Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai
Sindibad Matafiyi ya kirgo dinari dari ya ba dan
dako, suka yi ban kwana ya tafi. Sauran tajirai
ma suka fita suna mamkin wadannan labaru da
Sindibad mai teku ke bayarwa, domin kullum
suka zo sai su ji labarin yau ya fi na jiya dadi da
ban mamaki. Suka yi ta alla-alla gobe ta yi
domin su ji labarin tafiyarsa ta biyar wadda ya
ce
ta fi sauran da ya yi a baya ban mamaki.
Haka Sindibad dan dako ya koma gida yana
mamaki, bayan ya yi salla sai ya kwanta barci
zuciyarsa cike da tunanin labarin da ya ji. Da
gari ya waye ya tashi ya yi salla ya yi wuridi, sai
ya kimtsa ya nufi gidan Sindibad Matafiyi. Yayin
da sauran tajirai suka hallara sai mai gida ya fito
ya harde bisa abin zamansa. Aka gaggaisa da
juna, aka kawo musu abinci suka cika tumbinsu,
suka dauraye makogwaronsu da abin sha mai
sanyi. Daga nan sai mai gida ya fara bayar da
labarin tafiyarsa ta biyar a cikin teku.

TAFIYAR SINDIBAD TA BIYAR A CIKIN TEKU
Kuna ji abokaina, bayan na dawo daga tafiyata
ta hudu na ci gaba da sha'anina kamar yadda
na saba, na manta da duk wasu wahalhalu da
na sha a baya. Bayan wani lokaci mai tsawo,
rannan ina zaune gaban gidana ina shan iska,
ina tunanin duniya, sai bakin halin nan nawa na
son tafiye-tafiye ya motsa. Na ji babu abin da
nake so kamar in sake shiga cikin duniya, in ga
duniya, duniya ma ta gan ni, don an ce na zaune
bai ga gari ba.
Nan take sai na shirya kayan haja masu yawa
na yi niyyar fita zuwa fatauci. Na yi ban kwana
da abokaina da 'yan uwa, na nufi birnin Basara.
Da zuwana sai na nufin bakin teku inda jiragen
ruwa ke tashi zuwa sauran sassa na duniya. Na
tarar da wani jirgi sabo fil a bakin teku. Jirgin ya
ba ni sha'awa, na yi cinikinsa gaba daya aka
sallama mini. Na sa kayana a ciki, na dauko
hayar matuka, na sayi bayi wadanda za su rika
yi mini hidima. Wasu daga cikin fatake suka biya
ni kudi suka saka kayansu a cikin jirgin. Kafin
mu fara tafiya sai da aka yi addu'a aka shafa
Fatiha don neman tsari daga hatsarin teku da
kuma neman sa'a bisa ga fataucin da za mu
tafi.
Yayin nan jirgi ya motsa, ya nausa da mu cikin
teku. Muka yi ta tafiya daga wannan birni zuwa
wancan, daga wannan tsibiri zuwa wancan,
daga wannan teku zuwa waccan, muna saye
muna sayarwa, muna kuma kashe kwarkwatar
idonmu a duk birni ko tsibirin da muka yada
zango. Har wata rana muka iso ga wani babban
tsibiri wanda babu kome a cikinsa sai rairayin
hamada. A cikin tsibirin muka hangi wani farin
abu kamar dutse mulmulalle mai siffar kubba,
rabinsa a kafe cikin yashi, girman wannan dutse
kamar rumbun ajiye hatsi. Sauran fatake suka
nufi wurin farin dutsen nan, ni kuwa na yi zaune
cikin jirgi ina kallon su.
Ashe abin nan da suka gani ba dutse ba ne face
kwan tsuntsuwar nan da na taba ba ku labari
mai suna Rukki. Fatake suka sami duwatsu
suka fara bugun kwan nan. Wani daga cikinsu
ya rugo wurina ya ce mini, "fito ka ga wani irin
daki na farin dutse mai ban mamaki da muka
gani a cikin wannan tsibiri." Ko da na je kusa da
dutsen nan sai na gane ko menene. Na yi musu
tsawa ina cewa, "kar ku fasa wannan dutse, ba
