Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai, mutum ko aljan? Ya aka yi ka zo
nan?"
Na amsa masa, "Kada ka ji tsoro. Ni mutum ne,
falke. Labarina yana da ban mamaki. Yadda na
shiga cikin wannan kwari kuma na fito abu ne
mai matukar daure kai. Ina so ka kwantar da
hankalinka, idan dai don lu'ulu'un da ake samu ne
a cikin wannan kwari zan ba ka wanda zai ishe
ka har tsawon rayuwarka."
Sai na ga fuskar tajirin nan ta washe da farin
ciki. Ya duka ya yi ta gode mini kamar wanda
aka ba duniya duka. Muka yi ta mayar da zance,
ni da shi, har 'yan uwansa suka jiyo mu, suka fito
daga inda suke labe suka zo wurin mu.
Kowanensu kuwa ya jefa dabbarsa a cikin kwarin
nan. Muka gaisa da juna.
Suka ja ni muka nufi cikin gari, muna tafe ina
gaya musu labarina. Na gaya musu yadda muka
shigo cikin teku tare da 'yan uwana fatake, da
yadda muka yada zango a cikin tsibirin da barci
ya dauke ni, aka bar ni can. Na fada musu
dabarar da na yi na daure jikina a kafar Rukki har
ya kawo ni cikin kwarin lu'ulu'u, da irin macizan
da na gani a cikin kwarin. Na gaya musu dabarar
da na yi na fito daga cikin kwarin.
Da suka ji wannan labari sai na ga suna ta kada
kai don mamaki. Na debo lu'ulu'u mai yawa na
ba mai dabbar da tsuntsu ya fito da ita. Su ma
sauran tajiran na 'yan musu wani abu. Suka yi ta
godiya suna murna. Suka yi ta yi mini addu'a
suka ce, "Mun rantse da Allah ka zama dashi mai
yawancin rai. Ai babu mahalukin da ya taba
shiga wannan kwari ya fito da rai sai kai. Tajirai
da yawa sun gwada shiga da kwanduna wajen
dibar lu'ulu'u amma babu wanda aka kara jin
duriyarsa. Godiya ta tabbata ga Allah da ya
kubutar da kai."
Da dare ya yi ba mu isa gari ba sai muka sami
wuri muka kwanta. Ina cike da farin cikin kubuta
daga kwarin macizai da kuma tsibirin tsakiyar
teku da babu dan Adam ko daya. Yanzu kuwa ga
ni cikin karkara tare da mutane 'yan uwana. Na
kara gode wa Allah.
Bayan gari ya waye, rana ta fito ta watsa
haskenta bisa kasa da duwatsu, muka ci gaba da
tafiya tare da tajirai. Wannan kasa cike take da
duwatsu da kwazazzabai. Kowane kwari kuwa
cike yake da macizai.
Muna cikin tafiya muka iso ga wani tsibiri mai
cike da bishiyoyin kafur. Kowace bishiya daya
mutum dari na iya zaunawa karkashinta ya sha
inuwa saboda girmanta.

Tajirai suka gaya mini cewa daga jikin wadannan
bishiyoyi ake fitar da kafur. Yadda ake dibar sa
kuwa shi ne, sai a soka wa itacen wani karfe mai
hanya a tsakiyarsa, a sa karfen cikin gora.
Ruwan itacen zai ta biyowa ta cikin karfen yana
shiga cikin goran, da haka sai a cika goruna
masu yawa daga bishiya guda. Idan ruwan ya
taru da yawa sai ya daskare kamar danko. Shi ke
nan kafur ya samu. Sai dai daga nan kuma itacen
zai mutu, ya zama kwaure. Sai a sare shi a yi
icen wuta.
Haka kuma a cikin wannan tsibiri na itacen kafur
na ga wasu dabbobi tika-tika suna kiwo. Tajirai
suka ce mini dabbobin nan su ake kira karkanda.
Suna da girma sosai jikinsu kamar na rakumi,
amma sun fi rakumi girma nesa ba kusa ba.
