Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai da na ji na kai masabar gatari.
Na yi hamdala ga Ubangiji da ya kubutar da ni
daga kabilar zindirawa.
Bayan mutanen nan sun cika kwandunansu da
goran yaji, sai suka sanya ni a cikin jirginsu suka
tafi da ni zuwa ga nasu tsibiri. Muna zuwa sai
suka kai ni ga sarkinsu. Sarkin nan kuwa
mutumin kirki ne, ya karbe ni da hannu biyu-biyu
cikin fara'a. Bayan mun gaisa sai ya tambayi
labarina. Na duka na kwance masa bakin jaka.
Sarki da fadawansa suka yi mamaki mai yawa da
jin wannan labari nawa, ya umurce ni da ina
zauna kusa gare shi. Ya sa aka kawo abinci da
nama, muka ci tare da shi. Bayan mun gama
muka wanke hannuwanmu da ruwan wardi muka
goge da adikon da aka yayyafa wa miski. Na yi
godiya ga Allah Madaukakin Sarki. Na kuma gode
wa wannan Sarki kwarai da gaske bisa ga
wannan irin karimci nasa.
Bayan an watse daga fada sai na shiga cikin gari
ina zagayawa domin ganin yanayin garin da
al'ummarsa. Garin cike yake da jama'a, kowa
yana harakar gabansa, babu ruwan wani da wani.
An bubbude rumfuna ana ta ciniki, kowace rumfa
cike da kayan masarufi. Na lura da cewa
mutanen garin mutane ne masu hannu da shuni,
kuma 'yan kasuwa ne sosai. Hankalina ya kwanta
da mutanen wannan gari. Kwanci tashi har na yi
abota da 'yan kasuwa masu yawa. Na kasance
abin girmamawa a cikin wannan gari kamar
wanda ya yi shekara da shekaru. Wani abu da ya
ba ni mamaki da mutanen wannan gari shi ne,
ban taba ganin sun hau doki da sirdi ba. Kome
tsadar doki haka za a hau shi babu sirdi babu
wata kwalliya. Hatta Sarki da fadawansa duk
haka suke hawan nasu dawakin.

daga Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ12. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO

Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Sabuwar Fassarar:

