Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kenan ta hango Asad da baba shehu suna karasowa , xuciyar Asad ta buga wani kishy ya rufe shy dan ji yayi kamar ya shake su, ta sunkuyar da kai har suka shyga, Ayda ga mijinki chan ki tafi dan karya ji haushy, idonta ya ciko hammad ya basar ya wuce abnsa, ta shyga simi simi taci karo da Asad a corridor, ke kada na kara ganinki da wancan yaron kina jina? Ta kalleshy sama da kasa aikuwa baka isa ba dan uwane fa dan haka wlh baka isa ka rabani da danuwana ba ehe 😏, aikuwa na isa ayda har nayi yawa har nawa kike? Daxaki ce min haka to nikuma na kafa miki wannan sharadin kuma dole kibi manner less human being kawai mtseww, xatayi magana kenan Asad ya fisgota jikin shy ya fara tsotsar lips dinta da kyar ta kwace kanta yace saura gobe ma kimin raahyn kunya. Ya fita ya barta anan.


Jarabawar su Ayda tapito with flying colourz kowa ya mata murna sosai, baba yace shykenan sai a saka biki a kusa kokuwa? Ayda tace baba ai ABU xan nema mama daria kamar me auran kuma fa? Ai mama kice ya barni anan kawai baba ya jinjina yarintar ayda yace to xa'a tambeshy aji ta mike tayi daki.

Asad ya bita daki daya dawo yace naji sakonki a wajan mama amma tace bana kula dake yanda yakamata, dan haka dole ki bini UK, kaga Asad ka barni dan Allah ni kana kara chaja min kai plz😭 ko dole ne nakula ka? Xai magana sai juyo salatin mama sukayi a palour kafin ta mike tyni Asad ya fita.


Daga taskar jamila💞 da khairy😘
[4:20PM, 5/13/2017] ‪+234 703 035 3461‬: 🍃ABAR KAUNATA🍃

Na. JAMILA MO ALI💞

Da KHAIRY MOHD😘



Page4⃣6⃣4⃣7⃣4⃣8⃣


Hankalinu na chan wani guri daban sai maganar Asad sukaji a Kansu,kunya ta kama hammad amma ya share kawai Asad ya kalli hammad sosai yace hammad na Dade ina jinku,Ashe har yanxu kanason Ayda? Asad kabar maganar plz ayda dai matar ka CE ISA yanxu ma danasan haka xata kasance wallahi da banxo ba, Asad yayi guntun smiling ya kalleta sosaai a hankali ya furta Ayda kece ruhina kuma abar kaunata ayda akanki na fada tarkon kangin shedan nan da nan ayda tace yi shuru Asad wannan sirrin mu ne kabar xanxen kawai, kan hammad ya daure kangin shedan kuma? Kar dai nemanta Asad yayi? Chabdi impossible , Asad yayi jugum yace hammad na hakura na bar maka ayda dan tafi kaunarka dani dan haka xan fada musu biki Yakoma kanka, hammad yayi daria Kasan Allah Asad baka isa ba na hakura dan ni tuni na cire Ayda a lissafina,ran Ayda ta baci xatayi magana kenan hammad ya musu sallama yaja mota ya kara gaba, Ayda sai hawaye ran Asad ya baci wato yarinyar nan ma ta maidani dan iska ya buga tsaki ya bar wajan, Ayda ta mike ta koma ciki jikinta a Mace kai maxa yan buhun uba ne😜.

Bayan kwana kowannen su da tunanisa, Ayda na tunanin yadda xata xauna da Asad ga rashyn sonsa, Asad na jimamin irin son da ayda keyiwa hammad sannan hammad na mamakin magagannun da Asad yayi sannan da rashyn hana shy furucin da Ayda tayi,wato Asad ya nemi ayda kenan amma sabida ta raina masa hankali takeso ya aureta? Hmmn bama ta da kai wallahi gara da yafada yaji ai ( xargy dai da kaxafi ba kyau Malam hammad ).

