Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Da yawa mutane a wurina
suke kamun kafa idan suna neman wata bukata
ga Sarki.
Na zauna a wannan birni cikin dadin rai da
kwanciyar hankali. Sai dai abu daya kawai ke
tayar mini da hankali. Wannan abu kuwa shi ne,
na sha tambayar mutanen wannan birni labarin
Bagadada har na gaji, amma ban samu wanda ko
ya ce ya taba jin sunan birnin ba. Wannan shi ne
kawai damuwata. Domin duk wannan daula da
nake ciki ina matukar son in koma kasarmu, cikin
'yan uwana da abokai.
Wata rana na shiga wurin Sarki Mihirjanu sai na
same shi tare da wasu baki 'yan kasar Hindu. Na
yi musu sallama, suka mayar mini da sallamata.
Bayan mun gaisa sai suka tambayi labarina da
kuma kasar da na fito. Ni kuwa na ce musu ku
fara gaya mini labarinku. Suka ce mini su 'yan
asalin kasar Hindu ne, amma ba kabilarsu daya
ba. Akwai 'yan kabilar Shakiriya daga cikinsu,
wadda kabila ce mai son zama lafiya, ba ta
takalar kowa kuma ba ta yaki da kowace kabila.
Akwai kuma 'yan kabilar Burahamiya, wadanda
babu ruwan su da shan giya, sai dai masu arziki
ne sosai a kasar Hindu, sun mallaki shanu da
rakuma da tumaki da awaki. Haka kuma suka ce
mini akwai kananan kabilu a kasar Hindu har
guda saba'in da biyu. Na yi mamaki da jin
wannan labari nasu.
Ni kuma na duka na kwashe nawa labari na gaya
musu, na kuma gaya musu na fito ne daga kasar
Bagadada.
A cikin abubuwan mamaki da na gani, wadanda
ba zan manta da su ba, a dan zaman da na yi a
tsibirin Sarki Mihirjanu, akwai wani dan karamin
tsibiri mai suna Kasilu, wanda ke makwabtaka da
na Sarki Mihirjanu. Kullum sai dare ya yi tsaka
sai a yi ta jiyo ganguna da algaitu na tashi kamar
ana biki, duk da cewa babu dan Adam ko daya a
cikin wannan tsibiri. Sai dai ana jita-jitar wai
mutanen boye ne ke wannan shagali da dare.
Haka kuma na taba ganin wani kifi mai tsawon
zira'i metan a cikin teku, inda masunta ke su.
Girman wannan kifi sai da ya tsorata kowa.
Masunta suka hadu suka dauko itace suka kore
shi ya gudu cikin ruwa.
Na taba ganin kuma wani kifi mai kai irin na
mujiya a cikin wannan tsibiri. Kai, abubuwan
mamaki da na gani suna da yawa a wannan
tsibiri.
Na ci gaba da zama tare da Sarki Mihirjanu,
kullum ina zuwa bakin teku domin daukar rahoton
jiragen da ke shigowa da kuma masu fita.
Wata rana ina bakin teku kamar yadda na saba
ina jiran isowar jigi. Na yi tsaye na dogara ga
wata sanda ina kallon ruwa. Can sai na hangi
wani babban jirgi yana nufo gabar ruwa inda nake
tsaye. Da jirgi ya iso bakin gaba sai ya tsaya.
Aka daure shi da igiya, aka aza itatuwa masu
fadi daga cikin jirgin zuwa ga saman kasa, inda
mutane za su taka su fito. Fataken dake cikin
jirgin suka yi ta fito da hajojinsu daga cikin jirgi.
Ni kuwa ina tsaye ina daukar lissafin kayansu.
Bayan sun fito da kayansu duka sai na tambayi
madugun jirgin, "Iyakacin kayan da kuka zo da su
ke nan?"
Ya amsa mini, "Ya shugabana, akwai 'yan
uwanmu da suka halaka a cikin wannan tafiya,
mun sayar da kayansu duka, saura na mutum
daya daga cikinsu muka zo da shi wannan birni.