dutse ba ne face kwan wata tsuntsuwa mai suna
Rukki. Idan kuka fasa shi tsuntsuwar nan za ta
zo ta kakkarya jirginmu ta halaka mu gaba
daya." Af, kafin in rufe bakina har sun fashe
wannan kwai, wani irin ruwa mai yawa mai yauki
ya fito daga cikin kwan, daga nan sai dan
tsuntsun ya biyo wannan ruwa ya fito.
Kafin mu san abin da ake ciki sai muka ga wuri
ya yi duhu, hasken rana ya bace. Wata iska mai
karfin gaske ta taso har muna faduwa kasa.
Muka daga kawunanmu sama mu ga ko hadari
ne ke tasowa, sai muka ga ashe tsuntsun nan
ne Rukki da muka fasa wa kwai ya taso. Da ya
ga mun fasa masa kwai sai ya rika yin wani irin
kuka mai karfi kamar aradu, nan take sai ga
wasu tsuntsayen biyu irin sa suna shawagi bisa
ga kawunanmu. Da na ga haka sai na kira
matukan jirgi da sauran fatake na ce musu, mu
yi gaggawar komawa cikin jirgi mu bar wannan
tsibiri kafin tsuntsayen nan su halaka mu. Muka
fada cikin jirgi da gudu, matuka suka tuka da
sauri muka juya wa tsibirin nan baya.
Da tsuntsayen nan suka ga haka sai suka
dauko duwatsu manya-manya da kafafunsu,
girman kowane dutse kamar daki, suka biyo mu.
Tsuntsu na farko ya sako dutsensa daidai kan
jirginmu, cikin zafin nama matukan jirgi suka
kauce wa wannan dutse, ya fado dab da
jirginmu. Karfin fadowar dutsen ya sa jirginmu ya
tangada kamar zai kife, Allah ya kiyaye dai bai
kife ba. Matukan jirgi na kokarin shawo kan jirgi
sai tsuntsu na biyu ya sako nasa dutse, wannan
karon sai dutse ya sauka a tsakiyar jirginmu,
nan take jirgi ya tarwatse, ya yi dai-dai. Dukkan
fatake da hajarmu suka nutse cikin ruwa, ni
kuwa Allah ya taimake ni na kama wani allon
jirgi na hau, na yi ta iyo da kafafuna iska na tura
ni har na isa bakin wani tsibiri. Na isa shajaran
majaran, na gaji likis ga kuma yunwa da
kishirwa na koda ni. Na ja jiki na shiga cikin
tsibiri, na yi kwance kamar matacce saboda
gajiya da yunwa. Bayan na huta, sai na tashi na
fara tafiya cikin wannan tsibiri.

Tsibiri ne mai yalwar itatuwa da furanni, da
koramu suna gudana. Ga 'ya'yan itatuwa
nunannu, da tsuntsaye masu launi daban-
daban suna shawagi tare da rera wakoki masu
kwantar da hankali. Kasan tsibirin kuma ciyawa
ce ta fito kore shar ta lullube wurin lif kamar an
shimfida darduma. Wannan tsibiri da kyawo
yake kamar wani yanki ne na aljanna. Na tsinki
'ya'yan itace na ci na koshi, na sha ruwan
korama na kore kishirwa. Hankalina ya dawo, na
yi godiya ga Allah Madaukakin Sarki.Na
sami inuwa mai sanyi na zauna har sai da rana
ta fadi, duhun dare ya fara shigowa, ban ga
kowa ba, ban ji muryar kowa ba sai kukan
tsuntsaye. Daga nan sai na kwanta a wannan
wuri na mimmike, barci kuwa ya yi awon gaba
da ni. Ban farka ba sai da gari ya waye.
Bayan gari ya waye sai na tashi na ci gaba da
tafiya a cikin tsibirin, ban gushe ba ina tafiya har
na iso ga wani dan tabki wanda ruwan koramu
ke taruwa a cikinsa. Na iske wani dan tsoho
tukuf zaune a gindin wannan tabki, jikinsa duk
tsumma, ya daura igiyar rama ga
kwankwasonsa. Na ce a cikin raina, "watakila
wannan dan tsoho shi ma jirginsu ne ya karye
Allah ya kubutar da shi zuwa wannan tsibiri."