Kafafunsu gajeru ne kwarai. A tsakiyar kansu
daga can gaba suna da kaho guda daya tal, mai
kauri da tsini, ya dan lankwaso baya kadan,
amma ba ya da tsayi sosai. Suna cin ciyawa da
ganyen itatuwa kamar bauna da saniya. Na taba
ji fatake da alhazai na cewa, wannan dabba mai
suna karkanda tana iya tsire babbar giwa da
kahon nan nata, ta yi ta yawo da ita bisa kanta
tana kiwo ba tare da ta damu da nauyinta ba.
Har sai giwar nan ta mutu ta fara rubewa, idan
rana ta narka kitsen giwar sai ya dararo ya shiga
cikin idon karkanda, wannan shi zai yi sanadiyyar
makancewarsa. Sai ya yi kwance a bakin teku.
Daga nan kuma idan tsuntsun nan mai suna
Rukki ya fito farauta ya ga wannan makahon
karkanda a kwance, sai ya fyauce shi duk da
giwar da ke bisa kansa ya kai wa 'ya'yansa su yi
kalaci. Hmh! Kun fa ji ikon Allah.
Duk dai a cikin tsibirin kuma na ga wasu irin
shanu da babu kamarsu a wannan kasa tamu. Da
muka iso cikin gari na sayar da wani abu daga
cikin lu'ulu'un da na samo, na sayi irin hajar
kasar, wadda na tabbata idan na dawo da ita
gida zan sami riba mai yawa. Na sayi dabbobi na
lafta musu hajata, na bi ayarin fataken wannan
kasa. Muka rika bin kasashe muna saye muna
sayarwa. Na ga abubuwan mamaki iri-iri, na ga
kasashe daban-daban da al'adunsu. Kwanci tashi
har Allah ya kawo mu Birnin Basara. Bayan na
huta kwana biyu, sai na bi wasu fatake muka nufi
Bagadada gidan aminci.
Na sadu da 'yan uwa da abokan arziki. Na
rarraba sadaka da kyaututtuka ga mabukata. Na
rarraba wa abokaina dukiya mai yawa. Na koma
ga dabi'ata ta cin abinci mai kyau da abin sha.
Na rika sanya tufafi na alfarma ina kece raini. Na
manta da duk wasu wahalhalu da na sha a baya.
Na kasance babu wata damuwa a cikin raina.
Mutane kuwa suka yi ta zuwa suna yi mini barka.
Ni kuwa na yi ta ba su labarin abubuwan
mamakin da na gano a cikin wannan tafiya tawa.
Suka yi ta mamaki da jin wannan labari.
"Wannan shi ne karshen labarin tafiyata ta biyu a
teku," in ji mai gida. "In Sha Allahu gobe zan
gaya muku labarin tafiyata ta uku a cikin teku,
wadda tafi wannan hatsari da ban mamaki."
Sindibad dan dako da sauran tajirai suka yi
mamakin wannan labari na Sindibad mai teku.
Daga nan aka kawo musu abinci da abin sha,
suka ci suka koshi. Mai gida ya kawo dinari dari
ya ba dan dako, ya sallame shi. Dan dako ya
karbi kudi ya yi godiya, ya nufi gida cike da
mamakin labarin da takwaransa ya bayar.
Koda ya isa gida dare ya yi, bayan ya yi sallah
sai ya kwanta yana alla-alla gari ya waye ya
koma gidan tajirin nan domin ya ji labarin
tafiyarsa ta uku.
Gari na wayewa kuwa bayan Sindibad dan dako
ya yi sallar safe sai ya nufi gidan Sindibad mai
teku. Aka yi masa iso, ya shiga ya zauna a dakin
shakatawar mai gida. Can jimawa kadan sai ga
shi ya fito. Bayan ya zauna sai suka gaisa da
juna, suka jira kadan har sauran tajirai suka iso.