Ibrahim Malumfashi,
Danladi Z. Haruna,
Bukar Mada.
Sindibad mai teku ya ci gaba da labari ya ce,
bayan an watse daga fada sai na shiga cikin gari
ina zagayawa domin ganin yanayin garin da
al'ummarsa. Garin cike yake da jama'a, kowa
yana harakar gabansa, babu ruwan wani da wani.
An bubbude rumfuna ana ta ciniki, kowace rumfa
cike da kayan masarufi. Na lura da cewa
mutanen garin mutane ne masu hannu da shuni,
kuma 'yan kasuwa ne sosai. Hankalina ya kwanta
da mutanen wannan gari. Kwanci tashi har na yi
abota da 'yan kasuwa masu yawa. Na kasance
abin girmamawa a cikin wannan gari kamar
wanda ya yi shekara da shekaru. Wani abu da ya
ba ni mamaki da mutanen wannan gari shi ne,
ban taba ganin sun hau doki da sirdi ba. Kome
tsadar doki haka za a hau shi babu sirdi babu
wata kwalliya. Hatta Sarki da fadawansa duk
haka suke hawan nasu dawakin.
Ran nan dai sai na kasa hakuri, da aka tashi
daga fadanci sai na tambayi Sarki, "Allah ya ba
ka nasara, me ya sa ba ku hawan doki da sirdi?
Na ga cewa sirdi yana sa mahayi ya ji dadin
zama bisa doki, kuma yakan kara wa doki karfi
da kuzari."
Sarki ya dube ni cike da mamaki, "Menene kuma
sirdi? Ban taba jin wannan abu ba tun da nake."
"Allah ya ba ka nasara, idan ka yarda zan yi wa
dokinka sirdi, ka hau shi ka ji yadda ake ji."
Cikin doki, Sarki ya ce ya amince. Na ce a
sassako mini itace. Nan take Sarki ya sa aka
sassako mini itace irin wanda nake so. Na nemo
wani kwararren masassaki, na kwatanta masa
yadda zai sassaka sirdi da wannan itace. Na
sami tawada na zana masa, a kan itacen, siffar
yadda nake so sirdin ya kasance. Masassakin
nan gwani ne, nan da nan ya yi kamar yadda
nake so. Na samo fata na lullbe sirdin da ita na
dinke. Na sami wani masaki ya saka mini rigar
sirdin da gashi mai taushi da laushi, kamar yadda
na kwatanta masa, na shimfida rigar gashin bisa
ga sirdi na dinke ta tare da fatar.
Bayan sirdi ya hadu yadda nake sonsa, sai na je
ga wani makeri na kwatanta masa yadda zai kera
mini likkafu da ragama. Ya aikata yadda na
umurce shi. Ya goge su suka yi fari tas, ya shafa
musu bulari, suka yi ta daukar ido kamar azurfa.
Na sami wani mai tufkar igiya ya tufka mini
linzami na alharini. Na hada kayan nan wuri
guda. Na tafi bargar Sarki na zabo wani ingarma
cikin wadanda Sarki ke hawa. Na daura masa
sirdi da likkafu da ragama, na jawo linzami na
aza bisa ga sirdi, na ja ragamar doki na nufi
wurin Sarki da shi.
Sarki ya dubi doki ya cika da mamaki, ko ba
kome dokin ya kara kyau. Na nuna masa yadda
zai taka likkafa ya hau. Ya taka ya haye bisa
doki, na mika masa linzami na fada masa
amfaninsa. Ya yi tafiya da doki kamar taki
hamsin, ya juyo ya dawo. Nan fa ya shiga gode
mini kamar ya dauke ni ya goya. Ya kawo dukiya
mai tarin yawa ya ba ni ladar wannan aiki da na
yi. Yayin da Wazirin Sarki ya ga sirdi ga dokin
Sarki sai ya ce lalle in yi masa irinsa. Nan da
nan na hado masa nasa sirdin, shi ma ya yi mini
kyautar dukiya mai yawa.
Daga nan fa sai fadawa da attajiran gari kowa ya
taso yana so a yi masa sirdi. Na hada abokan
aikina muka yi ta sassaka siradda muna sayarwa,
kasuwa ta bude gare mu. Muka sami dukiya mai
yawa wadda ba ta kidayuwa. Na zama
hamshakin attajiri cikin kankanen lokaci. Sai ya
kasance har daga makwabtan wannan birni ana
zuwa sayen sirdin doki gare ni. Na kara samun
daukaka ga Sarki, ya rike ni tamkar dansa, barci
kadai ke raba ni da shi.
Ina nan cikin wannan birni cikin kwanciyar
hankali da jin dadi, ran nan ina tare da Sarki
muna hirar duniya sai ya takale ni da wata
magana, ya ce, "Ka sani ya kai Sindibad, yanzu
ka zama daya daga cikinmu, kuma na dauke ka a
matsayin dana, har ba na so in rabu da kai. Ina
so ka bi umurnina a cikin wannan magana da zan
gaya maka yanzu?"
Na dukar da kaina kasa cikin ladabi na ce, "Allah
ya ba ka nasara, ai yadda ka dauke ni a matsayin
danka haka na dauke ka a matsayin ubana. Babu
wani abu da za ka umurce ni da shi, face na
aikata shi. Menene wannan abu da kake so ka
umurce ni da shi?"