Idan mun sayar da kayan za mu kai wa iyalansu
kudin a Birnin Bagadada, Gidan Aminci."
Yayin da na ji ya ambaci Bagadada sai gabana
ya fadi, na tambaye shi, "Menene sunan falken
da kuka zo da kayansa?"
Ya amsa mini, "Sunansa Sindibad."
Da na ji haka sai na kalli madugun nan da kyau
sai na gane ashe dai madugun jirginmu ne da
muka fito gida tare. Saboda saje da gemun da
suka fito masa ne buzu-buzu a fuska ya hana in
shaida shi da farko. Na yi wata irin kara don
murna, har sai da ya tsorata.
Na dube shi na ce, "Ya madugu, shin ba ka
shaida ni ba? Ai ni ne Sindibad da muka fito tare
da kai da sauran fatake daga Bagadada. Lokacin
da ka yi kiran mu da mu koma cikin jirgi kafin
katon kifin nan ya nutse da mu, muna nesa da
jirgi. Kafin mu yi taku daya har ya nutse da mu
cikin ruwa, sauran wadanda muka nutse tare duk
sun halaka. Amma ni sai Allah mai girma da
daukaka ya jeho mini wani gungumen itace na
haye bisa gare shi. Iska ta yi ta tura ni har ta
kawo ni cikin wannan tsibiri. Ina yawo cikin
tsibirin na hadu da 'yan bargar Sarki Mihirjanu,
suka kawo ni gaban Sarki. Na gaya masa
labarina, ya tausaya mini har ma ya nada ni mai
kula da gabar teku inda jiragen ruwa ke sauka.
Don haka wadannan kaya da ke cikin jirgi nawa
ne da na fito da su daga gida domin yin fatauci."
Da madugu ya gama jin zancena sai na ga ya
rike baki cikin mamaki yana yi mini wani irin
kallo na rashin yarda. Ya rika tafa hannu yana
sallallami, "Babu Sarki sai Allah. Mhm! Lallai
zamani ya lalace, mutane ba su tsoron Allah!
Sun mayar da yin karya kamar a sha ruwa a tafi."
.
Za mu ci gaba ==>Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ4. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD
DAN DAKO
Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Sabuwar Fassarar:
Ibrahim Malumfashi,
Danladi Haruna,
Bukar Mada.
...
Sindibad mai teku ya ci gaba da labari ya ce, na
ce wa madugu hajar da ke cikin jirgi tawa ce
wadda na zo da ita daga gida domin yin fatauci.
Da madugu ya gama jin zancena sai na ga ya
rike baki cikin mamaki yana yi mini wani irin
kallo na rashin yarda. Ya rika tafa hannu yana
sallallami, "Babu Sarki sai Allah. Mhm! Lallai
zamani ya lalace, mutane ba su tsoron Allah!
Sun mayar da yin karya kamar a sha ruwa a tafi."
Da na ga dai madugu bai yarda da zancena ba
sai na ce masa, "Ya Ra'isu, Wallahi gaskiya nake
gaya maka. Shin ba ka gane ni ba ne?" sai na
rika duba kaina wai ko wani abu ya canja ne a
jikina.
Madugu ya amsa mini, "Watau don ka ji na
ambaci haja wadda mai ita ya mutu a cikin ruwa,
kake so ka yi mini karya don kawai in ba ka
hajar. Hala kurege ya cije ni da zan yarda da
maganarka? Muna kallo da idanunmu duk
mutanen da suka nutse cikin teku suka mutu.
Babu daya daga cikinsu da ya tsira."
Na kara maraairaice masa, "Haba Ra'isu! Don me
zan yi maka karya gemai-gemai da ni. Ai karya
na daya daga cikin alamomin munafuki. Saurari
labarina da kunnen basira." Na kara gaya masa
labarina, tun fitowar mu daga Birnin Bagadada da
biranen da muka ya da zango muka taba ciniki.
