Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Muka
sakankace ga halaka, muka yi kalmar shahada,
ni dai sai na runtse idona ina jiran in ji abin da
zai faru.
Ban san yadda aka fara ba, sai muka ji wata irin
tsawa mai karar gaske, muka ji an dauki jirginmu
an yi jifa da shi, ya fada bisa dutse, ya tarwatse,
ashe ba dutse ba ne, bisa bayan kifi ya fada.

Dukkanmu muka dulmiya cikin teku. Ni kuwa sai
na cire rigata na fara ninkaya, Allah ya koro mini
da wani allo na jirginmu da ya karairaye, na
kama allon nan na hau na yi kwance bisa gare
shi ina tura ruwa da kafafuna, iska da rakuman
ruwa na ingiza ni gaba. Da na gaji da wutsil-
wutsil da kafafu sai na yi kwance bisa allon nan
kamar matacce, yunwa da kishirwa suka taso
mini za su halaka ni. Na rika zargin kaina da
kaina a kan barin gida da na yi. Wata zuciya ta
rika yi mini fada tana cewa, "kai Sindibad! Kai
Matafiyi! Ai duk abin da ya same ka ba ka da
kaico! Sau nawa kana cewa idan ka kubuta
daga hatsari ba za ka sake fita fatauci ba? Shin
ka tsare wannan alkawari kuwa. Don haka kome
ya same ka yanzu ba ka da kaico!"

ya ce, ina bisa allon jirgi iska da
rakuman ruwa na tura ni, wata zuciya ta rika yi
mini fada da cewa, duk halin da na tsinci kaina
ba ni da kaico, ni na jawo. A cikin wannan hali
na yi da-na-sanin da ban taba yi ba, har na ce
a raina idan Allah ya kaddara na kubuta daga
wannan tafiya, to, ni da sake barin gida haihata-
haihata. Haka iska ta yi ta tura ni ina cikin
nadama mara iyaka, na sakankance ga halaka,
duk da haka bakina bai daina addu'ar neman
tsira daga Ubangijin talikai ba, mai tausayin
bayinsa. Na kasance cikin wannan hali tsawon
kwana biyu, har Allah ya yi ikonsa, iska ta tura ni
bisa wani babban tsibiri wanda yake cike da
itatuwa da koramu.
Na rarrafa na shiga cikin wannan tsibiri, na tsinci
'ya'yan itacen da suka zubo kasa na ci, na sha
ruwa daga wata korama, na jingina jikina ga
bayan wata bishiya har hankalina ya dawo
jikina. Da na ji na fara samun kaina sai na yi
godiya ga Allah da ya kubutar da ni daga
dulmiyewa cikin teku. Na ce a cikin raina, "yayin
da bawa ya debe kauna daga rayuwa, sai ka ga
taimakon Ubangiji ya zo masa ta inda ba ya
tsammani. Wanda duk ya kai kukansa ga Allah
ba ya tabewa. Hakika wanda ya jefa kansa cikin
wahala da gangan, to ba shi da kaico."
Na tashi ina zagayawa cikin tsibirin, ban gushe
ba har na iso ga wata babbar korama wadda
ruwanta ke gudu cikin sauri. Yayin da na ga
wannan korama na gudu sai na tuna da kwale-
kwalen da na taba yi na bi ruwan wata korama
har ya kai ni ga tsibirin mutane. Na tsaya ina
tunani, daga nan sai na yanke shawara a cikin
raina, babu makawa in aikata kamar yadda na
aikata a baya, watau in sana'anta dan kwale-
kwalen da zan bi ruwan wannan korama, yalla in
iske inda mutane suke, idan kuma na mutu, to,
shi ke nan, haka Allah ya so. Na yi rantsuwa
cikin raina, idan dai har na koma gidana lafiya
daga wannan tafiya, to, ba zan sake fitowa
zuwa ga fatauci ba.
Na zabura, na himmatu ga tattara dogayen
sandunan itace da kirare, na tara masu yawa.
Na debi ciyawa na tufka iggwai. Na daura dan
gado mai girma da tsayi kamar kwale-kwale, na
yi guzurin 'ya'yan itace saboda abinci, na jefa
dan gadon nan bisa ga korama, na shiga ina
cewa, mai rabon ganin badi sai ya gani. Na yi ta
tafiya cikin korama, ruwanta yana tura jirgina
gaba, na tafi a cikin rana ta farko da ta biyu da
ta uku har na fita daga cikin tsibirin, na rika cin
'ya'yan itacen da na yi guzuri ina sha daga
ruwan koramar. A cikin kwana na hudu sai na
ga koramar nan ta nufi karkashin wani dutse
mai girma, da na ga haka sai hankalina ya tashi,
na tuna irin wahalar da na sha a baya. Na ce a
raina, idan na kubuta daga waccan tafiyar ta
baya, to, yanzu fa? Ai ba kullum ake kwana a
gado ba. Na yi nufin in sauka daga kan gadon
nan kafin ya shiga karkashin dutse da ni, amma
saboda karfin gudun ruwan koramar ban sami
damar yin haka ba. Ruwa ya ja ni sai cikin
karkashin dutse.
Na buga sallallami, "babu tsimi babu dabara
face daga Allah Madaukakin Sarki." Sai dai ba
kamar yadda na zata ba, ban yi wata tafiya mai
nisa ba cikin kogon dutsen sai na ga na fita a
bayansa, haske sararin samaniya ya bayyana
gare ni. Da na duba gabana inda ruwan nan ke
tafiya sai na ga yana fadawa cikin wani katon
rami ne, na ji karar saukar ruwa a kasan ramin
kamar karar aradu. Na yi iyakar kokarina domin
karkata jirgina daga fadawa wannan rami,
amma ina. Da na ga dai babu makawa sai na
shiga wannan rami, sai na rike jirgin nan gam da
hannuwana don kada ya watsar da ni yayin da
nake sullatawa cikin ramin. Ruwa ya tafi da ni
na auka cikin ramin kwantsam! Allah ya kare ni
ban fada bisa dutse ba. Ban gushe ba kwale-
kwale yana tafiya da ni har guzurina ya kare,
yunwa ta taso mini, ga gajiya da rashin barci.
Na yi kwance bisa dan kwale-kwalen ina jiran
mutuwata. Can sai ga ni a gefen wani babban
birni. Gine-ginen birnin abin ban sha'awa, ga
mutane da yawa ko'ina suna ta harkokin
gabansu. Yayin da mutane suka gan ni cikin
wannan hali sai suka yi tsammani koramar nan
ciyo ni ta yi, suka jeho mini igiya domin in kama
su fitar da ni, ni kuwa lokacin ba ni da sauran
kuzari a jikina. Da suka ga haka sai suka jeho
raga ta nannade ni duk da kwale-kwalena suka
jawo ni waje bakin gaba.