"Ina so in aura maka kyakkyawar budurwa daga
cikin 'ya'yan manyan mutane, mai ladabi da ilmi
da biyayya. Ka sani mutum duka bai cika mutum
sai fa in yana da mata. Ina so ka yi mini biyayya
a kan wannan bukata tawa."
Na sunkuyar da kaina kasa cikin tsananin jin
kunya, na yi shiru ban ce kome ba.
"Ya na ji ka yi shiru ba ka amsa mini ba?" Sarki
ya tambaya.
Na amsa masa, "Allah ya ba ka nasara, ai don
wannan ba sai ka tambaye ni ba. Na amince ka
aura mini duk wadda ka ga dama."
Sarki ya ce, "To, madalla." Ya sa aka tara alkalai
da malamai da shaidu. Aka daura mini aure da
wata kyakkyawar budurwa 'yar manyan mutane,
wadda mahaifinta ya mutu ya bar mata dukiya
mai yawa ta kudi da dabbobi da gidaje da gonaki.
Bayan ubanta ya mutu sai Sarki ya dauki nauyin
kula da ita. Yarinya ce kyakkyawa tamkar wata
dan daren goma sha hudu.
Sarki ya aurar da ni ga wata budurwa kykkyawa
wacce ta gaji dukiya mai yawa daga mahaifinta.
Sarki kuma ya ba ni kerarren gida, na-gani-na-
fada, kusa da fadarsa, na tare da amaryata a
ciki. Ban da wannan gida kuma Sarki ya ba ni
bayi da kuyangi farare da bakake, ya kuma nada
ni daya daga cikin waziransa, ya yanka mini
albashi da ake biyana kullum. Na zauna cikin
dadin rai, na manta da duk wata wahala da na
sha tun daga kifewar jirginmu a cikin teku da
kuma wahalar da na sha a cikin tsibirin
zindirawa. Na zauna tare da matata wadda nake
matukar kauna, ita ma tana matukar sona kamar
ta hadiye ni. Har na rika cewa a cikin raina,
"Babu makawa idan zan koma gida Bagadaza in
tafi tare da ita." Sai dai kamar yadda masu iya
magana ne ke cewa, kana taka Allah na tasa.
Bari ku ji abin mamakin da zai faru.
Ina nan zaune da matata cikin tsananin soyayya,
sai ran nan matar makwabcina ta mutu. Na
zagaya domin in yi masa ta'aziyya sai na same
shi cikin tashin hankali da tsananin tsoro. Na yi
masa gaisuwar rashin matarsa ina rarrashinsa,
"Ka yi hakuri haka Allah ya kaddara. Allan da ya
dauke matarka shi za ya kara ba ka wata wadda
ta fi ta, ku ci gaba da rayuwarku cikin dankon
soyayya."
Yayin da makwabcina ya ji zancena sai na ga ya
kara fashewa da kuka, ya ce, "Ya kai abokina, ta
yaya zan sake auren wata mace bayan saura
kwana daya ya rage mini a cikin duniya."
Na dafa kafadarsa na ce, "Subhanalillahi! Don me
kake yi wa kanka fatar mutuwa ga ka da
lafiyarka?"
Ya ce mini, "Ai iyakacinka da ni yau, gobe war
haka ni ma na kwana kiyama."
"Saboda me?" Na tambaye shi cikin mamaki.
Ya gaya mini cewa, al'adar wannan birni ce idan
daya daga cikin ma'aurata ya mutu, mata ko miji,
tare za a rufe su duka biyun da mataccen da mai
rai a kabari daya. Wai don kada daya ya ci gaba
da rayuwa ba tare da dan uwansa ba, wai
soyayyar da aka yi a nan duniya ta dore har can.
Ko ya gaya musu ana soyayya a barzahu.
Wannan kuwa ko Sarki ne haka za a yi masa. Da
na ji haka sai na yi sallallami na ce, "Wannan abu
ai bai dace ba, don me za a rufe mutum da ransa
tare da gawa? Ya kamata a watsar da wannan
mummunar al'ada."

Ina nan zaune gidan wannan makwabci nawa ina
taya shi jaje, sai mutanen gari ke zuwa kungiya-
kungiya suna yi masa ta'aziyyar rasuwar matarsa
suna kuma yi masa ban kwana. Daga nan sai ga
masu binne gawa sun shigo da sunduki. Suka
saka gawar matar a cikin sunduki suka tafi da ita
tare da mijinta zuwa bayan gari. Suka isa ga
wani tsauni kusa ga gabar teku. Suka share
kasar wurin sai ga wani katon dutse mai fadi
kamar marufi ya bayyana, suka ciccibi dutsen
nan suka dauke shi da kyar suka ajiye gefe daya,
ashe rijiya ce aka rufe da dutsen. Da na leka
rijiyar nan ban ga iyakar zurfinta ba. Suka dauki
sundukin nan wanda gawar matar take ciki suka
ingiza cikin wannan rijiya. Daga nan sai suka
kama mijin suka daura masa doguwar igiyar kaba
mai kwari ga hakarkari. Suka rataya masa gora
cike da ruwa, da gurasa kwara bakwai a cikin
jaka. Suka rika zura shi cikin rijiyar nan a hankali
har ya kai kasan rijiyar, ya kwance igiya daga
jikinsa. Mutanen nan suka fitar da igiyar, suka
mayar da katon dutsen nan suka toshe bakin
rijiyar kamar yadda muka same ta da farko, suka
mayar da kasa saman dutsen. Muka tafi muka
bar abokina da gawar matarsa a cikin rijiyar.
Yayin da na ga abin da ya faru ga makwabcina
sai na ce a cikin raina, "Wallahi wannan mutuwa
har ta fi ta farko zafi. Gwamma mutum ya mutu
bisa gadonsa da a kashe shi da yunwa da
kishirwa." Na nufi wurin Sarki na ce masa, "Allah
ya ba ka nasara, me ya sa ake rufe mai rai tare
da matacce a cikin rami guda?"

Sarki ya ce mini ai al'adarsu ke nan kaka da
kakanni. Muddin miji ya mutu to za a rufe shi
tare da matarsa, haka kuma idan matar ce ta
mutu za a rufe ta tare da mijinta. Na tambaye
shi, to na ji ku al'adarku ce. Idan irina wanda
yake bako matarsa ta mutu, ko ni na mutu fa?
Sarki ya ce ai babu banbanci ga kowa. Da na ji
haka sai na ji hantata ta dauki rawa, tsoro ya
kama ni. Na ji kamar an sanya ni cikin wani irin
kurkuku mai kunci, nan take duk sai na tsani
wannan birni da al'ummarsa. Na ce a cikin raina,
yanzu idan matata ta riga ni mutuwa shi ke nan
ni ma na mutu, lalle da sake wai an ba mai kaza
kai.

