Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Any Mubeenah zaune akan kujera, muka gaida ta ni da su Ni'ima da alamun suma sai lokacin suka gaisa, ta amsa kamar ko da yaushe, babu yabo babu fallasa. Lamarin Anty Mubeenah sam ya daina bani mamaki, shi yasa bana ganin laifin dangin mijinta akan duk abinda zasu ce a kanta, tunda koma meye ai ita ta jawowa kanta. Ace kannen mijin auren ki wai kina amsa musu gaisuwa kamar wasu baki ko irin dangin nan na nesa? Kai ko dangin nesa ne ai ya cancanci ace ka dan nuna sanayya. Na saci kallon su Ni'ima da alamun su abun bai dada su da kasa bama. Muka nufi kan dinning muka zauna, har su na zuba mana funkasun muka fara ci muna er hira. Abbu ya shigo sanye da wata farar riga da farin wando, ya gyara sumar kan shi sai wani irin sheki take yi, da sauri su Ni'ima suka taryo shi suna babban bros! Da fara'ar shi ya tare su ya jingina kowaccen su da jikinshi yana kallonsu, "wato ku dai idan ba aiko ku aka yi ba ba a ganin ku sai a gida ko?" Sa'adiya tace "bros ai kasan halin Baba, baya bari muna yawo fa" yace "ba wani nan dadin baki, ai naji ance har weekend kuke zuwa gidan su Ameenah, wannan ba yawo bane ba kenan?" Ni'ima tace "kar ka damu bros, yau yini ma zamu yi anan" yace ban yarda ba, kwana zaku yi. Ni kam idanuna yana kansu, fadar irin burge ni din da suka yi bata baki da lokaci ne, ban san sun zauna ba sai dana ji muryar Ni'ima a saitin kunnena, "me kike kallo?" nayi firgigit na kalleta, "umh?? Babu komi" ta jefa min wani irin kallo alamun bata yarda dinnan ba, nayi saurin maida hankalina ga Abbu na gaida shi, fuska a cune ya amsa duk sai naji ba dadi, ba haka yake amsa min gaisuwa ta ba. Ji nayi abincin ma ya fita daga raina, na fara tsakura ina turawa a bakina ba don ina jin dadin abincin ba. Su Ni'ima kam hirar su suke yi da Abbu suna dariya. Sa'adiya ta dan tabo ni, na kalleta a sanyaye, cike da kulawa tace "you okay?" na gyada mata kai kawai, Abbu ya kalleni na dan lokaci kafin ya maida kallon shi ga Ni'ima. Anty Mubeenah tazo tayi joining dinmu itama, lokaci zuwa lokaci Abbu yana saka ta cikin hirar da suke yi da kannen shi amma bata cika maida hankali ba duk da nima suna sako ni amma sai dai kawai in danyi murmushi ko inyi nodding a haka dai muka gama cin abincin. Hirar su suka cigaba da yi, na tashi na hada kan kayan da muka 6ata na kai kicin. Kasa komawa inda suke nayi kawai sai na shige daki, Su Mommy na kira na hada mana video call, daddy ma yana gida don haka hirar mu muka sha sosai, na basu labarin bikin da muka je har hotuna da videos din da muka yi na tura musu. Ban yi kuskuren fada musu har dare nayi a wajen bikin ba wanda dalilin haka yasa Abbu ya mun fada kuma har yanxu yake fushi dani saboda nasan kuskurene hakan, kamar nayi kirari ne na dabawa kaina wuta. Su Ni'ima suka shigo dakin na wa su Daddy sallama, nan muka bude sabon shafin hira dasu.