Shirin biki ake ranga ranga dan kowa sabbgogi sun masa yawa, Ayda ya kamata fa kije kiyiwa umminki kwana biyu kinga next week biki kokuwa? Tace to kawai amma batason xuwa dan takula Ummi bata da xance sai ta kyautatawa Asad ita kuma ba so take ba, da yamma driver ya sauketa gidan Ummi tana shyga taga motar Asad a tsakar gidan, ranta ya baci gashy ba damar komawa dan driver yajuya, haka tashyga a sukwane tana hada rai kamar an aiko mata da mutuwa, salamu alaykum! Wa alaykumussalam Ummi ta ansa, a ayda Ashe kece a tape? Eh Ummi mama tace naxo na kwana 2 kafin biki Ummi tayi daria kawai ta mike, Ayda na tashy Asad ya jawota ta fado jikinsa, ke baki Iya gaysuwa bane? Ta sadda kai kasa dan tana shakarsa karfin halin fitsara takeyi kawai, ya Asad ina wuni ya kura mata ido woow shagwabar ki ta burgeni ya fada a ransa, lpy lau madam ya fitsara? Tayi shuru kawai, gobe kayan ki xasu iso amma naga kamar akwai abnda baxasuyi miki daidai ba yana kallon boobs dinta, cikani ya Asad nifa ba yar iska bace kana rikeni kuma kana karewa sura ta kallo😏
Ayda kenan nasan ke ba yar iska bace amma gani nayi hammad na kamaki any how ko karya nayi? Ina tambayarki Malama ko kinada ja ne?( hattara dai mata da maxa) tayi lamo tabbas tasan hammad na rike mata hannu suna magana Ashe ba daidai bane? Allah kiyaye mu da aikata haka ko a boye ko a xahiri, Asad yayi murmushy kawai ya cikata oya jeki abnki na wuce kya fadawa Ummi.

Kwanan ayda 2 Ummi na kara tsumata da kuma nasihar xaman aure tare da bata adduo sosai.

Biki ya rage kwana 3 Asad yaleko dakinta, ayda nata surutai ita kadai kamar mahaukaciya😂😂 ya yi daria a ransa wannan yarinyar sai a slow, ta dago tanata harare harare kawai yace hw many IVs kikeso na bachelor's nite? Tsaki ta banka Allah kiyaye naje wani bachelorz nite dan nasan bawani bachelor's yanxu haka ma giyar Ku xakuje kuyi ta kwankwada kusaka yaran mutane tangadi 😏😏, ran maxa ya baci amma ya shanye kawai dan ya daina kulata su haura, tabbas baki karya ba ai dole ayi bar note kuma dole kije sannan dole kisha kema mtsewwww , haushy ya turnike ayda tayi kwafa kawai ya harareta ya fita.



*************************

Yau kamun amarya Ayda tasha kyau kamar yar tsana,kawayenta sun mata kara sosai, anci ansha anyi kamu me kyau aka bar amarya da kuka, da daddare Asad ya kirata ki shrya xamu namu Wanda abokaina suka hada, ta rantse baxata ba sai da ya roka kausar ta mata wayo ta pito da ita,da kyar Kausar ta lallaba ayda ta shrya da wata hadaddiyar wite n silver gown, an rufe mata kai da farin mayafi, woow humaida ta fada aikinki na kyau anty Kausar sai xuxuta ta suke itakuwa ko a jikinta, Asad ya kira Kausar a waya amarya su pito ita da kawayenta a tapi, tace mu kuma fa? Gskia Kausar bnda Ku kicewa ruqayya kada na sake naga kafarta a wajan ya ajiye,ruqayya haushy kamar ta mutu amma ta hakura.

Tun a mota Asad ke takalar ayda amma ta masa bnxa har suka iso tahir guest inn,a bakin ruwa akayi waje yayi waje kowa da budursa suke xaune, aka hau flour ango ya riko amarya sunata tango dance huhuhuhu ayda kunya sai turo Baku take goga kuwa ko a jikinsa, hammad ya jone da yasmeen kawar amarya,Asad yace ga dan uwanki Chan da kike naci yayi sabuwar budurwa dama bawani sonki dayake, ranta ya baci ta xauna abnta har aka tashy.