Daga nan sai na fara shawarar in rabu da matata
ko kuma in tsere daga wannan birni, duk da dai
Allah kadai ya san gawar fari tsakanin ni da ita.
Na yi iyakar kokarina in kawar da wannan tunani
a cikin raina amma na kasa. Inan nan zaune da
matata lafiya, sai ran nan ta ce mini kanta na
ciwo. Wasa-wasa dai har rashin lafiya ya kai ta
kwance. Bayan 'yan kwanaki kadan sai ta ce ga
garinku nan. Mutane suka yi ta zuwa suna yi
mini ta'aziyya, suna kuma yi mini ban kwana,
kamar dai yadda suka yi wa makwabcina.
Aka yi wa matata sutura, aka sanya mata tufafi
masu tsadar gaske. Aka sanya mata sarka da
awarwaro na zinariya. Sai ka rantse da Allah idan
ka ce mata sannu za ta ce maka, "mhm!" Aka
dauke ta tare da ni aka nufi bayan gari wurin
rijiyar nan da aka rufe makwabcina tare da
matarsa. Da zuwa sai aka bude bakin rijiyar nan
aka jefa matata a ciki. Abokaina kuma suka
zagaye ni suna yi mini ban kwana, wasu daga
cikinsu har suna zubar da hawaye. Ni kuwa sai
na rika kururuwa ina cewa, "Wallahi Allah ya
haramta wannan danyen aiki da kuke shirin
aikatawa. Ba ku ganin ni bako ne, ba al'adarmu
daya da ku ba. Don me za ku rufe ni da raina?
Wallahi da na san haka al'adarku take da ban
yarda na yi aure ba."
Af, babu wanda ya kula da hargowata, suka
kama ni da karfi suka daure da igiya, suka zuba
mini ruwa a cikin gora da 'yar gurasa guda
bakwai, suka zura ni cikin rami kamar dai yadda
al'adarsu ta tanada. Da suka ji na sauka kasan
ramin sai suka yi mini magana da karfi, wai in
kwance igiyar da aka zuro ni da ita cikin ramin
daga jikina, ni kuwa sai na ki. Da suka ga ba ni
da niyyar kwance igiyar sai suka jeho mini ita
cikin ramin suna cewa, tafi da ita idan igiya na
amfani a lahira. Suka ja dutse suka rufe bakin
rami gam, suka tafi abinsu.

Na sami kaina a cikin wani irin rami mai duhu,
sai kasusuwan mutane ko'ina bargaja kamar an
watse kara. Ga wani irin doyi da hamami na
tashi, cikin dan kankanin lokaci sai na ji iska na
gagara ta shaka. Na zargi kaina da kaina, na ce a
cikin raina, "Wace wauta ta sa na yi aure a cikin
wannan birni? Babu shakka duk abin da ya same
ni ba ni da kaico."
Na ci gaba da cewa, babu tsimi babu dabara face
daga Allah Madaukakin Sarki. Duk lokacin da na
kubuta daga halaka sai in kara fadawa cikin
wadda ta fi ta. Wallahi mutuwa a cikin ruwa ta fi
wannan mummunar mutuwa da zan yi. Ina ma a
ce na mutu a cikin teku lokacin da jirginmu ya
kife, ko kuma yunwa ta kashe ni a cikin tsibirin
zindirawa.

Na ci gaba da zama cikin wannan rami, ba na iya
banbance dare balle rana, bakina kuwa ba ya
rufuwa, kodayaushe ina karanta duk addu'ar da
ta fado mini cikin rai.
Na jefa kaina bisa kasusuwan matattu na yi
kwance, hawaye na zuba daga idanuna. Na ci
gaba da rokon Allah ya kubutar da ni daga
wannan hali da nake ciki. Na yi ta jiran mutuwa
ta zo ta dauke ni, amma ba ta zo ba...

Whatsapp only pls
08032767547

kuna tare neda Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ13 HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO

Na jefa kaina bisa kasusuwan matattu na yi
kwance, hawaye na zuba daga idanuna. Na ci
gaba da rokon Allah ya kubutar da ni daga
wannan hali da nake ciki. Na yi ta jiran mutuwa
ta zo ta dauke ni, amma ba ta zo ba. Bayan
wani lokaci sai yunwa ta fara dafa ni, makoshina
kuma ya bushe don kishirwa. Sai na jawo 'yar
gurasar nan da aka turo da ita na ci daya, na
sha makwalwa guda ta ruwa. Daga nan sai na
tashi na fara dube-dube cikin ramin ina
nazarinsa, da yake yanzu idona ya saba da
duhun ramin. Na ga cewa rami ne mai fadin
gaske, daga kowane bangare na bangayen
ramin akwai hanyoyi da suka huda bangayen
suka yi rariya. A barbaje ko'ina a cikin ramin
kasusuwan mutane ne wasu har sun yi fari
saboda dadewa. Na matsa nesa daga tsakiyar
ramin na sami wata rariya wadda babu
kasusuwan mutane a wurin na zauna.
Na kasance cikin wannan rami har 'yar gurasa
da ruwana suka kusa karewa. Da ma kuwa
kullum sau daya nake ci na sha makwalwar
ruwa guda. Tuni wata zuciya ta ce mini, "ka ci
kadan daga gurasar, ka sha ruwa kadan, wa ya
sani ko kafin ka cinye ta Allah ya koro maka da
wani taimako." Rannan dai na kusa cinye 'yar
gurasata, ina zaune ina tunanin abin da zan yi
idan gurasar nan ta kare, sai na ji an bude bakin
ramin nan, wani irin haske mai karfi ya kwararo
cikin ramin. Watakila wani ne za a jeho cikin
ramin, na ce a cikin raina. Na hangi kawunan
mutane suna lekowa cikin ramin, daga nan sai
aka jeho sunduki cikin ramin ya fado tim. Sai
kuma na ga an zuro wata mace da igiya, tana ta
sheka kuka, an ratayo mata goran ruwa da jakar
gurasa kamar yadda sukan yi bisa al'ada.
Bayan ta sauko kasan ramin nan sai na kura
mata ido daga inda nake make, na gan ta
kyakkyawar mace ce, amma ita ba ta gan ni ba
saboda idonta bai saba da duhun ramin ba. Da
suka zuro ta sai suka janye igiyar suka mayar
da dutse suka toshe bakin ramin. Na dauki
kashin kwaurin wata gawa, na lallaba ta bayan
matar nan, na yi mata kum daya bisa madigar
kai, ta kwallara ihu ta fadi kasa sumammiya. Na
kara kwantara mata kashin nan bisa kai karo na
biyu da na uku har sai da na tabbatar da ta
mutu. Na lalube gurasa da ruwan da aka zuro ta
da su, na kuma ciccire kayan zinariyar da aka yi
mata kwalliya da su, da ma ga al'adarsu duk
mata da kayan kwalliya masu tsada ake zuro
su. Da na cire dukan kayan zinariyar da ke jikin
wannan mace sai na koma lungun da nake na
make.
Na rika cin gurasar nan kadan-kadan ina shan
ruwa kadan. Haka na kasance cikin wannan hali
tsawon lokaci, duk lokacin da aka turo wasu sai
in kashe mai ran in dauke gurasarsa da ruwa, in
cire zinariyar matar, da haka na tara zinariya
mai yawan gaske. Ni kuwa idan aka gan ni babu