Na matsa kusa gare shi na yi masa sallama, sai ya
amsa mini da hannu, amma bai yi magana ba.
Na tambaye shi, "Baffa, me ya zaunar da kai
wannan wuri?"
Ya yi doguwar ajiyar zuciya, ya yi mini alama da
hannu kamar yana cewa, "samari, ka taimake ni
ka dauke ni bisa kafadarka, ka kai ni karshen
waccan korama." Ya nuna wajen da hannunsa.
Na dubi inda ya nuna da hannunsa. Na ce a
cikin raina, "bari in taimaki wannan dattijo,
watakila ba shi da lafiya ne. Wa ya sani ko
sanadin taimakonsa Allah ya yi mini rahama."
Na duka na dauke shi bisa wuyana, na kai shi
wurin da ya nuna mini. Na ce masa sauko na
kawo ka inda ka ce. Amma sai tsohon nan ya ki
sauka, maimakon ya sauka ma sai ya kara
makalkale mini wuya da kafafunsa. Na ga
kafafun baki kirin, sirara lullube da gashi, kamar
kafafun dawaki har da kofato. Da na ga
wadannan irin kafafu nasa sai na tsorata, na yi
niyyar in jefar da shi in gudu, amma sai na kasa
cire shi daga jikina, domin ya makalkale wuyana
gam, numfashi ma da kyar nake yi. Ya kara
makalkale mini wuya har na kasa sheda, na fadi
kasa don wuya. Maimakon mugun tsohon nan
ya kyale ni yayin da ya ga na fadi kasa, sai ya
sake gyara zama bisa wuyana yana jira in tsahi.
Da ya ga ba ni da alamun tashi sai ya sa duga-
dugan kafarsa ya fara buguna ga hakarkari.
Wayyo Allah! Zafin wannan bugu ba ya
misaltuwa, kamar ana sa guduma ana buguna
ga awazzai. Ban san lokacin da na mike tsaye
ba da sauri, na ci gaba da tafiya kamar dokin da
ake yi wa kaimi.

Ya yi ta nuna mini wurare da hannunsa inda
yake so in kai shi, daga wannan bishiya zuwa
waccan, daga wannan tabki zuwa wancan. Idan
ya ga na rage sauri sai ya buga mini busassun
kafafun nan nasa ga hakarkari, sai in zabura in
kara mai. Haka tsohon nan ya yi ta wahalar da
ni dare da rana, ya yi fitsari bisa wuyana, ya yi
kashi bisa wuyana. Na zama dokinsa tsakanin
karya da gaskiya, dare da rana yana bisa
wuyana, ko barci zai yi sai dai ya yi bisa
wuyana. Idan zai yi barcin sai ya nannade
wuyana da kafafunsa, ya kwanta bisa gadon
bayana, idan ya farka sai ya yi mini ishara da
mu tafi.

Na zargi kaina da kaina bisa taimakon wannan
mugun tsoho, na gwammace mutuwa da
wannan bakar wahala. Na rika cewa a cikin
raina, "faufau ba zan kara taimakon kowa ba
tsawon rayuwata." Haka na kasance cikin
tsananin azaba da wahala, tsawon zamani. Ban
gushe ba cikin wannan hali, wata rana ina yawo
da tsohon nan bisa wuyana har na zo wani wuri
inda gorunan duma suka fito, sun zuba 'ya'ya
manya-manya a kasa. Na ciri gora daya na fafe
shi daga sama na yi masa 'yar kofa karama, na
katse tuwon da ke cikinsa na zubar, na shanya
shi ga rana har ya bushe. Na samo 'ya'yan inabi
na yi ta matse ruwansu a cikin goran nan har na
cika shi fal da ruwan 'ya'yan inabi. Na ajiye
goran nan a rana tsawon kwanaki har sai da na
tabbatar cewa ruwan inabin nan ya zama giya.
Na dauki goran nan na rika sha daga giyar nan
ina samun kuzarin da nake daukar wannan
tsoho, kuma tana taimaka mini wajen mance
damuwar da nake ciki.
Na ci gaba da shan giyar inabi har wata rana
tsohon nan ya yi mini ishara da hannu yana
tambaya ta, "menene wannan abu da kake
sha?"