Bayan an kawo musu abinci sun nada, sun kora
da abin sha mai dadi. Zuciyoyinsu suka yi fari,
fuskokinsu cike da annushuwa. Mai gida ya dube
su ya ce, "Ya ku abokaina, ku saurari labarin da
zan ba ku, domin ku tabbatar da cewa ikon
Ubangiji shi ne iko. Kuma Ubangiji shi kadai ya
san adadin abubuwan mamakin da ya boye a
cikin wannan duniya tamu." Mai gida ya ci gaba
da labarinsa:
TAFIYAR SINDIBAD TA UKU A CIKIN TEKU
Kamar yadda na fada muku jiya, na dawo gida
daga tafiyata ta biyu da dimbin dukiya, fiye da
tafiyar farko da na yi. Allah ya kara wadata ni da
dukiya fiye da wadda mahaifina ya bar mini gado,
wadda na barnatar da farko. Na zauna cikin
dadin rai da kwanciyar hankali, na manta dukan
wahalhalun da na sha a baya.
Ina nan zaune kan haka, kun san zuciya da debe-
debe, ran nan sai na ji babu abin da nake
sha'awa irin na sake shiga cikin duniya. In ga
kasashe da al'adunsu daga nan in dan taba
fatauci.
Na sayi kayayyakin da zan yi wannan tafiya da
su, na kulle su wuri guda. Na yi ban kwana da
'yan uwa da abokai, na nufi Birnin Basara. A can
na sami wani babban jirgin ruwa zai tashi da
fatake. Na yi wa Madugu magana, na biya kudi
aka saka kayana. Na shiga jirgi tare da sauran
fatake, kowa ya zauna bisa kayansa.
Jirginmu ya tsunduma cikin teku, bayan mun yi
addu'o'in neman kariya da neman sa'ar wannan
tafiya daga Allah Madaukakin Sarki. Muka yi ta
keta ruwa, daga wannan teku zuwa waccan teku.
Daga wannan tsibiri zuwa wancan. Daga wannan
birni zuwa wancan. Babu hadari daya da ya same
mu, muka ci gaba da saye muna sayarwa a duk
birnin da muka sauka.
Wata rana muna cikin tafiya a teku ashe ba mu
sani ba, iska ta kwashi jirginmu ta canja masa
hanya. Ba mu ankara ba sai muka ganmu cikin
wata teku mahaukaciya. Rakuman ruwa na ta
toroko kamar jirginmu zai kife. Sai muka ga
Madugu yana ta nazarin wannan teku da muka
shiga. Ya duba dama ya duba hagu. Ya tada
kansa ya yi duba nesa. Sai muka ga ya fara
sallallami yana tafa hannuwa. Daga nan sai ya
fashe da kuka, ya tube rawaninsa ya jefar a cikin
ruwa. Ya rika marin fuskarsa yana tsige gemanya
tasa.
Da ganin haka sai hankulanmu suka tashi, muka
tambaye shi, "Ya Ra'isu, me yake faruwa ne?"

"Ku sani ya ku 'yan uwana, iska ta canja mana
tafarki. Mun bar teku mai lafiya mun fada cikin
teku mai hatsari. Gaba kadan za mu isa ga
dutsen da ake kira Zugibu. Yana bisa wani tsibiri
wanda babu kome a cikinsa sai wadansu irin
manya-manyan halittu masu gashi kamar birai.
Babu wani mutum da ya taba zuwa wannan wuri
ya tsira da ransa. Ni kam tuni na yi ban kwana
da rayuwata." Sai ya ci gaba da kuka, kamar dan
yaro.
Madugu na gama mayar da jawabi sai jirginmu ya
tsaya a bakin gabar wannan tsibiri. Kafin ayi
haka sai muka ga birai sun kewaye jirginmu
kamar kuda. Wadannan birai abin tsoro ne. Dukan
jikinsu lullube yake da bakin gashi, baki kirin
kamar gawayi. Idanunsu launin rawaya, da
matsattsar fuska mara kyan gani, baki wuluk. Ga
su 'yan kanana kamar 'ya'yan karnuka. Suna ta
wata irin magana da junansu, Allah kadai ya san
abin da suke cewa.