Na fadi gabansu sharaf kamar matacce, babu
sauran karfi a jikina saboda yunwa da gajiya da
rashin barci. Mutane suka zagaye ni suna kallo,
daga nan sai wani dattijo mai kamala ya keto
daga cikin taron mutane, ya saka mini riga, ya
dauke ni ya tafi da ni gidan wanka, ya sa aka
wanke ni fes, aka sanya mini tufafi masu kyau,
aka feshe ni da turare mai kanshi. Dattijon nan
ya ja ni zuwa gidansa. Mutanen gidan suka yi
murna da zuwana kamar wani dansu ne ya
dawo daga tafiya. Suka zaunar da ni bisa abin
zama suka kawo mini abinci mai rai da lafiya, na
zauna na ci na koshi, na sha abin sha, tatacce
mai kyau. Kuyangi suka kawo mini ruwan dumi
na wanke hannuwana, suka kawo mini adiko
mai taushi na goge hannuwana da bakina. Na
gode wa Allah madaukakin Sarki wanda ya
kubutar da ni daga halaka.
Dattijon nan ya kai ni ga wani daki inda zan rika
kwana, ya sa bayi da kuyangi su rika yi mini
hidima. Na kasance cikin kulawar dattijo tsawon
kwana uku, in ci mai kyau, in sha mai kyau. A
cikin kwana ukun nan karfina ya komo jikana,
hankalina ya kwanta. A cikin kwana na hudu
dattijo ya zo wurina ya zauna, bayan mun gaisa
sai na ji ya ce mini, "hakika ka wadatar da mu
da zuwanka, mun amfana daga arzikinka.
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya kubutar da
kai daga halaka. Ya dana, shin yanzu
hankalinka ya kwanta mu tafi kasuwa ka sayar
da hajjarka? Yalla ka yi amfani da kudin domin
yin guzuri idan za ka koma gida."
Na yi shiru ina kallon dattijo. Na ce a cikin raina,
"wace hajja ke gare ni wadda wannan dattijo ke
magana? Ni ba ni da wata hajja a wannan birni."