Ranar dinner amarya ta matso kyau ita da ango a dinner, sai haskawa suke asad kyau Ayda kyau su mama sai liki suke dasu hajia da ummi ayda NATA kuka batasan sanda ta fada jikin Asad ba ko kunya ya rungumeta yana lallashynta haba my cwt water melon ki hakuri mana, ta dago ta buga tsaki dama a jikinsa take? Dalla Malam cika ni ni ina da kunya idan kai baka da ita😏, yayi tsaki dan ma na rugumeki kinaso kina kaiwa kasuwa dan nasan kinji dadi yanxu kiris kike jira kibada da kai bori ya hau, ranta ya baci sosai idonta ya ciko ta share sai ka dauka wata hirar masoya suke amma fada ake😂😂 ta DAURA dammarar sai ta rama haka aka rakashe aka tashy.
D next day aka DAURA aure amarya tasha kuka sosai shykenan taxama mallakin asad wayyo hammad naso kaine ( kuyi hakuri masoyan hammad ayda ma ta hakura bakomi kake samu ba a rayuwa) aka bar amarya a gidan mama dan sai nan saty 2 xasu tafi.


Wash gari ya shyga dakin ta yaga tana sallah yayi shame shame a gadonta, tayi sallama ta masa bnxa kamar bata ganshy ba, ayda ya kirata ta ansa kanta a kasa yace mekike bukata? Bakomi ta fada a takaice amma dan Allah inaso kafita a harkata kada ka kara shygowa Inda nake, ya mike ya tsuguna a gabnta ya rungumeta a kirjinsa yana buga bayanta a hnkl, ayda nifa mijinki a yanxu ina da rite a kanki , ta dago nasani amma bnda wannan tym din,kasani ba na sonka kuma ko inasonka sai kaxama tsarkakakke xamu shrya,ransa ya baci ya mike yayi baya.

Daga taskar

Khairy😘😘 da jamia💞💞
[4:20PM, 5/13/2017] ‪+234 703 035 3461‬: 🍃ABAR KAUNATA🍃

Na JAMILA MO ALI💞

Da. kHAIRY MOHD😘


Page 4⃣9⃣5⃣0⃣


Saida yakai bakin kofa ya dakata ransa yana suya ya kalleta sosai Ayda nine ba tsarkakakke ba? Taji wani tausayin shy ya shygeta d way yanda yayi maganar, ta sunkuya da kai kasa yace nagode Ayda sai anjima ya fice abnsa wani tausayin Sa ya kamata taji Sam bata kyauta amma ai shy ya jawo.

Asad na shyga daki abn duniiya ya isheshy, yarinya 18yrz na yaba masa magana any how lallai yaxama dole na daukewa Ayda wuta dole na rage sonta na fara nuna mata tsana a fili,haka ya kwana tunani.
Da safe ruqayya ta shyga daki suyi sallama dan a ranar xata koma kano tana shyga ta tarar da Ayda na murkususu, Ayda menene? Ya ruqayya cikina ciwo nan da nan ta pito palour, mama mama kuxo kuga, ba shiri mama da Ayda suka shygo aka tarar da ayda,hnkl su ya tasgy sosai Ummi ta ryko ta suka pito ruqayya ta jasu sai asibity, suna xuwa Dr maryam ta karbesu ta shyga da Ayda sun Dade akanta sannan aka shawo kan matsalar, ayda na kwance da drip ta rufe idonta kamar me bacci, Dr tace ya akayi Ayda bata tare ba a gdanta? Kunsan fa mtsalar yarinyar nan, mama tace ai sun kusa tafia ISA sannan ta fita,ayda kunya kamar ta nitse kasa,gaskia Ummi yakamata ko GDA ne Asad ya kama inji mama,tynda tafiar tasu ba yanxi bane yace be gama ayyukansa ba sai nan da saty 3, bawani GDA mama inji umi yanda yaran xamanin nan suke ba kunya,ai wuyarta daya basuga waje ba kowa ba😃 mama tayi dan tunani kwarai kuwa amma nasan abnda zanyi. Da daddare aka sallameta suka aje Ummi a gdanta sannan suka wuce.