abin da zai raba ni da gawa, ga shi dai na rame
na bushe kamar kwarangwal, 'yar gurasa da
ruwan da nake sha don dai na rayu ne ba wai
don ina koshi ba.
Rannan ina kwance cikin ramin nan ina tunani,
sai na ji wani abu yana motsi cikin ramin nan
kamar ana jujjuya gawarwakin. Na ce a cikin
raina, "mene ne wannan? Kar dai a ce kura ce ta
shigo cin gawarwakin mutane. Wannan dabba
akwai shegen kwadayi." Na yi zumbur na mike
tsaye, na lalubo katon kashin nan da nake
kashe mutane da shi na rike shi gam, na lallaba
na nufi inda motsin ke fitowa. Ko da dabbar nan
mai tonon gawarwaki ta gan ni sai ta ruga a
guje ta bi ta wata rariya da ke jikin bangon ramin
ta bace. Na bi cikin wannan rariya da rarrafe,
bayan na yi nisa sai na fara hango wani haske
daga can nesa, sai ya fito sai ya bace, kamar
hasken tauraruwa idan tana nisawa. Na nufi
wannan haske da sauri, ina matsawa kusa
hasken na kara karfi, daga nan sai na tabbatar
da cewa kofa ce mai fita waje zuwa ga bayan
kasa. Na ce a cikin raina, "lalle ruwa ba ya tsami
banza! Ko dai wannan kofa an yi ta ne domin
wani dalili na daban ko kuwa haka ta tsiru bisa
kudirar Ubangiji. Na tsaya ina tunani shin in ci
gaba da tafiya ne ko in koma da baya, domin ina
jin tsoron in kara fadawa cikin wani hatsarin
wanda ya fi na baya. Wata zuciyar ta ce in ci
gaba da tafiya, kome ta fanjama, fanjam.
Na tafi har na iso ga kofar nan, sai na ga ashe
dai kofa ce mai fita waje daga bayan tsaunin
nan wanda kusa gare shi ne aka gina rijiyar da
ake jefe mutane. Sai dai ga alamu, da, kofar
karama ce, dabbobi ne suka kara mata girma
domin shiga cikin rijiyar wajen cin gawarwakin
mutane. Yayin da na ga haka sai zuciyata ta yi
fari, hanyar tsira ta samu bayan da har na debe
tsammani daga kubuta. Na bi ta kofar na fita sai
na gan ni a bayan dogon tsauni wanda daga
bayansa birnin da na baro ne, a gabana kuwa
ruwan teku ne. Saboda tsawon wannan tsauni
ba zai yiwu mutum ya hau shi ya gangara
bayansa ba, don haka sai ya zama tamkar
ganuwa tsakanina da birnin nan. Na gode wa
Allah da ya tsirar da ni daga halaka.
Bayan na gama nazarin sabon wurin da na tsinci
kaina, sai na bi ta cikin rariyar nan na koma cikin
rijiya, na tattaro duka kayan zinariya da tufafin
mata masu tsada na fito da su gefen tsaunin
nan. Na sami wuri na kafa 'yar bukka, ina jiran
taimakon da Allah zai turo mini wanda zai yi
sanadin fitata daga wannan tsibiri. Na rika
komawa cikin rijiyar kullum idan an jeho mutane
sai in kashe mai ran, in dauke abincinsa da
dukiyar da aka turo, hatta tufafinsu ba na bari.
Na dawwama bisa ga wannan hali, ta haka na
jibge dukiya mai tarin yawa a cikin wannan
bukka tawa.