Na ce masa, "wannan shi ne ruwan farin ciki, mai
kore dukkan damuwa, mai sa nishadi a cikin
zuciya." Na kurbi giya na yi sassarfa da shi cikin
itace. Daga nan kuma sai na yi ta tikar rawa ina
waka cikin farin ciki. Yayin da tsohon nan ya ga
haka sai ya miko hannunsa alamun in ba shi wai
shi ma ya sha. Saboda tsoronsa da nake ji ban
ko yi musu ba, sai na mika masa goran giya. Ya
karba ya daga gora sama, makwal, makwal,
makwal, sai da ya shanye duka giyar da ke ciki.
Yana gama shanyewa sai shegiyar ta fara aiki,
abinka da bakon giya, sai ya jefar da goran nan
kasa ya mace. Ya rika wata irin jijjiga bisa
wuyana kamar wanda doki ke sukuwa da shi.
Daga nan sai na ji shar ya sako mini fitsari ga
jiki, ya jika mini tufafina duka da fitsari.
Giya fa ta hau kan tsohon nan, sai na ji dukkan
gabobinsa sun saki, kafafunsa da ya nannade
wuyana da su sun warware, nan take ya fita
daga cikin hankalinsa. Ina ganin haka ban yi
wata-wata ba sai na riki kafafunsa da
hannuwana biyu, na cire shi daga kan wuyana,
na yi hajijiya da shi na kwantara kafuri ga kasa...

DAGA Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ15 HIKAYAR SINDABAD MAI TEKU DA SINDABAD DAN DAKO

ga giya ta buge tsoho, duka gabobin jikinsa sun
saki, sai na riki kafafunsa na cire shi daga kan
wuyana, na yi hajijiya da shi na kwantara ga
kasa. Gudun kada ya farka daga maye ya kara
cutar da ni, sai na dauko wani katon dutse na
kwantsama masa bisa kai.
Kansa ya fashe, kwanya ta tarwatse ko'ina, bai
ko shura ba ya mutu cikin maye. Na tafi na bar
mushen banza a nan, ina mai rokon Allah ya
kona shi da wuta mafi radadin azaba.
Na yi wa Allah godiya da ya raba ni da shaidanin
tsohon nan. Na ci gaba da kasancewa cikin
tsibiri ni kadai, ina ci daga 'ya'yan itace ina shan
ruwan koramu. Na kasance ina zama kusa ga
gabar teku ko Allah zai koro da wani jirgi da zai
wuce ta kusa ga wannan tsibiri.