Muka ji tsoron mu far musu da kisa, domin idan
muka fara kisan su, to, kuwa za su yi mana
taron dangi, don kuwa an ce sarkin yawa ya fi
sarkin karfi. Muka yi tsuru-tsuru muna jiran mu
ga yadda biran nan za su yi da mu.
.
Bayan sun gama magana da junansu, sai suka
taru, kamar birai dari, sai su ciccibi mutum guda
daga cikinmu su fitar da shi daga cikin jirgi su
ajiye shi bisa tsibiri. Haka suka yi duk suka fitar
da mu daga cikin jirgin. Daga nan sai suka fada
cikin jirgin gaba dayansu, suka tuka suka tafi duk
da kayanmu, ba mu san inda suka nufa ba. Suka
bar mu nan tsaye muna karanta wasikar jaki.
Muka kasance cikin tsibiri muna ci daga 'ya'yan
itatuwa muna sha daga ruwan koramu. Wata rana
muna yawo cikin wannan tsibiri sai muka hango
wani gini daga can nesa kamar gida. Sai murna
ta kama mu, watakila mu iske mutane a cikin
wancan gida da muka hango. Muka nufi wurin da
sauri har muna tuntube, ashe ba mu sani ba, za
mu kai kanmu ne ga halaka. Da muka isa kusa
ga wannan gini sai muka ga ashe duk girmansa
daki ne daya kwal.

Wannan daki ba irin dakunan da muka saba gani
ba ne, daki ne babba mai tsayi. An gina shi da
dutse, an zagaye shi da dogayen katangu. Yana
da wata babbar kofa wadda sai rakumi ya shiga
da mutum yana tsaye bisa bayansa, ba tare da
mutumin ya sunkuyar da kansa ba don tsawonta.
Kofar na da gambu daya da aka yi da iccen
marke, an raba gambun biyu daga tsakiya ya
zama marufi biyu.

Muka je bakin kofar muka tura gambun sai muka
ga ya bude. Ba mu yi wata-wata ba sai muka
kutsa kai cikin dakin. Wannan daki babba ne, don
girmansa rakuma kamar hamsin na iya kwanciya
cikinsa ba tare da wani ya taba jikin dan uwansa
ba. A cikin dakin muka tarar da wani dogon
dakali mai fadi na dutse. Sa'annan kuma a
bangayen dakin an sassargafe kayan girki da na
cin abinci, irinsu tukwane da akussa da goruna.
Ga kuma murhun wuta, kusa ga murhun duk
kasusuwan dabbobi ne bargaja. Amma ba mu ga
wani mahaluki ba a cikin wannan daki, muka cika
da mamakin wannan abu, matukar mamaki.

Muka zauna bisa dandamalin nan na dutse, da
yake a gajiye muke tibis sai muka dan kwanta
domin mu huta, sai kuwa barci mai nauyi ya
dauke mu. Muka yi ta sharar barci tun da rana
har marece ya yi ba mu farka ba. Muna cikin
barci sai muka ji kamar kasa na girgiza, muka
farka a firgice, muka yi zaune zuru-zuru.
Kasa kuwa ta ci gaba da girgiza kamar za ta
tsage, muka rika jin hayaniya da hargowa da
tankiya ta nufo dakin da muke ciki.
Ba zato ba tsammani sai muka ga wani irin
mutum, shirgegen kato mai tsawo kamar iccen
dabino ya shigo dakin. Jikinsa baki kirin da gashi
ko'ina ya rufe jikin. Idonsa daya a tsakiyar goshi,
ja jawur kamar garwashin wuta. Bakinsa wagege
kamar bakin rijiya. Fatun lebbansa kuwa kamar
na rakumi sun sauko har bisa kirjinsa, da hakori
zaro-zaro kamar kasusuwa. Kunnuwansa kamar
na giwa don girmansu, sun sauko har bisa
kafadunsa. Ya shigo rike da wani busasshen
iccen wuta, kumbunan hannunsa kamar na zaki.
Da ya shigo sai ya mayar da kofa ya rufe garam.
