Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su fadi
kasa don tsoro, ina kallon abin da ke faruwa. Na
ji kasusuwan abokina na karairayewa a cikin
cikin maciji. Da ya gama hadiye shi sai ya juya
ya tafi abinsa. Aka bar ni saura ni kadai a cikin
wannan tsibiri.

Bayan gari ya waye ina kan bishiya, na duba
ko'ina amma ban ga alamun macijin nan ba. Da
na tabbar ba ya kusa sai na sauko daga itaciya,
jikina a sanyaye kamar mara laka saboda
tsananin tsoro. Na tabbata babu abin da zai
kubutar da ni daga wannan maciji. Kafin gobe
war haka, ko shakka babu, na zama tarihi. Wata
zuciya ta ce in fada cikin teku mana in mutu da
maciji ya hadiye ni, amma sai na kasa aikata
haka, kun san rayuwa da dadi.

zanci gaba insha Allah

daga Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ.

whatsapp only pls
080327675479. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD
DAN DAKO

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Sabuwar Fassar
Ibrahim Malumfashi,
Danladi Haruna,
Bukar Mada.
Sindibad mai teku ya ci gaba da labari ya ce,
bayan gari ya waye ina kan bishiya, na duba
ko'ina amma ban ga alamun macijin nan ba. Da
na tabbar ba ya kusa sai na sauko daga itaciya,
jikina a sanyaye kamar mara laka saboda
tsananin tsoro. Na tabbata babu abin da zai
kubutar da ni daga wannan maciji. Kafin gobe
war haka, ko shakka babu, na zama tarihi. Wata
zuciya ta ce in fada cikin teku mana in mutu da
maciji ya hadiye ni, amma sai na kasa aikata
haka, kun san rayuwa da dadi.
Daga nan sai wata dabara ta fado mini a cikin
rai. Na je na karyo rassan itatuwa dogaye guda
biyar, kowane daya ya fi ni tsayi sau uku, na ciri
ciyawa na tufka igiyoyi, na ajiye su inda zan
kwana karkashin wata bishiya. Da na ga marece
ya fara shigowa sai na zauna karkashin itaciyar
nan. Na dauko itatuwa guda hudu na daure su da
kusurwowin juna, daya a kasa, daya a sama, daya
a gefen dama, daya a gefen hagu, kamar dai an
shata kofar wani babban daki. Icce na biyar
kuma na daura shi a tsakiya daidai tsawona. Na
shiga tsakiyar itacen na daure tafin kafafuna ga
icce na kasa, na yi rawani da iccen tsakiya
wanda ya taba kaina, na kwanta rigingine a
tsakanin itatuwan nan, sun killace ni ta ko'ina.
Can da dare ya yi, sai ga macijin nan sa-ka-ka-ka
ya biyo warina, ya zo inda nake. Ya yi niyyar
hadiye ni amma babu dama saboda itatuwa sun
tsare ni ko'ina. Ya juya ko wane bangare yana
neman makamata amma bai samu ba. Ni kuwa
na yi zurui da ido ko kiftawa ba na yi saboda
tsoro. Macijin nan sai ya tafi sai ya dawo har
asuba ta matso, da dai ya ga babu yadda zai yi
ya hadiye ni kuma ga gari na shirin wayewa, sai
ya hadiyi miyau ya yi tafiyarsa. Da gari ya waye
sai na kwance kaina, hannuwana na rawa kamar
tsohuwar da sanyi zai halaka. Na nufi bakin gaba
da sauri ko na sami hanyar fita daga cikin
wannan tsibiri. Domin na san idan dare ya yi
macijin nan zai dawo da tasa dabarar, don haka
ba lalle ba ne dabarar da na yi jiya ta fisshe ni
yau ba. Ina nan tsaye bakin gaba ina addu'a ga
Allah da ya koro mini da mafita, sai na hangi
wani abu can daga nesa cikin teku kamar jirgin
ruwa. Na murje idanuna na kara hangawa, babu
shakka jirgin ruwa ne, kuma babba irin na fatake.
Sai dai jirgin ba tsibirin da nake ya nufo ba, yana
shirin gilmawa ne ya wuce. Nan da nan na karyo
ganye bishiya, na yi ta daga shi sama ina
kadawa cikin iska, ina kira da karfi domin masu
jirgin su ji. Allah da ikonsa kuwa sai suka hango
ni, sai na ga jirgin ya karkato zuwa inda nake.
Da suka zo sai na kwashe labarina duka na gaya
musu, suka tausaya mini, suka saka ni cikin
jirginsu muka tafi. Na gode wa Allah da ya
kubutar da ni daga sharrin maciji na tausaya wa
abokaina da suka halaka, na yi musu addu'a.
Masu jirgi suka kawo mini abinci da ruwan sha
mai sanyi, na ci na koshi, na gode wa Allah na
gode musu bisa wannan karimci nasu. Hankalina
ya kwanta, karfin jikina ya dawo, na kara yin
godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya kubutar
da ni daga halaka, sai na ga abubuwan da suka
faru sun zama tamkar a mafarki. Ba mu gushe ba
muna tafiya, iska kuwa ta yi wa jirginmu dadi,
har muka iso ga wani tsibiri mai suna
Assalahidati, wannan tsibiri kuwa cike yake da
itatuwan sandal, Madugu ya ce a yada zango a
cikinsa.
Aka daure jirgi a bakin gaba, fatake suka fita da
hajarsu domin yin ciniki. Sai Madugu ya juyo
gare ni ya ce, "Bawan Allah, ga shi kai bako ne,
ka gaya mana cewa kai falke ne wanda ya hadu
da hadarurruka iri-iri har ka rasa hajarka. Ina so
in taimake ka ka koma gida da dan abin
hannunka, kada ka koma hannu rabbana. Kasan
an ce alheri ba ya da kadan, masu hikimar
magana ma suna cewa, ya da alheri a baya ka
tsince shi a gaba."