Da yadda muka sauka bisa bayan kifi muna
tsammanin tsibiri ne, da yadda kifin ya nutse da
mu cikin ruwa. Na gaya masa yadda aka yi na
tsira har na zo wannan tsibiri. Na dai gaya masa
kome tun daga farko har karshe.
Yayin da sauran fatake suka ji labarina sai suka
ce lallai wannan Sindibad ne, babu shakka.
Madugu ya yarda da labarin da na gaya masa.
Suka yi mini barka da arziki da na kubuta daga
halaka. Suka ce, "Wallahi mun dauka dukanku
kun mutu."
Madugu ya ba ni hajata, na kuwa gan ta yadda
take, ko allura ba a taba ba. Lalle wannan
madugu da amana yake.
Na debi kayayyaki masu daraja da ke cikin hajar
na kai wa Sarki Mihirjanu kyauta. Na gaya masa
abin da ya faru, na ce masa masu wannan jirgi
abokan tafiyata ne da muka fito gida tare.
Ya yi mamaki matukar mamaki, ga shi kuma
gaskiyata ta fito ta labarin da na gaya wa Sarki
tun farkon zuwana gare shi. Sarki ya kara
girmama ni. Ya kara mini kyaututtukan kaya
ninkin wadanda na ba shi sau goma.
Na sayar da hajata a wannan tsibiri, na sami riba
mai yawa. Na sayi wasu kayayyakin da na san za
su yi tsada a Birnin Bagadada.
Bayan 'yan kwanaki kadan duka sauran fatake
suka sayar da hajarsu suka sayi wasu kayan da
za su koma da su. Da suka gama shirin tafiya na
sa kayana a cikin jirgi. Na tafi wurin Sarki na yi
ban kwana da shi. Ya kara mini wata kyautar fiye
da wadda ya ba ni a baya. Na bar wurinsa yana
kuka ina yi don sabo.
Muka shiga jirgi muka fada teku. Iska kuwa ta yi
mana dadin sha'ani. Muka yi ta tafiya kwana da
kwanaki ba tare da wani hatsari ba. Allah da
ikonsa ya kaddare mu da isowa birnin Basara
lami lafiya.
Bayan mun huta a birnin Basara mun kuma taba
ciniki, sai muka yi gaba zuwa gida Bagadada,
gidan aminci. Kwanci tashi muka iso bakin gabar
tekun birnin Bagadada. Kowane falke ya rungumi
kayansa ya nufi gida. Ni kuwa sai da na bidi
masu rakuma suka yi mini labtun kayana zuwa
gida.
'Yan uwa da abokan arziki suka yi ta zuwa suna
yi mini barka da dawowa. Bayan kwana biyu na
sake sayen kayayyakin da na sayar a gidana, na
kawata shi fiye da yadda yake da farko. Na sayi
bayi da kuyangi masu yi mini hidima. Na sayi
gonaki da gidaje da filaye. Na bude rumfuna a
cikin babbar kasuwar Bagadada ina ciniki a cikin
su. Na zama dai hamshakin mai arziki fiye da da.
Da yake an ce mai hali ba ya barin halinsa, sai
na koma wa halina na da, na rika tara abokai ina
kashe musu gara suna kwasa. Na manta da
wahalar da na sha a baya. Amma da yake ina
saye da sayarwa ina samun riba, dukiyata ba ta
ja baya ba.
Wannan shi ne labarin tafiyata ta farko. Idan
Allah ya kai mu gobe zan gaya muku labarin
tafiyata ta biyu, wadda ta fi wannan hatsari da
ban mamaki.
Yayin da Sindibad mai teku ya gama ba da
wannan labari, sai ya sa aka sake fito da
akussan abinci da abin sha. Aka aza wa kowane
tajiri akushin abinci da abin sha a gabansa. Shi
kuma ya ci tare da Sindibad dan dako.
Bayan sun gama cin abinci ya kawo dinari dari
ya ba dan dako, ya ce, "Karbi wannan kudi ladar
tsayawa da ka yi tare da mu. Mun hana ka zuwa
neman kudi."