Yayin da muka ga wannan shirgegiyar halitta, don
mun tabbata ba mutum ba ne, sai hankalinmu ya
tashi. Saboda tsananin tsoro da firgita sai muka
zama kamar matattu...

kuna tare da ==>Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ.

Whatsapp only
080327675477. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD
DAN DAKO
Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Sabuwar Fassarar:
Ibrahim Malumfashi,
Danladi Haruna,
Bukar Mada.
Sindibad bahariyi ya ci gaba da labarinsa ya ce,
yayin da muka ga wannan shirgegiyar halitta mai
kama da mutum sai muka rude don tsoro, muka
zama kamar matattu.
Da ya shigo cikin dakin sai ya zauna bisa dogon
dakalin nan na dutse. Ya dube mu da idonsa
daya mai kama da idon Dujjal, sai ya miko
hannunsa ya rumke ni cikin tafin hannunsa kamar
ya rumke kaza. Ya rika mammatsa jikina wai ya
ji ko ina da maiko, kamar yadda rundawa kan yi
idan za su yanka tinkiya.
To, ni kuwa da ma haka nake dan kyamas, duk
dadin nan da nake ci a gida ba ni da kiba, balle
kuma ga wahalar tafiya ta kara ramar da ni. Da
ya ji jikina duk kasusuwa ne sai fata, sai ya jefar
da ni gefe daya.
Ya mika hannunsa ya kara cafko wani falke, ya
mammatsa shi ya jujjuya a cikin hannunsa, sai
ya sake shi. Haka dai ya yi ta daukar mu daya
bayan daya yana latsawa cikin hannunsa har ya
dauki madugunmu. Madugun nan kuwa mutum ne
lukuti mai kiba sosai.
Da katon nan ya latsa shi ya ji shi kiba-kiba
kamar yadda yake so, sai ya fyada shi da kasa
kamar yadda ake fyada kwado a kasa. Nan take
Madugu ya mimmike bai ko shura ba.
Sai katon nan nan ya jawo wani dogon tsinke, ya
tsire shi kamar yadda ake tsire kaza idan za a
gasa ta. Ya hura wuta ga murhu, ya aza madugu
saman murhun yana jujjuya tsinke har ya gasu
ram, mai sai tsiyaya yake yi.
Da Madugu ya gasu sai dodon nan ya dauke shi
daga kan murhu. Ya rika yago namansa guntu-
guntu yana ci kamar mai cin kaza har ya cinye
shi duka ya watsar da kasusuwan gefen murhu.
Ya dauki ruwa ya kwankwada, ya zauna sa'a
kadan sa'annan ya kwanta bisa dakalin nan ya
mimmike, barci mai nauyi ya dauke shi.
Ya rika minshari da gwarti mai karfi kamar an
yanke bijimin sa. Bai farka ba sai da gari ya
waye, ya tashi ya fita wurin nasa harkoki, ya
mayar da kofar daki ya rufe.
Bayan mun tabbatar da tafiyarsa sai muka zauna
muna kuka saboda abin da muka gani na tashin
hankali. Muka ce da junanmu, "Ina ma a ce jirgi
ya kife da mu cikin teku duk mun halaka, ko
kuma a ce biran da suka dauke jirginmu sun
halaka mu da ya fi sauki da a gasa mutum bisa
wuta a cinye. Wannan wace irin mutuwa ce?
Amma abin duk da Allah ya kaddara zai sami
bawansa babu mai iya karkare shi sai ya same
shi. Babu tsimi babu dabara face ga Ubangiji
Madaukakin Sarki."
Muka sakankance ga halaka. Muka yi ta yawo
cikin dakin nan muna neman wani dan sako da
za mu boye kafin dodon nan ya dawo ya ce zai
gasa wani daga cikinmu. Muka zagaye dakin nan
kaf babu wurin boyew, kuma mun yi dabarar
duniyar nan domin bude kofar nan, amma abu ya
gagara.
Da muka ga alamun maraice ya yi sai
hankulanmu suka tashi, muka yi zaune muna
jiran dawowarsa.