"Wane irin taimako kake so ka yi mini?" Na
tambaye shi.
Madugu ya ce, "Ka sani cewa mun fito gida da
wani falke, tun da muka sauka a wani tsibiri
muka huta ba mu kara ganin shi ba, ba mu sani
ba ko yana raye ko ya mutu, har yanzu dai ba
mu ji duriyarsa ba. Da na so sai mun koma gida
in nemi iyalinsa in aika musu da hajar. Amma
yanzu ina so in ba ka wannan haja ka yi
kasuwanci da ita a cikin wannan tsibiri, ribar duk
da aka samu, idan muka koma Bagadada, sai a
raba ta biyu ka dauki rabi a ajiye wa mai kayan
rabi. Ka yarda da haka in dauko maka hajar ka
tafi tare da sauran fatake?"
Yayin da na ji ya ambaci Bagadada sai na ji
kamar ya tsire ni da allura, ashe ma wadannan
fatake na wajenmu ne. Na amsa masa da sauri,
"Na yarda da wannan sharadi." Na yi ta gode
masa har babu adadi. Madugu ya ce a fito mini
da hajar falken nan da ya bace.
Mai kula da kayan jirgi ya tambayi Madugu,
"Wane suna aka rubuta a jikin hajar?"
Madugu ya ce, "Wadda aka rubuta wa sunan
Sindibad mai teku. Wanda ya bata a tsibirin
tsuntsayen Rukki. Wannan bako za mu ba kayan
ya yi fatauci da su, ribar duk da aka samu sai a
raba biyu ya dauki kashi daya."
Mai kula da kaya ya ce, "Ai kuwa hakan da ka yi
ya yi daidai ya Ra'isu."
Yayin da na ji Madugu ya ambaci sunana, ban
san lokacin da bakina ya subuce ba don murna
na ce, "Wallahi ni ne Sindibad mai teku."
Suka kalle ni haka galalala kamar masu kallon
motsattse. Da na ga dai alamun ba su yarda da
zancena ba sai na tambayi Madugu, "Yalla ka san
Sindibad din ne?"