Dan dako ya karbi kudi ya yi godiya, ya tafi yana
mamakin irin wahalhalun da mutane ke fadawa
garin neman kudi. Ya kwana yana tunanin
wannan labari.
Da gari ya waye, tun da safe ya shirya ya nufi
gidan Sindibad bahariyi. Yana zuwa aka karbe shi
hannu bibbiyu, mai gida ya zaunar da shi kusa
gare shi.
Jimawa kadan sauran abokan Sindibad mai teku
suka iso gidan. Kuyangi suka yi ta fitowa da
akussan abinci da nama da gorunan ababen sha.
Bayan sun ci sun koshi, sai mai gida ya fara ba
da labarin tafiyarsa ta biyu a cikin teku:
TAFIYAR SINDIBAD TA BIYU A CIKIN TEKU
Ku sani ya ku abokaina, bayan na dawo daga
tafiyata ta farko na samo dukiya mai dimbin
yawa. Na zauna cikin jin dadi da kece raini,
kamar yadda na gaya muku jiya.
Ran nan sai zuciyata ta karkata ga son shiga
duniya domin ganin kasashe da tsibirai. Na yi
sha'awar kara fita zuwa fatauci. Na kwashi kudi
masu yawa na sayi hajar da zan tafi da ita.
Na yi sa'a kuwa wani sabon jirgi mai kyau,
wanda aka kawata da kyallaye masu ban sha'awa
zai fita da fatake. Na biya kudi na shiga tare da
kayana da sauran fatake. Jirgi ya motsa, muka
nausa cikin teku.
Muka dace da yanayin teku mai dadi, muka yi ta
tafiya daga wannan tsibiri zuwa wancan tsibiri,
daga wannan gari zuwa wancan gari. Duk garin
da muka je mukan tsaya mu yi ciniki, mu sayar
da kayan da muka zo da su mu kuma sayi
wadanda za mu ci riba a gaba.
Haka muka ci gaba da zagaya garuruwa da
tsibirai har wata rana Allah Madaukakin Sarki ya
kawo mu ga wani babban tsibiri a tsakiyar teku.
Tsibiri ne mai cike da bishiyoyi da nunannun
'ya'yan itace. Ga furanni launi daban-daban
kowace tana fitar da irin kamshin da Allah ya
hore mata. Tsuntsaye na ta rera wakoki iri-iri,
suna tashi daga wannan bishiya zuwa waccan.
Ga koramu ko'ina na gudana, ruwansu garai-garai
kamar mudubi. Amma duk kyawun tsibirin nan ba
mu ga alamun dan Adam ba a cikinsa.
Madugu ya ce mu sauka nan mu huta. Aka daure
jirgi a bakin gaba, dukkan fatake muka sauka
daga cikin jirgi, muka fantsama cikin wannan
tsibiri domin kashe kwarkwatar ido, muna
tu'ajjibin ikon Ubangiji, Buwayi gagara misali.
Na zo ga wata korama mai ruwa gawanin dadi,
na zauna karkashin wata babbar itaciya da ta
saki inuwarta ko'ina. Na zaro 'yar gurasa daga
cikin jakata na ci, na sha ruwan koramar nan na
zauna ina hutawa ni kadai.
Wanna wuri da dadin zama yake, ga sassanyar
iska na kadawa gami da kamshin furanni, kukan
tsuntsaye ya hadu ya kara wa wurin armashi.
Nan da nan sai na ji wata kasala ta rufe ni, na
dan kishingida wai in huta. Barci mai nauyi ya
dauke ni.
Bayan na shafe lokaci mai tsawo ina barci sai na
farka. Na nufi inda jirginmu yake da sauri, amma
ina, ashe na makara. Jirgi ya tafi ya bar ni a
cikin wannan tsibiri da ke tsakiyar teku, fatake
na tsammani ina cikinsu.