Dattijo ya ce, "kada ka damu, idan kana tunanin
ba za a sayi kayanka da daraja ba, to ni zan
ajiye maka su a cikin taskata har zuwa lokacin
da aka sami mai sayen su da daraja."
Da na ga dai kamar dattijo na yi mini wasa da
hankali sai na ce a cikin raina, "bari in bi shi
zuwa kasuwa in ga hajjar da yake cewa wai
tawa ce." Na dube shi cikin ladabi na ce, "ya
baffana, na yarda da abin da ka ce. Mu tafi
wurin kayan nawa."
Dattijo ya ja ni zuwa kasuwa, muna isa wajen
dillalai sai na ga daya daga cikin su ya sa tarin
sanduna da kiraren itacen kwale-kwalena a
gaba, ga masu saye sun zagaye shi. Ashe
sandunan nan duka na itacen sandal ne.

Tajirai suka zagaye dillali suna sayen
itatuwa, idan wannan ya saye sai wani ya yi kari,
wani ma ya yi kari bisa ga na biyu. Haka suka yi
ta kara kudi har aka sayi itatuwan dinari dubu.
Daga nan sai dattijo ya ja ni gefe ya ce, "ya
dana, wannan shi ne tamanin kayanka a cikin
wannan lokaci na rashin kudi, idan ka sallama a
karbi awalaja, idan kuma ba ka sallama ba in
dauke su in ajiye maka a cikin taskata har zuwa
gaba lokacin da suka kara kudi."
Na kalli dattijo cikin girmamawa na ce, "ya
baffana, na bar maka wuka da nama a cikin
wannan sha'ani, duk abin da ka zartar daidai
ne."
Dattijo ya ce mini, "za ka sayar mini da su dinari
dari, kari bisa ga abin da aka saya?"
Na ce na sallama masa. Ya sa bayinsa suka
kwashi itatuwa suka kai taskarsa suka kulle, ya
ja ni muka koma gidansa. Ya jawo wani sunduki
nasa da yake ajiyar kudi, ya kirgo dinari dubu da
dari daya ya sa mini a cikin jaka, ya saka jakar a
cikin wata 'yar karamar taska ya kulle da kwado,
ya ba ni dan mabudin. Bayan kamar kwana biyu
da haka, rannan muna hira da dattijo sai ya
kada baki ya ce mini, "ni kuwa ina da wata
bukata da nake so in nema gare ka, ban sani ba
ko zan samu?"

Na ce, "subhanalillihi, yanzu har akwai wata
bukatar da za ka nema a wurina in ki yi maka
ita. Me cece wannan bukata?"
Dattijo ya ce, "ya dana, ka ga dai ni tsoho ne, ba
ni da da namiji sai mace. Ina so idan ka yarda in
hada ka aure da 'yar nan tawa, sai ka zauna tare
da ni a matsayin dana, ka rika lura da dukkan
harkokin kasuwancina da dukiyata duka."

Na yi shiru cike da kunya, na kasa amsa wa
dattijon nan magana tasa. Da ya ga ban ce
komai ba, sai soshe-soshen kai nake yi kamar
mara gaskiya, sai ya ce mini, "ba tilasta maka
zan yi a kan wannan magana ba. Amma idan ka
yarda yau din nan sai a daura aure, matarka ta
tare. Kuma kada ka dauka yin auren zai hana ka
komawa kasarku. Duk lokacin da ka ga damar
komawa gida babu mai rike ka."

"Na rantse da Allah ya kai baffana, " na fada
kaina a sunkuye, "na dauke ka tamkar
mahaifina a wannan gari. Kai ne uwata kai ne
ubana, don haka duk abin da ka zartar a kaina
na amince da shi."