Wata rana kuwa ina zaune bakin gaba ina kallon
ruwan teku ina tunanin abin da ya faru a baya,
na tambayi kaina da kaina, "anya kuwa zan
koma gida daga wannan tafiya tawa?" Kamar an
ba ni amsa, sai na hangi wani jirgi daga nesa
yana keta ruwan teku, ya tinkaro wannan tsibiri
da nake ciki. Jirgi ya iso bakin gaba ya tsaya,
daga dama gare ni, nesa da inda nake tsaye ina
kallon sa. Mutanen da ke cikin jirgin suka yi ta
fitowa suna shiga cikin wannan tsibiri. Yayin da
na ga haka sai na nufi wurin su. Suna ganina sai
suka zagaye ni suna kallo. Suka tambayi
labarina da dalilin zuwana wannan tsibiri. Na
kwashe labarina duka na gaya musu. Suka cika
da mamaki suka ce, "ka sani cewa tsohon nan
da ya hau bisa wuyanka ana ce masa Shaihul
Baharu, ba mutum ba ne, tsohon dan ruwa ne.
Bai taba hawa wani mutum ya sauka daga gare
shi ba har sai mutumin ya mutu, idan kuma ya
mutu sai ya cinye gawar. Kai ne mutum na farko
da ya hau har ya sauka daga gare ka ba tare da
ka mutu ba."
Daga nan sai suka kawo mini abinci iri-iri suka
girke a gabana, na zauna na ci na koshi. Suka
ba ni sabbin tufafi na saka, na watsar da na
jikina domin tuni sun zama tsummokara. Bayan
sun huta a cikin wannan tsibiri, sai suka saka ni
cikin jirgi na tafi tare da su. Muka yi ta keta
ruwan teku har Allah ya kawo mu wani birin a
bakin teku, wannan birni ana kiransa Birnin Birai.
Gidajen wannan birni duka masu tsawo ne
kamar benaye. Birnin zagaye yake da ganuwa,
yana da babbar kofa daya ta shiga mai wani irin
kyaure na marke mai karfi, wanda aka adanta da
karafuna domin kara masa karfi. Wannan kofa
tana kallon teku, wanda duk zai shiga birnin, to,
sai in ya fito ne daga bangaren teku. Bayan
birnin kuwa tsaunuka ne masu tsawo, babu
kome a saman su sai birai.
Kodayake sunan wannan birni Birnin Birai, amma
ba biran ne a ciki ba mutane ne. Dalilin da ya sa
ake kiransa Birnin Birai saboda biran da ke
zagaye da birnin ne wadanda suke yi wa
mutanen cikinsa ta'adi daga lokaci zuwa lokaci.
Har ta kai ma kullum da dare sai mutanen birnin
su shiga cikin 'yan kananan jiragen ruwa su
shige cikin teku su kwana saboda tsoron barnar
wadannan birai.
Yayin da na ji wannan labari sai na ji gabana ya
fadi, domin na san arangamar da na taba yi da
wasu birai. Muka shiga cikin wannan birni domin
kashe kwarkwatar ido, ni kuwa da karambani sai
na ratse ta wani lungu na rabu da abokan
tafiyata. Lokacin da na gama duba wannan
birini sai na nufi bakin teku inda jirginmu yake,
lokacin kuwa marece ya yi, duhu ya fara sauka.
Ina zuwa sai na tarar da babu jirgi, babu
dalilinsa, abokan tafiyata sun tafi sun bar ni. Na
yi zaune cike da bakin ciki mara misaltuwa, na yi
ta zubar da hawaye kamar ruwa. Ina nan zaune
cikin wannan hali sai ga wani mutum daga cikin
mutanen birnin ya zo wurina. Yayin da ya lura
da halin da nake ciki sai ya ce mini, "amma kai
bako ne ko?"
"I, ni bako ne matafiyi," na amsa masa, "mun zo
wannan birini tare da abokan tafiyata, bayan
mun gama yawo cikin birnin da na dawo sai na
tarar da sun tafi sun bar ni."
Mutumin ya ce, "Allah Sarki. Tashi mu tafi, kada
ka kwana cikin wannan birni birai su halaka ka."

Na ce, "To." Na tashi na bi shi zuwa ga wani
kwale-kwale nasa, na shiga tare da shi. Na ga
sauran mutanen birnin duk sun shiga cikin nasu
jiragen ruwa, muka shiga cikin teku muka
kwana. Bayan gari ya waye sai duk mutane
suka koma cikin birni suka ci gaba da
kasuwancinsu. Haka na ga mutanen wannan
birni sun kasanace, duk wanda ya kuskura ya
kwana cikinsa sai dai da safe a isko gawarsa,
biran nan sun kashe shi. Da zarar asuba ta yi
sai biran su fice daga cikin birnin su koma bisa
tsaunuka suna cin 'ya'yan itace, haka ake
kullum, ga mutum da kerarren gida amma ba shi
da ikon kwana ciki. Birnin nan yana nesa kwarai
da kasashen bakar fata.
Na ga abubuwan mamaki da yawa a cikin
wannan birni, amma babban abin da ya fi ba ni
mamaki shi ne, wata rana muna cikin kwale-
kwale inda muka saba kwana ni da abokina, sai
ya tambaye ni, "abokina, shin ba ka da wata
sana'a ce ta hannu da za ka rika yi a cikin
wannan birni namu kana samun kudi? Ka ga
kafin ka tashi tafiya ka sami guzuri."