cikin tsibiri bayan tsauni, na rika
komawa cikin rijiyar nan ina kashe duk wanda
aka turo ina dauke abincinsa da ruwa. Na debe
tarin dukiyar da ake turo gawarwakin nan da su
na dangin zinariya da azurfa da tagulla da
lu'ulu'u da sauran duwatsu masu daraja, hatta
tufafin mamatan ban bari ba. Na jibge dukiya
mai yawa a cikin bukkata, na zauna zaman jiran
tsammanin warabbuka, wai malam ya ki noma
don zakka.
Wata rana ina zaune bakin bukkata sai na hangi
wani babban jirgi a tsakiyar teku zai wuce,
tozayen ruwa na yin sama da kasa da shi. Nan
da nan sai na dauki yankin adiko na daura shi
ga wata doguwar sanda, na nufi bakin gabar
teku ina daga wannan sanda sama ina karkada
adikon nan cikin iska. Allah kuwa ya nufi masu
jirgi suka hango ni, suka karkato da jirginsu
zuwa gare ni. Da suka iso kusa gare ni sai
Madugunsu ya ce, "kai, mutum ko aljani? Me
kake yi cikin wannan tsibiri kai kadai kusa ga
wannan tsauni da ba mu taba ganin wani
mutum ba?"

Wallahi ni mutum ne dan uwanku," na amsa
musu. Na ci gaba da cewa, "ni falke ne jirgi ya yi
hatsari da mu, duka 'yan uwana suka halaka, ni
kuwa Allah ya kubutar da ni da dukiyata zuwa
ga wannan wuri bayan na kama wani allon jirgin
na hawo, iska ta turo ni nan. Na yi bukka na
ajiye kayana ina jiran Allah ya koro mini da wani
jirgi da zai wuce ta nan."
Da fatake suka ji labarina sai suka tausaya mini,
suka dauke ni cikin jirginsu duk da dukiyata,
bayan na daure ta wuri guda cikin zannuwa. Na
kawo lu'ulu'u mai yawa na ba Madugun jirgi na
ce masa, karbi wannan ladar kubutar da ni da
kuka yi daga cikin wannan tsibiri. Amma sai
Madugu ya ki karbar dukiyar da na ba shi, ya ce,
"ai mu ne ya kamata mu taimake ka, domin ka fi
kowa bukatar taimako a halin yanzu. Idan muka
tsinci falken da jirgi ya yi hatsari da shi, mukan
taimaka masa, mu tarairaye shi, mu kawo masa
abinci da nama. Idan muka same shi tsirara, mu
ba shi tufafi ya sanya. Haka za mu yi ta kulawa
da shi har mu iso wani birni inda za mu hada shi
da mutanen kasarsa, daga nan kuma mu ba shi
guzuri daga cikin dukiyarmu. Hala ba ka ji masu
iya magana na cewa, Allah na taimakon wanda
ya taimaki dan uwansa ba."
Na duka na yi ta gode musu. Na gode wa Allah
Ubangijin talikai da ya kubutar da ni daga
halaka, na manta dukkan wahalar da na sha.

Abu daya ne ba zan manta da shi ba har in
koma ga Allah. Duk lokacin da na tuna lokacin
da aka rufe ni cikin rami da gawar matata sai
hantata ta motsa don tsoro. Muka ci gaba da
tafiya cikin jirgi a yanayin teku mai dadi, daga
wannan tsibiri zuwa wancan har muka iso ga
wani babban tsibiri wai shi Tsibirin Beli. A cikin
wannan tsibiri akwai wani babban birni wanda
tsayinsa da fadinsa tafiyar kwana biyu ne.
Bayan mun bar wannan tsibiri da kwana shida
sai muka isa wani tsibirin mai suna Tsibirin Kala,
shi kuwa tsibiri ne daga cikin kasashen Hindu.
Wannan tsibiri na karkashin mulkin wani babban
Sarki ne mai girman runduna. Mutanen tsibirin
gwanaye ne wajen samar da kafur da rama.
Kwanci tashi muka ci gaba da tafiya har Allah
mai girma da daukaka ya nufe mu da isowa
birnin Basara cikin kwanciyar hankali da dadin
rai. Na kwana biyu a Basara, daga nan na nufi
gidana a Bagadaza, Gidan Aminci. Na sami
gidana lafiya, babu abin da ya canza a cikinsa.
'Yan uwa da abokan arziki suka rika zuwa suna
yi mini barka da dawowa. Na yi ta rarraba musu
dukiya. Na kwashi tarin dukiyar da na dawo da
ita na jibge a cikin taska. Na ciyar da marayu da
miskinai da zawarawa. Na koma ga tsohon
halina na bushasha, na shiga cikin dukiya ina
bundum-bundum. Wannan shi ne labarin
tafiyata ta hudu a cikin teku. Idan Allah ya kai
mu gobe zan gaya muku labarin tafiyata ta biyar
wadda ta fi wannan ban mamaki.

DAGA Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ14 HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD DAN DAKO

Wannan shi ne labarin
tafiyata ta hudu a cikin teku. Idan Allah ya kai
mu gobe zan gaya muku labarin tafiyata ta biyar
wadda ta fi wannan ban mamaki.

Da Sindibad Matafiyi ya gama bayar da wannan
labari sai Sindibad dan dako ya rike baki cike da
mamakin wannan labari da ya ji. Aka hallaro
musu da abinci da abin sha. Sindibad dan dako
da Sindibad Matafiyi suka ci tare a cikin akushi
daya. Sauran tajirai kuma suka ci daga nasu
akussan. Bayan sun gama cin abinci

Please Login or Register in order to submit comment