"Ni ban san shi ba," in ji Madugu, "amma shi
mutumin Bagadada ne, ana yi masa lakabi da
Sindibad mai teku. Da shi muka baro kasar Iraki
har muka iso wani tsibiri na manyan tsuntsaye,
tun daga nan sai ya yi mana batan dabo. Muna
kyautaata zaton wata dabba ta cinye shi a cikin
tsibirin."

Daga nan sai na fashe da kuka, kuka mai
tsanani, na ce, "Ya kai wannan Madugu
amintacce! Wallahi ni ne Sindibad mai teku. Bari
ka ji yadda abin ya kasance haka. Yayin da muka
sauka a cikin wancan tsibiri da kake magana,
mun tafi tare da wasu fatake domin mu zagaya
cikinsa. Sai na zauna a gindin wata bishiya mai
sanyin inuwa, na ci abinci na sha ruwa, daga nan
sai na kishingida domin in huta sai barci ya
kwashe ni. Yayin da na farka sai na ga kun tafi
kun bar ni. Wallahi wannan hajar tawa ce, da a
ce za mu hadu da tajirai masu dibar lu'ulu'u a
kwarin macizai da sun shaida ni, domin na shaida
musu labarin yadda aka yi jirgi ya bar ni a tsibirin
Rukki, da yadda aka yi na baro tsibirin na fada
cikin kwarin macizai inda tajirai ke dibar lu'ulu'u
ta dabarar jefa danyen nama."
Lokacin da fatake suka ji jawabina sai suka
kewaye ni suna kallo, wasu suka yarda da
maganata wasu kuwa suka ce karya nake yi.

Amma yayin da wani daga cikin fataken nan ya ji
na ambaci kwarin macizai mai lu'ulu'u sai ya
kara dubana tun daga kasa har sama, ya juya ga
fatake ya ce musu, "Ku saurari zancena ya ku
'yan uwana. Idan ba ku manta ba lokacin da ina
ba ku labarin tafiye-tafiyen da na yi da abubuwan
ban mamaki da na gano, na gaya muku cewa
akwai wani kwarin macizai wanda yake cike da
lu'ulu'u, babu mai iya shigarsa balla ya kwaso
wannan dukiya. Na gaya muku cewa sai dai mu
rika yanka dabba muna fede ta, sai mu jefa
naman a cikin kwarin, lu'ulu'u mai yawa zai lillike
a jikin naman. Idan tsuntsaye masu farauta sun
shiga kwarin za su dauko naman su fito da shi,
sai mu kore su mu cire lu'ulu'un. Kamar yadda
na gaya muku wata rana na jefa dabbata a cikin
kwarin, yayin da tsuntsu ya fito da ita sai na ga
mutum a tsaye kusa gare ta. To, kun dai san
sauran labarin da na fada muku, daga karshe dai
kuka ce labarina zuki-ta-malli ne, wai babu wani
kwarin lu'ulu'u a duniya."

Fatake suka amsa gaba daya, "An yi haka kuwa,
ka gaya mana wannan labari amma daga karshe
muka karyata ka."

Falke ya nuna Sindibad ya ce, "To, wannan shi
ne mutumin da ya fito tare da dabbar da na jefa,
kuma ya ba ni dukiya mai yawa wadda tamaninta
ba ya misaltuwa, ya gaya mini sunansa Sindibad
mai teku. Daga nan muka tafi tare da shi har
birnin Basara, a can muka rabu ya ce zai nufi
Bagadada, mu kuma muka nufi tamu kasa. Na
gode wa Allah da ya turo shi nan, domin ya
gasgata labarin da na ba ku kuka karyata ni.
Kuna nan zaune kifin rijiya kawai, ba ku san
kome ba sai mutum ya kawo muku labari ku
karyata shi. Ni na yarda da shi, babu shakka
wannan hajarsa ce."
Yayin da Madugun jirgi ya ji zancen tajiri, sai ya
matso kusa gare ni, ya dube ni da kyau ya ce,
"Yaya yanayin hajarka take, idan har gaskiya
kake fada?"

"Abu kaza da abu kaza ne a ciki," na amsa masa.
Na kuma kara tuna masa wasu abubuwa da suka
faru yayin tafiyarmu a cikin jirgi daga Basara
zuwa tsibirin da suka bar ni. Daga nan sai ya
yarda lalle dai ni ne Sindibad. Ya rungume ni
cikin kirjinsa yana cewa, "Wallahi ya shugabana,
labarinka abin mamaki ne da ban tausayi. Godiya
ta tabbata ga Allah da ya kubutar da kai daga
halaka ya kuma sake sada ka da hajarka.".

kuna tare neda Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ10. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Sabuwar Fassarar:
Ibrahim Malumfashi,
Danladi Haruna,
Bukar Mada.
Sindibad mai teku ya ci gaba da labari ya ce,
Madugun jirgi ya yi godiya ga Allah da ya kubutar
da ni daga halaka ya kuma sake sada ni da
kayana. Na karbi hajata na shiga ciniki, in sayar
in saya, na sami riba mai tsananin yawa. Muka ci
gaba da zagaya tsibirai muna saye muna
sayarwa har Allah ya kawo mu kasar Hindu.
Muka sayi kayan yaji masu yawa irinsu citta da
tafarnuwa, saboda suna da riba sosai a Birnin
Bagadada. Daga Hindu kuma sai muka ci gaba
da tafiya har muka dangana da kasar Sin, muna
saye muna sayarwa.
A cikin tekun Hindu na ga abubuwan mamaki
wadanda ba su ko kidayuwa. Kadan daga cikinsu
su ne, na ga wani irin katon kifi kamar saniya, sai
ya fito da 'ya'yansa bisa ruwa yana ba su nono
suna sha, kamar yadda 'yan Adam ke shayar da
'ya'yansu. Saboda tauri da karfin fatar wannan
kifi, da ita ake yin sulke ko garkuwa wadanda ake
amfani da su wurin yaki. Haka kuma na ga wasu
kifayen, wasu siffar jakai wasu siffar dawaki. Na
ga kuma kunkuru wanda girmansa ya kai kafa
ashirin, wannan kunkuru zai iya daukar kato
kome girmansa, ya yi tafiya da shi bisa bayansa.
Na kuma ga wani tsuntsu wanda idan ya yi kwai
ba ya kyankyashe shi sai bisa ruwa.
Ba mu gushe ba muna tafiya cikin teku, cikin
kyakkyawan yanayin iska da tsarewar Ubangiji
har Allah ya nufe mu da dawowa Birnin Basara.
Na huta kwana biyu a Basara, daga nan sai na
dunkule kayana na nufi Birnin Bagadada, birnin
aminci. Na isa gidana lafiya, na tarar da 'yan uwa
da abokan arziki lafiya. A wannan tafiya na sami
riba bisa riba har abin ba ya kidayuwa. Na bayar
da sadaka ga mabukata, na ciyar da marayu, na
rarraba wa abokaina kyaututtuka iri daban-daban.
Na ci gaba da rayuwata kamar da, in ci mai kyau
in sha mai kyau. In sanya sutura ta alfarma in
harde bisa karaga ina hura hanci kamar wani
sarki. Wannan shi ne labarin tafiyata ta uku a
cikin teku. Idan Allah ya kai mu gobe lafiya, zan
gaya muku labarin tafiyata ta hudu a cikin teku
wadda ta fi sauran tafiye-tafiyen da na ba ku
labari ban mamaki.
Bayan Sindibad mai teku ya gama wannan labari
sai ya ba Sindibad dan dako dinari dari ya kuma
ce a kawo musu abinci da abin sha. Aka jera
akussan abinci da nama, Sindibad mai teku ya ci
tare da Sindibad dan dako a akushi daya, sauran
tajirar duka suka ci daga nasu akussan. Bayan
sun gama cin abinci, sun sallaci sallar isha'i sai
suka yi sallama da mai gida suka watse, kowa ya
nufi gidansa yana mamakin labarin mai gida. Dan
dako ya nufi gida zuciyarsa cike da mamakin
labarin da takwaransa mai teku ya bayar. Ya
kwanta barci yana alla-alla gari ya waye ya koma
gidan mai gida domin ya ji labarin tafiyarsa ta
hudu a cikin teku.
Tun da assalatu dan dako ya farka, bayan ya yi
sallar asuba sai ya zauna yana wuridi har gari ya
yi sha. Da ya ga rana ta kunno kai haskenta ya
sauka bisa jigayi da rufin gidaje, sai ya kimtsa ya
nufi gidan Sindibad mai teku. Ya isa gidan, bayi
suka shigar da shi dakin mai gida, ya zauna yana
jiran fitowarsa. Bai dade da zama ba sai ga
sauran tajirai suna shigowa daya bayan daya.
Bayan sun hadu gaba daya, can sai ga mai gida
ya fito cikin sutura ta alfarma, yana takawa dai-
dai kamar dawisu. Suka gaisa da sauran
abokansa tajirai, ya harde bisa karagarsa kusa ga
Sindibad dan dako. Aka kawo musu abinci suka
ci suka koshi, suka yi barkwanci a tsakaninsu
cikin annushuwa da farin ciki. Daga nan sai
Sindibad mai teku ya fara bayar da labarin
tafiyarsa ta hudu:
TAFIYAR SINDIBAD TA HUDU A CIKIN TEKU.
Ku sani ya ku abokaina, bayan na dawo gida
daga tafiyata ta uku da dimbin dukiya wadda ba
ta misaltuwa. Na zauna cikin farin ciki, ba ni da
wani aiki sai dai kullum in gayyato abokaina mu
wanke goma mu tsoma biyar. Ina nan kan haka
sai ran nan wasu attajiran fatake, abokaina daga
Basara, suka kawo mini ziyara. Bayan mun gama
kwasar gara sai muka shiga hirar duniya da
labarin tafiye-tafiye. Nan fa zuciyata ta motsa,
suka takalo mini sha'awar sake fita cikin duniya,
na manta kwata-kwata da wahalhalun da na sha
a baya. Na yi sha'awar ganin al'ummomin wasu
kasashe da al'adunsu. Nan take na yanke
shawarar sake fita cikin duniya domin yin
fatauci.
Tun daga wannan rana na fara shirye-shiryen
tafiya, na sayi kayayyakin zuwa fatauci masu
yawa da tsada fiye da wadanda na taba tafiya da
su a baya. Da lokacin tafiya ya yi sai na yi
sallama da 'yan uwa da abokai, na kwashi kayana
sai Birnin Basara, inda zan hadu da abokan
tafiyata, wadanda suke su ne manya-manyan
attajiran birnin. Muka shiga jirgi muka fada teku.
Iska ta yi wa jirginmu dadi, muka yi ta tafiya
daga wannan tsibiri zuwa wancan, muna saye
muna sayarwa. Ran nan muna tafiya cikin dadin
rai, kwatsam sai teku ta canja mana hali.
Guguwar ruwa ta taso, rakuman ruwa kuwa suka
yi ta kwallo da jirginmu kamar zai kife. Da
Madugu ya ga haka sai ya ce a dakatar da tukin
jirgi. Jirginmu ya tsaya cak a tsakiyar teku, yana
tangal-tangal kamar zai kife saboda rakuman
ruwa da ke juya shi, mu kuwa babu abin da muke
yi sai addu'a. Muna cikin wannan hali sai wata
guguwa mai karfi ta keto daga cikin teku ta bugi
jirginmu bugu mai karfi. Nan take jirgi ya
kakkarye, dukanmu muka dulmiye cikin teku duk
da kayanmu, babu wanda ya koma ta kan dan
uwansa, kowa sai ya yi ta kansa.
Na yi ta iyo cikin ruwa ina sallallami har
hannuwana suka gaji, na sakankance da halaka.
Ina cikin wannan hali sai Allah ya koro mini da
wani yankin itace babba na jirginmu da ya karye,
na kama shi da kyar na haye. Ashe akwai sauran
fataken da ba su nutse ba, su ma sai Allah ya yi
musu katari da hawa bisa wannan icen jirgi tare
da ni.

Muka rika tura ruwa da kafafunmu allon nan yana
tafiya da mu da taimakon iska. Muka kasance
cikin wannan hali kwana daya da yini daya, iska
da rakuman ruwa suka yi ta tura allon nan da
sauri. A cikin kwana na biyu sai teku ta lafa, iska
mai dadi ta rika kadawa, rakuman ruwa suka
kwanta. Ba mu gushe ba muna tafiya bisa allon
jirgi har muka dangana ga wani tsibiri a tsakiyar
teku.
Muka ja jiki muka sauka cikin tsibirin, muka yi
kwance kamar matattu saboda tsananin gajiya,
ga yunwa ga kishirwa, ga kuma uwa uba sanyi
mai tsanani da ke ratsa mana jiki. Bayan mun
dan sarara sai muka tashi muka rika zagaya
tsibirin. Wannan tsibiri cike yake da ciyawa, babu
wasu itatuwan kirki balle mu sami 'ya'yan itacen
da za mu ci. Da muka ga dai yunwa na shirin
halaka mu, tilas muka rika dibar ciyawa muna ci
kamar dabbobi. Da muka cika cikannanmu da
ciyawa, sai muka sami wuri muka kwanta, barci
kuwa ya yi awon gaba da mu, ba mu farka ba sai
da gari ya waye.
Bayan gari ya waye sai muka tashi muka ci gaba
da zagayawa cikin tsibiri, hagu da dama. Can sai
muka hangi wani gini kamar gida. Muka nufi
wannan gida wai ko za mu sami abinci da ruwa.

Yayin da muka isa bakin kofar gidan sai muka ga
wasu mutane suna fitowa daga cikinsa. Mutanen
nan tumbur suke haihuwar uwarsu, babu mai ko
bante balle riga, su ake kira zindirawa. Suna
ganinmu sai suka kama mu, suka ja mu suka nufi
cikin gidan nan, ba su zame ko'ina da mu ba sai
gaban wani tsoho, yana zaune bisa abin zama.
Ashe sarkinsu ke nan.
Tsoho ya yi mana ishara da mu zauna. Muka
zauna, amma jikinmu bai ba mu ba. Mutanen nan
suka kawo mana wani irin abinci wanda ba mu
san shi ba, ba mu kuma taba ganin irinsa ba duk
tsawon rayuwarmu. Abokan tafiyata ba su yi
wata-wata ba sai suka far ma abincin nan da ci,
saboda tsananin yunwa, kamar wadanda suka
shekara ba su ci kome ba, da ma an ce wanda
ruwa ya ciwo idan aka mika masa takobi sai ya
kama. Ni kuwa raina bai ba ni ba akan in ci
abincin nan, duk da matsananciyar yunwar da
nake ji, ko kyamar abincin ne ko kuwa wani abu
ne na daban ya hana ni cin sa, Allah kadai ya
sani. Ashe rashin cin abincin nan alheri ne gare
ni, shi ne sanadin kawowata har zuwa wannan
lokaci da nake ba ku wannan labari, ban mutu
ba. Domin kuwa abokan nan nawa na gama cin
abincin sai duk suka fita daga cikin hayyacinsu,
suka rika yin wasu halaye kamar mahaukata, ko
kuma kamar wadanda aljanu suka shafa. Daga
nan sai zindirawan nan suka kawo musu ruwan
wata irin kwakwa suka kwankwada, suka kuma
shafe jikinsu da ruwan kwakwar. Zindirawa na
gama aikata wannan abu ga abokaina, sai
abokan nan nawa suka rude, idanunsu suka rufe,
suka fada wa sauran abinci da ci, ba ji ba ga ni,
sai ka ce guzumar da ta ketare rani da kyar aka
kai ta cikin danyar ciyawa. Tausayinsu ya kama
ni saboda yanayin da na ga sun shiga. Ni kuwa
babu wanda ya kula ni daga cikin zindirawan nan,
kuma ba su tilastani in ci abincin nan ba, don
haka ba su shafa mini kome ga jikina ba. Duk da
haka zuciyata cike take da tsoron abin da zai
faru gare ni.
Ina ta kallon wadannan zindirawa a sace, can sai
na tuna wani labari da na taba ji game da su. Su
dai wata kabila ce ta matsafa, sarkinsu kuwa
dodo ne mai cin mutane. Duk mutanen da
kaddara ta koro cikin tsibirinsu sukan kama su,
su ba su wannan abinci na tsafi wanda zai juyar
musu da hankali, daga nan sai su ba su ruwan
kwakwan nan su sha, bayan sun sha su shafe
musu jiki da shi. Shi ke nan sai hankulan
wadannan mutane ya gushe, cikannansu su bude
kamar randa, ta yadda za su yi ta cin abinci ba
su koshi. Cikin 'yan kwanaki kadan sai su yi bul-
bul kamar turkakkun shanu. Su za a rika yanka
wa Sarki kamar raguna, ana gasa masa yana ci.

Su kuwa talakawan Sarki danyu suke cin nasu
mutanen, ba ma sai an gasa ba.
Yayin da na tuna wannan labari game da
wadannan zindirawa sai hankalina ya tashi, na
tausaya wa abokaina, ni kuma na shiga tunanin
abin da zai faru gare ni. Aka damka abokan nan
nawa ga wani mutum wanda zai rika kula da su.
Kullum sai ya rika fita da su kiwo cikin tsibirin
nan, suna cin ciyawa ba su kula ba, kamar
dabbobi. Nan take kuwa cikin 'yan kwanaki suka
yi kiba. Ni kuwa duk na rame na yankwane,
saboda ban yarda na ci abincinsu ba, duk kuwa
da cewa kullum sai sun kawo mini abincin wai in
ci. Da suka ga dai na ki kula abincinsu, kuma ga
shi duk na rame, daga fata sai kashi, sai suka yi
watsi da ni suka ma daina kula ni. Ni kuwa da na
ga haka sai na saci jiki wata rana na sulale daga
gidan nan na gudu.

Bayan na yi nisa da gidan zindirawa sai na tasar
wa bakin gabar teku, wadda take da nisa kwarai
daga gidan zindirawa. Na kusa isa bakin gaba ke
nan, sai na hangi wani tsoho daga cikin
zindirawan nan. Ina ganinsa na shaida shi, shi ne
wanda ke kiwon mutanen da suka kama.

daga Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ
11. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.
Sindibad mai teku ya ci gaba da labari ya ce,
bayan na yi nisa da gidan zindirawa sai na tasar
wa bakin gabar teku, wadda take da nisa kwarai
daga gidan zindirawa. Na kusa isa bakin gaba ke
nan, sai na hangi wani tsoho daga cikin
zindirawan nan. Ina ganinsa na shaida shi, shi ne
wanda ke kiwon mutanen da suka kama. Yayin
da tsohon nan ya gan ni sai ya shaida ni, ya san
cewa kuma ina cikin hankalina ba kamar sauran
da yake kiwo ba, don haka sai ya tabbatar da
cewa ina shirin tserewa ne. Ga mamakina sai na
ga yana daga mini hannu yana yi mini ishara da
in koma da baya in bi ta hanyar da ta yi hannun
dama. Na ga yana nuna mini cewa wannan
hanyar da na biyo mai hatsari ce. Don haka ban
yi gardama ba, sai na juya da baya na nufi
hanyar da ta yi hannun dama. Na rika gudu don
tsoron kada a kama ni, idan kuma na gaji da gudu
sai in yi tafiya, har na bace wa tsohon nan.
Yayin da rana ta fadi duhun dare ya fara
mamaye tsibirin nan, sai na sami wuri na zauna.

Na yi niyyar in kwanta in yi barci saboda gajiya,
sai wata zuciya ta ce ahir! Don haka na yi zaune
ina ta karanto duk wata addu'a da ta fado mini
cikin zuciya. Can da dare ya raba sai na tashi na
ci gaba da tafiya. Ban gushe ba ina tafiya har
hasken safiya ya keto sararin samaniya, wuri ya
yi sha da hasken safiya gwanin ban kaye. Rana
ta dago sama, haskenta ya haske duwatsu da
ciyawa da jigayi. Daga nan fa sai cikina ya fara
kiran ciroma, na duka na ci ciyawa da hakukuwa
gudun kada in halaka da yunwa. Na lasa dan
danshi-danshin raba da ke jikin ciyayi a matsayin
ruwa, daga nan sai na ji karfin jikina ya dan
dawo. Na ci gaba da tafiya tsawon wannan rana,
ban gushe ba har sai da dare ya yi. Na zauna na
huta, bayan dare ya raba na ci gaba da tafiya har
zuwa wayewar gari. Na ci ciyawa, na sha ruwan
rabar da ke jikin ciyawa. Ban gushe ba cikin
wannan hali har tsawon kwana bakwai. A cikin
kwana na takwas ne na hangi wani abu can daga
nesa kwarai, ban gane ko menene ba.
Na nufi wannan abu ina cewa a cikin raina ko ma
menene ya kashe ni in huta da wannnan bakar
wahala. Yayin da na yi kusa da abun sai na ga
ashe gungun mutane ne suna dibar goran yaji. Da
suka hango ni sai suka taso mini, suka zagaye ni
suna kallo, kamar masu kallon wata bakuwar
dabbar da ba su taba gani ba. Suka tambaye ni,
"Mutum ko aljani? Daga ina ka fito cikin wannan
tsibiri."

Na amsa musu, "Ni mutum ne dan uwanku." Na
ba su labarin abin da ya faru gare ni duka, da
wahalhalun da na sha. Na kwashe labarina duka
na gaya musu, na kuma fada musu irin bakar
wahalar da na sha a cikin wannan tsibiri. Suka yi
mamaki matukar mamaki, suka ce, "Wallahi
labarika abin mamaki ne da tausayi matuka. To,
amma yaya aka yi har ka gudo daga al'ummar
zindirawa, wadanda babu wani mutum da zai
shiga hannunsu ya kuma tsere daga gare su?"
Na gaya musu ni ma ban sani ba. Allah dai ne ya
kubutar da ni daga hannunsu. Na gaya musu abin
da ya faru ga abokan tafiyata. Mutanen nan suka
zaunar da ni karkashin wata bishiya mai sanyin
inuwa, suka kawo mini abinci mai rai da lafiya
suka girke a gabana. Suka ce in ci abinci kafin
su gama dibar goran yaji. Na nade hannun rigata
na sa abincin nan gaba. Na yi ta wulka loma har
ina sarkewa, kamar wanda za a kwace wa
abincin. Ban cire hannuna daga cikin akushin
abinci ba har

Please Login or Register in order to submit comment