Asad wai bakasan matarka bata da lafia bane? Ya nuna be sani ba, mama ni bansani ba gaskia, tace to tana kwance gaskia Asad baka kulawa da ita Kaine fa Babba,ka shyga kayi mata sannu ni xan pita ne unguwa, bada son ran Sa ba ya mike amma xan gwada mata halina yau.

Ya shyga yana cin magani, ya jikin ki? Da sauki ta fada a hnkl, Ashe ciwon son auran ne ya tashy? Dan haka kixo a temaka a Baki magani kintsaya girman kai, ya Asad bara kaji Allah kiyaye naxo ka bani magani da dai hammad ne da a guje xanje ina tuntube😏 hhhhh Ayda kenan yanxu bata baci ba sai kije useless gal kawai yace kuma last warning kada na karaji kin ambaci sunan namiji a gaba mtsewww.

Mama na dawowa ta tarar da ayda ba wani Abu daya faru, ayda aiki akeyi ne? Eh wlh mama aiki nake sannu to amma aje kixo dakina,ayda ta mike a sukwane ta shyga ta xauna, mama tace Ayda na kula kamar ba jituwa a tsakanin ki da Asad ? Bude kunnenki da kyau ayda, sai kin tashy a tsaye namiji wawa ne beda wayo, yakamata ki San ya cikin mijin ki yake , girki gyaran shymfidarsa ki jashy a jiki sosai a haka xaku fuskanci juna, ko a haka kuke fatan Ku kasance a inuwa daya? To mama xan gyara, tace mike ta miko mata wani Abu a jarka ki saka a fridge kullum kisha cup 2 ta ansa to mama.

Da daddare suna hira mama na ganin 9 tayi tace oya mike ki shrya kije ki kaiwa mijinki abnci, amma ki wanka ki gyara akwai rigar bacci a dakina kisaka, kunya ta kama ayda sisai ta mike,wanka tayi ta fesa turaruka ta saka rigar kunyar kanta da kanta taji,oh mama kenan ko kunya ta ni wlh ba son xuwa nake ba amma ba yanda na Iya, ta pito ta Dade a tsaye a kofar dakin takasa shyga, tunani ya mamaye ta tarasa mafita ta kutsa kai dakin tare da sallama,Asad yana aiki a laptop mamaki ya kamashy ya ansa a ciki beko kalleta ba , ta kalleshy daga shy sai three qtr da singlet, ta kare mass kallo kut😳 Ashe Asad ya hadu haka ai ban taba gani ba sai yau uhmn, tana tsaye be CE xauna ba kamar besan tana dakin ba, ta gaji ta sulale ta xauna sannan ya dago lafia? Naxata kin Fita ma ya tabe baki to Mara kunya mekukaxi nema a dakina? Mama CE tace nazo,owk naji kixo kiyi me? Nima bata fadamin ba ya Asad yace koma ki tambeta me xakiyi a dakina, tayi sororo lallai ma gayennan da latsi ne mtseww takasa mikewa saboda kunya, ya kashe laptop din a haye gado ya barta a nan a xaune, yafara tunani inason Ayda so mai tsanani amma baxan Iya kusantarki ba ayda sai randa kika fara kaunata ina dreaming much much lurv, dole na dauke idona a kanki ayda bashiri ya sauko kasa yaganta inda ya barta a zaune, ya rike hannunta mike ayda nagode da ziyarar ki jeki daki ki kwanta kinji, kasa motsawa tayi ya kula jikinta yafara sanyi yayi murmushy ya cire hijabin jikinta..............

Hahahaha kawarmu m shakur me muryar yan gayu daina baxa ido 😜😜

Kuyi hakuri wlh biki muke shyasa nayi typing kadan , Wanda sukayi wishing ina buffday nagode sosai musamnan HAUWA M JABO dan ita tafara tnx for d lurv n cares.