Nan take sai dattijo ya aika bayinsa aka kira
alkalai da shaidu, ba tare da bata lokaci ba aka
daura mini aure da 'yar dattijon nan, aka kwana
uku ana biki. A kwana na hudu na shiga dakin
amarya, na tarar da ita kyakkyawar gaske, ta
sha tufafi na alfarma da aka layyace da zinariya
da azurfa da sauran kayan jauhari iri-iri. Haka
kuma dukkan sarkoki da awarwaro da 'yan
kunnen da ta sanya na jauhari ne mai tamanin
gaske, wanda sai manyan tajirai za su iya sayen
su.
Na zauna tare da matata, ina son ta tana so na.
Ba mu gushe ba tare da 'yar dattijo har mutuwa
ta zo wa dattijo. Aka yi masa wanka aka yi
masa sutura aka kai shi gidansa na gaskiya.
Daga nan sai duk dukiyarsa ta komo hannuna,
na zama ni ne mai iko da bayi da kuyanginsa
duka. Tajirai kuma suka hadu suka nada ni
Sarkin kasuwa, da ma dattijon shi ne Sarkin
kasuwarsu, na zauna a matsayinsa.
Na yi sabo da mutanen wannan birni kwarai da
gaske, na yi abokai attajirai masu yawa. A
zamana cikin wannan birni, na lura da mutanen
cikinsa na da wata tabi'a. Tabi'ar kuwa ita ce,
farkon kowane wata sai fuskokin wasu daga
cikin mazan garin duk su canza, su koma irin na
tsuntsaye. Sai kuma su daura wasu irin manya-
manyan fika-fikai su tashi sama, su haye bisa
wani dogon tsauni da ke bayan gari. Ko me suke
yi a saman tsaunin? Oho! Rannan da naga
sabon wata ya kusa kamawa sai na ce a cikin
raina, "bari in tambayi wani daga cikin mazan
garin nan masu irin wannan al'ada ya tafi da ni
inda suke zuwa."

DAGA Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ20 HIKAYAR SINDABAD MAI TEKU DA SINDABAD DAN DAKO

Rannan da naga
sabon wata ya kusa kamawa sai na ce a cikin
raina, "bari in tambayi wani daga cikin mazan
garin nan masu irin wannan al'ada ya tafi da ni
inda suke zuwa."
Yayin da farkon sabon wata ya kama, mazan
nan suka canza kama, suka koma siffar
tsuntsaye. Na tafi ga wani abokina na ce, "don
Allah ka tafi da ni inda kuke zuwa ni ma na bude
idona, idan kun tashi dawowa sai mu dawo
tare."
Ya ce mini abu ne da ba zai yiwu ba. Na yi ta
rarrashin sa ina yi masa magiya har dai ya
yarda da bukatata. Na tafi gidana na kimtsa na
fito, ban fada wa kowa inda zan tafi ba. Na je
wurin abokin nan nawa, ya ce in hau bayansa.
Na hau bisa bayansa, ya fiffika da ni sama cikin
sararin samaniya. Bai gushe ba yana tashi da ni
har sai da na yi tsammani ko za mu keta rufin
samaniya ne mu shiga ciki, domin sai da na rika
jiyo wasu muryoyi suna tsarkake sunan Ubangiji.
Lokacin da na jiyo muryoyin nan sai na amsa
musu, "tsarki ya tabbata ga Allah, Ubangijin
talikkai." Ai ina ambaton sunan 'Allah' sai aka
jeho mu da wata irin wuta. Mutanen nan da
suke cikin siffar tsuntsaye suka yi kasa da sauri,
suka kauce wa wannan wuta, duk da haka sai
da wasu daga cikin su suka kone suka zama
toka. Wadanda suka tsira sai suka yi ta zagina
suna la'anta ta. Suka jefar da ni bisa wani dutse
mai girma suka tafi cike da fushin abin da na
aikata, suka bar ni bisa wannan dutse da babu
kowa.
Na zargi kaina da kaina a kan fitowa tare da
wadannan mutane. Na ce a cikin raina, "babu
tsimi babu dabara face daga Allah madaukakin
Sarki. Duk lokacin da na kubuta daga hatsari sai
in auka cikin wani wanda ya fi shi." Na tashi ina
tafiya bisa dutsen nan, ban san inda nake nufa
ba. Kwaram, sai na hadu da wasu samari biyu,
ka ce su watanni ne don kyau. Kowane daya
daga cikin su yana tafe yana dogara sanda ta
jar zinariya. Da muka hadu sai na yi musu
sallama. Bayan sun mayar mini da sallama, sai
na ce musu, "don Allah 'yan samari, su waye
ku?"
"Mu bayin Allah ne," suka amsa mini, "muna
zaune ne a bisa wannan dutse." Sai suka miko
mini sanda daya ta jar zinariya, suka tafi abin
su. Da suka bace mini da gani, sai na ci gaba
da tafiya ina dogara wannan sanda. Ina cikin
tafiya sai na ji motsi wukur-wukur a bayan
dutse, sai na ja na tsaya. Can sai ga wani
babban maciji ya fito daga cikin wani kogon
dutse. A cikin bakinsa ya hadiye wani namiji
daga kafafunsa zuwa cibiyarsa, sauran jikinsa a
waje yana kururuwa yana cewa, "wanda duk ya
kubutar da ni daga wannan maciji Allah zai
kubutar da shi daga dukkan wahala."
Tausayin mutumin nan ya kama ni, ban yi wata-
wata ba sai na daga sandar da ke hannuna ta
jar zinariya na kwantara wa macijin bisa kai, nan
take ya amayar da mutumin da ke bakinsa.