Na yi yawo cikin tsibirin nan amma ban ga
mutum ko aljani ba. Hankalina ya tashi, zuciyata
kuma kamar za ta fashe saboda fargaba. Ga shi
dai an bar ni ni kadai babu abinci babu kuma
wani dan Adam da zan gani. Na sakankance da
halaka, na ce a cikin raina, "Lalle ba kullum
safiya take Jumu'a ba. Idan da farko na tsira
daga halaka a tafiyata ta farko, yanzu ba lalle ba
ne in tsira."
Hawaye suka yi ta zuba daga idanuna, na yi da-
na-sanin sake fitowa daga gida domin kwadayin
fatauci. Na tuna irin jin dadin da nake yi a gida,
ga nama ga abinci iri-iri sai wanda raina ke so
nake ci, ga sutura. In kwanta wuri mai kyau, duk
wani aiki kuma sai dai in sa bayi su yi mini. To,
amma yanzu fa? Kwayar abincin ma da zan ci sai
na nema. Da ma an ce garin tone-tone zakara ke
tono wukar yanka shi.
Na yi nadamar fitowa daga Bagadada, bayan duk
wahalar da na sha a tafiyata ta farko. Na yi ta
tafiya cikin wannan tsibiri ina cewa,"Daga Allah
muke, gare shi muke komawa."
Ina tafiya ina tangadi ina surutai ni kadai kamar
sabon mahaukaci ko wanda aljani ya shafa.
Bayan na yi tafiya mai nisa, babu alamun gari ko
kauye ko gida sai na yanke shawarar hawa wata
doguwar bishiya domin hango abin da ke nesa.
Na hau bishiyar na duba ko'ina, Gabas da
Yamma, Kudu da Arewa, ban ga kome ba sai
itatuwa, can gaba kuma ruwan teku ne iyakar
ganin ido. Har zan sauko daga kan bishiyar nan
sai na hangi wani abu fari tas can da nisa daga
shiyar Kudu. Na sauko na nufi inda wannan abu
yake.
Da na zo kusa gare shi sai na gan shi kamar
dutse, ga shi dai fari tas, girmansa kamar daki,
amma kuma siffar kwai. Na zagaya wannan
dutse amma ban ga kofar shiga ba ko wata
matakala da zan hau samansa. Wannan irin dutse
ya ba ni mamaki, sai na yi wata 'yar alama daidai
inda nake tsaye a gindin dutsen. Na rika tsagaya
shi ina kidaya takun kafar da na yi, da na zagayo
inda na yi alamar nan sai na ga na kidaya takun
kafa hamsin daidai.
Na tsaya ina tunanin yadda zan hau wannan
dutse mai santsi, lokacin kuwa rana ta yi tsakiya.
Kwatsam sai na ga hasken rana ya gushe wuri ya
yi duhu. Sai na yi tsammani ko gajimare ne ya
rufe rana, amma da na tuna ai wanna lokacin rani
ne, sai tunanina ya canja.
Na daga kaina sama da sauri domin ganin abin
da ya rufe hasken rana, sai na hangi wani irin
tsuntsu mai girman gaske a cikin sararin
samaniya, ashe fika-fikansa ne suka rufe hasken
rana.
Na yi mamaki da girman wannan tsuntsu, gayar
mamaki, sai na tuna da wani labari da na taba ji
fatake da alhazai na bayarwa. Wai a wani tsibiri
da ke tsakiyar teku ana samun wasu irin manya-
manyan tsuntsaye wadanda ake kira Rukki.
Wai wadannan tsuntsaye sukan fyauce giwa idan
tana kiwo, kamar yadda shaho ke fyauce dan
tsako, su kawo wa dan jinjirinsu wannan giwa ya
cinye ta shi kadai. Nan da nan na gane ashe
dutsen nan fari mai santsi dake gabana shirim
kamar daki, ba dutse ba ne face kwan wannan
tsuntsu, Rukki...