Can sai muka ji kasa na girgiza kamar za ta
tsage, daga nan sai muka ga an bude kofar daki
shirgegen dodon nan ya shigo, ya mayar da kofa
ya rufe. Ya zauna bisa dakali, ya rika daukar mu
daya bayan daya yana latsawa cikin hannunsa
har ya dauki wanda ransa ke so. Ya aikata masa
kamar yadda ya aikata wa Madugu. Ya gasa ci,
ya cinye ya watsar da kasusuwa, ya daga tulun
ruwa ya kyankyama. Daga nan sai ya kwanta
barci ya yi ta gwarti kamar yankakken bijimi har
gari ya waye. Ya tashi ya fita ya mayar da kofa
ya rufe.
Muka hadu wuri guda muka ce wa juna, "Wallahi
gwamma a ce jirgi ya kife da mu mun mutu a
cikin ruwa da a gasa mu a cinye."
Sai wani falke daga cikinmu ya ce, "Ya ku
jama'ar fatake ku saurari zancena. Mu hada
kanmu mu san dabarar da za mu yi mu kashe
wannan dodon banza mu tsirar da kanmu daga
halaka da kuma sauran musulmi da kaddara ka
iya korowa wannan tsibiri. Allah ya hore mana
hankali da dabara fiye da dukkan sauran halittu."
Sai na ce da su, "Ku saurari zancena ya ku
fatake. Idan har za mu jaraba kashe wannan
dodo ne, to mu fara daura 'yan gadaje da
wadancan tulin itacen da dodo ya tara kusa ga
murhu, mu yi su kamar jirgin ruwa. Ya kasance
kowane gado daya zai iya daukar mutum biyu ko
uku. Idan muka yi nasarar kashe dodon sai mu yi
amfani da gadajen a matsayin jiragen ruwa
watakila Allah ya nufa mu fita daga wannan
tsibiri. Idan kuma ba mu yi nasarar kashe shi ba
sai mu fada cikin teku bisa wadannan gadaje,
idan Allah ya kaddara za mu tsira shi ke nan,
idan kuwa mun nutse cikin ruwa sai mu yi
mutuwar shahada, domin an ce duk wanda ya
mutu cikin ruwa, to ya yi shahada. Kuma ma ai
gwamma mu mutu cikin ruwa da mu tsaya ana
gasa mu da ranmu."
"Mun rantse da Allah," fatake suka amsa gaba
daya, "Wannan shawara taka ita ce daidai."
Dukanmu muka yarda da haka. Muka yi ta jido
itace muna daura 'yan gadaje da su. Muka yi
gadajen da za su ishe mu hawa dukanmu. Bayan
mun gama wannan aiki sai muka zauna zaman
jiran dawowar dodo.
Can bayan rana ta fadi, maraice ya fara yi sai
muka ji kasa tana girgiza. Ba a dade ba sai muka
ga an bude kofar daki, dodo ya shigo da itacen
wuta rungume ga hannunsa, yana huci kamar
karen da zai yi cizo. Ya watsar da da itace
sharaf a gindin murhu, ya mayar da kofa ya
kargame. Ya zauna bisa dakali ya sa hannunsa
ya cafko daya daga cikinmu, ya mammatsa
jikinsa. Da ya ji ya yi masa yadda yake so sai ya
fyada shi da kasa, ya soke shi ga tsinke kamar
an soke kifi. Ya hura wuta ya aza falken nan
bisa, ya rika jujjuya shi har ya gasu. Ya cinye
tsokar ya watsar da kasusuwan. Bayan ya
kwankwadi ruwa sai ya mimmike bisa dakalin
nan ya fara barci yana minshari kamar an yanke
sa.
Da muka tabbatar da cewa barci mai nauyi ya
dauke shi, sai muka dauki tsinken nan da yake
tsire 'yan uwanmu da shi yana gasawa, girmansa
kamar shinshiniyar rumfa. Muka dora shi bisa
garwashin wuta, muka yi ta iza wutar har sai da
tsinke ya yi jawur kamar garwashin wutar, muka
dauke shi muka nufi inda dodo ke barci.