sake bugun ta na biyu, ta juya da sauri ta shige
cikin kogon nan da ta fito. Mutumin ya zo gare
ni, jikinsa na bari ya ce,"ya shugabana, wallahi
ba zan rabu da kai ba tsawon rayuwata. Kai ne
mai gidana a bisa wannan dutse, ka aikata duk
abin da ka so gare ni." Na ce masa babu laifi ga
yin haka.
Na shige gaba yana biye da ni a baya, muka ci
gaba da tafiya bisa dutse har muka iso ga
gungun wasu mutane. Da na dubi mutanen nan
da kyau, sai na ga har da abokin nan nawa da
ya dauke ni bisa bayansa, wanda kuma ya jefar
da ni bisa wannan dutse. Na matsa kusa gare
shi, na yi masa magana cikin harshe mai dadi
na ce: "ya abokina, bai kamata aboki ya aikata
abin da ka aikata gare ni ba."
Ya amsa mini, "kai ne ka jawo wa kanka abin da
ya same ka. Me ya sa ka ambaci sunan Allah
lokacin da kake bisa bayana? Wannan abu ya yi
kusa ya halaka mu duka."

Na roki gafara wurinsa. Na kuma roke shi ya
koma tare da ni zuwa cikin birni wurin iyalina. Ya
yarda zai dauke ni bisa bayansa, amma ya
gargade ni da kada in kuskura in kara ambaton
sunan Allah yayin da nake bisa bayansa. Na
kawo sandar zinariyar nan na ba mutumin da na
kubutar daga bakin maciji. Muka yi ban kwana
da shi yana kukan rabuwa da ni. Na dare bisa
bayan abokina ya tashi sama da ni tare da
sauran mutanen nan, kamar dai yadda muka yi
da fari. Ba mu gushe ba muna keta iska cikin
sararin samaniya har muka iso cikin gari. Ya
sauke ni cikin gidana ya yi gaba abin sa. Matata
ta taso ta tare ni da farin ciki, sa'annan ta
gargade ni da cewa kada in sake fita tare da
mutanen nan masu tashi domin su 'yan uwan
shaidanu ne. Ba su sallah, ba su salati, ba su
son mai sallah ko salati.
Yayin da na ji zancen matata sai na cika da
mamaki, na ce a cikin raina, "haba, ai biri ya yi
kama da mutum. Ba don haka ba me zai sa
mutanen nan su taso mini kamar za su cinye ni
danye, lokacin da na ambaci sunan Allah." Sai
na tambayi matata, "to, amma mahaifinki ba ya
tashi tare da su?"
Ta amsa mini, "mahaifina ba ya tashi tare da su,
shi musulmi ne mai tsoron Allah."