[12/8, 2:03 PM] ‪+234 810 910 7052‬: Wajen karfe uku na dare na farka, kishi ya dame ni sosai ji nake kamar numfashina zai dauke dole na farka daga daddadan barcin da nake yi, gidan dama duniyar gabadaya tayi shiru kamar babu mai numfashi babu ko karar fan saboda an dauke wuta. Fitilar wayana na kunna na lalubi goran ruwa dana saba shiga daki da ita a kullum Saboda na sanni da bukatar shan ruwa sometimes sai dai babu, da alamun na manta ban shiga da ita ba ranar. A hankali na bude kofar dakina na fito, na fara tip toeing zuwa kicin kamar wadda zata je yin sata. Daidai kafar dakin Anty Mubeenah na jiyo kamar alamun sautin tashin maganganu, ban san dalilin daya saka ni kara kasa kunne ba, muryar Abbu ce take tashi kamar cikin fushi, "For goodness sake Mubeenah! How long has it been?? Kin san yaushe rabona dake? Kina ma kirga yawan kwanakin kuwa? Me yasa ne?! Me yasa ne ba zaki yi treating dina kamar yadda kowanne namiji yake samun kulawa daga matar auren shi ba? Na tambaye ki time without numbered Mubeenah, idan ma wani laifi na miki don't you think it's high time da zamu manta da komi mu rungumi rayuwar yayanmu hakanan ba?" tsaki naji taja, "kace duk abinda zaka ce Ibrahim! Ba damuwata bace, yaya da kake magana a kansu inaga ai bai kamata ka sako su ba, kai kace I just need to have birth to them, you will take care of them, meye hadina dasu then??" shiru na tsawon mintuna biyu ya wuce yayin dana kara kasa kunne, a sanyaye naji muryar Abbu wannan lokacin, "hakkina fa kuma Mubeenah?" "ni fa kaga ka dame ni ka hana ni barci na haba! Saboda tsabar fitina da jaraba a kyale mutum yayi barci ma cikin kwanciyar hankali ma ba za ayi ba?" amsar Anty kenan. Cikin daga murya yace "am fed up with ur cruel habits Mubeenah, dole ki gyara halinki idan kuma ba haka ba....!" katse shi tayi ta hanyar sakin dariya, ".... Idan ba haka ba zaka kara aure? Go ahead then, ko a da can ma hakan bai dame ni ba Ibrahim balle yanzun ka gane? Allah yasa matan duniyar nan zaka auro, I wouldn't give a damn! Now can u get out please? Ina so inyi barci!!" ina jiyo hucin daya dinga fitarwa a fusace kamar zuciyar shi zata fito waje, cikin wani irin threatening murya yace "zan shayar dake ruwan mamaki kuwa Mubeenah" cikin muryar ko-in-kula, I bet she was shrugging her shoulder up ma lokacin kila tace "m looking forward to it" daga nan naji ana kokarin fitowa daga dakin nata, a sukwane na fada bayan labule tare da saka yatsa na danne saitin wajen dake samar da hasken flashlight a wayata. Yana fitowa ya maida kafar dakin da karfi ya rufe ji kake 6ammmmm!!! Ina jin lokacin daya bude kofar dakinshi ya shiga, sai dana bashi kyawawan mintuna goma kafin na fito daga maboyata na fada daki ruwan da ban sha ba kenan na koma kan gado na kwanta xuciyata fal cike da tausayin ma'auratan. Me ke damun Rayuwar Auren su ne haka??

Am sorry for the late update, jiya through out a kwance na yini ban jin dadin jikina ne sam. Yau din ma ta maza ce nayi shi yasa wallahi. Just kara hakuri dani pa!

*♡Jeedderh♡*

[12/8, 7:26 AM] ‪+234 816 390 1222‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*20*


*Sakon taya murna zuwa ga marubuciya MAIMUNA SANI BELI na lashe gasar HIKAYATA da BBC ta hada na gajerun labarai. Allah ya kara miki kaifin basira*



"I heard that You are leaving the lab at the end of this week koh?" cewar Mrs Smith Head of Lab dinmu. Na gyada kaina nace "yes ma'am" tace "bayan kin gama Program din me zaki yi? Zaki wuce da HND ne?" nace "I'm not very sure ma, I'm thinking of filling D E form" tace "ina fata a nan BUK ne?" na girgiza kaina da sauri, "no ma'am, ABU Zaria ne" ta kalleni tana murmushi, "why?" na sadda kaina kasa kawai, me zan ce? Nace "maa nafi son Zaria ne sabida mun fi kusa dasu, bana son yin nesa da gida" ....ina so nayi nesa da Abbu da Iyalan sa Saboda ina jin tsoron abinda zan janyowa kaina, naso in kara da gaya mata haka sai dai nayi shiru. Ta gyada kai, tayi signing din takardar dana bata ta miko min nasa hannu biyu na amsa, tace "am wishing you all the best Nafeesah" nace "thanks ma'am" na fita.
Mun gama ayyukan mu na ranar muna zaune a cikin lab din muna hira ni da Ramlah, su Khaleesat tuni suka gama nasu IT din sati biyu da suka wuce. Nayi scrolling down ta cikin facebook account dina, anan na ci karo da status din da Muneer yayi mintuna biyar da suka wuce, "Soon.....!" na dan rausayar da kaina cike da alamun tambaya, me yake nufi? Na danna button din like. Ramlah ta kalle ni tana tabe baki, "ni har na rasa abinda zan fada miki game da Muneer wallahi. Ki kyale gayen nan haka nan kin ki kiji, yanxu har ta account din shi kike bi kina stalking din shi?" na yamutsa fuska, "stalking kuma Ramlah sai kace wata mara aikin yi? Kawai ina chatting ne na ci karo da status dinshi nayi liking, shine nayi stalking saboda Allah?" tace "ni dake da marar aikin yi duk daya nake ganin ku wallahi, wani mara aikin yi din ma ya fiki Nafeesah. Kin makalewa namiji daya kamar wata wadda bata da masoya, da girman ki da class din ki da komi. Allah ban taba ganin mutum marar fahimta ba irin ki ban sani ba ko duk sangarta ce ko kuwa? Amma......" "For Heaven's sake Ramlah!!" na katse ta a fusace har ina hadawa da buga hannuna akan bench, "this is my life kin gane? You have no right da zaki zauna kina lecturing dina akan abinda yake feeling dina ne kina ji? Baki son Muneer fine!! Ni da nake son shi sai ki bar ni inyi ta son nashi please!!" cike da mamaki ta kalleni, ta daga baki zata yi magana nayi saurin tashi na bar mata wajen. Yinin ranar haka nan muka karasa shi cikin kuncin rai su kan su en lab dinmu sun fahimci akwai abinda ke faruwa damu don basu saba ganin mu a haka ba, we are always cheerful koda yaushe muna tare muna hirar mu mai burgewa muna tsokanar juna amma ranar kowa tashi yake yi a cikin lab din, ina kallon Ramlah sosai ranta ya baci don har sai data share hawaye, jikina yayi sanyi sosai, ni kaina nasan Ramlah bata cancanci abinda na fada mata dazu ba, Raina ne ya 6aci sosai, so many annoying thoughts were running through my mind a lokacin, zan iya cewa Ramlah Sara ne tayi akan ga6a na sauke fushi da takaicin wasu a kanta. Karfe biyu tana cika na suri jakar hannuna na musu sallama na fita, a bakin kofar na tsaya, bayan kamar minti goma Ramlah ta fito. Da sauri na tari gabanta, "am sorry babe, I shouldn't have said what I said earlier.... M sorry, really" ta kauce daga gabana, "me zan ce miki Nafeesah? Ban cancanci in miki magana bama balle inyi intruding din personal life dinki ba, m sorry!" nasan cewa magana ce ta gaya min, naji kunya ta kama ni a lokacin, A taron mu da Ramlah I must have hurt her feelings da maganganun dana fada mata, bata cancance su ba ko kadan. Da sauri na kara tarar gabanta tare da riko hannunta, "look Ramlah! Wallahi I really didn't meant what I said da gaske nake, ni kaina abun yana damuna Ramlah. I'm trying, ina kokarin ganin cewa nayi yaki da son Muneer a cikin raina amma na kasa. No matter how hard I try, na kasa shi yasa nake jin haushin kaina nima, ina jin takaicin abun nima Ramlah har na fiki sai dai ya zan yi? Zuciya ta taki aminta da hakan ban san ya zanyi ba Ramlah...." zuciyata ta karye na kasa cigaba da maganar, idanuna suka yi jawur, lebena na ciza ina kokarin tsayar da hawayen dake kokarin xubo min. Ramlah ta dafa hannuna fuskarta cike da damuwa, "m sorry too Nafee. Bana jin dadin abinda yake yi miki ne ko kadan, it's hurting me. I love you babe, duk abinda zai bata ranki ina kin shi har cikin raina, na ga alamun baki son kyale shi bayan nasan cewa yana bata miki rai, I didn't know, ki yafe min" rungumeta nayi ina tapping bayanta, "I love you too Ramlah, m sorry too. I shouted at you" ta rungume ni itama, mun dan jima kafin muka saki juna, ta kalleni fuskarta da wani expression dana kasa ganewa, ta sake cewa "m sorry Nafeesah" nace "what for again? Idan maganar Muneer ce ta wuce don Allah mu daina yin ta haka nan" ta gyada kai. Muka samu waje muka zauna muna er hirar mu har Malam Bala yazo na mata sallama na tafi tana daga min hannu, taren mu da Ramlah kenan!.

Shirye-shiryen komawa gida nake babu kama hannun yaro, ganin abun nake yi kamar a mafarki. Kamar yau ne fa nake shirin tahowa Kano gashi har watanni shida sun wuce, na fada a cikin raina ina karewa akwatuna na kallo wadanda na gama shirya kayana a ciki. Hafsy ta leko dakin, gani na a tsaye ina karewa dakin kallo ta shigo ciki tare da maida kofar ta rufe, gefen gado ta samu ta zauna ta kalleni a marairaice, "yanxu Yaya Nafee gobe zaki tafi ba zaki kara mana ko kwana daya bane?" na zaro ido ina kallonta, "Lallai ma Pretty ashe baki tausayi na, ko don ke kina gaban Mom and Dad dinki ne shi yasa? Nima ina so in je in gansu saboda nayi kewar su sosai" ta turo baki, "to ba kina zuwa kina ganin su ba duk weekend?" nace "dat's a different magana ai, so nake in koma kusa dasu gabadaya kin gane?" tayi rau-rau da idanu sai ga hawaye shar-shar, da sauri na zauna a gefenta na fara lallashinta har tayi shiru, nace "haba mana da girman ki kike kuka? Kar ki damu zan dinga zuwa kuma ina muku weekend kinji?" da sauri ta dago kanta ta kalleni, "da gaske?" na gyada mata kai ina murmushi, sai dai daga can kasan zuciyata nasan cewa yaudarar ta kawai nake yi don ta warware, ina fata idan na saka kafa na bar gidan Abbu ya zama fita ce ta har abada, ko a mafarki bana fatan in sake komawa. Da biyu nake gaggawar in koma gaban su Daddy na, ina so inyi nisa da Abbu da gaggawa, he has started putting some effects on me wanda duk iya kokarina nason ganin na hana su affecting dina abun ya ci tura, shi yasa nake so in bar gidan as soon as possible kafin abubuwan su fi karfina. Hira na fara jan ta dashi ina tsokanar ta, nan da nan ta ware ta fara dariya, tare da ita muka cigaba da shirye shirye, na fidda kaya masu dama da wasu daga cikin kayan kwalliyata na ba Harira tayi ta godiya kuwa. Ana kiran magriba muka bar shirin muka yi sallah, Hafsy ta dauko littafan ta na taya ta muka yi bitar karatu har aka kira Ishai'i muka yi, muka fita wajen cin abinci. Muna gamawa muka koma kan kujeru muna kallo, duk da kallon daga ni sai Hafsy ne su Abdullahi wasan su suke yi abin su. Abbu da Anty Mubeenah suka yi sallama suka shigo falon, muka musu sannu da zuwa duk suka wuce dakinsu da alamun kayan jikinsu zasu canza. Anty ce ta fara fitowa, kamar yadda nayi zato ta canza kayan jikinta zuwa doguwar riga, Kai tsaye kan dinning ta wuce ta zauna. Ba a jima ba Abbu yayi joining dinta shima ya canza kaya zuwa na barci, riga da wando na M$S, muka cigaba da kallonmu har suka gama cin abincin suka dawo inda muke suka zauna. Hirar su suka fara yi su da 'ya'yansu, Anty tace "Nafeesah gobe sai tafiya gida ko?" nayi murmushi tare da gyada kai, tace "eyyah! Zamu yi kewar ki ko don dadadan girke-girken ki" Abbu ya jefa mata wani irin kallo, Qaseem yace "Yaya Nafee amma zaki dinga kawo mana ziyara koh?" nace sosai ma. Hafsy tayi caraf tace "anan ma zata dinga mana weekend koh?" na kalli su Abdullahi da suke kallona cikin zakuwa da son jin amsa ta, murmushi nayi nace "ehh" a hankali. Suka dauki shewa suna ihun murna, kallon su kawai nayi ina murmushi. Karfe goma tana yi na tashi na musu sai da safe, Hafsy ta mike da sauri ta biyo bayana, ina ji Abbu ya tambayeta, "pretty ina zuwa?" ta juya tace "ni dai a wajen Yaya Nafee zan kwana yau" yace "a'ah zo ki wuce dakin ki, zaki takura mata" aikuwa ta bare baki zata fara kuka, nayi saurin janyota jikina, "babu komi Abbu, taho muje kinji?" ta ware hakora tana dariya, naja hannunta muka shiga daki. Brush muka yi muka fito, nace ta zauna bari inje in dauko mata kayan barci, na fita. Falon babu kowa duk sun tafi dakinsu, naje na dauko mata kayan. Na fito kenan daidai Abbu yana fitowa daga dakinshi, ya kalleni, da sauri na sadda kaina kasa nayi niyar wuce shi da sauri, cikin wata irin murya da ban taba jin ta a gun Abbu ba naji yace "Nafeesah!" na tsaya cak duk da ba haka naso in yi ba, so nayi in yi kamar ban ji ya kira ni ba in shige dakina wanda bai fi taku takwas daga inda nake tsaye ba, but damn me and my legs. Ya tako a hankali har inda nake tsaye, zuciyata bugawa take yi da sauri har naji tsoron kar ya jiyo sautin, shiru ya biyo baya na fiye da minti biyu, jikina ya bani cewa kallona yake yi don haka naki daga fuskata balle in kalle shi. Yayi ajiyar numfashi a hankali, yace muryar shi kasa-kasa, "are you sure Pretty ba zata takura miki ba?" na tabbata ko nayi magana ma da kyar muryata ta fita don haka na gyada mishi kai kawai. Yace "umh.... Da gaske zaki dinga zuwar mana weekend?" nan ma kaina kawai na iya gyadawa. Yace "good! I'm happy to hear that. Je ki kwanta sai da safe" da sauri na wuce har kafafuna suna hardewa na fada dakin kamar wadda aka jefa, Hafsy ta daga kai ta kalleni da sauri, murmushi na sakar mata na mika mata kayan barcin ta saka nima na sa nawa, wando ne iya gwiwa don nasan ba fita zan sake yi ba da rigar vest mai budadden gaba zan iya cewa Rabin kirjina a waje yake. Na mana addu'ar kwanciya barci ni da Hafsy muka shafa, na janyo bargo na rufe mu tare da kashe mana wuta. Ban sani ba tsautsayi ne ko kuwa Kaddara ya saka ni janyo wayata na shiga social media?? Well, that's the worst moment I've regretted the most in my life!!!.





*♡Jeedderh♡*
[12/8, 7:29 AM] ‪+234 816 390 1222‬: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*




*21*




Ban san lokacin dana saki wayar hannuna akan carpet din dakin ba, na jingina bayana da allon gado ina kallon wayar kamar wadda aka turo mata da ranar mutuwar ta, hoton Muneer ne shi da wata tsaleliyar yarinya ya dora a shafin shi na instagram, a kasan hoton naga yasa *Finally Engaged Alhamdulillah..., getting married in the next 6 months!*. Ban taba sanin cewa numfashin mutum ya kan dauke, zuciyar mutum ta daina bugawa ba alhalin mutum na raye sai a lokacin, lokacin da nayi kokarin warto numfashi na sai gani a tsakiyar carpet din dakin dafe da kirjina, Zufa ta shiga keto min ta ko'ina, jikina rawa yake yi kamar mazari. Allah kadai Yasan iya adadin lokutan dana kwashe cikin wannan hali. Kamar wadda aka zungura nayi zumbur na tashi tare da daukar wayata, ban damu da cewa lokacin karfe sha daya da rabi bane, abinda na sani kawai shine ina so inji daga bakin Muneer, cewa da gaske aure zai yi, wata zai aura ba ni ba. Na kalli Hafsy da take barcinta cikin natsuwa bana so in katse mata barcinta saboda nasan a yadda nake ji na ba zan taba yin kasa da muryata ba, ji nake kamar in bude baki inyi ta kwarara ihu har sai mutanen Duniya sun ji halin da nake ciki. Falo na fita, wutar falon a kashe take duk da haka akwai haske wanda kwayayen waje suka samar. Number Muneer na danna, take ta shiga ta fara kara. Kai kawo nake a tsakiyar falon na kasa zaune na kasa tsaye har tayi karan ta gama bai dauka ba, na sake danna mishi wani kiran, sai dana jera mishi missed calls takwas ina kirgawa ban kuma yi niyar dainawa ba, nayi imani a lokacin idan zai kwana bai daga kiran ba nima haka zan kwana ina kiran shi ba tare da gajiyawa ba. Ana tara ne ya daga cikin muryar barci, "hello Nafeesah lafiya??" sai na ma rasa abinda zan ce mishi, wani irin kuka yake shirin kufce min na datse hakorana ina maida shi ta karfi, Muneer bai kai wannan matsayin ba kuma, kuka akan namiji? Har abada! Ya sake cewa "Nafeesah, are you ok??" cikin gritted teeth nace "Muneer, you evil bastard!!" shiru ya biyo baya da alamun he was in shock, I couldn't suppressed my anger shi yasa, "what?! Excuse me??!" ya fada shockingly, cikin rawar murya mai cike da bacin rai nace "You betrayed me Muneer!! Kayi wasa da zuciyata ka maida ni sakara, abinda ka mun ka kyauta kenan? Kana ganin hakan dacewa ne?" yace "me kike fada ne haka Nafeesah? Me na miki? Ta yaya na yaudare ki??" cikin karaji nace "kasan ina son ka Muneer!! You know it all along amma what? Aure?? Baka yi tunanin halin da zan shiga ba?" yace "I never Loved you Nafeesah!! Saboda kawai kina so na sai kiyi tunanin zan tauye kaina da rayuwata saboda ke? Why would I?? I mean ban taba cewa ina sonki ba, in fact, ban taba nuna signs na so a gare ki ba ko na taba?" kai na nake girgizawa cikin tsananin bacin rai da bakin ciki, ni Namiji yake gayawa baya so na da Babbar murya!! Muryata ta fara rawa, nace "ka cuce ni Muneer! Kaki ka so ni ka hana ni inso wadanda ke so na, you are one big devilish bastard on earth!" yace "enough Nafeesah! I've heard enough please, bani nace ki so ni ba, ban taba rokon ki akan ki so ni ba don haka you have no right da zaki saka ni a gaba cikin daren nan kina zagina da tuhumata akan laifin da ban sani ba kin gane?" na gyada kaina a hankali kamar wadda take gaban shi, nace "you are right Muneer!! You are right!! Laifina ne, ni naki yarda inji maganar mutane da kashedin da suke min, duk a tunanina kana so na ashe yaudarar kaina kawai nake yi..... Sai da safe kawai, sai dai I'm not sorry about waking u up, ina maka fatan uncomfortable sleep through out the night!!" na kashe wayata gaba daya. Zubewa nayi a kasan falon saboda yadda kafafuna suka yi sanyi, zuciyana kuna take yi kamar wadda ake soyawa. Duk yadda naso akan in daure kukan da yake tuko ni kasawa nayi, gani nayi idan

Please Login or Register in order to submit comment