Na amsa masa, "ni falke ne mai arziki kwarai da
gaske, domin har jirgin ruwa na mallaka, sai dai
jirgin ya yi hatsari cikin teku ya nutse da
dukiyata mai tarin yawa." Na ba shi labarin abin
da ya faru gare ni, na kara da cewa, "ban da
fatauci ban iya wata sana'a ta hannu ba."
Lokacin da ya ji haka sai ya yi shiru yana tunani.
Daga nan sai ya kawo wata jaka da aka yi da
auduga ya ba ni, ya ce, "amshi wannan jakar ka
cika ta da 'yan kananan duwatsun da ke bakin
teku. Ka tafi tare da mutanen da zan hada ka da
su, ka aikata abin da ka ga sun aikata. Da
yardar Allah madaukakin Sarki za ka sami
dukiya fiye da wadda ka rasa a hatsarin jirgi."
Muka tafi bakin teku tare da shi, na tsinci
tsakuwa manya da kanana na cika jakar nan da
su. Muna nan sai muka ga wasu mutane suna
fitowa daga cikin birni kowane yana dauke da
jaka irin tawa. Abokina ya je kusa gare su ya ce
musu, "ku taimaki wannan mutum, bako ne. Ku
tafi tare da shi ku koya masa abin da kuke yi, ko
ya sami sana'ar kore wa bakinsa kuda. Ku kuma
Allah zai biya ku a kan taimakon bako."
Suka ce mun ji mun yarda. Muka gaisa da su, na
yi sallama da abokina na bi wadannan mutane.
Muka yi ta tafiya cikin daji har muka iso ga wani
kwari mai fadin gaske. Babu abin da ke cikin
wannan kwari sai wasu irin dogayen bishiyoyi
masu tsayin gaske, jikin bishiyoyin kuma sumul
yake babu ta yadda za a yi a hau saman su.

Muna shiga cikin wannan kwari sai muka tarar
da birai masu yawa suna barci karkashin
wadannan bishiyoyi, suna jin motsinmu sai suka
farka, suka bazama cikin daji da gudu, wasu
kuma suka haye saman itatuwan nan suna
kallon mu, suna yi mana gwalo.
Sai abokan tafiyata suka tsaya, suka bude
jakarsu suka rika dauko tsakuwa guda-guda
suna jifan biran da suka haye saman dogayen
bishiyoyin nan. Su ma birai sai suka rika tsinko
'ya'yan itacen suna jifar mu da su, wai su rama.
Da na dubi 'ya'yan itacen da suke jifar mu da su
sai na ga ashe kwakwa ce irin ta kasar Hindu.
Sai ni ma na je ga wata bishiya wanda na ga
birai da yawa sun taru samanta, na yi ta jifarsu
da tsakuwa suna jeho ni da 'ya'yan kwakwa. Na
yi ta tsince 'ya'yan kwakwar ina zubawa cikin
jakata, ko kafin tsakuwata ta kare har jakata ta
cika da 'ya'yan kwakwa. Sauran abokaina kowa
ya cika jakarsa da 'ya'yan kwakwa, daga nan
sai muka juya zuwa gida. Ko da muka isa har
marece ya yi.
Na nufi wurin abokin nan nawa dan kirki, wanda
ya hada ni da wadannan mutane, na ba shi abin
da na samo, na kuma yi masa godiya mai yawa.
Amma sai ya ki karbar 'ya'yan kwakwan nan, ya
ce mini, "ka tafi da su cikin birni ka sayar ka
amfana da kudin. Ka ci gaba da yin haka
kullum." Ya kawo mabudin gidansa ya ba ni, ya
ce, "idan ka samo 'ya'yan kwakwar, ka zabe
masu kyau ka adana a cikin gidana, ka sayar da
wadanda ba su da kyau. Idan ka bar wannan
birni namu za ka sami dukiya mai yawa daga
'ya'yan kwakwar da ka tara. Domin da yawa
fatake kan zo takanas domin sayen wadannan
'ya'yan kwakwa su kai kasashensu su sayar."