zanci gaba

Yusuf Æbdullâhi Æ Jibagâ links5. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD
DAN DAKO
Daga Littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA
Sabuwar Fassarar:
Ibrahim Malumfashi,
Danladi Haruna,
Bukar Mada.
...
Sindibad mai tekui ya ci gaba da labarinsa ya ce,
yayin da na daga kaina sama domin in ga abin da
ya rufe hasken rana sai na ga wani katon
tsuntsu, wanda girmansa ba ya misaltuwa, ashe
fika-fikansa ne suka rufe hasken ranar.
Na yi mamaki gayar mamaki, sai na tuna da wani
labari da na taba ji fatake da alhazai na bayarwa.
Wai a wani tsibiri da ke tsakiyar teku ana samun
wasu irin manya-manyan tsuntsaye wadanda ake
kira Rukki. Wai wadannan tsuntsaye sukan
fyauce giwa idan tana kiwo, kamar yadda shaho
ke fyauce dan tsako, su kawo wa dan jinjirinsu
wannan giwa ya cinye ta shi kadai.
Nan da nan na gane ashe dutsen nan fari mai
santsi dake gabana shirim kamar daki, ba dutse
ba ne face kwan wannan tsuntsu, Rukki.
Ina nan tsaye kusa da kwan nan ina mamakin
sarautar Ubangiji har tsuntsun nan ya sauko
kasa. Ya lullube ni tare da kwansa, ya yi kwance,
nan take barci ya dauke shi.
Tsarki ya tabbata ga Ubangiji wanda ba ya
gyangyadi balle barci.
Yayin da na ga tsuntsun nan ya yi barci, sai wata
dabara ta zo mini. Na tube rawanina na yaga shi,
na murda shi ya zama kamar igiya. Na yi damara
da shi sa'annan na daure kaina ga kafar Rukki
mai kama da jikin bishiya don girma.
Nufina idan ya farka daga barci zai tafi neman
abinci ya tafi da ni. Ta haka zan sami damar fita
daga wannan tsibiri ke nan, watakila ya kai ni
kusa ga wani birni ko kauye.
Haka na kasance daure ga kafar wannan tsuntsu
tun da rana har gari ya kusa wayewa ban runtsa
ba, gudun kada ina cikin barci ya tashi da ni ban
shirya ba.
Da gari ya waye sai Rukki ya farka daga barci,
ya yi kuka da karfi ya kada fika-fikansa ya tashi
sama da ni daure a jikin kafarsa.
Ya yi ta yin sama har sai da na zaci ya kai
kololuwar sama ta farko sa'annan sai ya yiwo
kasa-kasa a hankali ya sauka cikin wani kwari.
Lokacin da na ga tsuntsu ya sauka cikin kwari
sai na yi sauri na kwance kaina daga kafarsa. Na
fita daga karkashinsa ina neman inda zan boye
don kada ya gan ni, watakila ya hadiye ni. Amma
sai na ga bai ma lura da akwai wata halitta kusa
gare shi ba, saboda kankantata gare shi.
Daga nan sai na ga ya tura kafarsa cikin wani
katon kogo ya kamo wani abu ya tashi sama da
shi. Da na lura da kyau sai na ga wani irin maciji
ne mai girman gaske ya kama, yana ta
wutsilniya. Ya tafi da shi tun ina kallonsa har ya
bace mini. Na yi mamaki matukar mamaki.
Ashe ni ban sani ba, a cikin wani irin kwari nake
mai fadi da zurfin gaske. Ban gane haka ba sai
da na daga kai na sama, sai na gan ni kamar ina
cikin rijiya.
Yayin da na ga haka sai hankalina ya tashi, na
zargi kaina bisa wannan halin da nake ciki. Da
ban baro gida ba da duk wannan wahala ba ta
same ni ba. Tsibirin da na baro ma ya fi wannan
rami kwanciyar hankali. A can ina samun 'ya'yan
itace da ruwa, amma nan ban da duwatsu da
rairayi babu kome.
Babu tsimi babu dabara face daga Allah
Madaukakin Sarki! Duk lokacin da na kubuta
daga wata halaka sai kuma in kara fadawa cikin
wata halakar.