Da isarmu kusa ga kansa sai muka dubi idon nan
nasa daya muka caka masa tsinken da iyakar
karfinmu a tsakiyar idon, ji kake cus kamar an
jefa garwashi a cikin ruwa. Nan take muka mayar
da shi makaho.
Dodo ya farka a gigice ya dafe idonsa da hannu
ya yi wani irin ruri mai karfin gaske har sai da
bangayen daki suka motsa kamar dakin zai
rushe. Muka tsorata tsoro mai tsanani. Don
tsananin tsoro ma sai muka fadi kasa kamar
matattu.
Dodo ya ci gaba da kara yana lalube-lalube ko
zai kama daya daga cikinmu. Da muka ga haka
sai muka fara zagaye-zagaye da shi a cikin dakin,
zukatanmu cike da firgici, tuni mun sakankance
da halaka.
Da ya ga dai bai kama mutum ko daya ba daga
cikinmu sai ya fara laluben bango har ya tarar da
kofar dakin ya bude ta. Ya fita waje yana
kururuwa mai karfi, kasa kuwa ta rika girgiza
kamar za ta tsage don karfin wannan kururuwa
tasa.
Da muka ga ya fita ya bar kofar dakin a bude sai
muka kwashi gadajen nan muka fita da sauri,
muka bazama da gudu muka nufi bakin teku, ana
kuwa kwala farin wata kamar rana, muka rika ce
wa juna, "Watakila wannan rauni da muka yi
masa ya zamanto sanadiyyar mutuwarsa."
Muna gab da isa bakin teku kamar an ce mu
waiwaya, sai muka hango wasu dodannin guda
biyu 'yan uwan wannan da muka soke wa ido sun
nufo wurinmu da sauri. Idandunan nan nasu
jawur a cikin farin wata kamar borkono, har ma
sun fi wanda muka raunata ban tsoro..

daga==>>Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ8. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA.

Sabuwar Fassarar:
Ibrahim Malumfashi,
Danladi Haruna,
Bukar Mada.
Sindibad Mai teku ya ci gaba da labari ya ce,
muna gab da isa bakin teku kamar an ce mu
waiwaya, sai muka hango wasu dodannin guda
biyu 'yan uwan wannan da muka soke wa ido sun
nufo wurinmu da sauri. Idandunan nan nasu
jawur a cikin farin wata kamar borkono, har ma
sun fi wanda muka raunata ban tsoro.
Da ganinsu sai muka kara azama muka isa bakin
teku, muka jefa gadajen nan bisa ruwa muka
haye, muna tura ruwa da hannuwanmu. Ko da
dodannin nan suka iso bakin gaba mun yi nisa
cikin teku, da suka ga babu yadda za a yi su
kama mu sai suka rika daukar manyan duwatsu
suna jifar mu da su.
Suka sami wadansu daga cikinmu, 'yan gadajen
suka kife da su cikin teku suka halaka. Ni kuwa
da wasu fatake kadan muka tsira daga jifar da
wadannan dodanni.
Iska ta yi ta tura gadajenmu da sauri a cikin teku
har muka ba tsibirin dodanni baya muka kasance
a tsakiyar teku, rakuman ruwa suka rika yin sama
da kasa da gadajenmu kamar za a kifar da mu.
Haka dai iska ta ci gaba da tura mu cikin teku ba
mu san inda muka nufa ba. Abokan tafiyata suka
rika mutuwa daya bayan daya, muka rage saura
mu uku, ni da wasu mutum biyu.
Iska ta yi ta tura mu cikin teku da sauri. Yunwa
da kishirwa suka taso mana, ba maganar gajiya
da rashin barci ake yi ba. Haka dai muka daure
iska ta yi ta tura gadonmu cikin ruwa.
