bachin nasa bai yi nisa ba ya soma jin kukan Lil Minal, kamin yayi wani yinkuri yaji kukan bakin kofar ɗakinsa,

“Wanene?”

Ya tamabaya jin ana buga kofar

“Nice”

Lubna ta amsa tana jijjiga lil minal, tashi yayi ya buɗe kofar ya karɓe ta

“Mi kika mata”

“Ban mata komai ba Momy ce tasa ayi mata ɗure madara tun shekaran jiya ba komai a cikin ta”

Kai kawai ya ɗaga mata ya maida kofar ya rufe ya shiga jijjiga ta saman kafaɗarsa,

“Mah mah mah”

Kawai take kira har bachi yayi gaba da ita, saman gadon sa ya kwantar da ita ya lulluɓeta da bargo, ya ɗauki jacket ɗinsa yasa, yana kokarin fita wayarsa tayi ringing, ya daɗe yana kallon screen ɗin ganin bakuwar number, sai da tayi ringing har ta tsare aka kara bugowa sannan ya ɗauka,

“Gani nan a waje ina son ganinka akwai magana mai muhimmanci da zan faɗa maka”

“Wanene”

“Idan ka zo zaka gani”

Dih dih dih..... Kiran ya katse, ya daɗe yana tunani sannan ya saka wayar aljihu ya fice.
     A harabar gate ɗin ya fito yana tunani har ya isa gakin gate ɗin, daker securities suk barshi ya fita wai saboda tsaron lafiyarsa duk da haka sai da wasu sojoji uku suka raka shi cikin farin kaya, ganin ba kowa a waje yasa ya ciro wayarsa ya kira number ana ɗauka yace

“Ina kake gani a waje”

“Ina nesa da gidan ku kasan ba'a bari mutun ya karaso ba tare da izinin ku ba”

Kashe wayar yayi ya fara tafiya suna binsa a baya, ganin tafiyar ba mai karewa bace yasa ɗayan sojan ya shiga gaba dan basu yarda da wanda inda zaije ba, ɗayan ma babu yadda baiso ya ki tafiyar ba wai ya kira mutum ne yace ya karaso amman Saif yaki dole suka kyalesa, a sannu suka fara hango mota fake gefen tt da bakin glass, sai da Saif ya kusa karasowa kusa da motar sannan ya fito daga motar sanye da farin yadi ya dora rigar sanyi a sama, Saif na ganinsa ya ya kalli securityn yace

“Za ku iya komawa nasan shi”

“No Sir just keep walking zamu tsaya a nan amman ba zamu koma ba”

Cigaba yayi da tafiya har ya isa gurin,

“Ya akayi”

Shine abunda Saif ya faɗa yana yi masa wani kallo, sai da ya rungume hannayensa sannan ya kalli Saif yace

“Baka bukatar waɗannan mutanen i won't hurt you”

“Ba shi na tambaye ka mike tafe da kai”

“Kan rashin lafiya Kairat ne”

Kallon tsaf Saif yayi masa,

“Kamar ya me ka sani akan rashin lafiyarta”

“Safiyyah ce musabbabin rashin lafiyarta, adalilin asirin da tayi mata, shin kasan dalilin warke war da Safiyyah tayi ne ya jefa Kairat cikin halin da take ciki yanzu”

Cikin rashin fahimta Saif ya kalleshi

“Ban gane ba ya akayi kasan da hakan?”

“ba zan faɗa maka ba yanzu amman ina son kaje ka samu Safiyyah da Shafa kayi musu wannan tambayar sune zasu faɗa maka hanyar samun lafiyar matarka”

“Safiyyah bata da lafiya bana jin zata iya yi min wata magana a yanzu”

“Ta samu lafiya idan kaje gida ka bincika”

Yana kaiwa nan ya buɗe motarsa har zai shiga sai kuma ya ɗago ya kalli Saif

“Sai dai kuma Kairat na samun lafiya zaka rasa Safiyyah”

“Deen.....”

Saif ya kira shi

“Idan na tararda labarin ba haka bane fa”

“Ka kashe ni”

Kai tsaye Deen ya bashi amsar, Saif ya sake cewa

“Miye dalilin ka

Please Login or Register in order to submit comment