"Allah ya yi maka albarka," na ce masa. Na rika
fita kullum tare da mutanen nan masu dibar
'ya'yan kwakwa, suka rika nuna mini itatuwa
wadanda ke yin 'ya'ya masu kyau. Cikin 'yan
kwanaki kadan na tara 'ya'yan kwakwa zababbu
masu yawan gaske, na kuma sami kudi daga
wadanda nake sayarwa kullum. Na rika sayen
kayan haja ina ajiyewa. Da kadan-kadan na
tara dukiya mai yawa a cikin wannan birni. Ina
nan kan haka, wata rana sai ga wani babban
jirgin fatake ya zo wannan birni. Suka saya,
suka sayar, da yawan su sai na ga sun sayi
'ya'yan kwakwa domin komwa da su
kasashensu.
Na je ga abokina na gaya masa labarin zuwan
jirgi, na ce masa ina so in koma kasarmu, cikin
'yan uwana. Ya ce mini, wannan daidai ne. Na yi
masa godiya mai yawa, muka rabu muna kuka
don sabo. Na tafi ga Madugun jirgi na nemi
izinin tafiya tare da su. Ya amsa mini babu
gardama. Na dauko hajata da na tara a wannan
birni, da 'ya'yan kwakwa na sanya cikin jirgi. Da
lokacin tafiya ya yi, aka kwance jirgi muka tafi
cikin teku, muka bai wa birnin Birai baya.

Muka yi ta bin garuruwa da birane,
mu saya, mu sayar, na rika sayar da 'ya'yan
kwakwar nan da kudi masu yawan gaske, cikin
dan kankanin lokaci sai na mayar da dukiyata
da na yi asara har na ninka ta ninkin-ba-ninki.
Daga cikin biranen da muka shiga har da wani
birni wanda mutanen cikinsa ba su da wata
sana'a sai noman citta da tafarnuwa da kayan
yaji, na sayi masu yawa domin za a sami riba
gare su a Bagadaza.
Daga wannan birni sai muka wuce zuwa wani
tsibiri mai suna Tsibirin Usirata, a nan na sayi
sandunan Indiya bayan na sayar da wasu daga
cikin 'ya'yan kwakwa. Daga nan kuma sai muka
ci gaba da tafiya bayan kwana biyar muka iso
ga wani tsibirin, a nan kuma na sayi sandunan
Siniya masu daraja fiye da sandunan Indiya. Sai
dai su mutanen wannan tsibiri maguzawa ne,
babu ruwansu da wani addini, sun mai da shan
giya kamar shan ruwa, zina kuwa a wajen su ba
su dauke ta a bakin kome ba. Haka suke kara
zube kamar dabbobi. Daga wannan tsibiri kuma
sai wani tsibirin, shi kuma mutanen cikinsa ba
su da wata sana'a sai a ba su kudi su yi nitso
cikin teku su lalabo wa mutum lu'ulu'u. Na ba
da 'ya'yan kwakwa aka lalubo mini lu'ulu'u mai
yawan gaske.

Haka dai muka ci gaba da tafiya daga wannan
tsibiri zuwa wancan, daga wannan birni zuwa
wancan. Har Allah mai girma da daukaka ya
nufe mu da isowa birnin Basara lami lafiya.
Bayan na huta kwana biyu, sai na kwashi
kayana sai Bagadaza, Gidan Aminci. Na ishe
gidana lafiya. 'Yan uwa da abokai suka yi ta
zuwa suna yi mini barka, a wannan tafiya ma na
dawo da dukiya mai yawan gaske. Na bayar da
kyaututtuka ga abokaina, na rarraba sadaka ga
mabukata, na ciyar da miskinai da marayu. Na
ci gaba da sha'anina na bushasha na manta da
duk wahalhalun da na sha a baya. Wannan shi
ne labarin tafiyata ta biyar, idan Allah ya kai mu
gobe zan fada muku labarin tafiyata ta shida,
wadda ta fi wannan ban mamaki.
Aka kawo musu abinci da abin sha, suka ci suka
koshi. Sindibad Matafiyi ya ba Sindibad dan
dako dinari dari, ya sallame shi. Sauran tajirai
suka yi sallama da mai gida suka tafi suna
mamakin wannan labari da suka ji.

Haka shi ma
Sindibad dan dako ya tafi yana mamaki, ya
kwanta barci yana alla-alla gari ya waye domin
ya koma gidan Sindibad Matafiyi ya ji labarin
tafiyarsa ta shida.
Gari na wayewa dan dako ya kimtsa ya nufi
gidan Sindibad Matafiyi. Bayan sauran tajirai
sun hadu an kawo musu abinci sun ci, sai mai
teku ya fara labarin tafiyarsa ta shida.

daga Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ
16 HIKAYAR SINDABAD MAI TEKU DA SINDABAD DAN DAKO

TAFIYAR SINDIBAD TA SHIDA A CIKIN TEKU.
Bayan na dawo gida daga tafiyata ta biyar, sai
na ci gaba da sheke ayata, ina more rayuwata
daga dukiyar da na tara wadda ba ta da alamun
karewa. Ana nan rannan sai wasu abokaina
fatake suka kawo mini ziyara, muka zauna muka
yi ta hirar duniya, da labarin tafiye-tafiye. Daga
nan sai bakin halina na son shiga duniya ya
motsa, na ji babu abin da nake so kamar in
shiga duniya, in gano kasashe da mutane da
tadojinsu. Daga nan sai na yanke shawarar
zuwa fatauci.
Na tafi kasuwa na saisayi kayayyakin da nake
bukata, na hada haja na kulle ta wuri daya. Na
yi ban kwana da mutanena na nufi birnin Basara
tare da hajata. Na iske jirgi zai tashi da fatake,
na biya kudi na sanya kayana tare da fatake. Da
aka gama shiri tsaf, sai jirgi ya motsa cikin teku.
Muka bar birnin Basara cikin aminci, muka
tsunduma cikin teku bisa ga kudirar Ubangiji
madaukakin Sarki.

Muka yi ta tafiya mu shiga wannan gari,
mu bulla wancan, mu shiga wannan tsibiri mu
shiga wancan, muna saye muna sayarwa muna
kuma ganin al'umma daban-daban, kowace da
irin al'adunta. Ba mu gushe ba cikin wannan
hali, wata rana ta daga cikin ranaku muna cikin
tafiya cikin teku, gaba ruwa, baya ruwa, dama
ruwa hagu ruwa. Kwatsam sai muka ga fuskar
Madugu ta canza, ya yi wata irin kururuwa mai
firgitarwa, ya cire rawaninsa ya yi jifa da shi cikin
jirgi. Ya yi tsalle ya yi faduwar 'yan bori, ya rika
marin fuskarsa yana tuge gemunsa, muka ji
yana cewa, "kaicona! kaiconku 'ya'yana! Shi ke
nan kun zama marayu!"
Muka zagaye shi duk hankulanmu a tashe,
muka tambaye shi, "ya Ra'isu, menene ke
damunka?"
Ya ci gaba da kuka bai kula mu ba, muka yi ta
rarrashin sa, daga nan sai ya ce mana, "ku sani
ya ku jama'ar fatake, jirginmu ya bar hanyar da
muka sani, mun shiga wani tafarki wanda ban
san shi ba. Idan ba Allah ya ji

Please Login or Register in order to submit comment