Na ci gaba da tafiya a cikin wannan kwari ina
tunanin yadda zan fita daga cikinsa. Da na lura
da kyau sai na ga ashe rairayin wannan kwari duk
lu'ulu'u ne. Da na isa ga bangon da dutse ya yi
wa kwarin sai na ga dutsen na jauhari ne mai
daraja. Na daga kaina sama amma ban ga wata
matakala da zan hau ba da za ta fitar da ni daga
cikin wanna kwari.
Wannan shi ake kira ga koshi ga kwanan yunwa!
Ga dukiya nan ko'ina a cikin kwarin, amma ni da
nake neman hanyar fita daga cikinsa ba ta
dukiya nake yi ba.
Ban da wannan kuma kwarin cike yake da wasu
irin macizai masu girman gaske. Kowane maciji
girmansa kamar iccen dabino, idan ya bude baki
kuwa sai ya hadiye doki. Wadannan macizai
sukan boye da rana saboda tsoron tsuntsayen da
ke farautarsu irinsu Rukki da mikiya. Sai cikin
dare macizan suke fitowa su nemi na su abinci.
Yayin da rana ta fara yin ja za ta fadi, sai na fara
neman inda zan boye wa wadannan macizai kafin
rana ta sake fitowa. Yunwa da kishirwa duk sai
suka bace saboda tsananin tsoro.
Ina nan ina dube-dube sai na hango wani kogo
mai kofa matsattsiya. Na yi sauri na shige cikin
wannan kogo, na jawo wani dutse mai fadi na
rufe kofar, na ce a cikin raina, "Zan kwana a nan,
idan rana ta fito sai in fita in ci gaba da neman
hanyar da zan fita cikin wannan rami."
Na jujjuya idanuna ko'ina a cikin kogon domin
ganin abin da ke ciki. Numfashina ya dauke
lokacin da na ga wata macijiya daga can saman
wani dutse a cikin kogon da nake, tana kwance
bisa kwayayenta tana barci. Nan take jikina ya
dauki rawa, gashin jikina ya mimmike, na daga
hannuwana sama na fara addu'a ga Ubangijin
talikkai.
A wannan dare dai ban runtsa ba har gari ya
waye. Da na ga hasken rana ya ratso ta cikin
kwarin sai na janye dutsen da na rufe bakin
kogon na fito waje. Na ci gaba da tafiya ina
tangadi kamar mai maye, yunwa kuwa sai dafa ni
take yi, ga tsoro cike fal a cikin raina.
Ina cikin tafiya ina jan kafafu sai na ga an jeho
wani abu daga sama ya fado kusa gare ni, tim.
Na yi tsalle gefe guda don tsoro. Da na duba abin
da aka jeho sai na ga kamar alfadari ne aka
yanka, aka fede fatar, aka cire kai da kafafu aka
jeho naman.
Na daga kaina sama, amma saboda zurfin kwarin
ba zan iya ganin wanda ke bisansa ba. Na yi
mamakin abin da ya sa aka jeho wannan nama.
Daga nan sai wani labari ya fado mini a rai.
Na taba jin fatake na cewa, a wata kasa akwai
wani kwari wanda rairayinsa na lu'ulu'u ne,
duwatsunsa na zinariya. Wai mutanen kasar kan
yanka wata dabba sai su jefa namanta a cikin
kwarin. Lu'ulu'un zai lillike naman da aka jefa.
Shi kuwa wanda ya jefa dabbar sai ya koma wani
wuri ya make yana kallo. Akwai wasu tsuntsaye
dake shiga cikin kwarin neman abinci, idan suka
ga naman sai su dauko shi su fito cikin kwarin
da shi, su sauka bisa wani dutse suna ci. Idan
mai dabbar ya ga haka sai ya fito ya kori
tsuntsun, ya cire lu'ulu'un da ke jikin naman ya
koma gida. Ta haka suke tara dukiya mai yawa.