For comments

08062204629

Daga taskar jamila💞 da khairy😘
[4:20PM, 5/13/2017] ‪+234 703 035 3461‬: 🍃ABAR KAUNATA🍃


Na JAMILA MO Ali 💞

Da KHAIRY MOHD😘


Page 5⃣1⃣5⃣2⃣5⃣3⃣


Ya cire duka innalillahi Allah yayi halitta anan ya fada a xuciyarsa ya kurawa jikinta ido beko kiftawa,kunyar dunia ta kama ayda kamar ta nutse kasa ita kuma ta kasa motsi kanta a kasa, Asad ya matso yanaso yayi huging dinta amma yana Shakkar ta fada masa magana ko rashin kunya, yace ki hau gadon ki kwanta mana tayi salo salo ta wuce a dadare ta kwanta tana kallon hagu, ba shiri hankalinsa yafara tashy ya haye gadon shyma ya juya baya, ga koshy ga kwanan yunwa Asad yayi lamo yana tunanin Abar kaunarsa ya juyo a hnkl yaga alamun dai idonta 2, ya mika hannu ya juyo da ita a hnkl, wani yarrr taji a jikin amma ta lumshe ido, matsowa daf da ita yayi suna jin nunfashyn juna amma ya kasa tabata,fiye da awa 2 yana kallonta itakuwa tuni barawo yayi gaba da ita, ya mike ya bude wani karamun akwaty ya dauko giya xaisha, ya bude baki kenan yaji baxai Iya ba ya mayar ya rufe abn dunia ya isheshy, shaawar ayda ta dameshy, ya Allah ka agajeni, ya matsa kusa da ita ya rungumeta a hnkl lallai aure rahma inji aysha tafida, har bacci ya daukeshy.

Da asuba ta riga Asad tashy, kai meya kawoni jikin Sa? Wani guntun tsayi tayi karaf a kunnensa amma yayi kamar yana bacci ta mike ta xura hijabi ta fita da sanda😂😂😂 ya grgyxa kai dama bankira ki ba bare naji haushy, anya rayuwa xata min a haka? Gara na hanxarta mu koma nakoyawa yarinyar kaunata.

Da safe ta pito, mama ina kwana suka gaysa, ta bita da kallo taga dai alamun ba abnda ya wakana, ayda ina Asad? Yana dakin Sa mama tace kirawo shy Ku karya ta mike ta tafi, kwan kwan yes waye? Tayi kasake kamar baxata kulashy ba ta ansa nice yace bismilla ta shyga ta dan russuna kadan ta gaidashy ya ansa a dakile lpy any prblm? Em mama na kiranka yace jeki ina xuwa yabi bayanta da kallo masha Allah ya fada a fili nan da nan ta juyo sukayi four eyes, ya basar kamar bashy yayi maganar ba dan bezata xata jiyo shy ba ta dauke kai ta kara mai tayi gaba.

Asad ya pito ya gansu a table yaja kujera shyma ya xauna suka gaysa da mama, ayda na satar kallonsa kai ya Asad ya hadu kowane kaya yasaka kyau yake masa kodayake ina ruwaa na , taji ya fara burgeta kawai taci gaba da satar kallonsa, yaushe kace xaku koma? inji mama, da saura fa mama tace yaushe ayda xata fara lectures? Ai sunfara jiya mama tasaka salaty ama kuke nan a jabe Asad ? Kai jibi Ku wuce Asad ya xare ido ya saci kallon ayda yaga shy take kallo ya yamutsa fuska yace to mama Allah kaimu, yanxu ka gama kuje kuyiwa su Ummi dasu hajia da duk Wanda ya kamata sallama ya ansa ta mike race mayda jeki shrya itakuma tayi daki.