Can bayan gari ya waye, rana ta fito ta baje
haskenta bisa ruwa sai muka hangi wani tsibiri
can nesa gare mu. Sai muka karkata gadon da
muke kansa, wanda yake shi ne tamkar jirgin
ruwa a gare mu, muka nufi wannan tsibiri.
Muka isa bakin gaba muka sauka cikin tsibirin,
muka iske shi cike da itatuwa masu 'ya'ya, da
tsuntsaye iri-iri suna shwagi bisa itatuwan. Ga
kuma ruwan koramu suna gudana ko'ina. Muka
debi 'ya'yan itace muka ci muka koshi, muka sha
ruwa, karfin jikinmu ya dan dawo kadan.

Muka zauna karkashin inuwar wata bishiya muna
hutawa. Muka gode wa Allah da ya tsirar da mu
daga tsibirin bakaken dodanni da kuma hadarin
teku. Muka ci gaba da zama karkashin wannan
itaciya har dare ya soma yi.
Daga nan sai muka share wuri muka kwanta,
abinka da gajiyayyu nan take sai barci mai nauyi
ya dauke mu. Ba mu yi nisa cikin barcin ba sai
wata iska mai karfi ta tayar da mu, muka yi
zazzaune muna neman dalilin wannan iska.
Sai muka ji wani irin huci mai karfi kamar ana
watsa wa wutar gobara ruwa. Mu duba haka sai
muka ga wani irin katon maciji shimil. Wannan
maciji girmansa ba ya misaltuwa, ba don yana
motsi ba sai mutum ya ce iccen rimi ne ya fadi
kasa aka sassare rassan aka bar gangar jikin.
Wanna iska da ta tayar da mu daga barci duk ta
hucinsa ce.
Kafin mu ankara har macijin nan ya zagaye mu
da jikinsa, ya sanya mu tsakiya kamar an zagaye
mu da katanga. Sai ya sa bakinsa ya cafko
mutum daya daga cikinmu, ya hadiye shi iya
kafada. Muka ga kafafun dan uwanmu na wutsil-
wutsil kamar dai yadda kafafun kwado kan yi
idan babba-da-jaka ko zalbe zai hadiye shi. Daga
nan sai macijin ya karasa hadiye falken nan gaba
daya. Sai muka rika jin wata kara rugugugu a
cikin cikin macijin nan yayin da kasusuwan dan
uwanmu ke karairayewa.

Daga nan sai maciji ya tafi ya bar mu nan cikin
tsananin tsoro da tashin hankalin wannan irin
mutuwa ta dan uwanmu. Muka fashe da kuka
muna cewa, "Wallahi wannan abin firgici ne da
tashin hankali! Duk lokacin da muka kubuta daga
halaka sai mu afka cikin wata wadda ta fi ta."
Da muna murna mun kubuta daga bakin dodo da
hatsarin teku, ga shi yanzu mun fada cikin wata
musibar da ta fi ta baya ban tsoro. Babu tsimi
babu dabara face daga Allah Madaukakin Sarki.
Idan da fari mun tsere wa bakin dodo yanzu yaya
za a yi mu tsere wa wannan maciji?
Daga nan sai maganar barci ta kare, muka tashi
muna zagaya tsibirin har muka iso ga wata
doguwar bishiya, muka yanke shawarar mu hau
samanta mu kwana saboda tsoron kada macijin
nan ya dawo. Muka haye saman bishiya muka
sami rassa masu fadi muka kwanta, ni ina daga
kololuwar bishiyar abokina yana daga kasana. Ba
maganar barci ake yi ba, ban da zulumi babu
abin da ke cikin ranmu.
Zuwa goshin asuba sai ga macijin nan ya zo
wajen itaciyar nan da muke kanta. Ashe ya tafi
inda muka fara kwantawa bai ganmu ba, sai ya
biyo warinmu har zuwa wurin bishiyar. Yana
zuwa kuwa sai ya yi rimi ya cafko abokin nan
nawa. Ya hadiye shi zuwa kafada, da ya gama
shure-shure sai ya iyar da hadiye shi.
Idanuna suka fito kwala-kwala kamar za

Please Login or Register in order to submit comment