Idan ba ta wannan hanyar ba babu mai iya shiga
cikin kwarin balle har ya kwaso abin da ke
cikinsa na dukiya.
Yayin da na ga an jeho wannan dabba cikin kwari
ta fado kusa gare ni, sai labarin fatake ya fado
mini ga rai. Nan take sai wata dabara ta zo mini.
Ban yi wata-wata ba sai na cika aljihuna da
lu'ulu'u na kuma kumsa wani mai yawa a cikin
rawanina. Ina cikin dibar lu'ulu'u sai na ga an
sake jeho wata dabbar jif, kusa gare ni.
Da na gama kwasar abin da nake iya dauka na
lu'ulu'u sai na kwanta kasa rigingine. Na dauki
dabbabr nan na aza bisa kirjina, ta rufe ni ruf, ba
a iya gani na. Na kama wani wuri a jikin dabbar
na rike gam.
Ina nan kwance karkashin dabbar nan, kamar
yadda na zata, sai ga wani katon tsuntsu, mikiya,
ta diro bisa naman nan. Ta dauke shi da
kafafunta ta tashi sama, ina rike da dabbar, ta
fito daga cikin kwarin ta sauka bisa wani dutse
mai fadi domin yin kalaci da abin da ta farauto.
Tun kafin ta fara cin naman nan sai na ji ana
tsawa da kururuwa ana buga itace ga kasa
domin dai a tsoratar da ita. Tsuntsuwa ta firgita
ta tashi sama ta bar dabbar a nan. Ni kuma sai
na ture dabbar daga kaina na mike tsaye.
Tufafina duk sun rine da jinin dabbar. Attajirin da
ya kori tsuntsuwar nan bai ko kula da ni ba,
hankalinsa na ga lu'ulu'un da zai cire daga jikin
dabbar. Sai da ya zo kusa ga dabbar sai ya gan
ni tsaye kamar gawar da ta tashi. Saboda
tsananin tsoro sai ya yi mutuwar tsaye, ya kasa
yin gaba balle baya. Ko bakinsa ma ya kasa
motsawa balle ya yi mini magana..

zanci gaba insha Allah.
6. HIKAYAR SINDIBAD MAI TEKU DA SINDIBAD
DAN DAKO

Sindibad ya ci gaba da labari ya ce, tun kafin
tsuntsuwa ta fara cin naman nan sai na ji ana
tsawa da kururuwa ana buga itace ga kasa
domin dai a tsoratar da ita. Tsuntsuwa ta firgita
ta tashi sama ta bar dabbar a nan. Ni kuma sai
na ture dabbar daga kaina na mike tsaye.
Tufafina duk sun rine da jinin dabbar.
Attajirin da ya kori tsuntsuwar nan bai ko kula da
ni ba, hankalinsa na ga lu'ulu'un da zai cire daga
jikin dabbar. Sai da ya zo kusa ga dabbar sai ya
gan ni tsaye kamar gawar da ta tashi. Saboda
tsananin tsoro sai ya yi mutuwar tsaye, ya kasa
yin gaba balle baya. Ko bakinsa ma ya kasa
motsawa balle ya yi mini magana.
Amma saboda son dukiya irin ta dan Adam, da
ya farfado daga mutuwar tsayen da ya yi, sai na
ga ya duka wurin dabbar nan yana duba
karkashinta. Ya juya ta gaba daya bai sami
lu'ulu'u ko daya ba. Sai ya buga sallallami yana
cewa, "Babu sarki sai Allah mai girma da
daukaka, wanda muke neman kariyarsa daga
sharrin Shaidan jefaffe!"
Ya yi ta tafa hannuwa yana salati cike da jimami
yana cewa, "Ya aka yi wannan abu ya faru? Shike
nan na yi asarar dabbata?"
Na matsa kusa gare shi. Yana ganina sai
hankalinsa ya komo gare ni. Ya tambaye ni,
"Wanene

Please Login or Register in order to submit comment