Tana cikin shryawa ya shyga tana saka under skirt kunya ta kamata ta tsuguna kasa, beko kalleta ba ya zarce kan dress mirrow ya dauka turare ya fesa ya fita,mamaki ya kashe ayda gayeennan lpy kuwa yake? Kaga mace half necked amma ba alamun tashyn hnkl hmn, ta karasa shirin ta tapito ta tadda shya tsaye yana waiting, ta firta a hnkl ya Asad napito,ya Kare mata kallo sosai , a haka xaki fita kina matar aure? Kalli kayan jikin a dame sannan da karamin vail waxaki nunawa jiki? Ko dan kinji xamuje gdan su saurayinki kika masa kwalliya, ranta ya baci sai kwalla yace jeki goge janbakinki sannan ki saka hijabi😎 kinajina? Kasa tafia tayi ya matso kusa da ita sosai ya rungumota ya tsotse janbakin tas ayda tsayawa ta gagareta taji kamar ta fadi ga wani Abu dake mata yawo a jiki,saida ya gama sannan ya jata dakinta oya dauko hijab mutafi, jiki a sanyaye ta dauko tasaka yace dauko min brush, brush kuma? Eh dan kin sakamin janbaki infact ma ban taba hada baki da kowa ba dan inada kyankyami ta tsaya jin ikon Allah wannan cin fuskar kuma fa? Ko nina sakashy dole? Mtseww , ya asad bnda sabo ai saidai na dauko maka naka a toilet dinka, ya mata bnxa ya wuce ya kuskure bakinsa sosai abin tabata daria lallai ma kai bnji kyaminka ba sai ni xakaji nawa hmmn muje dai xuwa.


Au ayda baku fita ba mama ta tambaya, Asad yace mayafi ta chanxa da alamar kunya, to sai kundawo suka pito tynda suka hau hanya Asad kebin wakar shape of my heart yana lumshe ido tamkar kwadadde har suka iso gdan hajia laura.
Suna shyga hammad na shrin pita da mota gaban ayda ya fadi amma ta dake, ya karaso ah ango da amarya😃 suka gaysa da Asad dakyar ta gaidashy yace kanwata ya kk? Lpy Lou ya Hammad yace mushyga mana suka rankaya, ya leka dan ya Kira hajia, ya xauna tana pitowa yanxu nikam na wuce rankai Dade, Asad yace ayya bakomi muma jibi xamu wuce UK ah habadai ya dawo ya xauna , AY bnsani ba wlh Allah kiyaye yace to Ayda kibi mijinki Sau da kafa,ki masa biyayya sosai bnda fitsara dan Allah ta fara hawaye,ki Sani aljannarki na tafin kafarsa kada ki sakaci idan tayi laifi danAllah asad kafadamin wlh saina ci mutuncinki, kada kisake yakawo min kararki kinaji? Naji ya hammad kaikuma Asad ga amanar kanwata nan kayi adalci a xamantakewarku bnda cuts da cutarwa plz ya ansa har hajia taputo itama ta DAURA nata akai sannan suka pito akayi sallama jikin ayda a mace. A mota ya saci kallonta yace kinji kowa namiki fadan kibini Allah yasa kin dauka dai tamasa bnxa.

A gdan Ummi suka tsaya, baba yamusu nasiha sosai sannan Ummi musamman akan hkr da xama da miji, ummi tajata daki ta karamata dantana tausayin yar sosai ya kamata ki kara addua sosai ayda,sannan ki rike sirrin mijinki dan Allah ta gyada kai tana kuka sosai ,Ku tapi sai jibin xanxo my kara sallama.


Ranar da xasu taxi jiki kowa a sanyaye ayda sai kuka ake kowace rayuwa xata fuskanta Oho,Ummi ta kara musu fada tace Asad ga amana nan ta ayda ka kula dan Allah yace ba mtsla Ummi kuyita mana addua ta rungume kowa tana daga musu hannu ya runguota suka wuce tuni✈ ya cilla sai UK.........





To fa muje xuwa muma munaa biye dasu dan jin kwaf.

Sonki a jinine ZEE UMAAR Allah barmu dake

Daga taskar Jamila 💞. Da khairy😘
[4:20PM, 5/13/2017] ‪+234 703 035 3461‬: 🍃ABAR KAUNATA🍃

Na JAMILA MO ALI💞

Da. kHAIRY MOHD😘


Page 5⃣4⃣5⃣5⃣


Ayda kanta a kasa sai kuka take a jirgy abin yana damun Asad amma ya nuna halin ko inkula da ita,yanaso yayi peting dinta amma idan ya tuno irin wulakancin data ke masa sai yaji duk ya sike gara ya barta ta nutsu tukunna,haka ta gaji da kukanta ta hakura tayi shuru, goshyn asuba suka isa suna dira motar office din su Asad ta dauke su a airport,sun sauka a kayataccen karamin GDA me 2 rumz da palour da kitchen,gdan ya mata kyau sosai daidai da students ko amarya da ango,tana xaune a palour Asad ya gama shygo da kayan su yace ga daki nan kidauki na hagun shyne naki,ta mike ta shyga shykuma ya kira mama dan tasan sun sauka lpy ,ya ayda ? Tana daki mama inaga baccin gajia ta kwanta kam tace ai dole, dan Allah Asad ka kula da yarinyar nan kaga marainiar Allah CE kaji? Tom mama ISA xanyi sukayi sallama.

Yafita world pier restaurant ya musu order na abnci sannan ya koma,ya tarar da ayda tana kallo bata ko kulashy ba,ya xauna yaga ko xata masa magana shuru shyma ya basar ya fara cin abnsa sosai,mamaki ya kashe ta sosai ganin be mata bismilla ba saida yagama sannan ya mike ya shyge daki abnsa hhhhh, tayi jigum taci ko karta ci? Ga yunwa ba shiri ta bude tafara Bawa ciki hakkinsa lallai da drama agdannan.

Da safe ya shyga dakin a dake da alamun zai tafi aiki, ta daure ta gaidashy amma ya basar,ga kayan abnci nan a kitchen duk abnda babu kimin text, ta kalleshy ya xuba kyau tace ai bnda layi ya xaro wani dan karamin bakin sim card ya mika mata kisaka a wayarki tayi godia yapita.

Koda yadawo da yamma yaga table wayam ba komi a kai ya wuce dakinta, yaganta xaune da addua buk tana dubawa yace ina abncina? Tayi shuru ya maimaita tace ya Asad ai nadauka baxaka ci ba nikuma bnyi dakai ba wlh, ya tsaya kallon ta d way she talks ba alamar cewa laifi tayi ko mantuwa harda gadara lallai yarinyar nan ya juya cike da fushy, na banu da mutuminnan kodayake damuwarsa ni nadauka ba ci xaiyi ba mtsew taci gaba da abnda take. Shyga yayi kitchen ya soya kwai da custard sannan ya gasa bread yana ci yana tunani lallai yaxama dole na gyara gdana dan vaxan dauki iskancin mace ba wlh.

Da safe ya pito ya jiyo tana waya yayi kasake yaji, tace to ya hammad nagode ina hajiyan nan ma suka gama harda humaida haushy ya cika Asad wato yarinyar nan da hammad take waya? Ya shyga ba alamar rahama a fuskarsa yace ke bani wayarki, tayi bnxa dashy yace bakiji ne? Ta tsorata ganin yanayin fyskarsa ta bashy ya fara bincike Allah ya temakeki ba messages daga hammad, yana duba calls yaci karo yakirata sau 4 ya hada rai wato waya kike dashy ko? Yayi kyau daga yau nayi seizing wayarki sannan makarantar wallh tllh saboda alkawari nayi shysa xaki cigaba shashashan bnxa ya pita, tarasa mexatayi kuka ko bashy hakuri haka ta yini ba kuxari hmmmn!

Wayarsa tayi kara ya duba yaga Ummi CE,ya ansa da faraarsa tace ya aiki? Lpy lau Ummi tace masha Allah! Dama nakira ta ne akashe

Please Login or Register in order to submit comment