Daga nan sai
ta canza zancen ta ce, "ka ga dai yanzu ba ni
da uwa ba ni da uba a cikin wannan birni, duk
sun mutu. Ina so ka tattara dukkan dukiyar nan
tamu ka sayar da ita, ka dauke ni mu tafi
kasarku, mu fita daga kasar wadannan
shaidanun mutane." Na amince da maganar
matata, na tattara dukkan dukiyar dattijon nan
na sayar da ita, na sayi wasu kayan da zan yi
fatauci da su a kan hanya. Na shiga cigiyar
jirgin da zai nufi birnin Basara, na kuwa sami
wasu fatake suka ce mini su ma can za su
fatauci amma ba su sami jirgi ba. Na ce musu
me zai hana mu sana'anta jirgin da kanmu.
Suka yarda da shawarata, muka sami itatuwa
masu yawa muka daura babban jrigi wanda zai
ishe mu tafiya duk da kayanmu.
Fatake duka suka sanya kayansu a cikin jirgi, na
tafi tare da matata da wasu kayanta masu
saukin dauka. Muka shiga jirgi muka tsunduma
cikin teku, Allah ya tsare mu, muka tafi daga
wannan tsibiri zuwa wancan, daga wannan birni
zuwa wancan, muna saye muna sayarwa. Iska
ta yi mana dadi, ba mu gushe ba muna tafiya
har muka iso birnin Basara. Na yi sallama da
abokan tafiyata, na dauki kayana tare da matata
na nufi birnin Bagadaza, Gidan Aminci. Yayin da
muka iso Bagadaza sai na nufi gidana, na kuwa
same shi lafiya, babu abin da ya faru a cikinsa.
'Yan uwa suka yi ta zuwa suna yi mini barka da
dawowa. Na sanya dukiyata a cikin taska na
kulle.
Yayin da abokaina suka ji labarin dawowa ta
daga wannan tafiya ta bakwai wadda na share
tsawon shekara ashirin da bakwai ba na gida,
sai suka yi ta zuwa suna yi mini barka, da har
sun debe tsammani da dawowa ta. Na ba su
labarin abin da ya faru gare ni a cikin wannan
tafiya tawa, suka yi mamaki, gayar mamaki. Tun
daga wannan rana na yi rantsuwa ba zan sake
fita gida ba da niyyar tafiya, a bayan kasa ne ko
a cikin teku. Saboda wannan tafiya ta karshe ta
ba ni tsoro matuka. Godiya ta tabbata ga Allah
madaukakin Sarki wanda ya maido da ni cikin
kasata kuma cikin 'yan uwa da abokaina, lafiya.
"Don haka ya kai abokina Sindibad dan dako," in
ji Sindibad Matafiyi, "wannan ita ce irin
gwagwarmayar rayuwar da na sha kafin in tara
wannan dukiya da kake gani, ba don Allah ya
hore mini tsawon rayuwa ba, da tuni an manta
da ni a bayan kasa."

Sindibad dan dako ya dukar da kai kasa ya ce,
"ya shugabana, ina rokon ka don Allah ka yafe
mini habaicin da na yi maka a baya cikin waka."
Sindibad Matafiyi ya riki Sindibad dan dako
babban amininsa, ya ba shi dukiya mai yawa da
bayi, suka kasance cikin farin ciki da jin dadin
rayuwa har mai yanke farin ciki, mai rusa gidaje
da birane, mai raya kaburbura da makabartu,
kaskon da kowane mai rai zai sha daga gare shi,
ita ce mutuwa ta zo musu. Tsarki ya tabbata ga
Sarkin nan da ba ya mutuwa har abada.
Wannan shi ne abin da ya zo mini na daga
labarin Sindibad Matafiya da Sindibad dan dako.

wannan shine abunda yazo gareni na hikayar sindabad mai teku da kuma sindabad dan dako' wanda yadaukemu tsawon kwana ashiri muna kai'INSHA ALLAH Nan bada jimawa ba zan kawo wata sabuwan hikaya insha Allah, ANAN nake sallah na daku ni NAKU Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ.

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment