Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tausayin mu ba,
ya koro mana da hanyar kubuta, babu shakka
dukkanmu halakakku ne. Don Allah ku yi ta
addu'a, yalla a sami daya daga cikinku wanda
Allah zai karbi addu'arsa ya kubutar da mu."

Yayin da muka ji bayanin Madugu sai muka
dukufa ga rokon Allah, amma ba a jima da
wannan magana ba sai wata kakkarfar iska ta
taso ta yi ta juya jirginmu kamar ana juya waina.
Lokacin da muka ga haka sai duk muka fara
sallallami muna rokon juna gafara, don mun
tabbatar da halakarmu ta zo. Iska ta kwashi
jirginmu ta buga shi ga wani babban dutse a
tsakiyar teku, nan take ya karairaye, allo-allo,
muna gani dukiyoyinmu suka dulmiye cikin
ruwa. Wa ma yake ta dukiya ana maganar ceton
rai. Da yawa daga cikin fatake suka halaka a
cikin ruwa sai 'yan kadan da Allah ya tarfa wa
garinsu nono, suka kama dutsen nan suka hau.
Ina daga cikin wadanda suka hau dutse. Dutsen
nan kuwa dogon dutsen ne, saboda tsawonsa
har ba a iya ganin karshensa, ya tafi har cikin
giza-gizai. Dutsen kuma daga kasa ya rufe
ko'ina kamar an gina katanga. Ashe dutsen nan
bisa wani dan karamin tsibiri yake. Da muka
gangara cikin tsibirin sai muka ga babu kome a
cikinsa na daga itatuwa ko ciyawa, daga yashi
sai yashi, sai kuma allunan jiragen ruwa masu
yawa wadanda suka kakkarye, ga kuma dukiya
nan babu adadi wadda ruwan teku ya turo bisa
tsibirin daga duk wani jirgi da ya yi hatsari kusa
ga dutsen nan. Muka sami korama wadda
ruwanta yake gangarowa daga saman dutse,
ruwan mai dadi ne. Ruwan koramar nan ya yi
wutsiya biyu, daya wutsiyar na gangarawa cikin
teku, daya kuma sai ta bi tsawon dutsen daga
kasa ta koma karkashinsa. Fatake kuwa da
suka ga dukiya tsibi-tsibi a cikin wannan tsibiri,
sai suka zama tamkar mahaukata, suka rika
diba suna ta watsawa sama suna kururuwa. Na
nufi wurin koramar nan domin in sha ruwa, sai
na ga tsakuwar da ke cikinta duk lu'ulu'u ne mai
darajar gaske, rairayin wurin kuwa duka dussar
zinariya ce da sauran jauhari iri-iri, sai daukar
ido suke yi wal, wal, wal, kamar mudubi.
Haka kuma a cikin wannan tsibiri akwai
sandunan Siniya da sandunan Kumriya, ga
kuma ambar mai yawa wanda zafin rana ke
narkawa yana gudana gefen koramar nan yana
shiga cikin teku. An ce irin wannan ambar din ne
mai gangarawa cikin teku wasu dabbobi da ke
cikin ruwa kan hadiye saboda kanshinsa, amma
da zarar sun hadiye shi za su ji cikinsu yana zafi,
kamar ana hura musu wuta, dole sai sun
amayar da shi. Ambar din da suka amayar zai
daskare bisa ruwa ya canja launi, daga karshe
teku ta tura shi gefenta, idan fatake da matafiya
suka gan shi, wadanda suka san shi sai su diba
su yi ta cika goruna, su narka, suna sayarwa, shi
ne turaren ambar. Yanzu kuwa ga ambar a cikin
wannan tsibiri, gangariyarsa. Ba a samun irin
wannan ambar a cikin birane, saboda babu wani
dan Adam da ke iya zuwa wannan tsibiri har ya
same shi, wanda ake samu shi ne wanda
dabbobin ruwan nan kan amayar.
Muka ci gaba da zagayawa cikin tsibiri muna
kallon ikon Allah, muna cike da mamakin irin
tarin dukiyar da ke cikinsa, zukatanmu kuma
cike da zullumin abin da zai faru gare mu. Bayan
wani lokaci sai yunwa ta far mana, muka yi ta
bincike cikin tarkacen dukiyoyin nan har muka
sami wata jaka da gurasa a cikinta, duk ta
bushe. Wannan gurasa muka rika ci kadan-
kadan, muna jin tsoron ta kare babu wani abinci.
Karfinmu ya fara karewa, ciwo ya kama wasu
daga cikin fatake, suka rika mutuwa daya bayan
daya, ba mu gushe ba cikin wannan hali muka
rage saura 'yan kadan, da yawa daga cikin mu
sun mutu. Duk wanda ya mutu sai mu yi masa
wanka mu yi masa sutura, daga cikin wata hajar
suturu da muka samu, mu haka kabari mu rufe
shi. Ba mu gushe ba cikin wannan hali har sai
da dukkan fataken nan suka mutu, na rage
saura ni kadai ina gararamba a cikin tsibirin da
saurar 'yar gurasar da ba ta wuce guda biyar ba.
Duk lokacin da na tuna abokan tafiyata sai in
buga salati ina cewa, "babu tsimi babu dabara
face daga Allah madaukakin Sarki, da ma ni na
fara mutuwa kafin saura. Yanzu idan na mutu
shi ke nan babu mai rufe ni."17 HIKAYAR SINDABAD MAI TEKU DA SINDABAD DAN DAKO

Sindibad Matafiyi ya ci gaba
da labarinsa yana cewa, kuna ji na ya ku
abokaina, yayin da dukkan abokan tafiyata suka
mutu a cikin tsibiri, na kasance saura ni kadai a
cikin sa da 'yar gurasar da ba ta wuce guda
biyar ba. Sai na tona wani rami mai zurfi da fadi
ina cewa a cikin raina, "wannan shi ne kabarina.
Idan abincina ya kare, na fara sansanar kanshin
mutuwa, in kwanta a ciki in mutu, iska ta tura
rairayi ya rufe ni." Na yi ta zargin kaina da kaina
bisa ga barin gida da na yi, idan dai don dukiya
ne, ai ina da ita a gida wadda tsawon rayuwata
ba zan iya cinye ko da rabin ta ba. To me ya sa
na baro gida? Wata zuciya ta amsa mini da,
"kaddara!" Na tuna irin wahalhalun da na shiga
a tafiye-tafiyen da na yi a baya, da yadda Allah
ke kubutar da ni bayan na debe tsammani daga
kubuta. Na tambayi kaina, anya zan kubuta
daga wannan tafiya kuwa?
Ban gushe ba ina nadama sai wani tunani ya zo
mini game da wutsiyar koramar nan mai shiga
karkashin dutse. Na ce babu shakka in ga inda
ruwan wannan korama ke zuwa, wa ya sani ma
ko ruwan ya bulla har bayan dutsen, watakila
ma in sami 'yan Adam a wurin? Sai na debo
sandunan Siniya da na Kumriya, na samo alluna
masu fadi daga fasassun jiragen ruwan nan, na
adanta dan karamin kwale-kwale wanda zai iya
daukata da wasu kayayyaki. Bayan na gama
shirya wannan jirgi yadda nake son shi, sai na
jefa shi cikin koramar, kun san mutum game da
son dukiya, sai na debi lu'ulu'u da sandunan
Siniya da na Kumriya, na kwashi rairayin
zinariya, na debi turaren ambar daskararre,
gangariya, mai yawan gaske na cika goruna da
shi. Na sanya duk wadannan kaya a cikin
kwale-kwale na shiga, na tuka, na rika bin
wutsiyar korama mai shigewa cikin dutse. Na ce
a cikin raina, "idan Allah ya nufa in tsira, sai in
tsira, idan kuwa Allah bai nufa in tsira ba
gwamma in mutu cikin koramar nan da in mutu
cikin rairayin tsibiri. Na tafi cikin jirgi kamar
yadda aka fada cikin wannan waka:
Tashi ka motsa ka bar nan wurin,
Gida ne na tsoro da halin tsiya.
Ka nemi wadata cikin duniya,
Akan kama zomo da son juriya.
Kasan duk wahala takan zan gudu,
Sauki yakan zo bayan shan wuya.
Wurin duk da an kaddara mutuwar,
Mutum za ya komo ba ya tirjiya.
Ina gargadin ka a kan sirrukanka,
Ka boye su gam-gam cikin zuciya.
Ban gushe ba ina tuka jirgi ina bin tsawon
korama har na kawo inda take shiga karkashin
dutse. Wurin kuwa wani irin kogo ne mai girman
gaske. Kwale-kwale ya shiga cikin kogon da ni,
na ci gaba da tuka shi ruwa na ja na. Yayin da
na shiga cikin kogon nan sai wani irin duhu ya
mamaye ni har ba na iya ganin abin da ke
gabana. Bayan haka kuma sai na ji kamar ina
gangarawa kasa ne a cikin wani kwari mai zurfi.
Duk da haka dai ban karaya ba, na ci gaba da
bin ruwan koramar nan. Ina cikin tafiya sai na
kawo wani wuri inda fadin koramar ya ragu har
kwale-kwalena na taba gabar koramar, kuma na
ji kaina na tabo rufin wannan kogo, babu damar
juyawa da baya, a haka dole na ci gaba da
tafiya ina tunanin idan fadin koramar nan ya ci
gaba da raguwa ai kuwa jirgina ba zai iya ci
gaba da tafiya ba, watakila ya makale a nan, shi
ke nan na kawo kaina mahalaka.
Na ci gaba da tafiya cikin kwale-kwalena, kaina
na ta buguwa da bangon dutsen da ke
samansa, da na ga haka sai na yi kwance rub-
da-ciki cikin jirgi, na bar wa Allah ikonsa. Jirgina
sai tafiya yake yi kwana da kwanaki, ni dai ba
na iya bambance dare balle rana. Rannan dai ko
barci ne ya kwashe ni, ko kuwa suma na yi, ban
sani ba. Sai dai na farka na ji wata sassanyar
iska na bugu na, da na bude idona sai na ga
haske fayau. Na dubi inda nake na ga har yanzu
dai ina kwance ne a cikin jirgin nan a gefen wata
babbar korama. Na yi karfin hali na mike zaune,
in duba haka sai na ga ashe mutane ne suka
zagaye ni suna kallo, kamar masu kallon wata
bakuwar halitta. Na dube su da kyau sai na ga
ashe mutanen Hindu ne da mutanen Abasiniya.
Yayin da suka ga na mike zaune ina kallon su
sai wani daga cikin su ya yi mini magana, amma
ban ji abin da yake fada ba, saboda ba na
fahimtar wannan harshe. Duk abin nan da ke
faruwa sai na ga kamar mafarki ne nake yi.
Yayin da mutanen nan suka gane ba na
fahimtar zancensu, sai wani daga cikin su ya
canja harshe ya yi mini magana da Larabci,
"aminci ya tabbata a gare ka, ya kai dan uwana.
Wanene kai? Daga ina ka zo wannan wuri? Don
Allah menene bayan dogon dutsen nan wanda
babu wani mutum da ya taba zuwa wurin?"
Na mayar masa da sallamar da ya yi mini da
farko, "aminci ya tabbata a gare ka, ya dan
uwana." Maimakon in ba shi amsar
tambayoyinsa sai ni kuma na kora masa tawa
tambayar, "don Allah wannan wane wuri ne? Ku
kuma wadanne irin mutane ne?"
Ya amsa mini, "mu manoma ne. Mun fito ne
domin mu yi ban ruwa ga kayan lambunmu sai
muka same ka cikin wannan kwale-kwale kana
barci. Muka kyale ka har sai da ka farka da
kanka. Gaya mana yadda aka yi ka zo nan."
Na ce musu su kawo mini abinci idan suna so su
ji labari, na fada musu yunwa nake ji kamar za
ta halaka ni. Nan da nan suka kawo mini akushi
cike da abinci, na ci mai isa ta na koshi, na ture
akushi gefe na yi hamdala ga Sarki Allah. Bayan
hankalina ya kwanta, karfin jikina ya dawo, sai
na kwashe dukkan labarina na fada musu, na
kuma fada musu abin da ya faru gare ni lokacin
da na shiga karkashin dutsen nan.

Da suka ji labarina sai suka rika
tafa hannuwa don mamaki, suka ce da junansu,
"babu makawa mu kai shi ga Sarki ya gaya
masa wannan labari mai ban mamaki."

Suka kwashe ni duk da kwale-kwalena da kayan
da na labto masa na lu'ulu'u, da jauhari, da
zinariya, da turaren ambar, da sauran dukiya
mai yawa, suka kai gaban Sarkinsu wanda ake
kira Sarkin Sarandib. Suka fada masa labarina
duka, Sarki ya yi mamaki, ya yi mini barka da
arziki, ya marabce ni da girmamawa. Ya sake
tamabaya ta labarina, na duka na fede masa biri
har wutsiya, ya yi mamaki, matukar mamaki. Na
tafi ga kayana na debo lu'ulu'u da sandunan
Siniya da sandunan Kumriyya da turaren ambar
mai yawa na kawo wa Sarki. Ya karba ya yi
godiya mai yawa, ya sa mini albarka. Sarki ya sa
aka ba ni wani gida nasa nan kusa ga fada, na
zauna tare da shi cikin dadin rai da girmamawa.
Tsibirin Sarandib yana bisa wani yanki ne na
duniya wanda lokutan dare da yini duka sa'o'i
goma sha biyu ne maimakon ashirin da hudu,
don haka dare da yininsu takaitacce ne ainun ba
kamar na sauran wasu yankuna na duniya ba.
Tsawon tsibirin awo tamanin ne, fadinsa awo
talatin. Tsibirin na kewaye da wani babban
dutse mai tsawo, wanda ya yi wa tsibirin kamar
baka, fadin dutsen daga farkonsa zuwa
karshensa tafiyar kwana uku ce ba tsayawa.
Sa'annan daga can karshen dutsen akwai wani
kwari mai zurfi da fadi. Daga gefen dutsen akwai
itatuwa da tsire-tsire na kayan yaji masu yawa,
daga cikin dutsen kuma ana samun nau'o'in
jauhari iri-iri, kamar su zinariya da dangoginta. A
cikin kwarin kuma akwai irin su lu'ulu'u da
sauran wasu ma'adinai masu daraja. Nakan tafi
wurin wannan dutse ina kallon sa, ina mamakin
irin ajiyar da Allah ya yi a cikinsa, idan na gama
kallon sa sai in koma fada wurin Sarki.
Sau da yawa fadawa kan tambaye ni game da
mulkin Halifa Haruna Rashid. Nakan gaya musu
irin yadda yake tafiyar da mulkinsa cikin adalci
da yadda yake kaunar talakawansa. Idan suka ji
haka sai su yi ta mamaki suna sa masa albarka.
Haka ma idan na hadu da fatake sai mu zauna
mu yi ta hirar kasashensu da irin yadda
sarakunansu ke tafiyar da mulkinsu, ta haka na
sami labrin kasashe masu yawa. Akwai ma
lokacin da Sarki da kansa ya tambaye ni labarin
Halifa Haruna Rashid da yadda yake gudanar da
mulkinsa, na gaya masa kome na daga mulkin
Halifa a Bagadaza. Sarki ya yi mamaki ya ce,
"wallahi Halifa kuwa ya cika Sarki mai adalci.
Babu makawa idan ka tashi komawa kasarku
zan ba kyauta ka kai masa."

Na ce ma Sarki, "na ji, na karba. Zan kuwa
shaida masa cewa kana matukar kaunarsa
saboda adalcinsa."
Na ci gaba da zama tare da Sarki cikin
girmamawa da kwanciyar hankali. Muna nan
kan haka, wata rana ta daga ranaku sai na ji
labarin cewa akwai fataken da za su tashi zuwa
Birnin Basara, na ce a cikin raina, "ai kuwa bai
kamata fataken nan su bar ni ba." Na tafi wurin
Sarki na fadi kasa na sumbaci kafafunsa, na
fada masa labarin fatake, na ce ina so in bi su
zuwa gida.
Sarki ya dube ni ya ce, "duk abin da ka yi daidai
ne. Idan ka ga dama kana iya ci gaba da zama
da mu har bayan ranka, idan kuma ka ga dama
ka koma kasarku, babu mai hana ka."
Na kara sunkuyar da kai kasa na ce, "wallahi ina
jin dadin zama da kai, Allah ya ba ka nasara. Ba
domin zuciyata na shaukin ganin 'yan uwana da
abokaina ba, da na zauna tare da kai har
abada."

Sarki ya sa aka kira masa Madugun fatake, ya
damka ni a kan kulawarsa. Ya biya mini kudin
jirgi da kudin kayana. Ya sa Ma'aji ya kwaso
mini dukiya mai yawa daga taskarsa, ya ba ni
kyauta. Ya kuma kawo wata gagarumar kyautar
ya ba ni, ya ce idan na isa gida lafiya in kai wa
Halifa. Ya kuma kawo wasika ya ba ni, ya ce, "ka
kai wa Halifa wannan wasika, hannunka da
nasa. Ka ce muna gaishe shi sosai."
Ita wasikar an rubuta ta ne bisa fatar wata
dabba wadda ta fi fatar tinkiya kyau, nesa ba
kusa ba, launin fatar kuwa rawaya ne. An yi
rubutun da launin shudi, irin na ruwan teku ko
sararin samaniya. Abin da wasikar ta kunsa shi
ne:

Aminci ya tabbata a gare ka. Daga Sarkin Hindu
mai rundunar giwaye dubu, mai fadar lu'ulu'u da
zinariya dubu. Bayan godiya ga Allah
Madaukakin Sarki, da salati ga shugabanmu
Annabi Muhammadu da Alayensa, ga wata 'yar
kyauta nan da muka bayar a kawo maka, muna
fatar za ka yi murna da ita. Mun dauke ka dan
uwa kuma masoyinmu saboda irin labarin
alherinka da muka ji, muna fatar za mu sami
bayanin wannan wasika daga gare ka. Sai dai
kyautar ba wata kyautar a-zo-a-gani ba ce
idan muka yi la'akari da irin karfin arzikinka.
Amma ai an ce, dirhamin masoyi ya fi zinari dubu
na makiyi. Wassalam, mun bar ka lafiya. Sai
mun ji daga gare ka.
Kyautar da Sarki ya bayar a kai wa Halifa kuwa
ita ce ta wani babban gora cike da zababben
lu'ulu'u mai darajar gaske. An yi wa goran nan
ado da zane-zane iri-iri, masu ban sha'awa, da
ruwan zinariya da azurfa, an shafe shi da bulari,
yana ta kyalli. Akwai kuma karaga wadda aka
shimfida fatar maciji bisanta, irin fatar macizan
nan masu hadiye giwa. A jikin fatar akwai wasu
dabbare-dabbare ko digo-digo, girmansu kamar
dirhami, an ce duk mai kallon fatar macijin nan,
to, ba ya rashin lafiya har abada.

Akwai kuma miskali dubu na sandunan Hindiya, da kuma
wata kuyanga kyakkyawa tamkar rana.
Yayin da lokacin tashin mu ya kusa, sai na yi
sallama da Sarki da dukkan abokaina. Da ranar
tafiya ta zo na shiga jirgi tare da sauran fatake,
muka mika cikin bahar. Iska ta yi mana dadi,
muka tafi muna addu'ar neman kariya daga
Allah Ubangijin talikkai. Cikin kudurarsa da
ikonsa kuwa muka isa birnin Basara lafiya,
bayan na huta kwana biyu, sai na shirya kayana
duka na nufi Bagadaza, Gidan Aminci. Da isa ta
Bagadaza ko gidana ban leka ba, sai na nufi
fada wurin Halifa.

daga Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ18 HIKAYAR SINDABAD MAI TEKU DA SINDABAD DAN DAKO

Bayan godiya ga Allah
Madaukakin Sarki, da salati ga shugabanmu
Annabi Muhammadu da Alayensa, ga wata 'yar
kyauta nan da muka bayar a kawo maka, muna
fatar za ka yi murna da ita. Mun dauke ka dan
uwa kuma masoyinmu saboda irin labarin
alherinka da muka ji, muna fatar za mu sami
bayanin wannan wasika daga gare ka. Sai dai
kyautar ba wata kyautar a-zo-a-gani ba ce
idan muka yi la'akari da irin karfin arzikinka.
Amma ai an ce, dirhamin masoyi ya fi zinari dubu
na makiyi. Wassalam, mun bar ka lafiya. Sai
mun ji daga gare ka.
Kyautar da Sarki ya bayar a kai wa Halifa kuwa
ita ce ta wani babban gora cike da zababben
lu'ulu'u mai darajar gaske. An yi wa goran nan
ado da zane-zane iri-iri, masu ban sha'awa, da
ruwan zinariya da azurfa, an shafe shi da bulari,
yana ta kyalli. Akwai kuma karaga wadda aka
shimfida fatar maciji bisanta, irin fatar macizan
nan masu hadiye giwa. A jikin fatar akwai wasu
dabbare-dabbare ko digo-digo, girmansu kamar
dirhami, an ce duk mai kallon fatar macijin nan,
to, ba ya rashin lafiya har abada. Akwai kuma
miskali dubu na sandunan Hindiya, da kuma
wata kuyanga kyakkyawa tamkar rana.
Yayin da lokacin tashin mu ya kusa, sai na yi
sallama da Sarki da dukkan abokaina. Da ranar
tafiya ta zo na shiga jirgi tare da sauran fatake,
muka mika cikin bahar. Iska ta yi mana dadi,
muka tafi muna addu'ar neman kariya daga
Allah Ubangijin talikkai. Cikin kudurarsa da
ikonsa kuwa muka isa birnin Basara lafiya,
bayan na huta kwana biyu, sai na shirya kayana
duka na nufi Bagadaza, Gidan Aminci. Da isa ta
Bagadaza ko gidana ban leka ba, sai na nufi
fada wurin Halifa. Aka yi mini iso na shiga
wurinsa, na kawo kyautar Sarkin Hindu na ba
shi. Ya tambaye ni labarin Sarkin, na gaya
masa.
Yayin da Halifa ya karanta wasika sai ya
tambaye ni, "ya kai Sindibad, shin abin da Sarkin
nan ya rubuta kuwa gaskiya ne."
Na amsa masa, "ya shugabana, Wallahi duk
abin da ya rubuta gaskiya ne. Ni na gani da
idona fiye da abubuwan da ya rubuta a cikin
wannan wasika. Duk lokacin da zai yi wa
talakawa jawabi ana daura masa karagarsa bisa
bayan toron giwa, tsayin wannan giwa ya kai
zira'i goma sha daya. Daga gefensa kuma sai
fadawansa su yi sahu biyu, kowane sahu a
gefen hannunsa daya. A gabansa wani sadauki
zai tsaya rike da mashi na zinariya, a bayansa
da wani sadaukin rike da takobi ta zinariya. Idan
kuma zai yi kilisa zai hau doki tare da mahaya
dubu, kowane mahayi cikin sutura ta alfarma
wadda aka yi wa kwalliya da jauhari iri daban-
daban. Idan za a fita kilisar sai wani mai shela
ya rika shela yana cewa, 'wannan shi ne Sarkin
da babu kamarsa a duk cikin Sarkuna.' Haka
mai shelar nan zai ci gaba da yi wa Sarki kirari,
wanda ban rike kirarin ba duka, amma daga
karshe yakan ce, 'wannan shi ne Sarkin da ke da
kambin da duk wani Sarki bai da irin sa.' Idan
wannan mai shelar ya kare, daga can kuma sai
wani ya dauka yana cewa, 'duk da wannan Sarki
zai mutu, babu makawa wata rana zai mutu.' Sai
shi kuma wancan na farko ya ce, 'tsarki ya
tabbata ga Sarkin da bai mutuwa har abada.'
Saboda adalcin wannan Sarki, ya Halifa, ko
alkali babu a birninsa, dukkan mutane suna
tsare dokoki sau-da-kafa, babu mai yin laifi a
cikin su."
Halifa ya yi shiru yana mamaki, daga nan sai ya
ce, "yadda karfinsa yake wasikarsa ta rigaya ta
bayyana mini. Babu makawa shi Sarki ne mai
karfin mulki da karfin arziki."
Daga nan sai na kwashe labarun sauran tafiye-
tafiyen da na yi da hatsarin da na shiga a cikin
kowace tafiya da abubuwan mamakin da na
gano, na fada wa Halifa Haruna Rashid. Yayi
mamaki matukar mamaki, ya sa aka rubuta
wadannan labaru cikin takardu aka adana su a
dakin karatu domin na baya su karanta su karu
da abubuwan da ke cikin su. Halifa ya yi mini
godiya mai yawa, ya kawo kyautar dukiya
wadda har ta fi wadda na fita da ita zuwa
fatauci yawa, ya sallame ni. Na tashi na nufi
gidana cike da farin ciki, na iske gidana lafiya.
'Yan uwa da abokai suka yi ta zuwa suna yi mini
maraba, na rarraba musu kyaututtuka. Na bayar
da sadaka ga mabukata, na ciyar da marayu.
Na ci gaba da rayuwata kamar yadda na saba
cikin dadi da shagali, na manta dukkan
wahalhalun da na sha a baya. Wannan shi ne
labarin tafiyata ta shida a cikin teku, idan Allah
ya kai mu gobe zan gaya muku labarin tafiyata
ta bakwai kuma ta karshe wadda ta fi wannan
ban mamaki.
Da Maigida ya kare wannan labari sai ya sa aka
kawo abinci da abin sha, suka ci tare da dan
dako, da suka gama cin abinci ya kawo dinari
dari ya ba shi, suka yi sallama. Sauran tajirai
suka tafi suna mamakin wannan labari da suka ji.

Sindibad dan dako ya tafi gidansa cike da
mamakin wannan labari. Ya kwanta yana dokin
gari ya waye domin ya ji labarin tafiya ta bakwai
da mai gida ya yi a cikin teku. Gari na wayewa
dan dako ya yi salla, ya kimtsa ya nufi gidan
takwaransa. Bayan duka sauran tajirai sun
hallara sai Maigida ya fara labarin tafiyarsa ta
bakwai kuma ta karshe.

TAFIYAR SINDIBAD TA BAKWAI A CIKIN TEKU.

Sindibad Matafiyi ya ce, "ku sani ya ku abokaina,
lokacin da na dawo daga tafiyata ta shida sai na
ci gaba da harkokina kamar yadda na saba, na
manta kome na daga wahalhalun da na sha a
baya. Ina nan haka sai sha'awar tafiye-tafiye ta
motsa mini a cikin rai, na ji babu abin da nake
so kamar in shiga duniya, in ga mutane da
al'adunsu. Daga nan sai na shiga shiye-shiryen
zuwa fatauci. Na hada haja mai yawa wadda
zan fita da ita, da lokaci ya yi, sai na yi sallama
da 'yan uwana da abokai, na nufi Birnin Basara.
Ina zuwa kuwa na sami wani babban jirgi zai
tashi da fatake masu yawa, na biya kudi na
saka hajata a cikin jirgi.
Na yi abota da fataken nan, da lokacin tafiya ya
yi sai jirginmu ya motsa, muka tsunduma cikin
teku, muka bar birnin Basara cikin aminci. Muka
yi ta tafiya cikin yanayi mai dadi har muka iso
ga wani babban birni mai suna birnin Sindu,
muka yada zango cikin wannan birni muka dan
taba ciniki. Daga nan sai muka ci gaba da tafiya
cikin aminci, muna hira da juna. Muna cikin
wannan hali sai wata iska mai karfi ta fara
kadawa, ba a jima ba sai hadarin ruwa ya hadu
baki kirin. Aka kuwa goce da ruwa kamar da
bakin kwarya, muka lullube hajojinmu da
barguna gudun kada ruwa ya bata mana kaya.
Muka yi ta addu'ar Allah ya fisshe mu cikin wannan hatsari.

Muna cikin wannan hali sai muka ga Madugu ya
tattare rigarsa ya cusa cikin wando, ya haye
saman jirgi yana waige-waige cikin teku. Daga
nan sai muka ga ya cire rawaninsa ya jefar cikin
jirgi, ya rika kuka yana marin fuskarsa kamar
dan yaro, ya tuge gemunsa ya watsar. Da ganin
haka sai hankulanmu suka tashi, muka tambaye
shi, "ya Ra'isu, me yake faruwa ne?"
Sai ya amsa mana da cewa, "ku yi ta kank ya ku
fatake. Ku sani cewa iska ta karkatar da jirginmu
daga tafarki, mun shiga mahaukaciyar teku
daga cikin tekunan duniya masu hadari." Yana
gama fadin haka sai ya sauko da sauri, ya shiga
wani dan sako inda ya ajiye kayansa. Ya dauko
wata 'yar karamar jaka mai launin shudi wadda
aka yi da audugar rimi. Ya debo wani garin
magani kamar toka ya zuba shi bisa wani dan
faifai, karami. Ya cudanya garin maganin da
ruwan teku, ya jira zuwa wani dan lokaci, ya
lakaci garin maganin ya sansana ga hancinsa,
ya kuma lasa ga harshensa. Sa'annan ya bude
sundukinsa ya jawo wani littafi ya bude shi ya
fara karantawa da karfi yadda kowa zai ji a cikin
jirgin, "ku sani ya ku fatake, a cikin wannan littafi
akwai abin al'ajabi, daga ciki shi ne duk
mutumin da ya sami kansa cikin wannan teku,
har abada ba ya tsira daga cikinsa domin ana
kiran wannan teku da suna Mazaunin Sarki. A
cikin wannan teku ne sundukin da aka rufe
shugaba Sulaimanu dan Dawuda. A cikin
wannan teku akwai macizai manya-manya
masu munin siffa tare da wasu irin kifaye
wadanda duk jirgin da ya ratso ta cikin tekun za
su hadiye shi duk da kayan da ke cikin sa."

Yayin da muka ji haka sai tsoro ya kama mu, ba
mu ankara ba sai muka ji an dauke jirginmu cak
daga saman ruwa aka kuma sako shi ya fado
cikin ruwan. Daga nan fa sai muka rude muka
shiga addu'a babu ji, babu gani, muna neman
Allah ya kubutar da mu daga wannan hali da
muke ciki. Can sai muka ji wata irin kara mai
kama da aradu, muka firgita, don tsoro nan take
wasu daga cikinmu suka some, masu karfin hali
su ne wadanda suka saki fitsari cikin wando.

kuna tare ne da Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ19 HIKAYAR SINDABAD MAI TEKU DA SINDABAD DAN DAKO

Can sai muka ji wata irin kara mai
kama da aradu, muka firgita, don tsoro nan take
wasu daga cikinmu suka some, masu karfin hali
su ne wadanda suka saki fitsari cikin wando.
Kwaram sai ga wani katon kifi ya bayyana a
gaban jirginmu, girman wannan kifi kamar tsauni
yake. Sai kuma muka ga wani kifin ya bayyana
wanda ya fi na farkon girma. Kafin ayi haka sai
kifi na uku ya taso saman teku, wannan kifi duk
ya fi sauran biyun girma da muni. Ba zai yiwu in
bayyana muku irin halin da muka shiga na tsoro
ba. Kifayen nan uku suka rika zagaya jirginmu,
kamar kudan zuma na zagaya hure kafin ya
sauka kansa ya tsotsi zaki. Daga nan sai
babban ya bude bakinsa zai hadiye jirginmu,
girman bakin nan nasa tamkar kofar gari.

Please Login or Register in order to submit comment